kuma wlh bata jin dad'i sosai."
ta karashe maganar kamar zata zubda kwalla.
kasan cewar ya santa dan kusan a nan shagon nasa suke siyan maganin duk san da ya kare, ya ce to taje anjima takawo masa cukon. ta karb'a tare da yi masa godiya ta fita ta juya gida da sauri.
ta can bayan motocin da har yanzu suke cike kan titin ta wuce.
Tana isa gida ta sami Mama har lokacin a kwance, ruwa ta d'ibo ta b'are maganin ta zauna gefen ta tad'an tallafo kanta tasaka mata maganin a baki tare da ruwan ta sha.
cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke ta.
numfashi SEEDRAH ta sauke tana kallon fuskar Mama da take bacci,
kwallan daya ciko idanunta ne suka zubo yayin da ta fara zancen zuci
"Allah sarki uwata a sanadin haihuwa ta kika samo wannan ciwon gashi har yau kina fama da shi in sha Allah kamar yanda kika samo sa a ta sanadiyya ta zaki warke a sanadiyya ta da yardar Allah."
ta mike tashiga kimsa musu d'akin da yau Mama bata sami da mar gyara shi ba sabo da ciwon ta...
Mama ta jima tana baccin sai wajen bayan la'asar kafin ta farka, zuwa lokacin kam alhmdllh taji d'an karfin jikinta.
ko da Baba ya dawo SEEDRAH taje ta amso sauran cikiton kud'in mai magani har da dubu d'ayan Mama da ta d'auka kasan pillon ta tamaida mata kana ta wuce ta kaima mai magani cikon kud'in sa...
Washegari ranar asabar tun da safe su Suhailt ke ta shiri, ansha wanka an d'au kwalliya, Halimatu na tsaye gaban mirro sai faman feshe jiki da turare take.
SEEDRAH kam na kwance tana ta sharar baccin ta.
Suhailat ce ta matso bakin gadon tashiga bubbugata, mika tayi had'e da salati tayi juyi nata kokarin kuma komawa baccin ta.
Suhailat ta kuma bubbugata da karfi tana fad'in
"Wai nikam ke bakya gajiya da bacci ne wai duk surutun da za a yi ta yi a kanki idan kina bacci bakya ji ne?
yanzu fa karfe 11 har da rabi amma wai mutum na bacci wai bai gaji ba."
cikin magagin bacci yayin da idanun ta suke rufe ta ce
"To ni me zan miki Aunty Suhailat Allah ni baccin bai ishe ni ba."
ganin tana kuma kokarin komawa baccin duk uban bugun da tayi ta mata ta ce
"To da ma ke bacci na isan ki ne dalla tashi ko bazakije gidan Abba'n bane?."
tuni SEEDRAH kam ta koma baccin ta bata ma san abun da take fad'a ba.
Halimatu dake gyara gyalen data yafa ta ce
"Da ma kin rabu da ita dan ba jin ki take ba, in ba d'aukarta zakiyi ki tsunbulata cikin ruwan Fridge me sanyi ba, a duniyar nan bantab'a ganin mutum me mugun nauyin bacci irin na yarinyar nan ba."
fita sukayi suka rabu da ita, ita ko batama san sunayi ba.
SEEDRAH tana da nauyin bacci sosai sai aci a sud'e tana gurin tana aikin bacci batama san me ake ba, sanin nauyin baccin ta yasa duk ranar makaranta bata yarda ta koma bacci da asuba.
ai kuwa bata farka ba sai wajajen karfe 12 da rabi.
bayi ta fad'a tayi burosh tare da wanka ta d'auro al'wala dan lokacin anfara kiraye-kirayen sallar azaha.
sai da ta gabatar da salla kafin ta shirya cikin riga da siket na atamfa, ita ba wata ma'abociyar fente fuska da kulliya ba ce, pauda da man lips kad'ai ta shafa sai turare da ta bi jikin ta da shi, amma tayi kyau sosai abinka da me kyau.
d'akin Mama ta tafi ta same ta zaune a kan sallaya, zama tayi gefen ta ta ce
"Mama ya jiki?."
