Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
komai yace ya bari shi dai asirin shi ya rufu kawai. Amma har zuciyar shi yaso auren Batuul, yaso ya aure ta saboda Yana son ta kuskure daya na rashin hakuri da yayi har ya lalata ta. Dukka gidan wato su Mamaa suka ta tambayar ta ko wani abun ya hadasu Amma ta kasa magana se kuka kawai da suke, shi Kawu tun anan yayi sensing rashin gaskiyar ta Dan haka ya tattara ya kyale. Duk yadda kowa yaso yaji abin da ya faru Batuul Taki magana ta kulle bakin ta. To me zata ce? Itama abin zai dawo kanta, tun daga wannan kuwa ta nutsu ta daina yawo se zaman daki ko dakin Adda, ko gidan sisters din mu ta daina zuwa. Adda ba karamin damuwa tayi ba saboda yadda ta Riga ta saka buri akan wannan bikin, da auren ma Baki daya. Shiyasa idan Suka kebe da Batuul se tace Mata ta Kira honorable ta bashi hakuri Amma ita tsoron ta cikar wannan watanni ukun! Dabas Haka na zauna bayan ta gama kora min bayani, jiki na kamar an watsa min kankara Haka naji, na kasa cewa komai se kallon ta kawai nake, se kuka take, no wonder kullum Batuul na daki, Batuul har sallar tsakar dare take, magana ma ba sosae take Yi ba, wayar ta ma ba sosae zaka ganta a hannun ta ba, gaba daya tayi la'asar ta nutsu ta Shiga taitayin ta. Nace " Sannu Batuul! Allah ma Yana son ki shiyasa ya dawo Dake Kan tafarkin daidai. Kiyi kokari kiyi amfani da wannan damar ki tuba, tuba na gaskiya, Ina me tabbatar Miki Allah zai amsa, Allah Yana son bawa me tuba!" Hawaye ya sake gangaro Mata tace " Ina Yi Batuul, shi ne abin da yasa har yanzun banyi loosing sanity di na ba. Kuma Ina jin sauki cikin zuciya ta. Amma Batuul idan na kamu da HIV fa?" Na rike hannun ta dukda Nima a kasan zuciya ta tsoron nake ji, Amma ya zanyi dole nayi concealing nawa na Bata shawara " In shaaa Allah Babu abin da zai faru, ki cigaba da addua, Allah ba zai tona Miki asiri ba" Mun Jima tare da ita, har se da ta daina kuka sannan na zuba Mana abinci muka ci, gaba daya shekarun mu ashirin ne fa, Amma kalla yadda Batuul ta lalace Wanda Ni dai kullum laifin iyayen mu ne. Kuma na yadda da abin da tace wallahi wani lokacin kyau Yana daya daga cikin musiba da kuma trial na rayuwa, saboda Wanda suke da kyau gani suke wata alfarma ce daban Allah yayi musu, suna amfani da wannan kyawun suna yin abin da bai dace ba, ban ce kowa ba amma ku tuna yadda Batuul tayi, wani lokacin masu kyau har wani girman Kai suke ji, na menene? Da zasu dinga criticizing wanda basu Kai su ba. A hankali na shiga sabga na Fara shirin biki, gashi bani da kawa ko daya, ko cikin cousins dina ba wata kwaya daya da zaka ga Wai I'm very close da ita, Dan Haka komai da Kai na kawai nake, se Kuma abun mamaki Batuul ta ware kusan komai da ta hada na bikin ta ta fito da shi ta bani, tun daga Kan make-up, Mai kunshi da Kuma gyaran jiki dukka ta barmin. Da farko naki yadda se ta nuna min sede idan fushi nake na abubuwan da tayi min, se Adda da ta sakko itama tace " Ba refunding zasui ba, gwara ayi amfani da shi kada ya Zama waste" Se na shawarci Noor se yace min Babu damuwa na karba kada suga kamar fushi nayi, Haka na amince daga nan kuwa kowa ya zage damtse aka Fara Shirin biki. Sati daya ya rage biki Akram yazo ya samu Kawu akan Yana son zai tafi dani Qatar har ma yayi applying Mana visa. Kawu yayi murmushi yace " Banda abin ka Akram idan ka aura Bintu ai ta Zama karkashin ikon ka, so ni Dana baka auren ta, bani da matsala da duk inda