yau basu da walwala duk wan da ka gansa kasan yana cikin damuwa, gashi suna ta kiran Baba baya d'agawa.
tun safe sai wajen k'arfi uku kafin yadawo, gaba d'aya suka hallara a parlour'n sa, nan yake sanar musu banki sunyi iya binciken su sunce basu gano wad'an da suka aikata masa hakan ba, amma yaje wani sati yadawo kafin sun dad'a fad'ad'a bincike.
basuji dad'in jin hakan ba sai dai basu da yadda zasuyi..
Kamar yanda Kamal ya ce wa SEEDRAH zasu dawo da Mukhtar bayan kwana uku, hakan kuwa akayi da yamma suka zo kofar gidan su SEEDRAH ya ai ka aka kirata, tana ganin sune ta b'ata fuska a jikin get ta tsaya ta hard'e hannayen ta akirji.
murmushi Kamal ya yi suka karaso in da take.
Kamal ya dube ta da murmushi d'auke a kan fuskarsa ganin yanda tawani sha kunu, shi harga Allah yarinyar dariya take bashi idan yaga tana wani b'ata rai ga iya zare zance kamar wata babba, a kallon da yake mata shekarun ta bazasu wuce 17 zuwa 18 ba.
ya ce "Ranki shidad'e barka dawarhaka da fatan kina lafiya?.
kad'a kwayar idanunta tayi ta ce " Gashi dai kana gani."
kai ya girgiza Mukhtar daya d'an sunkuyar da kansa ya d'ago "Barka da yamma ya gida?."
batare da ta amsa masa ba ta ce "Kufad'i a bin da ya kawo ku nagode da gaisuwa."
Kamal yad'an gyara tsayuwar sa ya ce
"Ina fata zuciyarki tad'an sanyaya cikin kwanaki ukun nan, kamar yadda na fad'a miki zamu dawo bayan kwana uku gani ga Mukhtar dan Allah ki kirawo mana kawarki munimi gafarar ta."
"Bama bukata kuje abun ku kudai cigaba da zaman jiran kira daga kotu."
da sauri Mukhtar ya ce "Please dan Allah kiyi hakuri ki kirawo mana ita dan Allah! badun niba,
a shirye nake da karb'ar duk wani hukuncin daya sauka a kaina amma kafin nan ina so na had'u da ita nanemi yafiyarta dan Allah!."
baki ta tab'e kamar zatayi magana sai kuma ta juya ta nufi gidan su Nasiba.
a gurin wanke-wanke ta isketa tana wanke-wanke,ta sunkuyo kanta a hankali ta ce
"Mutanen nan ne suka zo wad'an da suka bimu a unguwar su Nabila, ranar d'ayan ne yazo wan da yad'auke ki a mashin d'in sa ya kaiki gidan goggo wai shi Kamal yaso nakiraki naki, shine ya ce zasu dawo bayan kwana uku ban fad'a miki bane,suna ta magiya wai dan Allah kifito hakuri sukazo baki da niman yafiyar ki."
rau-rau Nasiba tayi da ido ta ce "Ki ce wan da ya yi min fyad'e ni babu in da zan je yatafi bana ma son ganin fuskarsa."
SEEDRAH takuma rage murya ta ce
"Ki yi hakuri kizo wlh nayi ta musu kora da hali har nafito na ce musu bazan kirawo ki ba bakiga yan da suke ta rokona ba, shi kamma Mukhtar d'in bakiga yadda yake yi ba kamar zai zubda min kwalla."
kai Nasiba ta sunkuyar cike da d'acin rasa budurcin ta bata kuma yin magana ba.
