kiran S.MAN yashigo wayar Baba,
yana d'agawa ya sinkayo muryarsa yana fad'in
"Tun da ka kasa sata tazo to ni bazan kasa zuwa karb'ar gidana ba, duba takardun gidan ka gani anya suna tare da kai kuwa."
yana gama fad'in haka ya kashe wayar.
da sauri Baba ya mike yaje in da takardun gidan suke adane, wani irin bugawa kirjinsa yayi lokacin da yaga basa gurin.
bincike yashiga yi cikin d'akin ta ko ta ina amma babu su babu alamun su.
ya fito daga d'akin sa yanufi d'akin Mama har yana cin karo.
SEEDRAH dake cikin d'akin tana kad'ewa Mama gado zata kwanta ta mike da sauri ganin yanda yashigo d'akin.
Mama ma mikewar tayi tana tambayar sa lafiya.
Baba ya ce "Ina kuwa lafiya Usman ne yakirani yanzu, na tabbata har idan gobe yasa kafarsa a gidan nan to tabbas munbar gidan nan kenan dan kuwa ina da tabbacin takardun gidan nan suna hannunsa dan basa in da na ajiye su, bansan ta yadda akayi suka shiga hannunsa ba, maganarsa ya tabbatar min da suna hannunsa."
Maganar Mama taji ta na fad'in
"Shike nan SEEDRAH tun da bazakibi maganar mu ba abin da yafi tozarci da cin mutunci Usman zaici gaba da zuwa yana mana tun da haka kika zab'a."
da sauri tashiga girgiza kai tana fad'in
"Zanyi zanyi aikin zanje gidansa nayi aiki a matsayin 'yar aiki dan na kare kima da mutuncin mahaifi na, zanyi."
takuma fad'a tana sakin bedsheet d'in da take shinfid'awa ta fita da sauri zuwa d'akin su.
Wardrobe ta bud'e gefen da kayanta yake ciki ta janyo wani akwati wanda shima nata ne tashiga ciro kaya tana karawa cikin na akwatin cikin sauri, yayin da takejin zuciyar ta ya bushe tangaras ta sawa ranta zataje tayi aiki tukuru dan ta tseratar da mahaifinta daga tozarcin S.MAN bama shi ba har wanin sa.
Suhailat dake zaune tana kallon yadda take tura kaya cikin akwatin, ta yamusa fuska tare da fad'in
"Tun da ke bakya bukatar zuwa basai abar masu bukata suje ba kamar S.MAN zai bukaci aje masa aiki wai kiki zuwa, nifa ko gidan nasa yace nakoma gaba d'aya narika bautatawa gidan ko bazai biyani ba wlh da gudu zanje ganin sa ma kad'ai yabiya kud'in aikin da zan masa."
bata kula ta ba sai aikin tura kayan ta take cikin akwati tana gamawa tarufe ta d'au mayafin ta taja akwatin tayi waje.
A tsakar gida taga su Baba da Mama Umma duk a tsastsaye,
ta dubi Baba ta ce
"Baba na shirya ka kaini."
Baba ya dubi agogon wayarsa ya ce
"Goma da rabi ina ga kamar dare ya yi mubari sai gobe da safe."
kai kawai ta gyad'a taja akwatin zuwa d'akin Mama ranar a d'akin ta kwana.
washegari da sassafe Baba ya d'auketa a mota da kayanta suka d'au hanyar gidan S.Man.
suna isa ya yi hon maigadi ya wangale masa get yashiga ya faka a gefe, SEEDRAH ta fito Baba ya fito tare da ciro mata akwatin ta.
bin gidan tayi da ido wan da tsaruwan sa yakai tsaruwa,
"Ga gida har gida amma babu mutum."
tayi maganar a kasan ranta tare da yamusa fuska a fili tana kuma murgud'a baki, kamar S.Man d'in ne a gaban ta.
