Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ce "Yaya yaron nan ne Usman yadameni da batun kud'in nan nasa tun shekaranjiya har yau ko a d'an kwai wani abu a gurin ka abashi dai-dai a samu sauran." Baba dake gaban teburin sa na aune-aune wan da sana'ar aune-aune ya koma da d'an kud'in da Abba ya bashi kan yaja jari dan yasami yanda zai rika ciyar da iyalansa. tun da yafara sana'ar nan baya wani ganin ci gaba madadin yasami riba sai fad'uwa, a duk san da ya auno hatsi dan ya siyar dakyar uwar kud'in sa yake fita maganar riba kam dai babu ita, bai kuma fasa sana'ar ba dan yana sa ran watarana zai samu. damuwa ce sosai ta bayyana kan fuskar Baba a wannan lokacin a halin da yake ciki yanzu ina zai sami naira miliyan 30 ko miliyan d'aya bashi da su bare miliyon 30. cikin damuwa Baba ya ce "Wlh Sulaiman kud'in dai basu samu ba, kabashi hakuri yad'an karamin lokaci zan nima insha Allahu zan bashi kasuwan ne yanzu sai a hankali." Abba ya ce "To bari na sanar masa Allah yarufa asiri." Da misalin karfe 8 na dare S.Man yashigo parlour'n Ummi suna zaune ita da Yusrah. guri ya samu ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour'n, Ummi ta dubesa da murmushi tare da amsa gaisuwar da yake yi mata. Yusrah ta dube shi tana fad'in "Barka da dare Bro." ido ya zuba mata yana mai jingina bayan sa da jikin kujera ya ce "Bar wannan gaisuwar je ki kawo min abinci yunwa nake ji." baki ta turo gaba dan ita bata so tayi gaisuwa a ki amsa mata, shi kuma baya wasa da cikinsa yanzu idan ta b'ata lokaci bata d'auko masa abincin ba sai ya iya sab'a mata. ta mike tanufi dinning tana magana kasa-kasa "Wai ka gaida mutum yaki ammsawa ni bazan ma kara gaishe ka ba." ta zubo masa abincin a plt ta kawo masa, tana aje abincin ya cafko kunnen ta yamurd'a. hannu ta kai da sauri ta rike hannunsa tare da fad'in "Wayyo Allah Ya S.Man kunne na zai tsinke." dad'a murd'e kunnen yayi kana ya ce "Tsinke shi dama zanyi me kike fad'a?." murmushi Ummi tayi ta ce "Ai dai kasan bazai wuce rashin amsa mata gaisuwar da bakayi ba kasan ta ai." sakin kunnen ya yi tare da dungurin ta ya ce "Wuce ki bar nan sai aka ce dole sai an amsa miki gaisuwar." da gudu tayi hanyar d'akinta tana matse ido da shafa kunnenta daya murd'e mata. Ummi ta gyara zama tare da duban sa da kyau yana cin abincin sa cikin kwanciyar hankali. ta ce "Usman me zaisa bazaka kara hakuri har Yaya Musa yasami kud'in nan yabaka ba, tun da bawai baka da kud'i bane a hannun ka, na tabbata kud'in da ka bashi kana da irin su sau ba adadi, me zai sa ka damu da sai ya mayar maka da su yanzu ka kara hakuri har ya samu mana." a hankali ya had'iye abincin daya kai bakin sa kana ya ce "To ai bazai samu ba ko nan da shekara nawa ne." Ummi ta ce "To ai abun da nake so ka gane kenan kayi masa hakuri har ya samu." "Ya sai da gidan sa kawai ya biya ni tun da bashida wata kaddarar bayan ita, ai na fad'a musu duk san da na shigo Nigeria zai dawo min da kud'i na, Ummi kiyi shiru kada ki kara cewa komai game da maganar nan dan sai ya biya ni gobe goben nan dan ina da abun da zanyi da su." ganin Ummi tana