Wanda nasan dani take, dama kokarin fita nake tace
" Wuce kije ki Kira min kawun ku da Maman ku"
Ita fa Haka Iya take, matsawar idan tazo gidannan to se kowa ya koma hankalin shi, bana mantawa akwai wani zuwa da tayi ta samu ana ta zabar kayan sallah Ina daki a zaune, ta Fara tambayar Mamaa ni Kuma fa? Se tace ai Ni bana zaba saboda Kaya na daban kawu yake kawowa tunda ni baka ce. Ta bude idanun ta, Ina Gaya muku katsinancin nata ya motsa. Ta Fara fada tana tambayar su ko sun bawa Allah wani Abu ne da yayi su farare, dama har wani dadi ne ko afuwa ne Akan zaman ka fari. Kusan ranar yini tayi tana fada har kayan da aka kawo min se da aka mayar kasuwa aka canjo min, danma dai shagon Kawu ne.
To daga hajja har Iyan KT dukka basu shiri da Batuul, dukda tafi zuwa inda suke Amma Basu shiri saboda wani dalili da ban sani ba. Haka naje na Kira Mamaa da Kawu, suna tare ma tayi Masa serving abinci. Tunda suka Shiga suka zauna take fada akan Batuul saboda dukkan su sunsan ta tafi makaranta Amma Basu ma San ta tafi gidan sajida ba. Karshe da lallami kawu ya Kira sajida wadda ta tabbatar Masa tun maghrib Suka rabu da Batuul ta taho gida
" Kun bani kunya, har yaushe yarinya daya ku kasa kula da ita, wannan ya tabbatar min cewar Haka take kullum, Kuma Baku ma sani ba. Yaushe lalacewar ku ta Kai haka Hamisu, Asiya da Rukayya! Batular nawa take da zata gagare ku?"
Dake hajja Bata da fada, shiyasa maganganun ta ko fada take to kamar nasiha take, Kawu da kowa dukka sukai shiru ga shi sun kasa samun ta a waya, Nima Kuma Ina parlor se Kiran dayar number ta da duk gidan Ni kadai nake da ita, Nima wani birthday party zaayi na friend dinta shi ne ta Kira Ni da shi da suna min kwatancen in da zaa Kai musu cake shi ne Dana gane contact din ta ne nayi saving.
"Wai menene kike damu na"
Shi ne abin da ta Fara fada da ta dauka, kawai Dan bani da saurin fushi, Kuma Ina da hakuri bacin Haka da tuni gaba ce tsakani na da wannan marar mutuncin. Nace
" Batuul kina kallon lokaci kuwa? Ina kike?"
Daga yadda take maganar nasan ranta a bace yake tace
" Ina gidan sajida Mana yanzun Zan taho"
Ban Karya ta ta ba saboda ni bansan an Kira sajida ba, nace Mata tayi sauri ta dawo saboda Kawu na neman ta, ai shi Bata Gama Raina shi ba. in no time zakuga ta dawo!
" Sannan me yasa auren Batula kawai zaayi Banda Bintu?"
Hajja ta tambaya, Adda tace
" Batuul ce kawai ta samu miji, ita kawar taku ko saurayi Bata da shi, sannan wannan yaron Suleiman muka so hada ta da shi Amma tayi ta Masa wulakanci..."
Ai kuwa Adda Bata San ta ballo ruwa ba, Iyan KT tace
" Ita din BINTUN ba Yar ku bace ba? Tsinto ta kukai? Dan me zata Yi soyayya da abin da Yar uwar ta ta Bari? Wai ku a gidannan kanku daya kuwa? Wanne irin rayuwa kuke? Kun bani kunya, ta Yaya zaku fifita wasu daga cikin yaran ku Akan wasu wannan ba daidai bane ba. Itama kawar tawa tana zaune mijin ta tsalale na idon duniya zai fito, Kuma ba Baki nayi muku ba Allah ya sakawa Bintu kada kuga Kun haife ta, akwai hisabi tsakanin iyaye da yaran su. Ku fita ku bamu waje!"
Dukka suka Mike suka fita jiki a sanyaye, har lokacin Ina parlor Ina jiran Batuul wadda ta sake Kira na Akan Ina Kawu, nace Yana daki tayi sauri ta shigo. Cikin rashin saa tana shigowa suna fitowa su kuma, sukai kicibis akace Wai kicibis mugun gamo! Ran shi dama a mugun bace yake, Ina fata Baku manta kawu da zuciya ba dukda ba sosae yake nuna hakan ba, Yana zuwa ya dauke ta da mari Yana fadin
" Daga gidan uban wa kike? Ina Kika je se goma kike dawowa?"