Maigadi yakaraso inda suke da sauri suka gaisa da Baba kana ita ma ta gaida shi.
maigadi ya ce
"Oga bai tashiba tukun amma yasanar min da zuwan ku dan haka zaku iya shiga daga ciki, ke ce 'yar aikin ko?."
ya nuna SEEDRAH
Baba ya ce "Eh.eh.. itace eh itace."
kai SEEDRAH tajinjina wato ma tun kan tazo yagama yad'ata wai itace yau ake cewa 'yar aiki.
Baba ya ce
"A'a ita ce zata shiga ni zan koma daga nan tun da yana bacci, maza shiga ciki SEEDRAH, ni zan wuce kasuwa."
kai ta gyad'a maigadi yad'au akwatinta yana gaba tana biye da shi, Baba kuma yaja motar sa ya yi gaba.
Tsintar kanta tayi cikin wani dankararren parlour mai kyau da tsaruwa,
maigadi ya aje mata akwatin ta cikin parlour'n ya na fad'in
"Ki zauna ki jira fitowar Oga."
kai ta gyad'a tana zama kan d'aya daga cikin dankararrun kujerun parlour'n kana maigadi yayi waje yana jawo kofar parlour'n.
a hankali tashiga bin cikin parlour'n da ido sosai parlour'n yatafi da ita matuka ta shagalta da kallonsa.
tana nan zaune tana zuba idon ganin fitowar sa amma shiru, tashafi tsawon awanni biyu zaune amma babu alamarsa.
tsaki takuma ja akaro na sau ba adadi a fili ta furta
"D'an rainin hankali sai kace wani mai sarauta da sai an wani zaman jiran fitowarsa."
kwafa tayi tare da kad'a harshe yabada sauti.
zuwa yanzu ta gaji da zama sai ta gyara kan doguwar kujerar da ta ke kai tad'an kishingid'a.
tana nan zaune harta fara jin kiraye-kirayen sallar azahar, ta mike tare da sakin doguwar hamma had'e da mika tare da yin salati, gajiya junwa duk suke tare da ita.
waige-waige tashiga yi tana niman ta in da bayin parlour'n yake taje tayi al'wala.
can idanunta ya sauka kan wata kofa dake gefe shi kad'ai, ta nufi kofar dan shi take tunanin zai iya kasancewa toilet.
a hankali ta murd'a handle ta tura kuwa taga toilet d'in ne, tsaf-tsaf yake babu datti sai kamshin turaren toilet mai dad'i yake, tashiga tayi al'wala tafito.
akwatin ta tabud'e zaciro hijabi kana ta rufe, ta zare d'ankwalin kanta ta shinfid'a ta gabatar da sallar a kai.
ko da ta idar jingina tayi dajikin kujera tana tasbihi a hankali da 'yan yatsun ta.
idanunta ne yasauka kan kwalin sigari dake kan kujerar da take jingine da shi,
cikin jin kyamar abin ta mike tana yamusa fuska ta d'aga waya da gyalenta dake kusa da shi ta ajesu can gefe.
tad'au rimut d'in t.v da tagani a gun tashiga ture kwalin tabar cikin jin kyama ga yan da take ture abin zaka san bam bata kaunar hannunta ya tab'a shi,
ko da ya fad'o kasa kusa da kafarta tayi d'an tsalle ta masa gefe.
kana ta mika hannunta dake rike da rimut d'in ta tura shi kasan kujera.
aje rimut d'in tayi tare da rike kugu ta sauke numfashi kamar wacce tayi wani babban aiki.