"Naji sauki SEEDRAH." ta ce "Allah ya kara miki lafiya."
Mama ta amsa da amin, kana ta mike taje ta had'a ruwan zafi da lipton ta yanko biredi ta dawo kusa da Mama ta zauna tana sha suna d'an tab'a hira..
da karfe biyu SEEDRAH tayi shirin islamiyya sai wajen karfe biyar da rabi ta dawo gidan.
Sai yamma su Suhailat suka dawo SEEDRAH na zaune a d'akin su tana duba littattafan ta suka shigo,
Halimatu ta zube bakin gado Suhailat kuma ta wuce bayi.
SEEDRAH ta dubi Halimatu ta ce
"Aunty Halimatu ina kuka fito ne?."
da mamaki ta ce "Au bakima san in da mukaje ba?."
Suhailat da ta fito daga bayi ta ce
"Ina kuwa zata sani mutum kamar bugagge idan ya fara bacci,
ke da nayi ta tashin ki kitashi munje gidan Abba mu karb'o tsaraba kika ki tashi."
littafin hannun ta ta rufe ta ce
"Karb'o tsaraba kuma wa yayi tafiya ya dawo?."
murmushi Suhailat tayi tare da fad'in
"Ya S.MAN ne ya dawo gashi ma bamu had'u ba duk zaman da mukayi a gidan yana can abokan sa sun had'a masa shagali na musamnan."
Halimatu ta ce "Wlh ni na masu naga yanda ya koma naji ance yakara kyau ya canza gaba d'aya."
ido SEEDRAH ta bisu da shi sai yanzu ta fahimci wanda suke nufin wato Usman babban d'an Abba mazaunin kasar Spain, tana dai jin sunan sa amma sam bata san shi ba dan tun tana 'yar karama yabar kasar nan, kuma ba wani zuwa yake ba, da girman ta dai zata iya tunawa sau d'aya ta sami labarin ya zo lokacin ma bata Kaduna taje Zariya wajen kakarta mahaifiyar Mama.
maganar Suhailat ce ya katse mata tunani jin tana fad'i
"Ai wlh sai ma kin ganshi ranar dana je gidan Abba na samu suna video call da Ummi ke kin gansa kuwa hmm abun ba'a cewa komai, girman sa ya karu daya ciwo wa Nigeria kwallo."
SEEDRAH kam da ido ta bisu jin yadda suka dage suna ta zuzuta shi, baki ta tab'e dan ita bata ma sanshi ba bare ya dame ta.
wayar ta dake tsuwa ta d'auka ganin Kamal ne ke kiran nata ta saki wani lallausan murmushi kana ta mike tayi waje, ta barsu nan suna cigaba da hiran S.MAN...
Washegari da safe su Halimatu suka kuma shirin zuwa gidan Abba, yau kam SEEDRAH bata koma bacci ba dan yau tun kan gari yayi haske ta kwashi wankin ta da na Mama tayi.
ko da suka gama shirin duban ta Suhailat tayi ta ce
"Ki tashi muje ko baccin naki zaki soma?."
mikewa tayi taje ta d'au gyalenta kasancewar a shirye take dan tana gama wankin ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar les, ta yafa gyalen a kanta suka fito.
sai da ta shiga d'akin Mama ta fad'a mata in da zasu kafin ta fito.
suna fita suka tari a napep suka nufi gidan Abba.
suna isa Suhailat ta biya mai a dai-dai ta suka shige gidan, da sallama suka shiga parlour'n Ummi da Yusrah dake zau cikin parlour'n suka amsa musu.
suka karaso ciki tare da gaishe da Ummi, Ummi ta ce
"A'a tun baku zauna ba ku zauna mana."
suka zauna suna mai ci gaba da gaishe ta.
ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar su ya iyayen nasu, sukace suna gaishe ta.
