Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da abokan shi, mahaifin shi ya hango Yana murmushi, a take yaji duk wata nutsuwa ta sake shigar shi, da kyar ya samu suka sake shi ya tafi wajen baffanin na shi, kafin ya karasa wajen na su ya hango kakan shi da abokan shi shima, mahaifin shi da idanun shi yayi Masa alamar ya Fara zuwa wajen Alhaji Gidado, Babu shiri ya juya wajen Alhaji Gidadon dake kwasar gaisuwar mutane dake Masa Allah ya Sanya alkhairi, wani katon carpet ne da Kuma tumtum da ya samu ya shigida da shi, tamkar basarake Haka mutumin yake, Yana ji da kudi, mulki da Kuma izza. Yana hada idanu da jikan nashi se ya muke Yana bude hakoran shi alamar farin cikin isowar shi, ya cire sneakers din kafafun shi tare da karasawa ya rusuna cikin girmamawa Yana gaishe da kakan, Amma se ya rungume shi Yana jadadda Masa farin cikin ganin shi, anan ya umarci Sadiq da ya karbo Masa abinci a cikin gida, sannan ya dubi mujahid yace ya raka Imam ya gaida baffanin shi sannan su dawo , Yana jiran su suci abinci, Haka yaje cikin su ya gaishe su, suna ta murnar dawowar shi, mahaifin shi yayi Masa murmushin Yana shafa Kan shi kafin Suka koma wajen Alhaji Gidado, anan suka ci abinci kafin yace " Ango se kaje kayi wanka ka canja Kaya, ka dawo ku gaisa da mutane!" Haka ya mike jikin shi a matukar sanyaye Yana tunanin makomar shi shi da zainab, ko me take yanzun? Shi ne abin da ya Zama Yana Masa yawo cikin ran shi. Duk yadda su Sadiq suke zuzuta Masa amaryar ta shi da ya riga yasan Rukayya wadda ya San da alkawarin auren ta a kanshi tun kafin ya tafi UK, se Suka ga he's not excited at all, Sadiq cikin zolaya yace " Wai Imam baka murnar dawowar ka ne da Kuma sabuwar amrya da zaka hadu da ita?" Ya kalli Sadiq Yana wani fake smile Amma shi dai zuciyar shi ko kadan ba a nutse take ba. Se yanzun yake sake ganin wani tashin hankalin dake jiran shi. A gidan Baffa lamido Suma amaren dukka suna zazzaune da kawayen su, wasu kana kallon su zaka fahimci suna cikin farin ciki kada Rukayya da Safiyya suji labari Amma Fatima da Boddo gasu nan dai gasu nan. Haka sauran ma. Kanwar Imam wadda ya tafi ya barta tana da shekara shida, yanzun Haka ta Kai shekaru Sha hudu me suna Anisa ta rugo parlon da suke ciki tana kwala Kiran Adda Safiyya, Safiyya ta Mike tana gyara zaman veil din ta tace " Ya akai Anisa?" Tana panting saboda gudun da tayi tace " Adda! Hamma Imam ya dawo daga UK!" Wani karamin ihu Safiyya ta saki tana fadin " Da gaske Anisa? Oh Allah alhamdulillah!! Kin gan shi? Yana Ina?" Ta fada tana kokarin fita, Anisa tayi saurin rike ta tana girgiza Mata Kai alamar kada ta fita ta Kuma tsaya ta saurare ta. Hakan tayi ta tsaya amma she's so excited and eager to see him. " Ban gan shi ba Adda, naji Hamma mujahid na fadawa Innan su Boddo" Ta sake sakin murmushi tana juyawa alamar fita, wannan karon ma Anisa ta sake rike ta tace " Ke Adda Safiyya so kike wancan old hag din ya kashe ki? Kin manta ke amarya ce? I assure you Hamma da zarar yaji kece amaryar shi zai rugo wajen ki" Wannan abun ya sake sanyaya zuciyar Safiyya ta koma ta zauna sede ta kasa nutsuwa, ta dinga murmushi upon murmushi idan ta tuna mutumin nata ya dawo bayan shekara da shekaru! Duk yadda Imam yaso ya zille ya koma hotel wajen zainab Abu ya gagara, Haka ya cigaba da Zama cikin cousins din shi da abokan su. Se wajen goma ya samu ganin Ummiey wato mahaifiyar shi, farin cikin ganin shi sosae ta kasa boyewa, murnar ganin shi sosae tayi. Se da ya shiga zai kwanta zuciyar shi