shi ce, saboda a cewar ta shi ya Fara kawo Mata cartoon din Sofia the first, wannan shi ne dalilin da yake ce Mata Sofia. Bayan ya zauna yace
"Sofia the first!"
Ya fada da murmushi saman fuskar shi, ta gyara Zama Bayan ta jira ya gaida Alhaji Gidado, sannan Suka gaisa tayi Masa murnar Gama makaranta da Kuma dawowa gidan cikin aminci da alkhairi, yayi murmushi Yana Mata godiya, a hankali daya biyu Kuma se ga iyayen su suna zuwa, dukka Suka gaishe su, Amma ganin Safiyya bata tafi ba se ya tabbatar wa da Kan shi taron har da ita, shi Bai maga tashi matar ba, tun da yazo Bai ga Rukayya ba, baisan Rukayya na dakin Mujahid ba, shi ta aura ba shi ba. Ganin lokaci ya cika se kawai akai proceeding da tattaunawar da zaayi, anan ya gabatar musu sabon construction company da ya bude Wanda ya damka shi kacokam hannun Imam, sannan ya tabbatar wa Imam Safiyya ce matar shi, a hankali ya dago Yana kallon ta Haka itama tana tayi Masa murmushin nan Mata me kwantar da hankalin, Haka kawai se yaji kaso me tsoka na damuwar da take ciki ta tafi, idan har Safiyya ce then komai zai zo da sauki.
Bayan an Gama suka fito Bayan dogayen adduoi da Kuma nasiha da akai musu, suna tafe kowannen su yayi shiru zukatan su na tunani mabanbanta. A Haka Suka karasa wajen Ummiey shi, ta saka musu albarka, a ranar Bai samu damar komawa wajen zainab ba, se ya zauna a dakin shi yana tattaro bakin zaren, Yana ayyana yadda zai Fara, saboda kukan da zainab tayi yau da safe ba zai iya cigaba da ganin shi ba, ba zai iya boyewa ba saboda shi din ba Haka yake ba.
Da daddare aka raka shi well furnished gidan shi, gidan da akai Masa shi da Safiyya, Bayan dukkan abin da sunna ta tanada se Suka Fara Hira like the old friends they were. Ya tambaye ta dalilin fasa bikin shi da Rukayya? Se ta fada Masa ai ganewa akai suna soyayya ita da Mujahid shi ne yasa aka fasa akace gwara ta aura Mujahid tun da dai har sun Riga da sun shirya Kan su. A bangaren shi se yace
" Safiyya! Ban taba kawowa cewar Zan aure ki ba, though I've been eyeing you akan auren Ashe ke rabo na ce"
Tayi murmushi tana sunkuyar da kanta kasa irin kunyar fulanin nan, yace
"Ina son ki saurare ni, Ina son ki nutsu nayi Miki bayani Safiyya"
Ta dago ta kalle shi taga fuskar shi Babu alamar Wasa, hakan ya tabbatar Mata da gaske yake maganar me muhimmanci ce,
"Ina da aure Sofia! Yes da gaske nake nayi aure shekaru wajen hudu Sofia, I can't tell anyone Sofia, kinsan yadda muke rayuwa a gidannan, I'm scared!"
Tabbas tayi mamaki, matuka ma kuwa Amma Kuma ba abin mamaki bane ba Dan dama kowa yasan Hamma Imam daban yake tun Yana yaro, duk wani abun Jan magana to ya iya dakko shi. Tasan tana son shi, tana son shi sosae, ko ranar da aka ce Mata zata aure shi, kusan murna hanata bacci tayi, har se da Dada wato mahaifiyar ta ta fahimta, anan ta Fara Bata dabarun yadda zata karkato hankalin shi gare ta tun kafin ma ya dawo, Kuma ko Ummiey ma Haka tayi ta Zama da ita tana nusar da ita dabarun sace zuciya tun da suka Haka akai musu aure ba tare da son rayukan su ba. Dole ka danne halin da kake ciki Dan ka faranta Masa Rai.
"Tana Ina? A Ina ka barta? Tana can UK din?"
Ya Kama hannun ta for the first time saboda abin da yake gani cikin idanun ta, she's trying hard to suppress kishin dake taso Mata, yace
" Nazo da ita..."
