Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kudin cikin asusun sa na banki wasu da baisan ko su waye ba suka kuma kwashe masa kud'i cikin account duka basu rage masa ko sisi ba. gashi yayi sintirin banki har ya gaji ba'a gano wad'an da suke aikata masa hakan ba. gashi yau banki ta nemesa kan kud'in ta daya ci, an kuma bashi wata guda yadawo da kud'in. hankalin Alhaji Musa bai dad'a dugunzuma ba sai da yaga wata gudan da a ka bashi ya kare. da sassafe tun bai tashi daga bacci ba yasami kira daga banki. ko da yaje banki suke shai da masa sun sami masaniya kan yasai da kaddarorin sa daya ajiye musu a mazaunin jingina kafin su bashi bashi, suka kuma nuna b'acin ransu a kan hakan, sannan suka ce masa sun bashi awa ashirin da hud'u yadawo musu da kud'in daya karb'a, idan kuma ba haka ba zasu sa gidan sa da yake ciki da motar hawan sa a kasuwa yau kuma zai bar gidan. cikin matukar tashin hankali yabaro bankin da tunanin in da zai sami kud'i, bashi da su bashida dalilin su,abun da yayi masa saura daga gidan da yake ciki da iyalinsa sai motar da yake hawa, hatta abincin da zaici da iyalinsa nason fin karfin sa dan ma d'an'uwan sa na tallafa masa da abincin. hankali tashe ya nufi gidan kanin sa Alhaji Sulaiman...........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ ( _Bismillahirrahmanurrahim_) _Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* 🅿️6 Ko da Alhaji musa ya isa a parlour'n kanin nasa suka yada zangon su, nan Baba yake shaidawa d'an uwan sa abun da ke faruwa. Alhaji Sulai ya jinjina lamarin matuka. ya gyara zaman sa ya ce "A gaskiya wad'an nan 'yan yawu d'in basu kyauta mana ba sakanin mu da su sai sakayyar Allah, wlh Yaya Musa duka-duka kud'ina da suke cikin account d'ina basu kai kud'in da banki suke bukata ba, kuma nasan tun da suka d'au zafi ba lallai bane su karb'i kad'an ba, amma dai muje ko Allah zai sa su karb'a su kara mana lokaci har Allah yasa mu samu a kaimusu sauran." Baba yashiga yi masa godiya da irin rufin asirin da ya yi masa suka d'unguma zuwa banki, sai dai sukayi rashin sa'a banki sun d'au zafi sosai bisa karya musu yarjejeniyar da sukayi kan siyar da kaddarorin daya nuna musu a matsayin jingina. suka ce bazasu karb'a kud'in da ya yi kasa da abunda suke binsa ba, haka suka baro bankin cike da matukar damuwa. gidan Alhaji Sulai suka dawo da tunanin mafita, suna zaune sunyi jugum-jugum Abba wato Alhaji Sulai yad'an zaburo tare da d'aukar wayar sa da yake kara alamun shigowar kira. ko da ya gamai kiran nasa zaman sa yagyara tare da d'aukar kiran ya kara a kunnen sa yana amsa sallamar da ake tacikin wayar. daga cikin wayar akace "Ina kwana Abba ya gida dasu Ummi?." Abba ya ce "Lafiya lau sai dai mu yanzu rana ce ba safiya ba, ya harkokin dai?." ya ce "Alhmdllh." "To masha Allah Allah ya taimaka." ya ce "Amin amma Abba yanaji muryar ka haka gidan lafiya dai ko?." kai Abba ya girgiza cike da alhenin halin da suke ciki ya ce "Gaskiya kam a kwai damuwa dan har nafara tunanin neman ka ma sai ga kiranka." bayanin abun da ke faruwa yashiga zayyana masa, daga cikin wayar yad'an ja numfashi kana ya ce "To basai ya basu gidan da motar ba kawai yaje ya kama haya." Abba ya ce "Gidan haya kuma Usman? da tarin iyalai ai gidan haya bazai yiwuba Allah dai ya kawo mana mafita kawai amma muna cikin damuwa." "Amin." yafad'a a takaice tare da kashe wayar sa. jugum su Baba sukayi kowa da