"Mttsss." taja dogon tsaki kana ta koma ta zauna.
zaman ta baifi da minti 5 ba tajiyo taku daga matattakalar bene
a sannu ta waigo da dubanta izuwa gurin.
yana sanye da jallabiya kalar ruwan madara yayi kyau sosai cikin rigar.
da d'an sauri yake saukowa yana kuma duba tsadadden agogon dake d'aure a hannunsa.
yanda yake sauka dasauri cikin zafin nama irin na zaratan maza, lallausar gashin kansa daya sha gyara da wani d'an a don aski irin na 'yan kwallo iska ke kad'ashi yal-yal.
cikin hanzari yakarasa sauka daga step's d'in jin ana fad'in sahuu daga masallacin da ake jiyo sautinsa rangad'au a cikin gidan.
yanufi kofa batare da ya kalli cikin parlour'n ba bare yama san da wata halitta agurin.
SEEDARAH ko baki bud'e tabi bayan sa da kallo cikin takaici tafurta
"Rainin hankali nashafe tsawon lokaci zaune a nan ina zaman jiransa sannan yafiyo ya yi tafiyar sa,wato ma nacigaba da zaman jiran nasa kenan, ai wlh bai isa ba idan ban d'au jakata nayi gaba abina ba."
d'an shiru tayi tana tuna tofa idan ta tafi tafiyar nata zai shafi Baba, da tunanin nan takuma gyara zaman jiransa.
S.MAN bai shigo gidan ba sai wajen karfe 2 na rana, tana nan zaune cikin parlour'n ya turo kofa ya shigo.
a sannu yatako izuwa cikin parlour'n
ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta,
kafarsa d'aya ya d'aga ya d'aura kan d'aya.
yayin da ya maida bayan sa jikin kujerar yashiga kad'a kafar a hankali.
kana ya d'au rimut ya kunna t.v tare da mai da idanunsa kan t.v
SEEDRAH ta cika har wuya kiris ya rage ta fashe ganin rainin hankalin nasa nason yin yawa yaganta sarai bawai bai gantaba amma yayi buris da ita kamar baisan da wata halitta agurin ba.
kwafa tayi a fili tad'an ja guntun tsaki kana ta ce
"Kafad'i abin da za'ayi maka idan kuma babu na tattara nayi gaba abina."
yatsa ya d'aura kan bakin sa ya ce
"Shiiiiit ni zan yi magana ba ke ba dan nan fadata ce........"!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 12
Zaman sa ya gyara tare da kuma maida idanunsa kan t.v yana cigaba da karkad'a kafa.
SEEDRAH ko kallon shekeke tabisa da shi tare da yamutsa fuska.
sai da ya d'au tsawon mintuna 20 zaune batare da ya kuma cewa komai ba ya yin da idanunsa kuma ke kan t.v har lokacin.
kamar an zamure sa ya sauko da kafarsa saman lallausar carpet d'in dake malale tsakiyar parlour'n, yazamo bakin kujerar da yake kai yashiga nunata da yatsa sannan yasoma magana cikin kakkausar murya
"Tun da nake babu wani wan da yatab'a tsayuwa a gabana yana fad'a min son ransa a kaina sai ke da bakifi cikin kokali ba,
ko uban naki bai isa ya tsaya gabana ya yi gigin gayamin bakar magana ba,
shiyasa nasashi da kansa yakawo min ke domin nakoya miki tarbiyya dan naga karancin sa atare da ke,
me ma kika ce?, d'an shaye-shaye ko!."
yafad'a cikin tsawa da har sai da ta d'an zabura ta matsa baya.
hannu yacigaba da nunata da shi ya yin da yakad'a yatsun sa suka bada sauti
"Zan nuna miki halin d'an shaye-shaye sai na kunttatawa rayuwar ki sai kinyi danasanin kasantuwar ki a yanzu,
sannan ki sawa ranki bakima sanni ba babu wata alaka sakani na da ke, ke kawai 'yar aiki ce a gidan nan."
Tarazana da jin kalaman sa sai dai sam bata bari ya fahimci hakan ba, tayi kokarin kawar da tsoronta ta hanyar tattaro jarumtarta had'e da tsiwar ta ta shimfid'a su kan fuskarta.
