Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan karon Bayan mun sake komawa gida na samu Kawu saboda career guide nace Masa " Kawu zanyi registering jamb, shi ne nazo nace maka wanne course Zan saka?" Ya Dan rage volume din radio din shi yayi kadan sannan yace " Ki zaba abin da Kika San Kan ki zai iya dauka, kinsan bana son failure a gida na" Na gyada Masa Kai sannan nace " Na saka architecture?" Yayi dariya yace " Waye zai iya architecture Bintu? Amma ba ke ba ko?" Na Dan Bata fuska nace " Zan iya Kawu!" Ya gyada Kai tare da fadin " Then carry on' Na fita zuwa dakin Yaya Auwal na fada Masa architecture zai cika min, da Kuma makarantar da nake so, ya danyi dariya yace " Bintu kin San menene architecture kuwa? Ke din ce Zaki iya wani architecture? To Ni Adda cewa tayi na saka Miki education na biology Kuma na Riga har na coke" Na dube shi wani Abu ya kawo min wuya nace " Biology education Kuma? Ni me yasa ba zaa ji raayi na ba? Haba Yaya" Ya shige ya barni a wajen, na koma daki kawai na Fara kuka, nayi me isata sannan na wanke fuska ta na karbo wayar Mamaa nayi dialing number BashPrince00 Wanda na Riga na haddace a Kai na. Ina magana yace "Princess me ya same ki? Kuka kikai?' Na gyada Kai na nace Ina Kara sakin wani kukan, ai se ya rikice gaba daya ya Fara tambaya ta abinnda ya faru, aikuwa Ina kuka na fada Masa duk abin da ya faru, se da nayi shiru yace " Are you sure zai iya architecture din?" Na gyada Kai na kamar Yana gaba na nace " I'm determined!" Se yace " To Ni Zan turo Miki kudi kije ki sake registration a nearby jamb office!" Nayi shiru Ina tunanin Anya kuwa na karba kudin shi? Ai Bai kamata ba, se na girgiza Kai na nace "A'a ka bar shi, I can't accept it!" "Saboda kin Raina ko? Me yasa kike min Haka ne Bintu? Baki dauke ni yadda na dauke ki ba ko? Kinsan yadda nake son ki kuwa? Ina Jin kamar akan ki I can move the mountain for you and I can melt the snow for you!" A take fuska ta ta cika da wani annuri me kayatarwa, bansan menene love language din ku ba, Amma nawa love language din is "words of affirmation" Ina son mutum constantly ya din ga tuna min Yana fadin how much I mean to him, yadda yake ji na cikin zuciyar shi, tamkar kuwa Bashir ya sani ko fahimta yayi he always does yadda nake so!!! Ta_kwalam ce BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI rubutu ne na kudi, Wanda N1300 kawai ta ishe ka subscribing... [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 015...Last free page Ayshatuuu *Kece me kallon mutane kice musu sun Yi kiba ko? Kece me kallon su kice ke Kinga ranar da kikai? Kun San illar bakin ku kuwa? Kunsan me maganar ki take jawowa?* "I finally got to see my BinGin" Ya fada Yana sake matsawa gefen da Samiha take, yayin da ko second glance Bai bani ba balle na saka ran zaiyi min magana. Wani irin Abu naji ya zamo min wuya na ya tsaya min tamkar an samo katon dutse an saka a gurin. Nayi shiru Ina kallon Samiha dake murmushi from ear to ear, na kalle shi ya lumshe idanun shi duk lokacin da wannan jijiyar ta goshin ta ta bayyana, there and then naji, I've lost this battle, wannan ba fadan da zanyi nasara bane ba, Amma se zuciya ta ke cemin " Bintu tafiya zakiyi? Ina Zaki je Baki fada Masa kece ba?" Se na tsaya saboda har lokacin Samiha taki tace ita ce BinGin, ta Kuma taki denying hakan, na cigaba da kallon yadda suke ma juna killer smile Kai ka rantse da Allah kace dama can sun San juna, kamar Zan Yi hakuri Naga gudun ruwan su, Amma a yau se hakuri na ya kare, na gagara yin