bayan wata biyu za ayi aure da yardar Allah.
dan su sunce a shirye suke kuma basa so a ja lokaci.
Baba dai nanan cikin zullumi yayi mamakin ganin har yanzu S.MAN bai kira sa ba kuma baizo ba.
Tun da akasa ranar auren Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko cokali bata ajeba ga biki wata biyu acikin watan kuwa har anci kwanaki 6.
a b'angaren Baba kuwa yanke hukunci ya yi zai saida motar hawan sa wanda acin kadddarorin sa shi kad'ai ya rage masa,
yaki sai da shi ne sabo da dashi yake samu yake fita 'yar buga-bugan sa.
zai sai da shi yasamu ya yi hidimar bikin amaneji.
A b'anggaren amarya SEEDRAH kuwa ganin har zuwa wannan lokacin bataji Baba ya yi magana kan komawarta aiki gidan S.MAN ba, sai ta saki jikinta,
dan dama tana ta langwab'ewa ita a dole bata da lafiya, tana da kuma tabbacin har yanzu S.MAN bai kira shiba da taga tashin hankali ya bayyana gare shi.
yanzu shirye-shiryen auren ta tasa gaba duk da basu da kud'i amma akwai rufin asirin Allah.
biki saura sati uku dai-dai Mama ta tura SEEDRAH Zariya.
'yan uwan Mama sun yi mata goma na arziki duk da ba wani karfi sosai suke da shi ba.
duk abun da uwa harda ma uba zasuyi sunyi mata dai-dai gwargwado.
Aunty Rashida autar su Mama ita kam cewa tayi zata kwankwajeta ne ta hanyar gyara ta in da zata mai da angon nata yazamo tamkar rakumi da akala.
gyara sosai take mata SEEDRAH ko ta bada had'in kai dan so take ta sakawa Kamal kan soyayya da kaunar da yake mata.
duk wani maganin da zata bata komai rashin dad'in sa zata shanye babu wani gargada.
satin SEEDRAH biyu a Zariya sabar tasha gyara har wani ciccikowa ta dad'a yi komai yayi zam-zam.
takara fari ta kara sheki ta kara wani irin bala'in kyau albarkatun jikin ta sun dad'a tumbasa.
Kamal sunzo gaisuwa amma ba a bashi damar ganawa da amaryarsa ba, al'adarsu ce haka idan har an fara gyaran amarya tofa ango bazai sake ganinta ba har sai an kai masa ita gidan sa, sai dai su rika waya.
Tun a sauran satin kuwa 'yan uwan Mama suka taho Kaduna da amarya SEEDRAH.
Mama tayi kukan farinciki ganin yan da 'yan'uwanta
suka share mata hawaye,
'yan gulma kuwa sai zuwa kallon kaya ake dan babu wanda ya yi zaton haka.
Halimatu da Suhailat kam kiri-kiri suke nuna hassadar su, duk kuwa wanda ya ce musu kanwarsu zatayi aure ta barsu sai suce.
su boko suka sa gaba yanzu, aure kuwa sai mai gida da mota, ba irin Kamal me mashin ba.
SEEDRAH ko ce musu ta ke haka ta ke son abinta idan kuma kud'ine insha Allah zasuje su tara tare su siya gida da motar..
Yau talata hakan kuwa ya yi dai-dai da saura kwanaki uku d'aurin auren SEEDRAH da Kamal.
gida yacika makil da dangi nakusa da na nesa, rufin asirin Allah duk wan da zaizo da gudumawar kud'i ko abinci yake zuwa.
dan haka ake samu aci asha cikin rufin asirin Allah.
SEEDRAH ce tsaye cikin d'akin Mama rike da mayafi a hannunta ta dubi Hafsat 'yar Umma Bishira kanwar Mama da suka taho tare ta ce
"Dan Allah Hafsat kibar wannan kwalliyar kamar wacce zataje gasar kyau, kizo mu tafi mana yamma fa tanayi."
"Yi hakuri d'ankwali kawai yanzu zan d'aura."
cewar Hafsat tana gyara d'aurin d'ankwalinta.
Yusrah da ke danne-dannen waya ta ce
"Ki barta mana tayi kwalliyar ta kika sani itama Allah ya bata nata muna fita."
