ke ciki.
Ita Bata faye Shan wuya idan tana da ciki ba, Amma wannan karon Kam se cikin yazo da sabon salo, tun kafin first trimester ya wuce se ga bump ya fito Dan Haka kowa ya Fara tunanin kilan twin gestation ne, wato Yan biyu amma duk lokacin da taje hoton cikin se ya nuna guda daya ake gani, Dan Haka komai da aka siya na Batuul ne, Babu Wanda yasan da zuwa na saboda tun a ciki Batuul ta danne ni, ita kadai ake iya visualizing. Se da ta Fara nakuda aka kaita asibiti, tuntuni sunyi da Kawu wannan karon ma Fatima ce Babu fashi, se Yaya Fatima ta ce to dama bamu da Batuul Dan Haka se ace Mata Batuul. Wannan shi ne Shirin su, Bayan an haife ta Kuma se wani ciwo ya turnuke, ko da aka zo examination se akaji alamar wani Babyn Amma Kuma presenting part din ba Kai bane ba, maimakon a barta ta haihu se aka bada shawarar kawai ayi CS, Har a yanzun akwai Wanda suke ganin CS mutuwa ce balle a shekaru da dama da Suka gabata, hankulan kowa a tashe yake, Danna ita din nurse ce Amma Kuma family din ta fa? Haihuwa hudu kayi su lafiya har da wannan ta biyar Amma se a ta shida Abu ya gagara! Haka aka tafi da ita, Babu jimawa aka fito da ni sede baa Basu ba saboda Wai na sha ruwa banyi kuka ba, I've to go for another resuscitation, cikin hukuncin Allah kuwa se gashi Ina jin zafin heater na Fara kuka, Kuma jiki na ya koma pink yadda ake so.
Su 'Yan biyu farin jini ne dasu sosae, musamman idan ba Kai ka Haifa ba, se kaji sun burge ka kana son ace naka ne, to Haka muma muke da wannan farin jinin, Amma yawanci Batuul ke da shi bani ba, Ni na kasance kamar wata shadow din ta!
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_
005
Top-notch season 3
Ayshatuuu
Gaba daya sukai shiru suna jin abinda dan na su yake Yi, a ganin su diban albarka ce kawai wannan, a ganin su bokon da yake yi ita ce ta saka yake dukkan wannan abun, Amma a ciki Kawu Mamman ya fahimce shi, har ran shi ya Kuma ji Dadi,ban sani ba ko Dan kasancewar shi mahaifi ne ga Salamatu? Allah masani
"Nagode sosae Hamisu, nagode da baka wulakanta min Diya ba ka dawo da ita da martabar ta, Ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwar ka!"
Kun fahimci abin da nake so ku fahimta? Shi Kawu Mamman he's grateful saboda lokacin da Kawu yaji Bai son Salamatu baiyi kasa a gwiwa ba yazo ya sanar musu, Bai wulakanta ta ba balle cutar da ita ba, da yake Yana da wayayyen Kai se gashi Bai ja maganar ba yazo ya dawo da auren. To bashi kadai bane ba, hatta malam mahaifin shi ya fahimce shi, Kawu Sabaru ne dai yake ta banbanmi, har da fada Masa kada ya sake taka kafar shi zuwa gidan shi, Wanda dama ko Bai fada ba Kawu Kam ya bar wannan dakin zauren.
Bayam duk sun tafi, Malam yayi Masa fada sosae da sosae, ya nuna masa rashin dacewar abin da yayi, ya nuna masa illar rashin hakuri, a karshe ya Masa fatan alkhairi tare da bashi shawara akan rayuwa, ba tare da ko Innar shi yayiwa sallama ba, kawai ya dauki hanya ya koma Kano, Yana zuwa yayi sallama da Inna talatu ya tafi Dan Kama haya da Fara sabuwar rayuwa! Salamatu taji dacin mutuwar auren ta, tayi kuka marar iyaka Amma da taji zata cigaba da Zama Kano se hankalin ta ya kwanta, saboda tsoron komawa Hadejia ayi ta Yayata maganar.
Shekara daya ta wuce da faruwar hakan, tun ana maganar ana kwashewa Hamisu albarka har aka manta, kunsan Haka Rai yake da mantuwa, itama Kuma se tayi aure nan a Kano shikenan se maganar ta sake mutuwa. Yayinda Kawu ke ta Fadi tashi wajen ganin ya nema na Kan shi, da adduar iyaye da yake yawan ziyarta Yana musu alkhairi dan ya goge laifin shi, ya kammalla karatun shi tas a BUK, ko aiki Bai tsaya nema ba ya cigaba da zuwa kasuwa, Allah ya nufe shi da siyar rumfa cikin kwari, ya Kuma Fara sayo Kaya Yana siyarwa, kwatsam se alkhairi da budi Suka ta ninkuwa se Kawu ya Zama Alhaji.
