bar ba, ai ba za ka hana ni nema ba. Kana ganin iyayena basu da shi mahaifiyata tana fama da jinya."
"Ni na ɗora mata? Tun da bani bane sai ki shafa mini lafiya. Ko da yake cigaba da karatun ma yana ƙila wa ƙala, tun da ɗan iya da ya sa ya ki shi ma ya kasa biya."
Gabanta ne ya faɗi tuna haka wanda hakan hawaye ya wanke mata fuska.
"Allah zai taimaka mini ba zai barni ba, tun da ya ga ina son karatun."
"Aci gaba in iska na hura wuta." Ya ce sai kuma ya kalleta ya ce,"Nasreen, za ki bani hakkinsa ko na je titi na nema? Tun da ga mata nan masu kyau waɗanda suka fiki."
"Ka je ba zan bayar ba wannan kai da Allah."
"Ke kuma wutarki daban ce, don in har Ina sama kina can ƙasa-ƙasa. Kina sane da Allah da Mala'iku suna tsine miki. Ki rinƙa buɗe murya kina karatun qur'ani ke a dole malama. Ƙiri-kiri ko bancin kirki ba kya bari na yi, amma in har na kawo buƙata ta sai ki koma kamar ba musulma ba."
Kallonsa ta yi cikin tsananin mamaki jina bin da yake faɗi."Dama ai ba ka nuna ilmin ka sai anan gurin, ni kuma ka ji na rantse in har ba za ka rinƙa yin soyayya ba, wallahi ba zan lamunta ba."
"Kin amince na kunna miki mu kalla sannan mu yi soyayyar? Domin ni sha'awarki kwata-kwata ba na ji."
"Allah ya kyauta! Ubangiji ya tsare ni da kallon surar wasu kai ma ina maka addu'ar ka daina domin babu kyau.
"Ashe jiki zai yi tsami." Ya ce tare da sanya hannunsa ya haɗata da jikinsa da ƙarfi.
Hannu ta sanya ta ture shi ta sanya kuka.
"Nasreen zan ci ubanki wallahi zan miki dukan tsiya a dakin nan!"
"Don Allah Abba, karka dake ta." Ya ji muryar Hairan tana faɗin haka.
Tsaki ya ja yana kallonta cikin takaici.
"Kina ganin abin da kike mini ko? Ba gaya miki za ki rinƙa kwana a ɗakina, amma wallahi ba da yarannan ba. In kin amince ki tashi mu je."
"Ni kuma ba zan bar yarana ba ƙanana saboda kai. Yarannan fa 'ya'yanka ne ba agola na taho da su ba."
"Ina ruwana ko daga jiki a suka fito. Ni wallahi yarannan suna ɗaya daga cikin abin da yasa na ƙara tsanarki. Duka shekararmu huɗu da aure, amma kin tara mini 'ya'ya biyu. Kin ji na rantse miki wallahi na ganki da ciki sai dai ki haifa a gidanku, tun da kin ƙi yin tsarin iyali."
"Ni ba zan kashe kaina ba, ai akwai na maza ka je ka yi mana. Sai ni? Da ba ni da gata, kuma 'ya'ya rahama ne wani na nema da kuɗin da bai samu ba."
"Ki je ki basu duk na yafe musu, ba ni buƙata saboda ina cikin tashen ƙuruciyata, ba za ki tara mini 'ya'ya ba ki tsigar da ni."
"Ka ji tsoron Allah kai ka ganni kana so ba tushe aka yi maka ni ba."
"Na yi dana sani saboda ba ki dace da ni ba. Sam da na san haka kike da ƙafiya da taurin kai babu abin da zai sanya na siyo ciwon kai na kawo gidana, kuma wallahi in har ba ki canza ba, kina gab da shiga cikin layin zawarawa don ba zan ɗauki iskanci ba."
Gabanta ne jin abin da ya ce, sai ta yi shiru can kuma cikin muryar kuka ta ce,"Allah shi ne gatana."
"Ni kuma ki ce sheɗan ne gatana in kin so." Ya ce tare da ɗaukar ta can ya yi ɗakinsa.
Tana kuka tana dukan ƙirjin shi, amma bai kula ba sai da ya biya buƙatar ta kamar yadda ya saba, sannan ya koma ya kwanta yana sauke numfashi.