SEEDRAH ta sunkuya ta shiga taya ta wanke-wanke dama saura kad'an ne ta gama, suna kammalawa Nasiba ta mike taje ta d'auko hijabinta taleka d'akin Mama Kubura ta ce da ita zata shiga gidan su SEEDRAH.
daga nan suka fito SEEDRAH na gaba Nasiba na biye da ita.
in da ta barsu nan suka iske su, tun kan su karaso gurin Mukhtar ya kafe Nasiba da ido yanajin zuciyarsa babu dad'i.
nan take yaji kunnuwansa sun amsa da ihu da magiyar da take masa lokacin da yake kokarin yimata fyad'e da kuma karanta mai tsananin karfi a lokacin da yashige ta yafasa budurcin ta.
rumtse idanunsa ya yi da karfi tare da kai hannunsa ya toshe kunnuwansa da karfi yana girgiza kansa tare da taune lab'b'ansa.
jiki a sanyaye Nasiba ta tsaya d'an gefe da SEEDRAH, Kamal ya kai hannu yana d'an bubbuga kafad'ar Mukhtar daya lura da halin da ya shiga ganin Nasiba, sai a lokacin ya bud'e idanunsa da suka kad'a sukayi jajir.
da sauri Nasiba ta juya zata bar gurin ganin fuskar mutumin daya keta mutuncinta.
da sauri Kamal ya ce
"Dan Allah kada ki tafi ki saurare mu ko da na mintuna biyu ne,
ki sani akwai masu yiwa y'ammata fyd'e su gudu ko da kuwa an neme su baza a same su ba, amma shi da kansa yakawo kansa domin ya nemi yafiyar ki kafin hukuncin da zai zartu a kansa, ki sani Allah yana son me yafiya idan kayafewa d'an uwan ka sai shima yagafarta maka."
cak ta tsaya yayin da hawaye ke zuba a idon ta,
Mukhtar da gaba d'aya jikin sa yagama yin sanyi ya jawo kafafun sa da kyar zuwa gaban ta ya zube guiwowinsa a kasa, tare da had'e hannayen sa biyu, murya a matukar raunace ya ce
"Dan Allah dan Annabin sa mai dubun daraja! ina mai rokon ki daki yafe min, ina mai nadama da da nasanin aikata miki haka, hakan ba halina bane dan ban tab'a ai katawa ba sharrin shaid'an ne, na roke ki kiyafe min daga nan kuma ki kaini in da zaki kaini aje a yanke min duk kan hukuncin daya da ce da ni, amma kafin nan ina mai rokon yafiyar ki."
Yadda yake maganar cikin rauni sosai ga hawaye nabin gefen fuskarsa namiji kamar shi da zuba goiwowinsa a kasa da kuka da magiya da roko.
yasa SEEDRAH jin jikinta ya yi sanyi, ta dafa kafad'ar Nasiba da ke hawaye ta dubi Mukhtar ta ce
"Ka tashi zata yafe maka in sha Allah amma dai ka cutar da rayuwarta kam."
kai ya jinjina ya ce "Na sani shi yasa nake son gyara kuskure na, idan ta amince zata aure ni nikuma a shirye nake nashare mata bakin cikin dana jefa rayuwar ta ciki."
wani irin d'agowa Nasiba tayi ta dube shi sai kuma ta juya da sauri had'e da sassarfa tanufi cikin gida, tana mai zubda hawaye masu zafi.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️5
Da mamaki SEEDRAH ta ke kallon sa sannan ta ce
"Aure kuma?." kai ya gyad'a cike da tabbatar da gaskiyar sa.
Kamal ne ya dube ta ya ce "Ko bakya goyon bayan hakan ne?, Har idan ta amin ce shine hanya mafi sauki da zai bi ya rarrashi zuciyar ta."
baki ta tab'e a kasan ranta ta ce "D'an shishshigi watakila ma kai ka tsara hakan ma." a fili kuwa ce wa tayi
"An tab'a auren da babu so bare kauna? bugu da kari kuma yanzu a kullace take da shi a zuciyarta ta ya ma hakan zai faru bayan shima ba son ta yake ba, kawai kuje ba lallai bane hakan ta yuwu."
da sauri Mukhtar ya ce "Ina son ta da gaske tun ranar dana yi mata fyad'e zuciyata takamu da son ta, son ta da damuwar abunda nayi mata sune suka had'u suke damuna, dan Allah ki tabbatar mata da ce wa zuciyata tana tare da ita."