Da fari ya saya fili da ake yankawa anan Yan kaba Dake Kan babban titin Hadejia road dake cikin Kano, a ganin shi nan din zaiyi kusa da daukar Hanya zuwa Hadejia, Ashe akwai ranar da zaa wayi gari a samu su sauna, dakata and the rest! A hankali yake ginin saboda shi mutum ne da ku kunsan Yana da high taste, komai Yana son ace nashi yafi na kowa, komai so yake ace nashi is outstanding. Karku manta fa da halayen shi nasan farar mace, Yana nan ba Wai ya canja bane ba, shi ne dalilin da ya Hana shi aure, Yana ta zuba idanu yaga kyakyawa Kuma Fara sannan siririya. Haka abokan da makwabtan shi na Rumfa a kasuwa zasui ta tsokanar shi Fara ko mayya ce! Sede yayi dariya kawai yace musu shi fa Abu me kyau yake so Bai wani zurfafa ba.
Akwai wadanda ko me suke so se kaga Allah ya Basu akasin hakan, akwai Kuma wadanda Allah ke Basu dukkan abin da zuciyar su ta kwadaita masu. In that case Kawu na daya daga ciki, shiyasa yake ganin shi Mai sa'a ne shi. To mahaifiya mutuniyar jahar katsina ce, Amma idan Kika zauna da ita Zaki fahimci ba Yan asalin katsinar bane ba, in fact bama asalin Yan Nigeria bane ba, kawai dai sun hauro Kuma sun Jima har suka Fara aure da hayyayafa.
Haduwar Kawu da Adda kamar yadda muke Kiran ta, a kasuwa ne, Bayan an idar da sallar azahar ya dawo shago, Yana fadawa daya daga cikin yaran sun je su siya Masa abinci gidan abincin da yake ci yunwa yake ji, Dan shi baya ma cin abincin da ake kawowa kasuwa, standard din shi ya wuce haka. Yana nan zaune kamar ance ya dago idanun shi, Yana daga idanu se cikin na Adda wadda take tare da iyayenta da Kuma kanwar ta Anty hajara, ganin Yana kallon ta ya Kuma ki dauke idanun shi se ta dauke Kan ta tana nunawa Anty hajara shi da Baki tana Mata kus din se kallon ta yake, shi kuwa a lokacin ganin ta ya tafi da komai na shi, Jin shi, ganin shi hatta da sense of stimuli din shi Adda tayi nasarar tafiya da shi!
" Kai halilu"
Wanda ya Kira da halilu ya dube shi Yana amsawa tare da jiran umarni, ya nuna masa inda su Adda suke yace Masa ya tabbatar da ya dakko hankalin su sun shigo shagon nan siyayya! Aikuwa halilu yayi nasara, ku kunsan bakin Yan kasuwa, kusan sun iya kalami, Haka kuwa Suka shiga ya tarbe su cikin mutunci da Kuma girmamawa, aka nuna musu kaya, ita dai Adda se Bata Rai take, saboda idan zata dago idanun ta sau Gama kuwa zata Kama Kawu Yana satar kallon ta, hakan yasa ta takurawa su Alhajin KT akan suje wani shagon su duba, su kuwa sun ga kaya, unique ga Kuma shimfidar fuska har da ta tabarma, Dan kafin su Fara saya ya bayar an sayowa kowanne zundumemen lemon kwalba 50cl dinnan. Bayan sun Gama ciniki yayi musu massive discount suka Masa sallama dan tafiya, hade da sake mishi godiya bisa karamcin shi, tare Kuma da Yi masa alkawarin dawowa wani lokacin idan bukatar hakan ta tashi! Ita dai Adda Babu bakin magana, daga harara se cone baki.
Kawu yaga da gaske tafiya zasuyi, Kuma tafiyar su na nufin sede yayi tunanin wannan kyakyawar budurwa dukda ma yasan sunan ta, yaji Maman ta na fadin
" Asiya ga shadda irin wadda Kika ce kina so, ba Zaki dauka ba?"
"Kalla kiga lace dinnan yayi kyau Asiya?"
