Wasa yace na daina Shan abin da nake sha ba, in fact shi kawai ya nuna min there are lots of healthy ways da mutum zaiyi maintaining jikin shi ba tare da ya Zama obese ba. Da Kai na na hango wannan hanyar Kuma na Fara amfani da ita. Lokaci kenan, tabbas komai Yana da lokacin shi, yanzun nawa yazo na accepting Kai na da Kai na.
Nayi murmushi sannan na zauna Ina kallon kwanon nawa, vegetable yafi yawa a cikin kwanon, na zauna naci sannan na shanye oranges din da na bare, Mamaa ta shigo dakin da sallama tana kallo na, na gyara Zama Ina amsawa, bayan ta zauna tace
" Bintu karatun ke sakawa kike rama ko Yaya ne?"
Nayi saurin kallon Kai na a madubi, ban wani rame ba, bayan idanuna da suka fada kadan, Suma tunani nake hakan na da nasaba da gajiyar da nayi, malaman sun sako mu gaba da test da sauran su.
"Ba komai!"
Ta gyada Kai tace
" Kizo kawun ku yana kiranki"
Nace Mata to Zan zo Ina kuskure Baki na. Ta fita na Shiga toilet na kuskure bakin sannan na fito se ga Kiran Noor Yana shigowa, da murmushi na dauka na Kuma Kara kunne na nace
" Tun dazun ka manta da ni!"
Yace
" Ni na Isa? I was busy ne kiyi hakuri!"
Na Bata Rai Ina sulking nace
" So har akwai abin da zai hanaka Kira na kenan! Shikenan"
Yayi dariya Amma kafin yayi magana nace
" Shikenan se anjima"
Kafin ya Kai ga magana na Riga da na kashe wayar Baki daya, na tsaya kallon ta Ina murmushi sannan na Masa message Kawu na neman na. Bayan nan nayi plugging wayar a caji na tafi parlon shi. Suna zaune da Batuul, Mamaa da shi Kawu da Kuma Adda. Na zauna bayan na gaishe su, kawu yace
" Na fada Masa gobe yazo kuje kuyi test a asibiti saboda Hadejia zaa daura auren ki Kuma jigawa dokar su se ka kawo result na HIV test"
Ta gyada Kan ta, idanun ta duk sunyi jawur, Ina tunanin ya fada Mata wani abun da yayi Mata zafi, itama Adda ranta a bace yake Dana kalle ta. Bayan ya sallami Batuul ta tafi ya dubeni yace
" Bintu! Wani yaro Akram ya same ni dazun a shago ya sanar min ya ganki Yana son ki, Kuma idan na bashi dama zai turo iyayen shi! Kinsan maganar ko ? Tunda yace Kun Fara magana da shi already ko?"
Na gyada Kai na a hankali, dukka iyayen nawa Mata Suka zuba min idanun na mamaki, Adda tace
" Shi ne Baki gaya Mana ba!"
Kawu yace
" Ki Bari na gama da ita tukunna!"
"Kina son shi? Nayi bincike ko Kuma kada na bata lokaci na, saboda bazan Yi tolerating abin da kikai min akan Suleiman ba"
Na Bata Rai Jin Wai har yanzun zancen Suleiman Bai kau ba. Ko kunya banji ba nace
" Ina son shi!"
Aikuwa Adda tace
" Jimin fitsararriyar yarinya marar kunya. Da bakin ki Zaki ce kina son shi"
Ga mamaki na se kawu yace
" Asiya Ina ruwan ki? Se yaushe Bintu zatai Abu ta burge ki? Ki kyale ta Mana"
Tayi shiru tana juyar da Kai, ita dai Mamaa ba tace komai ba, kawu yace na sani Babu canji yadda nace Ina son shi Haka magana zata Kai har karshe. Na amince da hakan na tafi, Ina zuwa daki na samu calls din shi da nayi missing, nayi dariya nasan yayi tunanin ko fushi nayi irin dinnan. Kiran shi nayi Yana dauka yace
" Kin bani tsoro, nayi tunanin da gaske fushin Kika Yi!"
Nayi murmushi nace
" Banyi ba, Wasa nake maka. Ni bani da saurin fushi ai"
Yace
"Shiyasa nayi mamaki ai. So kunyi magana da kawun?"
"Munyi! Ashe kaje ka same shi? Baka ji tsoro ba?"
Yayi dariya yace
"Da Abba Zan tura mishi ma, na dai je neman izini ne and soon su Abba zasu same shi. Ko yau da safe se da yace yaushe nake son aje ayimin tambaya. Ita Kam Ummaah har ta Fara siyayya!"
