biyar din Bayan ya maka min harara ya fice, Ina ganin lokacin da bakin shi ya motsa yace
"Shegiya kurbusu kawai!"
Naji wani Abu ya Dakar min zuciya ta, Amma ban kula shi ba kamar yadda kuka sani, se ma Zama da nayi na karba wayar Mamaa na Fara Kiran mutumin, aikuwa ya dauka na bashi hakuri sannan na bashi address din.
Wannan tsayawa da Mamaa tayi min, yayi min dadi cikin rayuwa ta ya Kuma bani karfin gwiwar yin Hira da ita, na Kan fada Mata labarin fitar da nayi idan har na fita, hakan ya rage min yawan kadaicewar da nake Yi, Amma har yanzun ban daina kin shiga mutane ba, ban Kuma daina jin yadda zanyi na rage kibar jiki na ba. Ana Haka aka Fara bada admission, cikin hukuncin Allah na fito cikin Wanda Suka samu gurbin karatu cikin BUK, Architecture din da na cike shi din aka bani, farin ciki ranar kowa a gida se da ya fahimci hakan, naje na fadawa Adda bayan ta dawo daga office, tayi murmushi tace
" Bintu kin tabbatar Zaki iya kuwa? Kinga University da secondary ba daya bane ba. Nasan Dan kin Dan samu luck kin ci exams shiyasa kike ganin kamar architecture din Wasa ne bko?"
Adda ba zata daina muzanta ni Akan da ban kasance me kokari ba, Amma ni dai nasan yanzun kowanne course aka bani bana tunanin Zan Fadi, Dan kuwa I'm determined sosae da sosae! Duk jiki na yayi sanyi, saboda akwai abin da nayi lacking a rayuwa ta, toshe kunne na daga abin da mutane ke fada, ko Kuma kada na bar maganar su ta dame ni tunda mutane ba a iya musu, Amma bana iya hakan ko nayi niyyar hakan se na gagara, shiyasa Abu kadan zaa fada se ya tayar min da hanklai na, yaci ace zuwa yanzun na sike na Kuma Dake Amma ko kadan bana iya hakan.
Kawu ya bani duk kudin da ake bukata na Yi registration da komai, da farko nace Ni hostel Zan zauna Amma Kuma se na fasa tuna cewar yanzun hostel din akwai mutane da dama a cikin shi, Kuma zaa din ga criticizing di na anyhow Wanda ba Zan iya jurewa ba, ba Kuma Zan iya bada amsa ba, se kawai na yadda na bari akan na dinga day, dukda Nisan Dake tsakanin mu. Na Fara karatu cikin hukuncin Allah, da farko it was hard to adjust Amma dana Yi wata daya se na Fara daidaita yanayi na. Bana iya fitowa daga aji duk lokacin da Naga mutane sun yawaita, bana shiga harkar kowa saboda gani nake kowa kallo na yake Yi Kuma babu Wanda zai so yin kawa dani. Ko da nazo da wuri to can baya nake zama Abu na, kullum fuska ta dauke da mask, sannan kayan jiki na ma kadai Kara min kiba suke. Idan Babu kowa a class to Zan saka earpiece kunne na Dan kada ma naji wani Abu da zai Bata min Rai na. Ranar Ina zaune Babu kowa cikin aji, Ina nufin lecturer, se mu kadai suna ta hayaniya, nayi shiru Ina rufe idanu na cikin tunanin duniya, se naji an taba ni, nayi firgigit na bude idanuna, wata Mata ce zatayi wajen shekaru ashirin da biyar zuwa sama, ta zauna kusa dani tana fadin
" Sannu baiwar Allah!"
Nace
"Yawwa!"
Se tace min
"Ina kike Kai Babyn ki raino kuwa?"
Se naji wani banbarakwai wani namiji da suna...nace
" Bani da Baby, banyi aure ba"
Kunsan wasu ba suda hankali ko kadan, instead ta tashi ta tafi se cewa tayi
" Ke din? Tabdi me Kika tsaya Yi har yanzun bakiyi aure ba?"
Nayi Mata banza ban Bata amsa ba, maimakon ta tafi se ta dauki ID card dina na school Dake makale jikin lanyard, a jiki akwai date of birth, a take tayi wani exclamation
" Ke din ce shekarar ki Sha shida? Tabdi kina da girman jiki wannan ai we can mistaken you for someone of fourty years!!!"
