roƙe ni ba, kuma a tunaninta farinciki za ka yi, saboda maƙiyinka ba zai taba..."
"Ke! Fitar mini da ga ofis." Ya furta cikin tsananin fushi yana nuna mata hanya."Kin san Allah? In har kika ƙara gigin tako mini har ofis, sai ka wulaƙanta rayuwarki."
"Ba ka isa ga wulaƙanta rayuwata ba, saboda bacin darajar da Ubangiji ya yi mini. Ba ka kuma san ni waye ba? In har Kasan Damir Hussain Gamawa ba za ka yi gigin nuna mini ɗan yatsa ba."
Idanunsa ya zare lokaci guda ya ji zufa na keto masa. Tsananin mamaki ya kama shi tare da tunanin yadda aka yi Nasreen har ta ƙulla abota da ita. Haƙiƙa sanin ita ko wace ce, ya yi matuƙar razana shi sosai.
"Wane ne a duniya bai san Damir ba yaro matashin mai tashen nera. In har kuwa ƙanwarsa ce za ta iya mata kyautar da ya fi haka.
"Ina dole na raba ta da ita, domin shigowa wannan zuriyar a rayuwar Nasreen tamkar arziki ne ya shigo a cikin rayuwar su Nasreen gabakiɗaya." Ya furta yana share zufan da ya tsatso a goshinsa.
"Ba na zo na yi maka barazana da arzikin Yayana bane, don ka daina wulaƙanta matarka. Na zo na gaya maka zaman aure ba wasa bane, ko shirin Film da za ka rinƙa tozarta matarka, kuma duk zaman da kuke yi a ranar gobe kiyama, sai Ubangiji ya tambaye duk wanda ya cuci wani a cikinku, saboda iyayen Nasreen talakawa ne hakan bai zama hujjar da za ka rinƙa wulakanta rayuwarta ba. Ina rokon ka da Allah ka ji tausayinta ka daina cutar da rayuwarta."Ta ƙarashe maganar tare da ficewa daga ofishin.
Jaɓar ya zauna yana share zufan da take kwararo masa. Idanunsa ya zaro yana kallonta da ta rufe ƙofar da ƙarfi, har sai da ya rintse idanunsa zuciyarsa na bugu.
Wani irin kishi da baƙin ciki, sosai ya ji na ganin mutanen da Allah ya haɗata da su.
Miƙewa ya yi, da sauri ya fice daga ofishin zuciyarsa na bugu, saboda magungunta sai kuwwa suke masa a kansa.
Nasreen na kwance a falo, tana kallon Raihan da take ta tsalle-tsalle a falon tana murmushi.
Jin hon ɗin motarsa, ya sa ta tashi da sauri don ta buɗe masa get, tare da mamakin abin da ya dawo da shi da wuri.
Bayan ta buɗe masa get, ya shigo ta kalle shi ganin yadda ya shigo babu fara'a. Gabanta ne ya buga sosai, saboda ta san hushin a kanta zai sauke.
"Sannu da zuwa Abban Raihan." Ta ce masa tare da matsawa gaban motan, tana jiran ya fito don ta ɗauki kayan da ya siyo.
Kallonta ya yi tare da jan tsuka ya shiga cikin falon.
Sororo ta tsaya tana kalonsa har ya shige cikin gidan. Idanunta suka kawo ruwa, ganin ita da miji babu maganata arziki kullum cikin faɗa da hushi.
Yana zaune ta yi sallama ta shigo hannu ta riƙe da leda. Ƙarasawa gabansa ta yi, ta ije tare da juyawa za ta shiga cikin ɗakinta.
Farouk ya bita da idanunsa cikin damuwa. Tsoro da fargaban abin da zai faru, da rayuwar ta in har ta ji gaba da hurɗa da Marwana suke damunsa.
"Ina ba zan bari ta ci gaba da hurɗa da waɗannan family ba, dole na raba su." Ya ce yana girgiza kansa.
"Nasreen," Ya kira sunanta daidai lokacin da za ta shiga cikin ɗakinta.
"Na'am," Ta amsa tare da dawowa gabansa ta tsaya.
