damuwa.
hayakin sigari ya zuko tare da buso shi kana ya bud'e idonsa d'aya ya kalli Baba da shi cikin kanne ido da rashin daraja ya ce
"Ka taho da kud'ad'en?."
hannu Baba ya rungume jiki a sanyaye.
S.MAN yakuma mai da idonsa ya lumshe yana fad'in
"Au na mance ashe kai fakiri ne, to ni ko fashi zakaje kayi kaje kayi kakawo min kud'ina wan da kaci bashin sa naira million 30 da kuma wacce 'yarka ta la'anta motar million 80."
Baba ya ce
"Dan girman Allah Usman kayi hakuri a ina zan sami wad'an nan kud'ad'en?."
da sauri S.MAN yabud'e idanunsa ya ce "Anya ba kaika sata ba ma kuwa? dubi yadda ta goge min mota ta b'ata shi, kai komai akayi ma da sa hannunka, duba fa dubafa ka gani."
yayi maganar yana nuna parking lot can in da motar take.
Baba ya ce "Haba Usman taya zanyi na sata tayi maka b'arna wlh sam banda masaniya a kan haka, ina SEEDRAH take?."
"Tana ciki kaje ka fito da ita dan wlh yau sai na saita mata tunani."
Da sauri Baba ya shiga ciki yana waigen motar da SEEDRAH ta goge fentin sa kamar zata sake masa wata fentin.
tun daga bakin kofa Baba ke kiran ta har ya shiga ciki.
S.MAN daya biyo bayansa yakaraso yana fad'in
"Can kofar zakaje ka fito da ita in ba hakaba kuma na b'alle kofar ni naje na same ta."
ya nuna masa kofar d'akin da SEEDRAH take ciki.
Baba ya matsa bakin kofar da sauri shiko S.Man ya haura sama.
Tana nan zaune cikin zullumi da tunanin rashin mutuncin da yanzu S.MAN yaje yake kanyiwa Baba tajiyo ana bubbuga kofa.
a d'an firgice ta mike tazo bakin kofar
Baba yakuma bubbuga kofar tare da fad'in
"Ke SEEDRAH bud'e kofar nan hauka kikayi ne wani shashanci ne wannan kin san kuwa barnan tulin dukiyar da kikayi? maza bud'e kifito nan."
jin muryar Baba yasata bud'e kofar tafito tana rarraba ido tare da turo baki.
Baba ya ce "Zonan maza."
yafad'a yana nufar in da kujeru suke ya zauna, ta karaso ta zauna kasan carpet gefe da shi.
Baba ya dube ta hankali tashe ya ce
"Meyasa hakan meyasa zaki sa abu ki goge masa jikin mota kin san kuwa kud'in motar nan SEEDRAH?, ta ina ne zan iya samo kud'in motar nan SEEDRAH ata ina ne zan iya samo miliyan 80 ban da kud'in da yake bina iye SEEDRAH, meyasa zakiyi haka."
"Baba ai nace masa ban iya wankin mota ba ya ce sai nayi."
"Tafi can da'alla sai kuma dan baki iya ba sai ki saka abu ki goge motar har sai kin cire fentin jikin sa, yanzu ko kud'in fentin motar ce ma a ina zan samu nabiya sa asake yi masa fenti bare kuma kud'in motar."
baki ta kuma turowa zatayi magana sukajiyo muryarsa yana sauko wa daga matattakalar bene
"Ko da kana da kud'in fentin ma bazan karb'aba sabuwar mota nake bukata."
yakaraso ya zauna kan kujera tare da d'aura kafa d'aya kan d'aya.
Baba yashiga basa hakuri kamar zai zuba guiwowinsa kasa yana had'asa da Allah da manzon sa, shiko sai wani cika yake yana batsewa daga bisani yad'aga wa Baba hanu ya ce yaje amma fa zai neme sa aduk san da bukatar hakan ta taso dan bai hakuraba.
Baba ya tafi yana mai jaddadawa SEEDRAH ta kiyaye kada wata matsala takuma faruwa.
