An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️1
Dandazon matasa ne ke cike tap a filin kwallon dake cikin wata makarantar kwana, hayaniyar mafiya yawa daga cikin dandazon matasan ne ke tashi suna faɗin
" *LOCKY* sai ka sha *LOCKY* sai ka sha!."
dai-dai lokacin wani matashi wan da a kalla shekarun sa bazasu wuce 19to20 years ba, cikin kwarewa haɗe karsashi, ya buga k'wallo tashi ga cikin raga.
wani irin ihu filin ya kaure da shi kan kace me y'an'uwan sa matasa da suke buga ƙwallon y'an team in sa suka d'aga shi sama suna ihun murna da faɗin.
"Locky Locky Locky!!."
cikin matukar farin ciki da tsantsar jin daɗi.
tuni filin ya kacame da hayaniya baka jin komai bakin mutane sai kalmar sunan Locky ke fita daga bakin su.
fuskar matashin da ake ta kira Locky sai fidda annuri yake ya na d'aga hannunsa sama wa muta ne.
har suka fito daga cikin filin kwallon duk in da ya gilma sai mutane sun mika masa hannu sun gaisa tare da yi masa kirari.
can gefe suka karasa shi da y'an team ɗin sa da sauri coch d'in su ya iso in da suke da murmushi d'auke a kan fuskarsa ya rungume Locky yana bubbuga kafad'ar sa cike da jinjinawa da yabawa hazaka da kokarin sa wan da a yau ya sha musu kwallo uku.
yana matukar alfahari da shi dan duk san da za'a buga wasa to kuwa tabbas cikin amincin Allah sai ya cimusu wasan da kyauta mai tsoka.
suna tsaye suna shan ruwa da huta gajiyar da suka kwaso, wani yaro dake kusa da Locky ya ciro wata kwaya daga cikin aljuhun wandonsa sai ya afa a bakin sa kana ya kora da ruwa.
sauran ragowar kwayar ya mikawa Locky yana faɗin
"Locky gashi ka kora." karb'ar kwayar yayi ya wasar da su kasa, ido yaron ya ware ya ce
"Zubarwa kayi na baka abin da gaba idan kacigaba da sha zaka ciyo mana kwallon duniya shine zaka zubar?."
bayan keyar sa ya sotso yace
"Anwar kana da damuwa bana yanayin da zan iya shan wad'an nan abubuwan."
kafad'a Anwar ya d'aga kana ya kunna sigarin da ya ciro yanzu ya kai bakin sa yana zuka,
Sagir dake gefen Anwar ya ce "Ai dai kasan wannan bazai tab'a shigo wa gari ba gara ma ka daina damin kanka."
baki Locky ya tab'e, kana
a sannu ya mika hannu ya zaro sigarin da Anwar ya kunna ya kai nashi bakin yashiga zukarta a hankali..
da mamaki Anwar ke kallon sa dan a sanin sa da shi ko sigarin baya sha,bare kuma kwaya, duk da yawancin abokan su suna huld'a da irin wad'an nan abubuwan, a cewar su wai yana kara musu kuzari wajen buga kwallo.
sai dai shi Locky sam baya shan komai, ko da sun nima da ya sha ma wai dan ya kara kwazo kan wanda yake da shi, sam baya sha.
sai gashi yau ya karb'i sigari da hannun sa yana sha.
dariya Anwar da Sager sukayi, Anwar ya ce
"Mutumin fa yafara shigowa gari."
hararar su Locky yayi
gaba ki d'aya lissafin sa da hankalin sa baya gun, da sauri-sairi yake zukar sigarin yayin da gaba d'aya lissafin sa yayi nisa...
Kamar daga sama yaga motar ta sharo kwana da mugun gudu,
daga bayan ta can wata mota na biye da ita, cikin hanzari yazare sigarin bakin sa yayi wurgi da shi, kana cikin azama ya nufi in da keken sa ke kafe, cikin sassarfa ya haye kan keken da iya karfin sa yake gudu kan keken ya rufawa motar baya, hanyar barin wajen gari motar ta nufa bai kuma fasa bin sa ba, sai dai a wannan karon ya sauka a kan titi gefen hanya yake bi wato ta kasa,
d'aya motar da take bin d'aya na gaban ne ya sauya hanya,
shiko bai fasa bin motar da ya sa a gaba ba,
har suka fice daga cikin gari suka fara shiga jeji, ta cikin bishiyoyi da ciyayi yake bi batare da ya bar wan da yake bi d'in ya gansa ba.