Aunty Rashida da yanzu shigowarsa rike da wasu kaya a hannunta ta ce
"Ke me zan gani haka wai SEEDRAH fita zakiyi?
oh so kike kije ki had'u da Kamal d'in ki b'ata mana al'ada, to babu in da zaki."
kafa tashiga bubbugawa a kasa cikin muryar shagwab'a ta ce
"Kai Aunty Rashida Allah ni ba wani Kamal d'in da zan had'u da shi, fa gyaran gashi zamuje."
aje kayan da ke hannunta Aunty Rashida ta yi tare da fad'in
"To zo ki karb'i nikaf ki saka sabo da tsaro."
dariya SEEDRAH ta yi ta ce
"Allah Aunty Rashida d'auke min numfashi ya ke ban iya sawa ba."
"To shike nan kuyi sauri ku dawo kada ki sake ku had'u."
ta ce to.
Hafsat da take ta dariya tun d'azu ta ce
"Wai dan Allah a hana mutum ganin matarsa, ni wannan al'adar a soketa daga kan SEEDRAH kada ya iso kaina."
"Ungo naki ai har jikoki da tattab'a kunne sai sun samu."
cewar Umma Bashira.
dariya duk sukayi suka fice a d'akin.
Suna fita waje dai-dai lokacin wata mota ta dumfaro kofar gidan.
ido SEEDRAH tad'an zubawa motar tana son tuna in d ta tab'a ganin shi.
a b'angaren Yusrah ma kallon motar take dan ta gane motar yayanta ne.
daga can gefe motar ta faka a hankali aka zuge glass d'in motar.
karaf idanunau ya sarkafu da juna, wani irin mummunar fad'uwar gaba ne ya ziyarceta tasan duk yanda akayi ba alkairi bane ya kawo sa.
da sauri ta dubi Hafsat da Yusrah ta ce
"Ina zuwa."
ta nufi inda motar take.
a hankali ya maida bayan sa yakwantar jikin sit ya yin da idanunsa ke kanta harta karaso jikin motar, taja ta tsaya tare da bin sa da wani kallo sannan ta ce
"Wani rashin mutuncinne yakawo ka, ina mai had'aka da girman Allah kada ka tozarta mahaifina cikin bainar jama'a, kaje idan mutanen da suka taru dan tayasa murna sun wase sai ka dawo, amma kasani wannan karon mu zamu kai kararka kan tozarci da rashin d'a'ar da kake gwada mana, dan talauci bata tab'a zamowa hauka ba."
tun da tafara maganar idanunsa a kanta wani irin kallo yake mata kamar bai tab'a sanin ta ba, a hankali yad'an lumshe idanunsa tare da shakar fitinannen kamshin dake fita a jikinta kana yakuma bud'e idon a kan lips d'in ta.
a hankali ya gyara zamansa ya kunna motarsa yaja yabar gurin batare da yace da ita komai ba.
SEEDRAH ko numfashi ta sauke tare da yiwa Allah godiya da yasa baizubar mutu da mutunci ba, tazo ta ja hannun su Hafsat sukayi gaba.
Hafsat na tambayarta shid'in wane ne ta ce d'an kanin babansu ne kuma yayan Yusrah.
sai wajen magriba aka gama musu gyaran gashi suka dawo gida.
Da daddare bayan sallar isha Baba na nan zaune a d'akinsa shi da Mama suna tattaunawa kan yadda shagalin bikin zai gudana, kira ya shigo wayarsa.
ganin mai kiran yasa hankalin sa ta shi da sauri yad'aga kiran
"Gani a waje."
abunda ya ce ke nan yakashe wayar.
Baba ya mike da sauri bai ko tsaya shaidawa Mama ba yafita.
yana jingine jikin motar sa ya hard'e hannu a kirji Baba ya karaso inda yake jiki na rawa yana fad'in
"Barka da zuwa alhaji Usman."
hannu yad'aga masa ya ce "Rike gaisuwar ka bashi ya kawo ni nan ba."
tsayuwar sa ya gyara kana ya ce
"Zaka iya sanar wa mutanen cikin gidannan su fita za a kulle gidan, hanzarta kada su b'ata min lokaci, idan kuma baza ka iya ba ni naje da kaina."
da sauri Baba murya na rawa ya ce
"Dan Allah dan girman Allah Usman karufa min asiri idan suka fita ina zan kaisu, ka taimakeni agama hidimarnan in yaso koma mene ne yabiyo daga baya."
