her addua ko da Bata Raye"
In dai maganar Zainab ce to har yanzun ita ce weakness din Imam, cikin wani irin yanayi yace
"Tsoron yadda zai fahimce ni nake shiyasa duk wannan lokacin na kasa sanar da shi saboda nasan zai kalle ni a matsayin Wanda ya Gaza ya Kuma kasa protecting Babar shi"
"Bana tunanin hakan Abba, Akram is an understanding person, na tabbatar da kwakwalwa zai saurare ka ba da zuciya ba. So Allah ya kaimu goben."
Wannan Daren Imam Haka yayi ta juyi, yasan Babu ranar da tazo ta wuce baiyi adduar bayyanar zainab ba, saboda kullum Yana blaming kanshi a matsayin Wanda ya lalata Mata rayuwar ta, saboda yasan ita soyayyar shi Babu abin da ta samar Mata Banda tsananin tashin hankali, hargitsi da Kuma lalacewar rayuwa! Amma yasan lokaci yayi da ya kamata ya sanarwa Imam wacece zainab!
Washegari da wurwuri Safiyya ta kammalla breakfast, dukka a tare suka ci abinci dukda Akram nashi daban ne da Wanda sauran ke ci. Bayan sun Gama Safiyya ta dakatar da Akram daga komawa dakin shi, saurin da yake yaje ya Kira ni kamar yadda yayi min alkawarin. Sauran yaran ta tura su daki. Safiyya ta dubi Imam da ya Zama kamar anyi Masa mutuwa, tace
" Abba let's get started! Akram Abban ka Yana son magana da Kai me muhimmanci, Ina son ka bashi aron hankalin ka kaji?"
Ya gyada Kan shi, a lokacin ta Mike zata tafi, Amma duka suka tsayar da ita saboda ita ce strength din kowannen su. Haka ta koma ta zauna. A hankali shi Kuma ya Fara bawa Akram labarin shi da zainab, har ya Gama sannan yace
" Kayi hakuri na rufe maka all this while, inata kokarin ganin na ganta before you come up age wannan shi ne dalilin na"
Akram da idanun shi yayi jawur Yana ta furta innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Wani irin mawuyacin yanayi zuciyar shi take ciki, shiyasa ko sau daya Bai taba Jin wannan community din ta burge shi ba, shiyasa ya tsani Alhaji Gidado da wasu daga cikin kakkanin iayyen shi, Ashe abin da sukai ma mahaifiyar shi kenan? Ya rasa abin da zai fada se shiru kawai da yayi!
Ta_kwalam
[1/3, 20:28] Maman: 039
Dakin shi ya koma a hankali, yayi tsaye Yana kallon dakin ba tare da Sanin abinnda ya kamata yayi ba, tuntuni yasan Safiyya tabbas ba ita ta haife shi ba amma Bai taba tunanin wannan shi ne abin da wannan mutanen da suke Kiran Kan su family sukai yiwa mahaifiyar shi ba. Bayn maida ta kasar ta, Bayan zaman shekaru bakwai da aure a Kanta Kuma babu miji, an barta da ciki ba tare da mahaifin cikin ya ma San da zaman cikin ba. Allah kadai yasan the hell she went through while raising him alone. Se Kuma dare daya, Rana daya, lokaci daya bayan ta hakura ya Kuma Saba da rashin kowa a ryuwar ta, da Zama ita kadai a rayuwa. Se Imam ya sake lallabowa ya dawo Mata da dukkan wasu memories da sukai fading, memories da ta Riga ta aje a gefe ya dawo dasu, he conspired and took him away ba tare da ta sani ba. Ya wannan abun zai je ma mutum? Duk da memories din na shi akan ta fragments ne, Amma dai zai iya tuna har lokacin da take murnar zuwan Imam, da Bayan ya dawo daga school take fada Masa Imam ne mahaifin shi, se Kuma tafiyar da sukai me tsawo daga kasar Qatar din wadda da bai masan ya sunan kasar ba se yau.
Ya dunkule hannun shi Yana sakin numfashi dai daya, zuciyar shi Banda zafi Babu abin da take Yi,duk wani kokarin Kare Imam da yake, da kokarin Yi Masa uzuri ya kasa Yi a yau, yama zaka dauki responsibility din abin da kasan ba zaka iya ba, ya zaka Fara wannan? And he shamelessly tell him Wai Yana son ta? Wannan shi ne so? Idan har wannan shi ne so to shi nashi abinda yake ji akam Bintu ba so bane ba, saboda ya saka Bintu a matsayin zainab, idan shi ne se de ya bar duk wani wealth and fame ya zauna da Bintu, Amma mahaifin shi ya zaba company over his mother that sacrificed everything for him!
