Yi Masa marhaba da Dan guntun larabcin da ya Dan tsinta only God knows where? Amma fur Akram yaki zuwa, dole Haka Suka tafi. A gida Safiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye, shiri take sosae na tarbar mijin ta, ko kadan Bata da masaniyar zaa dakko Akram ne, ita tunanin ta ma wani abun Suka tafi.
A gajiye ya shigo parlon Akram na biye da shi da katuwar beach ball a hannun shi, Safiyya ta taho tarar shi amma tana ganin yaro taja ta tsaya tana kallon yaron tana Kuma kallon Imam questioningly, ya Dan zauna Yana fadin
" Daga Qatar muke, Akram ga Ummaah ka go to her!"
Das das ya nufi Safiyya da take ta kallon yaron idanun ta sun ciko da kwalla, gashi dai yaron Kama yake da Imam sosae amma Kuma akwai features din shi da suke nuna shi din Dan zainab ne. Ta tsugunna daidai tsawon Akram ta bude Masa hannun ta, abun mamaki ya karasa ta rungume shi tana kuka, ga ikon Allah, kenan zainab da ciki ta tafi kenan? Shiyasa take ce Mata ta dafa Mata zobo da tuwa miyar taushe. Kankame shi tayi sosae a jikin ta . Imam ya dube su ganin Akram ya shagwabe fuska zaiyi kuka yace
"Wife zaiyi kuka fa!"
Tayi saurin sakin shi tana dariya hade da share hawayen fuskar ta, yau Kam tana cikin tsananin murna ta dago ta Fara tambayar shi inda maman shi take, yace cikin turancin shi da larabcin Qatar ya gurbatar yace
" She's home!"
Ta dubi Imam tace
" Ba tare kuka zo ba? Acan ka barta? Me yasa ka barta baka taho da ita ba"
Yayi shiru Kan shi ciwo yake, Bai son magana a wannan lokacin, gaba daya Kan shi a cunkushe yake. Yace
" Wife Zan yi Miki bayani, na gaji I need to rest!"
Tayi saurin bashi hakuri sannan ta ja hannun Akram ciki, tayi Masa wanka ta bashi abinci sannan tace ya kwanta ya huta. Se dare suka samu magana da Imam, yayi Mata bayanin abin da ya faru, a Karo na farko yaga fushin Safiyya tace
" Ka bani mamaki, har yaushe zaka biyewa wancan tsohon kuyi Haka? Ya zaka raba uwa da danta ba tare da Sanin ta ba, iko da takamar ka danka ne ko? To baka kyauta ba, bakai Mata adalci ba ko kadan"
"Na sani wife bansan ya zanyi ba, nima hankali na ba'a kwance yake ba, I'm guilty tension"
Fushi ma babu abin da zaiyi ko kadan, Dan Akram da shi kan shi Imam abun tausayi ne. Haka Safiyya ta zame ma dukkan su sanyin idanuya, a hankali tun Akram Yana tambayar imam yaushe zasu je gurin Amma har ya daina. Imam ya koma Qatar din a zuciyar shi wannan karon zai gyara dukkan kurakuren da yayi a baya, dole ne ya dawo da zainab rayuwar shi, Amma kaddara wata abace da baka da say akan ta, baka San ya zakai ba. Yana zuwa ya tarar zainab bata nan, Babu Kuma Wanda yasan inda ta tafi, a wannan kasar da Bai San kowa ba Kuma ba shi da kowa Ina zai Fara neman zainab shi kuwa? Haka yayi sati Yana garari inda ya samu labarin family business din su da take kula da shi tayi hiring sabon manager dan ya kular Mata da komai, Amma su dunma since Basu San inda ta tafi ba.
Akram Yana girma Yana Kuma rayuwa cikin Jin dadi, har lokacin Bai sakin jiki da mutane sosae, shiyasa ko school Imam ke kaishi ya dakko shi ko Safiyya, baya bin bus din family da take sauran yaran. I'm fact makarantar shi daban Imam ya saka shi da sauran, gani yake tunda yaran Bai son relating da kowa da yawa gwara ya nisan ta shi. Dukda hakan a cikin yaran gidan akwai Wanda suke zuwa gurin shi kuma yake kula su shima Yana Wasa dasu. A Haka yayi ta girma Yana ta karatu cikin hukuncin Allah ya shekara goma Sha hudu Wanda anan ne ya Fara rashin lafiya da aka kasa gane abin da yake faruwa saboda poor health system a lokacin.