kokarin kuma jefo wata maganar yad'au plt d'in abincin sa yayi hanyar side d'in sa... Washegari da misalin karfe 2 na rana motar S.Man ne yashigo gidan Baba. yana dai-dai ta parking yafito yana mai karewa gidan kallo, a sannu ya jingina da jikin motar tare da hard'e hannunsa a kirji yana d'an kad'a kafarsa d'aya daya sarkafe su guri guda. hannu yasaka cikin aljuhun wandon sa yazaro wata sigari babba irin na rurawannan had'e da makunnin sa. ya kunna kana asannu yakai bakin sa yashiga zuko sa ya na buso hayakin, cikin nutsuwa. sai da yasha tabar natsawon mintuna biyar kana ya jefar da ragowar kasa, yasa kasan had'ad'd'en takalmin kafarsa ya murkushe. A sannu ya mike daga jinginen da yake yasoma tafiya yanufi kofar da zai sada ka da cikin gidan sannan ya tsaya batare da ya karasa bakin kofar ba. tsayuwar sa ya gyra da kyau tare da bud'e baki yashiga kwad'awa Baba kira, batare da yin sallama ba. Kamar daga sama su Mama dake zaune a tsakar gida suka jiyo kiran da S.Man yake kwad'awa Baba. Mama ta ce "Waye kenan da irin wannan kiran mafarautar haka, babu ko sallama." Umma ta ce "Wlh kuwa wannan ai sai ya tsinkewa mutun gaba da irin wannan kira." Suhailat da Halimatu na zaune ko waccen su na daddanna waya. SEEDRAH na gefe tana wankin kayan Mama. wani irin d'ago wa tayi jin yakuma fad'in "Alhj Musa!". a kufule ta mike tare da fad'in "Wai wani irin d'an rainin wayo ne wannan daga jin wannan murya dai bana abokin Baba bane sai dai in ko aiko sa akayi ya kira sa, sai ya rika yi masa irin wannan kira kajimin rainin wayo da rashin tarbiya." taja mayafinta dake kan igiya tanufi kofar gida tana cigaba da mita. Suhailat ta mike zumbur tana fad'in "Wannan muryar kamar na S.Man kada dai kuma shine kije kiyi masa rashin kunya." bata saurare ta ba tayi waje ita ma ta bi bayan ta. Tsabar jin haushi idanunta ya rufe tun kan ta kara fita tashiga fad'in "Ka koma a koya maka tarbiyya ta yadda ake kiran babba, kai idan akaje gidan ku ana kiran sunan Baban ka haka zakaji dad'i ne?." ido ya tsurawa kofar cike da mamakin son ganin wata isasshiyar ce, tana sako kafarta waje Baba na sako nashi. dan tun kiran farko da ya yi masa kasan cewar yana zaune cikin parlour'n sa ne ya mike ya fito bakin kofa dan tabbatarwa kansa da gaske shi d'in ake kira. jin kiran da gaske ne da sauri yariga Suhailat bin bayan SEEDRAH. da mamaki yake kallon S.Man dayake tsaye yana bin SEEDRAH da mugun kallo. Baba ya maida kallonsa gare ta sannan ya ce "Shiga gida SEEDRAH." sai da ta wasa masa wani irin kallo daga sama har kasa sannan ta murgud'a masa baki cike da tsiwa had'e da jin haushin sa ta yadda ya ke raina Baba wan mahaifinsa, tayi kwafa tare da juyawa ta koma ciki. Suhaita tun da taga shine har wani b'ari jikin ta yake,ta washe baki tana fad'in "Kamar na sani kuwa na ce wannan muryar Ya S.Man ne ashe dai kai ne anwuni lafiya ya gida." kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai, batare da ya amsa gaisuwar da take mika masa ba. itako ko a jikin ta bai dame ta ba da rashin kulatan da yayi, sai dad'a fad'ad'a annurin fuskarta take. Baba ya ce itama ta