A hankali ya kwashe komai da komai ya fada Mata, tun daga soyayyar su day komai da komai, labarin soyayyar tasu se ta kayatar da ita ta Fara murmushi tana Jin Bai kamata su rabu ba, se da ya Gama yace
" Bansan ya zanyi ba Sofia, Kai na ya kulle na Rasa yadda Zan fadawa wani cewar bake kadai bace Mata ta ba!"
Ta saki nannauyar ajiyar zuciya tace
"Ina son na ganta please, zaka kaini?"
Yayi murmushi Yana matsa hannun ta yace
" Of course Dear! Ya zanyi? Ki bani shawara"
"Take it easy and slow, kasan gidannan ko bango na da idanu da kunnuwa!"
Wannan abun da tayi Masa ya Bata kaso me girma cikin zuciyar shi, washegari ta shirya suka fita, Basu zame ko Ina ba se hotel din da zainab take. Baiwar Allah tana zaune yau ko breakfast din da aka kawo Mata Bata bude ba, tayi kuka cikin dare har ya hakura Dan kuwa tasan ta rigada ta shiga one chance, tana ganin rayuwar ta ta lalace, sede she's already stuck in this mess, soyayya a ganin ta batyi Mata adalci ba, Dan kuwa ta kawo ta kushewar ta, ta Ina zata Fara wannan yakin? Ina zata Fara wannan fadan da mutanen da bata San su ba, Bata San yaren su ba balle wani Abu nasu. Hawaye ya cigaba da sakko mata a kuncin ta, ta kalla lokaci past 10am Amma har yanzun Bai zo ba. Kawai se taji knocking a kofar dakin, cikin sauri ta Mike jikinta har wani rawa yake ta fita, tana zuwa ta bude ba tare da ta tambaya ba balle taji ko waye. Sofia tsaye da wani murmushi da yake saka mutane suji kaunar ta a zuciyar su, a Bayan ta Imam ne tsaye Yana Mata murmushi shi ma, da sauri taji wata nutsuwa tana saukar Mata, sede ta Kara kallon Safiyya tana ayyana wacece ita? Amma se taga suna Kama shi da ita, banbancin su kasancewar Safiyya tana da haske shi Kuma Imam duhu ne da shi. Ta sake sakin ajiyar zuciya sannan ta Basu hanya suka shigo, at least taga wani Dan uwan Imam hankalin ta a bit ya dan kwanta. Ta bawa Safiyya guri ta zauna, cikin sauri ta wuce t hado musu coffee cikin kananun mugs ta kawo musu sannan ta zauna. Suka gaisa, ta tamabye shi cikin simple larabcin da ta koya Masa Akan wacece wannan kyakyawar da batta gajiya da murmushi? Cikin turanci ya Bata amsa yadda Safiyya ba zata tsargu ba, yace matar shi ce ta jiya kuma cousin din shi, tayi shiru ba tare da tace komai ba, Safiyya ta matsa gefen ta a hankali tare da rungume ta tana murmushi tace
" Jiya dare muka raba Yana bani labarin ki, se gashi da na ganki se naji you were underestimated!"
Zainab ta Dan saki murmushin Jin dadi na maganar da Safiyya ta fada, Amma dai Bata ce komai ba, se da Safiyya tace
"Naji labarin soyayyar ku, tayi min Dadi I'm mesmerized by the story, sede Zan taimaka muku iya bakin kokari na wajen ganin Baku rabu ba. But be patient zai Dan dauki lokaci"
Wannan abun da tayi gaba daya ta jefa musu yardar ta cikin zukatan su. A karshe ta dan nema izinin shi Dan fita ta Basu waje su zanta. Tana fita zainab tana murmushi tace
"I like her!"
Sun Jima suna Hira kafin ya Mata sallama Suka tafi, to shikenan se ya zamana Haka suke kusan kullum zasu zo tare tun da Bai Fara zuwa aikin ba saboda company baa gama wasu touch ups ba. Wannan ya Sanya shakuwa me karfi tsakanin zainab da Safiyya, Suka Zama tamkar siblings, har lokacin mutum daya kaf wannan family Suka fadawa wato Ummiey, ta tsorata sosae, ta dinga yiwa Imam fada Amma se Safiyya ta nuna Mata tayi musu addua Dan tana ganin zainab zata ji soyayyar ta.
A Haka wata guda yazo ya wuce, kamar Wasa Haka Imam yake gani, Wai duk mazantaka da tsaurin idanu da rashin tsoro ya kasa bayyana wannan maganar. Hatta Safiyya ta fishi jarumta Dan ita tayi yunkurin fadawa old Man kamar yadda suke Kiran shi, Imam ke hanata saboda tsoron makomar zainab, idan Dan ta shi ne zai iya jurar komai da zaayi masa.
