Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
data d'aura kayan brekfast. batare da ya kalli inda take ba ya ce "Tsayuwa kalle kalle kikazo yi ko aiki?, ai babu hutu cikin rayuwar ki acikin gidan nan, ko hutun sama da minti 10 bana kaunar naga kinyi sa a cikin gidan nan, wuce yanzu kije ki gyara min bedroom da bathroom sannan ki wanke min kayana ki goge." wucewa tayi cikin d'akin da ta ga yafito daga cikinsa batare da tace komai ba, duk yanda idanunta keta son janta izuwa kallon katafaren makwancin nasa zuciyarta kuwa yaki bada damar hakan. duk abin da yace tayi shi tayi kafin ta fito a d'akin. yana nan zaune in da ta barshi yagama yin brekfast d'in. tana kokarin barin parlour'n tajiyo muryarsa yana fad'in "Kin gama duka aikin?." kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta gyad'a masa kai. "Baki da baki ne? da bazaki amsa min da bakin ki ba." yafad'a yana jefinta da mugun kallo. "Idan haka ka d'auka to hakan ne, ka tambaya kuma na baka amsa ai ba sai na amsa da baki na ba, amsa magana da baki baya daga cikin jadawalin aikina, sannan kuma duk abin da ka lissafo na aikina na gama ko a kwai abin da ya yi saura ne." ta karashe maganar tana d'aga hanci sama cike da tsiwa. da d'an mamakin jin zata iya kuma tsayuwa gaban sa yana fad'a tana fad'a dan zaton sa gargad'insa na jiya daya shakota ya shige ta, sai yaga akasin haka. idanunta tarmazai take jera masa zance. afusace ya mike yana fad'in "Kin gama kike cewa kin wanke mota da zubawa fulawa ruwa da gyarashi." ta ce "Ban iya ba sai dai ka fad'o wasu aikin a madadin su." "Su zakiyi idan kuma ba haka ba zan kira Alhj Musa nan yazo ya yi,tun da ya iya cin bashi dole ya iya aiki ma." "Ka iya bakinka ka dai na jefin mahaifina da miyagun kalamai zan iya jure komai amma ban da cin mutunci wa mahaifina, ai bashi hanji ne yana cikin kowa, yafi karfin yazo ya yi aiki a karkashin ka tun ya haifa gani nan a gabanka yawuce tozarci." ta karashe maganar da murgud'a masa baki tare da binsa da kallon sama da kasa. batayi aune ba sai ganin sa tayi a gabanta, baiyi wata-wata ba yakai mata bugu a bakin ta da bayan hannu. da sauri ta dafe bakin cikin jin azabar zafi. ya ce "Fasa shi zanyi sai na fasa bakin ki aduk san da nake magana kina mayar min, wuce maza yanzu kije ki wanke motar sannan ki gyara fulawar ki zuba musu ruwa yanzun nan ko na kirawo sa yazo yayi!." Baya ta shiga ja yayin da ta d'ago hannuta data kai baki tana kallon d'an guntun jinin daya fito a gefen bakin ta. shiko komawa yayi ya zauna yana fad'in "Yanzu karfe 11 saura minti 25 mintuna 25 ne kad'ai suka rage miki, ki tabbatar da kin gama komai kafin cikar mintuna 25." Kuma duban d'an guntun jinin dake hannunta tayi kana ta dube sa sannan ta ce "Ba a haifowa katon gardi jaka ba wlh Allah ya'isa mugu wlh kasake kuskuran kai hannunka jikina sai kayi dana sani." a fusace ya mike ganin haka yasata zurawa da gudu tana had'a steps tasauka a guje tayi cikin d'aki ta murza key. a jikin kofar takasa kunnenta jin dai shiru bai biyo ta ba tabud'e kofar asulale tayi waje. Tsayuwa tayi a farfajiyar gidan tana karewa fulawowin da