koma ciki har ta kule ciki tana waigen sa. Baba ya dube sa ya ce "Usman barka da zuwa shine zaka tsaya daga waje ai da ka shiga ciki, bismillah mushiga daga ciki." girman idanunsa S.Man ya rage tare da fad'in "No sauri nake kud'ina nazo karb'a d'auko min su na wuce sauri nake" Baba ya ce "A ai munyi magana da Sulai bai fad'a maka ba, ka kara hakuri inata kan kokarin neman kud'in kenan nasamu na had'a maka kud'in dan Allah ka kara hakuri." fuska ya d'aure tamau kana yashiga kad'a makullin motar da ke rike a hannunsa sannan ya ce "Bazan jira har sai an nima a bani ba yanzu nake bukatar su, nan da kwana uku zan dawo ka adana min kud'ina." yana gama fad'a ya juya yashige matarsa yabar gidan. Baba yabi bayan motar da kallo kana jiki a sanyaye ya koma ciki. S.Man na barin gidan gidan sa dake New G.R.A ya nufa, gida ne mai girman gaske ginin zamani tsarin ginin turawa yatsaru iya tsaruwa. ya bada kwangilar gina gidan tun yana kasar Spain, anjima da gina gidan anzuba kayan more rayuwa babu abun da babu. ankule gidan babu kowa cikin ta amma da ma'aikatan da suke zuwa gyaran gidan duk bayan wata 1, shiyasa idan kaga gidan bazaka tab'a cewa babu mai rayuwa cikin sa ba. kasancewar shi bawani zuwa Nigeria yake ba ko da yazo ma baya kwana a gidan sai dai yazo d'an fisha ya tafi, wani lokaci kuma yakan zo da abonsa suyi hira. koda yazo gidan bai wani jima ba yafita ya dawo gida a kitchen ya tadda Ummi tana aiki. sannu da aiki yayi mata kana yayi kokarin wucewa. Ummi ta dakatar da shi da fad'in "Wai yau ina kaje ne Usman baka ko tsaya kaci abincin rana ba?." hannunsa ya d'ago tare da duban tsadadden agogon da ke d'aure a hannunsa yaga karfe 3:30pm ya ce "Gidan Alhj Musa naje daga gun nawuce gida na." yayi maganar naya wuceta yabi ta kofar dake cikin kitchin d'in ya nufi side d'in sa. da mamaki Ummi tabi bayansa da kallo, dan tasan maganar kud'in sa ne kawai zai kaisa gidan Baba, dan haka siddan baya zuwa gidan idan yazo kasar nan. kai ta girgiza a fili ta furta "Allah shi kyauta." A b'angaren Baba kuwa jiki a sanyaye ya koma gida Mama da Umma har suna rige-rigen tambayar sa dalilin daya sa S.Man d'in tsayuwa a kofa ya na yi masa irin kiran da yayi masa batare da sallama ba. Baba yagirgiza kai cike da damuwa ya ce "Kunsan a zamanin da muke yanzu mai nima baya fushi haka za idan ana binka dole ka jure wulakanci,kud'i yake bina shine yazo karb'a." nan Baba yashiga yi musu bayanin yanda a kayi yabashi aron kud'i yabiya bashin banki, dan dama basu san ya amshi bashin banki ba basu kuma san da bashin bankin duka aka kwashe a accoun d'in sa da akayi masa sata ba . su Mama sun jinjina batun kwarai da gaske tare da tausayawa mijin nasu, sai dai sukayi ta karfafa sa tare da yi masa fatan samin bud'in Allah yabiya sa kud'in sa, duk da kuwa yawan kud'in da samun su zai iya d'au lokaci mai tsawo musamman a yanzu da suke cikin halin rashi. SEEDRAH da ta gama wankin da take tana shanya kayan taja tsaki wan da a zuciyarta tayi bata sammaci fitowarsa ba, tayi kwafa tare da kad'a harshen ta yabada sauti. dukkaninsu suka juyo gare ta Halimatu ta ce "Ke kuma da waye kk tsaki?." ta ce "Da wancan S.Man d'in mana yanzu dan yana bin Baba kud'i sai ya zo ya na yi masa irin wannan kira, ai ko wan da bai sansa ba bazai yi masa irin haka ba bare kuma Baba." kai Baba ya girgiza ya wuce d'akin sa. Umma ta ce "Ai kuwa bai kyauta ba, dama rayuwa cikin turawa mene ne." SEEDRAH ko kunkuni ta cigaba da yi kasa-kasa. "To ai sai kuma kiyi shiru haka dan ke rashin kunya baya baki wuya yayanki ne dai ba kece gaba da shi ba ko sai kin zage sa kihuta." Suhailat ta fad'a tana aika mata harara. baki SEEDARH ta murgud'a sannan ta ce "Shikuma yanzu da yazo yabo yayi ai ba rashin kunya wa nagaba da shi ba." ta juya tawuce d'aki. Suhailat tabita da harara... Tana shiga ta tadda wayarta na ring jin sauti na musamman dake tashi cikin wayar yasa ta sakin murmushi dan sanin mai kiran nata, ta isa in da wayar yake ta d'auka tare da niman guri ta zauna bakin gado, kana tayi picking na call d'in ta kai kunnenta tare dayin sallama. daga cikin wayar Kamal ya ce........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ ( _Bismillahirrahmanurrahim_) _Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 9 "Albishirin ki." murmushi mai sauti tayi sannan ta ce "Goro." a b'angaren Kamal shima murmushin yake zubawa da kaji shi zakasan yana cikin farinciki sosai. ya ce "An bani ke yau alhajin mu yake fad'a min yazo gurin Baba neman izini tun d'azu nake kiran ki nabaki daddad'an albishir d'in nan bakya d'aga wayar." cikin shaukin kauna da soyayya ta ce "Wayar tana d'aki ne ni kuma ina waje ina yiwa Mama wanki, lallai ka kawo albishir mai girma zan kuwa baka tukuicin ka yanzu." ta karashe maganar tana y'ar dariya ya ce "To ina jira ina jin ki bani tukuici na." zaman ta ta gyara a sannu ta mai da bayanta ta kwanta jikin pillo, cikin murya mai zaki da narka zuciyar masoya ta ce "Rufa idanunka." a b'angaren Kamal d'in shima zaune yake kan katifar sa a cikin d'akin sa, yana rungume da pillo a kirjin sa. a sannu ya maida idanunsa ya lumshe yayin da sautin muryarta mai zaki ke rasa cikin kwakwalwarsa, sonta da kaunarta suna tsarga jini da jijiyarsa. "Uhm ina jiran tukuici na." yayi maganar yana dad'a lumshe idanunsa ya dad'a rungume pillon ya cusa shi cikin kirjinsa sosai. a hankali cikin wani irin sauti mai dad'i da zaki ta ce "I love you!." ajiyar zuciya mai sauti yasake tare da fad'in "Godiya mara adadi hakika kin bani tukuici mai girma wannan tukuicin yafiye min kyautar gida da mota har da karin mata ko da indiya ce." fuska ta kwab'e ta ce "Me ye na sako wata mace cikin zancen." dariya yy cikin tsigar zolaya ya ce "To ke da za ayi miki kishiya bayan aure da shekara zaki hana zancen wata mace." d'ip ta kashe wayar tare da jefar da shi gefe ta mike tana fad'in "Ka auro uku rana d'aya." ta shige bayin Mama, wanka tayi ta fito tatafi d'akin su ta shirya cikin riga da siket na atamfa kalar ja. tayi kyau sosai cikin shigar duk da batayi wa fuskarta kwalliya ba dan ita ba ma'abociya penti wa fuska bace, mai da pauda da manbaki sune kad'ai kayan kwalliyar ta. waje tayi jin Mama tana kwad'a mata kira. wayar ta