Mugun kallo ya watsa mata, sai kuma ya gyara zama ya ce,"Na raba ki da wannan yarinyar, amma saboda ba ni da daraja da ƙima a gurinki, sai kika je kika sanar mata da ina cutar ki ta zo ta ƙwayar miki 'yanci, tun da ga ta human right ko?"
Hankalinta ya tashi matuƙa gaya, jin abin da ya faɗa."Idanunta suka suka yi raurau za ta yi kuka.
Sam ba ta ji dadin maganar da ta yi masa ba, saboda ta san cewa da ma babu abin da maganar zai jawo mata, sai wata damuwar.
"Wallahi ban aike ta ba kuma.." Ta kasa ƙarashe maganar tana in'ina.
"Ok, ita ce ta ga ya dace ta zo ta yi mini fitsara da rashin kunya ko? Saboda kin ba ta labarin rayuwar aurenmu ko?"
"Ka yi hakuri ni ban gaya mata..."
"Dallah! Rufe mini ba ki shashashar banza." Ya ce mata tare da miƙewa cikin ɓacin rai yana kallonta.
Ganin yana matsawa, ta fara ja da baya cikin tsanannin tsoro.
"Abban Raihan, don Allah ka yi hakuri karka buge ni." Ta ce masa cikin raunin murya, tare da sa hannu ta kare fuskarta, don ta san zai iya wanka mata mari.
Kunnenta ya kama ya riƙe da ƙarfi." Wallahi Nasreen, kin ji na rantse miki. In har ba ki rabu da wannan yarinyar ba, Allah sai na wulakanta rayuwarki. Bana son hurɗa da ita, in har kika ce za ki ci gaba da hurɗa ita zan yi mummunar saɓa miki, don haka ki sanar da ita kar ta ƙara zuwa mini ofis. Saboda iskanci. Ita tana yawo ta kasa samun mijin aure, ke Allah ya raba da yawo a titi ya baki miji sai ta hure miki kunni."
"Ka yi hakuri zan gaya mata." Ta furta tare da zubowar wasu hawaye a ƙuncinta.
Tsaki ya ja tare da ture ta, ya wuce yana bambami.
Nasreen kunninta take murzawa, saboda ba ƙaramin riƙo ya yi musu ba. Maganganun da sun firgita ta, amma sai dai ba ta tunanin za ta iya sanar mata da kashedinsa, kuma ba za ta iya daina hurɗa da ita kamar yadda ya buƙata ba. Tsananin mamakin rashin tsoron Marwana ya kamata, da har ta iya zuwa har ofis ɗinsa ta yi masa kashedi.
Ko da suka haɗu a makaranta washegari, ba ta yi mata magana ba. Bayan sun tashi daga lecture suna hanyar dawowa gida.
Hira suke yi sosai Marwana tana gaya mata yadda ƴaƴanta yake matuƙar sonta. Da irin darun da take yi masa. Sosai take dariya tana kallonta cikin matsanancin farinciki. Tuni ta fahimci Marwana irin mutanen nan masu sanya mutum cikin farin ciki ko da ba su shirya ba, saboda rabon da ta yi irin dariyar nan ba za ta iya tuna ranar ba.
Marwana dariya take yi sosai tana tuki, tana kallonta yadda take dariya cikin farinciki. Ƙara kallonta ta yi, sannan ta ci gaba da tuƙa motarta cikin kwanciyar hankali.
A lokacin da suka isa inda za ta ije ta. Marwana ta kalleta ta ɗauko.
"Ga shi ki je kici gaba da aiki da shi, domin a yadda na ga Faruk ya razana ba zai hana ki ba."
"Haka kike tunani? Faruk sam ba shi da tsoro."
"In har kina jin tsoronsa ba za ki taɓa ƙwatar 'yancinki ba. Rayuwar aure ba ƙangin bauta bane, domin ya kamata Faruk ya mutuntaki a matsayinki na matarsa kuma uwar 'ya'yansa."
"Ba na son abin da zai kawo mini saɓani tsakanina da shi..."
"Kar ki damu ki karɓa, kuma in sha Allahu, babu abin da zai faru."
"Na gode da ƙaunar da kike mini Allah ya barku tare."
"Tsakaninmu babu godiya domin kin zama 'yan uwa."
Fita ta yi daga cikin motar, tana ɗaya mata hannu har ta ɓace daga gurin.