kalar tunanin sa.. A can kasar Spain USMAN SULAIMAN inkiya S.MAN kyakkywan saurayi ne ajin farko, yahad'a duk wani abun da cikakken namiji yake takama da shi, S.Man d'an kimanin shekaru 30 da 'yan d'ori, dogo ne me faffad'an kirji yana da haske sai dai ba can ba, yana da zubin karfafan maza zaratan maza. juyi ya yi daga kwancan da yake a kan wata lafiyayyen gado, yana kwance ruf da ciki kafafunsa suna ririto a kasa yayin da kafafun nasa suke sanye cikin takalmi sau ciki irin na 'yan kwallo. yana sanye da kayan kwallo a jikin sa. cikin rashin damuwa da halin da wan mahaifinsa yake ciki da yanzu Abba yagama sanar masa abun da ke faruwa, ya wurga wayar can gefe kana ya mike tsaye. yashige bathroom dan yanzu ya dawo daga gurin kwallo gaba d'aya a gajiye ya dawo. bayan wasu mintuna yafito d'aure da farar towel a kugunsa yanufi gaban gado wayar sa ya d'auka tare da dannawa lambar Abba kira. Abba da suke zaune har lokacin shi da Baba ya d'aga kiran tare da sallama. cikin ko oho ya ce "Har yanzu zaman jiran mafita kuke?." Abba ya ce "To ya zamuyi Usman yanzu a bun da nake tunani shine na had'a kan takardun kaddarorina muje bankin abasu idan kud'in bai kai ba in yaso sai a cire na accaunt d'ina nasan dai zasukai." ya ce "No Abba hakan baiyi ba taya za a yi ka aikata hakan bayan nan gaba idan rai yayi halinsa kaddarorin namune, baka tunanin hakan zai haifar da matsala yau she kake ganin zai samu wad'annan kud'ad'en ya biya a ina ma zai samu tukun, bayan ya rigada ya dawo talaka." Abba ya katse shi da fad'in "Kai kasan gawan fari ne wato fatan mutuwa kake min ko? kanka d'aya kuwa Usman kasan me kake fad'a kuwa nafa fiskanci zaman kasar arnan nan nason mai daka wani iri, a shekaran nan zaka dawo kasar nan dan babu abun da zaman can ke tsinanawa sai rashin daraja, tun da ka kammala karatun ka kadawo gida imma kasuwancin ne a kasar mu ma anayi, idan aikin gwamnatin ne ma duk akwai a nan in kwallon ne ma duk anayi, idan ba ka kira ka bada taka gudumawar bane to ka kashe wayar ka." baki S.Man ya tab'e tare da d'aga kafad'a cikin halin ko oho ya ce "To Abba ai dai gaskiya ce kuma ni ba fatan mutuwa nake maka ba,zan bashi aron kud'in idan yana bukata amma da sharad'in zai dawo min da kud'i na duk san da na duro Nigeria." da sauri Abba ya ce "To..to...to ba damuwa turo..turo mana." Abba ya juyo yana duban Baba cike da murnar samun mafita ya ce "Yaya kaji ko Usman zai bada aron kud'in." cikin murna mara misaltuwa Baba ya washe baki yana fad'in "Kai masha Allah Allah yayi albarka Usman kai madallah ai to mutashi muje bankin sai ya turo a can." kuma tab'e baki S.Man ya yi kana ya kashe wayar sa dan duk abin da yake fad'a yana ji.. cikin hanzari suka mike suka tafi banki, a can S.MAN yaturo musu kud'in direct bankin. ranar Baba yasamu yayi bacci mai dad'i dan tun da banki suka sashi gaba baya iya bacci mai nisa... SEEDRAH ce kwance tana manne da waya a kunnen ta suna waya da K'amal sai murmushi take sake wa tare da juyi a kan gado. Suhailat da ta shigo yanzu ta zuba mata ido tare da rike hab'a tana fad'in "Ikon Allah wacce take cewa a na damin ta da surutu yana hanata bacci idan ana waya itace manne da waya a kunne?, to nima kada a hanani bacci dan nima bacci zanyi." tayi maganar tana zama bakin gado. dariya SEEDRAH ta yi ta ce "Kai Aunty Suhailat ke dai kiyi baccin ki bazan dame ki ba." daga cikin wayar K'amal da ke jin su yasaki