Kunsan menene? gaba daya idan kuka duba harshe bana tunanin anatomically akwai inda Kashi ya tokare shi, shi din tsoka ce amma Kuma tafi mashi kaifi, harshe masifa ne saboda shi yake magana, akwai lokutan da yawa da connection din da harshe ke dashi da kwakwalwa yakan tsinke, harshe ya ta fadan abin da Bai kamata ba. Kunga wannan abin da ta fada min, Wai nayi Kama da Yar shekara arbain se naji gaba daya zaman ajin ya gundure ni, tana ta surutu na Mike tare da daukar jaka ta na fita, Ina tafe Ina ayyana how old am I looking? Shiyasa Ashe idan naje submitting Abu se Naga ana cemin Hajiya? Hawaye ya Shiga sakko min, ta Yaya ma zaa hada budurwa Yar shekara Sha shida da shekara arbain? Wannan cin mutunci bashi da na biyu. Na karasa gida na cigaba da tsayuwa gaban mirror din dakin mu, na kalla fuskata, bani da kibar fuska in fact hallitar fuska ta irin ta Yara ce, idan ka dauke Baki da kurajen ta bana tunanin akwai wani abun assha a fuskar, na duba jiki na, a take na Fara kuka Ina ganin nayi kiba da yawa, a ranar se Naga kibar tafi ta kouaushe fitowa ma...
Ta_kwalam ce
BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free! Contact the writers to make payment.
[1/3, 20:28] Maman: 022
Lokuta da dama na kanyi mamakin me yasa bakin mutane baya shiru? Me yasa suke Jin dole se sun Yi magana akan abin da bai shafe su ba, ni dai nasan ance idan zaayi magana a dinga taunawa kafin a fito da ita, saboda wani lokacin baka San how powerful your words are. Akwai wata Pakistan woman wadda ta kasance motivational speaker, muniba mazari ta taba wani video da na taba kalla take cewa
" Be careful with your words, because words are so powerful that they can break you, deform you and destroy you..."
Ma'ana tace kowa yayi hankali da kalaman shi saboda ita magana tana da karfin da zata iya kassara mutum. To kunga idan Haka ne ya kamata mu kasance Muna tantance abin da bakin mu zai furta.
Bayan abinn da ya faru a class na fito na nufo gida, ba tare da na jira next lectures ba, nasan Hali na ko da ace na zauna to bazan iya Kara concentrating ba. Na shigo gida jiki na a matukar sanyaye, parlon Mamaa na Fara shiga Dan sanar Mata dawowa ta, Amma se na same ta ita da Suleiman a zaune, yanayin su dukka ya nuna they're in a serious conversation. Na dube ta na gaishe ta har Shi din ma sannan nace Mata na dawo, ta dube ni closely kamar wadda ke son fahimtar wani abu, na juya da sauri Ina fadin
" Kai na na ciwo Bari naje daki!"
Kafin ta bani amsa na wuce daki tare da yin sallama dukda bana tunanin Zan samu wani cikin dakin, tun da Batuul Kam tana makaranta, Ina shiga na karasa gaban dressing mirror na tsaya, kamar yadda na Saba a kullum kullum. Na juya na sake juyawa sannan na zauna Ina karewa fuskata kallo, idanu na suna cikowa da kwalla ta Ina ne nayi Kama da mutane masu shekara arbain, duk yadda nake ganin munin Kai na Amma nasan wannan abun is just a hearsay, Amma Kuma na kasa sakawa zuciya ta kada hakan ya dame ni. Ina nan zaune se naji sallamar Mamaa, na dago Ina kallon ta Bayan na amsa, ta zauna saman gadon tana bin gadon da kallo yadda na baza handouts anma fuskata da Kuma damuwar da take ciki ya tabbatar Mata ba karatun nake ba, kawai dai Ina zaune ne ina tunanin abubuwan da Bai kamata ace nayi dwelling akai ba.
" Wani abun ya faru a makaranta ne?"
Nayi saurin giegia Kai na nace
" Ba komai!"
Tayi murmushi tace
" BINTU fada min me ya faru? Wani yace Miki wani abunne?"
Se kawai hawaye Suka shammace ni Suka Fara tsirtuwa akan kunci na, wannan kadai da nayi se ya sake tabbatar mata akwai wani abun. Cikin kukan da nake son dakewa bana Kuma San Yi na Fara tambayar ta
" Mamaa ki kalle ni, ki kalli fuskata Wai tana kama da ta Yan shekara araba'in?"
