kasa bacci ta yi. Tana ta tausayinsa yadda ya zaɓi ya wahala don ta kula da ita. Addu'a ta yi masa sannan ta kwanta. Cikin dare ta yi wani mugun mafarki. Mafarkin da ya sa ta tun da ta farka ba ta koma ba. Ta yi karatun Alkur'ani sannan ta yi ta tasbihi tana roƙon Allah ya musanya mata mafarkin ya zama alkhairi. Duk da cewar ba za ta gane abin da yake cikin sa ba, amma tun da ta yi ta nemi natsuwarta ta rasa. A haka ta wuni sukuku da ita, don ko makaranta cewa ta yi ba za ta ce ba.
Tana kwance Mama ta shigo, Da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki yau kuwa?"
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 20
Tana kwance Mama ta shigo, da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki lau kuwa?"
"Mai kika gani Mama?" Ta yi mata tambayar, tare da miƙewa tana gyara Musaddik da yake shan nono.
"Gani na yi kin tashi sukuku da ke,kuma kin ƙi zuwa makaranta. Ko kina so ki koma gidanki ne?"
Jin tambayar da ta yi mata ya ɓata ranta."Haba Mama, yanzu har za ki iya mini wannan tambayar? Na koma gidansa ai sai ya yi bandana."
"To na sani? Kin san ance tsakanin mata da miji sai Allah, ko kin ga wahalar da muke ciki ba za ki iya zama ba."
"Kar ki manta a cikinta na tashi, sannan babu abin da na manta. Ko da sonsa zai kashe ni na haƙura da shi. Ballantana Faruk ba shi a gabana. Mafarki na yi mara daɗi, kuma na kasa gane komai."
"Ban da abin ki mafarki ba gaskiya bane, in har ki yi addu'a babu bin da zai faru sai alkhairi."
"Na yi Mama."
"Shikenan Ubangiji ya kare mu."
"Amin," ta ce tana kallonta.
Har ta ɗaga labulen za ta fita sai kuma ta kalle ta."Yayanki ya ce zai kira amma shiru. Ɗazu kin kira shi wayar a kashe."
"Eh, wallahi sai gwadawa na ke yi, ma bari na ƙara kira." Ta ce tana kallon wayar.
"Yauwa wayar ta shiga." Ta ce cikin murna, amma har ta gaji da jira ba a ɗaga ba.
"Ki bari an jima mu gwada wataƙila ya sanya wayar a caji."
"To," Ta amsa.
Har ta miƙa zata fita aka kira wayar. Gabanta ya tsinke a maimakon ta yi farincikin ganin kiransa.
"Assalamu alaikum Yaya." Ta ɗauki wayar cikin mutuwar jiki tana faɗin haka.
Amsa sallamar aka yi jin murya da ba nasa ba, gabanta ya yanke ya faɗi."
"Ina mai wayar?" Ta yi maganar cikin ruɗu.
"Wace ce take kira?" Tambayar ya sanya ta zauna cikin tsananin tashin hankali.
"Nasreen ce ƙanwar mai wayar, don Allah yana ina?" Ta ƙarashe tambayar cikin ruɗani.
"Ya za ki kira ni kuma ki tsaya kina tambayata? Ya ƙarashe maganar cikin tsawa.
Sororo ta yi jin tsawar da ta yi mata, sai kuma ta furta."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! A cikin zuciyarta.
"Yayane yake da wannan layin, ya tafi neman kuɗi ne zuwa kudu. Don Allah ka haɗani da shi, in yana kusa in kuma yar da wayar ya yi ka gaya mini."
Tsaki ya yi yana faɗin,"Wayata ce wannan kuma layina ne, kar ki ƙara kira na."
Jin abin da ya faɗa hankalinta ya tashi."Mai ya faru da Ya Ahmad, ya aka yi layinsa ya zo gurin wannan mutumin?" Irin tarin tambayoyin da suka cika kwanyarta kenan, har ta kasa aiki bisa ƙa'ida.
"Mama," Ta kira sunanta cikin rashin hayyaci tana jin kanta yana juyawa, tamkar ana murza sitiyarin kan motar da aka ƙure mata maneji.
Ƙarar ya sanya Mama shigowa, da sauri tana tofar da lomar shinkafar da ta kai baki."Lafiya Nasreen, Faruk ne ya sake ki?"