Yusrah ta gaida su Suhailat dan sune gaba da ita, mike wa tayi ta zo
kusa da SEEDRAH ta zauna tare da buga cinyarta ta ce
"Na gai da yayu na ke bazaki gaishe ni bane?."
hararar ta SEEDRAH tayi ta ce "Kin raina ni fa a kan ni d'in ban girme ki bane."
baki Yusrah ta rike ta ce "Ko kunya bakiji ba, ke d'in ce kika girme ni? amma yarinyar nan kin rainani."
murmushi Ummi ta bisu da shi a ko da yaushe idan suka had'u burin kowaccen su dai ta ce itace gaba da 'yar'uwar ta,
SEEDRAH da Yusrah sa'anni ne sakanin su baifi tazaran watanni ba.
Suhailat da tun shigowar su parlour'n ta kafe katon hoton S.Man dake like jikin bangon parlour'n, yana sanye da kayan kwallo yad'an sunkuyo yana dafe da kwallo yayin da ya d'aura kafar sa d'aya kan kwallon.
ainihin kyansa da suffarsa na zaratan maza ya bayyano sosai cikin hoton S
Man Handsome ne na karshe.
sosai ta shagalta da kallon hoton da take jin sa har cikin jinin jikin ta,
Suhailat
tana mugun son S.Man hakan kuwa yana daga cikin abin da ya hanata fidda gwani tayi aure.
a b'angaren Halimatu ma kuwa haka abun yake sai dai ita takan iya b'oye son da take masan amma acan kasan ranta soyayarsa ce zaune cikin sa, takan b'oye ne sabo da 'yar'uwan ta da take bayyana son da ita take masa a ko ina wan da shi baima san sunayi ba.
ganin kallon hoton nasa bazai wadatar da ita ba sai ta d'an muskuta tare da duban Yusrah da suke hira da SEEDRAH ta ce
"Yusrah Ya S.Man fa Allah dai yasa yana gida yau muyi masa sannu da hanya."
Ummi ta ce
"Ai kuwa yau idan da baku same shi ba zan ce ku huta abinku da jigilen hanya, yana nan amma ina ga bacci yake bai tashi ba dan jiya sai wajen 1 na dare ya shigo gidan nan."
murmushi Suhailat tayi tare da fad'in
"Yana huta gajiya kenan ya kamata kam ya huta."
ji tayi kamar ta tashi taje d'akinsa ta iske shi can.
magana ta somayi a kasan ranta
"Tausa ya kamace ka tun daren jiya zuwa yau ka huta da kyau."
murmushi ta sake a fili.
SEEDRAH kuwa hirar su suke kan lokacin da sukayi candy d'in su, suka shiga kallon hotunan Graduating d'in su a wayar Yusrah
dan Secondary school d'aya sukayi.
Yusrah ce ta kece da dari ganin wani hoton su da SEEDRAH ta zazzaro manyan idanunta ta ce
"Dan Allah dubi ido kina kallon me hoto kamar kin ga dodo."
SEEDRAH ta ce "Amma dai me hoton nan ya cuceni dubi yan da yamin da ido,ko ma dai wayar ki ce badaga gunsa bane."
cikin muryar dariya Yusrah ta ce
"Wlh kada kima wayata sharri ke kika zazzare idanunki kamar baki tab'a d'aukar hoto ba, ai akwai asalin hoton da aka wanke yana nan a d'aki na zo ki gani zaki san ba wayata ke sharri ba."
suka mike suna dariya suka shige d'akin Yusrah.
nan ta d'ebo musu hotunan suna kallo sunayi wa yuna tsiya.
daga can parlour SSEDRAH ta jiyo ring d'in wayar ta da ta bari can parlour, jin sauti na musamman tasan wake kiran nata wato Kamal dan shi kad'ai ta sakawa sautin.
mikewa tayi tana fad'in
"Ina zuwa." tafito parlour'n, kafin ta isa in da wayar take kiran ya yanke.
ta d'au wayar tana kokarin juyawa ta koma d'akin Yusrah tajiyo Ummi da ke waya tana fad'in
"Da dai ka fito kayi break d'in a parlour gashi anzo gaisheka a na jiran ka tun d'azu."
daga cikin wayar S.Man ya ce "Ummi ki bada a kawo min breakfast d'in d'aki kawai idan nagama zan fito ko wanka banyi ba har yanzu gajiyar bata sake ni ba."