Nayi dariya wa yaga zumudi, Nima jiya ta Kira Ni tana tambaya ta abin da nake so na lefe, I was so surprised irin wannan zumudi da Ummaah takeyi ai se kayi dariya. So washegari na tafi makaranta, Batuul tayi wanka tayi kwalliyya ta saka wata fitted gown ta atamfa, anyi fleeting kasan ta, dukka curves din ta da Kuma shape din ta sun bayyana. Tayi kyau Amma shigar Bai kamata ace an fita da ita ba. Wani siririn Chantilly veil ta yafa a saman daurin da tayi, ko kirjin ta Bai sauka ba, ta dauki Jakar ta ta rataya sannan ta dauki dalleliyar wayar ta ta rike a hannu. Tana cikin saka takalmin kawarta Nafi lamido ta kira, ta dauka suka danyi rudu yadda suka Saba sannan tace
" Ke Batuul Ginsau nayi contracting Fatima garo akan sourvenirs din da zamu raba a biki!"
Batuul tace
" Kayan suna da kyau!"
Ai tuni Nafi ta Fara fada Mata yadda kayan suke.
"Kin gane Adudum ne wannan local basket na kaba, akwai kayan kamu a ciki, ki Kuma ki fada Mata content din da kike so se a saka Miki. Amma ga contact dinta Zan turo Miki da IG handle din ta ki duba"
Batuul ta amsa da to sannan ta koma ta zauna daidai lokacin message din ya shigo
_Fgees_collection_
_08067802846_
Tuni Batuul ta gyara Zama se taga ai har home decor take siyarwa, Jewelry, bedsheets da Kuma sourvenirs na biki. Kayan sun hadu babu karya, a take ta tura mata DM sannan ta fita Dan message din honorable ya Riga da ya shigo wayar ta akan ya karaso. Babu Wanda ya yiwa sallama a gidan ta wuce. Yana zaune a Bayan mota ya Sha kananan kaya, hannun shi rike da wayar shi Yana going through!
Ta_kwalam
043
Bayan watanni biyu
Ban dauka komai zai zo.da sauki ba kamar yadda yazo da sauki Haka. Na dauka dangin Shi da yake cewa ai Yan kauye ne tun da har yanzun sun ki karbar canjin zamani, su gani suke old norms din su da values shi ne komai. Idan ya fadi hakan na kance Masa ba Haka bane ba, suna kokarin preserving bloodline din su ne. Se yace ba wani nan kauyanci ne da racism da hauka.
Ban sani ba ko dan sun ga abin da ya faru da mahaifiyar shi yasa Babu Wanda yaja da maganar kowa se yace Allah ya Sanya alkhairi, dama Kuma yadda Imam yayi Bai ma bada damar ko cikin Uncles din shi ko brothers ko cousins wani ya Fadi opinion din shi. Safiyya ta fada masa matsawar Yana son wanke laifin shi a wajen Akram to dole ya Kare Akram From critics dun family, ko Kuma wani yaga fuskar yace ya nema a cikin dangi, hakan yasa Imam yin tunani Kuma yaga tabbas Haka ne, dole ya tsayawa Dan shi tun da shi shekaru talatin da suka gabata Bai samu wannan goyon Bayan ba.
Dukda Haka akwai Wanda basu iya rufe Baki ba se da suka samu Imam suka nuna Masa abin da yake Shirin aikatawa Bai kamata ba, wasu Kuma matan Safiyya suke fadawa akan yanzun duk Yara matan da suke da shi cikin wannan katon community din Amma har se yaje waje ya dakko wata. Safiyya se tayi murmushi tace, zabin shi ne Dan Haka dole mu bar shi yayi abin da yake so.
To dai a Haka suka turo aka saka Rana Wanda watanni biyu kacal aka saka, zuwa lokacin na kammalla exams di ta ta session din. Wani lokacin haduwa da mutane yakan Zama kamar wani turning point ne a rayuwar ka. Shiyasa bana taba Dana Sanin haduwa da mutane, saboda Allah kadai yasan wanne Abu wannan mutumin ya shigo da shi cikin rayuwar ka.
