jiki."
Nasiba ta d'an zuge zip d'in rigarta ta baya kad'an tana kiciniyar cire mata bra,
ita kuma ta d'ago hannu da sauri tana kokarin susa in da taji yana kuma mata kaikayi, ai ko 'yankunnen ta ya rike gyalen ta data d'ago hannu sama gyalen yakuma rufe mata fuska.
kiciniyar raba gyalen da 'yankunnen take tana fad'in
"Wayyo nikam na shiga uku, Nasiba yi sauri ki ciremin dan Allah."
Nasiba na gama b'alle mata ma b'allin bra'n ta zaro shi ta bayan tana mata dariya ganin yan da take yi kamar zata tuma tsalle, sai bubbuga kafa a kasa take tana kuma kokuwa da gyalen daya rufe mata fuska ga kuma 'yankunnen ta daya rike gyalen ta gam tana ta kiciniyar rabasu.
dai-dai lokacin da Nasiba ta zaro bra d'in wani saurayi daya fito daga cikin shagon da suke tsaye gefen sa ya hasko su da hasken tocilan wayan sa.
"Su waye anan?."
ya fad'a yana zuwa in da suke, da sauri Seedrah ta cire 'yankunnen gaba d'aya ganin bazata iya cire shi jikin gyalen ba, ta had'o da gyalen ta rike shi a hannunta.
baya ta shiga ja ganin saurayin na dad'a masosu bai kuma fasa kashe musu toci a ido ba.
"Ku tsaya a nan!." yafad'a yana mai cigaba da masosu, ai sai suka juya suka rufa a guje, Nasiba ta yadda bra d'in hannunta a kasa Seedrah ma tayi wurgi da gyale da 'yankunnen ta a gurin, suka rufa a guje, da iya karfin su suke gudu ganin shima ya rufa musu baya a guje,
ta bayan layin suka shige a guje ta gurin kuma babu hasken wutan nepa sai dai farin wata daya dad'a kara haske sakamakon ruwan da aka d'auke sai d'an yayyafi kad'an-kad'an.
Shiko wannan saurayi mai suna Kamal dake biyo su ya tsaya tare da juya wa da sauri ya koma bakin kofar shagon,
ya d'ale mashin d'in sa dake fake a gun, cikin d'an d'aga murya yadubi wani dake tsaye bakin shagon ya ce
"Mukhtar d'auko mashin d'in ka kazo mu bisu sun gudu, irin 'yan iskan 'yammatan nan ne suke so su kawo mana iskanci unguwa."
yana gama fad'a yaja mashin d'in sa da sauri, Mukhtar ma ya rufa masa baya a kan nashi mashin d'in.
A b'angaren su Seedrah kuwa ganin ya daina biyo su, suka tsaya suna mai da numfashi,
Seedrah data dafe kirji cike da tsoro ta ce
"Kai Nasiba Allah ya rufa mana asiri anya wannan ba mahaukaci bane?, daga ganin mutane ka kama binsu."
Nasiba ta ce
"Ko kuma 'yan iskan layi ba."
bata kai ga rufe baki ba suka ji karan mashina a bayan su,
"Gasu can sune mu bisu."
sukaji an fad'a ai ko suka kuma zurawa a guje, suka sharo wata kwana.
kasan cewar su suna mashin su Seedrah kuma suna kafa, ganin suna daf da cin musu, ai ko suka nufi cikin wasu gidaje biyu da suke hango su.
Nasiba ta shiga gida na farko wan da gida ne da ake gina shi ba'a karasa ba, amma ta ciki an gama komai har da rufe.
Seedrah kuwa tsabar tsoro gaba ta kara a kid'ime ta shiga wani gida a guje.
mutanen gidan suna zaune a sakar gida ta fad'o ciki tana sauke numfashi, a birkice take fad'in a taimake ta wasu ke binta. wata mata dake zaune
ta mike tana fad'in,
"Shiga nan." ta nuna mata d'aki, ai ko da gudu ta shige ta d'ale kuryar gado ta dukun kune tana b'ari da maida numfashi.
