Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wadda kafin nayi kokarin maida ita har ta Fara zubo min a saman kuncin na, se yayi shiru Yana Jin Babu dadi cikin zuciyar shi, dama ya sani baiyi min magana ba, if at all yasan hakan zai Zama sanadin kuka na. " I'm sorry Fatima, kiyi hakuri bansan zai saka ki kuka ba" Tashi yayi ya bude backpack din shi ya Miko min handkerchiefs yace " Share hawayen ki kinji! I'm so sorry Yi hakuri" Kunsan wani lokacin idan ana baka hakuri kawai se ka Fara sakalci, Nima kawai se naji kamar Yana ce min I should open up to him. Cikin kuka nace " Ba Wanda yake so na, kowa criticising di na yakeyi akan inada kiba, a gidan mu ba Wanda yake so na..." Kuka yaci karfi na, yayi shiru Yana kallo na Wai Bai masan actual abin da ya faru ba kenan... Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 032 Ta zauna tana Masa sannu da zuwa, ya zauna Yana amsawa. Tace "Ya patient din naka? Ta tashi?" Ya shafa kan shi yace "She eventually regain consciousness, na Kai ta gida" Safiyya ta gyada kai tace "Abinci fa? Ko kaci?" "A'a Ummaah! Daddy bai dawo ba?" A lokacin tayi mishi bayanin Daddy wato Imam ya tafi gaida Ummiey, ta sanar Masa Ummiey har Dada ma na cigiyar shi. Yayi murmushi yace " Ni fa laifi sukai min Ummaah, Wai naje gaida Ummiey na samu Dada na wajen ta, Nausaiban Uncle Ali taje wajen su kawai suka Fara ce min Wai sunyi min Mata!" Safiyya tayi dariya tace " To Banda abinka ai is high time kayi aure, you're turning thirty two in few days Akram, ya kamata zuwa yanzun ka Fara tunanin aure ko?" Yayi murmushi yace "Ummaah nace Miki lokaci ne fa, Ni na fada Miki gaskiya ba zanyi aure cikin gidannan ba beside waye zai aure ni na zame Masa burden Ummaah? Ki Bari a hankali Zan samu wadda zata karbe ni regardless of ciwon da ke jiki na" Ya Dade da fada Mata hakan, dama ai Haka ne barewa ba zatayi gudu a jeji ba sannan ayi tunanin danta zaiyi rarrafe ba. Har yanzun a cikin gidan abin da ake yi kenan, mutane baifi uku Bayan Imam suka auro bare ba, yawancin ma Kuma auren mutuwa yake shiyasa da yawa Basu son aurar bare, Amma shi dai Akram ya kudiri niyyar shi na ba zai aura wata cousin ba, a waje zaije ya samo matar shi ya aura. Beside bashi da lafiya, kullum Safiyya tana Masa adduar ya samu wadda zata kula da shi, ta jure dukkan wata al'alar shi, amma idan ta duba se taga to wacece? Yanzun Mata are lazy kafin Kuma Azo ga extra burden. " Allah ya kaimu, adduar mu ba zata Fadi ba. I'm sure daughter in law Dita tana wani wajen a boye!" Yayi murmushi, Haka suke tamkar kawa da aboki Haka Akram yake da Safiyya, relationship din su is very healthy unlike na sauran matar uba da dan miji. Da kanta ta Mike ta kawo Masa abinci, Yana budewa ya saki murmushi tare da dago kai ya dubi uwar tashi yace " Ummaah Allah ya saka Miki da aljanna!" Ta amsa da Amin tana Zama inda ta tashi. Iman ta fito da spoon hannun ta, Wanda yasa Akram yace " To zaa Fara parasitism kenan? Zo mu ci" Tare suka ci dashishin da ya Yi washar ya Kuma samu wadataciyya Miya ta taushe, sosae Akram yaci Yana ta Mata santi kafin ya kammalla, tare da Iman suka kwashe komai, sallama yayi Mata akan zaije wajen mahaifin shi, a hankali suke tafiya shi da Iman, tana ta bashi labarin birthday din Anwar da akai school, ta Fara lissafa Masa abubuwan da Anty ta raba musu, Yana ta sauraren ta. Lokaci lokaci yana gaida uncles din shi da suke haduwa da Kuma wani lokacin cousins din shi. A Haka suka karasa bangaren Abba da Ummiey inda mahaifin shi da Kuma uncles din shi biyi ke