ganin motar tana kokarin gangara wa ta cikin daji, da sauri ya gangara da keken sa bayan wata katuwar bishiya ya b'oye a bayan bishiyar.
motar ta isa can kusa da wani kogon dutse wan da ya ke cikin motar ya fito da sauri ya buɗe bayan but d'in motar, yaciro wasu manyan ganamasgo guda biyar yarika kinkimar su yana kaisu cikin kogon dutse d'in nan yana saka su ciki.
sai da ya zuba su duka sannan ya juya yarika tsinko ciyayi yana rufe bakin kogon da shi har ya rufe shi gaba d'aya,
kana mutumin ya koma cikin motar da sauri yabar gurin.
numfashi Locky ya sauke daga in da yake b'oye yana ganin duk abin da yake yi...
Mutumin yabar gurin dakamar minti 10 Locky yafito daga gurin da yake b'oye, dai-dai lokacin sautin karar bindiga ke tashi,
ji kake tau-tau har sau biyu.
da sauri cikin azama ya haye kan keken sa ya nufi in da yake jiyo sautin harbin ke tashi.
tun daga can nesa yake hango motar mutumin da ya biyo sa a baya tsaye a tsakiyar titi, shi kuma mutumin yana yashe a tsakiyar titin cikin jini.
wasu mutane suna tsaye a kansa rike da bindigogi yayin da fuskokin su ke rufe da bakin kyalle.
cikin hanzari suka shige motar su suka bar gurin da mugun gudu.
ido ya kurawa motar nasu daga in da yake tabbas wannan itace motar daya gani tun da fari yake biye da motar mutumin.
da sauri ya kara gudun keken sa, kafin ya iso gurin tuni motar tabar gurin.
yana iso wa gurin cikin matukar tashin hankali ya diro daga kan keken,
yazube guiwowinsa gaban mutumin tare da d'aura hannayensa a kai yana salati, wasu hawaye ne masu matukar zafi suka shiga wanke fuskarsa.
da karfi yashiga jijjiga mutumin yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarsa.
wani irin mike wa yayi cikin azama, abun hannun dake daure a hannunsa mai d'auke da harafin(L) da babban harafi abun hannu ne na musamman wan da ake kera wa na musamman da kuma harafin da kake so a kera maka da shi a jiki. (L) yana nufin Locky kenan.
mab'allin jikin abun hannun
ya rike jikin rigar mutumin cikin matukar da muwa da tashin hankali, bai tsaya cire abun hannun nasa ba ya zare hannunsa abun hannun ya makale jikin rigar mutumin,
shiko Locky cikin zafin nama ya haye kan keken sa yabi bayan motar mutanen da sukayi kisan, da tuni sunyi nisa can nesa yake hango su.
gudu yake yi a kan keke da iya karfin sa,
duk da sunyi masa nisa sosai baisa yafasa binsu ba.
har sukayi nisa da gari sosai can suka sauka kan titi suka bi hanyar kasa,
tafiya sukayi me nisa har suka iso wani gida dake cikin jejin shi kad'ai a tsakiyar dajin.
har kuma lokacin Locky nabiye da su,
suka kashe motar suka fita dukansu suka shiga cikin gidan.
daga can nesa da gidan Locky yafito daga in da yab'oye, ganin sun tsaya gudun kada su ganshi.
cikin hanzari ya karaso gidan da suka shiga ta bayan gidan ya aje keken sa, a hankali cikin sand'a yashiga gidan, yana lab'ewa da tafiyar sand'a har ya shige cikin gidan.
Ta jikin windon wani d'aki dayaji magana ciki, ya make jikin windon tare da kasa kunnen sa.
wayar sa ya ciro daga cikin aljihu, yad'an d'ago hannunsa sama ta jikin windon yana d'aukar video'n su dakuma nad'an sautin maganarsu,
dai-dai lokacin da yaji a na fad'in
"Mun gama da shi yana can kwance mutacce, amma mun duba cikin motar sa sama da kasa babu kud'in nan ciki."
da karfi cikin karaji a ka ce
"Me yasa kuka kashe shi batare da kun karb'i kud'in ko sanin in da kud'in suke ba!, oh my god kun b'ata mana shiri, ai kin banza kukayi kun kashe shi bayan kuma baku karb'i kud'in ba,
ina kud'in yake matsiyaci a ina ka aje su, ka mutu banza bansan in da ka kaisu ba,
ku wasu irin marasa lissafi ne da zaku kashe shi batare da kun karb'i kud'in ba, ina ya kaisu to!!!."
ya karashe maganar cikin karaji sosai.