A Dan kwana biyun da Muka kasance very close ni da Akram, na gane mutum ne shi me cika alkawarin, zaiyi wahala yace I'll call you back, Kuma Bai Kira ba. So kamar yau da safe Muna cikin waya Yana Karan boosting confidence di na ta hanyar nuna min I'm beautiful the way I'm, shi ya yadda idan na danyi shading few kilos for the sake of my health, Amma Bai yadda Dan Wai muatne na zauna na dinga Shan abubuwan da zasu kashe min jiki in no time ba. Duk maganar da ya fada min, zuciyata da kwakwalwa ta kawai amsa take, Bata ma wani tsayawa yin musu balle ta nuna ba zata yadda ba, komai ya fada se naji kawai ya zauna cikin Kai na Kuma kamar wajibin dole ne na se nayi amfani da hakan. Nayi kusan awa Ina kallon waya ta Ina jiran Kiran shi Amma Bayan wajen awa da wani Abu se ga message din shi ya shigo
_Zan Kira ki anjima in the evening, I'm a bit busy please_
Na saki ajiyar zuciya har Ina mamakin irin wannan damuwa da nayi da shi, but Kuma ai Noor Dina ne, Wanda ya sama min farin cikin da nake ganin na Rasa Shi a duniya, confidence din da bani da shi se gashi na Fara Dan jin a bit of Nima fa dan ina da kiba I can stand out cikin mutane Kuma har babu damuwa. Karfe hudu nake ganin shi ne evening, so kafin hudu komai da komai da zanyi har karatu, girki da komai na gama kawai nazo na zauna na saka wayar a gaba in anticipation for his call, Amma har isha Babu Kira Babu dalilin shi, there and then na tabbatar Babu lafiya, duk inda Noor yake bashi da lafiya. Wajen takwas na dare na kasa jurewa se kawai na dauki waya na Kira shi dukda zuciya ta na tuhuma ta Akan zakewa da nake, Amma abin da nayi se nace ka gaida me gaishe ka ko bazai amsa ba, Kuma mutum ya damu da Kai dole ka nuna mishi kulawa. Da wannan na samu na Kare kai na daga tuhumar da zuciya ta take min.
Wayar shi bata shiga, har nayi bacci Ina trying Amma ban samu wayar ta shiga ba. Nayi ta mafarkin shi Wanda ma da na tashi na kasa gane me mafarkin ya kunsa, kawai dai nasan saboda he has been in my thoughts the whole day shi ne dalilin mafarkin na shi da nayi. Wannan ranar ma Haka ta wuce the whole day ban samu munyi magana ba, idan na Kira shi bana samun shi, gashi public holiday aieyi balle ace Zan iya zuwa makaranta na gan shi. Gaba daya na damu, nutsuwa ta ta ragu, bani da wani kwanciyar hankali ko kallo na kayi kasan akwai abin da yake damuna sosae, a kwana na biyu na tashi da kamar zazzabi zazzabi saboda damuwa, nayi ta Kiran shi a waya har wajen Sha biyu na Rana, wannan karon tana shiga dauka be baayi, zuciya ta ta gama tsinkewa na Kuma Fara gane zuciya ta ta zarme wajen son shi, wata kan Bata manta abin da ya faru ba da BashPrince00, ta Kara zuwa ta Fara son wani Kuma, but Amma a yanzun duk ba wannan me damuwar ba, damuwa ta shi ne yadda zaa Yi nasan me yake faruwa da shi.
Ina zaune Bayan na idar da sallah Ina ta adduar Allah yasa lafiya yake, Allah yasa ba wani Abu bane ba marar Dadi ya faru da shi ba. Wayata na sake janyowa a Karo na babu adadi na sake Kiran shi, cikin hukuncin Allah se gashi an dauka, ban tsaya nayi comprehending muryar da tayi min magana ba kawai cewa nayi
" Sir! Me ya faru? Are you ok?"