Kafad'a ta d'aga alamun ko oho
kana ta wasa masa wani kallo sannan ta ce
"Kada kayi gigin aibanta mahaifina a gabana dan ko wuka aka kawo sa kan wuyata bazai bani tsoro na lamunce cinmutunci wa mahaifina ba,
tarbiyya kuwa nasame sa dai-dai gwargwado sai dai godiyar Allah shiyasa ma nake tafe da albarka ta,
yaushe tarbiyyar ta ishe ka da zaka bani,
kaima bawata tarbiyyar bace gare ka,
da kana da ita da bazaka rika aikata irin abubuwan da kake aikatawa ba,
sannan kuma ni dama ban sankaba idan dama dawata alaka na dangantaka sakanin mu kajima da warwareta tun ranar da na fahimci rashin darajawarka ga mahaifina, babu wata alaka sakanin mu kai da ni da duk wad'an da mukafito uba d'aya kamar bare ne wad'an da ke tafe a kan titi, kaga babu wata alaka sakanin su,
gidan nan kuwa nazo ne amtsayin 'yar aiki zanyi aiki tukuru domin dawo da kimar mahaifina,
zan yi aiki a karkashin ka ta hanyar biyana albashi karike kud'in da kake bin Baba."
Wani irin murmushin takaici ya sake a zafafe ya mike tsaye ya d'aga kafa zaiyi ball da ita, sai kuma ya fasa, ya tsunkuyo tare da shako wuyarta da karfi, har sai da idanunta suka firfito,sannan yasoma magana cikin huci
"Zan azabtar da ke ta yadda idan nayi magana baki isa ki amsa min ba!,
a karamin tunanin ki kina sammanin ko shekara goma zakiyi kina min aiki zai fanshe kud'in da nake bin Alhj Musa ne,
million 30 nake binsa ba dubu talatin ba!!."
D'an sassauta shakar da yayi mata ya yi ganin yanda take ta fafutukar neman numfashi, kana yazare hannunsa a wuyanta tare da angizata tagaru da jikin kujera.
SEEDRAH kuwa da gab'aya ta d'auke wuta tayi saurin dafe wuyanta inda take ji kamar ba a jikin ta yake ba dan tsananin azaba, ta janyo numfashi dakyar tana mai da shi.
Cikin muryar fushi sosai ya ce
"Sai na rage miki numfashi duk ran da kika kuma tsayuwa a gabana kina fad'a min maganganun da suka fito daga karamin kwakwalwar ki!."
ya juya da sauri yanayin yadda yake taku kad'ai zai tabbatar maka da fusatar sa afili dan hatta cikin parlour'n amsa sautin takunsa yake, dip-dip-dip! haka yake tafiya kamar namijin zaki cike da KARSASHI!.
can gefe cikin parlour'n in da
na'urorin motsa jikin sa suke ya nufa,
cike da zafin nama yashiga wujijjiga jikinsa bisa na'urar yad'au tsawon mintuna 30 kafin ya sakaita motsa jikinsa ya sauka.
fridge dake zaune gefe a gurin ya bud'e ya d'au gorar ruwa mai sanyi, kan kujerar silve da suke jere a gurin ya zauna yabud'e gorar tare da d'aura shi kan lips d'in sa.
saida ya shanye ruwan duka kafin ya d'ago gorar tare da yin wurgi da shi cikin parlour'n.
numfashi yashiga maidawa a hankali yayin da yake share gumin da yake tsastsafo masa da wata karamar towel,
ya zaro sigari a aljuhunsa ya kunna yashiga zuka da d'an sauri-sauri.