dariya tare da fad'in "Ah to a she haka kike fad'a musu itama ta rama kenan, Aunty Suhailat koreta taje waje." murmushi ta yi me sauti ta ce "Sai na kashe wayata tun da a sanyin nan kake ce a kore ni naje waje." murya ya d'an rage dan yasan halin SEEDRAH sarai zata iya kashe wayar ta barsa cikin bege da tunanin ta. ya ce "Sorry Baby a d'aki ma sanyin nan bai barka ba na isa a kora min ke waje, kin gan ni nan lullub'e da bargo amma sanyi nake ji ke bakya jin sanyin nan?." "Ina ji mana nima a rufe nake yanzu." numfashi yad'an ja tare da kuma rage muryar sa ya ce "Alhajina yayi tafi zai dawo jibi gata zai zo yasami Baba ayi-ayi magana dan gaskiya wannan sanyin yana bukatar ainahin bargo ne, idan kina cikin jikina bazanji sanyin ba kema haka." da sauri ta kifa fuskarta jikin pillow cike da jin kunyar maganar tasa. murmushi ya yi ya ce "Bakice komai ba." dad'a cusa fuskarta tayi batare da ta ce komai ba. sanin bazata ce koman ba ya ce "Yaushe zaki fara zuwa makarantar?." ta ce "Ranar monday." ya ce "Ni dai in da za'a bi tanawa da an aje batun makarantar nan tukun ayi maganar auren mu dan bana son batun makarantar ya saida maganar auren nan,idan aka kawo min ke ni da kai na zan rika kai kaya ta makaranta, dan Allah kiyi wani abu yanzu kam hakuri na yafara karewa ina bukatar ki kusa da ni." a hankali ta ce "To ni me zanyi a kai?." ya ce "Ki aje batun makarantar tukun idan akayi auren sai ki fara zuwa." ta ce "Ina son makarantar nan fa kuma ai shi bazai hana komai ba." ya ce "To shi kenan amma fa ki sani idan ki kazo sai kinyi wata uku kafin ki koma makaranta dan sai na ci angwanci na sosai." hirar su suka cigaba da yi, har Halimatu itama ta shigo kwanciya ta haye karifar tana fad'in "Mun shige su SEEDRAH sabon shiga har yanzu wayan kike kanyi?." dariya ta mata ta juya musu baya suka cigaba da hirarsu... Yau Monday hakan kuwa yayi dai-dai da ranar da SEEDRAH zata fara zuwa makaranta, da ke tasa ranta a tafiyar ko baccin asuba bata koma ba, gudun ma kada ta kwanta baccin ta mai nauyin nan yasata makara. tana gama shiri ta fito daga d'akin su ta nufi d'akin Mama. tasha lipton da biredi tayiwa Mama sallama ta fita. parlour'n Baba ta shiga da sallama yana zaune yana kallon labaren safiya a TV. ta sunkuya ta gaishe shi tare da fad'in "Baba nagama shiri zan shiga makaranta." ya ce "To madallah Allah ya taimaka ya bada sa'a a kula sosai." ya zaro d'ari biyar a aljuhunsa wan da dashi kad'ai ya kwana ya mika mata ya ce tayi kud'in mota. ta karb'a tare da yin godiya ta fita. ta isa Kasu, open university, poly d.s Kaduna state. taji dad'in makarantar ba kad'an ba,har kawa tayi yau wata wacce tayi ta shige mata duk da ita SEEDRAH bata wani saki jiki da ita ba, samari kuwa sunyi ta kawo hari dan SEEDRAH Allah ya hore mata farinjini ga tsarin zubin hallitta. da misalin karfe 2 da rabi tsaye take a bakin get d'in makarantar, tana tunanin ta yadda zatayi ta koma gida dan d'ari biyar d'in da Baba ya bata saura d'ari da hamsin ne ga wani masifaffen yunwan da take ji. dan tun lipton d'in da ta sha da safe shine a cikin ta har yanzu. idonta ta lumshe tare da d'an matse shi jin yunwan nadad'a fisgarta. a hankali ta bud'e idanunta jin magana kusa da ita. ta sauke idanunta kan wata motar dake gaban ta, matashi ne zaune cikin motar ya leko ta jikin windon motar yana fad'in "Ya ne 'yanmata tsayuwa a rana ba irin taku bace wannan tsadedden surar