"Haka Ubangiji yake ikonsa, sai ya haɗa ka da mutanen ƙwarai." Ta furta tana kallon hanyar da ta wuce.
Faruk yana ta shirin aure ba tare da ya sanar da Nasrin ba. Har ana saura sati uku ba ta da labari.
Ta fara zargin ko aure zai yi ganin yadda yake ta gyaran gidan. Hankalinta ya tashi matuƙar gaske. Tana don ta yi masa maganar, amma tana tsoron abin da zai gaya mata.
Wata zuciyar ta shawarce ta da ta yi shiru ta zuba masa na mujiya, don ya fi mata alkhairi kan abin da zai gaya mata.
Faruk kuwa har ya kai kuɗin sadaki, da yake bazawarace ba a wani sanya ranar da tsayi ba. Sosai suke shirye-shirye a tsakaninsu.
Har ana saura kwana biyar bai sanar mata da maganar aurenta ba. Maman Muwaddat ce ta ji zancen bikinsa, wanda ya tayar mata da hankali. Sosai tausayinta ya kamata, duba ga halin da take ciki na zaman aurensa, ina ga kuma ya ƙaro mata kishiya. Ita ba auren ne ma ya fi tayar mata da hankali ba, wacce zai aura. Rashida bayerabiya ce amma ta zauna a cikin Hausawa. Mace ce jarabbiya sam ba ta da hakuri. Ko shi kansa bai san ruwan dafa kan zai ɗauko ba. Sannan ga shi ta girme wa Nasreen don ba sa'arta bace. Ko da ace Faruk zai ba ta shekarun bai wuce ɗaya ko su zo tsara ba. Idanunta a buɗe suke saboda mace ce wayyaya, wacce take cuɗanya da maza, don har sai da abinci a bakin titi ta yi. Daga baya ne da ta auri mijinta, sai da ta mayar da shi matsiyaci, sannan tsuka rabu. Bayan sun rabu ta kafa zawarci. Maza sosai take tatsa, don ko Faruk da fari ba ta yi ninyar auren sa ba. A cewar ta maza mugayen ne mayaudara masu daɗin baki. Mahaifiyarta tasha wuya sosai a gurin mahaifinsu, kafin Allah ya ɗauki kwananta. Su kansu ba su samu kyakkyawar tarbiyya da kula a gurinsu ba. Wannan dalilin ya sa ta ɗauki aniyar tsakaninta da su babu sausauci. Da fari ta yi ninyar shanye ƙwallon mangaro ta huta da ƙuda, amma kuma sai ta ga Faruk ya yi mata. Yana da zubin halitta mai kyau, sannan ga shi ɗan gayu, mai tashe da nera da ƙuruciya. Abin da ya ƙara jan hankalinta yadda yake kushe matarsa da cewar ba ta ba shi kula. Wannan dalilin ya sanya take son aurensa don ta more ƙuruciyarsa, domin har zuwa gurin malaminta ta yi don a karkato mata da hankalinsa. Abu ɗaya ta fara fuskanta game da shi wato maƙo. Duk yadda yake iƙirarin yana sonta, amma ba ya sakin mata kuɗi sosai. A ganinta hidimar da yake yi na bikinsu ya yi mata kaɗan, amma sai ta share ba tare da ta nuna masa komai ba, burinta kawai ta shigo cikin gidansa, yadda za ta samu damar juya shi, ya zamo mata janitalau.
A na saura kwana biyu, Maman Muwadda ta shirya sanar mata da bikin, ganin ranar da ta shiga cikin gidan ba ta yi mata maganar ba.
A ranar da ta je, sai ta tsokane ta don ji ko ta san da maganar, amma sai ta yi murmushin yaƙe ta ce,"Wallahi sai gyaran gida yake yi. Wataƙila aure zai yi, don ya sha gaya mini ba zai zauna da ni kaɗai ba."
Jin hakan ya sanya, a wancan ranar ta kama bakinta ta tsuke, don ba za a ji mutuwar Sarki a bakinta ba, amma daga baya sai ta ga in har ta bari aka yi bikin, kamar ta cuce ta ne.
Bayan ta shiga cikin gidan ta zauna. Nasreen da take zaune a falon tana yi wa Raihan tsifa. Ganin ta ya sanya ta miƙe tana murmushi. "Ban ji ƙwankwasa ƙofar ki ba?"