SEEDRAH nakokarin mikewa ta bar parlour'n ya dube ta yama rasa me zaiyi wa yarinyar, yaso yimata dukan da gobe idan akace takuma b'arnata masa wani abun bazatayi ba.
ya ce "Kizauna da shirin ki dan wlh sai nayi miki dukan kud'in motata."
wani kallon sama da kasa ta bisa da shi kana ta ce
"Ni kuma wlh ka kuskura ka tab'a ni sai nayi maka b'arnar da har ka mutu bazaka manta ba, duk ranar da ka sake kuskuran kai hannu jikina sai kayi da na sani, ba wankin mota kace ba'
shiyasa nikuma nayi masa wankin da zai dad'e bai yi datti ba ko gobe kakuma sani haka zan yiwa sauran motocin."
ta murgud'a masa baki tayi wucewar ta d'aki.
baki ya bud'e da mamaki yake kallonta harta shige d'aki sai kuma da sauri yabiyo bayanta yana fad'in
"Me zaki yi, me zaki iya yi?."
ta ce "Komai ma idan kuma kana ganin wasa ne to ka gwada."
tayi maganar ne cikin dakiya ganin yadda yake dad'a maso ta, ya mika hannu da zummar cafko ta, ta ja da baya tare da d'aukar plt dake kan mirro ta ce
"Idan ka kuskura ka tab'ani sai na buga maka."
murd'e ta yayi ya kwace plt d'in tare da angizata tagaru da jikin gado.
kana ya ce
"Baki isa ki b'ata min mota kici banza ba,
kinyi abakin abincin da kike ci a cikin gidan nan, dan nasan Alhj Musa bashi da kud'in da zai iya biyana b'arnan da kika min,
daga yau abinci sau d'aya zaki rika ci a gidan nan iya na safe kawai sai kuma wata safiyar, sannan kuma ruwan gidan nan ya haramce ki sai dai idan zaki rika shan nacikin bathroom."
baki ta murgud'a masa ta ce
"Sai me."
ganin yana kokarin kuma maso ta taruga da gudu tayi cikin bayi ta murd'a key..
Bata fitoba sai da ta tabbatar da yatafi, tana fita kiran wata 'yar ajinsu mai suna Firdausi na shigowa wayarta.
bayan sun gaisa Firdausi take cewa
"SEEDRAH kina da labarin gobe za a shiga yajin aiki kuwa?."
ido ta waro ta ce "Dan Allah fa wlh bani da labari."
Firdausi ta ce "Wlh nima d'azu K.B yake fad'a min zuwa yanzu kuwa ai labarin ya baza ko ina."
"Wayyo ban ji labarin ba Allah dai yasa adawo da wuri."
"Amin ya Allah."
nan sukayi sallama..
Tun daga ranar S.MAN bai kuma sa SEEDRAH wankin mota ko baiwa fulawa ruwa da duk sauran ayyukan daya shafi sakar gida ba.
aikin cikin side d'in kawai takeyi,
sannan kuma ya kwashe duk wasu kayan sha dake cikin fridge d'in parlour'n kasa zuwa kichin bedroom d'inta duk ya kaisu sama.
kamar yadda ya ce sau d'aya zata rika cin abinci kuwa hakan akayi duk san da zatayi abincin rana dana dare zama yake a parlour har sai ta gama tana gamawa kuwa zaice ta kai masa sama sannan yakulle kichin d'in yatafi da key d'in.
ganin haka kuwa idan tayi breakfast sai ta zuba da yawa cikin kula shi zatayi ta ci har dare.
a haka har ta shafi tsawon sati uku a gidan.
duk yadda taso zuwa gida yahanata yakuma ce mata idan ta sake ta fita to sai ya cire kud'in fitar cikin albashin ta,
tun da tazo aiki tofa aikin kawai zatayi babu fita.
idan tayi yunkurin fita kuma maigadi yaki bud'e mata kofa ya ce Oga ya ce kada ya barta ta fita.
duk san da tayi waya da Mama takan cewa Mama itafa ta gaji tana so ta zo gida ta ganta yakuma hanata fita.