sassanyan inuwa da ac ne ya kama ta dashi,taya abun da baka saba da shi ba lokaci guda ka ce zaka yi shi, shi yasa kike rufe ido baki saba da rana ba, in babu damuwa shigo na sauke ki gida." kai ta kawar gefe a takaice ta ce "Nagode." taja kafafun ta tamasa can gefe. hon taji a bayanta taki juyowa zaton ta saurayin nan ne, jin an kuma dan na mata hon yasata juyowa a fusace dan ya gama cikata ga yunwa ga shi bata sami abun hawa ba ga kud'in hannun nata ma ba lallai bane ya kaita sai dai in taje gida ta nima cuko, cikin masifa ta bud'i baki zatayi magana sai ganin K'amal tayi yana kuma kokarin dannan mata hon d'in. baki ta turo gaba tare da kwab'e fuska cikin muryar shagwab'a had'e da yunwa ga kuma gajiya ta ce "Da ma kai ne? Allah na d'auka wani ne." dariya ya yi ya ce "Wai a ina kika aje wayar ki nake ta kira baki d'aga ba? shine tafiya makarantar babu sanarwa sai da naji gida ake fad'a min." kai ta langwab'ar gefe ta ce "Ayya wayar ma mancewa da ita a gida nayi." "Sabo da ana sauri ayi azo makaranta ko? ni gashi yau d'aya ma har naga kin rame min, zo mu tafi." gyarawa tayi ta haye mashin d'in ta na fad'in "Rama kuma? na dai san ina jin yunwa." ido ya waro ya ce "Haka ake yi a haka zakiyi karatun babu tsayuwa cin abinci babu zuwa da abincin makaranta?, to ni gaskiya ban yarda ki rika wahalar min da kanki ba." baki ta washe ta ce "Zuwa da abinci sai kace 'yar Naziri." ya ce "To ai kusan haka ne nifa ina tunanin ma tsalle kikayi a Secondary dan 'yar kamar kin nan baici a ce har kin gama Secondary ba." baki ta murgud'a ta ce "To ko sau d'aya ban tab'a sallaken ajiba tun ina da shekaru uku nake zuwa makaranta sai kayi lissafi." dariya ya yi hango yanda ta murgud'a masa baki ta cikin mirro ya ce "Oh haka ne fa shekarun zasu iya kaiwa 16 ke nan." hararar wasa had'e da murmushi tayi masa tana fad'in "To nafi haka." dariya ya yi ya ce "Da d'aya ba in ma kin kai 17 d'in ke nan." ko da suka iso gida lura da yanda take nannarkewa yasan tana jin yunwar sosai ya ce ta shiga gida zai dawo da daddare.. tana shiga a parlour'n Mama ta wurga jakarta ta fito sakar gida da sauri. nan ta tadda mutan gidan kowa ya nad'e hannu gaishe su tayi kana ta nufi kitchen da sauri tana fad'in "Ko sallah bazan iya ba sai naci abinci." Mama ta ce "Idan kika samu abincin ki kawo mana muma zamu ci." turus tayi tana kallon Mama fuska a marairaice ta ce "Mama ba'ayi abincin bane?." kai Mama ta kawar Umma ce tayi magana "SEEDRAH duk muma yunwan muke ji har yanzu jiran Baban ku muke babu ko kwayar hatsin da za'a girka a gidan nan." ji tayi yunwar da take ji gaba d'aya ya d'auke jiki a sanyaye ta dawo da baya. ido ta zubawa kannen ta Walida da Walid da suke rab'e jikin Umma ga dukkan alamu wutar yunwa ce ke azalzalarsu. da hannu ta kirasu suka mike tayi d'akin Mama suka bi bayan ta, jakar ta ta d'auka ta ciro d'ari da hamsin canjin da ta dawo da shi ta mika musu ta ce "Kuje ku shago ku siyo garin kwake kuzo ku sha." ai ko da gudu yaran sukayi waje.. Zubewa tayi saman kujera tare da sauke numfashi, yayin data lula duniyar tunani. lallai Allah ya jarafce su jarafta mafi girma, wai yau gidan su ne a ka tashi babu abincin da za'a ci. wan da a da sukafi karfin komai sai gashi dare d'aya Allah yayi wa mahaifin su kariyar arziki. numfashi taja tare da saukewa a fili ta furta "Allah kakawo mana mafita." daga cikin gida tajiyo sallama jin muryar mai sallamar