A razane SEEDRAH ta d'ago jin fad'uwar abu dan har lokacin tana cikin tsoro, bakin nan nata ya mutu musurus sai zazzare ido take, dan har lokacin bata dawo hayyacin ta daga shakar da yayi mata ba.
yad'au tsawon mintuna 10 zaune sai a lokacin yaji zuciyarsa ya d'an sanyaya.
ya mike a sannu ya jefar da ragowar sigarin hannunsa saman wani table dake gurin, kana ya tako cikin parlour'n,
ya zauna kan kujerar da d'azu ya tashi.
kasa tayi da idanunta,
shiko murmushi mai sauti ya yi tare da shafa d'an karamin gemun sa irin wan da 'yan kwallo suke bare,
"Gargad'in ya shigeki kenan bakiga komai ba ma tukun."
ya yi maganar idanunsa a kanta.
lumshe idanunta tayi tare da kuma bud'e su a lokaci guda tad'an tauni gefen lips d'in ta.
magana ya soma ya yin da idanunsa ke kanta
"Gargad'i game da aikin gidan nan ina mai tabbatar miki da duk randa nasami wata kusku ranar zaki fuskanci fushi na,
kaf fad'in gidan nan daga sama har kasa kama daga cikin kowani bedroom's da bathroom's zuwa parlourn sama da kasa zaki rika gyara shi akowata safiya da maraice, girki safe rana dare,
wankin kaya, sharar farfajiyar waje baiwa fulawa ruwa wankin mota, sune aikin ki,
sannan kuma da karfe 11 nake tashi daga bacci kuma ina tashi nake bukatar abin da zansa wa cikina, kada ki kuskura lokacin ya wuce batare da kin tana da min abinci na ba,
sannan kuma brekfast a sama nakeyi sauran lokutan cin abinci kuma a kasa,
da karfe 11 nan kuma ki tabbatar da kinzo kin gyara min d'aki zuwa bathroom d'ina kafin gyaran kawani bedroom's,
idan kika kuskura aka sami matsala aduk cikin abun da na lissafa mikin nan to ina mai tabbatar miki
Alhj Musa shi zai fuskanci matsala!,
karfe 11 kin gama komai ko minti 1 kika kara a kai to kiyi kuka da kanki."
Shiru tayi tana nanata ayyukan daya lissafo mata a ranta, sai kace tazamo jaka to ma taya zatayi ta iya duk wad'an nan ayyukan daga asuba zuwa karfe 11,har da aikin da yakamata mazane suyi duk dasu zatayi.
kai ta jinjina zatayi bauta ko dun ta tseratar da mahaifinta daga tozarcin S.MAN.
Maganar sa tajiyo yana fad'in
"Da nayi niyyar can waje kusa da d'akin karnuka zaki zauna kirika shigowa kina aikin,to amma kinci albarkacin zan iya bukatar abinci cikin dare dan haka ga d'aki can kishiga kizauna ciki."
ya nuna d'aya daga cikin d'akunan cikin parlour'n.
kwayar idanunta ta juya izuwa kofar d'akin da yake nuna mata kana ta dawo da kallon ta a kansa sannan ta ce
"Nawa ne albashin aiki na?."
"Me yasa sai kin sani."
"Ko aikin gwamnati kaje nima ka samu ana sanar maka da iya albashin da za a rika baka, ka d'auka hakanne,
zan fara lissafi daga kan yau da zanfara aiki, nakuma san adadin hakkina da za a rika cirewa cikin bashin da kake bin Babana."
ido ya bita da shi wato bakin ta dai bazai tab'a mutuwa ba. ya ce
"Idan kika masa da tambaya amsar ga Alhj Musa zai isa, tashi ki b'ace min da gani, ki kai jakarki ciki kifito da shirin fara aiki."
bata kuma magana ba jin ya sanyo Baba cikin maganar tasan ba mutunci gareshi ba sai ya iya zuwa yaci mutuncin Baba.
ta mike a hankali taja akwatinta tanufi kofar d'akin daya nuna mata.
ta tura kofar a hankali takusa kanta ciki, a hankali tashiga takowa cikin d'akin yayin da take bin d'akin da kallo.