A bangaren mu, wato a gidan mu tamkar ba wani biki zaayi ba, Banga irin wannan a tafi kasuwa a dinga siyayya ba, da farko sun Fara da Mamaa da Adda Amma tun da akace biki na kawai zaayi se naga duk sunyi slacking, mamaki sosae nake na har yanzun sun kasa daina banbanci tsakanin mu. Ban ma damu ba saboda kunsan dai ina sanaa, Kuma kudin Babu abin da nake da shi, profit di na kawai aje su nake, Dan Haka a hankali nake siyan abin da Naga ya kamata Ina ajewa.
Shigowa ta kenan daga last paper da Zan rubuta a wannan semester, Kuma exams din ta Noor ce. Tun dare ya tashe ni karfe biyu yace na dakko reading materials di na, Babu musu nace ya jira na wanke fuska ta na dawo, Haka na kunna bulb na zauna muka Fara karatu ni da shi, Bayan awa daya yace naje kitchen na hada tea saboda karatun da nayi, he's sure glucose di na ya Kone. Haka na tashi saboda shi mutum ne da baya son musu ko kadan, nima Kuma Ina kokarin ganin bana Masa musu. Na hado Ina sha har muka Kara 30 minutes, se yace mu Yi sallah da addua na mintina goma, Bayan min idar yace na kwanta Dan brain di na ta huta, nayi Masa sallama hade da godiya na kwanta, Babu jimawa bacci ya dauke ni. Se asuba ya tashe ni , nayi sallah Bayan na idar na Yi wanka, kamar kullum muna cin abinci muna waya saboda yace Bai yadda Dani ba Akan skipping meals. Bai sani ba ko kadan rage kiba, saboda abin da mutane suke fada ya daina damu na, Kuma wani Abu Dana fahimta yanzun mutane Basu fiya ce min kina da kiba, ke ki rage kiba. Wato dai it's all about accepting yourself, that's when mutane zasuyi accepting din ka. Idan na zauna nayi tunanin rayuwar da nayi ta baya, se naji har kunya nake ji, idan Kuma na kalli Kai na se Naga to wai Ina kibar take da na damu Kai na akan ta, idan na duba se Naga ai akwai Wanda suka fini kiba sosae da sosae Amma suna rayuwar su cikin farin ciki Babu tsangwamar Babu Kuma takurawa Kai. Shiyasa nake fada muku kullum kusan irin maganar da zaku fadawa mutane, Baku San irin battle din da mutane suke ciki ba internally, kowa da ka gan shi bashi yaso ya Zama me kiba ba, ko siriri ko mummuna ba, se me idan Yana da kiba rayuwar ku ce? Ko Kuma jikin ku ne, kunsan how much critics din ku ke halaka mutane? Ina fatan Bayan karanta labari na, ba ruwanku da tanka jikin mutane. That's by the way!
Na shirya cikin Abaya olive, anyi Mata embroidery da bakin zare, na saka sannan na saka bakar hula, na dakko daya daga cikin turaren SCENTMANIA na murtsika a hannu na na shafe jiki na da shi sannan na yafa veil din, na kalla Kai na a mirror dakin mu Naga yadda nayi kyau, jiki na Bai dame ba Kuma nayi kyau. Zama na da Akram ya nuna min akwai gayu da zakai kayi kyau ba tare da kayi exposing jikin ka ba, shi yayi ta siya min Abaya sannan ya dinga encouraging di na na saka Naga yadda zanyi, ranar farko da na saka kunya nayi ta ji, shi Kuma yayi ta min dariya Yana cemin Wai no Yar kauye ce, a hankali Kuma na fahimci Yana son mace da Abaya se na dage har ya Zama jiki na, na daina Jin komai idan na saka. Jaka ta na dauka na fice zuwa dakin Adda, Bata nan hakan ya tabbatar min suna tare da Mamaa ko da Kawu, aikuwa dukka suna tare a parlon Mamaa, na gaishe su sannan na mike, Mamaa tace
" Yau shi ne ranar karshe ko?"
Na gyada Kai Ina gyara zaman veil di na nace
" Eh"
Dukka Suka hada Baki wajen yimin adduar nasara, naji Dadi sannan na tafi Abu na. Banyi expecting ganin shi a exam Hall din ba Amma ana farawa se gashi ya shigo shi da Dean, yayi kyau cikin kaftan maroon da ta kawata yanayin shi, Dake na saka mask a fuska ta hakan ya bani damar kallon shi da kyau, shima kallo na yake lovingly, nayi murmushi na cigaba da rubutu na. Ban sake dagowa ba se da naji kamshin turaren addictive ambergris na wajen SCENTMANIA tawa, birthday gift na bashi lokacin da ya cika shekara talatin da biyu, da yayi amfani da shi ranar yini yayi Yana Koda turaren nata, fada min yake it's the best gift da aka taba bashi a matsayin birthday gift. Ina dagowa idanun mu Suka Shiga na juna, na sauke ajiyar zuciya Ina Dan murmushi softly, yayinda ya danyi min wink da yasa naji wasu butterflies a ciki na. Kai na na mayar akan abin da nake rubutawa, shikuma se ya cigaba da karanta abin da na rubuta.