sukayiwa gidan kawanya kallo, wai su zata zubawa ruwa sannan ta gyara "To ma taya?." tayi wa kanta tambayar, ga kuma motoci can guda uku cikin parking lot wai duk ita zata had'a ta wanke su. kugu ta rike saita kalli motocin takuma kalli flaw's d'in. sai kuma a sannu tashiga takowa zuwa in da ta hangi tiyo da irin abin da ake rage tsawon fulawa da shi, ta d'au abin tashiga yanke kan flaw's d'in nan sai da ta kusa cire rabin na gurin, kana ta yi gaba shima sai da ta cire ganye jiki tas.. mai gadi dake zaune can bakin get yahango abin da take da gudu ya taho yana rabka uban salati da fad'in "La-la-la waya saki wannan aikin wace b'arna kike yi haka, kin san kuwa daga ina oga yataho da wannan fulawar? tun daga kasar turai ya taho da su, shine zakiyi musu aski irin haka waya fad'a miki haka akeyi." ta ce "Oho ba bashi ya ce a gyara ba." S.MAN dake sama yajiyo salatin da maigadi yake rabkawa ta windo ya leko ya hango su, ido ya waro kan b'arnar data tabka masa cikin d'aga murya ya ce "Ke!." maigadi yad'aga kai sama yana fad'in "Oga basai ma ka sauko ba amma dai tayi b'arna wanna ganyen turai d'in tasha tsinka yo ko kwad'o zakiyi da shi ai iya kaci." ganin ya rufe glaas d'in windon tasan saukowa zaiyi ai da gudu tayi ciki, tana shiga parlour shikuma yana step d'in farko na sama yana kokarin sauka. kafin ya sauko tuni tayi cikin d'aki ta murza key. kofar yashiga bubbugawa da karfi yana fad'in "Ki bud'e kofar nan!. ta ce " Wlh bazan bud'e ba bazan bud'e kayi min bugun uban wani ba, ni ba 'yar ka bace kajira ka haifa tukun ka buga." bugun kofar yake yana cigaba da fad'in "Na rantse idan kika shigo hanuna sai na ɓaɓɓalla ki na taraki anan." "Ai wlh baka isa ba zakaga gatana kuwa, aiki ka sani kuma nayi maka baka da bakin wata magana." naushin kofar yayi da kafa kana ya juya yabar jikin kofar. SEEDRAH ko ido ta zazzare dan ta gama zaton kofar ta b'alle dan ba naushin wasa yayi wa kofar ba. jin shiru bai kuma wata motsi ba sai ta koma bakin gado ta zauna tana mai da numfashi da fad'in "Haka kawai dukan da bazaka iya ramawa ba, ai wlh da baka fito bama da kaf saina yanke fulawan nan nazubar da su, ba aiki kace ba." (AFWAN NASAMI KORAFI GA WASUN KU SUN CE SU BASUSAN MEYE GARU BA KUMA DUK LITTATTAFAI NA DA KALMAR NAKE YAWAN AMFANI TO YA ZANYI TUN DA HAUSAN GARIN DA NAKE KENAN KUMA NA SABA AMMA ZANYI KOKARI ZAN RIKA RUBUTO MUKU IN DA ZAKU FAHIMTA. GARU BANGO KENAN KO KATANGA SHIMA DUK GARU NE KURIKE SUNAN DAN BAZANYI MUKU ALKAWARI A KODA YAUSHE ZAN RIKA SAKO MUKU BANGO BA KU DAI RIKE SUNAN SA GARU KAWAI DAN YA KAMA BAKI NA) Ranar SEEDRAH wasan b'uya tashiga yi da S.MAN ko ai ki take idan taji motsin sa saita gudu d'aki ta kulle kanta ciki a haka suka kwana. washegari kuwa data fito ta hango sa yana gurin motsa jiki, sai ta fasa gyaran parlour'n ta sulale tayi kichin sai da ta kulle kofar kichin d'in kafin ta soma aikin. ko da ta gama ta bud'e kofar a hankali ta leko kanta can ta kuma hango sa yana ta uban gudu bisa na'ura, cikin sand'a ta fito a hankali tahaura sama. tana aje kayan brekfast d'in ta shiga gyaran parlour'n da sauri-sauri tana kammalawa