Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da sallama. Maman Zeey tana sakar gida tana d'an aikace-aikace, ta amsa sallamar tana fad'in "A a yau ankawo min surukar tawa ce da kanka ba sai tazo abiyo ta ba." murmushi tayi cike da jin kunya tayi kasa da kai. "Ina yini Maman Zeey ya gida." ta fad'a tana d'an murmushi da wasa da bakin gyalen ta. Kamal kuwa dariya yayi tare da shafa gefen fuskarsa ya ce "Maman Zeey kuyi kuje ku d'auko min ita dan Allah nifa hakuri na yafara karewa." ido SEEDRAH ta waro cike da mamaki mai had'e da jin kunya tana aika masa da harara ta gefen ido. shiko gira ya d'aga mata. dariya Maman Zeey tayi ta ce "Allah ya shirya Kamal zamu d'auko maka ita." da sauri SEEDRAH ta d'aga kafa zata bar gurin. Zeey data fito daga cikin d'aki da sauri cikin muryar dariya ta ce "Tsaya-tsaya-tsaya, yauwa tun da kinzo yau zamuyi gwajin girki naji irin girkinki, Allah in baiyi dad'i ba daga yau Ya Kamal ka daina yimin gorin girki ehe." dariya tayi tawuce sashin Naseeba, Kamal yabi bayan ta yana fad'in "Yarinya asalin girki ta iya ke dai kishirya zuwa gidan mu kwad'ayi." Ihun murna Naseeba ta sake ganin SEEDRAH ta rungume ta tana fad'in oyoyo. SEEDRAH ta janye jikin ta tana fad'in "Ke kada kije ki matse mana baby irin wannan runguma haka." "Ai murnan ganin kine." Nasiba ta fad'a tana dariya. "So take ta janyo mana asara kibi a hankali fa." cewar Kamal yana karasowa ciki Mukhtar yafito suka tafa da abokin nasa, duk suka shige ciki. a parlour suka ya da zangon su. nan da nan Naseeba ta cike su da kayan ciye-ciye suna ci su hira. SEEDRAH ta dubi d'an karamin cikin Naseeba daya fara tasowa ta ce "Mace fa zaki haifa mana dan so nake nakoyi kitso a kanta." "Yauwa fad'a masa nimafa mace nake so wai shi namiji." Mukhtar ya ce "To dai son kai za a gwada mana, Kamal ko kai ma kana bayan su ne." kallon kasa-kasa Kamal yabi SEEDRAH da shi kana ya ce "Namiji muke so ita shugaban 'yan maganan ma ta shirya rainon maza biyu." baki SEEDRAH ta murgud'a masa ta ce "Kabaryi da ni." dariya Mukhtar yayi ya ce "Kayi kokari abokina." Hira sosai suke cike da zolayar juna, ko da aka kira sallar azahar Mukhtar da Kamal suka tafi masallaci, basu dawo gidan ba sai da akayi sallan la'asar. nan SEEDRAH ta ce zata koma gida Mama ta ce kada takai dare, kuma tana so ta shiga gidan Nabeela. tayi musu sallama Kamal ya d'auke ta sukayi gidan Nabeela daga nan ya mai da ta gida... Zaune Baba yake a d'aki yana huta gajiyar daya kwaso a kasuwa, kira yashigo wayar sa. ganin mai kiran nasa yasashi shiga damuwa, jiki ba kwari yad'aga kiran. daga cikin wayar S.Man ya ce.........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ ( _Bismillahirrahmanurrahim_) _Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* page 10 "Nazo gidan ka ji ina fata an fad'a maka, bazan kuma zuwa na uku nayi zuwan banaza ba, ka tabbatar da ka ajemin kud'ad'ena dan yau babu afuwa cikin zuwa ta." yana gama fad'in haka ya kashe wayar. Baba ko numfashi ya sauke yana jinjina kai . Mama dake zaune gefen sa idanunta akan sa ganin yadda ya zaro wayar jiki a sanyaye yana juya wayar cikin matsanan ciyar damuwa ta ce "Usman ne ko?." kai yagyad'a mata alamar Eh. kana ya ce "Bansan ta hanyar da zanbi na iya samo masa kud'insa ba sati guda nayi ina zuwa kasuwa da iya karfi na nake gudanar da kasuwan cinnan amma yar yau ban had'a ribar da ta kai naira dubu d'ari