A Haka ya fahimci sunan ta, Dan Haka yayi ta maza ya tari Alhajin KT ya durkusa har kasa tare da fada Masa abinda yake zuciyar shi
" Baba Naga daya daga cikin yaran ka, Asiya Kuma naji Ina son ta, idan ka amince ka bani dama Ina son na aureta idan ta amince idan Kuma bakai Mata miji ba"
Kafin wani a cikin su yayi magana tuni Adda tace
"Ni gaskiya a'a, bana son shi!"
Aikuwa iyayen duka biyu sukai kanta da fada, Ina ruwanta zata saka Baki a maganar manya, waye waye! Haka dai tayi shiru tana Kara hade fuska, Anty hajara nata murmushi a gefe. Alhajin KT ya dubi Kawu yace
" Zan Yi shawara duk yadda ake ciki zaka ji aike na!"
Idan Allah yayi wannan da wannan zasu kasance karkashin Inuwar aure to lallai lallai, duk kiyayya, duk tashin hankali sannan duk wani abu se wannan auren anyi! Haka suka tafi bayan yayi kokarin sake musu alkhairi Amma Alhajin KT ya dakatar da shi, a'a ranar yaran shagon Suka ta Masa tsiya suna zolayar shi, tare da zuzuta how much ya iya zabe, fada suke suna karawa Adda fa tayi karshe ce, shi Kuma Yana murmushi Yana Jin Babu ya shi.
A bangaren su Adda sun koma katsina lafiya, mahaifin ta bayan kwana biyu ya tada mutane har biyu daya yaje Hadejia ya gano Masa su waye dangin da Yar shi zata shiga, dayan Kuma ya tsaya a Kano cikin kasuwa Dan kuwa anan Kawu yafi Zama Kuma nan ce Hulda da mutane. Sede mu ce madalla da iyaye na gari, Allahu ya saka musu da mafificin alkhairi!
Sati daya ya samu kyakyawan feedback Akan komai da ya danganci Kawu, hakan yasa yayi naam da shi ya Kuma samu babbar diyar ta shi da mahaifiyar ta, bayan addu'oi yace
" Kisa a ran ki bazan Miki Dole ba, Amma musulinci ya bani damar Yi Miki zabi, to Ni na zaba Miki Hamisu ki aure shi, idan Kuma baiyi Miki ba har bayan Kun Yi magana, ko ki fahimci wani nakasu a addinin shi ko zamantakewar shi, Ina fata ki sanar Dani se a fasa..."
Wannan fasawar da yace ta dadawa Adda, zuciyar ta tayi haske Dan a ganin ta so ake a cusa Mata auren da Bata so. Haka Alhajin KT ya sake aike ma Kawu sakon Fara nema through wani abokin shi dake nan sabon gari market. Zuwan farko yadda ta tarbe shi duk se yaji Babu dadi, Amma yadda yake son ta se ya kasa hakura, zuwa biyu, zuwa uku zuwa hudu, Adda se ta amince saboda yadda ya damu da ita, yadda yake kuka da ita, yawan kyauta da nagartattun halayen shi yasa ta amince. Wata bakwai daga lokacin se ga Adda a dakin Kawu. Anyi sure cikin mutunci da kyautata wa juna.
Dukda Kawu ya kasance Dan kasuwa ne, to Amma wannan bokon da yayi har zuwa master's level ya saka yake shaawar ganin mace tayi Boko. Shiyasa bayan auren Adda da wata biyar wani abokin kasuwancin shi Dake matsayin Nurse a asibitin murtala yake fada masa, ai school of nursing Kano sun Fara Saida form, idan Yana da candidate ya kawo, bayan dogon tunani kawu ya samu Adda ya fada Mata ta kawo ssce din ta zai nema Mata makaranta. Lokacin da ta san school of nursing ne kamar zata maida Kawu ciki saboda murna, ita dai suna birgeta idan ta gan su a asibiti, wannan abun da Kawu yayi Mata ya sake zurfafa son shi cikin zuciyar ta.
Ko da ta Fara zuwa makaranta, Bayan wata shida akai intro cikin hukuncin Allah ta samu nasara, lokacin da Suka Zama cikakkun student nurses se ta Fara wani tunani cikin zuciyar ta, school of nursing ba wajen wasan yaro bace ba, idan tayi Wasa ta samu ciki shikenan zaa kore ta, Dan Haka a boye da little knowledge din ta na family health ta saya pills take Sha, kusan shi ne kuskuren farko da tayi, Amma wani lokacin ta kance hakan ba kuskure bane ba.