Marin ya girgiza ta ba kadan ba, Dan har Jakarta da Bata Gama rufewa ba Bayan ta karba kudi hannun honorable ta Fadi a kasa, a take kudin Suka fito, dukka Mamaa da Adda Suka bude bakin su suna fadin wannan wanne irin tozarci ne cikin dare. Kafin ta Kai hannu ta dauka har ya dauka, mint ne na 1k wrapper guda biyu, ai Ina Gaya muku wannan Daren kusan kashe Batuul yayi, duka dai seda hajja da iya da Kuma wani makwabcin mu suka so kafin aka kwaci Batuul hannun shi, kawu Bai hakura ba ya shigo dakin mu Dan ita se rusa kuka take ta gudu dakin Auwal, Ina tsaye Ina kuka saboda hankali na ya tashi na Kuma tsorota da dukan yace
" Ina ne wajen kayan ta!"
Hannu na rawa na nuna Masa, aikuwa ya bude ya dinga watso da kayan kasa, kudi Nadi Nadi Haka Suka din ga fadowa, kunsan se da aka hada kudin sun Kai 900k, ai Adda se ta Fara kuka, ana bude Jakar ta se ga mukulin wata Benz ya Fado, innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Munga tashin hankali wannan Daren Wai Saar mu saya sirikan kawu na nan, se da suka ji inama Basu ce Ina Batula ba da kilan hakan Bai faru ba. Tun da yaga key din motar ya ciri igiyar shanya ya nufi dakin Yaya Auwal ya fito da ita, tana ihu ga lokacin gari yayi shiru Bayan dare Kuma layout ce, kunga kowa na gidan shi, anan tsakar gida yace a gaban kowa ta Fadi motar waye? Da farko tace ta kawar tace, da ya zuba Mata wannan igiyar guys se tace
" Kawu wallahi tawa ce, tawa ce !"
Yace
" Uban waye ya siya Miki?"
Tana ihu Yana tafkar ta tace
" Honorable ne!"
Lokacin dukan yayi yawa har ya samu fuskar ta, nayi ta maza ganin kowa tsoron magana yake masa, na rike bulalar na tsugunna har kasa nace
" Kawu Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah!"
Kilan shima jira yake wani ya Hana shi, kunsan dai yadda kawu yake son Batuul, Dan da amincewar shi Batuul ta ruguza maganar Suleiman Dan abokin shi. Ya yarda bulalar sannan ya wuce dakin shi, Nima naja hannun kawaye na muka tafi, kowa jikin shi a sanyaye yake. Muna zuwa har sun kwanta se ga Batuul ta shigo har lokacin kuka take, tana shigowa Ina tattare Mata kayanta, warcewa tayi daga hannu na tace min
" Munafuka kawai!"
Sannan ta nufi gadon ta kafin ta hau ta hangi iya da Kuma hajja a gado na dake nawa na da girma tace
" Anan zasu kwana! Aikin banza uwar shishigi duk se kin da dakin mu yayi warin tsofi!"
Tana fadin Haka ta fice ta barni da Jin kunya, hajja tace
" Wannan yarinya iyayenta sun lalata ta da yawa!"
Ta_kwalam ce
Be reminded that BINTUN BATUUL is not free, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI! They're still ongoing with as low as N1300.
[1/3, 20:28] Maman: 037
A wannan Daren bana tunanin a cikin gidannan akwai Wanda yayi bacci me Dadi kowa bacci dai se barawo Wanda sukai Kuma cikin dare da sun farka abin da ya faru zai Fado musu. Washegari da wurwuri nayi ma kawaye na breakfast, ba tare da na jira kowa ya tashi ba nayiwa su hajja sallama na tafi makaranta, ranar ta Kama Friday amma Zan fita saboda akwai lecture daya da nake da ita. Se Bayan na fita sannan na duba waya ta Naga message din Alamin Akan the class will not hold so it will be a free day! Wani rashin Dadi naji saboda bayan na fita abubuwan da Suka faru a class din Dr Akram se Suka dawo min, rudanin jiya da yasa na manta komai se gashi ya lafa yanzun se Kuma asalin damuwa ta ta dawo! Haka na koma gida badan na so ba. Na samu Kawu Bai fita ba, Haka Adda ma, dukkan su suna parlor an rutsa Batuul ta Fadi inda motar take, could you imagine motar tana gidan zuhra, Ashe can ta maida ta. Nan kawu ya Kira mijin zuhra akan su zo Yana neman su, Haka shima honorable din Kawu ya Kira shi sede baya gari yabi earliest flight to Lagos, Dan Haka Kawu yace Masa to ya fadawa masu kawo kudi su wuce Hadejia Kuma biki ya fasa saka watanni shida kamar yadda Honorable din ta nema, ya maida shi wata biyu.