Kamal ya ce
"Kwarai kuwa dan aboki na baya karya dan Allah ki shawo mana kanta."
hararar sa tayi kana ta juya ta soma tafiya ta na fad'in
"Amma ya iya mugunta ai."
wani sassanyan murmushi Kamal ya bita da shi yana shafa gefen fuskarsa ya yin da idanunsa ke kanta har ta shige gidan su Nasiba, sai sannan sukuma suka tafi.
A d'aki SEEDRAH ta iske Nasiba kwance a kan katifa tana kuka, ta zauna a gefen ta tare da dafa kafad'arta kana tayi saurin mai da hawayen da taji sun ciko mata ido tayi kokarin rarrashin kawar tata gudun kada ta kuma karyar mata da zuciya.
SEEDRAH ta ce "Naseeba kiyi hakuri nasan d'aci da kunar da kike ji a zuciyar ki amma ki sani auren Mukhtar shine kad'ai rufin asirin mu, tabbas naga son ki cikin idanun Mukhtar kibashi dama kawai."
mikewa Naseeba tayi zaune tare da share zafafan hawayen da suke zubo mata tarike hannun SEEDRAH cikin zubda kwalla ta ce
"Ni ma hukuncin dana yankewa kaina kenan a yanzu haka na aminta da auren nasa,
dan nasan hakan ne kad'ai rufin asirina, dan babu wan da za'a kwashe masa ni a kaini gidansa ya iskeni sauran wani yazauna dani cikin aminci, shi d'in daya rusa katangar budurcina da shi zan rayu a haka ko da bana son sa."
kuka ne ya kwace mata takifa kanta a cinyar SEEDRAH tashiga rera sabon kuka.
duk dauriyar da SEEDRAH takeyi kan kada tayi kuka tacigaba da karfafa mata guiwa sai da ta fashe ita ma da kukan suka cigaba da rera kukan tare.
jin motsin Mama Kubura a tsakar gida yasa su sassauta kukan nasu, SEEDRAH bata bar gidan ba har sai da taga zuciyar kawar tata yad'an sanyaya...
A b'angaren su Mukhtar kuwa kullum sai sun zo unguwar su SEEDRAH watarana ta fito watarana taki fito wa,idan har kuma ta fito taje kira musu Naseeba bata yadda tafito haga zasu karaci tsayuwar su sutafi..
bayan sati biyu Mukhtar ne yakai kansa da kansa kotun musulunci dake nan cikin garin Kaduna, yakuma fad'i laifin daya aikata harya kai ga zuwa da kansa kotu dan a yanke masa hukuncin daya dace da shi a musulunce.
da fari alkalin yabukaci da azo da wacce yayi mata fyad'en Mukhtar d'in ya hana faruwan haka ta hanyar fad'in, shi bai ma san ta ba.
yayi hakan ne kuma badun komai ba sai dun kare martabar ta a idon duniya.
a take a gurin a ka yanke masa hukuncin bulalu kamar yadda addinin mu ya shar'anta, bakuma tare da tozarci ba, duba da irin namijin kokarin da yayi nakawo kansa da kansa domin a yanke masa hukunci, wanda a zamanin mu na yanzu ba kasafai ake samun masu tsoron Allah irin haka ba, su aikata laifi susan basuyi dai-dai ba har sukawo kansu gaban shari'a dan a yanke musu hukunci ba.
sab'anin da yanzu ma mutum zai aikata laifin gashi a bayyane a na gani kiri-kiri ya aikata ya kuma yi musu haka za'ayi ta tuka shari'a da shi karshe ma shari'ar tabi iska...
Bayan an gama yanke masa hukuncin yana kwance a kasa shame-shame yana sauke numfashi a jikkace. da kyar ya iya d'aga wayansa da tun zuwan sa kotun ya kashe, ya kunnata kana yakira Kamal da tun d'azu yake ta zaryar niman sa baigansa ba yakira wayansa kuma baya shiga.
