Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sis." Ya ba ta amsa tare da ɗaga mata kai yana dariya. "Na gode Ya Damir, Allah ya ƙara buɗi ya sanya ka fi haka." "Amin sis," Ya ce mata. Da ya sauke ta, gidan Hajiya ya wuce ya kai mata magani ta da ya siyan mata, sannan ya wuce gida don za su je check up yau. Da ya isa ƙofar get ɗin gidan, ya yi hon mai gadi ya taso ya buɗe masa. Shiga da motar ya yi, sannan ya yi parking. Kai tsaye falo ya shiga yana faɗin," Honey." "Na'am." Ta amsa tare da rungume shi ta ba shi hot kiss. "Ka dawo?" "Eh, da fatan kin shirya." "Am ready, we can go." Ta ba shi amsa tare da ɗaukar jakarta. "Karɓar jakar ya yi, sannan ya ɗauki makullin motarsa, ya kama hannunta suka fita suna sakarwa junasu murmushi. A asibitin teaching hospital na Ahmadu Bello University Zariya. Suna zaune kan kujeru, hankalinsu ya ɗauki ga siririn likitan da yake ta yi musu bayani cikin harshen Nasara. Jikin Damir ya yi sanyi, yana kallon abar ƙaunarsa da take kallon likita. Hannunta ya kama sannan ya ce,"Ina da burin matata ta haifa mini yara, amma saboda lafiyarta Doctor in ta haihu a juya mata mahaifar." Ya ƙarashe maganar cikin sanyi. "Yanzu shi ke nan ya'ya biyu kawai zan haifa maka Baby? Tun kafin mu yi aure ka sanar mini kana son ka cika family ɗinku da 'ya'ya tun da ba ku da yawa. Kenan aure za ka ƙara?" "Kece mace ta farko da na so kuma ta ƙarshe. Kin ji na yi miki alƙawarin ba zan taba auren wata 'ya mace ba." Duk da abin da ya ce hankalinta bai kwanta ba. Ƙara janke hannunta ya yi cikin wani yanayi. "Doc ka gaya mini yadda zan ƙara kula da lafiyarta saboda na rayu da ita har abada." "Ba ka da matsala, saboda kana kula da duk wani abu da mai cutar sikila zai kula." "Shi ke nan na gode. In Sha Allah, da zarar watan haihuwarsa ya tsaya zan kawo ta a cire babyn." "Allah ya kaimu." Ya ba shi amsa tare da miƙewa ganin sun mike. Jikinta a mace har suka isa gurin motarsu. Ya buɗe mata ta shiga. Zama ta yi bayan ya shigo ta rungume shi tare da fashewa da kuka. "Ina sonka mijina, sai dai ina ji a jikinsa kamar ciwonka ba zai barni mu yi tsawon rayuwa ba. Ga shi kuma alamu sun fara nuna wa, tun da ba zan iya haifa maka yara ba. Dole ka yi wani auren, ka samu matar da za ta haifa maka yara" Ta ƙarashe maganar tana kara ƙanƙame shi. "In har kika gaya mini haka sai na ji zuciyata ta sare. Ina jin za mu yi rayu dake har abada. Jikinsa yana bani kece mace ta farko kuma ta ƙarshe a gareni." "Ina fatan hakan mijina. Ina son na rayu da kai har abada." "Ni ma haka matata, in Sha Allahu zamu rayu tare." Ya furta yana shafa bayanta cikin tsigar rarrashi. FARUK Tun da daddaren da ya ci tuwon bai ƙara ci ba, don ko da safe da ta kai masa ɗumame, watsa mata mugun kallo ya yi. "Ba zan ci ba saboda ɗanye kika yi mini. Shi zu ku ci har kwana biyu." "Kwana biyu muna cin tuwo an ya da adalci kuwa?" "Babu ai dama ba ki ganin adalcina." Ya ce mata cikin ɓaci rai. "Gani na yi ko kai ba za ka iya cin tuwo har kwana biyu ba, don ba zai kai ba lalacewa zai yi." "Kisa a firjin dama ai amfaninsa kenan." "Tun da gas ɗin ya ƙare ka sanya ne?" "Ni fa na gaji komai ki ce ni zan yi a gidan nan. Mene ne amfanin ki?" "Lokaci ya kusa da zan taimaka." Ɗaukar brief case ɗin da ya yi zai fice ba tare da ya ce mata komai ba. "Allah ya dawo da kai lafiya." Ta ce tana kallon bayansa.Ba tare da ya amsa