"Okay bazaka iya ba ke nan."
ya d'aga kafa zai je da sauri Baba ya sha gaban sa hannu bibbiyu yashiga rokon sa da magiya kamar zai zuba guiwowinsa kasa.
hannu S.MAN ya d'aga masa kana ya ce
"Ya isa, kana son zama cikin gidan nan ayi hidimar biki lafiya?."
da sauri Baba ya ce
"Wlh babu abun da nafi bukata sama da haka, idan ka koremu ina zamuje ina zan kai wad'an nan jama'ar karufa min asiri."
"Okay zakaci gaba da zama amma da sharad'i."
jin haka yasa Baba har jikin sa na rawa sabo da farincikin ance zai cigaba da zama ya ce
"Fad'i ko ma mene ne na amince."
kai S.MAN ya girgiza kana ya ce
"Nawa nake binka?."
da sauri Baba ya ce "Miliyan 30."
"Kasan dai idan aka d'aga gidan nan za'a siyar da shi bazaikai 30 million ba ko."
kai Baba ya gyad'a ya ce "Nasani."
kai yakuma girgizawa tare da gyara tsayuwar sa da kyau kana ya ce
"Acikin 30 million aka cire 10 million saura 20 million to na yafe maka miliyan goman sannan kuma zaka cigaba da zama a gidan nan."
wani irin waro ido Baba ya yi kamar a mafarki maganar tazo masa,
ji ya yi tamkar ya yi ta tuma tsalle dan farin cikin, kamar zai rungume sa yashiga zabga masa godiya ba kakkautawa.
"Da kata har yanzu ban fad'i sharad'i na ba tukun."
"Fad'i ko ma mene ne kasamu."
cewar Baba yana washe baki.
baki ya tab'e kana ya juya yabud'e motarsa yaciro wata 'yar karamar jaka yamika masa.
ido baba ya zubawa jakar ya ce
"Wannan kuma mene ne?."
"Bud'e ka gani."
hannu na rawa Baba yashiga bud'e jakar ido ya zazzaro ganin kud'i ne d'aurin 'yan dubu-dubu da zasu kai guda ashirin.
ya ce "Me za ayi da su?."
bayan sa ya jingina jikin mota tare da zura hannunsa cikin aljuhu ya zaro sigari had'e da makunni ya kunna, kana yakai bakinsa ya zuko hayakin yabuso shi waje har kan fuskar Baba sannan ya ce
"Zaka mai da auren waccan yarinyar kaina wanna kuma sadakinta ne, kada ka sake asami wata matsala,
sannna sharad'i na gaba kada ka sake ka sanar wa Abbana wani abun da ba dai-dai ba, idan kayi yunkurin yin hakan."
ya girgiza kai tare da yin kwafa yajuya ya shiga motar sa yabar gurin.
Baba kuwa mutuwar tsaye ya yi, ta ya za ayi hakan ta kasance to me ma zaicewa mahaifan Kamal kafin ita SEEDRAH.
wani b'ari na zuciyarsa kuwa ce masa take.
"kai kam dai kakarka ta yanke saka ga yafiyar miliyan goma ga afuwan zaman gida ga wata miliyan biyu a hannunka, ya ishe ka magance wasu matsalolin da zasu kunno kai.
idan kuwa baka amince da bukatarsa ba to tabbas zaka bar gidannan, sannan kuma zai janye yafiyar miliyan goman da ya yi maka, sannan kuma ya karb'e miliyan biyu da ya baka madadin sadaki shike nan katashi a ziro."
da wannna kwarin guiwar da zuciyarsa ta basa yashiga gida.
har lokacin Mama tana d'akinsa tana zaman jiran sa.
sai da ya isa ya bud'e durowa ya aje jakar kud'in nan sannan yadawo in da take ya zauna.
ta ce "Bakon har ya tafi ne?."
ya ce "Eh, Usman ne bakon namu."
kirji Mama ta buga ta ce "Wani Usman d'in badai S.MAN ba?."
kai yagyad'a ya ce "Shi."
"Innalillahi'wa'Inna ilaihirraji'un! Allah dai yasa yaji hakuri yau ma."
Mama ta fad'a a raunace.
d'an murmushi ya yi kana ya ce
"Insha'allahu harma da rangwami mai tarin yawa."