Mama ta ce tabari kawai takula da aikin ta duk gidan suna nan lafiya.
haka SEEDRAH tayi ta mita wai sai kace tazamo matar kulle sai yarika nuna mata wani busasshen iko, ko shi a su wa oho,
dan tana aiki a gidan sa sai ya zamo ko waje bazata leka ba dan rainin tsintsi ma wai harda gidan su yahanata zuwa.
A B'angaren Kamal kuwa yagaji da zuba idon ganin komawarta gida,
gashi yana son ganin ta duk san da yace mata zai zo, sai ta ce masa yabari tukun.
Kwance take akan gado like da waya a kunnen ta suna waya da Kamal,
cikin hirar tasu yake ce mata
"Nifa yau hakurina yakare ganin kyakkyawar fuskarnan taki kawai nake da bukata."
murmushi tayi tare da fad'in
"Um bagashi kana jin muryata kullum ba."
"Inaa jin murya kad'ai bai wadatar ba ganin ki nake son yi, na dauren na daure dauriyar takasa kai ni ko ina, yau zan zo kawai naganki."
"To ai baka san gidan ba."
tafad'a cike da d'an zullumi da tunanin zuwan nasa, bakomai yasa taki barinsa yazo gidan ba sai dun gujewa wulakancin S.MAN dan tana da tabbacin zai iya wulakanta sa idan yazo dan abune mai sauki a gurin sa.
ya ce
"To tun da abun kauna ta tana ciki me zaisa sai na sani nemo sa kawai zanyi, in ban da abunki gidan jarumin namu ne zai gagare ni sani,
yanzu idan na bukaci hakan za'a kai ni har kofar gidan."
murmushin yake tayi
"Ni dai ka huta kawai bance ka wahalar min da kanka ba, kuma gobe ma zanje gidan Nabeela ta haihu daga gun zan wuce gidan Naseeba can zan wuni."
ya ce "Da gaske."
ta ce "Eh mana." "To shike nan Allah ya kaimu."
nan sukayi sallama.
numfashi ta sauke tana aje wayar a gefen ta, fatan ta kada Allah yasa yazo gidan dan bazata iya jurar ganin tozarcin S.MAN agare shi ba.
mikewa tayi ta nufi kofa dan lokacin d'aura abincin rana yayi.
tana fito wa cak taja ta tsaya nan bakin kofar,
da d'inbin mamaki take dad'a ware idanunta kan S.MAN dake zaune kan kujera wata budurwa na zaune a kan cinyarsa tawani sakalo wuyansa da hannayen ta, takawo fuskarta daf da nashi tana yi masa magana.
shiko hannunsa d'aya ya saka ya tallafo bayan ta ya yin da d'aya hannunnasa kuma ke rike da waya yana daddannawa.
baki bud'e SEEDRAH ta ke kallon su sai kuma tayi saurin janye idanunta tare da yin gyaran murya.
Da sauri budurwar mai suna Teema ta waigo tana bin SEEDRAH da kallon mamakin yadda akayi ta ganta a nan bayan tasan shi kad'ai ne cikin gidan.
SEEDRAH ko tafiya ta soma tazo ta wuce su ta shiga kichin, a ranta take ayyana girman lamarin nasa ashe dai ba iya shaye-shaye ya tsaya ba har da neman mata.
A parlour kuwa kallon tuhuma Teema take yiwa S.MAN mikewa tayi a jikin sa ta zauna gefen sa tare da ruko hanun sa sannan ta ce
"S.MAN wace ce kuma wannan?."
batare da yad'ago daga kallon wayar da yake ba ya ce
"Ƴar aiki ce." ido Teema ta waro tare da fad'in "Ƴar aiki, wannan ce 'yar aikin?
haba S.Man kada ka cigaba da rainamin hankali mana, ashe dama kayi aure ne shiyasa dana bukaci nazo kace min baka kasar, yaushe kayi aure S.MAN?."
gabaki d'aya ganin SEEDRAH yasa hankalin Teema mugun tashi tabi ta rikice.
d'an kallon ta yayi kana ya ce
"Na ce miki 'yar aiki ce."
cikin rashin gamsuwa da maganar sa tayi murmushi wan da yafi ihu ciwo, ganin rainin hankalin da yake mata yadubi wannan zankad'ed'iyar yarinyar ya ce wai ita ce 'yar aiki. sai kuma ta girgiza kai tare da fad'in
"Basai ka b'oye min ba ni ban damu da kayi aure ba zan cigaba da jiranka idan ka gama more amarci idan kana bukatar karin wani amarcin zaka iya nima ta, ko yanzu ne ashirye nake."