ba ya fice. Tun da ta karya da tuwon ta kasa ci. Fita ta yi ta siyo musu awara da yaji suka ci da rana. Da daddaren daurewa ta yi, ta ɗunduma tuwon suka ci. Cikin magagin bacci ta ji dirin motarsa. Da sauri ta sauko ta kunna fitilarsa, saboda babu wuta. Fita waje ta yi ta bude masa get ɗin gida. "Ba ki yi bacci ba?" Tambayar ta yi mata bambarakwai! Wai namiji da suna Hajara. "Na ɗauka kin yi bacci har zan buɗe get ɗin da kaina." Ya ce tare da rigata ɗaukar kayan da ya siyo. Sororo ta yi tana kallonsa cikin alamun bacci. "Mu shiga ciki." Ya ce mata cikin taushi murya yana mata kallon ƙasa-ƙasa, wanda ya sa ya ta ji wani iri. Da suka shiga falo zama ya yi a two seater sannan ya ɗaga idanunsa yana kallonta da ta yi tsaye kamar soja."To ki zauna mana." Ya ce yana nuna mata gefensa. Zama ta yi, tare da ƙasa da kanta tana mamakin canzawarsa. "Kin ci abinci?" WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 7 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kin ci abinci?"Tambayar da ya yi mata, ya sanya ta kasa amsa masa. "Na san kema ba ki ci tuwon ba, tun da babu daɗi." Ya ƙarshe maganar tare da kama hannunta yana mata wani irin kallo ƙasa-kasa."Ga shi na siyo miki." Ya miƙa mata ledar da ta kasa amsa sai dai ya ɗora mata a jiki. Ganin ta kasa ɗaukar ledar, tana mamakin sabon salon da ya fito da shi, wanda za ta iya cewar tun farkon amarcinsu. Aka yi yunwa halin kowa ya fito, ya dai na siya mata. "Ki buɗe ladar mana, sai ki ije wa su Raihan na su." Ya ce mata wanda ya sanya ta yi namijin ƙoƙarin buɗewa.. "Ikon Allah! Tabbas akwai abin da ya shirya." Ta ce a ranta, amma kuma ta san dai cewa ba don haƙƙin kwanciya zai yi mata wannan tattashin ba, saboda zai iya sanya ƙarfinsa. Gabanta ne ya faɗi da zuciyarta ta ayyana mata ko aure zai yi. "Kai ina ba aure bane, domin bani da ƙimar da don zai shigo da wata sai ya tattashe ni. To mene? Allah kaɗai masani da shi da ya shirya." Ta ba wa kanta amsa. Ba ta ƙara shiga cikin tsananin mamaki ba, sai da ta buɗe ledar. Wasu irin haɗaɗɗun kaji guda biyu da Rufaida yogot. "Na yanka maka ne?" "A'a, na ki ne ke da yara ku ci." Ya ce yana murmushi tare da shafa bayanta. Cikin tsoro da fargaba ta ci kazar da yogot ɗin, domin zuciyarta cike da fargabar abin da za ta biya da shi, don ta san in har ta kasa biya, sam ba zai yi mata sausauci ba. Sai da ta ci ta kammala ta kora da ruwa, sannan ya kalle ta ya ce,"Ga shi daga yau za ki fara sha." Ya ce mata tare da ɓarewa ya miƙa mata sannan ya tura mata ledar ƙullin magani. Cikin tsanannin mamaki ta kalli ƙullin maganin"Na sha magani, ba ni da lafiya ne?" Ta yi masa tambayar cikin zallar mamaki tare da juya ƙwayar maganin a hannunta. "Ban sani ba, jahila ce ke da ba za ki duba ki ƙaranta ba?" Ya ce mata da ɗan ɗaga murya duk da yadda ya so ya danne zuciyarsa. "Supplements na gyara jiki Abban Raihan ka siyo mini? Ce maka aka yi ina muzanta da yanayin surata?" "A'a, saboda ina buƙatar na ganki kin zama 'yar duma-duma komai yana rawa a jikinki." "You must be jorking Abban Raihan, don wallahi ba zan sha abu da zai cutar da ni ba." "In da kuma kika yi kaɗan kenan, don ko ɗure zan yi miki sai na yi. Su sauran matan da suke sha mutuwa suka yi?" "Akwai yiwuwar sun mutun, domin mata nawa na ji labarin shan supplements, na ƙara girman halitta ko canza fata ya sanya sun kamu da cutar kansa? Ni ba