mai 'ya'ya uku sai mai, hud'u kuma suna can suna kan karatun agidan mazajensu wasu kuma suna aiki,
duk kusanar wa maneman ku sufito."
Kai Halimatu ta takawar gefe tana mara baki ta ce
"Ni kam dai bani da wani tsayayye sai dai ko in Suhailat dan duk cikin samarukana banga mijin aure ba,
har yanzu ban samo mai gida da mota mai d'aukar albashi mai tsoka ba dan bazanyi auren da miji zai ajeni a gidan gado irin na Aunty Hajara ba, yaushe kasamu kaci me kyan ma bare ka bawa wani naka."
Suhailat ta ce
"Ai ni kowa yasan ma Ya S.MAN nake jira, idan har ban same sa ba to nima sai na jira zuwan mai kud'i tukun, Umma da kike cewa wai da katifa za a kaimu sai kace marasa galihu, wlh ba za'ayi wannan abin kunyar da ni ba sai dai Baba yasan yanda zaiyi ya nimo kud'in min kayan d'aki,
dan wlh bazan shiga bakin kawaye ayi ta yi da ni ba."
Umma ta ce "Sai dai kuwa kishiga bakin kawayen, a gidan uwar uban wa zai samo kud'in kina ganin abincin da za a cima nashirin gagara bare kuma wani kayan d'aki, har yaushe zaku cigaba da zaman jiran me kud'i ku fidda mai rufin asiri kawai,
ke Suhailat kun dai-dai ta da S.MAN d'in ne, in dai kun dai-dai ta ai ko shike nan kin ga zairage yiwa Baban ku wani abin ma."
ta ce "Zamu dai-dai tan ai dan ni shi nake so."
Umma ta jinjina kai tana gyara zama tare da fatan 'yar nata tasami S.MAN d'in dan itama tana son abin da 'ya'yan ta suke so, tana fatan susami mazaje masu kud'i dan acewar ta babu wan da yaki gidan hutu musamman ma shi S.MAN yaro da kud'i wan da taurarun sa yake haskawa.
Mama na zaune a d'aki duk kad'aici ya ishe ta, tunanin 'yarta d'aya tilo ya baibaye ta.
zaune take a kan sallaya tana karatun kur'ani dan shi ke d'ebe mata kewa.
bayan ta kai aya shiru tayi tare da yin tagumi tazubawa Al'kur'anin ido a zahiri a bad'ini kuma tunanin rayuwar da d'iyarta take awani guri take.
idan ba kaddara ba me zai sa tatura yarta gidan wani aiki gidan da babu mata ciki,
sai dai tana da yakini kan tarbiyyar data baiwa d'iyarta dakuma addu'ar da take aikamata akullum da ko yaushe.
a hankali ta rufe kur'anin tare da shafa addur'ar data yi, ta mike taje tad'au kofin kunun tsamiya data dama d'azu, wan da acikin d'an kayan abincin da Maman ta da 'yan'uwan ta suka aiko mata dashi ne daga Zariya dan akwanakin nan su suke ciyar da kansu kowa girkin ta take,
dan lamarin kasuwancin Baba sai dad'a tab'arb'ancewa yake, kud'in da Abba yabashi yaja jari yanzu ba uwar kud'i ba riba.
abin da hajara da dangin Umma suka kalato shi suke dafawa suci da 'ya'yanta. ita ma Mama ita d'ayan ta take girka nata wan da nata dangin suke turo mata, wan da duk san da zata saka wani abu a bakin ta sai ta tuna da awani hali 'yarta take ciki shin ita ma taci, duk da tasan in da take ba abinci ba abunda yafi abinci ma yafi karfin sa.
amma irin kauna da tausayin uwa a kan d'anta shike sata tunano ta aduk san da zata kai wani abu cikin bakin ta...
A b'angaren Suhailat wanka da gaye sosai tayi dan yau takuduri aniyar tinkarar abin kaunarta wato S.MAN d'akin Mama ta shiga tace ta bata aron kud'i zataje unguwa idan ta dawo zata bata, Mama ta tattara 'yan canjin ta duk ta bata tafita ta sami mai abin hawa tayi gaba.
abakin get d'in gidan S.MAN aka dire ta tabiya mai adai-daita kud'in sa kana ta karaso bakin get d'in tashiga knocking.
maigadi yabud'e karamar kofa tare da leko kansa yana fad'in
"Wane ne?."