ta shige bedroom nan da nan tagama ta fito da sauri tanufi kofar da zata sauko kasa. wani irin wawan burki taja sakamakon ganin sa ya sako kai zai shigo. tad'an tsorata da had'uwar da batayi zato ba sai kuma ta wayence ta had'e fuska ta masa gefe ta bashi hanya dan ya wuce. hannuta ya cafko da karfi ya murd'e hannun. tasaki uban kara tare da fad'in "Wayyo Allah na wayyo hannuna ya karyamin hannu." takuma sakin wani kara jin yanda yake cigaba da murd'e hannun wane zai karya shi. ido ya zubawa fuskarta batare da ya saketa ba burin sa kawai yaga hawaye cikin idanunta, duk ihun da take d'in nan kuwa babu d'igon hawaye a idanunta. sulalewa kasa tayi yabita batare da ya saki hannun nata ba yasaka guiwansa d'aya a kasa yana mai cigaba da mud'e hannun nata. cike da jin azaba tafashe da kuka cikin muryar kuka da tuni hawaye yashiga zubowa idonta ta ce "Wayyo Allah na wayyo hannuna wayyo Mama ya b'allamin hannu, wlh idanka karya ni kaima sai an karya ka." sakin hannun nata yayi kana ya mike tsaye tare da karkad'e hannunsa ya dube ta da kyau kana ya ce "Da ma burina naga hawaye a cikin wad'an nan marasa kunyar idanun naki, duk san da kika kuma yi min b'arna acikin gidan nan sai na sauya miki kamanni." yajuya ya shige d'aki ya yafito rike da key d'in mota yafice ya bar gidan. da kyar ta iya mikewa ta sauko kasa, a parlour'n kasa ta zauna bata iya shiga d'aki ba tana tallafe da hanunta datake ji kamar baya amfani. tajima sosai zaune a gurin sai da taji hannun yad'an rage mata zugi kana ta mike ta shiga d'aki. kwanciya tayi a kan gado ta d'aura hannun kan pilo. wasu zafafan hawaye ne zuka zubo mata takai hannunta mai lafiyar ta share haushi da tsanar S.MAN cike fal cikin zuciyarta "Lallai wan nan zai iya kashe mutum dan babu imani atare da shi." tayi maganar a kasan ranta, tana nan kwance a haka har baccin wahala ya d'auke ta. Ko da S.MAN yafita gidansu ya je, suna zaune a parlour gaba d'aya hankalin Ummi na gare sa. ta d'an numfasa kana ta ce "Amma Usaman meyasa ka zab'i ajiye 'yar aiki a gidanka akan mata?, madadin kayi aure ka ajiye mata agidan sai ka d'auko wata 'yar aiki, duk da ita d'in 'yar uwar ka ce amma ai itama nan bada jimawa ba zata iya yin aurenta, shikenan sai dai karika d'auko 'yan aiki bazakayi aure ka ajiye mata cikin gidan ka ba." "Bana da lokacin ajiye mace yanzu duba da abun da nasa gaba, Ummi bazai yuwu ma nayi aure yanzu ba har sai na nutsu guri guda." "Usman harsai yaushe ke nan girmafa kake 'yan kwallo nawani suke da mata kuma suna tafiya ko wani kasashe, kayi aure zanfi samin kwanciyar hankali ni ma naga jikokina." "Allah yakawo lokaci." yafad'a yana mikewa, wai shi da baya da ko budurwa ma ake masa wani zancen aure, dan shi dai har yanzu baiga mace cikin matan da suke bibiyarsa ba. ya yi wa Ummi sallama ya tafi... SEEDRAH da bacci kamar kasa har wajen karfe 2 na rana bata farka ba. S.MAN da yanzu dawowan sa daga masallaci ya yada zangonsa a parlour'n kasa, ya zauna tsawon wasu 'yan mintuna yana daddana waya daga bisani ya aje wayar kana yakai hannu yashafi cikin sa daya fara jin yunwa. bin parlour'n yayi da ido