nayi Masa nauyin rashin ganin zainab, rashin ji daga gare ta aka turo kofa, Bilal brother din shi ya shigo ya zauna Yana Masa sannu da zuwa, har lokacin Imam Bai ma San wacece amaryar ta shi ba, shi dai Yana kyautata zaton Rukayya ce. " Hamma old hag yace gobe akwai meeting karfe Tara, ka huta before then!" Ya gyada Kan shi daga Haka Bilal ya fita shi Kuma ya kwanta Yana planning yadda given shi zata kasance. Washegari Yana dawowa daga sallar asuba, yayi wanka karfe shida ya fita daga gidan bayan ya kulle dakin shi yadda kowa idan yazo zaiyi assuming baya nan. Taxi ya samu har hotel din, kamar yayi tsintuwa zuwa ciki Haka ya dinga ji, so yake kawai ya ganta yaga lafiya take, Yana knocking Babu jimawa tazo ta bude, tana ganin shi ta fada jikin shi tana farin cikin ganin shi. Suka zauna saman cushion din dake dakin, ya Fara binta da soothing touches Wanda yasa ta Fara melting a jikin shi. Bayan sun nutsu ya tambaye ta yadda Daren ta ya kasance, tace Masa missing din shi badly da kyar tayi bacci, yanzun Kuma se ta Fara tambayar shi yadda ya samu Ummiey da Baffa kamar yadda taji Yana Kiran sunan su. Se ya zauna suka Karya sannan ya Fara Mata bayanin tayi hakuri ta Kuma Kara hakuri he'll take her home soon, yanzun yazo ya samu anyi Masa aure ne! Waji irin dagowa tayi... Ta_kwalam ce Good morning lovelies! [1/3, 20:28] Maman: 023 Mamaki kamar zai kashe ni a tsaye, nace " Batuul kiji tsoron Allah! Kada abun duniya da zai Kare ya saka ki bata tarbiyyar da akai Miki a gidannan..." Tayi saurin katse ni da fadin " A'a tsaya Bintu, wallahi banyi wani abun ba. Kar ma zuciyar ki ta zarge ni, I only used the beauty of my face nothing more!" Ta fada tana wani irin murmushi tare da shafa fuskar ta, na girgiza Kai nace " Ki dai ji tsoron Allah!" Daga Haka na fice zuwa kitchen Dan yin meat bread din da aka saka ni. Awa daya na kammalla sannan nayi packaging, se da na jira aka karba kafin na dauki zobo da pieces biyun da suka rage na wuce daki na Fara ci Ina tunanin maganganun Batuul, yanzun da gaske take zata iya rabuwa da Suleiman? Duk yadda yayi dawainiya da ita da Kuma shakuwa da sukai Amma zata iya Haka? Se naji kawai al'amuran Batuul ya Fara bani tsoro. Ina nan zaune Ina ci Ina Kuma karatu se gata ta sake shigowa, ta zauna bayan ta gutsiri Rabin meat bread din tace " Dan Allah idan kin Yi ki dinga sammin!" Ta kusa saka ni dariya, nace " Ki saka order, kici ki barshi!" Ta tabe Baki tace " Matsalar business people kenan, you guys don't care about relation at all!" Nayi Mata banza Ina cigaba da duba book di na, kafin na Kai ga dauka ta dauke ta cinye tana dariya. Nima se nayi murmushi nace " Batuul!" Ta kalle ni nonchalantly tace " Bintu! Ya akai?" Nace " Zancen Suleiman ne, ba zakiyi reconsidering ba, ki tuna years of relation da kuka dauka ke da shi, to ma tsaya tukunna, ya Zaki Fara samun Kawu da wannan maganar?" Tayi dariya tace "Kudi da kike gani Bintu Babu ruwan su da wani years of relation, what matters is na samu abin da nake so. Na Dade da gane Suleiman ba class di na bane ba, zancen su Kawu da kike bani Zan same su ba su zasu same ni. Ke dai ki zaba idanu ki gani. Ni dinnan ta Honorable Kura ce da yardar ubangiji" Nayi wani sneering nace " A'a Honorable Zaki ba kura ba. Ke Kika sani" Ina kwanciya Bayan na Jima Ina karatu sannan na kunna data, wani lokacin tsautsayi ke saka kayi wani abun. Ina kunnawa na tafi nayi uploading story akan washegari zanyi glazed pancake for breakfast me so yayi order. Har Zan kashe data