zan sha abin da zai cutar da ni ba, saboda ban taɓa jin na raina halittar da Allah ya yi mini ba. A haka ka ganni ka aure ni, in da ka san mace mai ƙiba kake so da ba ka aure ni ba." "Sai kuma na yi laifi don na taimaka miki? Saboda na tabbata da ban aure ki ba, kina can kin yi kwantai. Ni ɗin ma tsautsayi da ƙaddara ya ja mini, in bacin haka ba zan sa ya kuɗina na auri mace kamar ki ba. Ke babu biyayya bare iya kissa da kwantar mini da hankali, sannan ɗan jikin ma ba za ki yi ba." "Ni fa duk abin da za ka ce ba zan sha ba." "Ki sha maganin nan tun kafin raina ya bace."Ya furta cikin ɓacin rai yana kallon ta. "Ba zan sha ba ko kashe ni za ka yi." Ta ba shi amsa za ta wuce. Fusata ya yi, tare da zare mata idanu ko mai ya tuna oho ya sausauta murya ya riƙe mata hannu. "Babu wani illa da yake sawa fa. Abokina ga ya siya wa matarsa, shi ne ni ma na ce zan siya miki. Da ma na sha tambayarsa yadda matarsa komai ya ji, ashe wannan maganin yake siya mata. Za ki sha safe da rana." "Ka san yadda na tsani magani shi ne kake cewa na sha. Ni ba zan zama 'yar kwaya ba." "Karɓa kisha tun muna mu biyu." Tsaki ta ja za ta wuce. Kau ya kaureta da mari. "Ina wasa dake zan miki umurni ki musa, sannan kuma ki yi mini tsaki?" Kuka ta fashe da shi tare da dafe ƙuncinta."Wallahi ko kashe ni za ka yi ba zan sha ba." Ganin ya nufe ta da sauri ta ruga da gudu ta shige ɗaki ta kulle ƙofa. Dukan ƙofar ya shiga yi, cikin tsananin fushi yana faɗin," Ki buɗe ƙofar na kafin na ƙaryata na canza miki halitta. Kin san nawa na sanya na siyo miki?" "Ba zaka iya bani abinci masu gina jiki ba na yi kyau, sai dai maganin da zai cutar da lafiyata to ba zan sha ba." Ta ce mishi tare da kwanciyarta. Tana jin yadda ya rinƙa buga ƙofar, amma ta yi banza da shi har ya gaji ya je ya kwanta. Da safe komai a cikin ɗakinta ta yi, kasancewar asabar ce ta yi zamanta a cikin ɗaki har ya fita, sannan ta fito ta girka ragowar indomie guda ɗaya ta bar musu. Kamar yadda ba ta yi tunanin zai bar mata abin da ya siyo mata ba, haka ta zo ta ga ko ƙashi babu. Wasan 'yar ɓuya suka fara har sai da suka yi kwana biyu. Ita ce ta fara gajiya da ɓuyan don kuɗin hannunta ya ƙare, sai garin kwaki da awara take ci. Ga shi Monday aka shiga dole ta nemi abin da za ta rinka bawa Raihan. Ranar Monday duk yadda ta so ya kulata ya ki. Har duƙawa ta yi ta bashi hakuri, amma bai kulata ba ya sa kansa ya fice. "Cikinku zai gaya miki." Ya faɗa yana murmushin mugunta. Idanunta ya raina fata. Ahmad ta kira ya tura mata da dubu ɗaya, ta siya wa Raihan abin da za ta ci a makaranta sannan ta wuce school. Marwana Kamar yadda ya yi mata alkawarin ya siyasa, Nasreen laptop mai kyau da waya tsaddadiya Rungume shi ta yi cikin farinciki. Dariya kawai ya yi mata ganin yadda take murna sosai. Bayan sun tashi daga makarantar. Nasreen na ƙoƙarin fita daga ajin ta ƙara so gurinta. "Ummu Raihan hanyarmu ɗaya, amma ba ki taɓa cewa na rage miki ba." Murmushin yaƙe ta yi, don tana tunanin abin da za ta ci in ta koma. "Ba haka bane. Na ga ke da ƙawayenki kuke tafiya." "To daga yau babu wanda zai ƙara shiga mini mota, daga ke sai Musaddik." Zare idanunta ta yi, jin abin da ta ce."Ayi haka? Mu dai shiga tare in ba zan takura ba?" "No, daga ni sai ke za mu rinka komawa gida." Daɗi ta ji sosai domin duka ɗari biyu ta rage mata ba zai isheta ba. "Bari na shiga, amma kar ki hana su." Ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe mata gaba ta shiga sannan ta zagaya ta shiga ta tada motar. Sun yi nisa babu wanda ya ce uffan. Marwana ta waiwayayo ta kalleta tare da mayar da hankalinta kan tuƙi. "Hala tunani exam kike yi da aka sanya time table?" "A'a, mai kika gani?" Ta ce mata tana kallonta. "Babu." Suka yi shiru na 'yan daƙika. Marwana tana mamakin yawan shirin da take yi. "Kalli wayar nan da laptop ɗin na sun yi kyau?" "Wow, sun yi kyau sosai wallahi." "To na ki ne." Tsananin mamaki ya sanya ta kalleta da sauri. "Ni kuma?" "Eh, Yayana ya siya miki." Ranta ne ya ɓaci sosai." Saboda kin ga wayata shi ya sa kika sa ya siya mini? Bana buƙatar su domin wayar nan da kika gani tana mini komai." Hankalinta ya tashi jin abin da ta ce."Wallahi ba haka bane. Ya ce zai ba ki presents saboda ƙoƙarin ki. Shi ne na bashi shawarar ya sai mai waya da laptop don kin fi buƙatar su." "Bana so ki mayar masa ina jin daɗin rayuwata a haka." Ta ce mata amma a ranta ta ji dadi sosai mamakin siya mata abubuwa masu tsada ta yi. Ga mamaki ta sai ta ga ta gangara gefen titi ta yi parking."Don Allah kar ki yi mini mummunar fahimta. Wallahi bani da nufin tozarta ki. Yayana he is generous and kind, amma in zai ɓata miki rai zan mayar masa." Ta ƙarashe maganar sai hawaye shar a fuskarta. "Ikon Allah! Wannan Mommy's pet zan ce ko daddy's?" Murmushin ta yi tare da share hawaye."Brother's pet. Yayana shi ne gatanmu. Mu uku mahaifiyarmu ta haifa. Shi ne ya ɗauki duk wani ragamar rayuwarmu." "Allah Sarki kamar Yayana dai Ahmad. Shi ne na uku a ɗakinmu, amma shi ne namiji, kuma yake ɗaukar duk dawainiyarmu. Shi ya sanya ni a makaranta yake biyan kudin." "Ba kina da aure ba?" "Eh," Ta ba ta amsa sai alokacin ta tuna ɓaranɓaramar da ta yi. "Allah ya ɗaukashi kamar Ya Damir." "Amin." "Yanzu za ki karɓi kyautar?" "Na gode ki yi masa godiya sosai. Allah ya ƙara ɗaukaka shi." Amsawa ta yi sai kuma ta sanya hannu a jakarta ta zato dubu biyar."Ki sa kati." Ta kasa karɓar kallonta kawai ta ke yi." Kar ki ce a'a wallahi Allah ya sanya mini ƙaunarki tamkar 'yar'uwata na jini. Watakila kuma don bani da 'yar'uwa mace ce." "Zan karɓi wayar da laptop ɗin amma ban da ku..."Maganar ta katse ganin ta ɗauke jakarta ta sanya mata. Murmushin ta yi cikin farin ciki ta ce,"Na gode Allah ya bar ƙauna." "Daga yanzu babu godiya a tsakaninmu fatana na yi ƙoƙari lamari. Ya Damir ya tura ni waje na yi masters a can." "Za ki yi ƙoƙarin fiye da ni in sha Allahu." Duk yadda ta so ta kaita gida, amma taƙi sai ta kafe ta ije ta a unguwarsu. Unguwar ta bi da kallon mamaki ganin yawancin gidajen duk na masu kudi ne, saboda za ta iya rantse wa babu gidan talaka a gurin. "To shi ke nan, Ummu Raihan my regards to her." Ta amsa mata sannan ta juya ta wuce ita kuma ta kunna motar ta wuce. Tsayawa ta yi tana duba wayar da laptop ɗin."Ikon Allah! Wayar nan da laptop ɗin nan masu tsada ne, kuma wai sun ba ni kyauta?" Gabanta ne ya fadi da ta tuna ko mai Faruk zai ce game da kyautar. Shago ta wuce ta siya indomie, har da ƙwai da madara, sannan ta sayi kati na duba ɗaya ta wuce gida. Da ta isa gidan sauke Musaddik da yake bacci ta yi. Kwanciya ta yi kan kujera tana hutun gajiya. Bayan ta huta sannan ta shiga kicin ɗin ta girka indomie ta ibarwa Raihan, kafin su dawo islamiya a kawo ta. Tana zaune a falo har