Ummi ta ce "To bari a kawo maka."
ta sauke wayar tare da
dakatar da SEEDRAH data d'sura hannu kan handle zata bud'e kofar Yusrah ta ce
"Zo SEEDRAH ki kaiwa yayan ku abin karyawan shi d'aki."
da sauri Suhailat ta ce "Bari na kai masa."
murmushi Ummi tayi tace "A'a barshi ita ta kaimasa ga kannen ku suna guri su sai suyi dad'in girman kenan, zo ki kai masa ga abincin nashi can kan dinning."
yuwayo tayi a sannu ta taka zuwa dinning ta d'au tray d'in da aka shirya masa breakfast d'in ciki, d'an dim tayi tsaye a gurin dan bata san ta ina ne d'akin sa ba, duk zuwan ta da take gidan daga d'akin Yusrah sai na Ummi sai kuma na Abba kawai ta sani.
ganin ta tsaye a gurin yasa Ummi fad'in
"Kai masa mana yan zu wannan sarkin mitar zai fara korafin ba'a kai masa da wuri ba, bi ta kofar kitchen ki kai masa."
a hankali ta nufi kofar kitchen d'in bawai kodun ta san daga nan sai ina zatayi ba.
sai da ta isa kitchen d'in taga kofofi guda biyu d'aya dai tasan store ne d'ayan ne dai bata san ko menaye bane dan SEEDRAH ba mutum bace me shiga lamarin da bai shafeta ba, gashi dai gidan kanin Baban ta ne uwad'aya uba d'aya amma ko da tazo gidan bata fiye shishshige ba abin da yakawo ta kad'ai take yi.
d'aya kofan ta bud'e sai taga ashe hanya ce da zai fiddaka waje ta baya, can ta hangi wani d'an ma dai-dai cin side da tuntuni take masa kallon side d'in bak'i ne.
kofar side d'in ta nufa a hankali tayi knocking d'in sa sau uku kana ta d'an tsaya.
jin shiru ba'ayi magana ba sai ta tura kofar a hankali ta sa kai ciki.
parlour ne d'an ma dai-dai ci me d'auke da kujeru set d'aya sai d'an ma dai-dai cin TV a like a jikin garu-bango, sai fridge a gefe. parlour'n sai tashi da daddad'an kamshi mai garwaye da sanyin ac yake.
sallama ta shigayi amma shiru babu amsa,
hukunci ta yanke wa kanta ta dire masa abincin ana idan yafito ya d'auka, amma sai tayi tunanin ko dai ba nan ne d'akin nasa ba.
har zata juya ta fita sai kuma ta d'an tsaya tare da zubawa kofar bedroom d'aya dake cikin parlour'n a sannu ta taka zuwa bakin kofar, d'an numfashi taja tare da fesarwa kana ta yamutsa fuska jin wani wari-wari kamar warin sigari.
nan ma knocking tayi daga cikin bedroom d'in akace
"Yes." tsayuwa tayi nawasu 'yan sakanni kana ta tura kofar a hankali da sallama tasa kanta cikin d'akin.
sassanyan kamshi mai had'e da kaurin hayakin taba su suka yiwa hancinta maraba.
yana zaune a bakin gado sike da sigari a hannunsa yana d'an zuka a hankali cikin nutsuwa yayin da d'aya hannunsa ke rike da waya yana d'an daddannawa,
gajeren wando ne kad'ai a jikin sa babu ko riga a jikin sa duk tulin sanyi irin na hunturo amma fanka had'e da ac ne ke ai ki cikin d'akin.