Suhailat ta ce
"Ni ce."
"To wace ce ke."
mai gadi yafad'a yana waigen gefe da gefe.
ta ce "Eh baka sanni ba kam ni ce Suhailat kanwar S.MAN ce ni yana ciki ne?."
"Wa ce kanwar tasa ni sam ban gane ba Yusrah kad'ai na sani kanwarsa."
yayi maganar yana kokarin rufe kofar
da sauri cikin hura hanci ta ce
"Sai kuma akace maka itace kad'ai kanwar sa bashi da 'yan uwa, to ni 'yar yayan Baban sa ne Alhj Musa."
maigadi ya ce
"Au to yanzu kikayi bayani to dai oga baya ciki sun fita da abokin sa."
ta ce "SEEDRAH fa tana ciki?."
ya ce "Eh ita tana ciki."
ta ce "To bari na shiga zan jirasa ya dawo."
Ya bud'e mata kofa tashiga tana tafe tana karewa gidan kallo a fili ta ke fad'in
"Duk ranar dana zamo matar gidan nan ko bacci bazan iya ba wannan gida wane aljarnar duniya, S.MAN had'ed'd'en namiji ne shiyasa gidan sa ma yazamo na daban Allah ka mallaka min shi."
da ire-iren wad'an nan maganganun ta isa kofar da zai sadata da ainahin side d'in gidan knocking tayi tare da murd'a handle ta tura kofar tashiga tana rera sallama.
"Wow." tafurta lokacin datayi tozali da tsararren katafaren parlour, wani irin taku take tana juyi cikin parlour'n daya gama tafiya da imanin ta, aduk mafarkin ta nason auren mai kud'i bata tab'a hasasho irin wannan duniyar ba.
sai take jin kanta lallai ita mai sa'a ce a fili ta furta
"Ya S.MAN duniya ce."
hoton sa dake like cikin parlour'n ta isa inda yake tana kare masa kallo wani murmushi ta sake tare da mika hanu tashafo kyakkyawar fuskarsa tana mai cigaba da sakin murmushi.
"USMAN SULAIMAN S.MAN had'ad'd'en namiji babu wani abu ragagge tare da kai."
tawani lumahe ido tana mai cigaba da shafa hoton...
SEEDRAH dake kwance cikin d'aki tajiyo sallama asama jin bata kuma ji ba sai tayi zaton ko kunnen tane kawai yajiyo mata ba dai-dai ba, har ta gyara kwanciyar ta sai kuma ta mike ta fito dan tabbatar wa ganin ta.
can ta hango Suhailat tsaye jikin hoton S.MAN tana ta faman shafawa tana sakin murmushi cike da shauki.
ido ta waro sai kuma tatafi da gudu taje ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo Aunty Suhailat dama ke ce ke sallama."
Suhailat tajuyo tana kare mata kallo daga sama har kasa dafad'in
"Kaji manya ana daga ciki anbaje."
dariya SEEDRAH tayi taruko hannunta ta janyo ta suka zau na
tana fad'in "Nayi matukar farincikin ganinki Aunty Suhailat wlh nayi kewarku sosai ina so naje gida na ganku amma wannan S.MAN d'in ya hana ban isa nafita ko nan da canba yahana maigadi ma yabarni na fita,
yasu Mama da Baba Umma Aunty Halimatu dasu Walida da Walid sai nake ji kamar shekara nayi ban ganku ba."
sosai take nuna tsantsar farincikin ta naganin 'yar uwar tata.
Suhailat ta ce
"Ke dalla dakata ba wannan ba yana ganki haka ban ga kin wani kara jiki ba,me kike jira kina wannan katafaren masarautar da baki aje kiba ba?,
sai dai kin kara haske kam fatar nan ta murje tayi luwai-luwai da ita anji sanyin AC."