ba, ina da tabbacin koda shekara zanyi bazan iya samun naira miliyon 30 ba." Numfashi yaja kana ya ci gaba "Idan ba gidan nan zan d'aga na siyar ba to bansan ta inda zanbi na samo masa kud'in sa ba, kud'i yana da wuyar sha'ani kud'i ke sa karami ya raina babba, d'an d'an'uwana yake gaya min maganganun da suka fito daga bakin sa, wan da ko shi Sulaiman d'in bazai iya duban tsabar idona ya gayamin kwatankwacin sa ba." "Yanzu sai da gidan za'ayi." Mama ta fad'a cike da damuwa. "Baza a sai da gidan ba, idan aka sai da ina zamu je, idan kuma gidan haya zamu koma a wanna lokaci da haya tayi tsada ga shekara yanzu babu wuyan ta zago, y'an kud'in da nake juyawa bazasu wadacemu abiya haya sannan aciyar da kai ba." kai Mama ta jinjina cike da tausayin halin da suka tsinci kansu ciki.. Wunin ranar Baba yayi ta zuba idon ganin da me S.MAN zaizo yau kuma, amma har dare bai zoba, a daren ranar yakira Abba ya ce yaroka masa S.MAN d'in yakara masa hakuri. ko da Abba yakira S.MAN da batun kin dawowa gidan Abba yayi, yayi zaman sa a gidan sa. Bayan kwana biyar har lokacin Baba na zuba idon ganin S.Man shiru sai dai shi S.Man d'in ma baya kasar yatafi kasar spain sakamakon kiran gaggawar da yasamu kan buga wani wasan da zasuyi. watan S.Man guda da tafiya kenan zuwa lokacin sosai Baba ya dage da niman kud'i duk da yasan kasuwan cin da yake yi in shekara goma zaiyi bazai sami ribar da zai kai kud'in da yake bin sa ba, sai dai yasan hanyar Allah tana da yawa. in yaso sai ya bud'a masa a cikin rabin shekara yasami kud'in sa ya basa. ya sanyawa ransa haka sai dai ina, jiya kamar yau wata guda bai ajiye kud'in da yakai dubu d'ari ba... Da sauri SEEDRAH ta fito daga d'akin Mama cikin shigar tafiya school tayiwa Mama sallama tayi waje, da d'an sauri take tafiya dan ta d'an makara sai da ta haura can bakin titi kafin ta sami abin hawa. Yau Baba na gida bai fita kasuwa da wuri ba har wajen karfe shad'aya da rabi, yafito daga d'akinsa, su Mama suna yi masa a Allah bada sa'a. yana fitowa farfajiyar gida tsayuwa yayi da d'inbin mamaki ganin S.Man da wasu mutane ga dukkan alamu shigowarsu kenan. da kaga mutanen zakasan hukuma ne su dan ga alamun hakan a tattare da su. Baba ya karaso in da suke jiki a sanyaye yana fad'in "Usman kaine tafe sannunku fa yaushe ka dawo kasar?." hannu S.Man yad'aga masa batare da ya amsa gaisuwar had'e da tambayar da yake masa ba. kana ya dubi mutanen dake tare da su ya ce "Shine wannan kusashi yanzu ya fita a gidannan nakulle shi." cikin matsanan ciyar tashin hankali Baba ya ce "Haba Usman dan Allah dan Annabi kayi hakuri idan kafitar damu a gidan nan ina zamu koma, ka kara hakuri ina ta kokarin nima maka kud'in ka ko yanzu ma gurin niman zanje." "Kuzauna a titi ma bai shafeni ba, yau zakabar gidan nan sannan kasani idan har nasiyar da shi yagaza kud'in da nake binka dole zakayi min ciko, kana b'ata mana lokaci dukkanin mu muna da abin yi kusashi ya miko min takardun gida, idan kuma ka hana yanzu ni me iya sawa ne a buga min wasu." hukumar dake tafe da shi su suka ce "Shiga ka d'auko takardun gidan sannan ka sa mutanen ciki sufito had'e da kayan ku." hannu Baba ya had'a bibbiyu yashiga rokon su da magiya kan suyi masa hakuri su barshi a gidan sa, amma me kamar dad'a ingiza S.Man ake yana kwararowa Baba rashin mutunci sinki-sinki. Hayaniyar da su Mama sukaji ne yasasu fitowa ganin abunda ke faruwa