"Rangwami kuma wani irin rangwami?."
zama Baba ya gyara ya fuskanceta da kyau kana ya ce
"Wani babban al'amari yazo da shi amma idan zayi duba da mahanga mai kyau to hakan itace kad'ai mafita a gare mu,
ya ce yana so nabashi auren SEEDRAH, sannan kuma ya yafe min naira miliyan goma cikin kud'in da yake bina, kuma mucigaba da zama cikin gidan nan,sannan yabada sadakinta miliyan biyu."
wani irin mikewa tsaye Mama ta yi tare da buga kirji ta ce
"Abashi auren SEEDRAH Alhj ko ka mance ne saura kwana uku d'aurin auren ta, sannan me zamuce wa jama'a da dangin Kamal."
"Zauna dan Allah ki nutsu ki saurare ni."
ta zauna jiki ba kwari.
ya ce
"Lokacin da Usman ya ke zuwa gidan nan yaci min mutunci akwai wani mutumin daya tab'a zuwa taimako na ne? su dangin Kamal d'in suna da kud'in da zasu iya biyan bashin da yake bina ne,
abun da nake so ki fahimta, hakan fa shine kad'ai rufin asirinmu, daga zaran ya auri yarinyar nan inada tabbacin nan gaba ma sauran kud'in zai ce ya yafe,
yanzu idan akace baza a bashi auren ta ba wani tsiyar zai tada,
karshe mukunyata a idon jama'a,
ke ba abun farinciki bane yaro da kud'i irin Usman ya ce yana son auren d'iyarki, karfa ki mance shid'in fa d'ane ga Sulaiman kanina ko ba komai ai ko dun Sulaiman d'in za a bashi,
abun da nake so da ke kije ki natsar da yarinyar nan, kiyi mata bayani yanda zata fahimta kuma nima zan kirata, sannan kiyiwa 'yan uwanki bayani idan kuma ba so kike yau ki nuna min iyakata ba!
su kuma dangin Kamal d'in da shi kansa zanji da su."
Mama ta mike jiki a sanyaye ta fita.
ko da ta sanar wa 'yan uwanta abun da ke faruwa sun girgiza ba kad'an ba, sai dai ba'a sanarwa SEEDRAH a daren ba.
washegari Baba yakira Abba a waya bayan sun gaisa Baba ya d'aura da fad'in
"Sulaiman zaka sami zuwa d'aurin auren nan kuwa?."
Abba ya ce "Da naso haka amma ayyuka sunyi min yawa inaga kawai zan saka maka gudumawa na ta account, idan na dawo zanje na t
duba zaman ta a d'akin ta, Allah ya basu zaman lafiya."
Baba ya ce
"Amin amin sai dai yanzu auren ya sauya daga kan yaron da za ayi da shi zuwa kan Usman, dan ya same ni ya ce min shi fa yana son ta wai bai fad'a bane kawai, na ce kaji min ja'irin yaro gida bai koshiba za a kai wa na waje, idan Allah ya kai mu jibi da shi za a d'aura."
Abba ya ce "Usman d'in kada ya mai damu kananan mutane mana, yasan da yana son ta tuntuni bai fad'a ba sai da aure yarake saura kwana biyu,
haba Yaya hakan ai bazai ma yiwu ba barima na kira shi kada ya mai damu mutanen banza mana."
da sauri Baba yatari numfashin sa
"A'a da kata mana, ai babu batun wasu mutanen banza, ko sune ma hakan ta kasance da su hakan zasuyi,
tun da Allah yasa ya furta yana sonta to a bashi ita,
harsai yaushe ne zaiyi aure yakai har i wannan lokaci baiyi aure ba, gida bai koshi ba a kaiwa na waje."
"Yanzu Yaya kana ganin hakan bazai tab'a mutunci muba bazasuce munso kanmu da yawa ba."
"A'a babu abun da zasuce ni zanji da su."
Abba ya ce "To shi ke nan Allah ya tabbatar mana da alkairi."
sukayi sallama.
Abba a wani b'angare na zuciyar sa yana mai matukar jin farinciki d'ansa da 'yar d'an uwan sa zasuyi aure akara kulla dankon zumunci, nan take yakira Ummi ya sanar mata.