A cikin kichin kuwa SEEDRAH na d'aura girki tafito, bata kuma kallon in da suke ba tazo zata wuce su tajiyo muryarsa ya na fad'in
"Ke ba kiga bakuwa bace ki kawo mata abun sha."
cak ta ja ta tsaya tare da juyowa da zummar ce masa baya daga cikin jadawalin aikin ta kawowa karuwa abin sha.
sai kuma ta juya ta hanyar tausar zuciyar ta tahaura sama domin kawo mata, dan duk yakwashe duk wani abin sha ya kaisu sama.
Teema ko baki bud'e take binta da kallo harta haura sama tana ta son ta gaskata wai shin da gaske ne 'yar aiki ce.
sai da takawo drink's d'in yasata ta bud'e ta zuba mata a kofi kafin ta gaskata cewa 'yar aikin ce dai da gaske,
sai dai tana ta shan mamaki ace kamar wannan takasance a 'yar aiki, dan tayi imani har idan da matar sa ce ko auren kiyayya akayi musu dole sai taga kishi a kan idonta a yanda tafito ta samesu d'in nan, bare kuma har taje ta kawo mata abin sha.
ko da SEEDARH ta juya tanufi d'aki bayan ta Teema tabi da kallo har ta shige ciki.
gabaki d'aya tasha jinin jikin ta wai ace wannan ita ce 'yar aiki, ba sai wani yafad'a mata ba tasan SEEDRAH tafita komai da kamai kyau diri da komai ma na tsarin zubin halitta.
wannan itace S.MAN ya aje amatsayin 'yar aiki matarsa kuma to ya zata kasance kenan?.
tayiwa kanta tambayar acikin zuciyar ta, sai yanzu ta samo amsar da yasa yaki aurenta sannan kuma yaki amsar tayin bukatarta na mallaka masa kanta koda bai aure ta ba.
Wace ce Teema?.
Teema d'iya ce ga wani hamshakin d'an siyaya a Nigeria ta jima tana d'awainiya da dakon son S.MAN a zuciyar ta,
saboda tsabar son da take masa duk kasar da zaije buga kwallo sai ta bi jirgi taje ta same sa.
duk yan da taso ta juyo hankalinsa gareta ta garara dan har kanta ta ce zata bashi tasha tub'e kayan ta a gaban sa amma ko kallo bata ishe saba, wasu lokutan yakan tab'a jikin ta sai dai baya wuce gona da iri.
duk da S.Man yarayu cikin turawa baisashi mu'amalar banza da mata ba, ya kanyi iya bakin kokarin sa wajen kame kansa, ba Teema kad'ai ba akwai mata da yawa masu kawo masa kansu baya sauraran su.
wannan kenan...
Ko da SEEDRAH ta kuma fitowa duba girkinta basa cikin parlour'n yanzu, dan haka ta wuce taje tacigaba da aikin ta.
Da yammacin ranar tana zaune cikin d'aki bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa, tana zaune a bakin gado tana d'an daddanna wayar ta, gabaki d'aya kad'aici ya ishe ta kewar Mama da 'yan uwan ta duk sun addabe ta.
a hankali ta d'ago kanta jin an turo kofar
Ganin shine sai ta maida idanunta kan wayar tacigaba da abun da take.
yana tsaye rike da kofar daga nan bakin kofar ya ce
"Wa kika gayyato mun shi gida na?, kefa kawai 'yar aiki ce, baki da ikon da zaki shigomin da wani cikin gidan nan, na ce masa yatafi na aike ki."
da sauri ta d'ago tana duban sa akasan ranta ta ce
"Kamal kazo kenan."