A waje kuwa Kamal ne ya sai da mashin d'in sa dai-dai kwanan lungun da su Seedrah suka shigo, yana ta d'an waige-waige.
Mukhtar daya iso in da yake ya ce
"Ina suke sun gudu ne?."
Kamal ya kalli gida na farko da suke tsaye a kusa da shi, ya ce
"Naga shigan d'aya nan gidan bita ciki d'ayan ce dai ban ga ta in da tayi ba, amma nasan ita ma tana nan a nan eriyan bari na dudduba tacan."
ya sauko a mashin d'in ya kunna tocilar wayar sa yashiga haska gefe da gefen lungunan gurin.
Mukhtar kuma yashiga gidan da Nasiba ta shiga.
A can cikin gidan da Seedrah ta shiga, matar da ta ce ta shiga d'aki ne ta biyo ta cikin d'akin, ganin yan da take ta kakkarwa ta iso bakin gadon tana fad'in
"Wai su wa suka biyo ki ne taso ga jikin ki duk a jike ai duk abunsu baza su biyo ki cikin gida ba kam yanzu, zo ki cire kayan nan sanyi zai shige ki."
ta mike tana rarraba ido cike da jin tsoro wan da har yanzu tsoron bai bartaba ta zamo bakin gadon,
tana fad'in "Haka kawai suka biyo mu daga ganin mu muna tsaye."
matar ta miko mata wasu kaya ta ce
"Saka wad'an nan kicire jikakkun, mata san mu na yanzu ai sai Allah, musamman zauna gari banza suna nan suna harin 'yammata a hanya Allah ya shirya."
kar b'ar kayan tayi, matar ta fita ita kuma ta shiga tub'e jikakkun kayan jikin ta ta saka wad'an da ta bata har da hijabi data had'a mata da shi.
tana gama sakawa matar ta shigo ta ce ta fito taci abinci,
jiki a sanyaye ta fito dan har lokacin jikin ta bai fasa b'ari ba ga tunanin ta da gaba d'aya yanzu ya koma kan Nasiba, fatan ta d'aya Allah yasa ta sami mafaka kamar yanda ta samu.
a bakin kofar matar ta zauna kamar yanda matar tace mata,in da suke zaune suna cin abinci.
wata budurwar yarinya ce dake cin d'anwake ta turo mata plt d'in gaban ta tana fad'in
"Muci tare."
murmushi Seedrah tayi kana ta saka hannu cike da jin sha'awar d'anwaken wan da yaji mai da yaji da kuma kayan ganye, suna ci yarin yar tana d'an jan ta da hira.
Sallama a kayi aka shigo gidan, matan gidan suka amsa, ya karaso ciki yana fad'in
"Maman Zeey nazo cin tuwon dare, amma idan ba Zeey bace tayi."
murmushi Maman Zeey tayi ta ce "To bismillah da kaina nayi abi na yau."
budurwar da suke cin d'anwake tare da Seedrah tayi murmushi da fad'in
"Yau Mama ita tayi abincin ta da kanta nima kuma nayi nawa daban duba ka gani Ya Kamal d'anwake na girka abina."
karamar dariya yayi ya ce
"To gaskiya Zeey a zubo min d'anwaken nan dan naga alama zaiyi dad'i ga yan da kuke ta kai loma."
yayi maganar yana zama kan dakale gefa da su Zeey d'in.
Zeey ta ce "Ah haba Ya Kamal kai da kace ban iya abinci ba sai jagwalgwale, ai ina jin ku jiya kuna gulma ta kai da Ya Mukhtar wai ban iya abinci ba, ai zan ga kalar matar da zaku auro."
gefen fuskarsa ya shafo ya ce
"Ai kuwa zaki gani sai wacce tayi digiri a makarantar koyon girki, ke dai zubo min d'anwaken nan naji ko ma yayi dad'i ko ganin sa kawai nake a ido kamar zaiyi dad'in."