Kallonta ta yi kamar wacce ta taɓu."Mama wayar Yaya Ahmad na kira, wani ya ɗauka yake gaya mini wai wayarsa ce." Ta furta cikin tashin hankali.
"Kai anya ki kira numbarsa wani ya ɗauka. Ina ga dai ki sake dubawa, wataƙila ba numbarsa kika kira ba."
Jin abin da Mama ta ce sai ta yarda. Da sauri ta ɗauko wayar cikin ruɗani, domin ta tabbata layinsa ta kira."Wallahi numbar sa ce Mama. Haba ya za a yi na kasa gane numbarsa Yayana, da na haddace a kaina."
Ganin yadda ta rikice sai Mama ta kamata ta zaunar. "Natsu ki ƙara kiransa insha Allahu zai ɗauka Ahmad yana nan lafiya, jikina yana ba ni haka." Ta ce cikin ƙarfafawa duk da cewar zuciyarta na bugu.
"To Mama," Ta ce tare da fara danna wayar hannunta na rawa.
Kallonta ta yi cikin damuwa ta ce,"Na ƙara kira ya kashe wayar."
"Nasreen don Allah ki natsu Ahmad yana lafiya, duk ina yake zai kira. Addu'ar da na ke masa, Allah zai kare shi."
Ɗaga mata kanta ta yi ba tare da ta furta kalami ba. Mafarkin da ta yi ya dawo mata. Tunani take yi in ba shi ya za ta yi.
Duk da Mama ta ce ta bari zuwa an jima ta kira, amma haka ta rinƙa kiran waya ba ta shiga. Ganin dare ya yi sai hankalinsu ya tashi.
Da ƙyar bacci ɓarawo ya kwashe su. Da asuba kiran farko ta tashi ta ƙara kira, amma har lokacin wayar a kashe.
Tun suna jiran kiransu har suka fara shiga damuwa. Ganin an kwana biyu sai Mama ta shirya ta je gidan ogansa. Yadda ta tarar da matarsa cikin damuwa ya tayar da hankalnta ƙwarai.
"Wallahi sai dai mu yi addu'a, saboda ni ma ina ta kiran numbar Baban Intisar a kashe "
"Ikon Allah! Ko mai ya faru?" Ta ce cikin damuwa.
"Bamu sani ba sai dai mu yi addu'a."
"Addu'a ya zama dole. Allah ya jishe mu alkhairi."
"Amin,"Ta ce tare da sauke tagumi.
Nasreen da take tsaye tana zubar hawaye. Ta kasa cewa komai. Tunani take inda yake. Wane hali yake ciki? Da kuma tunanin dalilin da ya sanya layinsa yake hanun wani.
"Don Allah ga numbata in kin ji wani labari ki kira ni." Ta ce mata cikin damuwa.
"To in sha Allahu kuma mu ci gaba da kiran ƙila kuma rashin caji ne."
"Allah shi ya barwa kansa sani da su."
Sallama suka yi mata suka dawo gida. A ranta sun kasa bacci sallah suke yi suna roƙon Allah. Nasreen kuka take yi tana addu'ar Allah ya bayyana shi.
Ganin an kwana uku babu labarin da ya sanya ta tari Baba da maganar cikin damuwa. Kallonta ya yi jin abin da ta ce."To Amaduu yaro ne da za ki tashi hankalinki? Yana nan watakila bai samu damar kiranki bane."
"Ni dai na damu da halin da yake ciki."
"To mu jira iya wata ɗaya suka ce za su yi mana."
"To shikenan Allah ya bayyana mana su."
Fita ya yi daga gidan ita kuma ta tashi ta shiga ɗakinta.
Ganinta zaune a ƙasa tana shatatan hawaye ta yi tagumi ya sanya ta ƙaras kusa da ita."Don Allah ki bar sa wa kanki damuwa, mu yi addu'a kawai. In sha Allahu lokacin da suka ina za su dawo."
"To Mama Yaya Ahmad shi ne na ke gani nake jin daɗi, in har babu shi rayuwa ta zata munanta."
"Akwai Allah ki yi addu'a." Ta ce mata cikin tsigar rarrashi. Haɗiye kulan da yake son kumbce mata ta yi.