hankali tashe suma suka shiga basu hakuri. Suhailat da Halimatu sunyi jungum-jungum yayin da idanunsu ke kan S.Man... SEEDRAH da ke tafi kan abin hawa zuwa makaranta har sunyi nisa ta tuna bata d'au wani littafin ta mai muhimmanci ba, da sauri ta ce wa mai abin hawan ya juya da ita tayi mantuwa zata kara masa kud'i. suna isa kofar gida ta rika jiyo hayaniya da sauri ta sallami mai abin hawan ta shige gida cikin sauri har tana had'awa da sassarfa. turus ta ja ta tsaya daga bakin get tana kallon kowa d'aya bayan d'aya. can ta hango Mama da Umma da Baba suna ta zuba magiya kamar zasu zuba guiwowin su a kasa. S.Man na jingine da jikin motarsa ya hard'e hannayen sa akirji yana girgiza kafa cike da rashin daraja, wad'an nan mutanen dayazo da su kuma suna cewa su Baba suyi suje su fara fitowa da kayan su. Baba ya matsa gaban S.MAN cikin magiya da roko ya ce "Usman ni fa wan mahaifinka ne kada ka mance da Sulaiman da ni uwa d'aya uba d'aya, ko wani kagani zai yi min irin wannan tozarcin bazaka kyale ba sai kuma gashi kaine da kanka kake kokarin tozartani, haba Usman ka farka daga baccin da kake mana." hannu S.MAN ya d'aga masa kana ya ce "Dangantakar ka sakanin kai da mahaifina ne ba da ni ba, idan kai yayansa ne bai zama kai yayana bane so shine d'an'uwan ka bani ba, nifa a kan kud'i komai ma zan iya musamman wanda na tara da gumi na, idan baza ku iya fitar da kayan ba yanzu nabiya afitar dasu!!." "Wace doka ce tabada damar fitar da wanda ake bi bashi a gidan sa kai tsaye rana asaka batare da bincike da yanke hukuncin wad'an da suka dace ba!!." Maganar SEEDRAH suka sinkayo cike da amon sauti mai nuna zallar tafasar zuciya had'e da raurin d'iya mace. tattausar muryar ta mai zaki dake fitar da sauti cikin nuna zallar b'acin rai da takaicin tozarcin da ta taras akeyiwa mahaifinta, tashiga d'aga kafarta tana dumfaro inda suke ya yin da tashiga nuna S.MAN da hukumar dake tafe da su da hannu tacigaba da fad'in "Babu dokar da ta ce haka, dan haka baku da ikon da zakuce lallai sai ya fita a gidan sa ya baku a bakin kud'in da ake binsa, kuje kuyi sammacin sa a kotu idan kotu ta kirasa zai amsa kiranta dan acan ake zartar da hukuncin daya dace, daga nan fa duk kud'in da yake samu a sati ko wata ko shekara aciki za'a rika cirewa ana baka har bashin ka ya kare, baka da ikon da zaka zo da wasu kace sai yabar gidan sa, babu in da zamuje muna nan, idan kud'in ka kake so kaje ka kai karan Baba kotu!." ta karashe maganar da nuna S.MAN da yatsa had'e da murgud'a masa baki. Tun da tafara maganar ya kafe ta da ido ganin kokari da karfin halin yarinyar. cikin tsawa d'aya daga cikin d'ansandan da akazo da su ya ce "Ke hukuma ne zakija dasu yanzu zakiji ki a cikin cell." Mama ce tayi saurin ruko hannun SEEDRAH ta jata tana fad'in "Ke SEEDRAH hukuma ne fa zo ki shiga ciki." "Mama dan hukuma ne sai ayi shiru a kyale gaskiya bayan ga gaskiya ana gani a fili, tun da su ba mala'ikun zare rai bane kibari a fad'a musu.." da sauri Mama ta rufe bakin ta bata bari ta karasa ba, S.MAN yabi bayan ta da kallo har suka b'acewa ganin sa. da sauri yazura hannunsa cikin aljuhun wandon sa yana kokari zaro sigari sai kuma ya bari, yakai hannu ya shafo sumar kansa tare da furzar da iska daga cikin bakin sa. sai da Mama ta kaita har cikin bedroom d'in ta sannan ta sake ta ta kuma ce ta zauna anan kada ta fito. kuka SEEDRAH ta fashe da shi takifa kanta