yasa ta mikewa tafita, ganin babbar yayan su ce Hajara yasata fad'ad'a fuskarta da murmushi. Hajara itace babba duka a gidan itace 'yar farin Umma sai Suhailt da Halimatu, sai Walida da Walid sukuma tagwaye ne shekarunsu 6 kenan. Mama kuma 'ya d'aya Allah ya azirta ta da shi wato SEEDRAH ta dad'e kafin ta same ta daga kanta kuma bata sake haihuwa ba. Suhailat da Halimatu duk sun girmewa SEEDRAH shekarun Suhailat 25 Halimatu kuma 23 har yanzu Allah bai kawo musu mijin aure ba suna dai kan tab'a boko. SEEDRAH kuma shekarun ta 17 ne yanzu. babu laifi family'n suna zaman lafiya sai dai d'an abunda ba'a rasa ba. wannan kenan... "Oyoyo Aunty Hajara." cewar SEEDRAH tana rungume ta. murmushi Hajara tayi itama tana fad'in oyoyo. a sakar gida in da su Umma suke zaune ta zauna suka fara gaisawa, Halimatu da Suhailat suka fito bayan sun gaishe ta suka zauna aka cigaba da hira. hankalin Hajara yayi matukar tashi jin yau babu kwayar abincin da za'a girka a gidan nasu. ga Baba tun da ya fita bai waiwayo gidan ba bare a sa ran samun wani abun daga gare shi. 'yan kud'ad'en cikin jakarta ta curo naira dubu biyar a ka siya shinkafa aka kuma yi cefane nan 'yammatan gidan suka d'aura girki, shi suka ci har dare. har dare Hajara ta kai a gidan kafin ta koma gida, ta shiga tunanin ta yanda zatayi ta taimakawa mahaifan nata gashi mijin ta ba wani me karfi bane. d'an abincin da ya ajiye musu ta d'an sassakura ta aika da shi gida, sukuma sukarika manaje idan akayi abincin rana baza'ayi na dare ba. Baba kam dai yana zaune dan bashi da hanyar da zai nimo suci, abun da Hajara ta kalato da kuma wan da Abba ya d'an aiko musu da shi shi suke amfani da shi. nan fa karatun SEDDRAH ya fara tangad'i dan kud'in abun hawan da zata hau taje makarantar ma aiki ne. wani sa'in ta kira K'amal yazo ya kaita ida an tashi yaje ya d'auko ta, wani sa'in kuma taji nauyin kiransa haka zata zauna a gida. dan dole su Mama suka mike kowa ta nimi sana'ar yi a gida domin rufawa kansu asiri. a cikin wannan matsatsin da suke ne Abba ya bawa Baba naira dubu d'ari biyar ya ce yafara wata sana'ar in da zai samu yarika ciyar da iyalen sa... Bayan wani lokaci ranar wata juma'a dawowar SEEDRAH daga makaranta kenan, ta tadda Mama kwance numfashin ta sai sama da kasa yake. hankali tashe tayi kanta tashiga girgiza ta tana fad'in "Mama ciwon ki ne sannu bakisha maganin ki ba?, bari na kawo miki kisha." da kyar Mama ta iya bud'e baki ta ce "Maganin sun kare." hankali tashe SEEDRAH tayi waje tana fad'in "Bari naje na fad'awa Baba." ko da taje d'akin shi baya nan sai yanzu ta tuna shigowar ta bata ga motar sa bama a cikin get yafita kasuwa kenan. a rikice ta dawo d'akin, ganin halin da mahaifiyar ta take dad'a shiga yakuma birkitata. tsawon shekaru 17 kenan take fama da mugun ciwon hawan jini tun bayan haihuwar SEEDRAH. cikin bedroom ta shige da sauri ta shiga dube-dube a kasan pillow ta sami kud'i ta had'a kan 'yan canji duka naira dubu d'aya, takardan maganin Mama ta d'auka da sauri had'e da sassarfa tayi waje tana fad'in "Sannu Mama yanzu zan kawo miki maganin kisha." Tafiya take ko kallon gaban ta batayi, burin ta kawai ta ganta gaban shagon magani. gashi shagunan maganin unguwar su duk kanana ne basa sai da irin maganin Mama, dole sai ta tafi har babban titi. kamar zata tashi sama haka take sharar sauri,har ta iso daf da babban titi tana kokarin sallakawa. hon d'in da ya