hakan, Babu shiri nace Masa " Habiebie na!" Se ya juyo da sauri, I'm sure ya Gane murnar da Kuma salon da nake amfani da shi duk lokacin da Zan Kira shi da hakan, se Kuma ta juya ya kalla Samiha da murmushin fuskar ta ya Fara daukewa, ya kalle ni wani irin kallo na kada kice kece BinGin, na gyada Kai na nace " Nice Bintu Ginsau wato BinGin" "Kece?! How?" Ya fada cikin wata murya me wani irin amo, nayi shiru na rasa me zance masa, shima se yayi shiru yayun da nakan ga Yana stealing glance din Samiha wadda tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ko kadan ban taba kawowa Samiha zata iya yin abin da tayi min ba, ko da Wasa ban taba kawowa hakan ba. A hankali yace " I'm sorry Bintu but..." Se yayi shiru ya kasa karasawa, Kun taba Jin bugun zuciyar ku ya karu har Kuna tunanin Anya wannan zuciyar tawa ba kokarin balls kirji na take ta fito ba? To Haka naji, I was so scared da zuciya ta ta kasa controlling bugun da take, nayi kokarin rike kirjina Wai duk kokari na, na kada zuciya ta ta fito " Bansan Haka kike ba, kiyi hakuri but you're not my type, bana son Mata masu *KIBA* " Ya fada idanun shi na Kan Samiha da lokaci daya murmushi ya Kara bayyana akan kumatun ta da fuskar ta. Na kalle shi sosae, na Kara kallon shi a Karo na biyu kafin Kuma na samu brain Dita ta Gama processing maganar da yayi min. Se na fahimci Yana nufin ni Bintu by type din shi bace ba, type din shi Samiha ce, beside baya ma son mace me kiba. Ai ina Gama tantance hakan ban jira wata magana ba, na juya na Fara wulla kafata, a wannan lokacin wallahi na manta cewar visiting akeyi, ko kadan na manta Wai hall din a cike yake da mutane, idanu na ba abinda suke gani, idan kuka dauke memory cells Dake taimakawa kowanne Dan Adam wajen tuna abin da ya Riga da ya sani, to bana tunanin Zan iya Kai kaina hostel. Na manta Wai bana son mutane, na manta wai bana sakewa idan mutane na guri, all that matters shi ne na kadaice. Ina zuwa hostel na Fara cire kayan jiki na, se da na cire tas na bar towel Dake daure a kirji na sannan na zumbula hijab na fita, Ina zuwa waje na samu drum ana Kone kone, a take na zuba dukkan kayan a ciki sannan na dawo, ba Wai Ina cikin hayyaci na ba ne ba, a lokacin I've completely lost my sense, bana cikin hayyaci na ko kadan. Ina zuwa toilet na tsaya gaban katon mirror Dake corridor kafin ka Shiga cikin toilet, nayi ta kallon Kai na, Ina juya Ina kallon tun daga fuskata down to my feet, Ina dadewa ban ga Muni na ba, Amma a wannan lokacin se Naga duk duniya Babu mummuna, Babu wadda batai dacen figure ba iri n, gani nake Babu wani Dan Adam da yafi Ni Bintu kiba a duniya, na wuce toilet na zauna saman toilet seat na Fara wani irin kuka Wanda har yau bana son na tuna wannan ranar " Shike nan? Ya Kare? Shike nan har an gama? Yanzun da gaske na barwa Samiha BashPrince00 kenan?" Kai a cikin zuciya ta nace Samiha ba zata taba yimin hakan ba, ba zata taba son abin da nake so ba...lol! I was too innocent, I was too softhearted, I was too kind-hearted also! Ban kawo ko wildest dreams dina Samiha zata iya son habiebie ba. To Amma se na ayyana ya akai har yanzun Bata biyo ni ba, kenan itama ta yadda ta Kuma karbe shi a matsayin saurayi To dai na Jima Ina kuka, kukan da yasa hanci na Fara zuba, kunne na ya toshe kamar kurma, sannan Kai na yayi wani irin nauyi kamr idan na tashi Zan Fadi. Ban dai na kuka ba se da naji hawaye ya daina zuba daga idanu na kafin na sakarwa Kai na ruwa na wajen minti na ashirin kafin na Mike zuwa daki, Ina zuwa na Fara