"Allah ya saka mini ni da 'ya'yana."
"Ki fito kai tsaye ki zage ni." Ya ce tare da rufe idanunsa sai bacci.
Ita kuwa ta kasa yin bacci tana jin yadda Musaddik ya ke kuka yana faɗin,"Umma, fo." Wanda hankalinta ya ƙara tashi amma babu yadda za ta yi.Hankalinta ya kwanta jin Hairan ta sanya shi a fon.Miƙewa ta yi ta, shiga bayi ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta daura tawul ɗin da ta fito.
Ganin ya yi bacci yana jan rago ya sanya ta lallaɓa ta ɗaya kansa ta ɗauki key ɗin ɗakin.Buɗewa ta yi ta fice tana takaicin rayuwarsa, don ta san da kyar ya yi wankan sai gobe in zai fita aiki ya yi.
Daki ta koma ta gyara musu kwanciya, ta mike tare da sanya rigar sallarsa ta shinfiɗa dadduma.
Sallah ta fara yi. Raka'a biyu ta yi bayan ta isar sai ta mayar da kanta ta rinƙa fadin,"La'ilaha illa anya subuhanaka.inni kuntu minaz zzalimin." Har sau arba'in da ɗaya, sannan ta yi wa Allah kirari tana kuka, da ya shirya mata mijinta ya zaunar da su lafiya.
Haƙiƙa Ummar Faruk miji ne na nuna wa tsara. Yana da kyau daidai shi. Dogo ne amma ba shi da haske sosai. Sannan yana da jiki na maza hali ne kawai ba shi da shi. Sai shegen son 'yan mata duk da cewar yana da maƙo, amma yana sakin ma 'yan matansa.
Ba ta tashi daga daddumar ba, sai da ta aka kira sallar asuba, sannan ta miƙe ta yi Raka'atul fijr ta sallame tare da yin sallar asuba.
"Umma na tashi." Hairan ta ce tana miƙa da salati.
"Good girl, then go and brush your teeth."
"Ok, Umma." Ta ce tare da wucewa cikin bayin.
Bayan ta yi brush ta yi alwala, sannan ta fito ta shinfiɗa karamar daddumarta ta yi sallah.
"Ummu, good morning?"
"Morning baby how are you?" Ta ce mata tare da rungume ta.
"Am fine Umma."
"Good, mu koma bacci kafin gari ya waye ina da lecture zuwa ten, kuma test za mu yi, ina shirya na kaiku school sai na dawo na gyara gidan na tafi ko?"
"To umma, I wish you all the best."
"Thanks babyna. Allah ya yi wa rayuwarmu albarka." Ta ce tana shafa ka kansu tare da tofa musu addu'a.
Yaran sune duniyarta, a dalilin su take rayuwa a gidan ubansa, domin ta san matuƙar ta rabu da mahaifinsu rayuwarsu da na ta sun shiga garari. Wannan dalilin ya sanya ta ke jure duk ɗaci da uƙubar zaman gidan ubansa don ta tallafi rayuwarsu. Tana ƙoƙarin ba su tarbiyya ta gari, a yadda take son su yi karatun boko ko Hausa ba ta cika yi musu ba. Sannan tana kula da karatun Muhammadiya ta su. Da kyar da taimakon Allah ta sanya mahaifiyar Faruk, ta tilasta shi ya sa ya su a makarantar boko mai tsada da islamiya da hadda. Ga shi yarinyar kwanyarta na ja, don tana da wayo wani lokacin maganar da take yi ya girmi shekarunta. Kuma duka shekararta uku.
"Umma, zan je na gaida Abba." Ta ji yarinyar tana faɗi tare da ƙoƙarin sauka daga gadon.
"Karki damu ya yi sallah, ya kwanta kin san in ya yi sallah sai tara yake tashi." Ta yi mata ƙaryata hakan tare da mayar da ita ta kwanta.
"Mu yi bacci in muka tashi sai ki gaishe shi."
"Ok,".Ta ce tare da kwanciya.
Ƙarfe baccin awa ɗaya ta yi, ta tashi dama akwai wuta ta sanya ruwa a kettle. Ɗaukar ruwan ta yi ta yi musu wanka sannan ta shirya su.