"Haba Aunty Suhailat ina tambayar ki gida kina yimin zancen kiba taya ma za ayi nayi kiba ina zaman yiwa wani katon gardi bauta, duk kewar gida da Mamata ya addabe ni."
fuska Suhailat ta yamutsa tare da gyara zaman ta tana dad'a bajewa kan lallausar kujera kana tabi parlour'n da kallo sannan ta mai da duban ta kan SEEDRAH ta ce
"Mene ne a gidan da har zaki rika tunoshi har ya hanaki kwanciyar hankali in banda tarin yunwa da wahala,
ke kin san yanzuma su Umma su suke ciyar da kansu har shi Baban ma su suke d'an sakura masa wani abin yanzu komai yadad'a tab'arb'ancewa,
ki mance da wannan kedai kibaje kafarki cikin wannan daular har ranar da zan shigo gidan nan amatsayin matar Ya S.MAN,
daga ranar zaki 'yantu ki cigaba da zama a matsayin kanwarmu ba 'yar aiki ba,
kin ga kema ko ba komai zaki mori rayuwa."
Wani irin kallo SEEDRAH ke bin Suhailat da shi mai cike da d'inbin tarin mamaki sannan ta ce
"Aunty Suhailat kinsan me kike fad'a kuwa?,
duk talaucin gidan mu yafiye min nan sau dubu ko da za'a rikayin sati ne kafin a d'aura tukunya,
yanzu Aunty Suhailat mutumin da yake wulakanta Baba baisan darajarsa da kimarsa ba shine har kike mararin auren sa,
ina abin so agurin S.MAN wan da baisan darajar mahaifinki ba,
dan Allah Aunty Suhailat ki siya mana mutunci ba kaskanci da tozarci agurin S.MAN ba."
wani kallon shekeke Suhailat tabita da shi kana ta ce
"To me yakeyiwa Baban nifa sam bana ganin wani laifin sa akan kud'insa yake yin komai, kuma a wannan zamanin ko d'an ka da ka haifa acikinka ba lallai bane ya iya biyoka bashin makudan kud'ad'en da S.MAN yake bin Baba,
duk abun da ya faru ai laifin Baba ne in da ya biyasa kud'in sa da duk hakan bazata rika faruwa ba, baisan uzirin saba wata kila yana da bukatar amfani da kud'in sa ne shikuma ya hana sa, yabar masa gidan kawai yasiyar ya rike kud'in sa, ai ana wankan dare dan gobe ne kin ga gobe bazai kara basa bashi ba."
SEEDRAH data gama cika har wuya ta wasa mata harara ta ce
"Amma gaskiya Suhailat bakida cikakken lissafi uban daya haifeki wani can da tarbiyya bata ishe shiba yafi miki shi."
shewa Suhailat tayi har da tafa hanu ta ce
"Au Aunty'n ma an jingine shi a gefe sai Suhailat d'in kawai, to naji ni dai ko ma me zaki ce kan S.MAN bafa zan fahimce ki ba dan ke yarinya ce har yanzu da sauran ki tukun, wai ma dan Allah yafad'a miki ina zaije da yaushe zai dawo dan ni gurin sa nazo ba gurin ki ba."
tsaki SEEDRAH ta ja tamasa a kusa da ita ta koma gefe tana fad'in
"Yanzu kuma amsar a gurin sa zaki samu kijira dawowar sa."
fuska Suhailat ta yamutsa ta ce
"Ke dai bazaki tab'a canza halinki ba da wannan d'an banzan tsiwa da rashin kunyar."
baki ta murgud'a mata ta ce
"In dai a kan gaskiya ce sai dai a shekara ana ce min mara kunya suma masu fad'ar ai ba kunyar ce ta ishe su ba."
Suhailat zatayi magana aka turo kofar parlour Sager na gaba S.MAN nabiye da shi rike da waya a kunnen sa yana magana.
Suhailat na ganin sa ta mike tana wani karairaya tun kan su karaso cikin parlour'n take fad'in
"Sannun ku da dawowa."
Sagir ne ya amsa da yauwa S.MAN kam karasawa ya yi can kan kujera dake gefe ya zauna, har lokacin yana waya.