Safiyya ta lumshe idanun ta, hannun ta Yana cikin hannun Akram da har lokacin Bai farfado ba, kallon fuskar shi take wadda tayi kamar an zabge ta saboda ramar da yayi lokaci daya kamar Wanda ya jima Yana jinya, Dana sani ta kasa dainawa, Bata taba tunanin ko da Wasa wannan maganar zatai affecting din shi haka, da tuntuni sun fada mishi ko Kuma sun bar maganar. Tun ranar da ta fada Masa shekaran jiya da ya shige dakin shi Bai sake fitowa ba se sallah kawai yake fitowa yayi ya dawo, Yana dawowa Kuma zai kulle dakin shi deep in thought, ya rasa ta Ina zai Fara kamo zaren balle yasan ta inda zai Fara neman mahaifiyar shi, Haka Kuma ya kasa yiwa mahaifin shi uzuuri saboda Yana ganin duk abin da ya faru sakacin shi ne ba wani abun ba.
Safiyya da Imam har na da yaran.dukka hankalin su ya tashi musamman da yaki yaci abinci Kuma sunsan hakan zai iya leading to babbar matsala, Safiyya Babu ban Baki da batayi ba Amma sede ya Sha ruwa kawai, a Rana na uku wato yau din shi ne ya fito dan zuwa suyi magana da Safiyya ya yanke jikin shi ya fadi a kasa. Suna zuwa asibiti an Riga da an San condition din shi tun da nan yake ganin likita dama aka Fara bashi taimakon gaggawa, saboda abinci da baici ba glucose din Dake jinin shi ya sauka Wanda ko me lafiya ya sauka haka to tabbas jikin shi ba zai amfanu ba balle shi da dama yake.da issues.
"Fatima ce?"
Shi ne abin da Safiyya ta tambaya, saboda sunan da ya saka ta kasa gane maanar shi, duba kuma da yawan zance na da yakeyi, da maganar da sukai yasa ta fahimci nice me Kiran. Kamar zance a'a se nayi saurin fadin
" Ni ce"
Ko Bata ce komai ba nasan Babu lafiya, tunda da lafiya he supposed to pick up his phone himself, ba Wai a daga Masa ba, Amma Jin muryar ta se naji nauyin tambayar ta yadda yake, kamar tasan abinda nake tunani tace
" Fatima, Akram bashi da lafiya! Muna asibiti Bai masan inda Kan shi yake ba!"
Wani irin duummmmm naji cikin kunne na Kai na har da Kai na, na Yi shiru Ina assimilating abin da ta fada,
"Kina ji na?"
Nayi saurin girgiza Kai hankali na ya Riga da ya Kai kololuwar tashi nace
" Me ya same shi? Wanne asibitin kuke?"
Ita ta fada min komai, na mike ba tare da nace komai ba na canja Kaya na, na zura gogaggen hijab sannan na fito zuwa dakin Mamaa idanuna sunyi jawur, kana kallo na kasan bana cikin nutsuwa balle kwanciyar hankali, Mamaa na zaune ita da Zuhriyya da tazo da bansan yaushe ba, na shiga nace Mata zanje dubiya, ko amsarta ban jira ba na fice Ina Jin kamar nayi tsuntsuwa naje gare shi. Mintina ashirin da wani abua suka kaini asibitin, ta Riga ta fada min bangaren da suke hakan yasa na tafi Kai na tsaye, har lokacin zuciya ta ce kawai take tafiyar da ni Amma ko kadan kwakwalwa ta Bata ankare da abin da yake faruwa ba. Se da naje kofar dakin inda na Dan ga mutane, se na Fara tunanin me yasa nazo? A matsayin wa nazo? Nayi shiru na kasa motsawa har seda wayata ta Fara ringing kafin na dawo daga dogon tunani hade da wasiwasin na shiga ko na juya da nakeyi
" Kina ina?"
Ta fada Bayan na dauka, a hankali nace
" Ina kofar dakin da yake!"
Se tace na jira gata nan zuwa, Babu jimawa se gata ta fito, dukda yanayin damuwa da fuskar ta ke ciki, Bai hanata yimin murmushi ba, na tsugunna har kasa Zan gaishe ta ta dakatar dani ta hanyar Kama kafadu na tace
" Muje, nagode sosae da Kika zo!"
Haka muka shiga ciki, Yana kwance ruwa na shiga jikin shi, bakin shi ya bushe yayi fari Haka jikin shi baya wannan shekin da yake a Koda yaushe. Noor ne a kwance Haka? Kawai se na Fara kuka a hankali, zuciya ta gaba daya ta karye ji nake kamar na tashe shi ni Kuma na kwanta madadin shi, to Babu halin hakan. Mahaifiyar shi wato Safiyya wadda naji suna Kira Ummaah ita tayi ta lallashi na dukda wani lokacin se ta goge hawayen da yake zubo Mata, kowa yazo dubiya se ya tambaye ta ni wacece? Bata ma fiye bada amsa ba. Anan na lura yadda suke Kama sosae da junan su day fullanci da suke tayi gwanin shaawa, Nima naso ace na iya wani yaren Bayan Hausa da turanci!