Ragowar abincin ta ɗumama ta saka mata a kula sannan ta zuba mata ta ci.
"Umma, don Allah ki daina sa mini ɗumame lalacewa ya ke yi kafin na ci. Kuma 'yan ajinmu bobo da biskit suke zuwa da shi."
"Ba na gaya miki ki daina sa ido kan abin da suka zo da shi ba?"
"Sorry Umma."
"Good girl. Na ce miki ina gama makaranta na samu aiki zan rinƙa siya miki duk abin da kike so."
"To, Umma Allah ya taimaka ya sa ki gana kuma ki samu aikin."
"Amin." Ta ce tana kallonta tana murmushi.
"Bari na rinƙa sa miki abincin a roba kar ya lalace, sannan kuma mu je shagon Dauda na siya miki biskit guda ɗaya."
Ɗaya mata kanta ta yi sannan ta ci gaba da cin abincin.
Kallonta take yi cikin tausaya wa, ganin mahaifinta na da halin da zai siya nata duk abin da take so, amma tsabar maƙonsa da son abin duniya, tare da rashin girmama yaran ya sanya shi ƙin siya mata.
Kasancewar babu wani tafiya tsakanin gidansu, da makarantar ba ta jima ba suka isa.
Miƙa mata biskit ta yi tare da kama hannunta." Ga shi ko kawo jakarki na sanya miki. Ki ci kin ji sam kar ki roki kowa, in kuma kika yi haka aljanuna za su faɗa mini."
"To ba zan riƙa ba ai na daina tun da kika ce babu kyau."
"Yauwa, Allah ya yi miki albarka ya ba ki ilmi mai amfani." Ta karashe maganar tana ɗaga mata hannu ganin ta shige cikin makarantar.
Bayan ta dawo a gauguace ta gyara gidan ta shiga wanka. Ba ta jima ba ta fito ta sanya doguwar rigarta tare da rolling ɗin ɗankwalin abayar ta dauki jakarta da littafanta.
Ɗakinsa ta tura ta shiga yana zaune kan sallaya da waya a hannunsa da alama lokacin ya yi sallah, don ko tashi daga gurin bai yi ba. Zuciyarta ta ɓaci ganin tsadadden murmushi da yake yi a fuskarsa, amma sallamar da ta yi ya canza fuskar daga farinciki zuwa ɓaci rai.
"Abban Hairan, ina kwana?" Ta furta cikin sanyi ta tare da danna kishinta.
Harara ya watsa mata sannan ya ci gaba da danna wayarsa tuna abin da ya faru juya.
"Da ban kwana ba za ki ganni?"
Dariya ce ta suɓuce mata, ta san dama yana da shegen riƙo shi zai ɓata maka, kuma ya riƙe mutum sai su yi sati yana jin haushinta.
"Zan wuce school."
"Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta.
"WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 3
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Zan wuce school."
"Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta.
"A'a, Allah ya ba ka haƙuri." Ta furta tana ƙoƙarin juyawa.
Tsaki ya yi tare da gyaran murya."Umma ta gaida ashsha. Kin san dai ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba, don ban aike ki ba. Shegen baƙinciki da son gogayya da ni, ya sanya kika nace karatun. In kika gama digirin sai ki ɗaura da masters sannan Phd kin ga mun zama ɗaya."
Ba ta ce masa komai ba ta miƙe za ta tafi.
"Nufin ki ba za ki haɗa mini breakfast ba za ki tafi? Kin san dai ba zan ci wannan ɗan iskan abincin, da kika cika gishiri da barkono ba."
"Sai mu da ba mu da gata." Ta ce a ranta amma a fili narai-narai ta yi da fuska.
"Haba Abban Hairan na yi matuƙar latti fa. Kuma in ban da tsatsuba yaushe rabon da ka yi breakfast a gidan nan?"
"Saboda ban da ra'ayi yau kuma yunwa nake ji, saboda jiya don mugunta abincin da na ci duk kin ƙwaƙule ni."
Harararsa ta yi jin abin da ya ce sai ta kalli agogo.
"Don Allah ka yi haƙuri ka je ka ci a inda ka saba ci, na riga na yi latti, kuma test na ke da shi."
"Allah ya sanya exam za ki zana wallahi sai kin dafa mini abinci. Ki ma godewa Allah indomie ne, kar kuma ki ja na ce taliya ko shinkafa."