Mama ta mika mata tana fad'in "Karb'i tun d'azu ake ta kira." tun kan Mama ta rufe baki wani yaro ya shigo yana fad'in "Wai SEEDRAH tazo inji wani a waje." karb'ar wayar tayi daga hannun Mama tana duba mai kiran nata murmushi tayi ganin kiran Kamal yacika wayar, tasan za'a yi haka ko yanzu ma da akazo kiranta tana da tabbacin shine yazo. D'aki ta koma tad'au mayafin ta tafita, a tsaye ta iske shi a kofar gida tacikin get. baki ta turo tatsaya daga can d'an nesa da shi ta hard'e hannayenta a kirji ta kawar da fuskarta daga kallon shi. murmushi ya sake me sauti ya tako gabanta ya tsaya yad'an tsunkuyo tare da loko fuskarta. fuskanta ta kuma juyawa gefe tare da kuma turo baki gaba. fuska ya marairaice kamar karamin yaro yakai hannu yarike kunnuwansa ya narke murya kalan tausayi ya ce "A yafewa bawan Allah afuwa yake nima bazai kara ba." baki ta murgud'a tare da kad'a kwayar idanunta ta ce "Ka koma kaje ka sami 'yar india." dariya ya tuntsure da shi sosai ita ko ta juya da sauri zata koma gida. da sauri ya sha gabanta yakuma kai hannu yarike kunnuwan sa ya ce "Yi hakuri mana rikicacciyata ai ko matan duniyar nan gaba d'aya zasu taro babu wacce ta isheni kallo bare saurare, ayafewa bawan Allah, bazai sake sako wata cikin zance ba daga yau." baki ta murgud'a ta ce "Oho ba ni inaruwa na ma." dariya yy cikin zolaya yaleko fuskarta ya ce "Ashe haka ake kishi na?." kwayar idanunta ta kad'a sannan ta ce "Waya fad'a maka." murmushi yy ya ce "Gashi nan ina gani." baki ta murgud'a ta ce "To ba haka bane." dariya yayi yana mai jin shaukin tsiwarta da sonsa da yake hangowa tattare da ita. nan suka shiga hirarsu cikin so da kaunar junansu, zuwa can sukayi sallama ta koma gida... S.Man ne yafito cikin shigar manyan kaya, yayi matukar kyau cikin shigar, kasan cewar shi bai cika saka jamfa ba yafi mu'amala da kananun kaya. idan kagansa da manyan kaya to yazo Nigeria ne ranar juma'a ko halartar d'aurin aure sai ya saka manyan kaya. cikin d'an sauri yake tafiya yakara so cikin parlour. Ummi tadube sa tana fad'in "Inazuwa da sauri haka Usman? yanzu nake shirin nimanka muyi magana." hannunsa ya d'ago tare da duban tsadedden agogon dake d'aure a hannunsa kana ya ce "Zanje d'aurin auren wani abokina ne a Abuja sauri nake Ummi bayan sallar juma'a za'a d'aura, idan na dawo sai muyi maganar." "To Allah ya tsare adawo lafiya." "Amen." yafad'a yana fita daga parlour'n... da misalin karfe 12 na dare S.Man ya dawo, ganin dare yayi bai wuce gidan Abba ba. gidan sa yawuce. yana isa ya yi hon maigadin dake gadin gidan duk da babu kowa cikin gidan da akwai mai gadin gidan, yabud'e masa get ya kusa hancin motarsa ciki. A gajiye ya fito daga cikin motar yana amsa gaisuwar da maigadi ke miko masa ya wuce cikin gidan. direct d'akin sa dake sama ya wuce, yazuba wayoyin sa saman bedside yarage kayan jikinsa ya fad'a bathroom. minti 20 ya d'auka cikin bayin yafito d'aure da towel a kugunsa, ya isa gaban wardrobe yazaro wata tattausar rigar bacci mai mad'aurin igiya had'e da boxes ya saka. ya haye lafiyayyen gadon sa dake a gyare tsaf sai baza kamshi yake, yarage