"Kada ki kara gaiyato min wasu 'yan iska cikin gida daga yau."
ya juya yana kokarin fita
da sauri ta ce "Shine zakace masa ka aike ni alhalin ina nan, shi ba d'an iska bane kamilin mutum ne, ko waccan karuwar da tazo ba'a ce mata baka nan ba bare kamilallen mutum."
kofar ya janyo batare da yayi magana ba sakamakon kira data shigo wayar sa.
da sauri ta mike zatayi waje kiran Kamal ya shigo wayar ta, cikin hanzari ta gad'aga
Kamal ya ce
"Yanzun nan nabar kofar gidan Yayan mu nayi rashin sa'ar samunki nayi kuma farin cikin had'uwa da kwarzon mu har sai da muka d'au selfi da shi, dama nazo ne na sanar miki gobe idan Allah ya kaimu zamu d'an yi tafi da Alhajina."
numfashi ta sauke jin dai S.MAN bai gwada masa bakar halin sa ba.
tayi masa fatan isa lafiya nan suka lula duniyar masoya tana like da waya a kunne suna ta zuba love d'in su...
Bayan kwana biyu.
SEEDARH ce kwance cikin d'aki tana kallo a t.v hamma ta yi tare da yin salati, a hankali ta mike ta janyo kular da ta saka abincin breakfast ciki wan da take ajewa tarika ci har dare ta zauna bakin gado ta soma ci.
taci yadda cikin ta zai iya d'auka kana tarufe sauran.
fuska ta yamutsa dan yanzu ruwa kawai take da bukata, dama ruwan pampon kichin take tara cikin kofi ta kawo d'aki tarika sha duk da sam baya kashe mata kishi haka take maneji da shi, gashi kuma gaba d'aya ta mance bata tari ruwan ba lokacin da ta gama girki, gashi ya kulle kichin d'in yatafi da key d'in.
tsaki taja tare da fad'in
"Dole ma in nemo ruwa dan wlh bazan mutu da kishi ba."
tamike da d'an sauri tafita, cikin sauri ta nufi steps dan taji fitarsa d'azu a mota bata kuma ji dawowar sa ba.
tana shiga parlour'n sama in da fridge yake ta nufa ta bud'e, babu ko gorar ruwa aciki drinks ne kad'ai a ciki.
rufe fridge d'in tayi tana fad'in
"Ruwa nake jin kishin sa ba lemo ba."
da sauri ta juya tanufi kofar bedroom d'in sa ta tura kofar a hankali............!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 15
Tashiga ciki da sauri ta isa inda fridge yake ta bud'e, cikin hanzari ta d'au babban gorar ruwa har hannunta na b'ari tabud'e shi dan bakarami kishi take ji ba.
sai da ta sha kusan rabin gorar kana ta sauke gorar ta mai da marfinsa tarufe, takuma d'aukar wani babban gorar ruwa sannan ta rufe fridge d'in
tana fad'in
"Zan shaku har dare."
ta juyo tare da d'aga kafarta zata bar d'akin aka turo kofar.
da sauri cikin rawar jiki tayi baya da hanunta tab'oye gorunan ruwan a bayan ta.
Ido S.MAN ya zuba mata ganin ta tsaye cikin d'akin sa cikin yanayin nuna rashin gaskiya, sai kuma yasoma d'aga kafarsa ya tako zuwa gabanta yayin da yake cigaba da binta da kallon tuhuma.