Shiru kawai ta yi ta tsaya tana kallonsa don ta san zai iya.
"Ga shi." Ya ɗauki guda uku ya miƙa mata.
"Ki hanzarta ni ma zan yi latti."
Banza ta yi da shi ta juya tana ƙunkunai."Wallahi kika zage ni saina naɗa miki na jaki kuma babu inda za ki. Dama kwana biyu ban more fata ba." Ya ce tare da komawa ya zauna wannan karon da ya ɗauki wayar kiranta ya yi suna bidiyo call.
Cikin sauri ta kunna wutar, sannan ta zuba ruwan zafi Allah ya so ta tana da shi a fulas. Da sauri ta jajjaga sauran kayan miyan da ta rage jiya. Burinta ta gama kafin lokacin ya ƙure. Bayan ta gama, ta rage kaɗan ta zuba masa sauran don ta san in ta iba da yawa, zai iya mata tijara.
"Ga shi." Ta ce tana ƙoƙarin fita.
"Ina za ki?"
Ya yi mata tambayar tare da miƙewa, ya ƙaraso inda ta ije abincin ba tare da ya kashe wayar ba.
Ranta ya ɓaci hawaye suka zubo mata a fuskarta. Kauda kanta ta yi, daidai lokacin da ya kalli wacce suke wayar ya ce mata.
"Baby, zan kira ki I love yo..."
Maganar ta katse sakamakon ganinta da ya yi ta nufi gurin wayar cikin huci.
"Na gaji Faruk! Na gaji da tozarci da wulaƙanta ni da kake yi, domin na kasa gane mata ko baiwa ka ɗauke ni. Ba ni da 'yanci da ƙimar da za ka bari ka rinƙa waya da sheɗanun 'yan matanka?"
"Matar da zan aura kike kira sheɗaniya?"
"Wallahi in da abin da yafi sheɗaniya zan kirata. A cikin gidana kake waya da ita ki kunya ta ba ka ji. Ban isa na ga dariyar ka ba, sai in kana waya da wasu matan. Ni ma fa ina da haƙƙi a kanka kamar yadda kake iƙirarin kana da shi a kaina."
"Ke dai na lura wallahi baƙicikin zan yi ajalinki. Saboda kin ganta yar duma-duma kalar madara shi ne kake tada hankalinki. To ni dama mai zan janyo mini na je na ƙara ɗauki irinki? Ina ciyar dake ana zargina ina barin ki da yunwa. Kalle ki fa Nasreen kullum sai ƙara tsukewa kike kina komawa wata tsohuwa, saboda fitinar da kika sanya a kanki. Ki kula karki jawo abin da zai sanya na tura ki gidanku, kin ga wannan ya'yan na ki da yake tada jijiyan wuya ina barin ki da yunwa, sai na barki in gani in zai iya cida ke. Saboda baƙin ciki kamar jaka haka kike."
Wasu irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska. Ji ta yi kamar ta mutu."Ni kake kira haka?"
"Ƙarya na yi in aka dafa taliya ɗaya tana kwana ta wuni?"
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Allah ka jarabace ni da mijin da bai san darajar mace ba."
"Ni zan roƙa Allah ya kawo mini ɗauki da ya haɗa ni da mace bagidajiya mara wayewa. Sai aikin ɗaukar jaka da sunan an tafi makaranta. Haka kika ga matan jami'a suna yi? Ko irin shigar da kike yi suke yi? Ba kya ganin mata masu kyau da zubi da tsarin da suke sace zuciyar maza?"
"Kana siyen mini kayan ne Faruk? Tun da na shigo cikin gidanka yaushe ka siya mini sutura? Ko haihuwa na yi a gidanka turmi ɗaya ke haɗani da kai. Su kuwa maza na yi musu hidima. Ko fa gida ba ka iya siya mini ka ji tsoron Allah da ranar da Ubangiji zai tsayar da mu don yin hisabi."
"Ke ma ki ji tsoron Allah ranar da Allah zai tuhume ki bisa kasa ɗauke mini ido da kika kasa yi ga matan waje. Kullum sai dai na yi ta raba idanuna kallon abubuwa a gurin matan waje, amma matata ba ta da maraba da tsinke."