" Dr. Akram zaka zauna na tafi?"
Mukaji muryar Dean, hakan yasa ya girgiza Kai sannan ya Fara kokarin janye idanun shi daga Kai na yace
" Idan kin fito, call me I want to drop you home!"
Daga Haka ya fita Nima Babu jimawa na kammalla nayi submitting Muka fito tare da Sadiq, ya tambaye ni exams nace Masa alhamdulillah Dan kuwa Allah shi ne abin godiya. Yace
" Ina Jin ki?"
Na dube shi da rashin fahimta nace
" Menene fa?"
Ya bude backpack din shi ya Ciro wata envelope me kyau ta IV yace
" Sir Akram gave me! Ashe aure zakuyi Amma shi ne Baki fada min ba. Akwai aminci kuwa?"
Nayi dariya cikeda Jin kunya nace
" Kayi hakuri, nayi tunanin Alamin ya fada maka, saboda na fada Masa shi!"
Yayi murmushi yace
" Alhamdulillah! I'm happy for you! Allah ya sanyar muku da alkhairi, farin cikin ki shi ne namu!"
Nayi murmushi Ina Masa godiya, waya ta ta Fara Ringing se na tuna ban Kira shi ba, cikin sauri na dauka nace
" Yanzun Zan Kira ka fa!"
Yace
"Shiyasa Naga kina tsaye da Sadiq Kuna dariya!"
Nayi saurin juyawa Ina waiwayen Ina Zan gan shi, Sadiq da ya fahimci aabin da yake faruwa ya nuna min motar tashi, nayi saurin kashe wayar na ma Sadiq sallama tun da hutun session zamu tafi Kuma kowa yasan irin dadewar da ake. Tun da na shiga yake cona Baki Wai shi yayi fushi, nayi murmushi Ina connecting wayata da Bluetooth din motar shi ba tare da na kula shi ba, se Dan Kan shi yace
" Fushi nake fa! Baki gani ba?"
"Na gani Mana!"
Na fada Ina murmushi, shima se ya Fara murmushin yace
" Ba Zaki kula ki ba Kuma? Ko lallashi babu?"
Na Kara fadada murmushin fuskata Wanda in dai Muna tare fuskata Bata dauke wa da smiles, har mamakin Kai na nake, am I that grumpy Bintu kuwa ko dai wata ce daban. But this is all in the past, Kuma all credit goes to Noor di na!
"Noor!"
Na fada softly, ya Dan kalle ni sannan yace
" Naam Noor!"
Shima Noor din yake cemin, nace
" Kasan duk mazan duniya Kai kadai nake so ko?"
Ya gyada Kai da sauri, nace
" Kuma Kai kadai na zaba ko?"
Nan ma yayi saurin gyada Kan shi, nace
" So, Ina son na Kara tabbatar maka no matter what I'll choose you over all the Men in the world! Kaji Noor di na?"
Ya saki ajiyar zuciya, kayataccen murmushi a fuskar shi yace
" Thank you Noor! Na Miki alkawarin farin ciki na har abada! See"
Se na kalle shi anan yake fada min, shi fa ba zai zauna a community din su ba, na tambayi dalilin se yace kawai saboda Yana son privacy, Kuma Bai son wani ya takura min, Yana son nayi rayuwa me yanci kamar kowacce matar aure!
Noor di na bashi da na biyu, you can argue with your keyboard...lol. Asibiti mukaje mukai gwajin da ya kamata sannan ya kaini gida, a gajiye matuka na shiga, se Dana fadawa Adda dawowa ta sannan na Kuma Bata result din mu ni da shi kafin na leka wajen Mamaa, da ta baje kayan kitchen, Ina shiga tace nazo na zaba, na girgiza Kai nace
" Kawai ki zabar min duk abin da Kika ga ya dace!"