Ummi tayi matukar farinciki dan a yanzu bata da burin da ya wuce taga auren d'an nata duk da kuwa auren yazo musu a bazata cikin rashin shiri.
nan take ta d'aga waya ta kira S.MAN ta ce yazo yanzu tana niman shi.
ko da ya iso gidan farincikin Ummi yagaza b'oyuwa
kamar ta goyashi haka ta ke ji.
ta dube shi fuska d'auke da murmushi ta ce
"Usman kana takan shiri kuwa? ya kamata yanzu mushiga Kano muje mu had'o lefe tun da abun yazo a kurarren lokaci da da sauran lokaci da a Dubai za aje had'o lefen nan,
to Allah ma yasa anan gida Nigeria muna da kayayyaki masu inganci kamar na kasashen ketaren."
baki ya tab'e ya ce
"Ummi wani lefe kuma auren nan da d'an wani lokaci."
ta ce "Ban fahimta ba kamar ya?."
kai ya d'an sosa kana ya ce "To ni me na sani game da hakan, duk abun da ya kamata sai kiyi."
baki ta washe ta ce "Ah to yanzu naji zance,
wlh kamar ka shiga raina na dad'e ina fatan hakan SEEDRAH yarinyar kirki ce."
zaman ta tad'an gyara kana ta ce
"Amma Usman me yasa bakayi magana tuntuni kana son SEEDRAH ba, sai yanzu da auren ta yarage kwana biyu me kake ganin mutane zasuce a kammu."
kafad'a ya d'aga alamar ko oho ya ce
"Ko me ma suce." Ummi kam shiru ta d'anyi kana ta ce
"To Allah yasa hakan shine mafi alkairi."
shiko mikewa ya yi tare da d'aga kiran da yashigo wayar sa yafice yashiga motarsa ya bar gidan.
nan da nan Ummi tashiga kiran 'yan'uwanta da abokan arziki tana sanar musu.
daga karshe takira lambar Sagir bugu d'aya a na biyu ya d'aga,
cike da girmamawa yashiga gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da farincikin da ke d'awainiya da ita.
kana ta ce
"Sagir zan shigo Kano anjima zakayi mana jagora zuwa kasuwa had'o lefen Usman."
cike da mamaki Sagir ya ce
"Lefe kuma na S.MAN?."
dariya Ummi ta yi ta ce
"Eh na shi kaima abun yazo maka a bazata ko bai sanar maka da auren nashi bane."
"Bamuyi maganar da shiba."
nan ta labarta masa ranar auren da kuma wacce zai aura.
Sagir ya girgiza da jin wacce S.MAN d'in zai aura ya ce "To ai ina ma kadunan dama yau zan wuce Kanon da yamma sai mu wuce kawai."
Ummi ta ce "To shike nan bari na fara shiri."
Sagir suna gama waya da Ummi cikin hanzari yanufo gidan S.MAN, tun kafin ya iso yakirasa a waya ya tambayesa ko yana gidan, ya ce yana nan babu in da yaje.
yana isa gidan a parlour'n kasa ya iske shi yana zaune yana kallon sa cikin kwanciyar hankali.
Sagir ya karaso cikin parlour'n ya zauna kan kujerar da ke fuskantarsa tun kafin ya karasa zama ya ce
"S.MAN da gaske auren yarinyar nan zakayi?."
d'an dubansa ya yi kana yamai da idanunsa kan TV
"Tantama kake?."
"Amma dai S.MAN kana son yarinyar nan? idan kasan ba sonta kake ba pls kabarsu suyi auren su, kada ka cutar da su."
baki ya tab'e kana ya ce
"I don't think I love this girl, even if we get marry I will divorce her."
"What! amma meyasa zakayi hakan dan Allah ka fita a sha'anin yarinyar nan, ka barta ta auri wanda yake son ta."
wani kallo ya wasa masa kana ya mike tare da fad'in
"Idan ka gama zaman zaka tafi ka kashe min TV."
ya haye sama yabar Sagir agun baki bud'e.
haka nan Sagir ya bar gidan yana alwadai da son kai irin nan S.MAN..