Mamaa dariya ce kawai batai ba saboda Bata son ta Kara Bata mood din, tace
" Kuma kin yadda Bintu? Duk yadda kike kallon madubi Baki taba lura ke din daban Allah ya hallitta ba? Har yaushe ma Bintu Zaki dinga barin maganar mutane na.shiga kunnen ki, Kinga ko ramewa kikai mutane se sun Yi magana. In dai kina son zaman lafiya, to abin da ya kamata ki toshe kunnen ki daga zantukan mutane"
Inama Zan iya toshe kunnuwan nawa, inama Zan iya ji na share Amma ba Zan iya ba, bani da wannan karfin zuciyar. Idan da ace Ina Jin nasihar ta da tuni na wuce bacin Rai, Amma bana iya yin abin da take cewa. Wannan dalilin yasa na kusa kwana biyu ban je school ba, Ina gida Abu na, Mamaa ma bata kula ni ba balle taji dalilin da ya hanani zuwa, balle Adda da Kawu kuma da Suka koma nuna halin ko in kula a kaina.
Wani yammaci na dawo daga school, a matukar gajiye nake, Bayan abin da ya faru sosae nayi kokarin ganin na sake rage cudanya ta da mutane. A kofar gida na hadu da Suleiman shi da wani abokin shi suna tsaye, ni kunsan ba wani shiri muke ba sosae, so briefly na gaishe su, Suleiman ya amsa Yana fadin
"BINTUN BATUUL!"
Na juyo ba tare da nace komai ba, yace
" Do me a favor, ki turo Mana Batuul please!"
Na gyada Kai na, Ina wucewa abokin yace
" Ga ga Yar Duma Duma Naz!"
Naz da yayi folding hannun shi tun da nazo yake kallo na yace Yana Yar dariya
"Wannan rindinar itama gidan take?"
Suleiman ya kwashe da dariya Yana maimaita rindinar da Naz yace, wani Abu me zafin gaske ya tsaya min a makogaro na, idanuna suka cika da kwalla Amma se nayi kokarin maida su na wuce ciki, straight daki na wuce na samu Batuul tana gyara zaman cajin sabuwar wayar ta. Na zauna Kan gado na Ina sakawa a Rai na akan ba Zan fada Mata sakon shi ba tun da ya Raina min hanklai. Amma se Naga to meye a ciki? Where's the lie? Ai ba Karya yayi ba da yace ni rindina ce.
" Batuul Suleiman na Kiran ki!"
Ta wani kalle ni wani irin, kafin ta tura Baki tare da fadin
" Wallahi ba inda Zan je, Dan rainin hankali"
Zakuyi tunanin Zan tambaye ta abin da ya faru ko? Tabdi ko uffan ban ce ba na cigaba da fito da books di na daga cikin jakar da na fita da ita, se Jin karar buga kudi da akeyi, na dago idanuna Ina kallon Batuul da ta gama rufe kofa Kuma take bubbuga wrapper new N500 notes tana stretching din su. Ta aje gefen gadon sannan ta zaro ta N200 notes mint din su ta hada su waje guda tana taunar gum, mamaki sosae ya Kama ni inda Batuul ta samu wannan uban kudin, Amma dai se bance Mata komai ba kawai na wuce toilet. Ko Dana fito ta Kara dakko wasu sabbi dal na N1000 mints da Kuma wata N500 din. Na tada sallah har na idar Bata kwashe ba, na mike Ina fadin
" Batuul ajiya aka baki"
Tayi murmushi tana adana su cikin jerin kayan ta Dake wardrobe tace
" Ko daya, nawa ne!"
"Naki?!"
Na tambaya Ina sake yin kasa da muray ta kada wani ya jiyo abin da muke fada, tayi dariya tace
" Shiyasa na yanke hukuncin ba Zan aura Suleiman ba"
"Batuul!"
"Bintu"
Itama ta amsa min da same murya da Kuma yanayin maganar da na yi,
" Ba Zan aure shi ba da gaske, shiyasa nake fada Miki kudi a gaban komai suke, har yanzun Suleiman wani matsiyacin aikin banki yake, Ina Zan iya? Mutumin da a probation yake, ko yaushe idan baiyi meeting requirements ba kora ce!"
Na zauna dabas akan gado, na manta order akai ta 12pcs meat bread Baki daya, Kuma tashin da nayi niyya ta na wuce kitchen na Fara aikin. Amma wannan maganar ta Batuul ta girgiza ni.