Bangaren Safiyya, rukon da tayiwa Akram irin rukon da uwa zatai wa danta ne, se ya zamana yafi sabawa da ita akan mahaifin shi ma, komai nashi ita ce itama Kuma yadda ta rike shi se Bata damu Dan Bata samu haihuwa ba. A shekarar shi ta goma Sha biyar Safiyya ta Haifa Yar ta mace aka saka Mata zainab kamar yadda kowa yayi expecting. Duk da nema da suke yiwa zainab din Amma har lokacin ba su samu nasarar samun ta ba. Shekarar Ihsan wato zainab biyu Safiyya ta sake haihuwa aka saka ma yarinyar suna Iman daga nan Bata sake haihuwa ba.
Akram Yana ta rashin lafiya sede Babu Wanda ya fahimci menene matsalar shi. Lokacin da ya Gama secondary School se Imam ya shawarci Safiyya akan kasar da take ganin su Kai Dan nasu karatu. Ta danyi little research kafin ta shawarce shi Akan ya Kai shi Qatar with the hope ko zai hadu da zainab, Haka ya tafi yana kewar mahaifiyar shi!
Ta_kwalam
[1/3, 20:28] Maman: 029
Maimakon ya saurari abin da Imam din ke fada Masa se baiyi hakan ba, hasalima wuce shi yayi ya nufi zainab, da har ta Fara kuka, ta Kan tuna labaran da Safiyya take ba ta na wannan tsohon, da dukkan alamu tasan shi ne ta Kuma San ta Kade har ganyen ta. Ta rasa yaren da zatayi amfani da shi tayi Masa magana, se da taji yayi Mata larabci, kunsan idan ka samu Wanda a dubban jama'a shi kadai ke Jin yaren da kake ji, zaka ji kwanciyar hankali ko? To Banda zainab saboda kawai kallon ma da Alhaji Gidado yake Mata is never pleasing, ta sunkuyar da kanta tana amsa Masa tambayar da yayi Mata na ita balarabiyar wacce kasa ce? A hankali cikin kuka tace
" Qatar!"
Yayi wani smirk yace
" Shi ne kika taho tun daga can har nan saboda ki zubar da mutuncin ki?"
Tayi saurin dagowa, a lokacin ba tashin hankali bane ba akan fuskar ta, se bacin ran abin da ya fada, sede Alhaji Gidado mutum ne da Allah ya hallice shi da kwarjini na gaske wannan yasa Babu Wanda yake iya ja dashi, ko ita zainab Banda ta kalla fuskar shi kilan zagin shi zatayi Amma suna hada idanu ta shanye bacin ran ta, sede Bata bashi amsa ba, hakan yasa yace ta dakko masa passport din ta, a lokacin kukan ta ya tsanan ta, ta Fara kallon Imam da idanun shi sukai jawur tamkar garwashi, wata irin wuta ce take ci cikin zuciyar shi, ya nufo Alhaji Gidado Yana fada Masa matar shi ce, ya tambaya a school din su kowa ya sani, Amma se ya daka masa tsawa yace
" Karka kaini bango yaro, kada ka Bata min Rai ban zo kanka ba, ka Adana kalaman ka tukunna!"
Duk da Haka baiyi shiru ba ya Fara fadin
" Kai Allah ne? Ko Dan Allah ya baka dama shiyasa..."
Mari yaji a kuncin shi Wanda uncle din shi ya saukar masa har yayi nasarar toshe bakin shi, jiki na rawa zainab tana Kuma kuka ta bashi dukka travel documents din ta, Bayan ya karba yace ta janyo suitcase din shi ta biyo, ta kalli Safiyya da se lokacin ya fito daga shock din marin, kuka take itama Amma bakin ta ya kasa magana, ta kalli Imam da yayi kukan Kura ya rike ta Yana fadin , matar shi ce babu inda zata je, Alhaji Gidado ya tsaya Yana kallon Imam da mamaki, Babu wani da a gidannan da ya taba mayar Masa magana se wannan tsageran yaron. Ya dubi zainab da take kuka har muryar ta ta daina fitowa yace ta zaba ko silently ta bishi ko Kuma yayi ma Imam abin da ba zai taba mantawa ba. Ta kalle su sannan ta rike hannun Imam kamar wadda take rada tace
"Chum Chum! Kayi shiru, lemme go. I'll wait for you ko da nan da ten decades ne..."