baiga alamar wata kula na abinci a gurin ba, ya maida dubansa can kan dinning shima babu komai. d'an shiru yayi yana tuna tun zaman sa a nan baiji motsin ta ba ko a kichin ne, sai ya mike ya nufi kichin d'in ya leka baiga kowa ciki ba, babu kuma alamun an d'aura girki. juyawa yayi yanufi d'akin da take yatura kofar, can ya hangota kwance kan gado tana ta sharar baccin ta. daga bakin kofa in da yake tsaye ya ce "Ke bacci ne yakawo ki gidan nan wa kika ajiye da zai miki girkin." nauyin bacci irin na SEEDRAH batama san yana yi ba, shiko ganin kamar tana jinsa tayi burus da shi ne yacigaba da magana a hatsale amma har lokacin bata ko matsa ba. a hatsale ya tako bakin gadon yana cigaba da fad'in "Ke wai ni sa'an ki ne ina magana kina kwance zaki tashine kosai na sauya miki kamanni a nan!." yayi maganar cikin d'aga murya sosai kuma cikin tsawa. sai a lokacin tad'an motsa tare da yin mika ta juya kai tare da cigaba da baccin ta dan ita bata ma san yana yi ba. cikin matukar jin haushi yarasa ma me zai mata sai ya juya yaje in da fridge yake ya bud'e yaciro gorar ruwa mai sanyi har wani turiri yake tsabar sanyi, ya dawo bakin gadon kana yabud'e marfin gorar ya saiti dai-dai fuskarta yashiga tuttud'a mata ruwan. a gigice ta farka tare da kwalla kara ta mike zaune tana ware ido a kansa dan ba karamin firgita tayi ba. shiko ragowar ruwan yakarasa sheka mata a wuya ya gangara cikin kirjinta, kuma zabura tayi tamike ta saka guiwawinta saman katifa tana fad'in "Wayyo Allah sanyi me namaka Allah bazan yafe ba." ya ce "Idan da baki tashi ba d'aukar ki zanyi nasakaki cikin fridge d'in na kulle ki ciki, ke har kina da wani ikon yin bacci ne a gidan nan, idan na sake ganin ki kin kwanta kina bacci kamar mushe sai na sauya miki kamanni, tukun na ma ina abincin rana?." baki ta turo gaba tare da d'an murgud'a shi tana d'an jajjan rigarta da ruwan yasa ya lafe ajikinta sosai, har ana iya hango shatin bakin ababen jirjinta da bata saka musu bra ba, ga kuma wuyan rigar daya d'an zamo. ya ce "Zaki tashi kije ki d'aura girkin ne ko ya." baki takuma turowa tare da sakar masa karamar harara ta ce "To ka fita mana ba ka fad'a ba zan fito ai." tayi maganar tana janyo hijabinta dake kan gadon ta rufe jikin ta. tsaki yaja kana ya juya yafita yana fad'in "Ki b'ata lokaci ki gani." Sauka tayi a gadon tana jan tsaki da fad'in "Mugu azzalumi kuma Allah ya isa." bayi ta shige ta tub'e jikakkun kayan tayi wanka tare da d'auro al'wa ta fito, sai da ta gabatar da sallar azahar kana ta sauya wasu kayan sannan ta fito. yana zaune a parlour'n rike da sigari yana d'an zuka yayin da idanunsa ke kan t.v tazo zata wuce shi ta nufi kichin dai-dai lokacin da ya buso hayakin sigari ya ce "Sai kinyi ra ayi ne ma kafin ki fito, aduk b'ata lokacin da zakiyi a kan wani aiki acikin kud'in aikin ki dan ko wace karya doka sai anyi mata kud'i." kai ta kawar gefe tare da yamutsa fuska tana kore hayakin sigarin da hannunta kana ta toshe hanci da sauri tabar gurin. sai da ta shiga kichin kafin ta saki hancin ta tana sauke numfashi, a fili ta furta "D'an kwaya ma da ban yake." Ko da ta gama