karkarwa saboda sanyi da ke ratsa jiki na, hakora na suka Fara karkarwa kamar an saka ni cikin kankara. Haka na kudundune cikin blanket Ina wani irin karkarwar sanyi, ku tuna I was only sixteen years old, Kuma dama duk rayuwa ta na kasance bakin ciki kawai nake kunsa, Samiha da BashPrince00 su ne mutanen farko da na Fara samun solace wajen su, se gashi Ashe su ne zasuyi betraying di na, Kuna ganin kuwa Zan iya sake trusting mutane easily? Ai Abu ne me wuya. Ina nan kwance bansan har lokacin da na Kai a kwance ba, rufin asiri na period nake shiyasa har lokaci yayi nisa bansan karfe nawa bane ba. Ina nan a kwance inata kuka Ina Kuma karkarwar zazzabi. Se da hidaya room mate di ta ta shigo sannan ta ganni a Haka, cikin tashin hankali ta nufe ni tana tambaya ta abin da ya faru, Amma ganin halin da nake ciki kawai se taje ta Kira matron din hostel din mu, Suka dawo tare, sannan Suka taimaka min na saka Kaya suka kaini sickbay, ban ma dai San abin da ya faru ba na samu bacci me nauyin gaske ya tafi dani. Bani na farka ba se yamma can sannan akai discharging di na na dawo hostel Amma ko duriyar Samiha Babu a wannan clinic din har na tashi. Mamaki sosae nake yadda ta iya karkade idanun ta, but can kasan Rai na Ina Bata benefit of doubt, Ina ganin kamar abin da nake gani ba hakan bane ba, a Haka na karasa hostel Amma dakin su na Fara zuwa, na same ta da Yan dakin su sun baje Kaya suna kalla, it's down on me cewar kayan da ya kawo min ne. Da sallama na shiga Wanda yasa ta Mike tana kallo na tace " Ance Baki da lafiya?" Ban Bata wannan amsar ba nace " Ina son magana da ke please, can you step out?" Ina ganin yadda jikin ta yayi sanyi, se ta biyo ni bayan ta tattare kayan cikin Leda, se mamakin ta nake Baki bude, mamakin karfin halin ta da Kuma karshen rashin kunyar ta kawai nake gani, Amma Kuma har lokacin Ina ganin ba Haka bane ba. "Samiha..." Tayi saurin katse ni hade da fadin " Kinga Bintu, nasan Zaki ce ko na yudare ki, ko Kuma na Miki snatching Amma Kinga ba Haka bane ba..." "Menene Samiha? Ina kallon yadda kike mishi murmushi fa" Ta saki wani murmushin da ya sake Kona min zuciya tace "He chose me Bintu, a gaban ki yace ni ce type din shi ba ke ba, Kinga idan akwai me laifi Bashir ne bani ba. Ni kawai dama na samu Kuma na bi, so I'm not at fault!' "Dukka friendship din da mukai karya ne kenan? Samiha dama Haka zakiyi min, kinsan yadda nake son shi ko?" Se kawai ta girgiza Kai tace " Don't push yourself hard Bintu, kije ki aura daidai dake!" Wannan maganar ita ce tafi duka na a kaf abin da Samiha ta fada min, na juya a hankali na koma daki na lalubo waya ta na Fara Kiran shi, se da na Kira sau biyu ana uku sannan ya dauka, "Kaje gida lafiya?" Shi ne abin da na Fara tambayar shi, haushi Kuma na Fara ji bayan maganar ta fita daga Baki na. To Amma ya zanyi? Son shi nake Kuma bana tunanin akwai abin da zai canja wannan son, a hauka na fa! "Naje lafiya Bintu, kiyi hakuri abin da ya faru, I know I did a mistake da ban tambaye ki picture din ki ba, amma kiyi hakuri I can't continue with you!" "Ka Manta kace min fuskata doesn't matter, what matters is kyakyawar zuciyar da nake da ita, so it was all a lie..." "Ba Karya bane ba Bintu, I loved you wholeheartedly!..." "Then me kake Yi yanzun?" Yayi shiru ya kasa ce min komai se kawai na saki wayar ta fadi akan terrazzo flooring din dake wajen, nasan ta fashe, waya ta C2 ce da kawu ya siya min, na tafi na dakko katon Dutse tun karfi na na fasa wayar tare da taune sim din, meye ya rage? Meye Kuma