Daga Haka ta bambare hannun ta daga nashi tabi Bayan Alhaji Gidado da dayan daga cikin uncles din su Safiyya! Tana kuka ta wuce tana ta waigen shi a tsaye yayi shiru ya dunkule hannun shi, idanun shi looks dangerous at the same time Kuma he looks pitiful, Yana kallo Haka zainab tabi Bayan Alhaji Suka tafi, a hankali Safiyya ta sulale tayi zaman dabaro a kasa, Alhaji Mamuda da sauran Suka fice suka bar su su biyu Babu me cewa da Dan uwan shi wani abu. Se da awa daya ta wuce kafin Safiyya tayi yunkurin karaswa inda yake zaune ta ruko hannun shi, tana rike shi kawai se ya rungume ta ya Fara kuka
" She has left me Safiyya! Ya zanyi? Ina Zan saka rayuwa ta?"
Itama kuka take dukda suna da yakinin kakan nasu ba zai citar da ita ba Amma Kuma me yasa baiyi bincike ba? Me yasa Bai Basu dama suyi magana ba? Ta Fara patting bayan shi saboda tasan lokaci ne da ya kamata ta kasance jaruma Dan kuwa Imam na bukatar ta.
Fast forward, Haka suka tafi gida kowannen su idanu sun Yi jawur kamar gauta, magana ta Riga da ta baza family akan Imam ya kawo karuwa tun daga UK Kuma Safiyya ta Goya Masa baya. Mahaifin Imam na Jin Haka ya Shiga wajen Ummiey Dan Jin kanin bayani, anan tana kuka tayi Masa bayani, ta Kara da fadin
" Ni nasan Imam ba zai taba kawowa macen da Bata hallata a gare shi ba, Kuma inada shaida akan Safiyya ba zata goya masa baya hakanan ba. Kuskure tabbas yayi da ya boye bai fada ba, Amma nasan tsoron abin da zaije ya dawo yakeyi"
Abba ya gyada Kai cikin gamsuwa da bayanin Ummiey yace
" Na yadda, Amma Ina son duk yadda Alhaji zaiyi kada kice kinsan zancen Dan Allah!"
Ta gyada Kan ta tare da tura Anisa taje taga yadda suke, sede tana zuwa.suna kokarin fitowa saboda ciwon Mara da Kuma bleeding da Safiyya ta Fara tun dawowar su. Da sauri ta koma ta sanar da Ummiey, Ummiey hankalin ta ya tashi tace tayi maza taje ta fadawa yakumbo halima wadda ta kasance kanwa ga mahaifin su Imam, cikin sauri ta sanar Mata aikuwa ta zaro mayafi ta same su har sun Shiga mota, tare suka tafi Bayan an tafi sanarwa Dadan Safiyya abin da yake faruwa. Suna zuwa asibiti aka tabbatar tana da ciki Kuma ya lalace, akai Mata wankin ciki Suka dawo washegari. Yan dubiya da masu tsegumi Haka suka ta zuwa, yayun da Imam ya zauna tsayin daka kula da Safiyya duk kuwa yadda yake cikin damuwa me yawan gaske.
Bayan sati da maganar basu Kara haduwa da Alhaji Gidado ba, maganar ma cikin community din tasu ta lafa, da daddare suna zaune sun Gama cin abinci, kowannen su yayi shiru Yana tunanin zainab, Amma kowa ya kasa furtawa Dan uwan shi Dan gani suke zasuyi hurting feelings din juna musamman shi Imam din. Sallamar mahaifin shi da yaji a kofar parlon yasa shi mikewa da sauri ya nufi wajen, aikuwa Abba ne da Kuma baffan Safiyya, suka shigo suka zauna, a lokacin Safiyya ta fito da mayafi, ta tsugunna ta gaishe su sannan ta kawo musu ruwa.
" Imamu me ya faru?"
Shi ne tambayar da baffan Safiyya ya fara Yi masa, aikuwa a take Safiyya ta fara kuka, Imam ya dube ta da kulawa yace
"Kiyi shiru kiyi hakuri"
Imam cikin kwantar da Kai ya Fara bayani yace
" Nasan nayi laifi Abba, nayi aure Babu Wanda ya sani ..."
A hankali ya Fara Basu labari komai da ya faru har karshe, Bayan ya Gama baffan Safiyya yace
" Me yasa baka fada Mana ba? Kana ganin muna Jin dadin abin da mahaifin mu yakeyi? Bamu Jin Dadi amma mu yaran shi ne ba yadda zamuyi, we want one of you to challenge him. You should have informed daya daga cikin mu da Haka Bai faru ba"
Imam yayi shiru me faruwa ai ta faru, Ina zai San iyayen shi zasu goye Bayan shi.