girkin ta d'ibo ta kawo masa sannan ta d'ibi na maigadi ta kai masa kana ta d'ibi wan da zataci tayi d'aki... Bayan kwana biyu SEEDRAH ce zaune cikin parlour bayan ta gama duk kanin ayyukan ta tana huta gajiya. wayarta ce tayi kara da jin sautin dake tashi na musamman wan da mutum d'ayane ke da wannan sautin, murmushi ta sake tare da d'aga kiran ta kara wayar a kunnen ta tare da yin sallama. a b'angaren Kamal kuwa numfashi mai sauti ya sake tare da amsa sallamar kana ya ce "Me yasa hakan?." ido ta d'an lumshe tare da bud'e su lokaci guda takai bayan ta jikin kujera tana mai dad'a manna wayar a kunnen ta sannan ta ce "Me ya faru?." ya ce "Gani a kofar gidan ku Mama ta ce min wai kina gidan yayan ku yau kwana nawa ma, amma shine babu ko labari ashe duk wayar da muke da ke ma kina can da ban zo ba da baza ma ki fad'a min ba kenan." to taya ma zatayi ta iya fad'a masa taje gidan wani aiki akan bashin da ake bin Baban ta, duk da tasan Kamal mutum ne mai fahimta amma ina bazata iya fad'a masa sirrin gidan su ba. ta ce "Ayya wai dama bamuyi magabar ba ai na d'auka na fad'a maka nazo gidan sa ayya na sha'afa ne to gaba d'aya, ayi min afwa." ya ce "Da nayi fushi amma yanzu na hakura." ta ce "To godiya nake." Nan suka shiga hirar su na kauna da soyayya cikin hirar yake tambayarta "Wai wani yayan ku ne ma?." ta ce "S.MAN yaron kanin Baba." ya ce "Oh S.MAN wannan d'an kwallon ko ai ina matukar son buga wasan sa dan wlh ya iya kwallo sosai dawowan sa ma daya ciyowa Nigeria kwallo ai damu akaje a ka cashe a hall." hab'a ta rike ta ce "Wai rawa kukayi?." dariya ya yi kana ya ce "Shagali ne kawai amma an d'anyi rawan ma, daga nan kuma mukaje muka buga kwallo saboda farin cikin kasarmu tayi gaba." "Wai dan Allah kaima kana wannan aikin wahalan ne." "Ke kwallon ne aikin wahala kinsan kwallo kuwa, to duk wanda kika gansa yana kwallo ki girmamashi daga yau ma ki kara girmama S.MAN fiye da da, dan shi d'in a can saman-sama yake babbane." baki ta tab'e a ranta ta ce "Ina abin girmamawa a tare da shi mutumin da baisan darajar mutane ba Allah ya sawaka." a fili kuwa dariya kawai tayi. maganarsa ta jiyo yana fad'in "Ashe ya yi aure ma amma dai auren sirri ya yi dan banji labarin ba ko a kafafen yad'a labarai, kai manyan nan fa yanzu sun dage da auren sirri babu mai sani zasuyi abunsu sululu su shige da matansu ciki, da gaskiyarsu su killace matansu ba suyi ta nunawa duniya tana gani ba, yafi ai suyi kishin kayansu, kai nimafa irin wannan auren zamuyi dan babu wani bikin da za'ayi daya wuce walima." d'an shiru tayi tana nazarin maganar tasa, wato shi tunani ya ke S.MAN d'in yana da mata, shi yasa ma tazo gidan nasa, to ma taya zatayi tace masa bashida mata kuma take zaune a gidan. maganar sa ta kuma sinkayowa ya na cigaba da fad'in "Ki gai da Aunty'n namu watarana zaki rako ni na gaida ta idan basu koma ba, amma dai yau zaki koma gida ko?." kai ta girgiza kamar yana ganin ta sai kuma ta ce "A'a ba yau ba." ta fad'a a takaice "Sai yaushe ko sai zasu koma tukun?." ta ce "Eh." ido ya waro ya ce "To gaskiya bazan iya jure rashin ganin kiba tun da bansan yaushe