Ta_kwalam
[1/3, 20:30] Maman: 041
Ban yanke hukuncin abin da Zan fada Masa ba har dare yayi, zuwa lokacin I was very anxious na San zai bukaci Sanin amsar request din shi, na zauna nayi tunani na Kuma Kara tuanani, abin da yafi komai Dadi da sauki a rayuwa shi ne nayi kokarin bawa wannan bawan Allahn chance. Se Kuma naji tsoro nake, what if idan tarihi ya sake maimaita Kan shi? To saboda me ma zanyi wannan tunanin? Kuma saboda me zai maimaita kanshi, tunda dama relationship di na dana BashPrince00 was a blind relationship, ko kadan bamu taba haduwa ba, Kuma a ranar da ya ganni yaji baya so na, se ya zaba wadda yake ganin ta dace da rayuwar shi!
Wajen karfe takwas na idar da sallar ishai, Ina zaune saman sallayar na bude littafin Ina dubawa saboda kada naje gobe ayi Mana test wadda zata hautsina ni. Ina yin karatun Amma fin Rabin hankali na Yana kan wayata, Kiran shi kawai nake anticipating a wannan lokacin. Bayan kamar mintina hudu se ga Batuul ta shigo, duk tayi wani cool da ita, tun wannan abun da ya faru, dukda tana Dan barin lecture ta tafi inda take son zuwa, Wai me Hali ance ba fa ya fasa halin na shi ko Yaya ne.
Zama tayi gefen gado tana shafa wani sunscreen a fuskar ta, waya ta ta Fara ringing, gaba na ya fadi saboda ganin sunan nashi ne, wannan alama ce ta shima jira na yake. Nayi saurin daukar wayar tare da mikewa na fita, Ina zuwa parlor Babu kowa na zauna sannan ma Kara wayar a kunne na Ina Masa sallama, a hankali naji ya saki ajiyar zuciya sannan yace
" Kinje gida lafiya? Thank you so much, abincin yayi Dadi thank you!"
Nayi murmushi cikin Jin Dadi nace
" I'm glad! Ya jikin naka? Yaushe zaa sallame ka?"
Yace
" Ina gida yanzun! Na Kira nayi godiya for your kind gesture and na fada miki da gaske banyi zaben tumin dare ba. From day one nasan zabi na bana Wasa bane ba!"
Nayi murmushi Ina Jin Dadi, dama Haka words suke, Haka nauyin kalamai masu dadi suke? Kunsan fa dama ni I'm a word of affirmative. Bana gajiya da a dinga fada min how worthy I'm sannan Kuma yadda mutum yake so na, bana gajiya, banki ace kullum a sake maimaita min ba, inaga I'll never be bored.
"To ka kwanta ka huta, kaga I'm sure ka gaji ko?"
Yayi murmushi yace
" Na gaji sosae Amma Kuma Ina son ma Dan ji yadda kike. Wait wai nikam ma how far da maganar mu? Kin amince Zaki aure ni?"
Nayi shiru Ina Jin yadda ake wani race cikin kirji na nace
" Ammm! Zan iya yin tunani?"
Yace
" Come on Fatima bazan zalunce ki ba fa, ba Zan Bari wani ya musguna Miki ba, I'll never be a source of pain to you. Give me chance kinji Fatima ta!"
Oh Allah Wai Fatimar shi, ai duka se kunya ta lullube ni, Amma Kuma naji dadin hakan da ya fada. To wa yaga farin Shiga. Lallaba shi nayi ya kwanta sannan Muka rabu akan se da safe zamuyi magana kafin na fita school. Na dawo daki fuskata dauke da wani madaukakin murmushi, zuciya ta kamar anyi min albishir da hajji ko Kuma aljanna ma gaba daya. Tunda na zauna akan gadon Batuul ke kallo na, ta dube Ni tace
"Saurayi Kika Yi? Naga kina ta murmushi kamar kin tsinci hakori"
Bance Mata komai ba se sake fadada murmushi na da nayi, har na kwanta tace
"Bintu!"
Na dago na kalle ta nace
" Ya akai?"
Tace
" Kinga bikin mu ya kusa Bintu, Amma kawu yace Wai ba zaayi.event ba"
Nace
"Me yasa?"