Wani dare Suka dawo daga wajen ta, sun samu Bata da lafiya, sun Kai Mata duk abinda take bukata kafin Suka rabu Dan da farko Safiyya ta yarje Masa kwana wajen ta, se zainab Taki amincewa kada a zargi wani Abu. A yadda Safiyya ke Bata labarin family din su ta fahimci she's trapped in a lion's Den. So itama hankalin ta yafi kwanciya zamanta anan Kuma a hakan. A wata na biyu Ummiey taga zainab, bisa rakiyar Safiyya, tabbas taji kauna da Kuma tausayin ta sun lullube ta Amma Yaya zatayi? Babu yadda ta iya, Dan Haka a wannan Daren cikin siyasa ta fadawa mijin ta wato mahaifin Imam abin da yake faruwa, Tsabar girgiza da yayi se da ya tashi ya zauna daga kwanciyar da yake, yace Mata cikin kasa da murya
"Fatima wacce irin magana ce wannan? Imamu na da hankali kuwa? Bazai daina ja min magana a wajen Baffa ba?"
Ta Kara kasa da murya tace
" Me faruwa ta faru, kawai ka fada Mana yadda zamuyi, ya kamata yarinyar nan a bayyana ta Haka.."
Ya girgiza Kai saboda ya kasance me tsoron mahaifin shi ne yace
" Ba Zan iya ba, bana son bacin ran Baffa, bana son tashin hankali kinfi kowa Sanin hakan ko?"
Tayi shiru tana tunanin mafita, wadda har safiya tayi Basu comma matsaya ba. Duk movement din su Ashe Alhaji Gidado ya sani, Malam magaji driver ya sanar Masa inda suke zuwa shi da Imam da Safiyya. Da yammaci zainab da ta dandana tuwo taji Dadi ta fadawa Safiyya tana son ta kawo Mata irin shi, Dan Haka Safiyya ta dage ta tuka tuwo tayi miyar da ta wadatu da nama sannan ta juye cikin kwanuka masu kyau, har zobo tayi Mata ya Kuma shirya tana jiran dawowar Imam...
To be continued
Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 028
"Baki ji ba? Baki ji abin da nace Miki ba?"
Na dubi Adda confusingly nace
" Adda Suleiman fa? Kai! Dan Allah kiyi hakuri, Dan Allah ku bawa Kawu hakuri Nima Zan samu miji na ko ba dade ko bajima!"
Tace cikin Bata fuska
" Waye yace miki opinion din ki ake nema? Waye yace miki option aka Baki, to Bintu ban da abunki waye zai zo kina shekara ashirin da biyu har yanzun Babu Wanda ya taba zuwa wajen ki, sannan kice Zaki samu mijin ki?"
Kunsan kullum Ina fada muku shi harshe mugun Abu ne, gashi dai tsoka ce amma kaifi ne da ita, zata iya yanka har zuciyar mutum, be wary of abin da kuke furtawa. I'm so sorry to say abubuwan da dama laifin iyayen mu ne, saboda yawancin wannan body shaming din Yana faruwa ne daga gidajen mu, yawancin iyayen mu su suke Fara aibata mu Wanda yake saka Mana shakku cikin zukatan mu, ni na zame muku misali a rayuwa, ya kamata ace mu iya bakin mu
" Adda me yasa kuke min Haka a gidannan? Wani laifi nayi da kullum bani da say a cikin rayuwa ta se abin da Batuul ta rage shi Zan dauka..."
Mari naji akan kunci na Wanda yasa nayi saurin rufe Baki na, nasan Nima tabbas Bai kamata na Fadi Haka ba, to Amma Kuma zuciya ta ta kekeshe, wanne irin Abu ne wannan? Ya zaayi a hada ni da Suleiman! Zuciya ta kamar zata fito Haka nayi taji, na mike kamar jiri zai fadar Dani nayi daki, Ina zuwa na samu Batuul a kwance tana waya
" To Hubby kwana nawa ne munyi aure? Why not ka jira ayi sealing deal kafin muma muyi sealing namu deal din"
Wannan shi ne abin da na Fara jiyowa da na shigo dakin, na fada Kan gado na Fara wani irin kuka har jiki na Yana wani irin rawa, tayi saurin sallama da shi ta taho waje na a rude tace
" Bintu me ya same ki? Bintu ya kike irin wannan kukan?"