zasu tafi ba zan dai zo narika ganin ki a can d'in, kar kumafa su d'auke min ke sutafi min dake kasar turawan nan ace sai nayi kud'in jirgin d'auko ki." dariya tayi ta ce "Haba dai sai ka tara kud'in jirgi kenan." shima dariyar ya yi ya ce "Da gudu ma kuwa." jin karar bud'e kofar parlour tasan S.MAN ne ya shigo dan haka tayi saurin cewa Kamal bari tayi wanka anjima zasuyi waya. ya ce to. sukayi sallama ta sauke wayan dai-dai lokacin da yake karaso wa cikin parlour'n yad'an kalle ta tare da fad'in "Zan fita yanzu kije ki wanke min mota ki goge yanzun nan." ya wuce yafara haurawa step's, mikewa tsaye tayi sannan ta ce "Ban iya ba." sai da yakai karshen matattakalar sannan ya ce "Alhj Musa kam dole zai iya dan nasan bashi da kud'in da zai iya kai gura-guran motar sa gurin wanki sai dai idan fashi zai koma so dole shi yake wanke sa da kansa, bare kuma wad'an nan motoci masu tsada wankin su ai bazai bashi wuyaba shi zai zo ya wanke su yanzu." Cikin d'aga murya ta ce "Ya ishe ka ka dai na kokarin rika aibanta Babana dan uba baifi uba ba." cak yaja ya tsaya tare da juyowa kana ya maimaita kalmar "Uba baifi uba ba." tarar numafshin sa tayi da fad'in "Kwarai kuwa amma ka sani duk yanda kake son ka kaini bango bazan tab'a iya fad'ar mummunar kalma akan Abba ba, dan har gaba da abadan yana da kima da darajar uba agareni dan abun da ya yi Baba shi ya yi Abba, duk nasan darajar su ba kamar kai d'an kwaya d'an shaye-shaye ba." Wani irin waro idanu ya yi kan kace me idanun nasa sun sauya kamanni, b'acin rai fushi tafasar zuciya kake iya hangowa cikin su, ganin yan da ya d'aga kafa cike da KARSASHI tamkar zai duro daga saman matattakalar izuwa kasa. ai ko ta d'aga kafa dagudu kafin tace zata shiga d'aki ya iso ta ya samata kafa ta zube kasa. bin ta yayi kasan tare da shako wuyarta. wani irin tsoro ne ya baibayeta, idanunta tarufe da karfi dan ji take bazata iya bud'i idanunta a kansaba dan ya koma mata abin tsoro. cikin fusatacciyar murya mai nuni da zallar tafasar zuciya ya ce "Ni ni ne d'an kwaya d'an shaye-shaye a ina kika tab'a ganina da kwaya a ina kika gansu!." yayi maganar cikin tsawa tare zuba mata gigitaccen maruka biyu da sai da suka d'auke mata jin ta na wucen gadi, yashiga nuna ta da hannu yana fad'in "Zan sauya miki kamanni sai na b'allaki na taraki anan." ya angiza ta kanta yagaru da kasa, ya mike ya haye sama yana huci. fizgar numfashin ta tayi da kyar ta tattaro ragowar karfin ta ta mike zaune da kyar ta iya mikewa tsaye ta shige d'aki a bakin gado ta zube, sai a lokacin taji wani kuka yazo mata ta fashe da kukan tare da kife fuskarta jikin pilo tashiga rera kukan cike da kuna dad'acin rai. kamar an zabure ta tamike tsaye tare da share hawayen ta tafito da sauri ta shiga kichin. in da ta tab'a ganin soson waya taje ta d'auka ta fita ta dasauri ta nufi parking lot. gindin pampo dake gurin taje takunna ruwa cikin boket d'in data gani a gurin ta d'auko ta kawo sa kusa da motocin, sai da ta dubi mota mai kyan ciki kana ta d'ibi ruwa a kofi ta wasa masa wannan soson wayar data fito dashi tashiga dirza jikin motar da shi. ta dage sosai