Se ta Fara kuka tana fadin
"Haba Mana Bintu ya zanyi aure lami Babu wani shagali kamar auren Hadi, ta Yaya ma kawu zaiyi hakan? Haka yace fa Wai indai biki ne ma a Hadejia zaayi"
Na saki ajiyar zuciya nace
" To kiyi hakuri ki yadda da hakan mana..."
"Ya zanyi na hakura? Kinsan yadda na gama fadawa kowa zancen bikin nan, na gama zuzuta mijin da Zan aura Kuma kawai ace a Haka Zan Kara!"
To Ni dai na Rasa me zance na Bata hakuri saboda nasan ko menene kawu ya yanke akan Batuul laifin ta, she break their trust. Da ace lafiya Lau suke batai wannan abun ba, na tabbatar kawu ba zaiyi hakan ba!
Washegari, na tashi da wurwuri na Kama hanyar school, tun asuba ya Kira Ni Bayan na.idar da sallah, Ina toilet Ina wanka ma, naji Batuul tana fadin
" Kaga farin shiga, wato sunan shi Noor kenan!"
Ina daga toilet nace
" Batuul kada kiyi picking call dinnan kina ji ko?"
Tayi dariya ta aje wayar tana fadin
" Aaaa lallai, Babu damuwa idan tayi wari zamu ji"
Ina fitowa na dauki wayar ko ruwan jiki na ban gama tsanewa ba, na Fara Kiran shi tare da Zama gefen gado na, Bai dauka ba se gashi yayi returning call din nawa cikin hanzari.
" I'm sorry, wanka nake"
Yayi murmushi yace
" Ina kwana Fatima ta!"
Na Dan sunkuyar da Kai na Ina murmushi a hankali nace
" Sir an tashi lafiya? Ya saukin jiki?"
Yace
" Alhamdulillah! So how far? Kin yadda na turo Abba ya nema min auren ki?"
Kamar na danyi tsalle saboda yadda yai twisting tongue din shi nace cikin kasa da murya kamar wadda nake whispering nace
" Na amince and I'll be glad"
Wani karamin ihu yayi yace
" Alhamdulillah! I promise you the world and beyond. I'll keep you happy no matter what!"
Nayi murmushi da na kasa gane dalilin wannan murmushi da nake sosae da sosae, gaba daya na Zama kamar wata sakarya ma. Mun Dan taba Hira sannan ya barni na shirya na tafi school. Haka nayi lecture din cikeda Jin Dadi da annashuwa, so this is the feeling of being loved?
Lokacin da na Gama lecture na wuce masallaci nayi sallah, Ina idarwa Kiran shi ya shigo cikin waya ta na dauka, Bayan mun gaisa yace nazo bayan faculty Yana jira na. Se na samu Kai na da tsayawa gyara fuska ta, abin da ko kadan bana Yi, in fact banma damu da hakan ba, to me gani nake ko me Zan shafa bazan taba kyau ba. Amma Bayan na samu skin care products masu kyau da tsada , jiki na ma se da ya canja, balle fuska ta da 80% na kurajen sun fita se Wanda ba zaa rasa ba. Na gyara zaman hijab di na sannan na nufe shi. Yana cikin mota, Nima na bude na shiga na zauna Ina kallon shi a hankali, shi Kuma waya yake so dukka hankalin shi Yana Kan wayar da yake. Se da ya Gama kafin ya juyo yace
"I'm sorry! Ya lecture?"
Na kalle Shi da kulawa, Babu laifi fuskar shi ta ciko ba kamar jiya ba, Haka Kuma ya Dan fi kyan gani akan jiya. Na amsa da alhamdulillah sannan ya taka accelerator Muka Fara tafiya a hankali. Muna tafe ya Fara fada min asalin shi Wanda ko kadan banyi tunanin shi din ruwa biyu bane ba, saboda kasancewar shi ya Zama complete Hausa fulani, saboda shi Bai ma son Yana fullanci ko a gida akai Masa to zai mayar da Hausa balle Kuma yanzun da yasan abinda sukai ma mahaifiyar shi kenan! Se da ya Gama Bata labarin shi tsaf ko Rabin tafiyar bamu Yi ba, saboda yadda yake tafiya a hankali kamar Wanda muke riding Keke. Na ji tausayin shi, na Kuma ji cewar kowa da nashi labarin Kuma kowa Yana da nashi dark story din. Na bashi shawarar neman ta duk inda take, se yace shiyasa yake son ya aure ni soon se mu wuce tare!