Zeey ta mike ta nufi kitchen tana fad'in
"Kad'an zan zuba maka dan nasan yanzu zaka kushe."
Seedrah da tun shigowar sa kanta yake kasa jin muryar sa da yayi sallama yasa gaban kirjin ta yanke wa, dan muryar yayi mata kama da na d'aya daga cikin wad'an da suka biyo su.
Zeey ta kawo masa d'anwaken ya gyara zaman sa tare da d'aukar cokalin data sako shi cikin plt d'in d'anwaken yana fad'in
"Bari muji ko yau anyi abin kirki."
yakai d'anwaken bakin sa, Zeey ta ce "Ni dai Ya Kamal in kasan kushe min girki zakayi kaci na Mama kawai."
"Ki dai tsaya yagama bin cikin baki na tukun zan fad'a miki in ma yayi dad'i ko baiyi ba."
Maman Zeey kam dariya tayi tana mikewa ta shige d'aki, dan ta saba jin rigimar su a kan abinci shi da Mukhtar idan Zeey d'in ce tayi girki zasuci kuma sun rika kushe wa kenan wai bata iya ba.
Loman d'anwaken yakuma kaiwa bakin sa kana ya dubi Seedrah da har lokacin kanta na kasa bata kuma yi magana ba, ya ce
"Wai wace ce wannan ita kurma ce?."
Zeey ta ce "Bakuwa ce kai Ya Kamal wannan kyakkyawar tayi maka kama da kurma ce."
ya ce "Da alama, a kwai kyan d'an maciji ai dan ni tun zama ta banji tace kala ba."
d'agowa Seedrah tayi suka had'a ido da shi, plt d'in d'anwaken ya tura gefe, ya kara hasken gurin ta hanyar kunna tocilan wayar sa ya d'ago wayar ya haska fuskanta
da shi.
ya ce "Ke ce?, dama hasashe na ya bani nan kika shigo."
mike wa Seedrah tayi a d'an hatsale dan kallamar dayiyi amfani da shi wajen jifanta da kalmar k'yan d'an maciji, ya sosa mata rai.
ta ce "Eh ni ce!." sai kuma ta saka takalmin ta ta soma tafi ta nufi kofar fita, shima ya mike da sauri yabi bayan ta.
Zeey kam baki ta bud'e tana kallon su har suka fice a gidan.
suna fita yayi saurin ruko hannunta gam ya ce
"Dube ki kamar wata mutumiyar kwarai wai a dole kin saka hijabi ta in da baza'a gane ko ke wace ce ba, wuce muje sai kun fad'a min daga ina kuka shigo mana unguwa kuna son baje k'olen iskancin ku a nan."
hannunta ta fizge da karfi ta ce
"Ina 'yar uwa ta take wlh duk abin da ya same mu kuyi kuka da kanku."
ta juya da sauri ta nufi gidan da d'azu taga Nasiba ta shiga sabo da birkicewar da tayi ita kuma tayi gaba.
yabiyo bayan ta da sauri.
da sauri ta shiga gidan tana kiran sunan ta, kasan cewar gidan babu mutane ciki babu ko hasken wutan nepa, tsayuwa tayi ganin gaba d'aya gidan da duhu, lokacin shikuma ya karaso in da take, gurin yad'an yi haske sakamakon hasken wayar sa da ya ke kunne.
shesshekan kuka suka jiyo a cikin wani d'aki, da sauri har suna rige-rigen suka shiga cikin d'akin,
Nasiba suka gani kwance a kasa jikin ta a rufe da zanin ta daga cikin ta zuwa cinyoyin ta, ga kuma pant d'in ta a gefe, idanunta yayi luhu-luhu da alama taci kuka dai ta koshi, sai fidda shesshekan kuka take irin na wan da ya gaji da kukan wahala.
hankali tashe Seedrah tayi kanta tana girgiza ta da fad'i.