din bansan me yasa ba se kawai na koma bangaren chat di na. Ina Fara scrolling se Naga wani message yayi popping, hannu na ya Kai Kan number, Ina shiga Naga image ne aka turon. Na bude na kurawa invitation card din da aka turo min. Abin da ya Fara daukar idanuna shi ne sunan Wanda zasuyi auren, wani irin mikewa nayi na zauna, na sake bude idanu na Dan na tabbatar sunan Samiha Suraj nake gani da Kuma sunan Bashir Garba Me yaki! Auren gaba daya sati biyu kawai ya rage, idanuna Suka ciko da kwalla Ina kallon sunan BashPrince00 da Samiha, so Haka sukai deciding, so a karshe dai aure zasuyi abin su, ikon Allah na sake ayyanawa a cikin zuciya ta. A take se Kuma naji kwallar da ta cika idanuna ta Fara sakkowa a hankali, na cigaba da sheshekar kuka a hankali Ina ayyana ni Kam akwai ranar da take zuwa take wucewa ba tare da hawaye ya fita a idanuna ba? Ko nace bazan Yi ba se wani abun ya gifta da zai saka naji kirji na yayi nauyi, Kuma the only solution is for me to cry! Duk yadda na dinga lallashin Kai Na se da na Jima Ina kuka kafin Kuma na Fara tuhumar Kai na dalilin Bata lokaci na Ina kuka dan kawai zasui aure? Kenan har yanzun Ina son BashPrince00 nake nufi Koko me? Se naji hawayen sun dauke daga idanuna, naji it's ok suyi auren su Nima watarana rabo na duk inda yake zai zo. Se na goge idanuna na kwanta Ina adduar Allah ya Kara min hakuri! Fast forward, rayuwa ta cigaba da tafiya, na cigaba da zuwa makaranta da Kuma neman kudi Abu na, na Zama expert a bangaren snacks har da abinci ma, wani lokacin har order seminar nake samu ko na daurin aure. Dan wasu su samu yasa na samu ma'aikatan da duk lokacin da Muka samu massive order to Zan Kira suzo muyi tare na Kuma biya su. Wannan sanaar ta zame min madogara da abin da nake Jin Dadi. Yayinda Yan gidan mu Suka rage abin da suke min. A bangaren Batuul tana ta soyayyar ta da Honorable Kura ne ko Zaki ? Oho Mata! Suleiman a Yan watannin nan bana so mu hadu, saboda idan muka Hadi se ya tsayara da Ni yayi tayi min korafi bisa canjawar Batuul da yadda take wulakanta shi, Ni dai kullum amsa ta ta kasance guda daya wato yayi hakuri yayi Mata uzuri, Amma na kasa fitowa na fada Masa gaskiyar Batuul ta Riga ta canja shi, Dan Batuul har Mota ce da ita, wadda Babu Wanda ya sani se ni da komai nata se ta fada min Koda Zan Mata menene, har tambayar ta nayi inda take packing ta fada can ne wani underground public parking lot, nan take Kai motar ta Kuma je ta dauka. A ranar se nace Mata "Yanzun ke Batuul Karya Kika koma Yi kenan? Ina ke Ina wata mota a age din ki?" " Ke a ganin ki nayi kankanta da mota?" Tayi dariya ta buga cinya tana sake applying sunscreen a fuskar ta tace " Ke Yar kauye ce Bintu ba Zaki waye ba Wallahi, kike kiga Yara less than age din mu suna fantamawa da motar su!" To me zance Mata? Se kawai naje na samu Adda wadda suke tare da Mamaa suna Hira, na fada musu abin da yake faruwa, na boye kudi da Kuma motar da take da shi. Nace " Ni ba gulma nake Yi ba, Amma kunga Suleiman ya Jima Dan Allah kada ku bari tayi haka!" Mamaa ta Fara ce min " To ai Bintu Suleiman ne yace ya fasa ba Batuul ba, Nima banji Dadi ba musamman shekara da shekarun da suka dauka tare" Wato abin da Batuul ta shirya kenan dama, shiyasa take yawan ce mini da kafafun shi zai gudu da Kuma bakin shi zai ce baya Yi, kenan abin da ta dinga yi shi ne halin ko in kula da Kuma Yi Masa wulakanci shiyasa ta tunkuda shi ya fasa, surely Batuul is wise and smart. Ga Kuma iyayen ta a zaune Amma dukka sun Goya Mata Bayan