Sagir ma ya zauna yana fad'in
"Sannunku da gida."
cike da karairaya Suhailat ta zauna tare da gaishe sa ya amsa cikin sakin fuska.
S.MAN sai da yakai tsawon mintuna biyar kafin ya sauke wayar, Suhailat na ganin haka ta suke murya cikin tsigar jan hankali ta ce
"Barka da warhaka Ya S.MAN ya gida ya aiki."
batare da ya d'ago ya dubi in da take ba ya ce
"Lafiya." a takaice.
saikuma yasoma magana
"Ke ina abinci ko sai ance ki kawo ne kafin ki kawo."
sarai SEEDRAH tasan da ita yake tayi masa banza sai ma kokarin mikewa tayi tabar gurin dan bazata iya ganin rashin darajar da Suhailat ke son siya musu ba.
a hatsale ya d'ago dan yasan taji sa rai, ganin haka yasa
Sagir saurin cewa
"SEEDRAH kawo mana abinci munkwaso yunwa bamu tsaya munci abinci a in da mukaje ba."
"Rokon ta kake ko da sisin Alhj musa ne cikin kayan abincin gidan nan."
S.MAN yafad'a yana tsare Sagir da ido
murmushi Sagir ya yi ya ce
"Bata ji abin da ka fad'a bane shi yasa na fad'a mata."
baki ya tab'e.
SEEDRAH kuwa kugu ta rike tana yi masa kallon sama da kasa kana ta ce
"Ka saisaita kalaman ka dan shi d'in ba sa'an yin ka bane uba ne shi daya haifa."
ganin yan da yawani d'ago a fusace da sauri Sagir ya ce
"Dan Allah S.MAN."
bai saurare sa ba ya mike SEEDRAH ko na tsaye bata gudu ba dan zuciyar ta yagama bushewa.
saukar mari taji a kan bakin ta har sai da bakin nata ya fashe gefen lips d'in ta yana tsiyayar da jini.
zai kuma kara mata Sagir ya rike hannunsa ya ce
"Ya isa Haka dan Allah ke SEEDRAH je ki tafi nace."
ganin yan da S.MAN d'in ke huci yakuma ce mata ta tafi.
da sauri ta juya had'e da sassarfa yayin da zuciyar ta ke tafasa duk azabar zugin da bakinta ke mata ko d'igon hawaye babu a idon ta.
d'aki ta shiga tasoma dube-dube can ta hango wuka data yanka appel d'azu tajanyo wukar tajuyo da sauri da zummar fita taje ta same sa sai ganin sa tayi a bayan ta.
wukar ta d'ago tana fad'in
"Ni ba jakar ka bace ba a kawo maka jaka ba aiki kad'ai aka kawo ni na yi a gidan ka aduk san da kayi kokarin aibanta mahaifi na bazan kyaleka ba ko da hakan zai zamo karshen numfashi na aduniya,
mugu azzalumi."
hannunta yarike yamurd'e ya karb'i wukan,
yatura ta jikin garu yamatse ta tare da shako wuyanta yasaka wukar a wuyan ta,
ya jefa kwayar idanunsa cikin nata kana ya soma magana
"Shi waye Alhj Musan da kika isa ki hana magana a kansa ke har wani uba kike da shi anan!!."
A guje Sagir ya iso in da suke yana fad'in
"Subhanallahi S.MAN meye haka lafiyar ka kuwa."
da sauri yaruko hannunsa dake rike da wukar ya ce
"Ka dai na fa ka bari dan Allah kada ka jawo mana damuwa."
cikin fusatacciyar murya ya ce
"Meye abun damuwa akan kashe wannan yarinyar sai na canza miki kamanni saina illataki mara kunyar banza."
ya gara kanta da jikin garu.
da sauri Sager
ya daddage ya janye hannunsa kana yakukkusa yashiga sakanin su yatura shi gefe yana fad'in
"Dan Allah kayi hakuri ka kyale ta kawo wukar nan."
ya karb'i wukar yajanyo hannunsa yana cigaba da bashi hakuri suka fita a d'akin.
sai a lokacin SEEDRAH ta sulale kasa tare da sakin kukan bakin ciki...