"Naseeba me ya same ki me ya faru da ke?!."
tayi mata tambayar da karfi cikin matsanan ciyar tashin hankali, tana mai ci gaba da girgizata da kokarin d'ago ta daga kwancen da take.
Jiki a d'an sanyaye Kamal ya zubawa Naseeba ido, kana ya kai duban sa ta kasa gurin cinyoyin ta da zanin yad'an yaye yayi sama.
ido yakuma ware wa da karfi a kanta ganin jini a jikin cinyanta, dasauri ya janye idanunsa tare da rufe idanunsa ya damke su da karfi, a fili ya furta
"Ya salam!."
sai a lokacin Seedrah ta lura da halin da take ciki, lokacin da ta janyo ta ta d'ago ta zaune sai taga zanin ta ba'a jikin ta yakeba sannan kuma babu pant a jikin ta gashi a gefen ta, ga kuma jini na fita daga gaban ta, Naseeba sai yarfe hannu take tana fad'in
"Wayyo Allah na."
wani irin kuka Seedrah ta fashe da shi cikin tsananin kad'uwa da firgicin gano halin da kawar tata take ciki, cikin muryar kuka take fad'in
"Waya miki wannan aiki Naseeba wayyo Allah mun shiga ukun mu."
mikewa tayi da sauri ta rirrike rigar Kamal dake tsaye idanunsa a rufe yana jin kansa nayi masa wani irin mugun nauyi.
cikin muryar kuka sosai tashiga bubbuga kirjin sa da hannayen ta duka biyu tana fad'in
"Me tayi muku zakuyi mata irin wannan zalincin mene ne gamin ku da mu da zaku rika bibiyar mu, me yasa zaku zalince mu ku biyo mu ku idda mummunar nufin ku a kanta?,
kun cutar da ita cuta mafi muni,kun zalince ta kun raba ta da abu mafi muhimmanci a rayuwar ta, to ina amfanin nawa tun da na kawa a miniya ta ya salwanta, nima kuyi min fyad'en gani a gaban ka kayi min babu amfanin nawa budurcin tun da kuka illata nata."
kuka sosai take tana bubbuga kirjin sa.
Kamal yakuma rumtse idanunsa yanajin yanda kalaman ta da kukan ta ke dukan kwakwalwar sa.
Seedrah kuwa hijabin jikin ta ta shiga kokarin cire shi tana cigaba da fad'in
"Jiran me kake kayi gaggawar yimin fyad'en nima azzalumai ma ha'inta tun da abun da yasa kuka biyo mu kenan."
hannunta Kamal ya rike da sauri batare da ya bari ta cire hijabin ba, gaba d'aya lissafin sa ya jagule bai san ta yan da akayi aka aikata mata wannan aika-aikan ba.
Ya ce "Wlh ba abun da yasa muka biyo ku ba kenan, dana ganku a tsaye kuna tab'a junan ku wlh nayi zaton irin 'yan iskan titi nan ne, da kuma na biyo ku naga kun gudu sai na dad'a gaskata hakan a raina, shi yasa muka biyo ku, amma wlh bada mugun nufi muka biyo ku ba, sabo da yawai tan irin wad'an nan 'yan titin masu shashanci shine muka kafa kwamiti duk wan da muka gani bamu yarda da shi ba mukan tuhume shi musan gaskiyar sa, shi yasa muka biyo ku domin sanin ko ku suwaye."
wasu zafafan kwalla ta share
ta ce "Kwamitin yiwa 'yanmata fyad'e? ai ba 'yan titi bane 'yan'iska kune manyan 'yan'isakan, kun san me ya saida mu a gurin?."
sai kuma ta kuma sakin kuka mai d'aci ta ce
"Tai mako na take, ni na ce ta cire min rigan ciki na sabo da ruwa daya tab'a ni yake min kaikayi."
juyo wa tayi ta sunkuya hawaye na cigaba da wanke fuskarta ta taimakawa Nasiba ta mike tsaye ta gyara mata d'aurin zanin ta.
