Shiga ciki kawo min ruwa!'
Na gyada Kai na, Ina Shiga ko hijabi ban cire ba na tafi kitchen na dakko masa ruwa me sanyi na koma inda yake zaune, nan na samu Batuul na zaune suna cin abinci da shi har da zuhra ma. Na aje Masa ruwan yace min ya gode, na juya Zan tafi Batuul tace min
" Bintu shi ne Kika tafi Baki tsaya nu ba, Kuma nasan an Kara karatu"
Na juyo Ina harar ta nace
" Dama Ina jiran ki ne? Anyi"
Na fada Ina tafiya ta, zuhra Dake gefe tace
" Bintu Allah ya shirya ki"
Ko Amin bance ba balle ma na juya, se Suleiman yace
" Itama a gidannan take?"
Batuul tayi saurin fadin
"Eh Mana, ka ganta baka ko? Haka take ita ce daban da kowa a gidannan, Kuma har a school ba ta da kokari!"
Haka Batuul take, Haka halinta yake, ba'a sirri da ita, ko kadan Bata iya file bakin ta ba, Haka take sakin Baki tayi ta surutu kamar tababbiya, Suleiman da ke kwasar abinci yayi dariya yace
" Ai kinfi ta kyau!"
Batuul tayi murmushin Jin dadi, Suka cigaba da hirar su ni Kuma ban masan me suka fada ba. A hankali Suleiman ya fahimci ni twin din Batuul ce, shikenan ya lakana min BINTUN BATUUL. Idan yazo ya dinga tambayar Batuul Ina BINTUN ta, se tace Masa Ina daki. A Haka Suka shaku wani lokacin na Kan jiyo Mamaa nace masa ko dai ta bashi Batuul ne? Shikuma se yayi ta murna Yana washe baki Yana fadin
" Wallahi kuwa Mamaa nagode sosae, Dan Allah Ina kamu"
Shikenan kamar wasa se gashi sun Fara soyayya shi da ita, duka duka lokacin shekarar mu Sha uku there about, bana mantawa muna js3. Wannan soyayyar da Batuul ta Fara da Suleiman ya sake bude Mata idanun ta. Ta sake Jin Kan ta ita wata abar ce, yadda Kuma siblings din mu suke mata, ko biki zasu je ko wata unguwa ta fita kunya to zaga ka sun Aiko Batuul tazo su tafi unguwa, ko dinki zasu yi zaku ga Batuul zasu yiwa. I remembered a day, sallah ta kusa, kamar yadda aka Saba ministan harkokin cikin gida wato Mamaa, ta karbo Kaya daga shagon kawu, da daddare Ina daki da Yar karamar wayar da nake da ita Ina Facebook, zuhra ta shigo tace naje parlor, na tashi na tafi na tarar suna ta dagawa kowa se zaba yake, na zauna ni ma na Fara kokarin janyo wata coffee atamfa, se Naga duka suna dariya, na kalle su Mamaa tace
" Ke Bintu wannan kayan idan kin saka ai ki fuskar ki ba zaa gani ba!"
Suka Kara kwashewa da dariya, Batuul ta miko min wata ledar tace
" Ga naki fa!"
Tsabar abin da naji, se na kasa bude nawan balle ma naga wasu iri ne a ciki, kada fa kuce wani Baki ne da ni irin na kuzo ku gani dinnan! Ana Haka se gashi an aiko da lace na Batuul daga gidan Yaya Adawiyya, lace din yayi kyau se murna take, Ni kuwa inata kallon su Adda ta kalle ni Dan taga yanayin da nake ciki,
" Ke Adawiyya Ina na Bintu Kuma!"
"Whoa! Kinsan Adda zabar ma Baki Kaya wallahi wahala ne da shi, niyya ta na Bata kudin kawai ko powder ne ta siya!"
Ana jimawa kuwa ta dakko kudi ta Mika min wai na saya wani abun, na girgiza Kai da wannan murmushin nawa nace
" A'a nagode, ki bar shi!"
Ta kasa ta raya Amma fur naki karba, karshe Mamaa ta bawa, na koma daki na tsaya gaban madubi Ina kallon Kai na, a hankali hawaye ya Fara sakko min daga idanu na, a lokacin nayi ta kallon fuskata da Kuma jiki na, na juya na Kara juyawa, se na Fara Jin to me yasa na kasance daban cikin gidannan? Me yasa na Zama baka? Me yasa ni banyi kyan su ba? Me yasa...