"Wayyo Allahna!" Ta ce tare da zubewa a ƙasa tana kuka.
"Ki mutu gaskiya ce ɗaci gareta kuma ba zan dai na gaya miki. Sai dai ta kashe ki." Ya furta yana saka lomar abinci a bakinsa.
Kallonta kawai ta yi sai ta miƙa tsam ta saba jakarta ganin ta yi latti.
Ɗaukar Musaddik ta yi za ta fita ba tare da ta yi masa magana, daidai lokacin da ya saki tsaki.
"Kuma wallahi kika daɗe ba ki dawo ba har inda kike zan biyo ki na tozarta ki. In aka ci amanar Allah ya isa ban yafe ba."
Da sauri ta juyo yayin da hawayen ta suka ci gaba da zuba, sai kuma ta fice ba tare da ta ce komai ba. Gurin famfo ta je ta buɗe ta wanke fuskarta da wasu hawayen suke zuba.
"Umma, kuka?" Musaddik ya ce yana goge mata hawayen da ya haɗe da ruwan fuska.
Sai da ta kai bakin get ɗin gidan ta tsaya ta ciro wayarta da duk ta ragwargwaje. Da kyar ta samu ta numbata domin kashe kanta take yi. Ɓacin assignment da take yi da ita, da tuni ta yi jifa da ita tun kafin ta yi ajalinta.
Numbar Ahmad ta laluba ta yi masa peep wanda ko minti ɗaya ba a yi ba, ya kira ta.
"Ya Ahmad!" Sai kawai ta fashe da kuka.
Daga can ɓangaren ya ja ajiyar zuciya, cikin damuwa yana jin yadda kukan yake damunsa.
"Nasreen!"
"Na'am." Ta amsa cikin sheshsheƙar kuka.
"Kina ji na ko? Kiyi haƙuri har yau ita ce kalmar da zan rinƙa baki. Na san halin da kike ciki, amma wallahi kin ji na rantse miki zaman gidanki yafi miki kwanciyar hankali. Ki karbi jarrabawar aurenki. Ubangiji yana sane dake. Ni kaina ina cikin damuwa. Jiya wallahi ba mu yi bacci ba, saboda ciwon Mama ya tashi. Yanzu haka na sanya Zainab ta gyara ta zamu wuce asibiti, kuma Baba ko ƙwandala bai bamu ba, tun da ya shigo ya yi mata sannu ya fice daga gidan."
Damuwarta ta ƙara yawa har ta ji dama ba ta kira shi ba.
"Yaya, Faruk baiwa ya ɗauke ni ba mata ba. Ina cikin damuw.."
"Hakurin da kike yi ki ƙara, yanxu zan sanya miki dubu ɗaya na san za ta ɗan yi miki kuɗin mota da ko gurasa ki ci a makaranta. Za mu wuce da Mama asibitin in an kwantar damu zan kira ki, sai ki taho in kuma dawowa mu ka yi duk zan gaya miki."
"Don Allah ka bani ita na gaishe da ita."
"Ba za ta iya ɗaga waya ba. Ki je makarantar Allah ya tsare."
"To Yaya Ahmad, ina dawo zan biyo, kuma ka bar kuɗin ina da sauran ɗari biyar, da ka bani ranar Monday na yi amfani da sauran na ije. Ka je ka kula da ita, zan tafi a mashin tun da na yi latti ina dawo sai na tako."
"Karki damu juya na yi aikii na samu kudi, saboda don ciwon Mama ya tashi dubu biyar zan tura miki."
Tausayinsa ya kamata ganin yadda yake ɗawainiya da ita." Na gode Allah ya ƙara budi ya biya maka buƙatunka."
"Amin ƙanwata." Fatana ki ci gaba da fito da sakamako mai kyau ki samu aiki ki tallabi rayuwarki."
"Da kuma na bukatun da na Mama da sauran ƙannina."
"Ina sha Allahu." Ya ce mata yana murmushi tare da kashe wayar.
Maganar da ta yi da shi, ya sa ya ta ji ɗan dama sama-sama, har ta iya taran acaɓa ta hau zuwa bakin get ɗin makarantar.
Wani ƙaton tangamemen falo ne wanda yake ɗauke da kaya na alfarma. Tabbas falon ya cancanci waɗannan kaya da aka shake falon dashi duba ga yadda ya tsare an kashe dukiya tamkar aljannar duniya.