"Me ya kawo ki cikin d'aki na lokacin zuwan aikin ki baiyi ba, sata kika zo min ko?."
ya jefa mata tambayar ya na mai cigaba da tsare ta da ido.
d'an dibirbircewa tayi sai kuma ta saita nutsuwar ta ta ce
"Ni bana sata ban tab'a yi ba bazan kuma faraba da yardar Allah."
tayi maganar had'e da murgud'a baki da d'aga hanci sama cike da tsiwa.
ya ce "To idan ba sata kika zo min ba me kike b'oye shi a bayan ki."
yafad'a tare da miko hannunsa ya cafko hannayen ta da suke b'oye a bayan ta,
ba shiri tasaki gorunan kasa, sabo da yan da ya ruko hannun nata da salon mugunta.
bin gorunan ruwan ya yi da ido kana ya mai da duban sa gare ta ya ce
"Okay satan ruwa kika zo min a d'aki?."
baki ta turo ta ce "Kai nifa ba b'arauniya bace kishin ruwa nake ji dan kuma na d'auki ruwa na sha baizama nayi sata ba,
idan kuma hakan sata ne to kowa ma b'arawo ne tun da kowa yakan iya shan ruwa a duk in da ya gansa, ruwa kuma ai na Allah ne bana d'an mutum ba."
"Idan kuma mutum ya siya da kud'in sa ne ya ajiye wani yad'auka fa shima ba sata bane, to bazaki sha wannan ba akan ba ruwa cikin bathroom d'in d'akin da kike ne, ko da a gidan ku ruwan gora kike sha, wani samin guri kawai wuce ki bar min nan na daina ganin ki."
yayi maganar tare nuna mata kofa yana yi mata alamar ta fita.
baki ta turo gaba ta ce
"Allah bazan sha ruwan bayi ba ni ko a gidan mu ma bana shan ruwan pampo dan baya kashe min kishi, sauyin rayuwa ce kawai amma muma ruwan gorar muke sha a gidan mu da, yanzu kuma da Allah yaso ganin mu a haka bai hana mu kud'in da zamu siyi ruwan fiyowata ba, ni ban iya shan ruwan pampo ba dan baya kashe min kishi."
Ya ce "Zaki b'ace min da gani ne ko sai na murd'e wannan bakin rashin kunyar, tun da bazaki sha na pampo ba sai ki zauna haka."
fita tayi tana kunkune da fad'in wlh bazata sha na pampon bayi ba kam...
Haka kuma bata sha na bathroom ba har sai da tazo girkin dare kafin tasha a kichin ta kuma d'iba ta kai bedroom d'in kwanan ta.
shan ruwan kawai take bawai ko dun yana kashe mata kishi ba,
SEEDRAH ma abociyar shan ruwan dare ce.
duk nauyin baccin ta kishin ruwa na tadata cikin dare.
hakan ne ta kasance da misalin karfe biyun dare kishin ruwa ya tashe ta, ta mike cikin magagin bacci ta isa in ta aje ruwan da tad'ibo a kichin aikuwa garin gigin baccin ta tamika hannu zata d'au kofin ta tureshi ruwan ya kife a kasa.
sai a lokacin ta gama bud'e idanunta da bacci ke cike fal cikinsu.
tsaki taja cikim muryar bacci ta ce
"Shine ka zube."
sai kuma ta nufi bathroom dan ji take bazata iya bacci idan bata sha ruwa ba.
pampo ta kunna ta kafa kanta tasoma sha babu kakkautawa cikin ta yacika tam sai dai bata fasa jin kishin ba.
mikewa tayi tana yamutsa fuska dajin yanda lokaci guda taji zuciyar ta na tashi,tasan za ayi hakan dan tana kyankyanin shan ruwan bayi babu in da ta iya ne kawai.
da sauri ra sunkuya kan toilet tashiga sheka amai daya taho mata, sai da ta amaye ruwan data sha duka kana ta mike ta wanke bakinta tana mai da numfashi.
sai da ta gyara in da ta b'ata kafin ta fito.
abakin gado ta zauna tana cigaba da maida numfashi.
wani irin mugun kishin ruwa takeji yin aman da tayi tamkar dad'a kara mata kishi ya yi, zuciyar ta kuwa sai hurewa yake da azabar kishin ruwa.
da kyar ta iya tattaro yawun bakin ta ta had'iye. ta mike da sauri ta d'au hijabin sallarta ta saka tafita a d'akin dan yanda take ji har idan bata sharuwa yanzu ba tana ji kamar bazata wayi garin gobe ba.
direct sama ta haura rike da wayarta tana haska hanya dan duk wutan cikin side d'in a kashe yake.