har ta karaso ciki bai d'ago ba idanunsa yana kan waya, gefe kan table ta dire tray d'in ba tare da ta kalli in da yake ba, dan tun shigowar ta da idanunta ya sauka kan shi ganin shi zaune kamar tsirara yasata saurin janye idanunta.
tana kokarin mikewa yasoma magana
"Yusrah kice wa Ummi tabaki ruwan zafi na wanka ki kawo min hitan bathroom d'ina ya ki aiki yau."
jin shiru bata amsa ba yasa shi d'ago wa yana fad'in
"Bakiji abun da na fad'a bane."
yayi maganar cikin d'an tsawa, karaf suka had'a ido dai-dai lokacin da ta mike daga tsunkuyen da take.
da mamaki yake kallon ta kamar yanda itama mamakin ne a bangaren ta, tana ta son tuno in da ta tab'a ganin fuskarsa.
a 'yan dakikan ta tuno in da ta tab'a ganin fuskar shekaran jiya da taje siyan magani har wasu ke ce mata ta tsaya mai kasa ya wuce kafin ta wuce.
a b'angaren sa shima a take ya tuno da in da ya tab'a ganin ta duk da hakan ba d'abi'ar sa bane, bai damu da dole sai ya tuno in da ya tab'a sanin ka a karo na biyu a had'uwar ku cikin rayuwar sa ba.
mamakin da yake wace ce ita sannan kuma me yakawo ta cikin d'akin sa.
juyawa tayi a hankali tanufi kofa bayan ta yabi da kallo har ta fice.
gajeren tsaki yaja kana yacigaba da shan sigarin sa.
lambar Ummi ya dannawa kira tana d'agawa ya ce "Ummi abincin fa yunwa fa nake ji."
Ummi da ta zubawa SEEDRAH ido da yanzu shigowar ta parlour'n ta ce
"Abinci kuma? bayan wan da SEEDRAH ta kawo maka."
sai a lokacin idanunsa suka sauka kan table d'in data d'aura breakfast d'in kai, fuska ya had'e ya ce "Wace ce ita? takawo shine bazatayi magana ba."
murmushi Ummi tayi ta ce
"SEEDRAH ce fa baka gane ta bako 'yar Baban ku Musa."
kashe wayan yayi batare da yakuma cewa komai ba.
a parlour'n ta zauna ganin Yusrah ta fito suka cigaba da hirar su.
sai da yashare kusan awa guda da rabi kafin ya shigo parlour'n, cikin shigar fararen kaya da yadin ya amshi jikin sa matuka sai baza kamshe yake yayin da yake gyara d'aura agogon hannunsa.
tun kan ya karaso cikin parlour'n Suhailat ta kafe shi da ido gaba d'aya ta shagalta da kallon sa, yayi masifar yi mata kyau ba kad'an ba, ashe duk yanda take tsara kyan sa cikin zuciyar ta kyan nashi da tsaruwar sa yad'are tunanin ta.
Halimatu ma sosai ta tafi wajen kallon sa.
gai da Ummi yayi ta amsa tare da fad'in
"Tun d'azu suke jiranka ko suma baka gane su bane Halimatu da Suhailat, jiya ma anan suka wuni baka dawo ba shine yau suka kuma dawowa."
da sauri Suhailat cikin yin fari da ido ta ce
"Ina kwana Ya S.Man kazo lafiya ya hanya? muna tayaka murnar nasaran da a ka samu."
batare da ya amsa gaisuwar da Suhailat d'in take masaba ya ce
"Ok 'ya'yan Alhj Musa ko?."
yayi maganar yana nuna Suhailat da Halimatu dan su ya gane su kasan cewar su suna zuwa duk san da yazo Nigeria,kuma kafin yabar kasar ma su da wayon su.
wani irin d'agowa SEEDRAH tayi jin yan da ya ambaci sunan mahaifinsu babu ko girmamawa ciki a matsayin sa na wan mahaifinsa kai tsaye ya kirasa da Alhaji Musa.
wayar sa ce tayi kara ya d'aga tare da nufar kofa batare da ya amsa gaisuwar da Halimatu itama take mika masa ba.