Kamal na d'agawa ya ce "Mukhtar ina ka shiga ne tun d'azu nake ta kiran wayar ka baya shiga?."
ido Mukhtar ya rumtse jin yadda jikin sa ke masa rad'ad'i da mugun tsami ya ce
"Kazo ka taimaka min muje gida."
jin muryar sa hankali tashe Kamal ke tambayansa meke faruwa yana kuma ina?.
ya shaida masa inda yake, hankali a mugun tashe Kamal yanufo koton cike da tunanin abun da yakai Mukhtar d'in koto, dan Mukhtar bai fad'a masa zaizo kotu ba.
da tunanin ko iyayen Naseeba ne suka kaishi koton Kamal ya iso kotun.
ganin halin da abokin nasa yake ciki hankalin sa yakuma mummunar tashi.
da taimakon mahukuntan kotun Kamal ya iya d'aga Mukhtar da baya iya motsa ko da d'an yatsansa, suka d'aurashi a mashin.
direct asibiti yanufa da shi,
da fari a kaki karb'an shi a kace sai yazo da hukuma, sai da Kamal ya yi ta had'asu da Allah kafin suka karb'e shi suka shiga bashi taimakon gaggawa.
har yamma suna asibitin sai sanan Mukhtar ya farka daga baccin da ya ke, sakamakon alluran baccin da a ka masa.
Kamal ya matso bakin gadon da yake kwance cike da tausayi yana yi masa sannu, kana ya juya da sauri yana fad'in
"Bari naje na samo maka abun da zaka ci."
Mukhtar ya ce "A'a bana jin yunwa Maman Zeey fa tasan ina asibiti kuwa?."
shiru Kamal yad'anyi kana ya ce "Ni ma tunanin da nake tayi ke nan tun d'azu idan har ta ganka cikin wannan halin me za'a cemata."
ido yad'an rumtse tare da bud'e wa ya ce
"Ka fad'a mata ina asibiti itama tazo ta yanke min hukuncin daya dace da ni."
ya yi maganar yana mai taune lab'b'ansa cike da kunar zuciya.
Kamal ya girgiza kai tare da zaro wayarsa ya lalub'u lambar Maman Zeey.
bugu d'aya a na biyu ta d'a, bayan sun gaisa ya ce da ita suna asibiti da Mukhtar.
cikin matukar tashin hankali take tambayar sa abun da ya sami Mukhtar d'in, bata iya nutsar da zuciyarta bama taji amsar da zaibata ta ce masa wani asibitin?.
yafad'a mata sunan sa ta kashe wayar tare da d'aukar mayafinta da kud'i tayi waje.
Zeey tabi bayan ta da sauri tana tambayarta meke faruwa ta ce mata Mukhtar ne yake asibiti.
itama hankali tashe ta d'au mayafin ta tabi bayan mahaifiyar tasu, suka tsari napep suka nufi asibitin.
Ko da suka iso ganin halin da d'an nata yake ciki yasa Maman Zeey nufar gadon da yake kwance tana fad'in
"Me ya same ka haka Mukhtar b'arayi ne sukayi maka haka kokuma hatsari kayi?."
rumtse idanunsa ya yi da karfi yana mai cike da dana sani. tabbas baka da makiyi irin shaid'an idan kuma kabiyewa zuciya da shaid'an ke tunzura shi izuwa aikata sab'on Allah hakika kana cikin asara da tab'e wa had'e dajin kunyar duniya, idan baka hankalta ba kuwa har da ma kunyar lahira data fi ta duniya.
Maman Zeey ta ruko hannunsa tana cigaba da fad'in
"Mukhtar meya sameka haka!?."
tayi maganar hankali a matukar tashe kana ta juya ta dubi Kamal ta ce
"Kuyi min magana mana me ya same shi haka!?."
