Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma duk da cewar ba ta da ƙiba kyakkyawar gaske ce na nunawa tsara. Tana da haske amma ba irin sosai ɗin nan ba, doguwa ba sosai ba, sannan jikinta mai kyau, irin wanda yake nunawa in ta samu hutu za ta yi hibs. Idanunta dara-dara, sannan fuskarta doguwa ce da hancinta mai tsawo sosai. Tsananin kyawunta ya ruɗar da ita, musamman ƙuruciyarta, domin ita a tunaninta matarsa babba ce. Ta yadda ta ga ta ta san za ta girme mata sosai. Hankalinta ya tashi, amma kuka da ta tuna duk kyawunta ba ta a idanunsa sai hankalinta ya kwanta. Kallo-kallon juna suka yi, wa junansu kowacce da abin da take tsaƙawa a cikin ranta. Hanyar ƙofar ɗakinta ta yi, zuciyarta a dake ba tare da tanka musu ba za ta shiga. Wata uwar tsawa ya daka mata mai ƙarfi. Tsawar da in ya yi mata a da, sai ta ji hatta hantar cikinta ya kaɗa jikinta ya kama rawa, hawaye ya fara zuba a ƙuncinta, amma a yanzu sai kawai ta juya tana masa wani kallo kamar kashi. Idanunta ta ware sosai ta ɗora a cikin nasa fuskarta babu alamun tsoro. Kallon banza ta watsa masa da shi da Rashida, ta take cikin jikinsa kamar za ta shiga cikin jikinsa, tana shafa sajensa. Ta kama hannun Raihan za ta shiga. Faruk sai ya tsaya sororo, yana kallon ta cikin tsananin mamaki. Goge idanunsa ya yi yana kallon ta da take taku cikin isa za ta shiga ciki. Ya kalli Rashida ta take kallonsa cikin tuhuma. Ya gaya mata cewar ko muryarsa ta ji, sai ta rikice in ya sanya kara ba ta iya tsallake wa, amma sai ta yi mamakin kallon wulaƙanci da rainin da ta ke masa. Ganin ganin haka ya kira sunanta da ƙarfi. "Nasreen!" Ba tare da ta amsa ba, ballantana ya yi tunanin za ta juyi, sai ya ji ta saki tsuka mai ƙarfi ta ci gaba da tafiya. "Kutumar uba!" Faruk ya furta tare da dumfarota tamkar kububuwa. Sai dai, ya cika da mamakin ba ta gudu ba, kuma ba ta jirga daga inda take ba. A zuciyarta ta riga ta rantse ba za ta ƙara yarda ya taɓa jikinta ba, in kuwa ya yi sai ta yi masa abin da ba zai ƙara gigin dukanta ba. Za ta ƙwatarwa kanta 'yanci ba za ta yarda su wulaƙanta ta ba. Lokaci ya yi da za ta zama mace mai 'yanci kuma ta samu walwala a gidan cikin rayuwarta. A shirye take da duk wani hukunci da zai ɗauka. Lokaci ya yi da zai daina dukanta kamar jaka a gaban yaranta. Ni kaina yadda ya dumfarota sai da na tsorata na yarda sahara, amma sai na ga ba ta razana ba. To fa Nasreen anya capacity Faruk zai ɗauka kuwa? Kin ga san halinsa. To ban dai san yadda kika ɗauki alwashin ƙwatowa kanki 'yanci ba, amma bari mu ci gaba da bibiyarki. Laifin daɗi ƙarewa😁😁😁😁 Anan na kammala littafin WASU MAZAN book one sai mun hadu a book two wanda yake na kuɗi ne 500 in aka gama 800. Allah Sarki Nasreen baiwar Allah. Ubangiji ya na sane da halin da kike ciki kuma ba ya bacci. Ki ci gaba da addu'a kina kai masa kukan. Watarana zai ɗube ki kuma ya kawo miki sauki. Masu karatu ya rayuwar Nasreen za ta cigaba da kasancewa a gidan Faruk?😭😭😭😭 Shin za su yi zaman lafiya da Rashida? Wane irin zaman kishi za a yi🙄🙄 Nasreen za ta ci gaba da hakuri ko za ta mike ta ƙwaci yancin ta? Kuna ganin faruk zai ɗauki abin da za ta yi masa? Garin zai yi adalci kuwa tun da ya samu kalar madara zubin ajebota ko ina a cike?😆😆😆 Allah Sarki Damir bawon Allah zai dawo Nigeria kuwa? In har ya dawo wane irin rayuwa zai yi? Ya labarin Ya Ahmad?😭😭😭😭😭 Marwana da take addu'ar Faruk ya rabu da Nasreen har take tunani Innhar ya saketa sai ta yi duk abin da za ta yi ta haɗa soyayya a tsakaninsu har ya aure ta🙄🙄🙄🙄 s. Shin kuna tunanin haka zai yiwu? Damir zai iya kallon Nasreen har ya aure ta su zauna lafiya, bayan babu wacce ya tsana samaa da ita? Ƙarku manta har yanzu ba mu ji Asalinsa ba, sannan ya aka yi rayuwarsu ta rikiɗe ta koma haka. Duk za su samu amsar tambayoyinku a cikin littafin WaSU MAZAN book two wanda paid book ne kan naira 500 zai zo muku, in kuma aka gama 800. Posting safe da yamma babu fashi, domin an riga an gama book ɗin. Ga masu son shiga don su karanta sai a tura kuɗin ta wannan account ɗin. 8144072423 Jamila Lawal opay A turo shedar biya ta wannan numbar 07072971093 Kar ku sake a baku labari ku kasa sannan ku tare har ku karanta. Wannan dai maribuciyar taku ce, mai son faranta muku da kuma.sin ganin farincikin ku. Jamila Lawal Zango Jamsy. Ta shirya ta wasa ƙwaƙwalwaarta don ta sanya ku nishaɗi. Labarin yanzu aka fara don ba a je ko ina ba. Akwai wata irin soyayya mai kama da ƙiyaya, sannan akwai gaba mai ƙarfi da take haddasuwa a tsakanin abokan hamayya biyu. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 17 of 17