"Bamu San inda ya kaita ba, Kuma baice Mana komai ba"
Abba yace
" Ya maida ta Qatar, Ina ce baka sake ta ba?"
Ya gyada kai, se Suka ce ya Basu lokaci. Haka suka cigaba da rayuwa kamar Imam ba zai Kai ba saboda kullum dare idan ya tashi sallah se yaji kewar zainab a cikin jikin shi, kullum faking yake Amma rashin zainab, tunanin halin da take ciki na saka zuciyar shi cikin kunci. Safiyya tayi kokari dukda wani lokacin tna Jin zafin zainab tun da kishi gaskiya ne Amma Kuma tana kokarin danne shi. A hankali shekara tazo ta wuce Babu wani labari Haka shima Alhaji Gidado baice komai ba, sede duk kokarin barin kasar da Imam yake Yi ya gagara saboda strings da Alhajin yayi pulling. Safiyya Bata sake samun ciki ba har shekara bakwai tazo ta wuce.
A wannan shekarar Kuma Alhaji Dake da sauran karfin shi ya saka Imam a gaba akan su tafi Qatar dakko yaron shi!
Somewhere in Qatar
Da yammaci jirgin da ya dakko ta ya Isa kasar tata, kuka har ta gaji da yin shi musamman idan ta tuna yanayin da ta bar shi a ciki, ta kalla ko Ina ko a mafarki batai tunanin zata dawo kwana kusa ba,. Se gashi ta dawo ba tare da ta fahimta ba. Gidan jadda ta wuce wadda zuwan zainab din ya daga Mata hankali Amma ganin ta kamar hankalin ta baa kwance yake ba se kawai ta kyale ta, se da ta saka tayi wanka ta kawo Mata abinci Wanda tana cin shi ya dawo ta barta ta huta. Se Bayan kwana biyu zuciyar ta ya danyi sanyi kafin ta sanar ma jaddar abin da ya faru a Nigeria, ba karamin gudunmawa ta bawa daidaituwar zainab ba, wadda Suka fahimci ciki ne da ita. Ana ta raino har ta haifi Dan ta namiji ta kuma saka mishi Akram Bayan dogon deliberation. Kullum idan ta kalle shi mahaifin shi take gani a tare da shi, tana Kuma kewar Imam da Safiyya, lokuta da dama Haka zata shuga daki ko cikin dare tayi kuka ta godewa Allah, tayi tunanin wanne halin suke ciki Bayan tafiyar ta. A Haka shekaru sukai ta tafiya, Babu means din da zatai communicating da shi.
Kullum jiran ta inda Imam zai zo take amma Babu Imam Babu dalilin shi, har Akram yayi shekara uku, a shakarar jadda ta rasu, zainab ta rasa kowa se ita se Akram, she's strong even for the sake of Akram. Se Bayan shekara bakwai, Akram ya Fara girma se ga Imam out of nowhere yazo gurin ta. Ku kaddara irin farin cikin da zuciyar ta zata kasance a ciki!
Refer to page 1
Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 033
Bayan na fito daga office din na tsaya can nesa da gurin, na Fara tuhumar Kai na akan dalilin da zai saka na bude Masa ciki na, menene tsakanin mu? Yaushe ma na san shi da har Zan zauna Ina amsa tambayar shi kamar Wanda yayi bewitching dina irin dinnan! Se Kuma wata zuciyar tace ke kuwa Kika San shi tunda kuwa he saved your life ba sau daya ba, duk da bai san ke din wacece ba, gashi yayi kokarin Sanin matsalar ki Dan nema Miki magani. Se na tuna lokacin da nayi attempting suicide a Niger, I remembered Doctor din ya fadawa iyaye na akan lallai lallai su kaini wajen therapist, Amma kalla sun Kai ni? Bayan na dawo ma baa sake tuna maganar ba Tasha ruwa. Kuma tsangwamar da suke yimin ba dainawa sukai ba. Dan har yanzun zancen auren Suleiman bai gama mutuwa ba Dan ko shekaran jiya se da Adda tayi min maganar Shi, shi ba Kira na yake ba ba komai ba Amma sede yace musu yana ta Kira na naki dauka, na kasa gane abin da gayen yake nufi Dani.