zaka kaita. Allah ya Baku zaman lafiya me daurewa!" Akram yayi godiya sannan ya shiga ya gaida Adda da Mamaa da Kuma siblings di na wanda se lokacin Suka fara ganin shi ma. Bayan ya tafi Suka ji labarin tafiya ta Qatar, kowa Baki da magana Amma anyi kum, to dama Haka Allah yake abin shi, Ina Suka taba tunanin cewar Zan yi aure kwana kusa, I still remembered irin maganganun da suka fada da naki yadda da maganar Suleiman, har cewa sukai Ina tunanin Zan samu anything better than him? To se gashi na samu Wanda yafi shi komai da komai. Da na dawo da yamma ni da Batuul da take kaini ta jira ni a Gama gyaran jiki naji labarin zuwan shi, Dan Ni Bai fada min yazo ba. Kuma Babu kunya se gasu suna fadin wai nayi dace miji na kyakyawa gashi me kudi. Kinji wani Abu Kuma, I hate it when people capitalize over money! Kafin wani lokacin ko nace kafin mu ankare se gashi biki har yazo, imagine the simplest wedding ever to shi nayi. Kamu ma Ina zaune a parlor akai min, Babu kawa ko daya se Batuul da cousins di na. Washegari juma'a aka daura Mana aure ni da Akram. Wata super atamfa na saka red da brown tayi min kyau sosae da sosae, sannan Mamaa ta daura min lafaya me ado irin na atamfar jiki na. Nayi kyau ga kamshin turaren nan na SCENTMANIA duniyar kamshi, ko a lefe na shi Akram ya saka min. Har kyaututtuka ta bamu ni dashi na appreciation. Da ya shigo Bayan an daura aure muka danyi pictures, shima ba wasu abokai ke gare shi ba se tarin Yan uwa. Zuwa yamma aka kaini family community din su, ba Wai da son ran shi aka kaini ba, so yayi kawai a wuce da ni gida Amma se Safiyya ta nuna Masa yayi hakuri ayi wannan formalities din idan ba Haka ba kuwa zai barta da surutun mutane. Hakan yasa ya amince se gashi ya Kira Ni, na Gama canja kaya kenan an lullube ni ana yimin turare, Batuul ta miko min wayar tana fada min "Noor din ki ya Kira!" I've to smile fa, saboda farin cikin da nake shiga, Ina Kuma adduar Allahu yasa wannan farin cikin, soyayyar mu ta daure har abada! Na karba bayan nayi sliding nace "Noor!" Maimakon ya Kira Ni da Noor se yace " Wife! Ya kike?" Nayi murmushi nace " I'm fine!" "Zaa kawo ki gida, I mean community din mu. Ban so ba Amma Ummaah tace wai formalities ne. I'm sorry!" Nayi murmushi nace " Ba komai Noor, ba damuwa" Yace " Kinsan dai I chose you over many ladies ko a family din mu ko? So nasan idan kikaje people will talk. Dan Allah wife kada ya Dame ki, ki sani I love you and you only no compromise." Nima tun da aka fada min can zaa Kai Ni jiki na yayi sanyi, Amma Kuma wannan maganar se yasa zuciya ta tayi sanyi, nace " I promise you!" Ile kuwa, ko da mukaje, nasan na shiga gidan yawa, saboda ko ta Ina mutane ne, gidaje sosae da sosae masu kyau. Dukda Kai na a sunkuye yake Amma Ina iya ganin inda muke wucewa. Se da na canja Kaya sannan aka kaini wajen da zaayi budar Kai. Bayan an yaye min lullubin fuskata ta bayyana, se naji duk na takura, Batuul tazo ta tsaya kusa da ni, akai pictures da sauran su sannan aka Fara kokarin tashi. Lokacin da na mike Zan tafi wasu yanmata dake gefen can suna dariya tace " Ikon Allah ! Su Hamma Akram Kuma duk yadda aka tsallake mu akan wannan ya kare!" Dayar tayi dariya tace " Kede bari, wannan ai se ta goya shi!" Naji komai da suke fada, Batuul ta juya nayi saurin rike hannun ta, a hankali nace " Dan Allah kada kice komai, wannan opinion din su ne Kuma kowa is entitled to his own opinion. Karki kula su" Ba Wai ban ji haushi