Ummi ta d'aga murya tana fad'in
"Ai da ka tsaya kun gaisa tun fa d'azu kai suke jira."
Picking call d'in yayi ya kai wayar kunnen sa tare da fad'in
"Ummi idan na dawo ma gaisa yanzu wasu ke jirana na."
daga nan yayi waje a binsa.
tsaki SEEDRAH tayi a karan ranta wan da har sai da yafito duk suka juya gare ta.
taji matukar haushin yanda yakira sunan Baba babu ko kara, gashi a na gaishe sa yana wani batsarwa Allah ma yasa ita batama ko kalli in da yake ba bare ta gaida shi har yaki amsawar, da bakin cikin yafi haka, kwafa tayi tare da cigaba da daddanna wayarta da take.
a b'angaren su Suhailat kuwa ko kad'an hakan bai dame su ba musamman ma ita Suhailat d'in da take ji kamar ta tashi tabi bayan sa.
mikewa SEEDRAH tayi ta dube su ta ce
"Mu tafi ko nayi gaba ne? kunsan ina da islamiyya karfe 2 ga azahar ta kusa."
Ummi ta kalleta tana karanto rashin jin dad'in yadda yaron nata yayi musu a gareta, sai tayi murmushi ta ce
"To ai da sauran lokaci yanzu."
murmushin yake SEEDRAH tayi ta ce
"Banyi guga bane zanje na goge Uniform d'ina kafin."
Ummi ta basu dubu biyu ta ce suyi kud'in napep sukayi mata sallama suka tafi.
a hanya SEEDRAH da har lokacin a cike ta ke taja tsaki tare da fad'in
"Amma wannan mutumin d'an rainin wayo ne."
Halimatu ta dube ta tace "Wani mutum kuma?."
ta ce "Wancan S.MAN d'in mana wai dan tsabar rainin wayo sunan Baba fa ya kira wai wani Alhaji Musa, ai ko Baba ba yayan Abba bane zaici albarkacin girma tun da ya haifesa, idan ma bazai iya kiran sa da Baba ba ai yana da yara sai ya kirashi da Baban wane."
tsaki takuma ja tare dayin kwafa ita har cikin ranta taji haushin hakan.
shekeke Suhailat ke kallon ta ta ce
"To meye nawani jin haushi shifa babban yaro ne ko Abba ma wani sa'in Alhaji yake ce masa, to meye dun yacewa Baba Alhaji Musa akan ba sunan sa bane."
Halimatu ta ce "Gane min hanya meye najin haushin ki?, ai barashin kunya bane dan ya ce haka."
da mamaki SEEDRAH ke kallon su kana ta ce
"Rashin kunya ne mana tun da bazai iya cewa Abba Alhaji Sulai ba, sai dai ya ce Alhajin kawai ashe yasan ma wan da yake yi mawa sabo da shi ya haife sa ko Hmm."
kai ta girgiza.
hararar ta Suhaital tayi ta ce
"Kina da damuwa wlh, kiyi abin da yake gaban ki kawai mu dai bamu ga wani rashin kunyar sa ba ai ba zaginsa yayi ba."
baki ta tab'e had'e da murgud'a shi sannan ta ce
"Na rantse duk san da yakuma kiran Baba da sunan sa, ni sai na tsayar masa, tun da shi dai ba sa'ar sa ba ne tun da Aunty Hajara ma ta girme shi, ya haife shi ya juya."
ta karashe maganar had'e da kuma murgud'a baki.
Halimatu ta ce
"Kina da tsinannen rashin kunya shi d'in bana gaba da ke d'in bane."
shiru tayi bata kuma ce da su komai ba sai tsakin da take ta ja jefi-jefi har suka isa gida...........?