Ban sake komawa class saboda nasan we've closed for the day, na Gama dukkan lecture din da nake da shi a timetable. Gida na wuce kamar yadda na saba, na Shiga dakin Mamaa na sanar mata dawowa ta sannan na wuce dakin mu Bayan na tabbatar Adda Bata dawo ba. Ina zuwa na tarar da dakin a kulle which is odd, Ni nasan bama kulle daki no matter what, kitchen na Shiga na dauki ruwa sannan na tambayi Alawiyya ko tasan Wanda ya kulle dakin. Se tace min ai Batuul ce, tun dazun ta dawo Kuma ta rufe Kan ta a ciki. Se da na shanye ruwan na yadda sachet kafin na wuce dakin, na Fara knocking a hankali, na kusa minti na biyar a tsaye kafin tazo ta bude min kofar. Idanun ta sunyi jawur sannan sun tashi, ko baa fada ba kasan kuka tayi ta godewa Allah. Na Shiga ciki na Fara cire kayana sannan na wuce toilet nayi wanka, anan na Fara kallon ciki na, I can swear Naga yayi kasa ba kamar ko yaushe ba. Tabbas slimming pills dinnan da lemun tsami suna aiki. Har karamar rawa nayi a toilet din kafin na fito, har lokacin Batuul na kwance akan gado tayi rub da ciki se sheshekar kuka take yi, se da na Gama saka kayana sannan na dawo na zauna a gefen gado na yadda Ina iya kallon ta, se Kuma na mike na rufo dakin hade da saka lock a kofar sannan na dawo na sake Zama nace
" Batuul me ya same ki? Me ya faru?"
Ina ga dama neman Wanda zata fadawa take Yi, Dan kuwa Ina Mata magana tayi saurin tashi ta zauna, se da na kwalalo idanu da naga yadda fuskar ta tayi, tayi jawur ga swollen eye na alamar ta dade tana kuka, hancin ta Kan shi diga yake mura har ta Kama ta, na duba kasan daki yadda ya baci da used tissue paper, alamar ta kusa bata roll daya saboda fatar hanci. Rungume ni tayi ta sake fashewa da kuka, a'a se na saki Baki Ina mamakin ruwan da ta sake ballowa, saboda a gaskiya tarbiyya dai Batuul tayi lacking, an sakar Mata da yawa, iyayen ta suna kallo tana abubuwa Amma sun kasa Hana ta. Ni na raaa ma Ina suka saka gaba, idan kudi ne ai Babu laifi muma muna da daidai rufin asiri to me yasa suka barta take hakan
"Batuul me ya faru? Fada min"
Saki na tayi tana kukam tace
" Honorable ne!"
Na saki Baki Dan Ni ban ma gane waye honorable din ba. Kamar ta fahimci abin da nake tunani se tace
" Wanda Zan aura fa! Could you imagine Bintu wai hotel ya kaini Kuma Wai he wants to have..."
Se ta kasa fada min sauran maganar, ni Kuma se yayi Popping Kai na, ance hotel anzo Kuma ance have, ai karshen magana sex ake nufi. Ban wani kidimu ba saboda nasan mutane ba kowa ke tsoron Allah ba, yadda ya dinga Mata ruwan kudi abun zai Baku mamaki amma ba kowa ke hakan saboda Allah ba, wasu suna yi Dan Allah saboda son da suke wa mutum yayinda wasu su Kan yi Dan wani manufar su. I dunno tun ranar da na fara ganin shi, wani dare da yazo zance, irin kallon da yake Mata kawai naji ban yadda da shi ba. To Amma wa Zan cewa hakan Nima da ba yancin kaina na samu ba.
" Me kike tunanin Yi yanzun?"
"Ni bansani ba Bintu, bansan ya zanyi.ba!"
Nace
" Ki fadawa Kawu kawai!"
A take kukam ya dauke tace
" Kawu kuma? Idan na fada musu ai zasu ce a fasa auren."
" To ke meye damuwar ki Dan kin rabu da shi. Hakan Bai Isa gaya Miki jikin ki yake so ba?"
Na fada Ina gyara Zama na, ta girgiza Kai tace
" Ba zan fada ba, kema Dan Allah kada ki fadawa kowa Dan Allah."
Bance Mata komai ba kawai na janyo lottafi na dan nayi karatu, to dai Batuul ba shawara take nema ba, gwara na barta tayi abin da take so. Ina nan zaune se naji wayar ta na ringing da farko taki dauka se a Karo na biyu ta dauka. Na kalle ta ta Kara Bata fuska kamar a gaban shi take,
" Tohm!"