abin da take Yi, to me zance Kuma se na tashi na tafi, aikuwa Ina tafiya Adda tace " Ni Kam Mamaa to abun da nauyi ace yaronnan an bar shi ya tafi Haka, ko hooking din shi zakiyi da Bintu Yar dakin ki. Naga kamar Bata da saurayi ko daya Kuma Kawu ke ya fadawa Yana son aurar da su ko?" Mamaa tayi murmushi tace " Idan mu Kai Haka min wanke Kan mu kuwa, Dan yaron yayi jira sosae mutane se su zage mu ai" Anan suka kulla wannan abun without even considering anyone of us, wato ni da Suleiman din. Ko da suka fadawa kawu se yace ai hakan yayi indai yayi musu. Daga Haka aka bawa Honorable Aliyu Kura yazo akan ayi magana. Ranar Naga Abu, ni aka saka nayi girki kala kala, Batuul tun safe akw yiwa jiki spa, se kallon yadda kowa jikin shi yake rawa nake, hatta wasu daga cikin siblings din mu a gidan aure se da suka zo. Ina gamawa na fice na bar gidan zuwa makaranta Dan nayi karatu, bazan zauna Naga wannan abun bakin cikin ba, Yaya Fadima ta sokoto ita kada da sajida suka nuna rashin goyon Bayan su, Amma kowa Fadi yake ai dama can Suleiman ba tsarar ta bane ba, Ashe suna ta cewa a hada shi da Bintu ita ce daidai shi. Kuji fa Dan Allah. Ban dawo gida na se bayan maghrib saboda naje gidan Zuhriyya na zauna da yaranta tunda tana gida, se da ta taho sannan Nima na taho gida nazo na samu ana ta bude kayayyaki, I was so annoyed Amma Dan kada a ce bakin ciki nake se na zauna Muka kalla nayi Mata barka na wuce daki abu na. Inata makakin kokarin Yan gidan mu, ko kunya basa ji se wani zazzakewa suke yi kamar Basu taba Jin dadin kudi ba se yanzun. Duk abin da ake kullawa wallahi ban sani ba, abin da na saka gaba na shi ne shiga ta level 3 Ina kokarin ganin nayi scaling na Zama architect. Su Yan gidan mu sunyi focussing akan Batuul yayinda takurar da suke min ta ragu Amma a waje Kuma cikin mutane ban huta ba, kusan kullum se na hadu da me ce min " Kinyi kiba da yawa! Ki daure kiyi shedding a bit of weight." Haka dai suke fada duk da kowa is entitled to his or her own opinion, ya kamata mu din ga considering feelings din mutane, kunga yadda nake battling da mutane to Bai Kai Rabin abin da wasu su ka fuskanta ba, people are losing their minds silently saboda critics din mutane, kullum Ina fada a Rai na why must you talk? Dole ne se ka tanka halittar mutum? Idan ba dole bane ba ya kamata ki bar mu Haka nan muyi numfashi... To be continued In shaaa Allah! Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 027 Gaba daya na kasa gane Kan Batuul balle inda ta dosa, ta Zama wata iri magana ma da kyar take yi, Ni mamaki take bani kamar ba Batuul din da na sani ba. Sati biyu da faruwar abun yazo ya wuce, ranar Saturday da yamma Ina kitchen na kammalla shawarma Ina packaging, se naji sallama a kofar kitchen din, na Yi saurin juyowa anan Naga mahaifiyar Suleiman, da Dan murmushi saman fuska ta na gaishe ta, itama se Naga ta saki fuska ta amsa min da kulawar ta. Na fito Baki daya nace mata "Na fadawa Mamaa kinzo?" Tace "Eh har Asiya ma ki fada mata Ina jiran su" Wannan abun da ta fada se ya tabbatar min ba wani abun kirki ya kawo ta ba. Amma ni Ina ruwa na da abun su, ni ai tayi kokari sosae a gani na da ta iya hakuri ake juya Dan ta kamar waina a cikin kasko, he was devoted Dan abin da Suleiman yake Yi da Kuma errands din da yake wallahi ko daya daga Yaya Auwal ko sani basa ma kwatantawa. Mamaa Bata daki da naje se habiba yarinyar kanwar ta da tazo hutu gidan mu, na tambaye ta Mamaa tace min tana wajen Adda, na juya zuwa wajen Adda nan ma basa