"Batuul Suleiman din? Akan kudi Zaki guje shi ? Tun kafin ki San kanki yake kula da ke Amma sakayyar kenan?"
Ta zauna gefe na tace
" Bintu, Baki waye ba. Kilan Baki da saurayi ma har yanzun. Kada ki damu Zan bar Miki Suleiman din se ki daura daga inda na tsaya!"
Ayi hakuri a Kuma Kara hakuri, Dan Allah I'm sorry for ghosting, for typing little. I've a strong reason, I hope you can pray for me and understand me.
[1/3, 20:28] Maman: 024
Shiru shiru akace Wai malam yaci shirwa, Imam nata Kira yaga ta inda ciki zai bullo daga jikin zainab Amma babu amo balle labari, Babu ciki Babu dalilin shi, itama tana ta saka ran zata Yi conceiving Amma shiru kake ji. Dukda hakan suna rayuwar su cikin aminci da alkhairi, suna zaman su cikin soyayya da kauna. Anan Imam ya kammalla karatun shi, ya Fara tunanin tafiya Nigeria, sede Allah is always the kindest, se Alhaji Gidado ya dakatar da shi da fada Masa akwai course akan administration da Kuma planning, Budget and implementation da yake son jikan na shi ya koya, saboda big plan da yake da shi ga rayuwar Imam din. Fatin ciki ba ga zainab ba Kuma ga Imam ba. Shekara daya ta Kara zuwa ta wuce, wannan lokacin tuni zainab ta kammalla makarantar ta, shima shekara ya rage, tare suka he Qatar aka zagaya da shi dangin ta. Ya gansu Suka gan shi sukai kwanaki sannan Suka koma inda suka fito, tunda Suka dawo Imam ya Zama wani irin mutum da zainab ta kasa gane Kan shi gaba daya. Wani yammaci ya dawo daga lecture a gajiye, ga Kuma yawan tunani da yake yi duk yabi ya rame. Bayan ta yi Masa serving wani local dish din su na kasar su ya zauna ya Fara ci cikin kwanciyar hanklai, tana ninke inners din shi tana Kuma karantar yanayin shi. Se da ya Gama ya Mike Dan Kai kwanon kitchen kamar yadda ya Saba, in dai yaci abinci to da Kan shi zai Kai kitchen ya wanke, to ka'idar shi ma idan ta tashi kafin ya tafi lecture zai tabbatar yayi Mata wanke wanke, idan ya dawo har girki yake mata. Yana dauraye hannun Shi Bayan ya kammalla wanke plates biyu da Kuma sauce pan da ya gani a cikin sink din. Bayan ya kammalla ya juyo se ganin ta yayi a tsaye ta kura masa idanun ta masu kaifi tana kallon shi. Ya Sha jinin jikin shi tare da matsowa inda take Yana dan sunnar da Kai yace
" Solace what's up?"
Ya fada Yana daga Mata hannu, maimakon ta mayar Masa murmushin da yake Mata se kawai ta ja hannun shi zuwa Kan sofa, bayan sun zauna yace
" Solace menene?"
Tace
" Kai Zan tambaya, ka fada min menene yake damun ka?"
Ya dauke Kan shi yace
" Ba komai, na gaji ne"
Ta Bata fuska saboda da gaske tasan akwai abin da yake damun shi, akwai abinda ya saka a ran shi yake Kuma damun shi, Kuma kowacce irin rantsuwa zaiyi Mata ba zata yarda cewar Wai Babu abin da yake damun shi ba. Yadda tayi da fuska ta Kuma sunkuyar da kanta tana fidgeting fingers din ta yasa shi fadin
" Solace menene?"
Tace cikin murya me rauni
" Ka gaji da ni saboda ban haihu ba ko? Saboda har yanzun..."
Yayi saurin rike ta wan da yasa maganar tata komawa cikin ta, idanun shi yayi jawur kamar zaiyi kuka, it's pains him so much idan yaji tana maganar haihuwar da Bata samu ba, saboda yasan ko menene ya faru to shi ne sanadi, duk wani Abu da akai yasan laifin shi ne. Ya gyara zaman shi Yana fadin
" That will never be solace, ba Zan taba juy miki baya ba saboda Baki haihu ba, bazan tana ba, I assure you"
Ta Fara kokarin bambare jikin ta da nashi, Amma se ya hanata se kawai ta kwantar da Kan nata tace
" Then tell me, me yake damun ka? Wani Abu ya faru a Qatar ne? Naga tunda muka dawo you've not been yourself!"