Daga Haka ta tashi ta Shiga toilet ta wanke fuskar ta, ta sake fitowa ta canja Kaya zuwa wata embroidered Abaya color baka, ta Ciro Addictive Ambergris daya daga cikin collection din SCENTMANIA. Turaren nan duniya ne, indai nice, cool and soft scent kake so ka nema SCENTMANIA. Ta fice Babu jimawa se gata ta dawo da wata katuwar leda a hannun ta, mamaki sosae ya Kama ni, ta zauna sannan ta dauki wayar ta ta Kira shi, Babu jimawa se ta Fara fadin
" Bribe ne wannan din?"
Bansan me yace Mata ba se Naga tayi dariya, a'a se na sake Baki Ina kallon matar da tuntuni take kuka. Bayan ta dauki wajen mintina ashirin tana waya sannan ta kashe ta dube Ni
" Kinga hakuri ya bani, Wai Bai San me ya hau Kan shi ba"
Na gyada Kai nace
" Batuul kenan!"
Ta Fara Ciro kayan Dake cikin ledar, wani zungureren roasted fish ta ciro, ta baje shi hade da juice ta Fara ce min
" Nasan Baki ci abinci ba, kizo muci"
Na girgiza Kai nace
" Thank you!"
Ta zauna taci abin ta sannan wannan ya wuce. Bamu sake haduwa da Dr Akram ba se da wani sabon satin ya kama, a class Muka hadu zuwa lokacin na Fara ramewa, wani.pills na samu nake Sha, ranar farko da na Sha ko gado na a durkushe nake sakkowa daga kan gado naje toilet, cikina kamar zai fita Dan ciwon da yake min, Amma zuwa dare se da naji jiki na ya Fara saki. Da nasha na biyu ya bani side effects din Amma Kuma Bai Kai ranar farko ba, a hankali Ina sha side effects din na tafiya shikenan se Kuma na Fara ramewa a hankali. Anan naga wata me yawan siyan cake waje na tana tallar wani herbal slimming tea, na saya ta Aiko min na tafasa nake sha, a hankali abunnan Yana bin jiki na Ina Kuma Dan ramewa. Bayan na Gama lecture di na na ranar ya rage se tashi kawai, na Ciro slice cake din da na taho da shi a jaka ta na cinye sannan na Sha ruwa, Babu jimawa se gashi ya shigo, a Karo na biyu ya karaso inda nake zaune fuskar shi da murmushi yace
" Fatima howwa u?"
Nace
" I'm fine sir!"
Ya gyada Kai sannan ya aje min meat pie da Schweppes, nayi saurin fadin
" Sir naci abinci!"
Yace
" Mhmm it's an add more!"
Daga Haka ya juya ya tafi, Alamin da Sadiq Suka juyo suna min dariya, se da yayi gyaran murya kafin dukka muka sake maida hankalin mu Kan shi. Cikin nutsuwa ya gama lecture din mu sannan ya tabbatar Mana akwai possiblity din zaiyi Mana test mu Zama cikin shiri. Yana gamawa ya dake yace
" Fatima ki same ni a office di na!"
Nayi saurin kallon shi sannan Kuma na kalle saura Yan class din mu da wasu ke murmushi, kamar nayi ihu Haka naji, Wai shi baya tsoron bakin mutane? Shi baya tunanin zaace ko wani abun ne tsakanin mu, shi baya wannan tunanin. Har ya tafi ban fara kokarin bin shi ba se da Alamin ya sake yimin magana kafin na tashi na tafi. A zaune na same shi wannan karon Yana cin danwake, har na juya Zan koma ya dawo dani ta hanyar Kiran sunana, na kalle shi yace
" Dawo ki zauna na Gama!"
Ya rufe kyakyawar warmer ya aje gefen table, magani ya ballo ya hada da bottled water ya Sha kafin yayi excusing din Kan shi zuwa toilet ya kuskure bakin shi sannan ya dawo ya zauna tare da ce min
" A Ina muka tsaya Fatima?"
Na danyi kasa da Kai na nace
"Na manta!"
"Ni ban manta ba"
Ya bani amsa Yana sake gyara zaman shi yace
" Me yasa kike son rage kiba, Zaki iya bani labari!"
Wani lokacin wata tambayar se ta dawo.maka da dukkan wasu past and painful memories, a lokaci daya dukkan rayuwa ta tayi flashing ta idanu na. Amma na kasa magana saboda Ina ganin idan na fada Masa zai ga iyayen na Basu da hanklai. Kafin nayi magana se naji yace
" Were you body shamed? Shi ne dalilin da yasa?"
Na gyada Kai na a hankali, idanu na suna cikowa da kwalla
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 18