nan. Suka gaisa suna tambayar shi aiki da Kuma jikin shi, ya Basu amsa da Yana lura da kyau. Daga Haka Imam ya mike yayi musu sallama Suka tafi gida. Yana zuwa yayiwa iyayen shi sallama ya wuce wani daki dake jikin na shi, machines ne Wanda suke a gym, daya ya hau bayan ya cire kayan shi ya rage daga shi se singlet da short, timer yayi setting na mintina talatin. Yana kammallawa ya sakko ya dauki ruwa ya.sha sannan ya wuce dakin shi yayi wanka, ya fito sanye da robe. Se da ya kammalla Sanya pyjamas kafin ya dakko wani Dan karamin bakin jaka, wata karamar na'ura ya Ciro ya zura Mata wani stick kafin ya dauki karamar allura yayi pricking Kan shi, Dan drop din jinin da ya fito ya samu ya saka jikin stick din dake jone jikin na'urar. Babu jimawa wasu figures Suka bayyana a jikin na'urar 6.8... ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida ya rufe ya dawo ya runtse idanun shi Dan yin baccin. It has been a long day actually with all Bintus' issues. Se ya Fara tuannin me yake damun ta, from the looks of gidan da ya kaita jiya Babu alamar rashin abinci to Amma me yake faruwa. Haka kawai se zuciyar shi take fada Masa he needs to know the girl ko zai iya gane matsalar ta! Washegari da wurwuri na tashi, Bayan na Shiga kitchen na kammalla aikin da zanyi, noodles na dafa naci sannan na matse lemon tsami guda hudu cikin karamin cup sannan na zuba tafasasshen ruwan zafi kadan na runtse idanu na na kafa Kai na na shanye tas. Sannan na koma daki na karasa shiryawa Dan tafiya makaranta, Babu Wanda nayiwa sallama na fita, saboda naji haushin abin da sukai min jiya, na wuni a waje Amma Aki Kira aji me ya faru. Ina zuwa class na wuce wajen khalifa Ina tambayar shi abun da nayi missing jiya. Ya dakko ya bani sannan na koma inda nake na zauna. Bai shigo class din ba se karfe biyu, kafin lokacin bayan nayi sallah na fita na Nemo Coke na Sha sannan na dawo na zauna, I can't take this embarrassment anymore, ya kamata nayi wani abun Kuma. Yana shigowa ya dube ni bayan yazo daf Dani yace "Have you ate?" Nayi saurin gyada Kai na nace " Yes sir!" Ya Miko min sandwich me dumi da Kuma gwangwanin coke me sanyi yace " Eat it silently, don't disrupt my class!" Innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Shi ne kawai abin da na furta, kunya kamar na nutse a wajen, kafin nayi wani Abu se kawai na gan shi har ya isa gaban system din shi Yana adjusting glasses din idanun shi, cikin turancin shi sassauka me Kuma saka tsikar jikin mutum ta tashi ya Fara bayanin topic din da ya Riga ya rubuta jikin white board. A hankali Ina jotting Ina Kuma munching sandwich din, a gani na dole naci kada jiki na ya sake betraying di na. Har aka kammalla class din garau nake ji na. Bayan ya fita se ga Alamin yazo ya zauna gefe na yace " Da kinsan yunwa ce take saki Haka me yasa Baki cin abinci?" Bance komai ba se Dan murmushin Jin kunya da nayi, yace " Shikenan! Kije Dr Akram Yana Kiran ki" Nayi saurin kallon Shi nace " Ni Kuma? Me yasa?" Shi ma se ya kalle ni irin yadda na kalle shi yace " A'a ya Zan sani? Malamin ke ne akwai dalilin Kiran ki Bayan karatu?" Se na Mike tare da sake Jin na kwafsa, tunanin me nakeyi da? Tunani nake zai ce Yana so na ko me? Nayi wani dariyar Bintu Baki da sense ko kadan. Irin wannan gaye me zaiyi da Ni? Jibgegiya da ni, kilan nayi size din mahaifiyar shi. Se naji Kuma wani irin rashin karfin gwiwa ya Kara maimaye ni. Haka na wuce zuwa office din da se da akai min kwatamce. A hankali nayi knocking kamar wadda take jin tsoro, nayi mamaki da naji an