Baba musamman yayi tattaki zuwa gidan su Kamal yasa akayi masa sallama da mahaifin Kamal.
nan Baba yashiga shirya masa zance cikin hikima da dabara daga karshe ya d'aura da fad'i.
ai tun da dad'ewa dama da alkawarin aure sakanin S.MAN da SEEDRAH tun mahaifinsu na da rai.
sai da wannna auren ya taso kafin aka tono maganar da aka jima da binne ta, dan haka suke son cika alkawarin da suka d'auka, sucika burin mahaifinsu.
ya maido masa da kud'in sadakin su, kud'in da ya dawo musu da shi kuwa yacire ne cikin kud'in da S.MAN ya bashi.
wani d'an uwan Baban Kamal ya buga kasa ya ce
ba a isa ayi musu wannna aikin ba sai da suka tara jama'a tukun za a tozarta su.
Baban Kamal daya shiga rud'ani sosai ya ce yabar maganar, kana ya ce wa Baba shike nan Allah yasa hakan shine mafi alheri.
Baba ya koma gida a kunyace dan kuwa mutane sunyi ca a kanshi kowa yana fad'in ba ayi wa dangin Kamal da shi Kamal d'in adalci ba.
amma ya gwammace jin wannan kunyar da kunyar da S.MAN zai janyo masa...
Ko da labari yashiga kunnen Kamal tamkar zai haukace sabar kid'ima.
ya yi ta kiran lambar SEEDRAH bata d'agawa hankalin sa yakuma mummunar tashi, saiga Kamal kuka wui-wui da idanunsa, yaso yaje gidansu SEEDRAH amma Baban sa ya hanasa. ya ce har idan shi ya haifesa bai yarda ya taka kafarsa a kofar gidan su SEEDRAH ba.
yana zaune a d'akin sa Mukhtar da wasu abokansa sai bashi baki suke, shikam ina baya jin su sai aikin kiran wayar SEEDRAH ya ke wan da har lokacin yana ringin ba a d'agawa, lokaci zuwa lokaci kuma ya share hawaye.
yana mikewa tsaye ya yanki jiki ya fad'i, nan aka garzaya da shi zuwa asibiti.
A b'angaren SEEDRAH kuwa har yanzu bata san abunda yake faruwa ba, dan 'yan uwan Mama da ita Maman kanta babu wanda ya sanar mata abun da ke faruwa.
ta nimi wayarta kuma ta rasa Aunty Rashida ce ta d'auke wayar ta b'oye dan tasan dole ne Kamal d'in zai kira ta.
Yau juma'a da misalin karfe 11 na safe Aunty Rashida tagama zizarawa amarya SEEDRAH jan lalle, mai matukar kyau da tsaruwa irin na amare.
abun ka da farar mace ba karamin kyau jan lallen ya yi mata ba.
SEEDRAH ce zaune gaban Mama da 'yan uwan Maman da suka zagaye ta.
jikin ta ya yi sanyi sosai dan zaton ta nasiha zasuyi mata dan tun da akasa ranar auren kullum acikin yi mata nasiha ake.
Umma Bishira tad'an nisa cike da fargabar abunda zaije ya dawo ta ce
"SEEDRAH kiyi hakuri da abunda zai fito daga bakin mu, amma idan kikayi nazari zakiga dacewar sa duba da halin yau da babanki ya ke ciki, SEEDRAH kizamo 'ya mai biyayya wa iyaye hakika zaki sami dace wa da rahamar Allah kiyi hakuri kiyi biyayya wa iyayen ki da kuma mijin ki, kiyi hakuri ina mai baki hakuri kizamo 'ya mai biyayya wa iyaye."
shiru tayi kanta a kasa tana sauraron ta. a kasan ranta take fad'in
"Yau kuma nasihar har da biyayya wa iyaye ne."
muryar Umma Bishira ta sinkayo tana fad'in
"SEEDRAH a yau auren da za a d'aura miki bada Kamal za a d'aura ba da Usman wato S.MAN za a d'aura, yasami mahaifinki ya sanar masa ya na sonki ankuma juya auren yadawo kansa,
dan haka kiyi biyayya wa iyayenki ki karb'i kaddarar data zo miki a haka."
duk suka shiga yi mata nasiha tayi hakuri ta d'auki dangana.
wani irin duuummm haka taji kunnuwan ta sunyi mata
ido ta ware kan Mama da tuni idanunta suka cuko da kwalla cikin harhad'a kalma da sarkewar numfashi ta ce
"Ma..Ma..Mamaaa wai.wai..me.mee..suke fad'a ne!."
cikin matukar tausayi Aunty Rashida ta riko hannunta cikin nata ta ce
"Kiyi hakuri SEEDRAH haka Allah ya hukunta miki S.MAN ne mijin ki ba Kamal ba wannan rubutacce ne tun ran gini ranzane."