A parlour kuwa Suhailat na ganin fitowar su ta mike tana wani yauki da kaud'i ta iso gaban S.MAN ta narke murya tana fad'in
"Sorry bro kasan yarinya ce har yanzu kuruciya na damin ta,bari na d'auko ma abincin."
hannu ya d'aga mata kana ya juya yanufi step's ya haura sama.
Sagir ya dube ta ya ce
"Je ki bata hakuri kawai bari ni zan ji da shi."
ya wuce ya je dinning ya d'au tray'n data shirya abinci ciki ya haura sama ita kuma Suhailat ta shige d'akin da SEEDRAH ke ciki.
har lokacin tana zaune dirshen a kasa tana tsiyayar da kwalla, Suhailat ta zauna bakin gado ta kalle ta tana fad'in
"To ni ban maga abin da zaisa na baki hakuri ba, rashin kunyar ki yajanyo miki duka idan baki daina rashin kunya ba to kuwa bazaki fasa shan duka ba, ke fa baki fahimci Ya S.MAN bane, bafa zagin Baba yake ba, wai ke daga zaran yakira sunan Baba sai ki jingina hakan da zagi,
gaki ke a dole zaki iya tsare masa fad'a haka zakiyi ta shan duka a banza."
kallon Suhailat take cike da bakin ciki tama rasa me zata ce sai kawai ta mike ta shige bayi..
wanka tayi tafito bata ganta cikin d'akin ba.
Suhailat ko tun shigarta bayin tafito parlour tana zaman jiran S.MAN ya sauko.
ta b'ata tsawon lokaci zaune har ta fara tunanin ko ta haura samanne ta same shi,
nan ta jiyo takon sauka daga step's da sauri ta d'ago ganin shine tashiga wani kwarkwasa da fari da idanu.
ya iso cikin parlour'n can kan kujerar daya zauna d'azu ya isa ya d'au wayar sa daya bari a gurin dan dama abin da ya sauko da shi kenan.
ganin yana kokarin barin parlour'n ta yi saurin ce wa
"Am Ya S.MAN dama fa gurin ka nazo."
da ido ya bita batare da yace komai ba
ganin haka yasata kuma narke murya tana wasa da yatsun hannunta sannan tayi d'an kasa da murya ta ce
"Ko zaka iya bani wayar ka na saka maka lamba ta."
"Babu bukatar haka zaki iya tafiya."
yafad'a tare da nuna mata kofar fita.
zata kuma magana ya d'aga mata hanu tare da kuma yi mata alama da ta tafi,
simi-simi taja kafa tana waigen sa tayi waje.
shiko tsaki yaja ya haura sama.
Kwanan Sagir uku yakoma Kano dan acan yake da zama da matar sa da 'yarsu d'aya.
shima d'an Kaduna ne aiki ne yakai sa can Kano aduk san da yashigo Kaduna har idan S.MAN na kasar gidan sa yake sauka har yagama abin da zaiyi ya koma...
Bayan kwana biyu
SEEDRAH ce a kichin tana ta sauri tagama breakfast dan ganin kamar lokaci yad'an tafi tana gamawa ta kwashi nasa tayi sama.
a parlour ta dire abincin kana tanufi bedroom d'in sa da d'an sauri dan ta makara da gyaran nasa shima, da sallama ta tura kofar sai da ta d'an yi jim a bakin kofar kafin ta shiga.
da sauri taja burki a bakin kofar hango S.MAN tsaye gaban mirro d'aure da towel a kugunsa yana taje gashin kansa ya yin da Teema ke rungume da shi ta baya ta sakalo wuyanta a gefen wuyan sa tana kare masa kallo tacikin mirro,
yayin da hannayenta ke kan kirjin sa tana shafa kwantaccen lallausar gashin kirjinsa zuwa kan d'an nonuwan sa tana kuma manna masa kiss a gefen wuya had'e da shinshinar gefen wuyan nasa.
sai mammanna ababen kirjin ta take a bayansa duk da suna cikin riga.