bude kofar, na Dan ja da baya har Ina neman zamewa, yace " Come in!" Yana fadar hakan ya shige ciki, a hankali na rufa Masa baya, ya zauna Kan kujerar shi, ya nuna min daya na zauna sannan ya amsa gaisuwar da nake Masa. Bayan ya cire glasses din idanun shi yace " Bintu ko?" Na gyada Kai yace " Fatima kenan! Yaushe Kika Fara wannan fainting din?" Kunsan wani lokacin akwai abubuwan da suke faruwa kaima baka San me yasa hakan yake faruwa ba. Ko Kuma se kaga a single soul ya shigo rayuwar ka ya canja maka komai, ko kuwa kaga ka daina wasu halaye ka kirkiri sabon Hali to someone particular. Kunsan duk wanda yayi min irin wannan tambayar ba lalali na kalle shi ba balle ya saka ran Zan bashi amsa. A hakan a Kan shi se naji I just want to open up. " Last week!" Ya gyada kai yace " Episodes nawa kikai kenan?" Nace " Uku!" Ya danyi shiru kafin yace " Fatima!" Na dago a hankali na dube shi, kallo na yake kamar akwai wani Abu a fuskata, yace " Ina son Miki tambaya, amma idan kinga akwai takura ba se kin amsa Ni ba! I just feel obliged to know your problem. Meye matsalar ki Fatima? Me yake hanaki cin abinci" Nayi shiru Ina Wasa da hannu na, na Rasa ta Ina Zan Fara bashi amsa, abun da nauyi Amma ya kamata ace shi daya duk duniya da ya taba damuwa da Sanin matsala ta ya kamata na fada masa. " Ina son rage kiba ne!" Na fada more of a whisper Amma Kuma se nayi mamakin yadda akai yaji, se yace " Kiba kike so ki rage? Me yasa can you share with me?" Kafin na.bashi amsa akai knocking a kofar Wanda yasa banyi magana ba, messenger Dean ne yazo ya sanar Masa Dean na neman shi da sauri, hakan yasa yace " Fatima I'm sorry, session din mu zai Kare daga nan, I hope we meet some other time!" Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 031 Dr. Akram ya Kara kallon wrist watch din hannun shi a Karo na babu adadi, ya sake duban Alamin Dake can gefe akan kujera hannun shi rike da wayata a hannun shi, wannan lokacin awa wajen uku kenan da na Fadi a cikin class, tun da ya hango fuska ta ya Fara tattakowa daga Kan podium Dan zuwa seat Dina Amma kafin ya karaso already nayi losing consciousness, a cikin tashin hankali dukka suka rufu akai na, ya sake wullawa Alamin mukullin motar shi ba tare da yayi magana ba, Alamin ya cafe ya Kuma fice a guje Dan dakko wannan set din da ya dakko.jiya, sede yau din glucose di na ya sauka sosae. Yana ganin Haka ya daura min ruwa a hannu na sannan yace su Kama ni mu tafi asibiti, na Dan motsa kadan Amma ban bude idanu na ba. Se da suka Shiga mota suka tuna baa dauki waya ta ba, Haka ya aika Alamin ya dakko Amma wayar is coded, Kuma an duba Emergency contact di na babu ko mutum daya a ciki. "Kuma ka tabbatar Doctor ba diabetes take da ita ba, wannan Karo na biyu kenan cikin satinnan fa tana Yi!" Likitan ya dubi Dr Akram yace " Bana tunanin diabetes ne, nafi kawo tana Wasa da abinci ne. Ka Dan Yi hakuri ta farka se muji abin da ya faru daga gurin ta!" Akram ya gyada Kan shi kawai tare da sake yiwa likitan godiya ya fito, ya samu Alamin da Sadiq Dake zaune da Ni. Ya dubi Alamin Bayan ya duba agogon hannun shi yace " Har yanzun Babu Wanda ya Kira daga family dinta? It's after maghrib fa!" Ya fada cikin kosawa dan so yake ya tafi gida, Yana Kuma ayyana dalilin da zai sa har yanzun a gidan mu Basu Kira ba, bugi da Kari Alamin ya tabbatar Masa a gida nake zaune ba hostel ba. Alamin yace " Har yanzun Sir!" Ya danyi tsaki yace " She doesn't have a friend? Ko da daga wani faculty ne?" Sadiq wannan karon ya bashi amsa da fadin " Babu fa