Yayi shiru ya kasa Yi Mata magana, Amma kuma dole zai fada Mata makomar su Dan abunnan ko yace maganar nan sooner or later zata fito. Ya danyi shiru sannan yace
" Solace Ina son Miki bayani Akan family di na"
Tace
" What about them! Ba zasuyi accepting di na ba?"
Ta tambaya har zuciyar ta tana Jin Babu dadi hade da tsoro Yana kamata, ya rike hannun ta Yana zana Mata soothing circles a jiki Dan ya Dan kwantar Mata da hankali. Bayan sun yaga alamar ta Dan daidaita ya Fara fada Mata
" Family na basu yadda su karba wani ta auratayya other than mu aura na dangi. Se yanzun nake Jin tsoron yadda Zan Yi na kaiki wajen su"
Tayi shiru tana assimilating abubuwan da ya fada, dama tana tunanin hakan saboda a shekaru uku zuwa hudu da sukai aure ko da mutum daya daga dangin shi Bata taba magana da shi ba, ko da ta tambaya zai Nemo wani excuse din Dan ya Kare Kan shi. Amma se ta dauka ai Babu komai tunda sun ruga da sunyi aure.
"To me yasa ka aure ni in the first place? Me yasa?"
Ya Kara matse ta a jikin shi yace
" Saboda Ina son ki, saboda bana son losing din ki"
"Then what if your family refuse to accept me? Ya zakai?"
Yace cikin narkar da murya har se da tsikar jikin ta ta tashi yace
"Shiyasa na aure ki, ko ba komai idan muka je nasan ba zasu raba mu ba"
Ta Fara kuka a hankali me cin Rai Amma ta kasa fadar komai, gaba daya hankalin shi yayi masifar tashi, ya dinga lallashin ta with all the sweetest words da yasan zai iya sakawa tayi shiru Amma abun mamaki se hakan ta gagara, ta dauki lokaci sosae tana kuka sannan tayi shiru, Amma taki tace komai se ajiyar zuciya da take saukewa. Shima se ya Dan kyaleta amma duk da Haka ya kasa zuwa ko Ina duk kuwa da Kiran dasu Charles suke masa. Har ya dawo daga sallar maghrib Bata canja yanayi ba, tana zaune ta idar da sallah Amma kuka take tana Jin tausayin rayuwar ta, tana ganin watan lalacewar rayuwar ta ya tsaya, ita ba wani ta sani ba, all these years Imam ya kasance uwa da uba a gare ta, aboki da Kuma kawa, Babu wani wanda take kulawa ko ta saki jiki da shi idan ba Imam ba, hatta acan Qatar din jadda ce kawai, bayan jadda Kuma Bata da wasu shakikan Yan uwa makusanta. To ya Kuma ba zata tada hankalin ta ba, Bayan tasan rabuwar ta da Imam kamar rugujewar rayuwar ta ne!
"Solace! Dan girman Allah, Dan Allah ki daina kuka kiyi hakuri, I promise you zanyi duk yadda zanyi Naga na tsaya Miki, ke kanki kinsan Zan iya ja da kowa akan ki ko?"
Ta gyada kai tana rungume shi, Haka dai yayi ta bata Baki kafin kuma suka fita Dan Yana son iskar Dake kadawa ta tafiyar Mata da dukkan wani kunci Dake ranta. Idan Kuna Jin ana zancen Sharukh a soyayya, Romeo a fagen kauna to I assure you (inji Baba buhari 🤣) to Imam ne. Cikin darennan he made sure ya goge kaso me yawa na daga cikin abin da take ji akan wannan maganar da sukai. A kwana biyu se da ya tabbatar Mata shi din ba wani ba zai iya protecting din ta tare da yin fito na fito koma da waye.