Zeey da itama hankalin ta ya mugun tashi ta ce
"Ya Mukhtar meya same ka haka?."
tayi magana hawaye na ciko mata ido.
sai sannan Mukhtar ya bud'e rinannun idanunsa ya zubawa mahaifiyar tasa kana yakankame hannun ta dake rike da nashi sannan ya ce
"Maman Zeey kiyafe min kiyafe min dan Allah."
wasu zafafan k'walla ne suka zubo masa.
Kamal ya dubi Zeey da tuni hawaye ya soma zuba a fuskarta ya ce
"Ki d'an bamu guri zamuyi magana."
jiki a sanyaye taja kafafunta tayi waje.
hannun Maman Zeey
Mukhtar yakuma rike wa gam hawaye na wanke fuskarsa, gaba d'aya jikin ta yagama sanyi tana tunin wani irin babban abu ne yasami d'an nata haka.
cikin rawar murya Mukhtar yake fad'in
"Maman Zeey kema ki yanke min hukuncin daya dace da ni kamar yanda suma suka kayi min sannan kiyafe min."
cikin rashin fahimta ta ce
"Me kake fad'a ne kam mene ne? kayi min yan da zan gane wani irin hukunci a ka yanke maka haka me ka aikata haka akayi maka irin wannan mummunar hukuncin haka!."
"Fyad'e na aikata, hukuncin fyad'e a ka yi min ke ma kiyi min naki kuma dan Allah idan kika yi min ki yafe min."
wani irin waro ido Maman Zeey tayi tare da d'an ja da baya.
a hankali Kamal ya matso yashiga yi mata bayani cikin sanaki, yadda abun ya faru da zuwa gidan su Naseeba yanzu da suke akan niman aurenta da yake har zuwa yau dayakai kansa kotu a ka yanke masa hukunci.
hawaye tashiga sharewa kana ta matso taruko hannun Mukhtar ta ce
"Nayefe maka Allah ya yafe maka, duk da ina da tabbaci da yakinin yafiyar ubangiji a gare ka, tun da har kabi ta hanyar da zai yafe makan, Allah ya dad'a tsare ku da sharrin shaid'an me ingiza mutum izuwa ga halaka."
wani irin dad'i ne ya mamaye zuciyoyin su ganin yan da ta fahimce su cikin sauki...
kwanan Mukhtar biyu a asibitin a ka sallame shi,babu wan da yasan dalilin da yasa a ka kwantar da shi a asibiti ko 'yar uwarsa na jini wato Zeey har yau bata san dalilin kwanciyar nasa ba, ko ta tambayi dalilin sai dai ace mata hatsari yayi duk da kuwa shatin bulala da take gani a jikin sa sai dai bata kawo komai a ranta ba, a ranar kwanan sa na biyun a ka sallame sa.
A cikin satin manya suka shiga maganar auren shi da Naseeba, hamaifin Naseeba ya aminci da batun auren sakamakon kiran Naseeba da ya yi ya tambayeta tana sonsa bata da zab'in daya wuce Eh dan hakan ne kad'ai take ganin mafita cikin rayuwar ta da take wa kallon ragegge.
aka kuma sa aure wata biyu masu zuwa, har kuma yau babu wan da yasan da batun fyad'en da Mukhtar ya yi wa Naseeba in ban da Kamal da SEEDRAH sai kuma Maman Zeey kasan cewar mahaifin Mukhtar d'in baya raye 'yan uwan mahaifin su ne suka wuce gaba kan maganar auren, sai dai har yau Naseeba taki ta bawa Mukhtar da ma ko da sau d'aya ne su had'u. ko da sunzo kofar gidan su sai dai SEEDRAH ta fito, dan yanzu tafara rage jin haushin su tun da Kamal ya bata labarin hukuncin da Mukhtar d'in yakai kansa a ka yanke masa....
yanzu shirye-shiryen biki SEEDRAH ta ke dan ita ke gudanar da tsare-tsaren bikin dan idan ta Naseeba ne ma kada a yi komai, ita dai a d'aura aure a kaita shine take ganin rufin asirin rayuwar ta.
bayan watanni biyu aka d'aura auren Naseeba da angonta Mukhtar, ta tare a cikin gidan su Mukhtar d'in a d'aya shashin dake bayan na Maman Zeey.
a ranar da yamma kowa ya watse yarage Naseeba da SEDDRAH sai kawarsu Nabila kasancewar gidanta babu nisa dana Naseeba'n. har wajen sallar isha suna tare da Naseeba a shashinta.