karad'e kunnuwan ta ne ya dawo da ita cikin nutsuwar ta, ta d'ago kanta da sauri. sai lokacin ta lura da gosulon daya cike titin had'e da hayaniyar mutane. gefe guda kuwa daga can gaban titin sautin kid'a ne mai had'e da taken Nigeria ke tashi, tsakiyar titin kuwa matasa ne had'e da motoci tam kan titin, matasan sai rawa da hele suke. ko wannen su rike da tutar Nigeria. idanunta ne ya sauka kan wata mota dake tsakiyar motocin matasa na zazzaune a kan motar ko wannen su na sanye da riga kalar tambarin tutar Nigeri yayin da suka sanya wani dake rike da kofin kwallo na zinari a tsakiya, ya d'aga kofin sama. daga gefe kuwa polisawa ne suke ta faman bud'e gosulo d'in... Kai ta saka da sauri da zummar fasa cikin mutanen ta wuce dan sai ta ketare titi kafin ta sami shagon magani. cikin tsawa taji ance mata "Ke ina zakije a nan, ki tsaya sai mai k'asa ya wuce kafin ki wuce!." da sauri ta juyo in da maganar ke fita sai taga daga cikin matasan da suke zazzaune kan motar nan ne wani yayi maganar. daga cikin su wani ya kuma yi mata hannu alamar ta koma da baya. wani irin kallo ta wasa musu mai cike da kunar rai tuno yanda ta baro mahaifiyar ta cikin mawuyacin hali,cikin dakewar zuciya ta wasa musu harara dukansu kana ta ce "Me k'asa a she shi ya halitto k'asar ma, bai san darajar uwa bace tana can kwance cikin mawuyacin hali, sabo da baku da imani da tausayi." da sauri ta saka kai dan gani take tsayuwar ta a gun ma b'ata lokaci ne...........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ ( _Bismillahirrahmanurrahim_) _Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690734_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* 🅿️7 Kokarin kuma dakatar da ita sukayi, wan da yake sakiyar su rike da kofin kwallo na zinari ya dakatar da su ta hanyar d'aga musu hannu alamar su rabu da ita. da sauri tarika fasawa cikin tarin jama'ar nan ta sallake titi. wani shago dake nan ketaren titin ta shiga, sai dai babu kowa cikin shagon. waige-waige ta shiga yi tana duba mai shagon amma baya ciki ko yaran shagon ma basa nan. can ta hango shi tsaye ta waje yana aikin d'aukar mutanen nan a waya. cikin hanzari ta zo in da yake ta ce "Malam kazo ka bani magani kabar gurin sana'ar ka kazo kallon wad'an can marasa aikin yi d'innan." ido ya waro ya ce "Ke sune marasa aikin yi d'in?, to wlh a kansu sai na iya kulle shagonan muje mu cashe a babban filin taro, da daddare karfe takwas ma duk wan da yazo shagon nan ba sami na zaiyi ba muna can muna murnar nasarar da d'an Nigeria kuma d'an jahata Kaduna ya buga kwallon duniya ya ciyowa kasar mu Nigeria a kwallon duniya baki d'aya, to bari kiji wannan taron da za'ayi gomna da shugaban kasa ne suka shirya, to ki dai na yi musu kallon marasa aikin yi." baki ta tab'e dan ita bata masan meye ma'anar wani kwallo ba dan ita gani ma take masu buga kwallo marasa aikin yi ne kuma wahalallu,suje suyi ta gudu duk su had'a zufa wani ma har ya karye, in ba rashin aikin yi ba meye wannan. ta ce "Ni dai muje ka bani magani ciwon Mamana ya tashi daga nan sai ka tafi gurin taron in kaje ka kwana a gun." k'arb'ar takardar maganin da kud'in yayi, ya shiga shagon ya d'auko mata ko da ya kirga kud'in ya dube ta ya ce "Ya naga dubu d'aya? maganin dubu uku da d'ari biyar." fuska ta marairaice ta ce "Dan Allah kayi hakuri ka bani maganin zan kawo maka cikon idan Baban mu ya dawo yanzu baya nan ne

Chapter 5 of 19