kamar daga sama muryar mai magabar yado ki kunnen Locky,cikin kad'uwa da jin muryar mai maganar ya d'ago tare da leka windon, idanunsa ya sauka kan mai maganar, yana tsaye sakiyar wad'an da sukayi kisan nan yana ta kaiwa da komowa yana cigaba da fadin
"Kun yi shirme da kafin ku kashe shi kun tirsasa shi ya fad'a muku in da kud'in yake tun da baya tare da shi, to ma ina yakai kud'in bayan dasu ya fita a mota!."
d'aya daga cikin makisan ya ce
"Abin da yasa muka kashe shi take batare da tunanin komai ba sabo da munsan da kud'in yake tafe,
bayan ya sheka kuma muka duba motar babu kud'in."
"Ku shiga gidan sa da daddare ku bincika ko ina ya shammace mu wata kila ya baro sa a gidan, ku tabbatar da kunzo min da kud'in, duk wan da yakawo muku gardama ku kashe shi."
su ka ce "To oga."
da sauri Locky yayi baya yana save din video d'in daya d'auka a wayar sa, ya jefa watar cikin aljihu cikin sand'a ya sulale ya fita a gidan...
keken sa ya haye cikin hanzari yabar gurin da mugun gudu, yayin da zuciyar sa ke wani irin tafarfasa.
daga can yarika jiyo jiniyar 'yan sanda,
mutane ya hango cike a kan mutumin da aka kashe, 'yanjaridu nata d'aukar hoton gawar, yayin da 'yan sanda keta faman korar mutane su samu sugudanar da aikin su.
jiki a santaye ya karaso gurin, yayin da yake jin gaba d'aya duniyar tayi masa zafi zuciyar sa kuwa naci gaba da wani irin tafarfasa.
wani d'an sanda ne ya sunkuya kan gawar yakai hannu ya ciro abun hannun dake makale a jikin wuyan rigar mutumin da aka kashen,
ido ya kurawa abun hannun yana jujjuya shi a hannunsa.
a fili ya furta "L. wane ne shi duk yan da akayi shi yayi wannan kisan!
babban abun hannu ne wan da ba a samun irin sa a kasuwa sai dai a kera maka shi, duk yanda akayi zai kuma kera wani irin sa."
wani irin bugawa kirjin Locky ya yi, cikin hanzari yayi baya da hannunsa wan da ke sanye da d'aya abun hannun irin wancan, wan da dama guda biyu ne a hannun sa d'ayan ne ya makale jikin rigar mutumin.
d'an sandan ya mikawa d'an uwan aikin sa abun hannun tare da fad'in.
"Daga kan wannan za'a fara bincike da wannan zamu sami nasarar kama shi."
suka d'au gawar suka saka cikin motar asibiti da yanzu ta iso gurin sannan suka yi gaba...
Locky yaja keken sa zuciyarsa a jagule ya nufi cikin makaranta wan da acan yake da zama cikin hostel,
yana isa direct d'akin su ya wuce wan da su hud'u ne ke kwana ciki, shi da abokansa Anwar Sagir da kuma Bashir.
yana shiga d'akin yashiga fatali da kayan cikin d'akin yayin da idanunsa suka kad'u sukayi jajir, sai huci yake,
d'aya abun hannun sa ya cire yajefa shi cikin jakar shi.
sai kuma cikin hanzari kamar wan da aka zabura yayi in da su Anwar suke ajiye kayan shaye-shayen su ya d'auki kwalaben da kwayoyin yarika afawa a bakin sa.
su Sagir ne suka turo kofa ganin halin da yake ciki da sauri suka iso in da yake, Bashir daya ruko sa yana fad'in
"Kai Locky an fad'a maka da haka ake fara shan kwayar so kake kwakwalwar ka ya tab'u?, muma da kaga muna sha ai ba irin wannnan shan muke masa ba,
ko munsha babu mai gane munsha wani abun sai dai kai da kake tare da mu, dan bama sha yanda zai fidda mu daga hayyacin mu,
sai dai kawai musha dan muji karfin jikin mu tare da nisha d'i."
Hannun sa ya fiske daga rukon da Bashir ya masa, yakuma kai wata kwayar bakin sa.
da sauri su ka shiga tattara magungunan su ganin da gasken sa yake narkawa cikin sa, kada ya kashe kansa ko ya haukata kansa a kamasu.