Wata farar mace siriya take zaune da 'yarta ɗaya wacce take kan cinyarsa tana bacci.
Kyakkyawar matar waya ce a hannunta tana chatting, yayin da fuskarta ke bayyanar da wani irin tsantsan annuri, wanda zai tabbatar maka da wanda take chatting ɗin da shi mutum ne mai daraja da ƙima a gurinta. Darajarsa da ta wuce darajar gwal da Dirhami.
Murmushi ta yi, tare da amsa kiran da ya yi mata domin iya chatting ɗin ba zai gamsar da zuciyoyinsu ba. Sun dade suna waya tamkar ba za su rabo ba, sannan daga bisani suka yi sallama bayan ta yi masa kiss din da iya ƙwaƙwata ba zan iya lissafawa ba.
Kashe wayar ta yi sannan ta shiga cikin galary ta yi ta kallon hotunansa, duk da cewar akwai wani mai kyau wanda ya ɗauka da kayan saurauta a fuskar wayarta, amma bai ishe ta ba.
Hankalinta ta mayar kan tanƙamemen tibin bangon, da take kallo a cikinsa kafin ya kira wayar.
"Mommy, yaushe Daddy zai dawo?" Yar kyakkyawan yarinyar mai suna Marwana ta furta tana murza idanunta da bacci ba su gama sakin su ba.
"Daddy will come back tomorrow. Ok?"
"Yes, kuma ya siyo mini teddy ɗina?"
"Sure."
"Mommy how many?"
"Ten." Ta ba ta amsa wanda ya sa ta daki dariya tana tsalle murna.
"Mommy call daddy I will give him a peck."
"Ok,"Ta ce tare da ɗaukar wayar tana ƙoƙarin kira.
"Hello, babies." Ta ji muryarta cikin bazata ya buɗe ƙofar falon yana faɗin haka tare da ware hannunsa.
Tsananin mamaki ya kamata, duk da cewar ya saba yi mata bazata, duk tafiyar da zai yi baya gaya mata lokacin da zai dawo. Wani lokacin in ta rage kwanakin sai ya ƙara in kuma ta ƙara sai ya rage, wannan dalilin ya sa sam ba ta shiri in zai dawo, duk da cewar da ma ko da yaushe cikin gayu da ƙwalisa take mace ce wacce take kula da kanta, saboda sanin mijinta kamar Bature yake. Akwai son classical things musamman ga matarsa. Everything na sa it is extraordinary and rare.
Da gudu suka ruga har da ita da take ɗauke da ƙaramin ciki wata huɗu."
"Oh no, baby easy." Ya furta tare da ƙarasowa ya haɗe su duka ya rungume yana kissing.
"I really missed you my babies like crazy!"
Dukan ƙirjinsa ta yi cikin wasa tana harararsa." Yanzu shikenan an tauye mini wannan yaƙin?"
"Subuhanallahi! Baby don't say that. Hakkinsa wajibi ne da ya kamata na sauke ke. Faɗa mini waya, mota jari ko abroad kike son zuwa? Ko kuma gidan ne kike son canzawa. In ma nine na fara miki tsufa sai na yi kwaskwarima You know." Ya faɗa yana kashe mata ido da cige lebbensa.
Dariya ta saki tana kashe masa ido sai kuma ta ɓata fuska.
"Haƙƙina da ake tauye mini, na rashin gaya mini lokacin da za a dawo don na gyara kaina, ta yadda zan sace zuciyarka na zama ni kaɗai."
"Aike kadai ce babu wata fa? Kin ga nan ɗina?" Ya nuna mata ƙirjinsa.
Dariya ta yi tare da ɗaya mata kai ta sumbaci goshinsa.
"Ke ce dai ke ba wata sai ke. A jirgi haka wata haɗaɗɗiyar bab ta rinƙa kallonta tana kashe mini ido. Ina gani na yi maza na ɗauke kyalle na rufe fuskanta har muka iso Nigeria."
"Oh my goodness baby, you are so funny." Ta ce masa cikin dariya wanda shi ma ya taya ta.
"Amma duk da haka I have to know."
"Do not worry ke fa zazzafa ce kullum a hot
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 17