ba, naji wani irin rashin karfin gwiwa kamar zai shige ni, da na tuna abin da Noor ya fada min se naji zuciya ta tayi sanyi, naji kwarin gwiwa ya Kama ni! Ta_kwalam ce Finale A hankali wayar ta shi ya Fara Kara, yayi saurin barin tarin mutanen da yake ciki Yana sakin murmushi, he has been anticipating for her call da jimawa, Amma yau yasan account din sa se sunyi kukan farin ciki, Dan shi tuni yasan yau labarin da zai bayar zai dada Mata zuciya! Bayan sun gaisa kamar yadda suka Saba yace " Akwai labari me dadi. Yau Akram yayi aure" Cikin wani irin excitement zainab tace " Ma shaaa Allah! Alhamdulillah!! A family din su yayi aure?" "A'a fa, shima kamar mahaifin shi wata ya auro daban a wani family!" Tayi murmushi tana Jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta gan shi, hakika tayi kokari, ba kadan ba tayi namijin kokari wajen kauda idanun ta akan Dan ta na tsawon wannan shekarun, dukda bege da zuciya takeyi na son kasancewar da shi Amma ta Bari yazo ya neme ta da Kan shi. " Ma'am! Yanzun Haka Yana kokarin zuwa Qatar shi da amaryar ta shi Dan su neme ki, should I divert their attention away ko na bar su..." Cikin sauri ta katse Shi da fadin " Don't do that, allow them to meet me! Zan tura maka mail di na da zarar sun shirya tahowa please notify me!" Daga Haka sukai sallama da shi ta kashe wayar, kujerar da take zaune irin ta executives dinnan ce, to ita din ma ai executive ce a wannan company, tunda kuwa ita ce chairwoman ta company. Tana nan a yadda kuka santa kyakyawar nan ta gaske, se alamar ta Dan manyanta da Kuma Kuma kwanciyar hankali da ya sake bayyana a jikin ta da fuskar ta. Dukda har yau zuciyar ta me naci tana son Imam wani lokacin ta kanji Bata Dana Sanin tarayyar ta da shi, yayin da wani lokacin ta Kan ji if she will start all over, she wouldn't have chosen him! To Amma Kuma ai a tarayyar ta da shi Imam ya sota da dukkan ruhi, zuciya, Rai, gangar jiki da komai. Sede duk abinda ya faru ta kasance ita din me Yi Masa uzuri ce, Abu daya ta gagara mantawa shi ne Dan ta da ya dauke Bayan ya yaudare ta, har wannan lokacin idan ta tuna se zuciyar t tayi kamar zata fito Amma dai ya wanke laifin shi da irin rayuwar da ya bawa Akram, tana da labarin komai na Akram Kuma she's forever grateful to Imam! *** Se dare sannan aka Mika ni daki na, ko nace gida na, gidan aure na. Yawancin mutane kafin muzo sukaje suka ga daki kamar yadda yake a al'ada. Siblings di na sukai wa gidan final touch kafin sukai min sallama har da Batuul Wanda wannan Dan satittikan da mukai tare da ita wani kyakyawan bond me karfi ya kara shuga tsakanin mu. Zasu tafi kowa yayi min Dan nasihar shi sannan suka tafi Suka barni ni daya zuru cikin wata sabuwar rayuwa. Amma dai ko kuka banyi ba, hasalima farin ciki nake Zan bude sabon babi cikin kundin rayuwa ta, tare da Wanda ya bani karfin gwiwa na Zama abin da nake a yau dinnan. Ban Jima ba se gashi ya shigo, shi kadai ba tare da rakiyar kowa ba, wannan Hadi namu ko zamu din ga samun mutane ma kuwa? Na ayyana cikin zuciyata. Bayan ya karaso tare da ruko hannu na cikin na shi bayan ya zauna gefe na, not minding kujerar ma tayi Mana matsi, shi dai abin da ya Dame shi ya samu wannan closeness din Dani. Shiru dukkan mu min kasa furtawa juna komai Amma zukatan mu Allah kadai yasan me ke wanzuwa a cikin su. Se can ya dubeni cikin saa Nima na karkata kaina Zan kalle shi yace " Muje muyi sallah!" Tare Muka tafi daki nayi alwala