Yadda take fada a muryar ta ta tabbatar min how much she cares, Amma Karo na farko se naji wata irin tsanar Batuul ta Shiga zuciyata, naji komai da yake faruwa saboda ita ne, why am I cleaning after her mess?!
Kuka kawai nake, da Naga zata takura min se na mike na wuce toilet na rufo kofar da karfin gaske, na sunkuyar da Kai na akan sink Ina wani irin kuka Wanda har addua nake dama ace numfashi na ya yanke na Fadi na mutu, nayi kukan har na gaji, Haka Batuul ta buga kofar kamar zata balla ta gaji, se ta Fara fada min
" Bntu kiyi hakuri koma menene? Bintu Dan Allah ki fito wannan wanne irin kuka kike? Me ya faru?"
Nayi Mata banza, se kawai ta fita taje ta samu Adda ta sanar da ita abin da yake faruwa, ta cigaba da kurbar tea din ta tace
" Tayi duk abin da zatayi, auren Suleiman dai babu fashi Kuma ta sani, kiyi kwanciyar ki ki rabu da ita!"
"To ai bazan iya bacci ba tana wannan kukan"
Se tace Mata
" Yi kwanciyar ki anan, taje ta Gama ihunta ita kadai!"
Wannan Daren banyi bacci ba, kuka nayi shi na Kara, na sake Yi na Kuma to addua shi ne abin da yasa na dan samu saukin abin da ke zuciya ta. Washegari da wurwuri na shirya na tafi school, bayan na Gama lecture ma ban dawo ba se na tafi wani guri can gefen wani faculty na shimfida sallayar da bana rabuwa da ita, na dauki waya ta na Fara neman tips na yadda mutum zaiyi shading kibar shi, abin da ya Fara popping a gurin shi ne dieting, se na kudura aniyar daina cin abinci ko na samu na rage kiba, walaallah a daina musguna min, na Kuma samu mijin da Zan aura ba Suleiman ba.
Present day!
A hankali na Fara kokarin ganin ko ta wanne Hali na samu na zabge wannan kibar dake jiki na, ko Zan samu na samu afuwar rayuwa, na daina Jin Kai na kamar wata alien wadda tazo daga wata duniyar ba Earth ba, na saki ajiyar zuciya Ina gwada nauyi na akan bathroom weighing scale din da na siyo, 85kg shi ne abin da na gani, na Fara duba jiki na tun daga fuskata da kurajen da suke mutuwa Kuma suke sake dawowa, na kalla fuskar da kyau Ina ayyana I need a tangible skin care products na fara amfani da shi ( for visibility and advert send in your product). Na lumashe idanu na wannan shi ne first step din da na Fara dauka. Na karewa jiki na kallo da kyau sannan na Yi wanka na fito na duba wardrobe di na , duk yawancin Kaya na boubou style ne bana son wani style Kuma saboda tun Ina yarinya idan nace Ina son style din da Batuul ta zaba se ace min, ai ba na masu kiba bane ba. Shiyasa nake karbar duk abin da aka Dinka min.
Na shirya fes sannan na murtsika Addictive Ambergris, shi ma daya daga cikin turarruka na SCENTMANIA ne, Yana da kamshi Yana da Dadi very affordable, wadda batai amfani da shi ba tabbas kamshi ya barta. Na wuce kitchen na dauki packages slice cake din da nayi saboda na kaiwa su Alamin, Bayan taimakon da sukai min da na Fadi a class ai they deserve more. Ina gamawa na kalla Irish da kwai da aka kammalla cikin warmer, ciki na yayi Kara Amma na dauke idanu na akan abincin I need to do it, I need to shed my weight ko na samu Abu yayi kyau, na samu mutane suyi accepting di na. Ban sani ba shirme nake Yi ko a daidai.