"A buɗe na ga gidan har na yi mamaki."
"Ikon Allah! Kuma ban san abuɗe yake ba, watakila da na fita siyo ashana na manta na kulle. Kin ga da Abban Rainah ya dawo dai ya zamar mini abin faɗa."
"To ki rinƙa kula." Ta ce mata bayan ta zauna.
"Raihan, tsifa ake yi?" Maman Muwadda ta yi mata tambayar tana shafa kanta.
"Wallahi kuwa, kin san gobe Monday shi ne na ke son muje kitso."
"Haka ne, ni ma can na barsu suna tsifa."
Sun ɗan yi shiru, babu mai magana a tsakaninsu. Nasreen ta fahimci kamar akwai maganar da za ta gaya mata.
Maman Muwadda ta gyara zama, ta buɗe baki kenan ta ji ƙarar motar Faruk yana hon.
Da sauri ta mike jikinta na zikiri. Ganin haka ya sa ita ma ta miƙe."Dama magana na ke so mu yi kuma ga shi ya dawo."
"Ok, in ya tafi zan shigo."
"A'a ki aiko Raihan ta kira ni, don na fi son mu yi ta a nan, zamu fi samun natsuwa."
Gabanta ne ya faɗi jin abin da ta ce."Lafiya Maman Muwaddat, ko laifi na yi miki?"
"Lafiya lau, kuma babu laifin da kika yi mini. Ai tsakanin mu babu wannan, domin da ace kin yi mini laifi zan sanar miki, saboda kamar 'yar'uwa na ɗauke ki."
Tunanin abin da za ta gaya mata yi, amma sai ta kasa fahimta."Ok, to shikenan, zan aiko ta gaya miki. Bari na je na buɗe kafin ya zama rigima."
A tare suka fito. Maman Muwaddat ta fice ita kuma ta buɗe masa get. Kallo ya bi ta da shi har ta ɓule, sannan ya mai da idanunsa kan Nasreen da take tsaye tana jiran ya shigo.
Harararta ya yi, sai kuma ya shigo da motar.
"Sannu da zuwa." Ta ce masa bayan ta buɗe masa motar.
"Nasreen, ba na hana ki shiga maƙota kuma suna na hana su shigowa ba, don kin san bana son gulma da munafunci?.
"Ka yi hakuri Maman Muwaddat ce."
"Ita ɗin fa tun da ba ciki ɗaya kuka fito ba." Ya ƙarashe maganar tare da fita. Gaban motar ta shiga, ta kwashi kayan da ya shigo da ita.
Gabanta ne ya faɗi ganin sabbabin kaya masu tsananin kyau a bayan motarsa. Hannu ta ɗauko tana kallon kayan, duk da cewar ta san yana kashe wa kansa kuɗi, amma ɗinkin da ta ga ya yi sabbabi, sai da suka sanya kanta ya juya, saboda kayan sun yi kala bakwai.
Jikinta babu ƙarfi ta shigo da su. Yana zaune a falo ta shigo da kayan. Ɗakinta ta kai ta dawo ta wuce da cefanen da ya yi musu.
Ƙaramin tsuka ya ja ya shiga cikin ɗakin. Bayan ta kammmala girkin ta ɗauka ta kai masa. Tana ƙoƙarin shiga cikin ɗauki da ta ji muryarsa yana waya. Da sauri ta fasa murɗa ƙofar ta laɓe don ta tabbatar da zargin ta.
Dariya mai sauti ta ji ya yi, sannan ya faɗi wata magana wacce sai da ta ji kishinsa, saboda batsa da ta ji yana yi a cikin wayar. Kalamansa na ƙarshe, ya sanya ta ji kamar za ta faɗi ta kuma fara tabbatar da zargin ta.
"Sai ta shigo gidansa ya kwanta da ita zai tabbatar da ya auri mace? Faruk aure zai ƙara ba tare da ya sanar mini ba?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tashin hankali, yayin da idanunta suka ciko.