sir! Kullum Bintu ita kadai take rayuwar ta, idan an Gama lecture ta tafi gida!" "Then she's not normal kenan" Akram ya fada Yana sake duba na, ban tashi ba Amma Kuma Doctor din ya tabbatar musu kawai stress ke damuna shi ne dalilin da yasa ban tashi ba, Amma dukka abubuwan da zasu nuna akwai damuwa a jiki na, are ok so Shi ya dauka hakan a matsayin brain Dita ke hutawa. Ya Kara kallon fuskata Yana ayyana ko ni wacece? Wayar shi ta katse Masa tunani Wanda hakan yasa shi cirowa daga pocket din shi, da murmushi a saman fuskar shi ya dauka Yana fadin " Ummaah! Ina wuni?" Daga dayan bangaren tace " Alhamdulillah! Me ya faru yau baka dawo gida ba, baka Kuma Kira ni ba. We're all worried here!" Ya dube ni da na Dan Yi juyi kadan alamar na Fara regaining ya sauke ajiyar zuciya yace " Kiyi hakuri Ummaah, wallahi wata student Dita ce ta fadi a class di na. Mun kawo ta asibiti Kuma har yanzun mun rasa family dinta" Kafin tayi magana na Fara bude idanu na a hankali, se yayi saurin yu Mata sallama akan Bari yaga ni gashi na tashi, a hankali na tashi na zauna Ina rarraba idanu Dan na fahimci a Ina ma nake in the first place, me Kuma ya faru, Amma muryar shi da naji tazo daf da Ni yasa na sake bude idanu na, wannan karon Sadiq da Alamin har shi ma suna tsaye a kaina. Kawai se na rufe idanu na saboda wata irin kunya ce ta rufe ni, da ace kasa zata tsage I'm very sure I'll gladly jump in ta hadiye Dani. Wannan wanne irin embarrassment ne na yiwa kaina. Na tuna vividly har tamabya ta yayi ko naci abinci saboda a cewar shi baya so nayi distracting class din shi. Amma kalli abun da ya faru. Kamar na kwala ihun da nake Yi cikin Kai na, suji ko zasu San cewa I'm embarrassed to the core! Shi ya fahimci halin da nake ciki se ya bar su Sadiq akan Bari ya Kira doctor yazo ya dubani, Ina Jin ya fita na bude idanu na Ina kallon su Alamin da tsanain kunya nace " Fainting na Kara Yi?" Yayi dariya yace "Eh mana, gashi kin dade yau Baki farka ba" Na daura hannu na akai na nace " Na shiga uku. Alamin, Sadiq thank you. Ya Zan kalla fuskar shi?" Sadiq ya Fara dariya kafin yace " Wai me yake Hana ki cin abinci ne? Kinsan wannan abun kuwa na barazana ga rayuwar ki?" Na Dan marairaice fuska bance komai ba, su barni da kunyar da nake ji kadai ta ishe ni. Babu jimawa se gasu sun shigo, nayi saurin runtse idanu na dan kada mu hada idanu da shi Amma se yace " I've caught you! Tashi a duba ki" Haka na tashi Ina ta sunkuyar da Kai na, doctor ya dududduba ni yace I'm fit zamu iya tafiya, nayi Masa godiya sannan Akram ya bishi Bayan ya jadadda min akan lallai lallai na dinga cin abinci idan ba Haka ba Kuma Zan iya mutuwa. To ai ni da Zan mutu inaga it will be for the best, wannan a wani sashe na zuciya ta ne, se Kuma nayi saurin istigfar, anything but Banda kashe kai, saboda Allah ya bani chance wancan karan wannan Karan ba lallai nayi surviving ba, Kuma na tabbatar idan na kashe Kai na, jahannama ta tabbata akai na! Shigowar shi ya dubeni bayan yazo daf da gadon yace " Ya jikin naki?" Nace " Alhamdulillah!" Ya gyada Kai sannan ya dube mu suka yace, kuzo mu tafi. Dukka Suka tashi Nima Haka a sanyaye na sakko daga gadon tun da nasan har Dani yake nufi, musamman da ya iya jira tun laasar har yanzun Bai tafi ba, yanzun ma nasan ba zai barni anan ba. Muka fita zuwa hadaddiyar motar shi, irin tafkekiyar motar nan ce katuwa. Ya bude sannan yace min na Shiga gaba su Kuma su shiga baya. Muna tafe Bai ce min komai ba har mukaje BUK lokacin ana ta Kiran sallar ishai, ya sauke su sannan yace na jira