wutan d'akin yayi addu'a ya kwanta babu jimawa bacci yayi gaba da shi. Washegari yana dawowa daga sallar asuba can gefen parluorn kasa ya isa in da na'u'rorin motsa jiki suke. bai sakaita ga motsa jikin da yake ba, sai da yashafi tsawon awa uku. yazube kan wata kujera dake gurin yana maida numfashi tare da share gumin dake sauko masa da karamar towel yayin da d'aya hanunsa ke rike da gorar ruwa yana sha. wayar sa ya d'aga ya lalub'o number Ummi, tana d'agawa ya ce "Ummi yunwa kisa a kawo min abinci yanzu ina gida na." yana gama fad'a ya kashe wayar. mikewa yayi yahaura sama, bathroom ya shiga yayi wanka kana yafito d'aure da towel a kugunsa yana tsane ruwan jikin sa da wata tattausan farar karamar towel. yashirya cikin riga singlet da wando iya guiwa, sai tashi da daddad'an kamshi yake. ya haye gado. kwance yake a kan gadon yayin da waya ke rike a hannunsa yana d'an daddannawa. hannunsa yakai saman cikinsa ya shafa. number Ummi ya kuma dannawa kira "Ummi har yanzu ba a kawo min abincin ba." "Kasan dai sakanin nan da gidan ka akwai nisa Yusrah tana hanya tafita bada jimawa ba zata iso." Yana kashe wayar bada jimawaba Yusrah ta iso. ko da yagama breakfast kwanciya yayi, sai wajen azahar ya farka. wanka ya kuma kana ya shirya cikin kananun kaya, ya d'au makullin motarsa ya fita. a masallacin dake jikin gidansa yayi salla kana yad'au motarsa yanufi unguwar rimi gidan Baba. ko da ya isa gidan yana dai-dai ta parking a farfajiyar gidan ya fito ya jingina da jikin motar yayin da ya hard'e hannayensa a kirji. murya ya d'aga yashiga fad'in "Alhj Musa Alhj Musa!." a can cikin gidan kuwa SEEDRAH data fito daga d'akin Mama zataje kichin, rike da tray da shingafar da zataje dafawa ciki. cak tatsaya jin kiran da akewa Baba, ko ba a fad'a ba tasan S.Man ne da irin wannan rashin darajar. da sauri ta dire tray'n shinkafar kasa ta nufi waje cikin sauri tana fad'in "Idan ba a ja masa layi ba zaiga kamar ko tsoronsa a ke ji, ai ba akan Baba kad'ai aka fara cin bashi ba gwamnati ma tana ci." ta karashe maganar da take acikin ranta dai-dai lokacin da take karaso wa inda yake. kugu ta rike tana yi masa wani irin kallon sama da kasa. cikin murgud'a baki cike da tsiwa ta ce "Rashin daraja nagaba ne ko karancin tarbiyya? har idan zakazo kacigaba da yiwa Baba kiran dirar mikiya batare da girmamawa ba kai ma baza a girmamaka ba, sannan kasani mu musulmai ne mun iya amsa sallama, kud'in ka kuma kaje duk san da Baba ya samu zai baka yanzu bashi da su." Wani irin kallo mai had'e da zalrar mamaki yake bin yarinyar da shi, ransa yayi mugun b'aci. wannan yarinyar da bata wuci sa'ar Yusrah ba itace ta tsaya a gaban sa take gaya masa bakaken kalaman da babu wan da ya tab'a tsayuwa gaba da gaba ya fad'a masa. da sauri ya kai yannu cikin aljuhun wandon sa ya zalo sigari had'e da makunnensa, makunnin nasa kad'ai abin kallo ne dan ba irin na kasar mu bace haka ma sigarin irin na kasashen turai d'in nan ce, yasaka tabar a bakin sa kana yakunna sigarin. ya zuko hayakin sigarin tare da huro hayakem waje, da sauri-sauri yake zuko hayaken tare da huro