ido Kamal ya zubawa wani agogon daya fad'o kasa lokacin da Nasiba ta mike tsaye,
ya sunkuya tare da d'aukar agogon yana juyashi a hannunsa,
a kasan ransa ya furta
"Mukhtar me yasa zakayi haka!!.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690734_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️3
Hannun Naseeba SEEDRAH ta ja tana hawaye ita ma tana hawaye, da kyar Naseeba take iya d'aga kafar ta sabo da azaba, har suka fice cikin gidan.
jiki a sanyaye Kamal yabiyo bayan su.
SEEDRAH ta dube ta cike da matukar tausayawa ta ce
"Naseeba ki daure mufita bakin titi mu sami abin hawa ya kai mu gidan goggo tun da duk bamu fito da kud'i ba idan mukaje gaggo sai ta biya sa, duk da babu nisa gidan daga nan amma nasan bazaki iya tafiya da kafa ba, dan Allah kiyi hakuri Naseeba duk ni na janyo miki da bance mu tafi ba da duk haka bata faruba."
takarasa maganar tana mai dana sanin cewa su fito cikin daren nan.
da sauri Kamal ya iso su ya ce
"Ina ne zaku je kuzo na sauke ku in da zakun, kin ga tafiyar wahala yake bata."
wani uban harara SEEDRAH ta banka masa, kana ta cigaba da jan Naseeba da ke d'aga kafa a hankali kamar mai koyon tafiya, sai yarfe hannu da zubda kwalla take cikin jin azaba.
gaban su yasha da sauri ya ce "Da dai kin tsaya na sauke ku tana bukatar taimako."
a hatsale SEEDRAH ta ce
"Bama son taimakon naka ku har wani taimako kuka iya ban da zalunci, ma ha'inta wlh zakuga karshen ku."
kai ya girgiza ya ce "Eh..Eh naji amma dai dan Allah kibari na kaiku duba fa kiga yadda take tafiya tana bukatar taimako kibari a taimake ta, kiyi hakuri zo ki hau mashin d'in na sauke ku in da zakuje kin ji."
yayi maganar yana duban Naseeba da fuskar tausayawa. shiru SEEDRAH bata kuma magana ba, tasan kawar tata tana bukatar taimako a irin halin da take ciki yanzu tafiyar kafa bazai yuwu a gare ta ba,
tsayuwa tayi batare da ta ce komai ba,
ganin haka yasa Kamal saurin hayewa nashin d'in sa yana fad'in
"Yauwa kuzo ku hau muje."
hannun Naseeba ta ja zuwa gurin mashin d'in ta taimaka mata tahau, cikin b'ata fuska take yi masa kwatancen in da zai kaita wato gidan goggon ta, sakanin su da gidan babu nisa sosai.
ya ce ya gane gidan to tahau bayan Naseeba
su tafi tare mana,
wani harara ta dalla masa ta ce bazata hau ba.
bai kuma magana ba yaja mashin d'in suka soma tafiya a hankali dan yaga ita wancan tad'au zafi da yawa ga dukkan alamu kuma masifar tsiwar tsiya ce da ita.
bayan su ta bi a kafa, sun isa suna tsaye a kofar gidan SEEDRAH ta karaso.
ta ja hannun Naseeba suka shige cikin gidan, suka bar Kamal tsaye a gurin yana yi musu magana bata ko saurare shi ba...
jiki a sanyaye Kamal yaja mashin d'in sa yatafi, duk in da yake zaton zai sami Mukhtar ya je baya gun, gaba d'aya lissafin sa ya jagule sai gani yake kamar mafarki yake,
wai Mukhtar ne da aikata haka, shi a sanin sa tun da suka taso bai san sa da irin wannan halin ba...
A can gidan su Maman Zeey kuwa jin fitar su Kamal yasa Maman Zeey fitowa daga d'aki, tana tambayar Zeey ina yarinyar take,
Zeey ta ce "Sun fita da Ya Kamal ni fa ina ga su suka biyo ta, dan naji yana ce mata dama yayi zaton nan ta shigo."