Ita Kuma Batuul hatta school din ta sede Auwal ya Kai ta ya dakko ta, duk wani Wanda zata hadu da shi ya kasance a gida ne. Har lokacin kuka take yi, ta bani tausayi sosae da sosae yadda Baku tunani, Koda dai ta kasance a wayward child Amma ai ba laifin ta bane ba ita kadai, laifi har da iyayen mu Dana yayin mu. Ai kamar yadda hajja tace ne, wani lokacin idan yaranka sukai aure sukan canja, sukan Zama dafi ga yaranka da basui ba. Ku kalla dai yadda zuhra ta yadda Batula tayi ajiyar motar ta a gidan ta, for only God knows when, Allah kadai ya San tsahon lokacin. Kuma yawan fitar da suke da ita da yadda suke nuna Mata ita me kyau ce tayi amfani da kyanta na daya daga cikin abin da ya sake hatgitsa tunanin ta!
Bangaren Akram, bayan shi da Alamin sun kammalla tattare dukka answer sheets din mu, ya dube shi yace Kai min office di na, messenger ya bude maka, Zan karaso Jima yanzun. Alamin yayi yadda akace sannan shi Kuma Akram ya fita Dan duba ni, Amma cikin rashin saa ko wata me mustard yellow din hijab bai gani ba, yafi mintina biyar a tsaye kafin yayi concluding na tafi, shima se ya wuce zuwa office din shi, inda ya tarar dukkan papers din mu aje akan desk din shi. Ya zauna Yana ayyana dalilin da yasa na tafi da wurwuri Haka, he thought that we're friends Amma se yaga au shi ne Bai kula ni ba. Kam shi ya shafa daidai shigowar Kiran Ummaan shi wayar shi, ya gyara Zama ya dauka bayan sun gaida ta sanar Masa ai Alhaji Gidado ya samu sauki an dawo da shi gida, yayi musu murna sannan ta tambayi yaushe zai dawo, yace ai se dare saboda Yana son marking test, se ta sanar Masa zata Aiko Masa abincin shi kawai! Har ya kashe se gashi ta sake kira, Bayan ya dauka tace masa
"Ina Bintu Fatima?"
Yayi murmushi yace
"Baki manta sunan ta ba? Ban Jima da barin class dinnsu ba"
Tayi murmushi tace
"Ya Zan manta Bayan ita ce mace ta farko da ka taba bani labarin. She must be sweet tunda har idanun yaro na ya sauka Akan ta!"
Yayi murmushi, baisan dalilin wannan dadin da yake ji ba yace
"Ummaah, Zaki so Fatima idan Kika ganta, idan Kika zauna da ita Zaki ga how pure her heart is!"
"Yaushe zaa kawo min ita? Na ganta mu gaisa!"
Ya bude Baki Yana murmushi yace
" Kai ba zata yarda ba Ummaah, na dai hada ku a waya watarana"
Uwar tashi tayi murmushi ba tare da ta Kara cewa komai ba, sukai sallama Akan se sun hadu anjima. Aikuwa Babu jimawa se ga driver ya kawo Masa abinci, ya karba Yana me Yi Masa godiya, kafin ya Fara ci seda yayi wa Kan Shai gwajin jini, bayan results din ya fita saman Dan censor din se ya bude madaidaiciyar warmer din, alala ce hadadiya , wani karamin flask Kuma anyi Masa vegetable soup wadda zata tafi da alalar, ga jug shake da kunun Aya. Sosae yaci sannan ya bawa messenger din wajen ya Kuma Fara marking. Yana ta tunanin menene reg. No dina Amma ya kasa tunawa tunda dama ba sani yayi ba. Se ya dauki wayar shi ya Fara kokarin Kira na, yayi ta scrolling Amma ya rasa me yake yi ko Kuma dalilin hakan. Then it down on him cewar bashi da contact di na gaba daya. Se ya Fara dariyar abin da ya faru, instead kawai se ya Kira Alamin da niyyar yace masa ya tura Masa contact dina Amma Yana dauka se hankalin shi ya dawo jikin shi, ya kasa tambayar sa contact din instead se cewa yayi ya Kira yaji ko Yana school akwai aikin da zai saka shi, se yace Masa ai ya tafi tun dazun, Amma zai dawo yanzun, se yace Masa
" Nooo... Ma hadu Monday. Thank you!"