Mama ko hawaye ta share cikin jin tausayin d'iyar tata.
d'ipp jinta da ganin ta suka d'auke sai fafutukar fizgo numfashin da yake kokarin barinjikin ta take.
a kid'ime duk sukayi kanta Aunty Rashida da tafi kusa da ita ta janyo ta jikin ta ganin tana kokarin sulalewa kasa,
nan take numfashin ta ya d'auke.
ruwa aka shiga yayyafa mata amma ko gizau batayi ba.
Mama kam tama rasa me zatayi sai gefe taja ta zauna tacigaba da sharar kwalla.
hayaniyar da Umma tajine had'e da salati yasata shigowa d'akin Mama da sauri, ganin halin da SEEDRAH ke ciki tafita tacewa Halimatu tayi sauri taje ta kirawo Dr Maryam wata makociyarsu.
sai a lokacin Umma ta sami labarin abun da ke faruwa ta tausayawa SEEDRAH matuka, sai dai a wani b'ari na zuciyarta bataji dad'i ba dan tasan irin kaunar da 'yarta take yi wa S.MAN tajima tana mata fatan samin sa, amma ina yanzu kam ya dad'a mata nisa.
Dr Maryam tazo ta duddubata nan tashiga bata taimakon su irin na likitoti.
ta ce musu dogon suma tayi amma zata farfad'o insha Allah.
ta d'aura mata ruwa da zai taimaka mata wajen dawo hayyacinta had'e da allurai.
ta ce kada a rika surutu kusa da ita sukayi ta mata godiya kana tayi musu sallama ta tafi.
nan aka ragu a d'akin kamar yadda likitar ta ce.
nanfa gidan biki ya kacame kowa da fad'i albarkacin bakinsa,
masu san barka sunfi yawa dan a cewarsu a yanzu samin miji kamar S.MAN yana da wuya ga dukiya ga kuma d'aukaka.
Suhaita da Halimatu kuwa kamar su kashe kansu dan bakinciki.
musamman Suhailat dake mahaukacin son S.MAN SEEDRAH tasha tsinuwa yafi cikin kwando a gurin ta.
har cewa tayi wai dama ashe sonshi take shiyasa tayi ruwa tayi saki wajen ganin taje gidan sa aiki.
har kuma fatan mutuwa tayi mata wai Allah yasa kada ta farka daga wannan suman sai dai ta farka cikin kabarin ta.
A b'angaren Kamal kuwa 'yan uwa ne tam kansa a asibiti bayan ya farfad'o, abin tausayi da kuka ya farka kamar karamin yaro.
sai baki ake basa yayi hakuri ya bar wa Allah komai.
Maman Zeey da ta shigo d'akin da aka kwantar da shi hankali tashe labari ya isketa, Zeey na biye da ita.
cikin matukar tausayawa Maman Zeey ta maso bakin gadon taruko hannunsa tana fad'in
"Yi hakuri Ya Kamal."
hannunta ya kankame yana wani irin kuka.
duban Alhj Tahir mahaifin Kamal Maman Zeey tayi kana ta ce
"Aje a cigaba da shagalin biki baza a fasa komai ba idan lokacin da aka saka na d'aurin aure ya yi aje a d'aura da Zainab."
tayi maganar tana nuna Zeey dake tsaye duk tausayin Kamal ya cikata, sai sharar kwalla take.
Alhj Tahir da maganar yazo masa a bazata ba shiba duk wanda ke cikin d'akin, musamman Kamal da Zeey.
Alhj Tahir zaiyi magana Maman Zeey ta ce
"Alhj yanzu ba lokacin tsayuwa magana bane an tara jama'a aje a ji da jama'a kada kuma lokaci ya kure."
Bayan sallar juma'a dandazon jama'a suka shaida d'aurin auren Usman Sulaiman S.MAN da amaryarsa SEEDRAH.
kamar yadda aka shaida d'aurin auren Kamal da Zeey.
Bayan d'aurin aure kuwa wasu 'yan'uwan Ummi da Goggo Larai suka kawo akwatuna set uku ko wanne cike
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 19