bayan na fito ya Shiga yayi sannan ya jamu sallah, Bayan min idar yayi Mana addua doguwa ganin na Dan Fara hamma yace muci abinci, kowa na shi daban Haka mukaci. Sannan ya zauna saman gado yace " I need to work out, saboda na samu abincin ya zagaye jiki na. Shirya ki kwanta nasan kin gaji!" Babu musu na shirya sannan na kwanta ya lulluba min duvet ya daidaita sanyin dakin kafin yayi pecking di na a goshi ya fita, nayi murmushi Ina saka hannu na a wajen da yayi min peck din, a Haka dai baccin gajiya me nauyin gaske yayi gaba da Ni. Bayan wajen awa biyu se gshi ya shigo ya saka wasu lallausan pyjamas, ya Jima a Kai na Yana kallon fuskata da yadda nake bacci hanklai a kwance se yaji ba zai iya tashi na ba, karshen gadon yaje ya kwanta Babu jimawa bacci ya dauke shi. Bamu farka ba se asuba mukai sallah sannan na hada Masa oats na kawo Masa, ya amsa sannan ya koma ya dakko wani spoon din muka Sha tare, daga haka muka gaisa yace " Muje mu huta ko Noor!" Muka wuce zuwa daki, Muka kwanta duk da naso na Fara gyara gidan Amma banyi hakan ba, na bishi na kwanta, a wannan kwanciyar ne we became so intimate har akai deflowering di na, pains ne da bana son na tuna, ba Kuma Zan iya bada labarin yadda naji ba. Dan Haka baccin wahala ne ya tafi dani na barshi shi.kadai Yana caressing gashin Kai na. A washegari da daddare muka je community din su, bayan munyi sallar maghrib muka je, kafin muje gida Ummaah tace mu bibbiya inda tayi Masa lissafi Kuma kada ya tsallake ko daya a ciki, Dan ta San halin shi. God suna da yawa Haka muka ta yawo Allah yasa saukakken Kaya na saka da Kuma takalmi da bansan irin gajiyar da zanyi ba. Yawancin Yan matan ke mun kallon banza Ni kuwa ban bi ta kansu ba se da Muka Isa wajen Ummaah kafin na saki ajiyar zuciya, ta zauna Bayan min gaisa tace " Kin gaji ko?" Nayi murmushi kawai, ta cigaba da Jana da Hira har na warware mukai Dan Yi Hira da Abban ya dawo suka hadu sukai mana nasiha me ratsa jiki, kafin ta nuna min yadda Zan dinga calculating calories din dake cikin each meal da zanyiwa Akram, ta bani tips da Kuma abubuwa da dama da zasu taimaka min wajen kula da lafiyar shi. A karshe sukai tayi min godiya har naji kunya. Washegari Muka je gidan mu, Suma Suka tarbe mu da kyau bamu Jima ba muka tafi yayi ta yawo Dani Dan naji dadi, a cewar shi zaman will be boring idan bama fita. Daga Haka se Muka maida hankali Kuma akan junan mu, yadda zaman mu yake tafiya kwanciyar hankali ce kawai da farin ciki a ciki, shiyasa duk lokacin da naji ance aure ya mutu within first month se na kasa fahimtar what actually went wrong? Like nasan har lokacin kowa Bai Gama fitowa da true colors din shi ba, har lokacin zaman dauki ake kowa Bai Saba da kowa ba. That's by the way! Bayan wata daya sannan visa din mu ta fito, mukai sallama da kowa se Qatar. Muna jirgi ne nake tambayar shi ko yasan inda Maman take? Se yace shima dai kawai Zai duba company mahaifin ta yasan zasu San inda take ko da mutum daya ne. A Haka Muka Isa kasar. Se da mukai kwana biyu Wai muna hutawa, Wanda Ni dai ba wani hutu Banda Tsabar soyayya da yake nuna min, wani lokacin na Kan ga rayuwa ta kamar mafarki komai yake faruwa, ku tuna irin kuncin da na kwasa a ryuwar ta, ku tuna how much criticism akai min a rayuwa ta Amma Wai ya wuce shiyasa nake adduar wannan labarin nawa yasa ya Zama solace to mutane iri na, Ina fatan zamu samu sauki cikin zukatan mu, za Kuma mu karba rayuwar mu yadda tazo