tarika dirzan motar nan gefe da gefen sa gaba d'aya ta goga soson wayar ta zazzana motar gaba d'aya tayi kaca-kaca da fentin motar. mikewa tayi tana haki tare da rike kugu, ta girgiza kai tare da ciza baki ta juya da sauri ta bargurin. tana shiga ta ganshi yasauko cikin sabuwar shiga da d'an sauri yake tafiya ga dukkan alamu dai fita zaiyi. bin ta da ido yayi ganin duk ta jike ya ce "Kin wanke motar ne ko ya?." ta ce "Ah sosai ma kuwa har na gama." tawuce da sauri ta shige d'aki, bin bayan ta yayi da kallo ganin yan da tayi saurin shiga bedroom, sai kuma ya juya yafice waje.. Tun kan ya karaso parking lot d'in yake hango motar kamar an shafa mata wani abu, da d'an sauri ya karaso gurin, wani irin waro ido yayi kan motar da yake ganin abin mamaki ajikin sa, hannusa ya d'aga ya naushi iska ya kai hannayen sa duka biyu yacusa cikin sumar kansa ya yamutsa. sai kuma yashiga kai koma a gurin yama rasa me zaiyi. sai kuma da sauri ya zaro wayar sa tare da lalub'o lambar Baba ya dannan masa kira Baba ya d'aga da sallama batare da ya amsa sallamar sa ba ya ce "Kud'in motata naira million 80 kazo ka had'a kabiya...........! Mommyn Twins ce 🌺 *ƘARSASHI!* 🌺 *NA* *RASHEEDAT S DIRECTOR* ( _Book 1_) ~Free page~ _Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko 08034690723_ *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* page 14 Da sauri Baba cikin matukar shiga tashin hankali ya ce "Wata motar kuma?." S.MAN ya ce "Motar da 'yarka ta la'anta shi yanzu kud'in motar na fad'a maka kazo yanzu ka biya ni." ya na gama fad'in haka ya kashe wayar sa. Baba kuwa cikin matukar tashin hankali yafito a bujajan ganin yan da yafito daga d'akin sa hankali tashe yasa su Mama tambayar sa abun da ke faruwa, bai iya tsayuwa basu amsa ba yayi waje yaja motar sa ya yi new G.R.A gidan S.MAN. S.MAN kuwa na kashe wayar yajuya da sauri sai huci yake yaje yarika bubbuga kofar SEEDRAH taki bud'ewa yarika buga kofar yana fad'in "Wlh yau sai na canza miki kamanni ki bud'e kofar nan." ta ce "Bani bud'iwa kuma ina mai tabbatar maka a duk san da ka sake kuskurin kai hannunka jikina da sunan duka ko shaka wlh karika yin na kud'in ka kenan, kad'an ma ka gani." naushin kofar yayi dakarfi har sai da ta ja da baya cikin matukar tsoro, dan gani take kofar ma ta b'alle. cikin fusatacciyar murya ya ce "Kin jawa wanjan tsohon." jin shiru bai kuma magana ba yasa ta komawa ta zauna jiki a d'an sanyaye dan tasan gurin Baba yanufa yanazu, Allah ne kad'ai yasan cin mutun cin da zai je ya yi masa. A b'angaren Baba kuwa cikin mintuna kalilan yakawo shi gidan S.MAN yayi hon maigadi ya bud'e masa get. yana faka motar da sauri ya fito, can yahangi S.MAN a gurin hutawan shi na musamman a cikin gidan wan da aka kawata shi tamkar a turai. yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun da suke zagaye da gurin ya d'aura kafarsa d'aya kan d'aya yana d'an girgiza kafar, sigari na rike a hannunsa yana sha, idanunsa kuma suna lumshe. da sauri Baba ya karaso in da yake yana fad'in "Usman ina motar take ina kuma ita SEEDRAH?." Baba yayi maganar cikin nuna tsantsar

Chapter 10 of 19