Maman Zeey ta rike hab'a tana fad'in
"Jimin tsiya ina ruwan su da ita da zasu biyo ta yara da niman magana haka."
A b'angaren su SEEDRAH kuwa
Yanayin dare gidan shiru side d'in goggo suka nufa, shiru side d'in babu motsin kowa ciki, direct d'akin goggo Larai suka wuce, goggo Larai bata ciki tana can side d'in maigidan ta, kasan cewar 'ya'yan ta duk maza ne suma suna nasu d'akin.
a bakin gado SEEDRAH ta ce wa Naseeba ta zauna kana ita kuma ta wuce cikin bathroom, ruwan zafi ta had'a mata cikin
Bathtub kana ta fito ta taimaka mata suka shiga cikin bayin.
tagasa jikin ta sosai, Naseeba na masar kwallar wahala SEEDRAH kuma na zubda kwallar tausayin ta tare da jin d'acin rasa wani kima mafi girma da daraja a rayuwar ta.
sosai ta taimaka mata ta gasa jikin ta dan sai da ta sauya mata ruwan zafi har sau uku.
kana ta sarkake jikin ta suka fito,
babu laifi taji dad'in jikin ta sosai dan ko tafiyar ta ma ba irin na d'azu ba.
Wardrobe d'in goggo Larai ta bud'e ta ciro mata wasu kaya wan da take ga bazai mata girma sosai ba tabata ta saka, natan daya gama cukurkud'ewa a turb'aya ta koma bayi ta wanke mata ta shanya shi cikin bayin.
ko da ta fito bakin gado ta matso in da Naseeba ke kwance shiru bawai ko dun tana bacci ba,
ta zauna gefen ta cike da tausaya mata cikin murya mai rauni ta ce
"Kiyi hakuri Naseeba narasa da wani irin baki zan baki hakuri, wlh in da nasan haka zata faru da ban ce mu fito zuwa nan ba."
hawaye ne yafara zuba a idanunta tana mai ci gaba da baiwa kawar tata hakuri.
ta ce
"Sai naji ina ma ace a kai na hakan yafaru bawa ke ba."
hannunta Naseeba ta rike ta ce
"Haba SEEDRAH ki dai na d'aura alhakin haka a kanki duk abin da kikaga ya sami bawa to da sanin ubangiji, tawa kaddarar kenan dama Allah ya hukun ta ni tawa budurcuin a haka zai tafi, amma sam baki da laifi ki dai na d'aurawa kan ki laifi, dan ina da tabbacin bazaki tab'a so abin da zai cutar da ni ba bare ya tab'a min kima."
zafafan hawaye SEEDRAH ta share ta ce
"Wlh baza a kyale su ba sai an gurfanar da su gaban shari'a azzalumai."
kai Naseeba ta girgiza yayin da take jin d'aci cikin ranta cikin rawar murya da kuka ke son kwace mata ta ce
"A'a SEEDRAH kirufa min a siri bana son maganar nan ta fita
nasan zan zamo abin nunawa a gari, gara naji da abu guda kyara da tsangwama gurin mijin da zan aura a lokacin da yagane bani tare da budurci na."
kuka ne ya kwace mata, sai kawai suka had'a kai sukayi ta rusar kuka, babu mai iya baiwa d'an'uwan sa hakuri,
sai da suka gaji dan kansu kafin sukayi shiru.
sai da dare ya raba kafin bacci ya sami damar d'aukar su.
Washrgari da asuba goggo Larai ta dawo d'akin ta, turus tayi ganin mutane kwance a kan gadon ta suna bacci,
da mamakin ganin SEEDRAH ce da kawar ta. ta karaso bakin gadon tashiga bubbuga su da fad'in.
"Kai ku tashi kuyi sallah wai yaushe kuka zo ne ma kada a ce a nan kuka kwana."