yayi sallah. Nayi saurin kallon shi nace " Sir Zan iya zuwa gida daga nan. Nagode Allah ya saka da alkhairi!" Ba tare da ya amsa godiyar da nake Masa ba yace "Idan kin fita Ina Zaki samu abin Hawa. Come on stay still nayi sallah nayi dropping din ki!" Babu abin da zance Kuma se kawai nayi shiru Ina ayyana yanzun dai ya kamata na aje dieting a gefe, is not for me gwara na Nemo natural hearbs da Kuma slimming tea da veniger na din ga Sha. Wani taimakon Allah bana sallah balle nayi ramuwa, shima Kuma bai tambaye ni ba, Babu jimawa se gashi ya dawo su Sadiq sun wuce hostel daga nan, ko sallama ba muyi ba. Ya Miko min waya ta bayan ya tada motar yace "Ki duba wayar ki muna sallah an Kira ki" Ya fada Yana kokarin yiwa motar key, nayi saurin dubawa se Naga Mamaa ce ta Kira da Batuul, na sake going through log din babu Wanda ya kira ni tun dazun. Kenan hakan na nufin Babu Wanda ya lura ban dawo gida ba se yanzun kenan? Se naji ban ju haushi ba tunda dama se an damu da Kai ake kulawa da rashin ka. Na Kira Mamaa Amma wayara Bata Shiga ba, instead se na Kira Batuul lokacin har mun fita daga gate din BUK. Na Kara kunne na saboda tata ta shiga "Ke Bintu Ina Kika je har yanzun Baki dawo ba?" Rai na ya baci saboda na tsani abubuwan da Batuul take yimin, tana magana da wata irin gadara, banyi tunanin volume din is that loud ba har Yana iya jiyo maganar Batuul din nace " Gani nan na taho ai" " Se kizo kiyi bayanin inda Kika je, tun dazun se neman ki ake, kin tayarwa da mutane hankali!" Ban Bata amsa ba na sauke wayar daga kunne na tare da hanging up, bansan amsar da Zan Bata ba ma. Ya dube Ni yace " Wacce unguwar kike?" Na bashi amsa da Badawa layout sannan ya cigaba da tukin shi. Babu jimawa wani Kiran ya sake shigowa waya ta, ya kalle ni ganin na Bata Rai se Kuma ya sake maida Kan shi ga titi, wannan karon Mamaa ce " Mamaa gani nan na taho!" "Ina Kika tsaya Bintu?" Nace " Na taho ai na kusa zuwa" Se ta kashe wayar kawai, can Muna tafe se yace " Me yasa ba Zaki fada musu inda kike ba" Meye amfanin fada musu? Ai bashi da amfani tun da ba damuwa zasui Dani ba. Allah ya sani duk wannan a zuciya ta nake fada Amma bansan yadda akai na samu betrayal daga inner mind di na har abun ya fito waje ba. Ya dube ni yace " Ba a gidan ku kike zaune ba?" Na kalle shi da Dan sauri nace " Gidan mu ne, they're my parents" Se ya gyada Kai kawai Bai sake magana ba har Muka shigo unguwar, se na Fara nuna Masa turns din da zai dauka har ya kawo ni kofar gidan mu. Dama Ina ta adduar Allah yasa Babu kowa, cikin saa har na sauka nayi Masa godiya sosae ba Wanda ya fito, na juya Zan Shiga ciki se ya Dan Kira Ni da muryar da ya tabbatar zanji "Fatima!" Wasu na Kira na Haka Amma Basu da yawa ko kadan, na juya a hankali na same shi, yace " Kici abinci, Kuma gobe I've your class don't come and faint again!" Na Dan sunkuyar da kaina in embarrassment nace " Nagode sir" Yaja motar ya tafi ni Kuma na shige gida, Ina shiga wajen Mamaa na wuce, na samu tana zaune ita da Adda, na gaishe su sannan na Fara yiwa Mamaa bayanin inda na tsaya, cikin tashin hankali tace " Allah ya sawwake. Ni bansan Baki dawo ba wallahi se da Alawiyya tazo ta fada min Baki dawo ba" Alawaiyyar fa Yar aikin mu ce, ita ce kadai ta fahimci bana gidan, ikon Allah! Adda Dake kallon mu tace "To Ina zaa gane Bata nan bayan kullum kina daki kamar daddawa. Kije Kan dressing mirror di na akwai wani skin product Dana gani ko zai sa wannan kurajen su tafi!" Nayi Mata godiya sannan na tafi. Ina dauka na zauna akan gadon ta Ina