shiko gaba d'aya ya mai da hankalinsa kan gyaran gashin sa da yake.
daga cikin mirro SEEDRAH suka had'a ido da shi.
da sauri tayi baya tare da janyo musu kofar tasauka kasa gaba d'aya tana Allah wadai da hali irin nasa..
ta koma d'aki tayi kwanciyar ta har bacci yafara d'aukar ta tajiyo magana a kanta,
ta bud'e idanunta a kansa ya ce
ta tashi taje ta gyara masa d'aki yana fita itama ta fito, can ta hangosu suna fita shi da Teema.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 17
Yau SEEDRAH ta tashi bata jin dad'in jikinta tanajin zazzab'i a daddafe tagama aiyukan safe.
kwance take rab'uke a jikin pillow idanunta a lumshe.
kiran Kamal ne yashigo wayarta ta janyo wayar batare da ta bud'e idanunta ba ta d'aga kiran tare da kai wayar kunnen ta.
jin muryar ta hankali tashe yake fad'in
"Me ya faru me ya same ki me ke damin ki?."
ya jera mata tabayoyin cike da kulawa hankali tashe.
idanunta takuma lumshewa tana dad'a manna wayar a kunnenta ta ce
"Zazzab'i zazzab'i nake ji."
da sauri ya ce "Subhanallah bari nasa Mukhtar yazo ya kaiki asibiti sannu kinji yanzunnan zaizo."
kai ta girgiza tare da fad'in
"A'a nasha magani zai sake ni."
"Anya kuwa kin tabbata kawai yazo ya kaiki."
"Na tabbata zai sake ni, yaushe zaka dawo?."
numfashi ya sauke ya ce "Gaskiya ni hankalina bai kwanta ba ko dun ciwon nan naki ma zan dawo."
murmushi tayi ta ce
"A'a ka tabbatar da ka gama taya Alhajin Mu aikin daya kai ku tukun."
"Amma dai ki kulamin da kanki sosai dan wlh sai na iya guduwa na dawo, dan ma
Alhajin mu ya fahimci halin da nake ciki ya ce muna dawowa zai zo asa mana rana, bana so a sa yakai ko wata ne so shine samu sati biyu zuwa uku."
ta ce "Allah ya kaimu yadawo min da kai lafiya da Alhajin mu."
ya amsa da amin amin.
nan suka d'an tab'a hira irin na masoya kad'an ya ce tayi bacci anjima zai kira yaji jikin nata.
tana kashe wayar kiran Mama na shigowa.
da sauri ta d'aga dan tun shekaran jiya rabon da suyi waya da Mama.
ta kai wayar kunnenta da sallama daga cikin wayar tajiyo yan da Mama take amsa sallamar tana jan numfashi da kyar.
ido ta waro tare da mikewa zaune cikin rawar murya ta ce
"Mama lafiya me ke da mun ki ciwon ki ne ko!?."
tayi maganar hankali a mugun tashe.
dakyar Mama ta iya furta
"SEEDRAH magani na ya kare babu kud'in siya kizo ki d'au wani abina ki siyar ki siyo min magani."
wani irin dirowa tayi a kan gado cak ta nimi zazzab'in da take jin tarasa, da sauri ta d'au hijabi had'e da wayarta tanufi kofa da sauri har tana had'awa da sassarfa.
gabaki d'aya kwakwalwarta ya tsaya cak burin ta kawai ta ganta cikin d'akin Mamarta, idan kafin taje ta siyar da wani abunsu a sami kud'in siyan magani ai ciwo yagama galabaitar da Mama, mafita kawai zata nima ta in da zata samo kud'i kafin siyar da wani abun nasu,
da wannan tunanin tafice cikin d'akin.
can ta hango S.MAN zaune cikin parlour yana daddanna seystem nashi da sauri ta isa in da yake ta zube a gabansa tayi zaman dirshem a kasan carpet.
cikin matukar tashin hankali ta ce
"Dan Allah dan annabi kabani wani abu daga cikin kud'in albashina nawannan watan, Mama ta ce batada lafiya zan siya mata maganin ta, idan wani watan yayi sai a soma lissafi kan kud'in da kake bin Baba,
dan Allah ka taimaka ciwon Mamata ya tashi."