aka kira sallah magariba, daidai lokacin da Raihan ta shigo. Alwala suka yi sannan suka yi sallah. Ɗaki ta ja su suka koma. Bayan ta kulle ƙofar ta ɗauko laptop ɗin da wayarta. Da ma ta sanya katin da ta siyo Tana ta danna wayar ta kasa bacci har dare ya yi. Ko da ta ji dawowarsa ba ta damu ba, tun da ta san cewa ɗakinta a kulle yake. Faruk kuwa tun da ranar da ya siyo mata maganin ta ƙi sha yake jin haushinta. A ranar da ya sanya matuƙar ba za ta sha ba, shi kuma ba zai ba ta abincin ba. Mamakin inda take samun abinci ya kama shi matukar gaske. Duk da ya san ba ya wuce wannan ɗan'iskan Ƴaƴanta Ahmad. A yau dole sai ya ganta, don haka ya je ya nemo makullin ɗakin ya sanya a aljihunsa. Sai da ya shigo ya ci abinci da ya ƙoshi sannan ya buɗe ɗakin. Jin kiciniyar buɗe ɗakin, ya sa ya ta yi maza ta mike za ta ɓoye wayar, domin har yanzu ba ta san mai za ta ce masa, don ta san ba lailai bane ya yarda. Sai dai, duk ƙoƙarin ta na son yin hakan, kafin ta ɓoye har ya buɗe ƙofar ya shigo. "Saboda kin mayar da ni ɗan'iska, ba ni da matsayi a gurin ki. Shi ya sa kike kull..." Maganar ta maƙale masa sakamakon wayar da laptop ɗin da ya gani. "Ai iyye!" Ya faɗa cikin tsananin mamaki yana kallonta. "Ke! Gidan uban wa kika samu waɗannan?" Ya yi mata tambayar tare da ɗauka yana kallonta. Haɗa wayar ya yi da tasa yana kallo, duk da cewa ya san tafi ta sa tsada. "Nasreen?" Ya kira sunanta cikin tsanani mamaki. "Na..am,"Ta furta cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa tana matsawa. "Gidan uban wa kika samu waya?" "En..uhm..e." Ta ce mishi tana zare ido. "Ta tabbata mazan jami'a kike bi. Shi ya sa kika raina ni, sam ba ki ɗauke ni a bakin komai ba. Ni da matsiyaci a gurin ki duk ɗaya." Zare idanunta ta yi cikin tashin hankali tare da matsawa ganin yana dumfarota. "Tsaya ka ji Abban Raihan, wallahi ban taɓa bin wani ɗa namiji ba. Don Allah karka buge n.." Ta yi shiru tare da ƙwala ƙara ganin ya kai hannu ya mangareta. "To in ba maza kike bi ba uban wa ya baki?" Ya faɗa tare da kai mata wani bugun. Faruk lafiyarka kuwa? 'Ya mace ba abin duka bane. Tsakanin mata da miji ya kamata akwai kyakkyawar fahimtar da kowanne zai san abin da ɗan'uwansa zai yi. To mu je dai zuwa mu ji yadda za ta kama Ba kwa comments lafiya?🙄🙄 In har ana son posting safe da yamma na ga ruwan comments. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 8 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kyauta yar aji.." Sai kuma ta canza maganar tana cewa,"Ya Ahmad ne ya siya mini." Ganin yadda ya zare mata ido yana son jin abin da za ta furta, sai ta canza shawara ta ce,"Ahmad? Ƙarya ne domin aikin kanikancin da yake yi, da ci da mahaifiyar da nema mata lafiya, ba zai bari ya siyaiki ba." "Na rantse da gaske ne ka kira shi ka ji." Ta faɗa cikin muryar kuka. "Na kira shi na ji uban me? Maza kike bi da aurena kike kula maza? Wannan dalilin ya sa ya har kwana biyar ban baki abinci ba, kuma ba ki damu ba." Ya faɗa tare da cire bell ɗin da ya shiga fuskanta tana ihu. Ganin yana shirin illantata, ya santa ta yi maza ta faɗa bayi ta rufe ƙofa. "Ki buɗe ƙofar nan, kafin na buɗe da kaina na yi maganinki." "Don Allah ka yarda da ni, wallahi ba zan taɓa cin amanar ka ba." Yaran sun yi tsuru-tsuru, suna kallonsa don Raihan kuka take yi sosai. Duk da cewar sun saba ganin yana dukanta, amma na

Chapter 5 of 17