nan se kawai na tafi oarlon Kawu tun da Sunday ce I'm sure baije kasuwa ba. Aikuwa suna zaune dukkan su, da wani kudi a gaban su suna kasfatawa, na Shiga da sallama a baki na, dukka suna dago suna kallo na, na karasa Shiga Bayan nayi musu sannu nace " Adda Maman Suleiman din Batuul ce tazo?" Ta dalla min harara tana fadin " Wacce Batuul Kuma? Bayan ga kudin auren ta an kawo" Na Kara kallon kudin dake gaban su, a gidan mu dai nasan Muna da rufin asiri daidai gwargwado to Amma me yake saka su kwadayun abun duniya Haka? Na tabe Baki ko Allah ya Sanya alkhairi bance musu ba, na fito suka biyo baya na. Mamaa tace da Adda "Ni fa Adda bana son haduwa da matar nan, bansan da me tazo ba!" Adda ta tabe Baki tace " Tsoron me kike ji? Kina da Baki tana da Baki ta fada mu mayar Mata. Ya zamuyi tun da Batuul tace Bata son shi?" Ni fa wani lokacin iyaye na bani mamaki, ta Yaya zaka Haifa da a cikin ka, ka Sha wahalar shi, kayi Masa komai sannan ya kasa bin ka se Kaine zaka bishi? Kalla dai gidan mu, ya zaayi Batuul tace Bata son shi rana tsaka har Kawu su biye Mata kamar ita ta haife su Basu suka haife ta ba, wannan Abu na bani mamaki kwarai da gaske. Ko da na sanar mata suna tafe se kawai na koma kitchen wajen sanaa ta, Ina zuwa na tarar Alamin ya Kira ni, class rep din mu ne, Wanda shi ma Yana daya daga cikin mutanen da suka fita zakka a wadanda nake haduwa da su. Alamin mutum ne me kirkin gaske, a bakin shi ban taba Jin wani aibu na halitta ta ya furta ba, se ma idan yaga Ina damuwa yayi ta zolaya ta har se na Dan wartsake sannan zai bar ni. Na Fara kokarin Kiran shi se gashi ya sake Kira hakan yasa na dauka tare da karawa a kunnen na Muka gaisa, ya Dan zolaye ni kadan sannan ya sanar min akwai fixed class washegari karfe takwas na safe, kada na Bari nayi missing, nayi Masa godiya sannan mu Kai sallama. Ina aje wayar na jiyo muryar Maman Suleiman tana fadin " Ai idan ance mutum kwadayayye ne to an Gama magana, magana ta kare. Meye Suleiman Bai Yi muku ba, wacce bauta ce baiyiwa yarku ba Amma sakayyar da zakuyi Masa kenan? Da izinin Allah se Yar ku Batuul ta dandani makamancin abin da ya dandana na bacin Rai ..." "A'a tsaya malama, karki ma yarinyar mu baki, Dan kawai ta samu Wanda yafi shi, kinsan Fadi tashin da muke na ganin yadda zamuyi compensating din shi? Amma abin naki Babu arziki balle girma!" Fada sosae Adda da maman Suleiman sukai, kafin ta Mike ta fita, wani irin rashin Jin Dadi nake ji har cikin zuciya ta, ya ma zaayi iyayen mu su Zama so shameless Haka? Bayan ta fita suka ta mita a parlon har bansan yaushe kowacce ta tafi ba. Ko da dare yayi Ina kwance daki Batuul ta dawo, she looks tired, ta cire Kaya ko magana ba tayi min ba ta wuce toilet, Babu jimawa ta fito Ina zaune inda ta barni. Hijab di na ta dauka tayi sallah ae da ta idar sannan tace min "Bintu Dan Allah wanne irin perfume kike using, me Dadi Haka?" Ba tare da na kalle ta ba mace " SCENTMANIA nake amfani da shi" Se ta Mike tana fadin " A Ina Zan samu? Turaren nan duniya ne wallahi saboda yayi kamshi me kwantar da zuciya." Daga zaune na Fara Mata bayanin su, nace " Ai matar ta san lakanin turare Batuul, oils ta ke yi Kuma tana iya maida maka oil zuwa spray, Kuma idan Zaki siya, se kinyi Mata bayanin yadda kike son turare kafin tayi Miki recommending. Batuul ki gwada shi kawai..." Shigowar habiba ta dakatar da Ni daga bayanin SCENTMANIA, Nima bansan yadda akai na San shi ba, ba Zan iya tunawa ba, Amma fa yanzun bana tunanin akwai turaren da Zan iya amfani