amfanin wayar? Dama Dan shi nazo da ita, to it's all over then what's the essence? Ina nan tsaye Ina rike da kirji na dake zafi na hango Samiha ta fito da waya a kunnen ta, yadda kuka najr na shake ta Haka nake ji, Amma se kawai na juya zuwa daki. A wannan Daren kwana nayi banyi bacci ba, ga shi ni daya ce cikin dakin, wani irin dare ne na bakin ciki a gaba dayan rayuwa ta, bana fata wani ya dandana abin da na dandana a wannan Daren. Se komai na rayuwa ta ya Fara dawo min, tun daga Kan yadda Yan gidan mu suka ta tsangwamar ta Akan kiba ta, da yadda kowa ma idan na fita yake kallo na kamar wadda nayi laifi, se naga to ai bani da amfani, meye amfanin rayuwa ta gaba daya? Idan na cigaba da numfashi Haka Zan ta kullar bakin ciki, Dan Haka na mike zuwa locker ta na bude Dan lokacin shida na safe, Ina bude locker se ga kwalbar Dettol, a hankali dukda wasi wasi da nake Yi Amma na dauka Ina bude murfin...a Raina Fadi nake " Bari na mutu ko Zan huta da wannan rayuwar!!!" Har yanzun Wai bakiyi subscribing tafiyar top-notch season 3 ba? Kinsan kuwa irin fascinating stories din da Muka zo dasu? Wannan karon fa ba TSINTUWA bace ba, ba Kuma ASHRAF bane ba balle SANIN GAIBU! Magana ake ta GEN NASIR ZAKI, NAZNEEN da BINTUN BATUUL. N1300 kacal jama'a [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 Ayshatuuu 014 *Kina da kiba? Ko ke gajeriya ce? Ke siririya ce? Doguwa ce ko Kuma ke siririya ce? Are you being criticized saboda hallitar ki? To tsaya kiji wannan halittar, wannan kamanin uniqueness naki ne Wanda Allah ya Baki kyauta! Don't ever look down on yourself, it's your pride, don't body shame yourself* Shi ya biya min kudin sake registering jamb, zuwa yamma na shirya tare da saka Kaya na na fita, Ina zuwa aka ce min na makara sede na dawo washegari, Haka na dawo Babu yadda Zan yi Haka nan na dawo gida Rai na Babu dadi, washe gari da wuri na fita, kunsan mu a gidan mu muna da a bit of freedom, zaka iya fita ko baka tambaya ba, wannan shi ne kuskure na farko da iyaye ke Yi, Bai kamata ace yaro Yana da so much freedom ba, hakan zai Bata Masa tarbiyya sosae da sosae. Ko da naje wajen nayi generating remita da komai na biya, sannan na dawo da taimakon su a cafe din na cike komai nayi finger prints, Suka bani wasu books da zasu fito a English part. Ina kammalla na fito Ina kokarin tarar napep Dan komawa gida, wasu samari dake tsaye bakin titi, suna ta Hira, tun da na taho suke kallo na, kunsan Ni bana fita idan ba dole ba, bana kuma Shiga cikin mutane, ko yanzun da Zan fito Babu yadda Zan Yi shi yasa na fito. Ina tahowa daya daga cikin su yace " Kaga wata tana tahowa, kalli wata uwar kiba!" Har Wanda ma ba dasu yake ba dukka Suka juyo suna kallo na, a take na Fara Jin wani irin yanayi, kamar kasa ta tsage na shige, ko Kuma na ruga a guje na buya Amma Babu halin hakan tun da na riga da na taho. "Yanzun fa se tace ita budurwa ce, Ina salis shi ne me son masu kiba" Ina tunanin wannan shi ne salis din yace " Kaiiii! Barta dai yau waye zai aura wannan abun, ruguzaza!" Kunsan wani lokacin kana ji Amma se kaki ji, ka gani kaki gani. Akwai wani human instinct da mutum yake da shi, ability mutum ya saurari abin da yayi niyya. Haka nan na blocking kunnuwa na daga sauraran munanan kalaman su. Bayan na koma gida na tsaya a gaban madubi, Ina kallon Kai na, ta Ina Zan Fara rage wannan kibar? Ta Ina Zan Fara gyara wannan fuskar tawa? Me yasa nake muzanta cikin mutane. Kawai s na Fara kuka a gaban mudubin, nasan Ina da kiba, idan ka kalle ni dukka