Ta_kwalam
[1/3, 20:30] Maman: 042
Tunani dai baya taba karewa, Bayan dogon nazari da nayi akan labarin mahaifiyar shi da ya bani se na Fara tunanin, should I ko Kuma shouldn't I. Saboda gaskiya Ina Jin tsoro sosae, kada ya Zama na Nima se munyi aure family din su su Kore ni ko wani Abu marar kyau ya faru da Ni ya zanyi kenan! Nima haka.zan tafi na bar yaro na a hannun only God knows who? Se naji duk jiki na yayi sanyi naji Anya Zan iya Zama cikin wannan family din. Ina son Akram, so na gaskiya Wanda bana tuannin rabuwa da shi a yanzun zai Zama Abu me sauki, na kuma.tuna yadda yake min alkawarin protecting di na. Se naji Dan kwarin gwiwa har na Kira eldest sister din mu ta sokoto. Babu laifi Muna Dan Yi da ita, plus ni kawai Ina son wani ya bani shawara. Bayan ta dauka tace
" Bintu tunawa kikai da ni yau?"
Nayi murmushi Ina fadin
"Kai Yaya ko daya, ya su Khalilo?"
Tace
" Lafiya su kalau. Ai mun kusa zuwa muma in shaaa Allah"
Nace
" Bikin Batuul ko?"
Tace
" Eh!"
Se nace
" To Nima Yaya akwai wani lecturer din mu Yana so na, dukda baifi sati daya mukai tare da shi ba. Amma na Kira na fada Miki ki bani shawara!"
Tace cikin muryar farin ciki
"Alhamdulillah! Ai dama na sani, komai lokaci ne. Ko jiya se da na fadawa Adda nace ta daina damuwa akan ki mijin ki zai zo. Yana da Mata? Kina son shi?"
Na girgiza Kai nace
" Ina son shi, Kuma Bai taba aure ba!"
Tace
" To daidai kenan ai. Se yaje yayi magana da kawu ko Kuma akwai abin da kike son fada min?"
Na sauke ajiyar zuciya cike da shakku nace
" Yaya Kinga su gidan su basa auren bare, dukkan su family daya ne fulani. Shi mahaifiyar shi Yar Qatar ce balarabiya ce, so tun shekaru talatin da wani Abu baban shi da ya aure ta yaje karatu london, da ya dawo da ita family din shi Suka ki karbar shi karshe ta bar kasar fa! Tsoro nake ji kada Nima hakan ya faru a kaina!"
Ta numfasa da karfi tace
" Eh abun tunani kam hakan Bintu, you've a good foresight Kam. To tambayar anan Bayan mahaifin shi akwai Wanda Suka sake auren wani daga waje ko Kuma se Akan ki?"
Nace
" Yace wasu sun aura sede wasu sun rabu, very few suke tare!"
Ta danyi shiru kafin tace
" To kiyi addua kinji? Ki dage ki fadawa Allah ya zaba Miki mafi alkhairi. Duk hukuncin da Allah ya yanke ki karba a Haka. For now keep following your heart!"
Sosae nayi Mata godiya, na Kuma ji dadin adduar da tace min nayi, Dan kuwa idan kun fahimci Abu a tattare da ni, I'm not much of a prayer type, nasan Ina addua Amma Nima a karon Kai na Ina Jin I'm not totally devoted, kilan shiyasa abubuwa suke cushe min. Daga ranar na Fara addua sosae, ko da Ina zaune, ko Ina cin abinci ko me nake Sai se nayi addua, wallahi se na Fara jin wani irin peace of mind, duk wannan tsoron da nake ji wallahi se ya ragu, se nake Jin Babu wani da ya Isa yayi min wani abun ba tare da Allah ya nufa ba, Dan Haka I cleared my mind nayi devoting ma soyayyar Akram sosae. Shi dinma baya bada wani space da har zanji tantama ko shakku a cikin zuciya ta.
Wani dare na dawo daga school na gaji sosae da sosae, wanka nayi sannan na dakko abinci zanci, na bude drawer se naga tarin herbs, tea bags da nayi amfani da su Akan slimming, na tsaya a wajen Ina kallon su da mamakin Kai na, Wai nice da Kai na na daina shaye shayen nan da nake, yadda na Zama determined Akan shading weight di na ban taba tunanin akwai abin da zai hanani ba, Amma kalla abun mamaki Wai na daina Sha. Na tuna ko a nasihar Akram da yake yimin Bai taba ko da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 18