Babu haihuwa Babu labarin ta, shi Kuma Kawu Yana son Yara, lokacin ta Yi shekara uku suna Shirin yin hospital final, a wannan lokacin ya hadu da Mama! Idan aka hada maka Mama da Kuma Adda you'll be confused to who's more beautiful, dukkan su farare ne Kuma kyawawa, sirara masu diri me kyau. Mama Yar Yola ce, ita din I'm not sure of yadda Suka hadu da Kawu Amma dai yazo yace da Adda zaiyi aure, lokacin tana Shirin yin final nursing qualifying exams.
BINTUN BATUUL na kudi me...
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_
Ayshatuuu
Top-notch season 3
007
Da farko dai bansan me mutane suke ji ba idan sun tanka hallitar ka, bansan pleasure din da suke driving ko kuma wani satisfaction da suke samu daga hakan ba, na Kan Dade Ina tunanin Ina ruwan mutane da hallitar mu, those shape, complexion, figure matters? Akwai wani alfarma da kyawawa suke samu a rayuwa? Akwai wani favor ko afuwa da rayuwa take bawa kyakyawawa? Nayi tunanin Allah cewa yayi Yana amfani da zuciya da Kuma ayyuka, Amma baya la'akari da suffar bawan shi! To me yasa mutane Basu iya dauke idanun su akan hakan? Me yasa se sunce Kinga yadda kikai kiba? Kai wannan kiba ce da ita! Wannan siririya ce! Tab Kinga kumatun ki? Ina ruwan ku? Meye matsalar ku? Jikin ku ne? Kunsan yadda muke ji kuwa?
Nasan zuwa yanzun Kun fahimci wacece ni ko da kuwa kadan ne daga ciki, na rayu cikin tsoro, fargaba da kuma tantama da kokonto Haka na rayu, nasan da dama akwai Wanda suke fuskantar abun da nake fuskanta ko Wanda ya fi hakan
.
Bayan haihuwar mu, jikin Adda yayi sauki aka sallamo mu, kamar kowa Nima aka rada min Fatima Amma ana Kira na da Bintu, sati daya da haihuwar mu Adda ta dubi Mamaa dake min wanka tace
" Nikam Mamaa kunnen Bintu kamar baya fita, kullum se kiga yayi duhu!"
Ta sake gogar sabulu ta goga a wajen tace
" Wallahi fa Adda, Nima na lura Amma na dirza yaki fita!"
Wata kanwar Kawu, Anty zainab tace
" Ai baka ce, ba datti bane ba!"
"Me?"
Suka hada Baki wajen fada tare da Kuma kallo na da nayi lamo cikin ruwan dumi, Anty zainab ta kalle su da mamakin wannan exclamation tace
"Eh! Baka ce shiyasa kunnen ta yayi duhu, ai da nan ake gane bakin yaro"
Duka sukai shiru suna bi na da kallo, kowanne cikin su Yana ayyana abubuwa daban. Kafin a rufa wata daya da haihuwar mu nayi wani irin baki Kai ka rantse da Allah kace ni ba jaririya bace ba, wannan kyan da suke da shi, ko daya ban Kama kafa ba, kamanni na daban suke da na kowa a gidan Amma Kuma da Kawu nake Kama, saboda su din na Kama da iyayen mu Mata yasa na fita daban kamar ba Yar gidan ba. Batuul ta kasance me kuka, kuka ne da ita sosai, se ya zamana idan Adda zata je makaranta da ita take tafiya ni Kuma kullum Ina gida ana dirka min madara, se idan ta dawo ta karbe ni tayi breastfeeding di na, Amma kusan lokuta da dama ko da tana gida to tana tare da Batuul ni Kuma Ina hannun Nanny. Kafin lokacin yaye na yaye Kai na, ko ta bani nono bana kamawa se kawai ta yaye ni ta cigaba da rainon Batuul abun ta!
Muka Fara girma na Fara kiba, ga Baki ga Kuma kiba Wanda nake ganin ba laifi bane ba, Haka halitta ta take Amma Yan gidan mu kullum suna cikin zuzuta yadda nake, idan tafiya anguwa ya tashi, to Haka zasu dauki Batuul su tafi da ita leaving me behind, kawai saboda ni baka ce ba yanayin su ba!