Bansan me yasa ba har yanzun wasu abubuwan.basu bar zuciya ta ba, dukda lokaci ya Dan tafi Amma har yanzun bana iya zaben Abu in dai a gida na, gani nake why should I choose. Daki na wuce dukda tace min gida na ne fa, nazo na gani, Ni dai na tabbatar Mata Babu damuwa. Ashe bayan na fita Yaya Fadima ta Kira su tace musu gwara su fitar da kudi Dan kuwa ga irin gidan da Zan shiga, se kawu yace ma Adda ta fito da kayan Batuul da yayi ta bata kudi dama ai shiyasa har yanzun Bai bada kudin siyayya ba saboda he believes kayan da aka siyawa Batuul sun Isa kitchen di na. Da farko tace ai da sunan Batuul aka siya Dan Haka se de a siya wasu. Adda nada abun mamaki, kowa se yayi mamakin da gaske ita ta haife ni kuwa? Wannan raayin ta ne. Wuta Kawu ya bude Mata yace ya ishe shi banbancin da take nunawa, da waya ce ta kawo kayan? Yanzun dole ta kawo kayan tunda Ni kadai zaa yuwa biki!
Ina Shiga daki na samu Batuul a kwance tayi ruf da ciki, dake ta Saba kwamciya a Haka so se nayi tunanin ko bacci take, nayi sallama sannan na rage kayan jiki na, na zauna Ina tattare books di na waje daya, Ina hakan se Naga ta juyo da fuskar ta kamar nunnanen tumatur, fuskar tayi jawur kada idon ta da hancin ta suji labari. Nace
" Batuul are you ok? Me ya same ki?"
Tun watanni biyu da Suka wuce, tun da aka fasa auren ta gaba daya ta Zama wata iri, Bata Shiga mutane Bata fita, makaranta ma daina zuwa tayi Kuma kamar Babu Wanda ya damu a gidan, Dan kawu cewa yayi gwara tayi zaman ta kawai yafi sauki da ta dakko musu magana.
" Ke ma kin daina so na ko Bintu, Baki taba tambayar abin da yake damuna ba. Duk Kun tsanenu ko?"
Nayi saurin komawa kusa da ita nace
" Haba dai Batuul! Kiyi hakuri Naga idan na tamabye ki kuka kike shiyasa na barki tace!"
Tana kukan ma sannan tace
" Bintu kinji dadi, rayuwar ki gwanin shaawa! Har burge ni kike Yi, you lead a silent life Amma a karshe kinyi achieving Abu. Ki yafe min"
Na danyi murmushi nace
" Ke ma kinyi achieving wasu abubuwan ai. Dan an fasa auren ki ai wasu na zuwa, Kuma life always offers a second chance!"
Ta danyi tsaki tace
" Bintu I've messed up! Kinga Honorable Allah kadai zai saka min abubuwan da yayi min! Allah ya Isa tsakani na dashi!"
Bari muji me ya faru da Batuul tukunna!
Bayan fitar Batuul da shigar ta motar Honorable, straight wani first class hotel Suka tafi, yadda Batuul take lokacin da suka Shiga ta underground kawai zai tabbatar maka wannan ba Karo na farko bane ba, ba Kuma na biyu ba balle na uku. Suna shiga Presidential suite din shi ta Fara bashi abin da ya kawo su. Ba wani Ina nufin just a common smooch ba, a'a Ina nufin having an affair shi ne abin da Suka Yi. Shi baiji kunyar kawo yarinya wadda autar shi ta girme ta ba, ita Bata ji kunyar stripping kayanta gaban wanna tsohon dattijon ba, Bata Kuma ji komai na cin amanar iyayen ta da tayi ba. Ita dai Abu daya ne a zuciyar ta, she can go to any length ta samu kudi sannan ta aure shi. Barin ta yayi tana bacci ya nufi asibitin da ya kamata suje test, se da ya tabbatar babu me Gane fuskar shi saboda yadda yayi disguising Kan shi. Ciki ya shiga, ya samu daya daga cikin clinicians din yace Yana son Sanin status din shi, Babu jimawa kuwa aka dakko kayan test a cikin Lab din dake jikin building din, anayi se ga HIV nan positive Rado Rado!
Bayan an Shiga counselling ya fadawa clinician din shi yasan status din shi Kuma Yana Kan magani, Amma akwai yarinyar da yake son ya aura to Yana son kawo ta suyi test tunda Yan gidan su sun matsa, Amma Yana son a boye status din shi su Zama dukkan su negative. Clinician din se kallon shi yake with a plain face wadda take emotionless, ba lallai ka fahimci abin da yake tuanani ba. Kafin yayi wani Abu har honorable ya fito da bandit din N1000 notes bandir biyu, 200k kenan a matsayin toshiyar Baki!