Daga Haka sukai sallama ya aje wayar tare da dafe Kan shi Yana tunanin what has gotten into him shi kuwan? Why is he so desperate Akan son Jin muryar Bintu ne, a ran shi ya ayyana ai shi therapist din ta ne, Dan Haka ko Yaya ya fahimci slight change a mood din ta, ya kamata ace ya tambayi dalilin hakan.
Har ya koma gida Bai samu wani kwakwaran dalilin neman number ta ba, se kawai ya wuce gida ba tare da Jin Dadi ba. Yana shiga abinci kawai Suka ci Safiyya ta saka shi a gaba Suka tafi side din Alhaji Gidado Dan duba shi, tasan tabbas idan ta bar shi ba lallai yaje ba, Kuma hakan Bai kamata ba. Suna zuwa suka tarar yana cin abinci, suka zauna har ya Gama saboda ba Wai ta daina mulki bane ba, dukda mulkin na shi yaran shi da jikokin shi yake yiwa kawai, Ina wannan Yan bana bakwai din zasu amince da wannan mulkin mallakar, wasu ma daga ciki ko aure sukai Basu Zama a apartment din Gidado community, waje suke fita su Zama independent, wasu ma Adamawar duk suke komawa. Bayan ya kammalla ya amsa gaisuwar su sannan ya dubi Safiyya Dake kokarin fita Dan bin Bayan Akram da ya Riga ya fita, cikin fullanci yace
" Kun shafa min bakin penti a fuska, yaron ku Kiri Kiri yake nuna ko ganina Bai son Yi"
Tayi murmushin Jin kunya tace
" Ba Haka bane ba Grandpa, kasan Akram yadda yake ko da sauran cousins din shi!"
Ya tabe Baki yace
" Ai nasan Yana fushi Dani Akan abin da ya faru da uwar shi zainab ne ko? Amma ai ba wani laifi nayi ba..."
Tayi saurin juyawa Dan ganin ko Akram Yana nan ko ya tafi, ta saki ajiyar zuciya ganin baya nan tace
" Ayya Bai masan komai akan mahaifiyar shi ba, kamar yadda Bai taba tambayar wadda ta haife shi ba, dukda nasan yasan bani na haife shi ba"
Shigowar Uncle Ali yasa tayi.masa sallama ta tafi, Akram na tsaye Yana jiran ta se gata ta fito Suka wuce. Washegari Friday, very early ya fito Dan zuwa office, slice of wheat bread kadai yaci da wani spread din su na masu condition irin na shi, Amma sede ajin na su babu kowa, se ya Kira Alamin ya tabbatar Masa ai ba su day class ne. Washegari ya gaji da wannan wasan Dan Haka kawai ya rufe idanu ya saka Sadiq ya tura Masa contact Dina. Ina tsaka da aiki a daki Dan zaman lafiya a gidan ya Dan wanzu har kawaye na sun tafi, nasan mun kusa Fara exams dole na dage da karatu. Unexpectedly se kawai Naga Kiran shi, bansan waye ba kamar yadda kuke tunani, Ina dagawa yace
" Fatima!"
Yana fada nasan shi ne saboda shi kadai ke Kira na da Fatima ba Bintu ba. Nayi saurin aje gum din hannu na nace
" Sir Ina wuni?"
Yayi murmushi yace
" I'm good fatima!"
Wai Kuma dukka se mukai shiru se shi ne yace
" Kina ji na?"
Nace Masa Ina Jin shi, ya gyara zaman shi yace
" Kawai Ina son naji yaushe zamu Gama session din mu? Ko you're busy!"
Nayi saurin ture kayan da nake hada delivery box da shi nace
" No Babu abinda nake sir! Mu cigaba"
Kunsan dai yawanci Wanda sukje zuwa therapy session Basu kaunar session din Amma ban dani, I was excited ma da zaa cigaba. Ya sake rike wayar a kunnen shi Yana gyara zaman shi saman couch yace
"Ina jinki"
Yau ko musu Babu nayi relaxing baya na a pillow na Fara bashi labari na tun daga abin da Zan iya tunawa har zuwa yanzun! Kunsan se banyi kuka ba, da alama dai zuciya ta ta kekeshe, nayi shiru Ina maida ajiyar zuciya me nauyin gaske nace
" This is all I went through sir! Ban sani ba ko inada laifin discriminating di na da akai a gidan mu, mutanen gari da suke criticizing dina Akan abin da bani da laifi"
Yace
" I'm sorry!..."