Lokacin da zaa saka mu makaranta yayi, aka saka mu a makaranta, ko a aji Batuul ce me kokari Amma ni bani da kokari, so ko a aji Batuul ake so Amma ban dani, Babu Wanda yake lura da ni, Babu Wanda yake ta tawa, kowa sede yace min sister Batuul as though ni din shadow din ta ce, tun Ina yarjnya na Fara Jin kamar I don't belong to inda nake, na Fara Jin haushin ita Batuul din da ake fifita ni akan ta. Idan akai classes ban iya ba se Anty din mu Miss Vivy tace naje wajen Batuul ta koya min, ita Kuma anan wulakancin ta yake tashi.
Ni fa na yadda kowa da kake gani halin shi Yana farawa ne tun daga lokacin da aka haife shi, nasan akwai abubuwa na zamantakewa ta rayuwa da muke koya later in life, Amma na yadda sosae halayen mu start with us! Yadda muke ba identical ba Haka ma halayen kowa da nashi, tun muna primary take kamar Jin kunyar ace ni din Yar uwar ta ce saboda abin da take gani a gida kenan! Har Muka Fara girma Bata canza zani ba, a Haka muke rayuwa kowa da hanyar da yake bi.
Lokacin da muka Kai shekara goma, na fara gane abubuwa da dama, dukda ban kasance bright child ba Amma Kuma I'm not too dull. Mun dawo daga makaranta dukkan mu a gajiye, driver dake Kai mu ya sauke mu kofar gida Bai Shiga ciki ba, a cewar shi min Yi Masa rashin kunya sede mu taka da kafafun mu, ranar yunwa nake ji saboda abincin da aka zuba min a flask di na kadan ne, na kasa gane me yasa kullum abinci na haka, ko kadan baya isata, tun da mu idan muka tashi da safe bamu cin abinci se mun he school lokacin break se mu ci Wanda aka zuba Mana.
Sajida na samu a kitchen ita da Mamaa suna karasa abinci, na shiga ba tare da nayi sallama ba,
" Mamaa yunwa nake ji"
Ko kallo na Bata Yi ba, se sajida tace
" Baki iya sallama ba ko? Fita kiyi sallama Yar baka kawai!"
Cikin rashin Jin Dadi na fita, kamar ba Zan dawo ba Amma saboda yunwar da nake ji, nayi sallamar sannan na Shiga bayan sun amsa, nace
" Mamaa sannu da aiki!"
"Yawwa Bintu!"
Ta fada tana kwashe abincin daga tukunya zuwa cooler, yawun Baki na har tsinkewa yake nace
" Mamaa yunwa nake ji"
" Idan an Gama zaa zuba Miki acici!"
Sajida ta fada ko kallo na Bata Yi ba, se na fita tunda aka bani wannan amsar, Ina nan tsaye ko minti uku baayi ba se ga Batuul tazo ta wuce ni, within minutes se gafa ta fito da bowl cike da shinkafa, mamaki ya Kama ni nace
" Batuul waye ya zuba Miki?"
"Mamaa ce!"
Ta bani amsa shortly tare da wucewar ta, se na sake komawa kitchen din, banyi magana ba na tsaya, wannan karon har Adawiyya da Zahra na nan suna dibar abinci. Gani na tsaye yasa Zahra daukar plate ta zuba min tare da miko min, Amma kafin na amsa Mamaa ta amshe daga hannun ta,
" Baban ku yace ta Fara tsallake abincin Rana saboda kibar ta tayi yawa!"
Ban da sajida dukka Suka kalle ta sannan Suka kalle ni, Adawiyya tace
" Mamaa! Se a Hana ta abinci saboda kiba? Ai kiba hallitta ce fa"
Mamaa tace
" Ai nasan da Haka, baban ku Zaki fadawa bani ba"
Zahra Dake mamaki har lokacin tace
" Idan Kuma tana Jin yunwa fa? "
"Ni dai na fada muku, idan Kuma Kuna son samun matsala da baban ki se ki bata taci"
Kafin ta gama fada ma na fahimci bazaa bani abincin ba, Dan Haka na juya na tafi dakin Adda, Bata nan nasan Bata dawo a aiki ba, Kuma ko tana nan zata goya baya akan Hana ni abincin da akai, tunda they all believed cewar idan na rage cin abinci Zan rame, ko sun manta kiba Babu ruwan ta da abinci ko tashin hankali, wani lokacin da yake cikin damuwa lokacin yake kiba, wani lokacin da ya daina cin abinci ba zai rame ba.