jikin pilo tana mai jin d'aci cikin ranta da mugun tsanar S.MAN Can waje kuwa har lokacin su Baba suna ta kan faman magiya da roko, S.MAN ya dubi d'aya daga cikin d'ansandan dake kusa da shi kana ya yi masa magana kasa-kasa. kai d'ansandan ya gyad'a kana ya dubi 'yan'uwan sa ya ce "Kuzo muje." suka shige mota shima ya shiga yaja suka fice a gidan. godiya wa Allah su Umma sukayi ganin sun tafi batare da sun ce komai ba. jiki bakwari sukaja kafafunsu suka koma ciki. Baba na shiga d'aki lambar Abba yakira sai yaji wayarsa a kashe ya ma gama mancewa da Abba'n yatafi wani kasuwanci shida abokinsa a Japan. Mama tashigo d'aki ta sami SEEDRAH zaune a bakin gado tagama kukan ta share hawaye ta turo baki gaba. ta dube ta tana fad'in "Su Usman d'in sun tafi ma wata kila ya hakura ne, yakamata ki tashi ki koma makaranta me ma yadawo dake ne ma?." kwanciya ta gyara kan gadon Mama ta ce "Sai kuma gobe yanzu kam." Mama ta ce "Allah ya kyauta." tayi waje. A b'angaren Baba ma kasuwan da bai fita ba kenan ranar dan gabad'aya jikin sa yagama mutuwa. Da misalin karfe 8 na dare S.Man ne zaune cikin parlour'n sa dan yanzu yadawo zaman gidan sa. in ka gansa gidan Abba to yaje gaishesu ne. d'agowa yayi daga kallon System daya mai da hankalinsa sosai yake aikin latsashi, sai dai fuskarsa sam babu walwala. d'an shiru yayi da alama dai nazari yake rufe System d'in yayi ya mike da d'an sauri ya zari makullin motar sa dake kan table d'in gaban sa yafita da d'an sauri. Baba da ya fito daga masallaci sallar isha yazo zai shiga gida yaga mota tsaye a kofar gida. ganin wan da yake tsaye jikin motar yasashi karasowa in da yake jiki a sanyaye, yana tunanin da wani abun kuma yazo yanzu. S.Man yagyara tsayuwar sa da kyau kana ya dubi Baba da duk jikin sa yagama sanyi yana zaman jiran jin ta bakin sa ya d'an karkata kai kana ya ce "Ina bukatar 'yar aiki da zata rika kula min da tsaftar gidana da girki zan rika biya duk wata, idan kaso sai arika cirewa daga cikin bashin da nake bin ka." tun kan ya karasa Baba ya ce "To-to-to bawata matsala ai ga yarannan in kyauta kake so ma sai surika zuwa suna yi maka ai bawata damuwa ai, ina dai shike nan abunda kazo da shi gobe sai suje su fara." baki ya tab'e ya ce "Ba gayya nake so ba mutum d'aya ma ya isa." Baba yawashe baki da jin dai ba maganar kud'i ko gida bane dai yazo da shi cikin kuma washe baki ya ce "Au to shike nan ai tun da Suhailat itace babba sai ta rika zuwa." katse shi ya yi da fad'in "Ba ita ba d'ayar...........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ ( _Bismillahirrahmanurrahim_) _Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* page 11 Baba ya ce "Ohoo Halimatu? ai ko gobe sai ta fara zuwa." d'an shiru S.MAN ya yi alamun nazari, Baba ya juya zai shige gida yana fad'in "In Allah ya yarda gobe da sassafe zata fara zuwa ai ba wata matsala kannen ka ne ai kana da iko da su, idan akwai wani aikin ma nan gaba sai su tafi duka da Suhailat d'in dun su gudanar da aikin da sauri, bawata damuwa ai gobe zata fara zuwa." "Ba ita ba, sannan kuma bana bukatar zuwa a matsayin dangi na amatsayin 'yar aiki nake bukata, kuma ba wacce zata rika zuwa tana dawowa ba sabo da kowani lokaci zan iya bukatar a gudanar min da wani abin, idan zuwa zatayi tarika dawowa lokacin da na bukaci wani abu bata nan fa?." Tsayuwa Baba ya yi tare da juyowa ya ce "To-to wa ke nan SEEDRAH kake