going through labels din Dake jiki, se na fahimci Bayan kuraje da yake kashewa Yana fading skin, so se na sakawa Rai na bazan Yi amfani da shi ba! A bangaren Akram ya karasa gida, kamar kullum Bayan yayi parking ya hanga Alhaji Gidado can a zaune yana cin abinci, ya tsufa sosae Amma har yanzun da guntun karfin shi. Ya dauke Kan shi ya nufi cikin gidan su, kafin ya shiga se ga Aiken Wai Alhaji Gidado yace yazo suci abinci, yace aje a fada Masa da Ummaah shi zaici, ya gode da tayi. Daga Haka ya wuce ciki, shi dai Bai son mutumin dan kuwa yaji labarin irin mulki da Kuma izza da yayi. Yasan Safiyya ba mahaifiyar shi bace ba, yasan fuskar mahaifiyar shi, Yana iya tuna kadan daga cikin rayuwar da sukai tare, har zuwa lokacin da Daddy wato Imam ya taho da shi, da farkon haduwar shi da Safiyya, Amma daga wannan ba zai tuna wani ya fada Masa ita din ba mahaifiyar shi bace ba, ko Kuma a fada Masa ga inda mahaifiyar shi take, lokuta da dama Yana son yasan rasuwa tayi ko me ya faru Amma baya son ya daga maganar saboda a duniyar shi, Safiyya ita ce uwa kowacce mace a bayanta take. Idan ya tuna ba ita ta haife shi ba ko Yana son Sanin inda asalin tashi uwar take se yaji kunyar Kan shi da Kan shi take, a ganin shi Safiyya ta wuce ya tuna ba ita ta haife shi ba. A hankali ya shiga parlon bakin shi dauke da sallama, ko Ina tas se kamshim turare Dake tashi in da ya hango burner na aiki, wannan wani Abu ne cikin zuciyar shi, Yana son kamshi Yana Kuma fatan aurar macen da zata kula da bama shi kanshi ba har da gidan shi. Rike shin da akai yasa ya dubi Iman dake da shekaru wajen goma yace " Imani" Bata fiye son Yana Kiran ta da Imani ba, a cewar ta ba Haka bane ba sunan ta. Ta Bata Rai tace " Ummaah Kinga Hamma ko?" Safiyya da ta shigo sanye da lace green da adon milk a jiki tana murmushi kamar yadda take a shkearun ta na baya tace " Hamma sannu da zuwa" Ya saki hannun shi daga wajen Iman ya nufi mahaifiyar shi da murmushi saman fuskar shi shima... Gobe in shaaa Allah, Zan danyi Abu and I'll not be able to post, idan Kuma na samu sarari zaku ganni Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 034 Akwai lokacin da baka fahimtar me kake ji a tattare da mutum, baka gane yadda zakai bayanin how that person meant to you, ko da duka ko da menene ba zaka iya gane meye matsayin wane a waje na ba. To wannan ma Haka take wajen Akram. Da farko da ya Fara ganin Bintu, yaji ta burge shi yadda akai ta iya surviving ita daya cikin wannan mazan, he respected her saboda yasan ba karamin efforts tayi putting ba, a tunanin shi ma ita din matar aure ce. Amma lokacin da ya kalle ta sosae se ya fahimci jikin ne kawai ba lallai akwai shekarun ba. Bai sake maida hankalin shi Kan ta ba se ranar da tayi wannan hypoglycemic episode na farko, a ranar yaji tausayin ta Amma Bai Bari ya wani dame shi ba se da tayi na biyu, sannan ya tabbatar akwai wani abu dake damun yarinyar. Kafin ta farfado ya tambayi Alamin, some few things game da ita Amma amsar da Alamin ya bashi cewar shi dai Yana ganin ta kawai, Bai San komai a tattare da ita ba, yasan bata kula mutane bata yawan magana, Bata Kuma San a gane tana waje. Ya Kara da cewar lokuta da dama idan an Gama classes ta leka taga an taru mutane da yawa, ta kwammata ta koma class ta zauna zuwa lokacin da zaa baje ta tafi, abin da Alamin ya fada da Kuma abin da yayi observing shi ne Bata da confidence Haka bata da self esteem ko kadan, tana Jin kanta kamar ita ce center of attention din mutane. Se Kuma gata a gaban shi tana

Chapter 13 of 18