d'aki ne babba komai na bukata yana ciki,
kama daga lafiyayyen gado babba da wardrobe wan da yacike b'arin bango guda, a gaban gadon wata kujera ce ta alfarma t.v manne jikin garu-bango yana fuskantar gado ga fridge a gefe bedside da ramb'asheshen mirro, da dai sauran su.
kayan d'akin duk irin na kasar waje tsaruwar sa yakai tsaruwa,
sai dai d'akin yad'anyi kura alamar dai babu mai rayuwa cikin sa.
a hankali ta isa ta aje akwatin ta kana ta cire mayafin kanta.
nan ta shiga kad'e d'akin ta gyara shi tsaf ta goge ko ina, kana ta sauya zanin gado data gansu jere cikin wardrobe dan na kan gadon shima yayi kura.
ta d'auki wan da ta ciren ta shiga bathroom dan ta wanke, nan ta tadda washing machine ciki, shima kansa bathroom d'in abin kallo ne dan kuwa yasha kayan alatu kamar ba band'aki ba.
da washing meshing d'in tayi amfani wajen wanke bedsheet d'in,
takuma yi amfani wajen busar da shi da goge shi, kana ta wanke bayin tsaf, sannan tayi wanka tare da d'auro al'wala ta fito.
tana fita ana kiran sallar la'asar tagabatar.
ko da ta idar akwatinta ta bud'e ta ciro kayayyakin ta tashirya su cikin wardrobe dan tagama sawa ranta zatayi zaman aikin da zata fanshi mahaifinta duk wuya duk rintsi.
tana saka akwatin cikin wardrobe taji ana bugun kofa sai kuma muryarsa data jiyo ya na fad'in
"Ba kwanciya yakawo ki gidan nan ba maza ki fito."
tsaki ta ja ta ce
"Sai kace kwanciya akace masa nayi."
Ko da ta fito parlour baya nan ciki, nan ta shiga tunanin ta in da zata fara.
nan ta talub'o kichin ta shiga
tasoma kiciniyar d'aura girki cikin awannin da basu fi uku ba ta shirya lafiyayyen girki, kan kace me gaba d'aya gidan yakaure da kamshin daddad'an girkin ta.
S.MAN da tun fitar sa bai dawo ba sai daf magriba yana sanya kafarsa cikin parlour yashaki wani daddad'an kamshi ba shiri ya lumshe idanunsa yana mai dad'a shakar kamshin.
SEEDRAH nagama gyara kichin d'in ta tarkaso kulolin data shirya abincin ciki tafito.
jin karar bud'e kofa yasashi bud'e idanunsa tazo tawuce ta gaban sa zata ta nufi dinning. ya ce
"Ke-ke-ke tsaya waya baki ikon girka abin da kikaga dama batare da kin tambaye ni ba, me ma kika girkan tukun?.
cigaba da tafiyar tayi batare da ta tsaya ba ta ce
"Idan kazo ci zaka gani ai."
ta haura dinnig ta aje tray'n data jero kulolon ciki, gani ya dumfarota da sauri yana fad'in
"Ke ni kike cewa haka?." da sauri ta sauko daga kan dinning d'in ganin yana ta kokarin zuwa inda take yana kokarin cafko ta aiko da sauri cikin had'awa da gudu tashige d'aki ta mai da kofa ta rufe.
numfashi ta sauke tana fad'in
"D'an rainin hankali kabar kakuma sa hannu a jikina."
Shiko bayanta yabi da kallo tare da yin kwafa ya haura dinning, in da kamshin girkin ke ta fisgarsa.
kular farko ya bud'e wani kamshi ne yabigi hancinsa babu shiri ya lumshe idanunsa ya yin da yaji yunwar cikin sa yad'a karuwa.
had'edden jalof ne dayaji busasshen kifi da nama da kayan ganye sai fidda sihirtaccen kamshi yake.
d'aya kular ya bud'e ferfesun kaza ce dataji kayan d'and'ano dana kamshi, tanuna luguf.
sai kofi mai d'an girma mai d'auke da kunun aya mai sanyi a ciki.
da d'an sauri ya zauna dan ba shakka yunwar cikin sa ta motsa.
sosai yaci abincin cikin matukar jin dad'in sa, yana ci yana tsiyayar kunun ayar nan yana korawa da shi.
sai da yacika cikin sa tam sannan ya mike yad'au kular ferfesun kazar had'e da kofin kunun aya ya haura sama da shi..