ido yad'an zuba mata ganin yanda gaba d'aya ta firgice tsananin damuwa da tashin hankali ya bayyana a gare ta,
nan da nan kuma hawaye yashiga zuba a idanunta.
sai kuma ya tab'e baki yad'an ture seystem d'in gaban sa gefe kana ya ce
"Kin san nawane albashin naki da kike cewa wani watan acire cikin kud'in da ake bin Baban ki?."
kai ta girgiza da sauri ta ce
"Ko ma nawa ne ni dai dan girman Allah kabani mahaifiyata tana bukatar taimako na dan Allah."
tayi maganar tamkar zata zubda kwalla.
kai ya jinjina ya ce
"Dube ta kamar mutumiyar kwarai to yau ina shegen bakin rashin kunyar nan take,
kinci albarkacin abu biyu girman Allah da manzonsa da kika had'a ni da su,
sai kuma darajar ciwo badun su ba babu abun da zaisa na bada."
sunkuyar da kanta kasa tayi batare da ta ce komai ba, dan bazata iya cewan bama a yan da take jin kanta ciki, tasan kalar ciwon Mamarta idan ya tashi tamkar zai tafi da ranta haka yake mata, to har yaushe zata zauna zaman yin fad'a da wani, bataje ta kai mata agaji ba.
Mikewa yayi ya haura sama jim kad'an yadawo ya zauna kan kujerar daya tashi, in da ya barta nan ya dawo ya taddata.
d'aurin kud'in dake rike a hannunsa ya nuna mata kana ya ce
"Nan 50k ne shine albashin ki."
sai ya kirga dubu goma a cikin kud'in ya zare su ya aje gefe sannan ya ce
"Wannan shine kud'in abincin ki nakwana goma, kin ga idan akayi lissafi kowani kwana d'aya kinacin abincin 1k kenan a ihisanin da zan miki."
yakuma kirga wasu dubu ashirin yakuma had'asu da wannan dubu goman sannan ya ce
"Haka ya kama kud'in abincin da kika ci na wata guda kenan kinga albashin ki yarage saura 20k kenan dan haka wannan shine kud'in aikinki."
ya nuna mata naira dubu ashirin d'in dake hannunsa sannan yazare dubu goma daga ciki ya mika mata yana fad'in
"Ga wannan kije ki siya mata maganin wannan kuma zan ajiye idan kikayi aikin wani watan sai na d'aura a kansa,
sai kiyi lissafi shekaru nawa zakiyi kina aiki kafin ki gama biyan bashin da Baban ki yaci."
tsananin mamaki ne ya kamata sai dai a yanzu bata da lokacin tsayuwa biye masa, ta karb'i dubu goman da sauri har hanunta na b'ari ta mike da sauri ta nufi kofa.
muryarsa tajiyo yana fad'in
"Kitafi da shirin dawowa yin abincin rana."
bata iya cewa komai ba tayi waje, can ta hango maigadi na gyangyad'i bakin get batabi ta kansa ba ta bud'e kofa tafita.
tana jiyo muryar sa yana fad'in
"Oga ne ya ce ki fita?."
bata saurare sa ba tayi gaba abin ta.
tana tafe kan abin hawa sai gani take kanar baya sauri, suna isa tunkan ya dai-dai ta parking ta duro tayi gida da gudu dan tun shiganta napen tabiyasa kud'insa.
direct d'akin Mama ta shiga a guje tana kiran sunan ta.
a sakiyar parlour ta iske Mama kwance a kasa tana sauke numfashi da kyar,
a guje ta iso gunta tazube guiwowinta a kasa tana fad'in
"Innalillahi sannu Mama, ke d'aya ce ba kowa ne a gidan ina su Umman suke?."
tayi maganar arikice tana d'ago kanta ta d'aurashi kan cinyarta tana cigaba da yi mata sannu.
Mama ta ce
"Basu jima da barin nan ba suma sunyi bakin kokarin su."
kai kawai SEEDRAH ta girgiza kana ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 19