kiba ce amma to ya zanyi? Ta Ina Zan Fara? Rashin Sanin yadda zanyi yasa kawai na hakura na cigaba da muamula ta da BashPrince00. Ana Haka Muka koma makaranta mukai jamb, Kuma cikin hukuncin Allah se gani da over 200 score. Nayi murna na Kuma godewa Allah babu iyaka. A Haka dai Muka Fara waec Wanda yasa Muka Fara zaman extension. Wani dare mun Yi chatting da BashPrince00 yayi min albishir din zuwa ya ganni da weekend. Murna da na dinga Yi na kasa tsayawa har safiya tayi na bawa Samiha labari me dadi, a Daren na wuce dakin su na samu tana kwance tana waya, na zauna gefen ta Ina sakin murmushi Wanda tana gani tasan it's something to do with BashPrince00, Dan tasan shi kadai ke sani irin wannan farin cikin. "Bani labari! Me ya faru?" Cikin murna da zakwadi nace " He's coming on Saturday!" Na fada Ina jujjuya Kai na cikin farin ciki, tayi murmushi tace " Finally wata zata ga habiebie dinta" Nace " Wallahi! I'm so excited Amma Kuma tsoro nke ji" Na fada har tsoron Yana bayyana a fuskata. Ta Kara gyara zaman ta tace " Tsoron me kike ji? Why are you afraid?" Nace "Mhmmm! Idan yace ban Yi Masa ba fa? Idan yace nayi kiba da yawa fa?" Tayi murmushi tace " Ba zai ce ba, ai ke yake so ba wai jikin ki ba, Kuma ya yadda Yana son ki irrespective of kamar ki ko jikin ki. Kullum ina fada Miki BinGin you've a good heart, duk Wanda ya aure ki yayi nasara, your soul is beautiful kumma wallahi fuskar ki Bata da Muni, jikin ki baiyi Muni ba, kullum Ina fada Miki cherish what you have, shi wannan jikin da wannan fuskar kyauta ce Allah ya Baki. Kiyi alfahari da jikin ki, feel proud about it ki daina sunkuyar da Kan ki, kiba ba laifi bace ba!" Ina ma ace kowa yana tunanin da Samiha take, inama ace kowa mind din shi irin nata ne, Ina ma kowa idea din shi da view din shi akan kiba irin na Samiha ne. Kilan da ire ire na bamu ji rayuwa tayi Mana zafi ba. Har wajen daya Kuna ta shirye shirye da ita, a Karo na farko naji confidence a cikin rayuwa ta, naji cewar Nima mace ce Kuma I can stand out gaban kowa. Muna ta shiru har Saturday tayi wadda ta kasance ranar visiting, dama nace dasu Adda ba se sun zo ba duk wahala ne, Dan su akwai kokarin zuwa visiting, sun dauke shi kamar wani Abu daban. Nayi wanka wajen karfe goma, na shirya cikin goggen house wears di na, na shafa powder na saka khol tare da saka lip balm a lebe na, wannan Shirin da nayi is once in my life, bana saka powder saboda Ina ganin powder daban fuskata daban. Balle Azo zancen su foundation ko wani concealer, Tun ranar dana taba saka foundation zamu je biki Hadejia, na saka skirt da Riga na yafa veil irin yadda suke yafawa, Ina fitowa Zahra ta kalle ni ta tuntsure da dariya, dariyar ta ta janyo hankalin Adawiyya da tazo Dan mu tafi tare, itama ta Fara kyakyatawa " Wai Bintu waya ce Miki kiyi wannan kwalliyar? Kin taba ganin mutum yasa foundation ba irin skin tone din shi ba" Zuhriyya da ta gama waya lokacin tace " Ku bar ta dai ai, ita Abu ba kadan ba kiga wani yafen mayafi da tayi!" Gaba daya naji am humiliated, naji na kasakanta na Kuma wulakanta. Nayi shiru rooted to the ground na kasa moving an inch, suka cigaba da hirar su Akan kiba da yadda Basu son ko kadan suyi gaining weight. Kun San ranar wallahi Hadejia da banje ba kenan. Kuma tun daga wannan ranar ban sake ko da wasa shafa powder ba, ko da kuskure in fact wallahi make up stuffs di na dukka na tattara na bayar da su! A ranar saboda rashin confidence, kasa kallon madubi nayi, saboda kada Naga abin da zai saka na wanke fuska ta. Ina