Nabila tayi ta zolayar Nasiba cikin zolayar da tun d'azu take ta mata ta ce
"Yau yarinya zaki gane shayi ruwa ne idan kika shiga hannun wannan bawan Allah'n, ba haka kukayi ta min dariya ba lokacin nawa,to ni yanzu anshani na warke har na saba yanzu babu wani ragowar zafi sai dad'i."
bugu SEEDRAH ta kai mata tana fad'in
"Allah ya shirye ki Nabila yanzu dai kin zama 'yar iska."
dariya ta yi ta ce
"Babu wani iskance ai gaskiya ce saura kema ki shigo hannu, ke kam nasan sai makota sun kawo miki d'auki sabo da tsabar tsoro irin naki."
"Allah ya sawake to ni anfad'a miki ma zanyi aure yanzu ne tun yayu na basuyi ba, kin san ai gidan mu bi da bi ne,sai Halimatu da Suhailat sun tashi kafin nan na kara girma babu katon gardin dazaici zalina."
SEEDRAH ta fad'a tana dariya.
Naseeba kuwa shiru tayi bata ce ko kala ba yayin da zuciyarta ke kuna, Nabila bata san komai game da fyad'en da akayi mata ba tana yi mata kallon wata cikakkiyar budurwace, k'walla ne suka ciko idon ta.
Nabila kuwa cigaba da fad'in
"Ko shekaru talatin zaki kai kafin kiyi aure ni na tabba a irin tsoron ki sai kin tara makota SEEDARH, yarin ya kiyi shiri yau fa zaki yabawa aya zakin ta, gobe da safe ina zuwa nakuma sake yi miki wani gashin dan nasan wanda zaiyi miki a darennan bazai wadatar ba sai an taimaka miki da safe."
ta karasa maganar tana duban Naseeba da tuni idanunta suka ciko da kwalla.
lura da yanayin da ta shiga yasa SEEDRAH girgiza mata kai ta dubi Nabila ta ce
"To tashi ki tafi gidan ki an fad'a miki kowa raguwa ce irin ki zuba ido kiyi kallo zakisha mamaki aure kuma ba yanzu ba."
"Sai yaushe? ni da nake saran a karshen watannan a ramawa kura aniyarta, yadda mukasha wuya a auren su haka kuma zasu rama mana."
cewar Kamal da yanzu shigowar su ya sinci cancen a sama yakuma cab'e. Mukhtar nabiye da shi suka shigo ciki.
SEEDRAH ta hararesa tare da murgud'a masa baki, dama taga take-taken sa tun ba yauba taki basa fuska ne.
shiko 'yar karamar dariya yayi yadubi Nabila yana fad'in
"Ko ya kikace kawar mu?."
dariya Nabila tayi ta ce "Wlh kuwa ina goyon baya d'ari bisa d'ari."
mikewa SEEDRAH tayi ta d'au gyalen ta da jakarta tana fad'in
"Sai kuyi kuma ai kanku a ke ji."
ta nufi kofa.
Kamal yabi bayan ta. Nabila ma ta mike tana dariya tayi musu sai da safe tayi waje.
a can waje ta iskesu suna ta dirama dariya tayi dan tasan halin SEEDRAH sarai bata kula samari tun suna makaranta ma irin samarin da ake nacikin aji ita bata sauraran su bare ma har ta tsaya zance da su, shi yasa da yawan samari suke ce mata wai tana da girman kai ko dun taga tana da kyau ne, kuma sam abun ba haka yake ba sai in kazauna da ita zaka fahimci halin ta sassanya kamar ruwan randa, ita dai haka rayuwarta yake da kin kula samari, a cewar ta wai bata kai na tsayuwa da saurayi ba sai idan yayun ta sun matsa sun bata guri..