shi, sumar kansa ya shiga shafawa da d'aya hannunsa. sai juya gefe da gefen sa yake, yama rasa me zaiyi wa yarinyar nan. ji yayi kamar ya b'ab'b'allata ya zubar da ita a gurin. da sauri ta kawar da kanta tare da toshe hancin ta tana yamusa fuska cikin yin kasa da murya ta ce "A she dai d'an shaye-shaye ne haba dole mana." Zaro sigarin ya yi a bakin sa muraran kake iya hango matsanan ciyar b'acin ransa kan fuskarsa kana ya ce "Zan nuna miki halin d'an shaye-shaye kuwa!." kafad'a ta d'aga kana ta juya cikin sauri dan ta d'an razana da jin kalaman sa da kuma yanda taga yarikid'e yakoma mata na mijin zaki. cike da karfin hali da dakiyar zuciya take fad'in "Koma meye kayi Allah na tare da ni." tayi cikin gida da sauri. Shiko wurgi da sigarin hannunsa yayi yashiga motarsa yajata da mugun gudu yabar gidan. gidan Abba ya nufa. yana isa direct side d'in sa ya wuce batare da yabi ta cikin parlour'n Ummi ba. yana shiga bedroom yad'au System d'in sa ya zauna bakin gado ya kunna kana yashiga dube-dube aciki. yad'au tsawon mintuna 15 yana sarrafa na'uwar kana ya rufe ya tura gefe. d'an kishin gid'a yayi a kan gadon kana ya d'au wayarsa ya daddanna ya kai kunnensa. magana ya soma wan da ni bana jiyo abin da yake fad'a, daga bisani ya kashe wayar. ya mike yashiga tarkasa abubuwan da yake bukata kana yad'au laptop d'in yayi waje. ta sashin Ummi yabi a parlour ya taddata, ya zauna tare da gaishe ta. ta amsa tana fad'in "Dama ka shigo ne?." "Ban jima da shigowa ba yanzu zan koma dan nayi ba'i." "Abinci fa da dai ka tsaya ka ci kada ka tafi ka soma kiran a kawo maka." mikewa tsaye yayi yana fad'in "Bani abincin natafi da shi sauri nake." Ummi ta mike ta nufi kichin tazubo masa abinci cikin kula ta sakashi cikin basket had'e da plt da cukali, sai kwalin lemo da gorar ruwa had'e da cup ta fito ta samu har yayi waje. Yusrah ta kira ta bata basket d'in ta kai masa cikin mota, ta bud'e sit d'in baya ta aje basket d'in ciki. tana rufe murfin motar ya ja motar da sauri yabar gidan.. Bayan kwana biyu Yau da wuri SEEDRAH tagama aikin ta kasancewar yau asabar ne tana gida. daren jiya Kamal yayi mata alkawarin kaita gidan kawarta Naseeba. karfe sha d'aya tagama shiri tafita rike da waya a kunnenta tana fad'in "Gani fitowa." d'akin Mama ta shiga tayi mata sallama dan tun ajiyan ta fad'a mata zataje gidan Naseeba, ta ce mata kada ta kai dare ta dawo da wuri. Kamal natsaye a bakin get takaraso in da yake tare da hararar sa cikin tura baki ta ce "Wannan kallon fa?." numfashi ya sauke tare da kyakkyafta idanunsa da tun fitowarta yakafe ta da su ya ce "Baby kinyi kyau fa kamar na kwana ina kallon ki." 'yar karamar dariya tayi ta ce "Kwana a tsaye ko a kwance." "Duk yanda kike so zaki shigo hanu ai zakiyi bayani." fuska ta b'ata tare da turo baki ta ce "Banson haka fa ni banja da tsawo ba." dariya ya yi kana ya d'an kwanto mata da mashin d'in ya ce "Hau muje nima ban warware zargen ba." Suna tafe suna hirarsu cikin so da kauna har suka isa gidan su Naseeba, a kofar gidan ya faka mashin d'in sa yana gaba tana biye da shi suka shige gidan

Chapter 7 of 19