Kawai haka yake fada saboda gaba daya zuciyar shi wani irin yanayi yake ji da ba zai iya misalta shi ba...
Ta_kwalam
[1/3, 20:28] Maman: 38
Somewhere in Nigeria
Gloves din hannun shi yayi saurin cirewa tare da tashi daga Kan cadaver da yake examining, wayar shi ya dakko da take ringing a Karo na biyu, Yana dubawa yaga Babu number se de anyi hiding din caller ID din, ba tare da damuwa ba yayi swiping green ya dauka tare da karawa a kunnen shi Amma baiyi magana ba, daga dayan bangaren cikin harshen turanci Wanda kana Fara sauraro zaka San turancin second language, saboda yadda take fitar da kalaman zaka fahimci akwai wani yaren da ya riga yayi staining harshen ta.
"Sadik Garba?"
Ta tambaya a hankali, yayi murmushi dan a take ya fahimci wacece, wannan kusan shekaru uku rabon da ta Kira shi, Bata taba barin ID din ta a bude ba, so idan ba ita ta neme shi ba, Babu yadda zaayi ya neme ta.
"Ma'am kwana biyu!"
Tayi murmushin Jin har ya Gane ta tace
" Ina lafiya! Ya Akram yake? Ya jikin shi? Yayi aure? Ya Gama makaranta?"
Yayi murmushi Yana zama nesa da examination table din da cadaver yake Kai yace
" Akram Yana lafiya, Babu wani episode da ya samu a shekara biyu da Suka gabata. Ya samu aiki Yana lecturing a wata prestigious University!"
Wani farin ciki ya saukar Mata tace
" Baiyi aure ba?"
Ya girgiza Kai yace
" Har yanzun dai babu wannan maganar a kasa!"
Ta gyada Kai tace
" Nagode! Bank details din ka sune har yanzun?"
Ya gyada Kai, kafin yayi Mata sallama har ta kashe wayar!!!
***
"Fatima!"
Ya fada a tausashe, na Dan ja numfashi kadan nace
" Sir!"
"Yana cikin abin da mu Dan Adam mukai lacking, da farko se kin so kanki kafin wani ya soki, you've to accept yourself before others accept you! Fatima Mata nawa ne suka fiki kiba, Suka fiki baki Amma suna rayuwa cikin farin ciki? Kinsan me yasa? To saboda sun rufe kunnuwan su Kuma suna alfahari da yadda jikin su yake, kema da haka kikai bana tunanin abin da mutane suka fada zai dame ki. Shi Dan Adam da Kika gani ko ubangiji da ya hallice shi baya iya Masa, Dan Adam bawa ne marar godiya, baa iya masa komai se yayi magana. So you can never impress people just impress yourself kiga yadda mutane zasu manta da sunyi criticizing din ki!"
Maganganun shi sun shiga kunnuwa na, Kuma sunyi sinking cikin Kai na, Kuma Haka ne tabbas idan Kai baka so kanka ba, kayi alfahari da kanka ba to duk duniya Babu me yi maka hakan, for the world to recognize you, you have to accept yourself. To Amma ta Ina Zan Fara ganin Kai na a matsayin Nima na Isa?
" Sir it's hard!"
Yace
" Na sani Fatima, shi ne next abin da zamuyi. So yanzun Naga an kusa daura lunch, don't just stay in your room. Go and help out!"
Nayi murmushi Wanda I'm sure yaji sautin shi nace
" Sir nagode! Sir nagode!! Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, thank you so much sir, I'm very grateful ! Nagode..."
"A'a tun kafin session din ya Kare, kada ki damu anything for you. Just make sure you saved my contact kinji!"
"Right away sir!"
Na fada Ina Jin wani Abu a kirji na, da wani farin ciki me sakawa kaji kamar a gajumare kake... Bayan na kashe wayar se na Fara kokarin saving contact din nashi, Amma bana son saka sunan shi, nayi ta kawo sunaye cikin Kai na Amma a karshe se nayi Masa saving da *Noor* kunsan me yasa? Saboda a rayuwa ta Akram haske ne da ya haska tawa rayuwar , ya Kuma haska min hanyar da nake takawa.