"Bari na yi wanke-wanke."
"To maza ki yi ki ɗora abinci."
Tun daga ranar suka cigaba da addu'a, kuma kullum sai sun kira layinsa, amma wannan mutumin ne, daga baya sai ya yi blocking ɗin su. Kafin wata ɗayan sun yi shi cikin tsoro, firgice da ruɗani. A ranta da wata ɗaya ta yi, sun shiga cikin fargabar ko zai dawo, amma shiru har aka ƙara kwana uku babu Ahmad babu ogansa. Lamarin sai ya firgita shi. Shi kansa Baba hankalinsa ya tashi matuƙar gaske. Cikin tashin hankali aka sanya cigiyarsu, amma shiru babu labarin su tamkar malam ya ci shurwa.
Iya tashin hankali wannan ahali sun shige. Kuka Nasreen take yi cikin damuwa ta ce,"Ya Ahmad shi ne gatanta yau kuma ya nace babu shi babu labarin sa. Na shiga uku Allah ka bayyana mini Yayana. Kuka take tana sumbatu taba faɗin kalaman da basu kamata ta faɗin ba Ganin haka Anty Binta ta kamata ta zaunar da ita. "Nasreen ki bar kuka ki yi hakuri kar ki yi saɓo, in sha Allahu Ahmad zai bayyana."
"Saboda me za ki hana ni kuka? Bayan kin san daga yau na rinƙa yi har ƙarshen rayuwata. Ya Ahmad shi ne gatanta kuma ya tafi ya bar ni." Sai ta ƙara fashewa da gigitaccen kuka.
"In sha Allahu za a gan shi mu cigaba da addu'a da sadaka." Mama ta ce zuciyarta na ƙarfafa mata yana raye.
Da ƙyar suka samu ta yi shiru tana faɗin."Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Domin ta yi kukan har idanunta sun bushe. Babu hawaye sai zafi da ƙunci da zuciyarta yake.
Ga dai Ahmad ya ɓace ya barsu da jimamamin rashinsa. Shi kansa Baba ɓacewarsa ta buge shi, saboda sai da ya ɗauki lokaci kafin ya dawo natsuwarsa. Da fari har sallah yana kiyaye a kan lokaci, musamman in ya tuna yadda Ahmad yake zubar hawaye a duk lokacin da ake kiran sallah yana zaune. Da ga baya kuma sai ya watsar ya koma ruwa. Dama ita sallah ginuwa take a jiki, haƙiƙa duk wanda ya yi sakaci da ita sai wani ikon Allah.
Ganin kukan ba shi da amfani, ya sanya suka maida lamuransu ga Allah. Kusan kwana uku take sauka tana fatan Allah ya bayyana shi.. Kullum gani take kamar zai yi sallama. kamar zai dawo daga tafiyar da ya yi. Kullum hotonsa take ɗauka tana kallo hawaye na zubar mata. Haka Damir ya ji a lokacin da matarsa ta mutu?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa, saboda ga shi ita tana tunanin zai dawo, amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta take ciki."Idan kuwa haka ne, haƙiƙa dole ya tsane ni ya yi fatan kar ya ƙara fatan ganin mai sunanta.
Damuwar yadda rayuwarta zai cigaba take tunani. Ta san cewa rayuwarta ta shiga cikin gararin, amma duk abin da zai faru ba za ta koma gidan Faruk ba, musamman da ya ɓace ko zuwa bai yi ba.
Tun ɓacewarsa na ɗanye a lokacin da tai wata biyu. Yau ga shi ya zama wata huɗu rayuwa ta yi musu ƙunci. Kullum sai sun yi kukan rashinsa, musamman gurin kula da abin da za su ci. Wayar da Marwana ta ba ta har ta sayar da ita. Ya rage laptop ɗin. Ita ma ganin halin tsotsan tsamiya da suke yi, ya sanya ta siyar, sanin babu wanda zai biya mata kuɗin makaranta ta cire kuɗin ta ije. A lokacin da aka gaya mata kuɗin da za a siya ta yi mamaki ƙwarai. Ashe ba ƙaramin kuɗi ya kashe gurin siya mata ba. Bayan ta cire kuɗin suka fara sana'ar cikin gida. Da cinikin take samu ta je makaranta ta kuma ɗan yi wasu abubuwan na makaranta.