Bansan akwai zancen test ba se da na karasa school, na samu me building construction and materials Yana kokarin yin test, na zauna na karba question paper nayi scanning da idanuna, Haka nan na karba ba Wai Dan inada tabbacin Zan iya ba, tunda ban taba bude littafin ba. A hankali na samu na amsa Wanda Zan iya na Yi ticking abin da zuciya ta ta Raya min. Muna kammallawa naji kaina ya Fara juyawa Yana Kuma ciwo, na daure na ji lecture din, Bayan ya fita na bawa Alamin sakon da na kawo yayi min godiya sosae na dawo na zauna. Lecture din karshe ta Akram ce, lokacin na gaji Kuma Ina da tabbacin yunwa nake ji, carrot din dake jaka ta na dauka naci sannan na Sha ruwa se naji saukin abin da nake ji. Babu jimawa se gashi ya shigo, kamar kullum fes da shi Dan gayu, ya Sha farin yadi me layi layi, Amma na kasa gane wanne color ne layin, Kan ya hau podium yazo Kai na ya tsaya, hakan yasa na gaishe shi a hankali, ya amsa ba tare da ya kalle ni ba,
" Have you ate?"
Se na Dan ji kamar I'm embarrassed, na gyada Kai na yace
" Better! Bana son a dinga interrupting class di na"
Bai jira amsa ta ba yayi gaba, na Dan daga murya yadda zaiji nace
" Sir thank you! Sakallahu khairan!"
Se naga ya Dan tsaya a hankali kafin Kuma ya juyo ya gyada min Kan shi ya koma Kan podium, cikin turanci shi me tsafta ya Fara binmu cikin course din, Ina ta fahimta se can na Fara hango shi bibbiyu, na kasa bude idanu na da kyau, se gumi me yawan gaske ya wanke min fuska a take na Fara wani irin numfashi, daga nan bannsan Kuma me ya faru ba....
***
Da murmushi Imam ya shigo, wani irin kallon kauna yake bin Safiyya da shi, tabbas a zaman su da farko bai sonta ko kadan amma wannan kauna da take yiwa zainab yasa zuciyar shi ta Fara karkatowa gare ta, cikin saa Kuma se ya Fara son ta, ya Fara Jin ya damu da ita albarkacin son da take yiwa zainab. Ko wannan basket din da yake aje se ya Kara sawa yaji kaunar ta a zuciyar shi. Ita dai tayi nasara dan kuwa zuciyar ta me kyau ta saka ta samu matsugunni me kyau a zuciyar da Imam yake ganin ta zainab ce kawai. Tare suka fita suna ta hirar su cikin soyayya, tana ta murmushi na Jin dadi, mahaifin ta Baffa Nasiru Yana zaune ya dube su bayan yayi musu izinin su tashi daga tsugunnon da sukai, yace
" Wai imamu Ina kuke zuwa kullum ne Kai da Safiyya?"
Ya Sosa Kan shi yace
" Aboki na ne bashi da lafiya zamu je duniya!"
Ya shi musu albarka sannan suka shiga mota inda driver ke jiran su. Kamar kullum kofar hotel ya sauke su suka shiga shi Kuma yayi parking karkashin bishiya. Zainab tana ta murna mussamman da taga abincin nan, ta zauna dukka suka hadu suna ci suna hira cikin Jin dadi. Knocking da Suka ji yasa dukka Suka tsaya da dariyar da suke, Imam ya dubi zainab yace
" Solace waye?"
Ta girgiza Kai tace
" Ya Zan sani, I dunno!"
Safiyya da Haka kurum taji gaban ta ya fadi tace
" Bari na duba na gani"
Ya dakatar da ita ya mike, yaje Yana budewa yayi mummunan gani, to mummunan gani Mana tun da kuwa Alhaji Gidado ne a tsaye da Kuma Alhaji Mamuda Wanda ya kasance kakan Safiyya na wajen uba, kakan Imam na uwa. Imam ya tsaya ya tokare kofar ba tare da ya matsa ba, Amma jinin shi kadai ma tafasa yake saboda ya firgita ba kadan ba har firgicin yayi nasarar bayyana saman fuskar shi. Jin shiru yasa zainab tace
" Chum Chum waye?"
A lokacin ya saki kofar Alhaji Gidado da Alhaji Mamuda da Kuma biyu daga cikin uncles din su Suka shigo Baki daya. Safiyya a firgice ta Mike Allah yasa ta hadiye abin da ta saka da babu yadda zaayi Bata kware ba. A take jikin ta ya Fara rawa kamar ana kada Mata mazari, ta dubi zainab da take tambayar ta su waye? Kafin ta Bata amsa taji saukar Mari a saman kuncin ta, wani dummm taji a kunnen ta, kafin marar ta ta tsikare ta, Amma zafin Marin yafi zafin ciwon da take ji a marar ta. Da sauri Imam ya taho ya tsugunna gwiwa kasa gaban Alhaji Gidado Yana fadin
" Matata ce! Auren ta nayi daga UK, don't get the wrong idea!"
Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 030
_Ni me laifi ne, bani da Kuma bakin da Zan Baki hakuri solace. I've hurt you ever since da na tafi Dake Nigeria, nasan ni coward ne, Ni matsoraci ne but wallahi zainab wannan shi ne kadai abin da Zan iya Yi nayi protecting din ki ke da Akram, thank you for raising this child alone. Thank you zainab, I never wanted to be a source of pain in your life, but this is the path we must cross. I'm so sorry, na sake ki saki daya to free you from this shackle..._
Kuka sosae zainab take tana kankame takardar, ta kasance mace ce me uzurin gaske, amma a yau zuciyar ta ta kasa yiwa Imam uzuri. Me yasa da yazo ba zai ce mata yazo tafiya da yaron shi be, must he stoop this low just to take away what belongs to him. Tasan shekaru bakwai da suka gabata tayi Masa uzurin zaman shi helpless, tasan Babu yadda zaiyi aka raba su, Haka tasan wannan tsohon kakan nashi ya saka shi shafe shekaru bakwai ba tare da ya waiwaye ta ba balle har yasan ta Haifa Masa Dan shi. Se wannan lokacin, out of nowhere yazo Kuma yayi sati Bayan tana ganin kamar komai ya warware se kawai ta bude idanu cikin dare taga babu Akram danta Kuma babu Imam, dukkan laifukan shi na baya ta yafe Masa Amma tana tantamar idan zata iya yafe Masa wannan, ga Kuma wani saki da yayi mata, ya sake ta! Hawaye ya cigaba da saukar Mata a kuncin ta, har yaushe zata ji dadi ita kuwa? Shima yaron se da suka samu labarin haihuwar shi Suka dauke shi, wanda shi ne kadai abin da ya rage Mata na Jin Dadi a rayuwar ta.
Dawowar police officers din se ta nuna musu tasan Wanda ya dauka yaran sunyi communicating, police din sukai shiru alamar basu yadda ba Amma yadda ta dinga convincing din su dole suka tafi. Daga Haka ta Fara tunanin yadda zatayi da rayuwar ta, ta San a duniya in dai Safiyya na raye, Ummiey na duniya to tana da tabbacin Akram ya samu uwa mussamman da yace Safiyyar bata haihu ba har wannan lokacin.
Ta Shiga dakin Akram tana Kara kallon kayan shi a barbaje na.wasa, hawaye ya zubo Mata tana Kuma adduar ya kasance kada Akram yayi kewar ta, sannan Allah ya Bata ikon cigaba da rayuwa yadda ya kamata.
Da Rana tsaka Suka iso kasar Nigeria, cikin birnin kano, driver na jiran su tun safe Dan Basu ma Fadi karfe nawa ne zasu dawo din ba. Bayan driver har da mujahid a masu tarban su. Tunda suka Shiga jirgi Akram ya lafe a jikin Imam, saboda adan kwana biyun da sukai tare ba karamin sabo sukai ba, har suka kwana a Abuja baya zuwa ko Ina se gurin shi, ko kallon Alhaji Gidado da lokaci daya yaji so da kaunar yaron ta tsarga masa cikin zuciyar shi Amma ko kadan Akram yaki ya yarda ya raba jikin tsohon kamar yasan shi ne Wanda yayi destroying rayuwar mahaifiyar shi. Imam dai Yana zaune ne Amma zuciyar shi se tuhumar shi take akan dalilin abin da yayi, he needs his freedom ya sani, Amma Kuma neman freedom ba shi bane ba abin da zai saka yayiwa zuciyar da ta so shi, ta kaunace shi, ta kyautata Masa Haka ba. Yasan Alhaji Gidado yayi Masa barazana da dakko Akram ya samu yancin zuwa kowacce kasa da yake so hakan yayi amfani da shi, sede Kuma ya kasa nutsuwa Yana ayyana a wanne halin zainab din take, ga rashin Akram ga Kuma mutuwar aure, Abu goma da ashirin!
Fast forward, Suka fito daga departure hall, Suka fito farfajiyar airport in da suka hangi driver na jiran su, Haka Suka karasa Yana sabe da Akram duk da girma da yayi. Mujahid da murna ya Fara kokarin karbar Akram tare da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 18