"Innalillahi na shiga uku!" Ta ce bayan ta ije tiren abincin kanta na juyawa. Da ƙyar ta samu ta daidaita kanta ta shiga ciki, tunawa da ta yi dama ya sha faɗan, sai ya ƙara aure kuma ga shi har sun ɗauki shekaru bai ƙara auren ba. Ta gaya wa zuciyarta hakan ne don kawai ta yaudareta ta samu kwanciyar hankali, amma cikin zuciyarta tana ƙarfafa mata aure zai ƙara.
Yana wayar ta yi sallama ta shigo. Bai fasa wayar ba, sai ƙasa da murya da ya yi. Ganin haka ta ije masa abincin ta fice cikin tsananin damuwa.
Satan kallonsa ta yi da zata fita. Tana matuƙar son mijinta domin ta ko' ina Faruk ya kai namijin da mace za ta damu da shi. Halinsa ne kawai bai yi ba, na rashin ɗaukar mace da daraja. Ko da yake ba za ta ce baya ɗaukar mace da daraja ba, ita ce kawai ba ya daraja ta, duba ga yadda yake waya da 'yan mata yana kashe murya.Ɗaki ta koma ta zauna sai kawai ta tsinci fashewa da kuka.
Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 12
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Sosai ta yi kuka tana baƙincikin rayuwar da suke yi da Faruk. Tunani take yi wane irin zama za su yi, da matar da zai auro don ta san ya riga ya gama zubar mata da ƙima a gurinta.
Bayan fitarsa ta aiki Raihan ta kira Maman Muwaddat. Ba ta jima ba suka dawo da Raihan. A yadda ta ganta a firgice, ta ɗauka ya gaya mata. Kallonta ta yi cikin tausaya.
"Ina jinki kin ce za mu yi wata magana, kuma na lura ke kanki ba kyau son faɗin maganar." Tausayi ta bata sosai tana mamakin mugun halin Faruk. Haba ai zalunci ne ace zaka yi wa mace kishiya ka ƙi sanar da ita.
"Nasreen, hakuri zan ba ki a rayuwarki. Na san cewa kina cikin wani hali na zaman ki da mijinki, amma yanzu dole ƙi ƙara saboda..."
"Saboda zai ƙara aure ko?" Ta furta tambayar hawaye yana shatata a fuskarta.
Dafata ta yi ganin yadda ta rikice."Ya gaya miki ne?"
"A'a bai gaya mini ba, ji na yi yana waya cewar yanzu zai san ya auri mace. Maman Muwaddat mai na yi wa Faruk, wanda ya zaɓi ya shigo cikin rayuwata ya cutar da ni? Don zai yi aure sai ya sanar da amaryarsa ba ni da ƙima a idanunsa. Da wane ido yake so ta kalle ni. Hakan da yake yi ya ba ta ƙofar da zata ɗauke ni mara daraja a idanunsa. In har ba zai yi mini kayan faɗar kishiya ba, na cancanta ya sanar da ni ko da ace ba zai rarrashe ni ba." Kuka take yi sosai tana ji tamkar zuciyarta za ta fito.
"Ki yi hakuri Nasreen, haka WASU MAZAN suke yi. Ba ke kaɗai aka yi wa hakan ba, domin mata da yawa mazajensu na ƙara aure ba tare da sun gaya musu ba, kuma in suka yi haƙuri sai kiga komai ya wuce. Ki ɗauki kishiyar da zuciya ɗaya kuma ki riƙe Allah."
Sosai take yin kuka tana jin bai yi mata adalci ba. Hawaye ta share tana kallonta."Na gode da sanar mini da kika yi, kuma na gode da shawarki. In sha Allahu zan haƙura na barwa Allah komai."
"Yauwa dama na san za ki jure ki ci gaba da hakuri Allah yana tare dake." Ta ce mata cikin tausayawa. Ta daɗe a gidan tana ba ta baki har sai da ta ɗan ji dama, sannan ta yi mata sama ta tafi.
Tana fita ta ƙara sakin kuka ta shige cikin ɗakinta. Ƙoƙari kawai ta yi ta daure ta nuna mata ta haƙura, amma Allah kaɗai ya san zafin da take ciki. Tayi kuka sosai har sai da ta ji hawayen sun daina zuba, sannan ta haƙura ta ɗauki maganin damuwar ta ta fara karantawa.