Damir zaune kan farar kujerar a bakin ruwa idanunsa lumshe. Zuciyarsa ɗauke da tunani barkatai. Tun ranar da suka baro Nigeriya, har yau ka kasa sakin jiki kamar yadda Mommy take so. Kullum ya kwanta bacci sai ta yi mafarkin ya, domin har yanzu zuciyarsa ta kasa daina zargin cewar shi ne ya yi ajalinta. Duk lokacin da ya tuna hakan sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu. Ya yi dana sani tafi cikin kwando dubu. A hankali ya buɗe manyan idanunsa ya ɗora su kan Little Marwana, da ke gudu a bakin ruwa tana dariya, Marwana na biye da ita. Kallonta yake yi cikin tsananin tausayawa. Hawaye suka taru a gefen idanunsa."Anya za ta yafe mini kuwa?" Ya tambayi kansa cikin tsananin damuwa. Miƙewa ya yi, yana kallon ruwan da ya kusa mamaye gurin.
Hannunsa ya ji little Marawana ta kama ta riƙe tana faɗin,"Daddy, ka zo mu yi wasan gudu da kai a bakin ruwa, kuma Anty Marwana ta ce in Mommy ta dawo daga tafiyar da ta yi za mu zo tare."
Hawaye suka cika masa idanunsa. Har yau ta kasa fahimtar Batula ta yi musu nisa."Mommy ba za ta dawo ba, domin ta tafi inda ba a dawo wa." Ya ɗauke ta tare da shafa fsskarta yana faɗin haka.
Kallon da ta yi kamar mai tunani,"Daddy, to za ka siyo mini wata Mommy?"
Tambayar da ta yi masa, ya sanya tashin hankali a zuciyarsa."Ba zan siyio miki wata ba, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki ƙular da kowace uwa za ta bawa 'yarta."
"No, daddy na fi so ka siyo mini wata." hankalinsa ya ƙara tashi jin abin da ta ce. Ije ta ya yi zai tafi ba tare da ya ce komai.
Hannunsa Marwana ta riƙe cikin hawaye."Ka yafe mini Yaya, har yau ina tuna ni na yi sanadin gushewar farincikinka, ina shiga cikin tsananin tashin hankali. Don Allah ka yafe mini Yayana." Kukan da take masa ya ƙara ninka masa damuwa.
"Sis, ki bar kuka komai ya wuce."
"Karka faɗi haka domin ka canza ka koma kamar ba kai ba, duk lokacin da na ganka a wannan yanayin ina jin kamar na kashe kaina."
"Kar ki damu ki manta komai lokacin ta ne ya yi, sannan bamu da ikon dakatar da mutuwarta."
"Ka yi mini alƙawarin za ka daina sanya damuwa a cikin ranka. Za ka dawo kamar da, yayana wanda na sani yake sani dariya da farinciki?"
Shiru ya yi yana tunani sai kuma ya ƙwace hannunta ya fara tafiya.
Sosai take kuka tana kallonsa har ya yi nisa ya zauna a can gefe.
Duk da cewar sun je gurin domin su sanya shi farunciki, amma haka suka dawo jiki a saɓule.
A lokacin da suka dawo Mommy tana zaune da qur'ani a hannunta tana karantawa. Shigowarsa ya sanya ta dakata, bayan ta kai ƙarshen ayar. Kallon sa ta yi har ya shige cikin ɗakinsa.
Marwana ta zauna kusa da ita tana hawaye."Ya Damir zai koma kamar da?"
"Ni ma na fara tunanin haka, ina ga za mu koma gida kawai, saboda zuwanmu bai yi amfani ba, kullum cikin damuwa, sannan ga campani babu mai kula da shi."
"Haka ne amma Mommy ya kamata mu ƙara lokaci kafin mu koma."
Shiru ta yi ba tare da ta ce mata komai ba.
Ganin wata biyar da ɓacewar Ahmad ba tare da Faruk ya zo ba, ya sanya Baba ya shirya ya je gidansa.