nan tsaye Samiha ta shigo da gogaggen house wears din ta, ba wani Abu ta shafa ba Amma tayi kyau sosae, se naji Ina tsoron kada muje fa ta kwace min habiebie. Se Kuma na kawar da wannan tunanin daga Rai na, a duk duniya Samiha ita ce wadda na Fara trusting, nake Kuma tsamannin ba zata taba ha'inta ta taba, aikuwa muka fita tare Bayan ta Gama "Ma shaaa Allah! Whoa! Wow! Kin gan ki kuwa BinGin, shiyasa nake cewa kiyi kwalliyya, Baki ga yadda fuskar ki tayi ba" Nayi murmushi Ina Jin Dadi tare da Jin wani nervousness na yadda haduwa ta da BashPrince00 zai kasance. A Haka dai muka tafi bayan ya Kira ya tabbatar min da zuwan shi. Muna tafe Ina haduwa da colleagues di na suna fada min nayi kyau ko dai BashPrince00 zai zo ne. Duk da ban Faye magana ba, ban Kuma faye shiga mutane ba Amma Ina yawan maganar shi har ta kasance Yan class din mu sun San shi, sun Kuma San yadda nake ji a tattare da shi. Visiting din mu a katon visiting hall ne wan da school ta ware domin hakan. Na Shiga ciki tare da Samiha Ina Jin wani irin yanayi saboda cikar mutane a gurin. Amma da ke kusa da Samiha nake I felt a lot relieved. Na wuce ciki Ina wuwwula idanun Inga ta inda Zan hango shi, ku kwace na San shi, wayar dake hannu na ta Fara vib, Cikin salo yadda wani ba zai gani ba na Kara a kunne na nace "Ban ganka ba" A hankali na hango wani can extreme a zaune, Yana waving hannun shi. A take naji dukkan jiki na yayi sanyi kamar an datse min gwiwoyi na Haka naji. Kunsan kalmar "elite?" Kunsan kalmar "butter?" To wadannan biyun su ne kawai kalmomi da zaa iya describing BashPrince00. Samiha ta saki murmushi tana rada min " Kai ba dai wancan shi ne BashPrince00 din ba?" Ni dai na kasa magana, har Muka karasa in da yake zaune, fuskar shi dauke da wani murmushi da kullum nake mafarkin gani, Ni kuwa na taba ganin namiji me dimple a rayuwa ta? Kai Anya kuwa? Inaga ban taba gani ba se Akan shi. Dimple din fa sosae fa Kuma both side, ba fari bane ba Amma kunsan caramel? Kunsan abin da ake cewa wancan caramel skin ne da shi? To Bari na fada muku caramel consist of butter, honey and sugar! Ku tuna irin sheki da shining din da caramel zaiyi, to kamar Haka skin din guy dinnan yake, ga wata gargasa da ta kayata wannan shiny skin din, ya zanyi na kwatanta muku BashPrince00 ni kuwa? Kawai jikin shi, kayan shi da komai nashi speaks of handsomeness, he's beautiful jama'a, ku manta ance beautiful is meant for girls, a'a fa yau fa shi ne kadai word din da zanyi muku kwatancen BashPrince00 da shi. Se murmushi yake da nake kallowa kasa kasa yayin da yake narkar min da zuciya ta. To Bari kuji kamannin Samiha, a'a ai na tuna na fada muku kammanin ta ai a other chapters, ta tunkuda ni Wanda yasa na Isa gaban shi babu shiri, na tsaya gaban shi Amma to my utmost disappointment hankalin shi da wannan murmushin Yana Kan Samiha... Wayyo ni BinGin! Kamar kullum kada ki Bari labarin BINTUN BATUUL, NAZNEEN da kuma GENERAL NASEER ZAKI ya wuce ki, kunsan dai tafiyar ba yau aka Fara ba, wannan season 3 ne! [1/3, 20:28] Maman: 016 Amma Kun San da gaske idan zaka aikata babban zunubi da gaske imanin ka tafiya yake, a lokacin da nake zaune gaban locker da Kuma kwalbar Dettol a hannu na, gaba daya bana ji bana Kuma gani, kawai abin da subconscious mind di na ke fada min, Bintu Ginsau kisha, kada ki tsaya, gwara ki kashe Kan ki ki huta da wannan bakin cikin, idan kin mutu ma Babu Wanda zai damu, Babu wan da zaiji wani Abu. Wannan zuga da zuciyata tayi min yasa hannu na na rawa

Chapter 6 of 18