Sai da ta ji ɗan dama ta shiga kicin ta ɗora abinci. Tana tsaye a kicin ɗin tun da ta ɗora ruwa ta kasa yin komai. Zuciyarta take tafasa da wani irin abu na kishin mai kama da ƙwallo ya taso mata kuma ya ƙi wucewa. Ita kanta ba ta san tana mugun sonsa ba sai yanzu. Tana tsaye har ruwan ya tafasa.
"Umma ruwan yana tausa." Ta ji muryar Raihan da take tsaye tana rike da hannunta. A maimakon ta wanke shinkafar ta zuba, sai kawai ta ɗauki ruwan zafin ta zuba a cikin ɗanyar shinkafar, ta sanya hannu don ta wanke. Tsananin zafin da ta ji ya farga da ita abin da ta yi. Da sauri ta cire hannunta tare da sanya ƙara tana salati. Hannu ta da ya tashi ya yi ja take dubawa hawaye yana zuba a ƙuncinta.
"Umma, kin ƙone ne?" Raihan ta ce mata tana kallon hannunta.
Tsintar kanta ta yi da rungumeta tana kuka sosai da kuma ƙarfi. Tuna shinkafar za ta iya lalacewa ya sa ya ta yi saurin sakinta ta mayar da shinkafar da ruwan kan wuta. Bisa abin da ya faru kan dole ta tafasa sannan ta zubar da ruwan ta girka abinci. Hawaye kawai take sharewa. Cikin dare da ta kwanta ta kasa bacci. Har ya dawo idanunta biyu.
Saboda haushinsa da take ji bayan ta buɗe masa get. Wucewa ɗakinta ta yi, ba tare da ta kalle shi ba, saboda mugun haushinsa take ji. Raka ta da idanu ya yi ganin yadda take. "Ko an gaya mata ne?" Ya yi wa kansa tambayar cikin rashin damuwa. Tsaki ya yi tare da ɗaga kafaɗunsa alamun bai shafe shi ba.
Shiga cikin ɗakinsa ya yi, bayan ya yi wanka ta fito da naman da siyo, ya ci ya ƙoshi ya kira da lemunsa ya kwanta. Rintse idanunsa ya yi yana ta ayyana surar Rashida da fanshe kuɗinsa da zai yi.
Har ana ɗaurin aure Faruk bai sanar mata ba. A ranar ta ga ya yi wanka ya ɗauki gayu ya fice daga gidan. Tana jin mutane suna kiransa a waya. Bayan ya fita ta fashe da kuka sosai. Tabbas ta tabbata yau za a ɗaura masa aure, don ko bai gaya mata ba, wankar da ya yi ya isa ta fahimci aure zai ƙara.
Tana zaune a gurin tun da ya fita ta kasa motsawa. Kuka take yi sosai tana tausayin kanta, ganin tana rayuwa da mutumin da bai san darajar ta ba. Tunanin zaman da za su yi da amaryar take yi.
Saboda bai sanar mata ba ya sanya babu wacce ta gayyata, don ko 'yan gidansu ba ta sanar musu ba. Kamar yadda bai gaya mata ba, duk wanda ya tambayeta sai ta ce ba ta da labari. Ita ma amarya kawai ta gani. Duk yadda take da Ya Ahmad ta kasa da ar masa, domin ta san babu abin da zai iya mata sai dai ta tayar masa da hankali.
Bayan fitarsa babu jimawa aka ƙwanƙwasa get. Sai da ta wanke fuskarta, sannan ta je ta buɗe get ɗin. Ganin Yarsa Asiya ce ya sanya ta yi murmushin yaƙe."Sannu da zuwa." Ta ce mata ba tare da sun haɗa idanun ba.
Turus ta yi ganin yadda idanunta suka kumbura."Nasreen lafiya? Ko kishin ne ya sanya kika koma haka?" Ta ce mata tana kallon harabar gidan ganin babu alamun ana taro.
Kasa magana ta yi saboda zubowar hawaye. Matsawa ta yi ta ba ta hanya. Ganin haka ya sanya ta tura ƙofar ta shiga ciki.
"Ke Nasreen, lafiya ban ga ana taro ba? Ko ba yau bane ɗaurin auren?"
Tambayar da ta yi mata, ya sanya ya ji kamar ta kwasa mata mari.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 17