fad'a?." d'an shiru ya sake yi yana juya sunan cikin ransa yana son tuna sunan da yaji Ummi ta kirata da shi randa yafara ganin ta a gidan su takai masa abinci. kai ya gyad'a masa duk da baya da tabbacin sunan nata kenan dan baisan sunan ta ba bai kuma tuna sunan da yaji Ummin ta fad'a ba. Baba ya ce "To ba matsala shikenan bari na shiga ciki muyi magana." Baba ya shiga ciki da sauri dan baya so ya tsaya har ta kaisu ga zancen kud'i ko gida. aransa kuwa yana tunanin ta yadda za'ayi SEEDRAH taje ta zauna a gidan sa bayan tana tafiya makaranta, kawar da tunanin ya yi da ayyana daga can d'in saita rika zuwa koma ta aje karatun. dan shi yanzu yana jin duk abunda S.MAN ya ke bukata zai masa har idan zai sarara masa kan maganar kud'i da gidan sa. Direct d'akin Mama Baba ya shige ya taddata zaune kan sallaya tana jan jarbi, yazauna bakin gado. ta d'ago ta dube shi tana fad'in "Barka da dare Alhj." ya ce "Yauwa." kana ya muskuta da kyau ya gyara zaman sa sannan ya ce "Usman ne yazo yanzu ina ga ma ya tafi." kirji Mama ta buga a d'an razane ta ce "Allah dai yasa ba da hukuma yakuma zuwaba, yau idan yad'aga mu a gidan nan ina zamuje." "Ba da kowa yazo ba, zuwansa na yanzu ya bambamta da zuwansa na ko yaushe, yanzu yazo ne niman wacce zata rika yi masa aiki a gidan sa yakuma ce wai SEEDRAH ya ke so taje tarika yi masa aikin." ido Mama ta waro tare da kuma dafe kirji ta ce "Meyasa sai gidan nan ne zai zo niman 'yar aiki meyasa kuma yazab'i SEEDRAH ita ce zatayi masa aikin, Alhj ina jin tsowa nasan SEEDRAH ma bazata amince ba tun da ga su Halimatu d'aya daga cikin su kawai tarika zuwa tana yi masa aikin." Baba ya riko hannunta ya ce "Haba meye kuma najin tsoro ai godewa Allah yakamata ma muyi tun da har ya tako kafa yazo niman wani abu a gurin mu ko tanan zamusan yad'an hakura zaiyi mana jinkiri zuwa musamu kud'in sa mu basa, zai kuma hakura yabarmu a gidan mu, har Allah ya kawo lokacin da zamu samu kud'in sa murabu da shi, kuma ma ya ce zai rika biyan kud'in aikin, sannan kuma kud'in albashin acikin kud'in da yake bina zai rika cirewa ai kin ga dai za'a d'an rage wani abin, kuma nima sai da na ce masa gasu Halimatu ya ce basu yake bukata suyi masa aiki ba ita SEEDRAH yake bukata." "Alhj to karatun ta fah sai dai tarika zuwa da farar safiya ta dawo ta tafi makaranta ke nan." hannuta Baba yakuma damkewa ya ce "Nima nayi tunanin hakan amma ya ce zama zatayi acan gidan nasa, ai inaga babu wata matsala in yaso daga can d'in sai ta rika tafiya makarantar." "Amma Alhj.." katse ta ya yi da afad'in "Hakan ne kad'ai mafita kituna fa idan mukace zamuyi masa musu to fa babu makawa sai munbar gidan nan, dan Allah kada kikuma cewa komai ki kirawo SEEDRAH kiyi mata maganar ta shirya idan Allah yakaimu gobe zan kaita gidan nasa." Numfashi Mama tasauke kana ta gyad'a masa kai jiki a sanyaye, Baba ya mike ya fita, yana fita Mama ta daga waya ta kirawo lambar SEEDRAH. SEEDRAH dake kwance a d'akin su manne da waya a kunne suna waya da Kamal, ganin kiran Mama yasa ta cewa Kamal d'in ya kashe bari taje kiran Mama, ta mike ta nufi d'akin Mama. Mama na ganin ta tamike daga kan sallayan da take zaune ta koma bakin gado. "Zo zauna nan." Mama tafad'a tana nuna mata gefe da ita. SEEDRAH ta karaso ta zauna kusa da ita Mama ta dube ta da kyau kana ta ce "Yayan ku Usman yazo." SEEDRAH ta ce "Waye kuma Yaya Usman Mama?." "Usman d'in Abba'n ku