SEEDRAH me nauyin bacci mika tayi had'e da yin juye ta kuma gyara kwanci.
Naseeba ce ta mike zaune tana mussuke ido,
goggo Larai ta ce "Wai yaushe kuka zo ne Naseeba? wannan kasar in ba ruwa a ka yayyafa mata ba, batashi zatayi nan kusa ba."
tayi maganar tana mai dad'a bubbuga SEEDRAH da ta koma baccin ta.
Naseeba ta ce "Jiya muka zo da daddare."
sai a lokacin SEEDRAH ta bud'e ido cikin magagin bacci sabo da bubbuga ta da goggo Larai take tayi, tana fad'in ta tashi suje suyi sallah.
da kyar ta mike zaune tana tura baki gaba, hamma tayi had'e da salati ta ce
"Allah sai nake ji kamar yanzu na kwanta."
goggo Larai ta ce
"Yo ke kam in tun magriba kika kwanta bacci kika tashi yanzu ai haka zaki ce, irin wannan baccin naki sai a sace ki ma baki sani ba, maza sauko kuje kuyi al'wala kuyi sallah."
goggo Larai tayi waje.
Naseeba ce ta fara shiga bayin sai da tayi sarki da ruwan zafi kafin tayi al'wala ta fito,
SEEDRAH ma ta shiga, suna idar da sallan, Naseeba ta koma gado ta kwanta dan zazzab'i take ji tun daren jiya.
gefen ta SEEDRAH ta zauna tana yi mata sannu cikin tausayawa.
goggo Larai ne ta shigo da flaks d'in ruwan zafi data girka ta aje,
suka gaida ta ta amsa tare da fad'in
"Shine baku kirani ba da kuka zo jiyan, me ya sa mi wannan take dunkulewa da rawar sanyi?."
SEEDRAH ta ce "Ba waya ne a hannun mu mun baro shi gidan Nabeela, nan aka kawo ta fa saman layin ku, zazzab'i ne ya dami Naseeba shine muka zo nan."
goggo Larai ta ce
"Subhanallah ta karya ta sha magani, ai ku yaran yanzu kun fiye sako bidi'a cikin hidimar biki ku, zirga-zirga ma kad'ai ya ishi mutum yayi ciwo, ki karya sai ki sha magani."
shiru sukayi basuce komai ba, gaggo Larai ta had'a mata tea me kauri ta ce tata shi ta sha, tana tsaye har sai da ta shanye,
kana tafita jim kad'an ta dawo da faracetamol ta bata tasha, sannan ta ce ta kwanta kafin gari ya dad'a waye wa a siyo mata magani.
babu jimawa kuwa bacci yayi gaba da ita.
goggo Larai ta fita domin yiwa y'ay'anta abin kari sutafi gurin aiki.
SEEDRAH kuwa ganin ta koma bacci ta mike ta shiga bayi,
kayan jikin ta da aka bata jiya agidan da ta shiga b'uya, tacire, sai da ta wanke shi tsaf kafin tayi wanka ta fito d'aure da towel d'in da tagani cikin bayin,
babban hijabin goggo Larai ta saka, kana ta fita can sakar gida ta shanya kayan domin iska ya busar da su dawuri.
ko da ta dawo d'akin kayan goggo Larai ta saka, ta isa gaban mirro ta shafa mai had'e da d'an murza pauda, dariyar kanta tayi ganin yan da take yawo cikin kayan dasukayi mata yawa.
kitchen ta nufa in da goggo Larai take had'a Breakfast nan ta iske Zaraddin da Faisal yayan goggo Larai,
tana shiga kitchen d'in Zaraddin ya fashe da dariya yana nuna ta cikin zolaya irin na d'an kawu da d'an goggo ya ce
"Wai kin gan ki kuwa kamar an rataya miki kayan ne."
baki ta murgud'a masa tana aika masa da harara ta ce
"To ina ruwan ka d'an sa ido."
bugu ya kaiwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 19