A lokacin yana falo yana kallo shi da gumbiyarsa da take kwance kan cinyarsa. Wasu irin arnan kaya ta sanya, wanda da su gwanda babu. Hakan ba ƙaramin yi masa daɗi ya yi ba, musamman da take da cikar jiki ko ina duk tsoka. Ya tasa ta ya yi ta kallo. Tuni suka fahimci juna game da tsarin iyali. Duk abin da yake so shi take masa, wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya kwanta har wani ɗan tumbi ya yi.
"Baby, kamar ana knoking get?" Ta ce masa tare da ɗaga kanta tana kallonsa.
"Ni ma haka na ji." Ya ce sannan ya miƙe ya sanya doguwar riga ya fice.
Ganin Baba ya ɗaure fuska yana kallonsa a wulaƙance."Lafiya?" Ya ce masa yana kallonsa.
"Lafiya lau, ba ka gane ni bane Farukuu?"
"Na gane ka mana ba uban Nasreen ba ne?" Jin tambayar da ya yi masa, ya sa ya jikinsa ya yi sanyi.
"Eh ni ne..."
"Allah ya sa dai lafiya? Kuma ina fata ba tambayata kuɗi ka zo yi ba?"
"A'a Faruk yaron kirki, ba ka san Ahmad ya ɓace bane?"
Ɗan jim kamar bai sani ba sai kuma ya kalle shi."Na ji wataƙila kunya ta sanya shi ɓoye kansa ya ga ba shi da kuɗin da zai iya biyana."
"Allah dai shi ya barwa kansa sani fatanmu ya bayyana shi."
Ba tare da ya amsa ba sai motsi da bakinsa da ya yi.
Ganin bai tanka ba, sai ya gyara tsayuwa ya rasa abin da zai ce, amma dai ya daure cikin rashin ƙwarin gwiya ya fara magana da cewa," Da ma na zo kan maganar matarka..."
"Ba kun ce za ku kai ni kotu ba? Ina jiran a yi mini sammaci sai na je na amshe kuɗaɗena kashe."
"Ka bar wannan maganar ai wanda ya tsaya mata ya ɓace. Ni kuma ka san dai ba zan goyi bayanta ba, dole gidan ka za ta dawo. Don ba za ta yi mini zawarci da yara ba."
"Na san ya ɓace, ina jiran na ga inda za su samu wanda zai tsaya musu ne. Tun da an gaya mini wanda yake hure mata kunnin ya bar ƙasar"
"Duk haka ba ta ta so ba. Ka san dai Nasreen da auren ka ba za ta kula wani namijin ba?"
"Ok, ka yarda da ita kenan? Tarbiya ka bata da har za ka shede ta?"
Shiru ya yi jin abin da ya ce sai kuma ya nisa,"Faruk duk wannan maganar ba ta taso ba, ka yi hakuri ka zo ka ɗauki matarka..."
"Na zo fa ka ce?" Ya katse shi yana faɗin haka, sai kuma ya girgiza kansa ya ɗora da cewa,"In har ba za ta dawo ba, sai ta yi ta zama har Mahadi ya bayyana. Ai ni wallahi rage mini aiki ta yi, don yanzu hankalina kwance na samu mace mai ladabi da biyayya."
"Yanzu dai duk zancen tone-tone bai ta shi ba, kai da Nasreen kin riga kun zama ɗaya. Ka yi haƙuri ko don tausayin yaranka."
"Tun da ba ta tausaya wa kanta ba sai ta ci gaba da zama ba. Na san dai rayuwarta a garari zai ƙare, wanda yake yi mata ƙaryar zai tsaya mata kunya ta sanya ya gudu."
"Ni zan wuce in sha Allahu za ta dawo yau."
"A'a ban shirya ta dawo yau ba." Ya ce yana kallonsa saboda ya yanke shawarar ya je ya gasa mata maganganu.
"Ka bari zan zo sai mun yi magana da ita na gaya mata dokokin gidana."
Jin abin da ya ce ya yi shiru ya kalle shi zai tafi.
Faruk ya raka shi da idanu ya ɓule, ya san kallon da yake masa ya ba shi kuɗi."Wallahi ai daga yau ka daina cin sisina. Yar ka ce yanzu na samu wacce ta fita, don inta ga dama ta zauna in ba ta buƙata ga hanya nan." Ya furta yana nuna hanya.