Zube wa yayi saman katifar sa tare da dafe kansa da hannayen sa biyu,
duk tambayar duniyar nan da su Anwar ke masa kan abin da ke damin sa dan sun hango damuwa sosai tare da shi, wan da yayi sana diyyar shan kwayar da yayi, amma yaki ce da su komai. suna cikin masa tambayoyin ma sukaga bacci yayi gaba da shi.
Sagir ya ce
"Anya bazamu d'auke shi mu kai shi
Pharmacy a duba shi ba kada fa kwakwalwar sa ya tab'u dan yasha kwayoyin nan da yawa."
"To amma taya zamuyi mu fita da shi idan a ka ganmu dole za'a tambayi abin da ya faru da shi kaga mu ma baza'a kyale mu ba."
Bashir ya fad'a cike da jin tsoron abin da zaije ya dawo.
Anwar ya ce "Kuma gaskiya haka ne mudai nemo wata hanyar."
haka sukayi ta sakawa da kwance wa sakanin su, shiko Locky yana ta kan sharara baccin sa...
Sai bayan sallar magriba ya farka kamar wanda aka zabura, Anwar ne kad'ai cikin d'akin su Bashir sun fita nima masa magani ganin baccin nasa yayi yawa, sun fara tsoron abin da suke zargi ne ya faru, wato ya haukace kokuma zai mutu.
da sauri Anwar ya taro shi ganin ya mike zunbur ya nufi kofa yana kokarin fita.
ya ce "Locky dakata dan Allah kada ka fita karufa mana asiri."
yana maganar ne cikin jin tsoro dan gani yake kamar haukan ce yayi zai fita ya gudu.
Locky da har lokacin idanunsa suna nan jajir kamar d'azu ya dube sa ya ce
"Bani hanya na wuce."
Anwar ya ce "Amma Locky kana cikin hankalin ka dai ko?."
wani mugun kallo ya watsa masa kana ya ce
"Kai ka haukatar da ni."
bangaje sa yayi yayi waje da sauri.
Anwar ya bud'e baki yana bin bayan sa da kallo ganin yana cikin hayyacin sa.
a haka su Bashir suka iso suka same sa tsaye bakin kofar,
suka ce ina Locky'n ya ce da su ya fita,
hankali tashe Sagir ya ce "Sai ka barshi ya fita yanzu kasan bolar da zamuje mu nemo shi?."
Anwar ya ce "Wlh lafiyar sa lau cikin hayyacin sa ya fita, nayi mamakin karfin kwakwalwa irin nashi."
gabaki d'ayan su suka rika jinjina karfin kwakwalwa irin na Locky, ace duk tulin tarin kwayar da yayi ta narkawa cikin sa a ce ya tashi tsaf batare da wani nakaso a tare da shi ba...
Shiko Locky yana fita keken sa yahau yanufi dajin da mutumin da aka kashe d'azu ya b'oye wasu ganamazgo cikin kogon dutse,
babu tsoro tare da shi duk da kuwa lokacin guri ya rufa yayi duhu,
a kan keken nan yarika kinkimar manyan jakukkunan nan da d'ad'd'aya yana fita da su daga cikin dajin ya canza musu wajen b'uya.
cikin sati guda ya nima wa kud'ad'en gurin ajiya na musamman wato banki bayan yayi wani cuku-cuku na musamman.
Bayan shekara shabakwai........!
Mommyn Twins ce
🌺 *ƘARSASHI!* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690734_
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿️2
Gidan cike yake da 'yan uwa da abokan arziki, sai tashin gud'a kake ji,
wasu 'yammata ne suka shigo cikin shiga irid'aya wato anko, da ka gansu basai an fad'a maka ba kasan kawayen amarya ne.
d'akin da amarya ke ciki suka shiga a gajiye wata kyakkyawar budurwa tazube kan gado tare da fad'in
"Wash Allah wlh nagaji."
hararar ta amaryar dake zaune can kuryar gado tayi ta ce
"Ke kam SEEDRAH kin ga ta kanki da son jiki, sai kace tafiyar kafa kika yi ba'a mota ba."
hararar ta Seedrah tayi tana kwanciya kan gado tare da fad'in
"Ke kam ai bazakiji gajiyar ba tun da gidan habibin ki muka kawo ki, Nasiba ke dan Allah baki gaji da jijjigar motar nan ba, da suke ta gudu da mutane kamar za'a tashi sama,
ni wlh addu'a na rinka yi ma dan na gama sadakar wa kifar da mu zasuyi."
dariya Nasiba dake zama kusa da Seedrah tayi ta ce
"Ai ango ne keta d'agawa direbobin hankali wai suyi sauri sai ka ce ance baza a kawo masa ita bane ko saurin me yake oho."
sauran kawayen ne sukayi dariya suka shiga zolayar amaryar, da yanda angon ta keta d'okin ayi a kawo masa ita...