da shi Bayan SCENTMANIA. " Adda Bintu kizo in ji Mamaa" Na Mike Bayan na.amsa ta nabi Bayan ta zuwa dakin Mamaa, tana zaune da bowl a hannun ta na kwadon salad a ciki, na zauna bayan ta yimin tayi nayi murmushi nace " Pizza akai order, nayi ta Dan so tayi.yawa shi ne na cinye aba ta" "Ke dai Bintu ba Zaki rabu da wadannan fast food din ba, ke ba exercise kike ba, shiyasa jikin ki jiya I yau" Na tabbatar Mamaa ba zata taba fadar Haka ba, Amma Adda ai ba zata fasa ba, Koda kuwa zata ga na rataye Kai na ne Dan takaici. Bance komai ba se kicin kicin da fuska ta da nayi, shikenan saboda kana da kiba you can't eat abin da kake so? Ni dai Ina Zan saka Rai na ne naji Dadi? " Kinsan an kawo kudin Batuul ko?" Na gayda Mata Kai na Ina fadin " En! Allah ya Sanya alkhairi Suka amsa Amin baki dayan su, kafin Adda tace "Kawun ku ya tambayi ko kina da saurayi a hannu, mun fada Masa Babu kowa dake zuwa wajen ki, ya yanke hukuncin zai aura Miki Suleiman tun da,.." Ai ban Gama saurara ba, tunda sunan Suleiman da Kuma nawa hade da kalmar aure suka shigo sentence daya naji na daina gane me ake fada tukunna! Ta_kwalam [1/3, 20:28] Maman: 026 "Did I heard you well? Aure Kuma?" Ta fada da wata irin murya da zata tabbatar maka a raunane  take, ya sake ruko ta zuwa jikin shi saboda Yana iya ganin kishi karara akan fuskar ta, kafin yayi magana ta Fara kuka a hankali tana fadin " Tsoro nake ji, tsoron family din ka nake, you already have a wife how will they accept me Chum Chum?" Yayi shiru Yana Jin tashin hankali hade da tsoro Yana shigar shi, duk wata hanya da yake ganin lallashin ta zaiyi sauki yabi Amma se yaga abin na zainab kamar gaba yake sakewa. Kuka take sosae kamar yau aka sanar mata mutuwar Fahad, ya duba agogon dake kafe a hotel room din yaga karfe takwas da mintina goma , ya Kamata yayi haramar komawa amma Kuma idan ya kalle ta se yaji ta Ina zai bar ta a halin da take ciki, duk yadda Imam take sahibul Kalam yau gashi kalamai sun gagari bakin shi, abin da kawai yayi was hugged her and patted her back. Anan suke ta zaune har yaji alamar tayi bacci, cikin sauri ya kwantar da ita ba tare da yayi wani abu ba ya fice daga dakin. Dakin shi ya koma baifi minti na goma ya rage Tara tayi ba jikin shi ya gyara ya canja zuwa manyan Kaya da Bilal ya kawo masa, da saura mintina biyar ya Shiga wajen Ummiey, ya gaishe ta a gaggauce kafin ya wuce inda yake da tabbacin anan zaayi taron. Yana tafe Yana kallon gidajen da ke mallakin su, kowanne da idan aka haife shi ya isa sure anan zaa Gina Masa gida ayi Masa sure, a tarihin Gidado close Babu wani bare a cikin wannan waje, Haka zalika bai taba Jin labarin in da akace Wai yau a tarihin dangin su dake nan wani ya taba auren bare, shi ne na farko shiyasa yake Jin tension Yana building a jikin shi. Alhaji Gidado na zaune ya mikar da kafafun shi akan tumtum, dalilin hakan kuwa saboda kumburin kafafun da yake fama da shi kwana biyunnan. In dai taro zaayi to Alhaji Gidado yakan kasance mutum na farko da yake fara zuwa wajen taron, ba dai ka Riga shi ba sede ya jiraka. Gefen shi Amarya Safiyya ce wadda tun tana yarinya ita ke serving din shi tea, to ko jiya bayan anyi auren ma yau seda ta dafa Masa tea ta kawo Masa, tana zubawa taji deep voice din da tayi shekara takwas ba taji ba yayi sallama, a hankali ta juyo da wide grin saman fuskar ta, tace "Hamma Imam! Ashe ka dawo? Ashe da gaske ne!" Shima Yana murmushi Wanda kowa yasan Safiyya da Imam yadda suke, tun tana yarinya mutuniyar

Chapter 10 of 18