Da ya shiga cikin gidan har lokacin tana zaune. Ganin ransa a ɓaci ya sanya ya dawo kusa da shi."Hala 'yan maula ne?" Ta yi masa tambayar haka, don ta san a tambaye shi kuɗi ne ya fi ɓata ransa.
"Baban wannan mara mutuncin Nasreen ne ya zo, wai na je na ɗaukota. Ni kuma na gaya masa ai ba ni na kaita ba."
Jin abin da ya faɗa ya sanya gabanta ya faɗi, don ba ta ƙi su zauna daga ita sai shi ba.Ɓata rai ta yi tana kallonsa cikin kissa."Yanzu baby, dawowa da ita za ka yi mu rinƙa sharing ɗinka."
Kallonta ya yi tare da jawota jikinsa."Ƙarki damu dawowarta ba zai hana mu jin daɗin rayuwarmu ba. Don ban damu da ita ba, in ta ga dama ta zauna, in ta ce za ta ɓata miki rai jikinta zai gaya mata, don yanzu kin fi mini kowa a duniyar nan."
Murmushinta saki tana kallonsa."Lallai aikin Malam yana ci, na samu kansa sosai, sai kuma ayi mini maganin maƙonsa." Ta furta hakan a cikin ranta.
"Shikenan ta dawo ka ga dama ni kaɗai nake aikin gidan nan."
"Ƙarki damu babyna, da zarar ta dawo ita za ta rinƙa aikin gidan, tun da ita ce take da yara."Daɗi sosai ta ji jin abin da yace.
Baba da ya koma gida ya sameta tana zaune a ɗaki ta zabga tagumi.Ganinsa ya sanya ta janye tagumin. "Sannu da shigowa Baba."
"Yauwa,"Ya amsa tare da zama kan kujerar.
"Gurinki na zo."
Jin abin da ya ce gabanta ya faɗi, har ta kasa amsa masa sai kallonsa da ta yi. Zama ya yi yana kallon ta.
"Nasreen, ki daina yaudarar kanki ki koma gidan aurenki, domin kin san dai wanɗanda suka ɗaure miki gindi duk sun gudu sun barki?"
"Ya Ahmad ba guduwa ya yi ba, Ya Ahmad ba zai taba guduwa ya bar ni da gangan ba."
"Ko ma dai mene ne ke kike tunanin haka. Don haka ya zama dole ki koma gidanki tun da babu shi."
"To don babu su dai na kasa ƙwatar 'yancina, wallahi na gwammce na fuskanci ko wace irin rayuwa da na zauna a gidansa, domin Faruk azzalumi ne macuci, a dalilin ayi masa hulɗi Ya Ahmad ya ƙarfafa tafiyarsa. Na tsane sa bana ƙaunarsa, kuma ba zan koma gidansa ba."
"Wallahi ba ki isa ba, in har ni na haife ki sai kin koma." Ya ce cikin tsawa yana kallonta.
Kasa amsa masa ta yi tana kallonsa cikin zubar hawaye, ganin haka ya ɗora da cewa,"Yadda Faruk, ya watsar da ke ya ishi ya nuna miki zai iya rayuwa babu ke, saboda kina nan kina shan wahala, amma shi yana morewa da amaryarsa. So na ke na wa 'ya'yanki da ke kanki gata, saboda wallahi in har ba ki hakura kin koma ba, sai kin zama abin tausayi. Kina gani dai yadda abinci yake nema ya gagareki, don haka na je na ba shi haƙuri, sai ki tattara ki koma gidanku."
Ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka."Yanzu Baba, duk wulaƙancin da Faruk ya yi mini, amma har ka iya zuwa gidansa ka ba shi haƙuri?"
"Taimakon ki na yi, kuma da kike wannan maganar mata nawa suke zaman ƙunci a rayuwar aurensu kuma suke haƙuri? Wasu matan babu abinci babu sutura, amma hakanan suke zama a gidajensu."
"Ka yi haƙuri Baba, ba zan iya komawa gidansa ba."
"Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa."
Sharhi game da Ahmad.
Jiya da na saki post na ji ƙorafinmu mutane da dama cewar kar na kashe Ahmad masu biyo ni pc da kuma masu comments a group. Duk na fahimce ku kuma na gane abin da kuke nufi. Ku kwantar da hankalinki Ahmad ba zai mutu ba, amma ku sani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 17