SEEDRAH kuwa bata kuma fitowa ba sai wajen karfe goma na dare nan ma sai da ta tabbatar da babu motsin sa cikin parlour'n.
ta wuce kitchin ta zubo abinci ta koma d'aki.
tana gama cin abincin kiran Kamal ya shigo wayarta ta haye gado suka shiga soyawan su...
Washegari tana idar da sallar asuba ta fito
can gurin motsa jikinsa ta hangosa yana ta faman gudu bisa na'ura.
hararar bayan sa tayi a fili ta furta
"D'an wahala kamar wanda akasa dole Allah ubangiji yasa ka fad'i ka karya kafa da kugu, ko idan kazo d'aga wancan katon karfen yafad'o ma a kirji."
takarashe maganar da jan guntun tsaki had'e da murgud'a baki kamar yana gaban ta.
ta shige tafara aiki.
gyaran parlourn kasa ta fara zuwa cikin bedroom's d'in cikin parlour'n kana ta wuce kitchin tashiga kiciniyar had'a brekfast.
tana kammalawa tashirya masa nasa kan tray, da sauri ta nufo waje ganin lokaci nata tafiya.
ko da ta fito daga kitchin baya gurin motsa jikin, da sauri tashiga haurawa kan steps har ta kai karshe, kana ta bud'e kofar dazai sadata da parlour'n sama da sallama ta shige ciki.
cak ta ja ta tsaya bakin kofar.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 13
Ganin tsaruwan parlour'n mai kamada aljannar duniya shi yasata jan burki a bakin kofar.
idanunta ya sauka kan katon hoton sa da ke manne jikin garun parlour'n yana sanye cikin kayan kwallo, a tsakiyar filin kwallo ya d'aga kafarsa zaiyi shot da ball aka d'aukesa a hoton, yayi matukar kyau sosai.
idanunta ta janye daga kallon hoton nasa da kuma tsararren parlour'n nasa.
sai kuma ta d'an batsar tana tambayar kanta to ma ina wani abun burgewa a wannan gida da mai gidan yakansace mutum mara d'a a.
taja gajeren tsaki kana tasoma takowa izuwa cikin parlour'n.
ta isa ta aje tray d'in saman table d'in sakiyar parlour'n.
nan tasha d'ammara da gyalenta ta shiga gyara parlour'n.
cikin mintuna kalilan ta tsaftace shi tas duk da dama dai bawani datti yayi ba.
tana gama gyaran parlour'n tad'ago ta na kallon kofofin bedroom's guda hud'u dake d'auke cikin parlour'n tana tunanin ta in da zata fara,
idanunta ne yatsaya kan d'aya daga cikin kofofin
wanda dizainin d'in kofar ma daban ne.
anyi rubutu ajikin kofar wan da ga dukkan alamu ba mannashi akayi ba da shi aka kera kofar.
ido tad'an tsurawa kofar tana son gane abinda aka rubuta duk da da manyan harufa akayi rubutun sai dai d'aya cikin d'aya akayisu,
kuma da yanayin kwalliya idan ma ba ka luraba zakayi zaton kwalliya ce kawai.
bata kaiga tantace ma'anar rubutun da take ji da wuya ma ta iya gane abin da ake nufi a ka bud'o kofar.
waya na sakale a kunnensa yana magana, sanye yake da singilet da 3qrt ya karaso cikin parlour'n, lokacin da yake sauke wayar a kunnen sa.
zama ya yi kan kujerar dake kusa da table d'in
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 19