Sulaiman S.MAN fa." baki SEEDRAH ta tab'e ta ce "Usman dai ko S.MAN d'in babu wani Yaya mutumin da baya ganin darajar Baba mezai sa shima a daraja shi, yakuma zuwa ciwa Baban mutunci ne?." kai Mama ta girgiza kana ta ce "Ki shirya kayanki gobe Baba ku zai kaiki gidansa zaki je ki d'an rika kula masa da gida ne." wani irin waro ido SEEDRAH tayi tare da d'an zabura tanuna kanta ta ce "Ni nine zanje gidan sa kula masa da gida?!." sai kuma ta shiga girgiza kai tana fad'in "Mama kinsan me kike fad'a kuwa tayama hakan zata kasance, ina bazai yuwuba babu in da zani, wato ta nan ya b'ullo, wata kofar wulakanta Baba ke nan ya samo ko, to wlh bazai tab'a yuwuwa ba ni kam babu in da zani." ganin yanda ta birkice gaba d'aya tana kokari mike wa Mama ta ruko ta tana fad'in "Ke SEEDRAH ki nutsu ki saurare ni kiji, bijirewa hakan tamkar kuma rura wutar da akeson mutuwa fetur ne, a daren nan yazo yasami Baban ku da batun, ya ce yanason kije kirika yi masa aiki a gidan sa sannan kuma zai rika biyan albashi wan da acikin kud'in da yake bin Baban ku za a rika zarewa." hannunta Mama ta dad'a rikewa da kyau kana taci gaba "SEEDRAH mutuncin Baban ku da kike son karewa tanan ne zakibi domin dad'a kare masa mutunci da kimarsa, har idan kika bijirewa hakan tamkar kin dad'a bada kofar da Usman zaizo yarika ciwa Baban ku mutunci ne daga karshe kuma ya karb'e gidan nan, mu bazama yawon gidan haya haka zamuyi ta tsugune tashe, kisawa ranki neman kud'i zakije domin ki kare mutuncin mahaifinki, ai wannan wata kofa ce muma da muka samu ta in da zamuyi aiki a karkashin sa sannan kuma musamu mubiya wani abu daga cikin bashin da yake binmu, ko kin fi so yaci gaba da zuwa yana tozarta mahaifin kine iye SEEDRAH?." Tuni hawaye yashiga sauka a idanun ta. bakinciki da takaici sune suka sata zubda kwalla wai ita ce zata je gidan wani amatsayin 'yar aiki wanin ma S.MAN mutumin da tafi tsana a rayuwarta. Allah kad'ai yasan manufar sa na son ta kasance 'yar aikin gidan sa, tama rigada da tasan wani tozarcin yake shiryawa Baba. kai ta girgiza tace "Bazai yuwu ba bazan tab'a zuwa karkashin sa nayi aiki ba, ko da ace kuwa shi yafi kowa kud'i a duniya bazan je gidan sa a matsayin 'yar aiki ba, idan aiki kuke so nayi to dan Allah Mama ga gidajen masu kud'i da yawa ku turani can narikayi musu wanke-wanke da shara da wanki kai harma da girki, murika tara kud'in ana rage masa bashin sa." "SEEDRAH kina tunanin albashin da za a rika biyanki a wani gida dan kina wanke-wanke da shara zai bada wani kwakkwarar gudumawa ne wajen biyan bashin da Usman ke bin Baban ku, kinsan kuwa nawa yake binsa to ko albashin gwamnati kika fara karb'a sai kin b'ata tsawon lokaci mai nisa kafin yakai adadin kud'in da yake binsa, to amma tun da shi yace da kansa zai rika cirewa cikin kud'in da yake binsa shike nan wata kila wata rangwami ya yi niyyar yi masa,na samun saukin biyan bashin da yake binsa." Duk yan da Mama taso SEEDRAH ta amince sam taki, dan acewarta dataje tayi aiki a gidan S.MAN gara taje tayi sharan titi. kwana biyu a na abu guda, Baba Mama Umma kullum sai sun tasata gaba. su Halimatu kuwa cewa sukayi tun da taki amincewa su zasu je, musamman Suhaital da wutar kaunar S.MAN ke balbalar ta har kayan ta ta had'a ta ce zata tafi gidan nasa, Baba ne ya hanata dan bai mance da wacce S.Man d'in ya ce ita zata je aikin ba. a daren ranar kwana na biyun

Chapter 8 of 19