Mana ba tare da mun kushe Kan mu kamar yadda mutane suke Mana ba! A kwana na uku shi ne mukaje company, Amma tun daga waje aka Hana mu Shiga saboda mu ba ma'aikata bane ba, gashi daga ni har shi Babu mai Jin larabci balle muyi ma securities din bayanin abin da ya kawo mu, shi Kuma ba turanci yake ji ba. Kunga akwai language barrier kenan! Noor yace min mu tafi Amma naki instead se nayi downloading translator, na fada Mata da turanci se ta fassara Masa da yaren da yake ganewa, karshe yace shi ba zamu ga chairwoman ba se Muna da appointment, sannan Kuma ba zaiyi disclosing address din ta ba. Karshe dai Haka Muka tafi duk jikin shi yayi sanyi, dukda kokarin rufe hakan da yake. Ko da mukai waya da Ummaan Haka na fada Mata se tace washegari muje da wurwuri tasan zainab is always punctual. Shi kin zuwa ma yayi ni ce na shirya cikin fuschia pink din abaya, na yane Kai na da veil din ta sannan na tafi, shi Kam shi security din se da ya jadadda naci na. Ina nan tsaye se gashi wata dalleliyar mota ta kawo kai, kamar ance ta tsaya se ta tsaya wajen security tana tambayar me nake a tsaye se da ya dubeni kafin ya Fara Yi Mata bayanin tun jiya muke nemanta , aikuwa.ta Fara Masa fada sannan ta fito cikin sauri ta nufo ni, tunda ta taho na gaskata miracle din Allah, sure baya Kama da ita Akram ko kadan but I can see him in her! " Kece BINTUN Akram?" Na gyada Kai na se ta rungume ni ta Fara tamabayr Akram nace Mata na barshi a suite din mu, ai tuni ta bude mota ta shiga bayan na shuga muka dauki hanya, Yana zaune Muka same shi, yayi Dana Sanin Bari na na tafi Ni daya yafi a irga se kawai yaji swiping card, aikuwa ya mike se gani ga Ummiey. Allah suka se da suka bani tausayi musamman ita, yadda take Masa ta rungume shi, ta shafa fuskan shi tana kuka tana fadin " My baby is all grown up!" Lallai akwai zalinci a raba uwa da danta. A wannan ranar muka bita gida, ban manta na Kira Ummaah na fada Mata ba. Aikuwa tayi ta murna. Sati na zagayowa se gata da Abba, mukai ta rokonta Dan sosae Muka Saba, musamman Dani da nake Jin ta kamar uwar da ta haife ni Akan Dan Allah ta komawa auren Abba Amma se ta kalle ni da Ummaah tayi ta dariya tace ai wannan ya wuce ba dai ita zainab din ba. Watan mu biyu Ni da shi sannan mukai Mata sallama Muka bar kasar , with the hope zata canja raayin ta ta komawa Abba, Amma dai nasan yaudarar Kan mu muke saboda she's so adamant Akan ta Gama wannan auren. Bayan min koma Adda da Mamaa suka.zo min, naji Dadi dukda Basu Jima ba suka bar Batuul da ta tabbatar min Bata da matsala anyi test har sau uku, wannan labarin ba karamin dadi ya yiwa kunnuwa na ba, na Bata shawarwari ta wuce se Kuma na Fara laulayi Wanda yasa ni wata irin Rama. Ranar dai da nake nema se a karshe tazo, Kuma se Naga nayi Muni, Naga duk banyi kyau ba musamman idan nasa Kaya Naga yayi min wani iri se naji Babu dadi. Tohm wannan shi ne labarin BINTUN BATUUL! Nasan akwai korafin nayi saurin rufe labarin, kowa yyai hakuri. Nagode sosae da sosae da dukkan mabiya na Wanda Basu gajiyawa ko kadan wajen gingering dina da nuna min rubuta na na da muhimmanci, nagode sosae da sosae Ina muku fatan alkhairi and hugs to each and everyone of you! Kada ku manta Dan Allah a dinga yimin addua, just pray for me. Ina fata Allah yasa na Kara samun damar yin wani rubutun nan gaba! Thank you so much lovelies. Allah ya bar zumunci. Ta_kwalam ce An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 18 of 18