Kwanci tashi asarar me rai, se gashi har lokacin kammalla course din Imam yayi, Kuma ko suna so ko basa so dole ne su koma gida, a lokacin kullum adduar shi Allah ya daura shi akan Alhaji Gidado, ya Fara shiga tashin hankali duk da kokarin boyewa da yakeyi Dan kada zainab ta fahimta, Amma ita dinma anata bangaren abin da ke faruwa da itan kenan, tsoro ne da tashin hankali fal zuciyar ta, yayin da yake bawa Alhaji Gidado benefits of doubt kamar yadda itama take bashi wato shi Imam din. Zuciyar shi nada yakinin Allah will do the miracle ita Kuma ta sakawa zuciyar ta cewar kome zai faru Imam ba zai rabu da ita ba. Da wannan tunanin Suka baro kasar masu jajayen kunnuwa zuwa gida Nigeria. A Abuja Suka sauka kafin washegari Suka sake bin wani flight din zuwa Kano, sede a wani irin tsorace yake shi Imam, hakan har ya fito zainab ta gani se itama ta Kara rikicewa, karshe ta shawarce shi Akan yayi Mata booking hotel yaje ya sanar da iyayen shi a gida, idan komai yayi daidai yazo su tafi. Se yaji kamar tayi Masa bushara da aljanna, farin cikin shi ya fadada yaji Babu yadda zaayi ya daina son ta a cikin rayuwar shi. Saukar su ke da wuya ya kammalla dukkan abin da zaiyi, Yana fitowa ya hango Malam magaji, yayi saurin janyo baseball cap din shi Dan yayi disguising Kan shi, shi yasan Alhaji Gidado dole se ya turo a tafi dashi musamman matsayin shi na shalele. Haka suka tare taxi Suka tafi, se da ya Kai ta har hotel yayi Mata booking daki under his name kafin ya jira tayi settling, tana zaune tana kallon shi da idanun ta da suke nuna rauni, ya dawo kusa da ita tare da rungume ta a jikin shi yace
" I assure you! I'll do everything in my power Naga ban rabu da ke ba, zainab ki sani kece farin cikin rayuwa ta, Babu wani wanda zai raba ni dake sede wani Abu daga Allah!"
Wannan maganar ta saka zuciyar ta dan haskawa, ta sassauta rungumar da tayi masa tace
" Don't abandon me please Chum Chum, kasan Kai kadai nake da shi ko?"
Ya gyada Kan shi tare da pecking goshin ta sannan ya fita jiki a mace. Wucewa yayi straight gida ba tare da ya koma airport ba wajen Malam magaji. Tun da yaje kofar gidan yaga gaban shi Yana mugun faduwa saboda taron mutane da ya gani!
What's happening?!
Ta_kwalam ce!
[1/3, 20:28] Maman: 025
Kowanne taro a yanayin fuskokin mutane ake gane na farin ciki ne ko kuwa akasin hakan, yanayin zirga zirga da Kuma walwalar jama'ar wajen yasa yaji hanklain shi yayi matukar kwanciya, yasan tabbas abun farin ciki ne ya faru, Kuma kafin yayi wani yunkurin wucewa se gani yayi ana fitowa da manyan silver tray shake da shinkafa da Mana, ga Kuma silver deep bowls masu girman gaske an hado tiwo da Miya, gidan su kenan, Haka suke biki shiyasa mutane ke son taron su saboda zaka ci me kyau ka Kuma Sha ka Kuma bar shi, Dan a wadace yake. Cikin kwarin gwiwa da Kuma tunanin yanayin da zainab take a wannan halin ya nufi gida, se de Yana shiga wangalelen iron gate din na su, yaga mutane nan ma da dama, Haka yayi ta bin gefe Yana wucewa saboda he's not ready for wani ya ganshi a tsaya ana ta gaishe gaishe plus ba kowa bane ba zai gane shi, se makusanta sosae, saboda shekarar shi wajen takwas a UK ko hutu bai taba zuwa ba. Se da ya kusa daf da gidan su sannan ne Suka hadu da mujahid, Ramadan da Sadiq, wadannan din duk cousins din shi ne kusan sa'anni ma suke da shi. Ai suna hada idanu da Sadiq tamkar wata mace se ya saki guda Yana fadin
" Lallai yau take juma'a, shiyasa akace jumaatu babbar Rana. Ango ya karaso"
Mujahid ya Kama hannun shi Yana fadin
"My English bro! Anya kaso dawowa daga UK dinnan kuwa!"
Ramadan Kam rungume shi kawai yayi Yana Masa barka da zuwa, shi dai tun da yaji zancen ango a bakin Sadiq, se ya ji kamar an watsa masa ruwan sanyi, shifa a wani dangin ana ganin nothing is possible ko, to ban da a Basu dangin, matsawar numfashim Alhaji Gidado ba ceasing yayi ba, Kuma kannen shi biyu da manyan yayan suna raye, to zasu cigaba da upholding duk wani policies din shi. Kafin wani lokaci Kam sauran cousins din shi dake kusa da Kuma Suka San shi duk sun yanyanbe shi, ga iyayen su acan Suma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 18