'Yan uwa da abokan arziki da suka kawo amarya suka fara watsewa kasan cewar magriba ta gabato,ciki har da wasu daga cikin kawayen amarya.
ko da Seedrah da Nasiba suka mike dan su koma gidan iyayen su, amarya Nabila ta tare su har da yi musu kuka wai su bazasu tafi ba su kwana sai gobe.
ido Seedrah ta ware ta ce
"Mu kwana a ina ai sai angon ki yazo ya fidda mu a gidan nan da kansa, kinga kibar mu mu tafi ga hadari ya fara taso wa kada ruwa ya tare mu a nan."
Nabila ta marairai ce fuska ta ce "Yau she zaku sami abin hawa daga nan zuwa unguwar rimi yanzu dare yayi dan Allah ku bari gobe da safe sai ku tafi."
fir suka ki suka ce su tafiya zasuyi, dataga dai fa bazasu kwanan ba sai ta ce
to su bari idan Kabir ya shigo sai ya mai da su gida a mota.
da haka dai suka zauna har wajen bayan sallar isha, kafin Kabir ya shigo,
lokacin har yayyafi yafara sauka.
ko da ganin yayyafi ya fara Kabir ya ce musu su kwana gobe sai ya maida su gida, badun sun so ba suka hakura.
Suna zaune a parlour ganin yan da Kabir ke ta bin amaryar sa da kallon kasa-kasa yasa sukaji duk sun takura su, sun san cewa a yanzu yana matukar matar sa.
Kabir ya mike ya shiga bedroom yana fad'in bari ya d'an wasa ruwa,
yana shige wa ciki Seedrah ta dubi Nabila ta ce
"Je ki kula da mijin ki, Nasiba taso muje ki rakani gidan goggo na can kasan layin nan, bari muje mu dawo."
tayi maganar tana mike wa Nasiba ma ta mike.
Nabila ta dube su tana fad'in
"A ruwan nan zaku fita ku bari gari yawaye mana."
"Yayyafi dai yanzu zamuje mu dawo."
cewar Seedrah tana janyo hannun Nasiba,
Nabila ta ce "To ku aje jakan ku da wayoyin ku, ai na gane so kuke ku gudu, daga nan har in da zaku titi ne ga hasken wutan nepa da farin wata, Allah nifa tsoro nake ji."
dariya Seedrah da Nasiba sukayi ganin tsoro fal tare da kawar tasu.
Nasiba ta ce
"To meye abin tsoro gaki ga mijin ki."
duka ta kai mata a kafad'a tana fad'in
"Ai shine abin tsoron."
dariya sukayi ta mata suna zolayar ta da fad'in
tayi jarumta dai, sukayi waje.
Suna fita basuyi nisa ba ruwa ya fara karuwa,
Seedrah dake gyara gyalen kanta daya jike ta ce
"Kaji ruwan nan kamar jira yake mu fito ai kuwa zamuyi wanka, Allah ya so mu bamu fito da wayoyin mu ba da sun jike."
Nasiba ta ce "Wai dagaske dawowo gidan nata zamuyi?."
kai Seedrah ta girgiza ta ce
"Haba dai amaryar yau me zai kaimu kwana gidan ta nafad'a ne kawai dan ta barmu mu tafi, can gidan goggona zamu kwana gobe madawo mu d'auki jaka da wayoyin mu, dan nasan dama ba bari zatayi mu tafi da shi ba."
Sunyi tafiya mai d'an nisa yayin da ruwan ke cigaba da karuwa, kamar yanda Seedrah ta fad'a kuwa suna tafiya ne cikin saib'i ruwan yana musu wanka.
hannu SEEDRAH takai cikin rigar ta karkashin bra d'in ta tana sosawa, ta ce
"Wayyo kaikayi Nasiba zo ki cire min bra d'in narike shi a hannu wlh kaikayi yake min a jiki tun san da ruwan nan yafara jika mu, gashi sai karuwa yake."
gefen wani shago ta tsaya,
babu kowa a gun shagon sakamakon ruwan sama da akeyi, kuma wan da ke bakin titi bazaigan su ba dan gurin babu haske sai dai idan yazo kofar shagon da suke gefen sa tad'an baya kad'an.
ta na cigaba da fad'in
"Yi sauri ki cire min wayyo Allah kamar wanda a ka zuba min karara a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 19