Kabir mijin Nabila da yanzu ya iso gurin d'aukar matar sa shima yayi ta taya Kamal d'in kamfen, ita dai SEEDRAH bata saurare su ba har ya d'au matar sa sukayi gaba.
da kyar ta amince Kamal ya d'auke ta a mashin d'in sa, dan cewa tayi abin hawa zataje ta nima ya kaita gida bazata hau mashin d'in sa ba. a hanya yayi ta fallasa mata irin son da yake mata da ke kunshe a zuciyar sa tun ranar da kaddara ta had'asu.
ita dai tana jin sa suna isa kuwa ta sauka ta shige gida ta barsa nan tsaye a kofar gida...
A b'angaren amarya da ango kuwa kamar yanda Mukhtar yasha alwashin samarwa zuciyar Naseeba salama da cire kiyayyarsa da kuma mantar da ita abun da ya faru cikin kwanakin da basufi bakwai ba.
ya samar wa zuciyarta nutsuwa had'e da tarin kwanciyar hankali da santsar kauna da soyayya da kulawar da yake nuna mata, ba shi kad'ai ba har da mahaifiyar sa da kuma kanwar sa.
a yanzu amarya Naseeba zamu iya cewa bata da wata matsala a rayuwar ta dan mijin ta yazame mata bango majingina, ga uwa uba kular mahaifiyar sa da kanwarsa gare ta.
cikin wata d'aya ta mance da wani mummunar abu yatab'a faruwa da ita, har take jin farin had'uwar su da shi shine yazamo first night d'in su kamar yanda Mukhtar d'in ya datsa mata jin hakan a zuciyarta.
sai dai muyi fatan d'aurewar farinciki ga wannan family....
A d'an wannan saikon kuwa Kamal ya sami nasarar sace zuciyar SEEDRAH amma fa sai da yasha wuya dan sai da yayi dagaske wajen iya sato zuciyar nata,
wani zazzafar sosaiya ce ke gudana sakanin su me cike da fahimtar juna.
SEEDRAH ce zaune tsakiyar d'akin Mama tana duba wasu litattafai, dan wata mai kamawa zata fara zuwa, Kasu open university, poly d.s, university Kaduna.
Mama ce ta shigo rike da flaks da laida a hannunta ta dire shi tsakiyar d'akin.
SEDDRAH ta ture littatrafan gefe tare da gyara zama ta mika hannu ta d'au cup tana fad'in
"Allah dama yunwa nake ji."
"Me ya hanaki tashi kinimi abincin."
cewar Mama tana zama gefen ta.
ta ce "Mama karatu nake kin san wani wata me kamawa Baba ya ce zan fara zuwa makaranta."
Mama ta ce "Uhm Allah ya nufa." kallon ta SEEDRAH tayi jin yanda ta amsa mata, sai kuma
ta d'au flaks d'in ta tsiyaye ruwan zafi tafe da bud'e laidar, ido tad'an tsura cikin laidar ganin biredi da lipton da siga ne kad'ai a ciki.
ta ce "Mama ina sauran kayan tea d'in?."
baki Mama ta tab'e kana ta ce
"Sha abunda ya sauwaka ki godewa Allah hakan ma an samu, kijira samuwar na rana ma tukun dan bamuda tabbacin samun sa."
kai SEDDRAH ta jinjina kana tashiga had'a lipton da siga.
Alhaji Musa wato Baba ne tsaye cikin parlour'n sa, kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin muguwar damuwa da tashin hankali.
a yaune karshen yarjejeniyar su da banki kan bashin banki daya ci, tun shekarun baya da suka wuce, lokacin da aka kwashe masa kud'i na farko a accaunt d'in sa, hannun jarin sa yayi kasa sai da yaje yaci bashin banki kafin ya d'an farfad'o.
gashi yanzu ankuma yi masa mai gaba d'aya, duk kaddarorin da yake da su ya d'auka ya siyar yazuba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19