ko da ta shigo parlour'n sama gurin fridge
ta nufa tabud'e da tunanin ko ya saka ruwa aciki, amma sai taga babu sai drinks d'in ne kawai aciki.
da sauri tashiga waige-waige ko Allah zai sa taga ruwa amma babu ko alamarsa.
numfashi ta fizga da kyar takuma had'iye miyau tare da rumtse idanunta da karfi tana jin yanda zuciyar ta ke dad'a hurewa da ƙishin ruwa.
bud'e idanunta tayi ta sauke su kan kofar bedroom d'in sa idan har tana son tasha ruwa tofa babu makawa dole sai tashiga d'akin sa.
sannan ta rokesa ya sammata.
bata da zab'in da yawuce hakan a hankali tashiga d'aga kafarta har ta tako bakin kofar.
Ta d'aura hannunta jikin handle sai kuma ta tsaya da tunanin har idan taje tarokesa tofa jin kansa zaiyi kamar yafi kowa, sannan kuma yakara kaimi kan wulakantata da yake,
to amma tana jin kishin da bazata iya sarrafa kanta ba dole sai ta sami ruwan da zatasha.
kashe tocin wayar ta tayi kana a hankali ta murd'a handle d'in ta tura kofar a hankali cikin sand'a tasa kai cikin d'akin.
cikin d'akin duhu babu haske ko tafin hannunta bata iya gani.
a hankali tasoma d'aga kafarta duk da bata ganin gaban ta amma takan iya hasko in da fridge yake acikin zuciyarta, tana jin zata iya isa gurin batare da haske ba.
wani irin garuwa tayi da jikin abu da sauri ta dafe goshinta datake sammanin fashewa ma ya yi dan bakaramin azabar zafi taji ba, gaba d'aya jikin ta ya d'au b'ari ga zafi ga tsoro bata kai ga dai-dai ta nutsuwar ta ba taji hannun mutum a kafad'ar ta.
wani uban kara ta sake mai cike da tsananin tsoro tayi baya da sauri takuma garuwa da wani abun, tana kokarin d'ago wayarta ta kunna tsabar b'arin da jikin ta yake wayar ta fad'i kasa, sai kawai takuma sakin wani karar.
"Ke rufamin baki me yakawo ki d'aki na a tsohon daren na me kika ajiye anan kika zo d'auka sata kikazo min?."
taji maganar sa daf da ita, wutar d'akin ya kunna yaci gaba da fad'in
"Alhj Musa ne ya turo ki ki kasheni ko?."
kai tashiga girgizawa sai kuma ta ce
"Nifa ruwa zansha ba wani abu yakawo ni ba, ni kuma ba b'arauniya bace ka dai na dangantani da sata, sannan kuma mezaisa Baba yaso kasheka."
"Ke ba magana nace ki jera min ba, bance kije ki sha ruwan bathroom ba d'azu, yanzu ma ki koma kije kisha."
"Allah ni bazan iya shan abin da zai kusa kashe ni ba."
tayi maganar tana janye idanunta daga kansa dan babu komai ajikin sa sai gajeren wando kawai.
ya ce "Oya wuce ki fita in kinje ki mutu."
a hankali ta juya harta kai bakin kofa tajiyo muryarsa yana fad'in
"Zo ki d'auka zan cire kud'in sa acikin kud'in aikin ki dan kin dai na cin abinci kyauta acikin gidan nan, duk wani abun da zakici acikin kud'in aikin ki."
da sauri ta juyo dan sosai take jin kishin ta d'au babban gorar ruwa tafita, a parluor'nsa tasha kusan rabin ruwan kana ta koma d'akin ta sai alokacin ta sami bacci mai dad'i yadda take so..
Washegari kamar kullum tana yin sallar asuba bata yadda ta koma ta kwanta ba sanin kalar baccin ta ba lallai bane tatashi dawuri.
kichin tatafi tafara d'aura breakfast kafin ta fito can ta hangosa gurin motsa jiki tawuce ta haura sama.
ko da ta gama gyaran
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 19