Ina fatan na wanke laifi na! Thank you guys for the call, wasu da yawa sun dauka bani da lafiya, not at all abubuwa ne beyond my control. Thank you for hanging around 😊
Ta_kwalam ce
044
Bayan Nan ya koma yaje ya dakko Batuul da ta kammalla shiryawa shi take jira. Suna tafe suna Hira gwanin shaawa, Kai kace gaske ne. Har Suka Isa asibitin Batuul bata kawo komai ba, saboda duk wayon ta mutum ce me yadda da mutane, shiyasa ni da ita muka banbanta. Bayan sunje gaban clinician dinnan, kamar yadda tsaurin yake kafin a dauka jinin ka zaa Yi maka bayanin gwajin da zaayi maka, ruwanka ne ka amince ko lace a'a, to Batuul ta amince Bayan an Gama pre test counselling, a tare aka dauki jinin su tamkar Babu abin da ya faru tsakanin clinician din da Kuma Honorable, kowa a cikin su ya basar tamkar haduwar su ce ta farko. Suna ta Dan Hira har se gashi result ya fito na su dukka biyun, as expected Honorable positive ita Kuma Batuul luckily for her nata negative. Ya dubi result din sannan ya dubesu ganin dukkan su sun bashi hankalin su. Yace
" Fatima Batuul na Fadi result din ki yaji?"
A take taji gaban ta yayi wani mugun faduwa ta dubi Honorable da yake ma clinician wani irin kallo, tace
" Akwai matsala ne?"
Ya girgiza Kan shi ganin yadda har idanun ta sun Fara Tara ruwa alamar zatayi kuka, se Kuma ya dubi Honorable yace
"Honorable na fada Mata result din ka?"
A take ya Bata Rai yayi kicin kicin da fuska Yana muzurai yace
"Fada mata!"
A wannan lokacin Batuul was confused, musamman da clinician ya bude drawer ya Ciro wannan wrapper kudin ya aje gaban Honorable Wanda yake kallon shi da wani irin yanayi yace
" I'm sorry sir! Ba Zan iya boye mata ba, abinda yasa na amince saboda nasan ko na ki zaka kaita wani wajen kilan ka samu masu son zuciya su karba"
Ya juyo Kai na yayinda ya bar Honorable cikin wasiwasin ya tashi ko Kuma ya tsaya ya gama ganin karshen iskancin yaron nan
"Batuul gwajin ya nuna Baki da matsala, Amma shi nashi akwai matsala!"
Idanun Batuul kamar zasu Fado a kasa, tun da akace akwai matsala ai Yana nufin he's HIV positive, tamkar an kwara mata ruwa Haka tayi tsumu tsumu. Yayinda Honorable ya dauki kudin shi ran shi a bace ya fice. Batuul Kam tana nan zaune tayi shiru Dan ta Riga ta fahimci boyewar da yayi mata, ta fahimci ha'intar ta yaso yayi ya rufe Mata. Clinician din yace
" Ki tafi Baki da matsala!"
Se ta Mike ta dauki Jakar ta tana Jin wani irin yanayi na rashin kuzari da karfi tace
" Nagode! Nagode sosae!! Nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Nagode sosae. Allah ya biyaka. Nagode!"
Mutumin yayi murmushi sannan yace ta zauna kafin ta zauna ya fara fadin
" Muna samun irin wannan cases din kala kala Amma shiyasa ake bamu kudi, kada kudin irin wannan mutumin su dauke Mana hankali. Kaddara na bari kin aure shi, se Kuma ya mutu, bayan nan kije ki auri kilan me Mata uku ki Kara yadawa, Kinga banyi Miki adalci ba ko kadan"
Ta saki ajiyar zuciya tana sake Masa godiya, har ta tashi zata tafi bayan exchanging numbers da sukai se ta dawo ta tambaye shi hanyoyin da ake dauka, anan ya fada Mata hanyoyi uku da ake dauka, tun da taji sexual intercourse se ta Fara kuka tana fadin
" Aikin Gama ya Gama! Na Shiga uku"
Wata sabuwa inji Yan caca, nan fa clinician yayi Mata nasiha sosae sannan ya dakko magani ya Bata yace ta dinga Sha kullum Bayan watanni uku ta dawo a sake gwaji in dai babu to ya tabbatar babun da gaske! Haka ta dakko ta taho gida kamar mahaukaciya saboda yadda take a gigice. Tana shigowa ta tarar da Kuma labarin ya Kira kawu yace ya fasa auren ta ya janye, wannan Bai ma dame ta ba saboda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 18