Jakar school Dita na dauka, na laluba ciki with the hope Zan ga guntayen biscuits a ciki, cikin saa na samu pieces Wanda idan aka tada su to zasu iya tashin guda biyu, wani Dadi naji a zuciya ta, na dauki ruwa daya na jefa cikin jakar, tare da rufe fridge din na fita can wani guri a gidan mu, inda duk lokacin da nake son kadaicewa wajen nake tafiya, na zauna tare da Ciro pieces din biscuits din Ina ci a hankali har lumshe idanu na nake saboda dadin da nake ji. Bayan na cinye na Sha ruwa se na Ciro quantitative reasoning di na na Fara Yi, na kusa awa Ina Yi kafin na kammalla na maida cikin jaka ta, na cigaba da Zama har bayan laasar, dama Babu wani zancen sallah, se lokacin da nayi niyya nakeyi, ba Wanda ke takura Mana muyi sallah kowa is busy a gidan mu, wasu irin mutane ne gidan mu.
Se yamma lis na koma ciki, shima yunwar ce ta Fara kwakula ta, straight na tafi kitchen, Ina zuwa na tarar hatta spoon an wanke an kife alamar abincin ya Kare, na bude freezer nasan akwai masu ajiya, Ina dubawa Naga Babu komai a ciki se su nama da kifi da Suka Zama block, hawaye kawai se ya Fara sakko min, wanne irin rayuwa ne wannan nake Yi a gidan mu, dukda bani da wayo can sosae Amma abun Yana damu na.
Ko kinsan har yanzun muna tare a tafiyar top-notch kuwa? Wannan karon ba Abinda ya baka tsoro bane ba, a'a NAZNEEN, Gen Nasir Zaki da Kuma BINTUN BATUUL. Me kike jira Yar uwa?
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL
Ayshatuuu
009
Top-notch season 3
Haka na cigaba da Zama da yunwa a jiki na, idan na ci abincin safe a school to se bayan maghrib kafin Zan Kuma cin wani abu, duk yadda suke son na rame ban rame din ba, sede ni a jiki na nake Jin yunwar. Gaba daya gidan ya fita min a kaina, na Kara tsangwamar Kai na ta hanya Zama a daki in dai Ina gida, da zarar anyi Baki ko me nake Yi to se na gudu zuwa daki, idan baayi da gaske ba kuwa har su tafi ba Zan fito ba, se dai idan Yan Hadejia ne ko Yan katsina ko Kuma Yan uwan Mamaa, amma bayan wadannan Babu Wanda nake shiga shirgin shi.
To a bangaren makarantar ma Haka ce take faruwa, duk da ban kasance me shiga mutane ba, Amma bana tsallake critics da Kuma tsokanar Yara Yan ajin mu, bana mantawa Anty din mu Haka take ce min Fatibombom, so Haka kusan dukka Yan ajin mu Haka suke fada min, wasu Kuma Babu ruwan su da tsokana ta, se ma Jana da suke a jikin su, Amma kasancewar kowa a idanu na is a monster yasa bana sakin jiki da su, ko Batuul da zarar mun shiga makaranta to tamkar bamu San juna ba Haka muke komawa, se idan Abu ya faru dole da zai hada mu!
Bangaren islamiyya kamar mutanen cikin ta daban Haka suke, bana tunanin I ever heard someone talking about my size or face, Kai idan hakan ta faru ma gaskiya ba Zan iya tunawa ba, shiyasa the only place I find joy and solace shi ne islamiyyar. So bana jiran wani yazo muje islamiyya, Ina shiryawa nake tafiya, har bana son alhamis tazo saboda ba zanje islamiyya ba.
Suleiman yaron abokin kawu ne, ba muda nisa da gidan su, zaman unguwa ya hada mahaifin shi abota da kawu, da ke su Adda wasu irin mutane ne yasa zumuncin su day maman Suleiman se idan Abu ya faru, ko haihuwa, ko jaje ko gaisuwa, itama tun tana zuwa har ta watsar da su. To shi Suleiman Yana yawan zuwa duk da ba shi da sa'a a gidan mu wato ba shi da age mate Amma bansan me yasa yake zuwa ba. Tun kowa Bai sakin jiki da shi har suka Fara sabawa da su, dama ni mujiyar gida se kazo ka tafi baka ma San Ina gidan ba. If I can remember shi ne ya Fara saka min BINTUN BATUUL, Bai taba Kira na Bintu sak ba se ya hada da Batuul dinnan! Ranar da muka fara haduwa, was a day na dawo daga islamiyya, na gaji matuka abinci kawai nake son na ci, na shigo da sallama a Baki na, Yana zaune Yana cin abinci, na gaishe shi se yace
" Idan kin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 18