A bangaren shi kamar wani Wawa Haka bakin shi ya kasa rufuwa, dukda tausayi na na gaske da yake ji Amma se yake Jin zuciyar shi is light like a feather, yake Jin kamar yayi ihu saboda murna Amma se yake kokarin suppressing hakan ta hanyar murmushi kawai. Sallamar Safiyya tasa yayi saurin aje wayar tare da mikewa har lokacin curve din da labbansa sukai saboda murmushi ya kasa gushewa, bayan ta aje tray din data shigo da shi ta zauna, shima ya zauna Yana gaishe ta, ta amsa tana fadin
" Menene labari, saboda fuskar ka ta nuna akwai abin da ake so a fada min!"
Yayi dariya yace
" Ummaah ya ake Gane idan ana son mutum?"
Ta dan bude idanun ta da kyau tana kallon shi, da farko mamakin tambayar tayi Amma a karshe adduar ta Allah yasa ya samu wata Yana son ta ne!
"Mhmmm! Ya danganta da me kake ji. Can you share with me?"
Ya gyara zaman shi, Dan Yana daukar Safiyya tamkar kawarshi ba mahaifiyar shi ba, saboda itama kamar aboki ta dauke shi ba dan ta ba.
" Ummaah Ina kin tausayin ta sosae da farko, ko na rabu da ita lokauta da dama se naji Ina son sanin me take Yi? Ko Kuma me yake faruwa da ita a wannan lokacin? Ummaah idan Ina magana da ita I feel the happiest a rayuwa ta and I cherish every moment da mukai magana da ita. Idan bata kula ni ba, Ummaah hankali na tashi yake. Kwana biyunnan I've checked har Google ko Zan ga da gaske son Fatima nake Yi"
Safiyya har lokacin Bata dai na murmushi ba, Dan ita din sarauniyar hakan ce Kuma hakan weapon din ta ne, tace
" Son ta kake, wannan shi ne feeling din soyayya Akram"
Se taga murmushin fuskar shi ya dauke, kamar tsoro ta gani saman fuskar shi Wanda ya Bata mamaki tace
" Are you scared? Why"
Yace cikin rauni
"Ummaah ta Yaya zata aure ni Bayan Ni bani da lafiya?"
Tace cikin kwantar da murya
" Kayi Mata bayani? Kace Mata kana da diabetes?"
Ya girgiza Kai yace
" I'm scared Ummaah! Kar tace ba zata iya daukar wannan burden din ba"
"Ba zata ce ba, Kai fa kace min she's very good,she has a pure heart ko? To kayi kokarin winning tata zuciyar. Ai nasan ba se na koya maka ba ko?"
Yayi murmushi a kunyace, Yana son Safiyya yadda take Kara karfafa Masa gwiwa. Gaba daya ranar Haka ya karasa ta cikin walwala da annashuwa, ji yake kamar ya tsinci hakori...
🎵🎶 _So idan ya Kai so, abin da baka zato kake yi_
_Baka gane haske balle duhu se ka sauka layi_
_Al'ajab na so ko da wanne lokaci ya kanyi sauyi_
_Bai da tausayi, Dan kuwa Bai barin gangar jiki cikin sauki_ 🎶
"Abbaa"
Safiyya ta Kira sunan Imam a hankali lokacin da ya Gama Shan tea din shi na kullum kafin ya kwanta, ya dago ya kalle ta Yana kokarin plugging system din shi jikin socket, ya juyo yace
" Akwai magana ne?"
Ta gyada Kai, hakan yasa ya koma ya zauna tare da Bata dukkan hankalin shi, tace
" Akram dazun munyi magana da shi, da alamar ya samu yarinyar da yake so..."
" Yar wacece?"
Tun da ya Fadi hakan ta fahimci yayi tunanin a nan community din su yake nufi, tayi murmushi tace
" Amma kasan barewa ba zatayi gudu Dan ta yayi rarrafe ba ko?"
"Me kike nufi"
"Eh Ina nufin outsider ya samu, Kuma nayi Masa alkawarin nu da Kai zamu Goya Masa baya dari bisa dari. We need cross breeding!"
Imam yayi murmushin cross breeding din da tace, yace
" Shi kenan, idan ya Baki details din yarinyar se na saka ai launching bincike akan ta ko?"
Se ta saki ajiyar zuciya tace
" Duk ba wannan ba, yaushe zamu fada masa shi din Yana da wata uwar bayan ni. Nasan yasan bani na haife shi ba, Amma Akram yayi min Kara da Bai taba nunawa yasan bani na haife shi ba. So Dan Allah Abba Ina son muyi Masa bayani, he owes
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 18