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090_ ko 08034690723
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️8
Da misalin karfe 5 na yamma S.Man ne ya shigo gida ya tadda Abba da Ummi zaune a parlour, da murmushi Ummi ke duban sa har ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour.
Ummi ta ce "Sai yan zu Usman?."
cikin yanayin gajiyar daya kwaso ya amsa mata tare da gaida Abba.
Abba ya amsa yana fad'in
"Tun da ka dawo bamu sami zama mun gaisa sosai ba kullum kana hanyar fita."
zaman sa ya gyara tare da soma latsa wayar sa kana ya ce
"Ni ma nagaji da fitar nan mutane sun hanani sakat."
murmushi Abba yafad'ad'a ya ce
"To ai cigaban kenan."
baki ya tab'e bai kuma cewa komai ba yayin da hankalin sa gaba d'aya ke kan abun da yake a waya. Abba da Ummi kuwa suna ta zuba masa zance, lokaci zuwa lokaci yake amsa musu.
zuwa can yasoma magana batare da ya d'ago ba.
"Abba ina bukatar kud'ina kace wa mutumin nan yabani kud'ina."
Abba ya dube shi tare da fad'in
"Wani mutumin kuma Usman?."
ya ce
"Kudi na dana bawa Alhj Musa aro nake so ya maido min dasu ina bukatar su."
Abba ya ce "To-to ai harna sha'afa, anya Yaya Musa ya aje wad'annan kud'ad'en ma kuwa, dan a gaskiya samun sa ya yi kasa sosai ai kasan kud'in ma banki yabiya da su, sai dai bari dai na tuntub'e sa naji ko da d'an wani abu ne yaba da a gurin sa kafin a samu sauran."
da sauri S.Man ya d'ago tare da da fad'in
"Duka kud'ina zai bani bada kad'an-kad'an
ba."
Abba ya ce "To idan kuma baya da shi fa sata zaije ya yi?, bari dai na tuntub'e sa naji in dai babu kam ai dai dole zakayi hakuri."
mikewa ya yi tare da fad'in
"Bazan karb'i kad'an ba duka kud'ina zai bani jibi nake bukatar su."
yana gama fad'a yayi waje.
bayan sa sukabi da kallo, cikin d'aga murya Abba ya ce "Sha-shan cin banza kai,
idan baya da su na ce sata zaije ya yi, ai dole zakayi hakuri sai ya samu yabaka."
Ummi ko kai ta jinjina tasan halin d'an nata sarai tun da taji ya tsaya matsaya d'aya to kuwa bazai tab'a canzawa ba.
S.Man na fita b'angaren sa ya nufa,yana shiga bedroom yajefa wayarsa a kan gado, kana a sannu yashiga rage kayan jikin sa, yarage daga shi sai boxes.
murjajjen surarjikin sa irin na kakkarfan zaratan maza ya bayyana,
ainahin kyau na tsarin kyakkyawan halittar sa yabayyana a fili.
doguwar mika ya yi tare da lankwasa jikin sa gefe da gefe, irin dai yan da 'yan kwallo suke yi, kana a sannu yanufi kofar bayi yashiga ya sakarwa kansa ruwa, wanka sosai yayi kana yafito.
ya shirya cikin kananun kaya wanda suka amshi jikin sa sosai, yana gama feshe jikin sa da turarukan sa masu dad'in kamshi, yafito parlour d'auke da na'uwar sa,
sosai ya mai da hankalin sa cikin system da yake daddannawa.
wayar sa ya d'aga tare da lalub'o wata lamba.
magana yasoma yi ga dukkan alamu maganar sirri ce dan ni dai banji abin da yake fad'a ba.
sai gani nayi ya mike da laptop d'in yayi waje.
Bayan kwana biyu kamar yan da S.Man ya ce yakuma samin Abba da batun kud'in sa,ya ce yana bukatar su a yau d'in nan.
bayan fitar S.Man daga d'akin Abba Abba yakira Baba bayan sun gaisa Abba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 19