Muna Gama junior secondary din mu, Batuul ta takurawa kawu Kan lallai se ya cire ta daga school din da muke ya maida ita wata, a cewar ta Wai dukka kawayen ta cire su zaayi. Kawu ya Kira mu tare a Kuma gaban iyayen mu mata, ya tambaye ta wadda take so ta fada Masa, ya kalle ni yadda na zauna kamar na gaji da zaman, yace
" Bintu ta! Zo man Bintu ya akai?"
Na karasa gefen shi na zauna amma a dadare, saboda Ni na tsani gathering, bana kaunar shi saboda in dai an hadu to se an Fadi abin da zai Bata min Rai na.
" Ya Haka take kamar tsoro na?"
Ya tambayi Adda, ta tabe Baki tace
" Ai Haka take, Bata kaunar shiga cikin mutane ko kadan, kullum tana daki".
Ya dube ni da kulawa yace
"BINTU fada min menene? Akwai abin da kike so?"
Na gyada Kai lokaci daya se hawaye ya Fara sakko min zuwa kunci na, kunsan kukan me nake? Dan kula ni da yayi, for unknown reason I felt warm inside me, har naji rush of emotion
"Kawu boarding school nake so?"
A lokaci daya Suka hada bakin fadin boarding Kuma? Na gyada Kai na in affirmation. Kawu yace
" A'a Bintu boarding da wahala fa, ba Zaki dinga gani na ko moms din ki baz ga Batuul ma ba Zaki dinga ganin ta ba"
Exactly why I want to leave kenan, na fada cikin zuciya ta, Amma a zahiri se na goge hawayen da yake saukar min nace
" Eh na yadda kawu"
Haka kuwa Babu yadda aka iya aka Fara processing makaranta, tun Adda da Mamaa da kowa a gidan suna ganin kamar wasa ne, se da aka kawo admission letter ta hade da dukkan needs din makaranta kafin Adda ta Kira ni daki wani dare, na zauna bayan ta bani umarni
" Bintu kije ki samu baban ki kice masa kin fasa boarding dinnan! Kinsan wahalar boarding kuwa? Idan Kika tuna ni kuka zakiyi fa!"
Na Dan Yi murmushi nace
" Adda Ina so a hakan".
Tayi shiru, thinking of a way to convince me, Amma fur naki yadda har ce mini tayi akwai mayu da aljanu a boarding, Ni kuwa nayi fatan idan naje can din Allah ya sa su cinye niš
BINTUN BATUUL, Gen Nasir Zaki and NAZNEEN. Wato Shatuuu, Azizat da Kuma me dambu akan farashin N1300.
[1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_
Top-notch season 3
Ayshatuuu
008
Rasuwar iyaye Rashi ne da duk abin da zaka samu a duniya ba zai maye maka gurbin su ba, idan ka rasa iyaye hakika ka rasa wani bngare na rayuwar ka, Haka babu Wanda zai fahimci ciwon da yake a rashin iyaye se Wanda ta faru akan shi! Ina adduar Allah ya jikan iyayen mu da Wanda suka rasu da Wanda suke da Rai, yasa aljanna ce makomar su, ya Kuma kyautata namu zuwan! Amin
Rasuwar Mr Fahad, ba karamin girgiza dukka kasar tayi ba Amma Kuma mussamman tilon diyar shi Zainab, wadda da farko kasa amincewa tayi da cewar Wai mahaifin nata ya rasu, ta dinga fadawa kakarta da ta haifi mahaifiyar ta cewar tace a duba shi fa, dogon Suma yayi saboda Bai ci abinci ba, wannan maganar da tayi ta Kara dagula lissafin kakar, tare da saka ta kuka sosae
" Jadda! Bai mutu ba, jadda ki fada musu Bai mutu ba"
Haka tayi ta maimaitawa har safiya lokacin da zaa tafi da shi makwancin shi, tunda aka fito da gawar Zainab ta yanke jikin ta ta Fadi, Wanda baa samu ta dawo hayyacin ta ba se da aka Kai ta asibiti, lokacin da ta farka taga kanwar mahaifiyar ta Raziya se ta sake fashe wa da kuka, ta dinga Yi Babu kakkautawa har se da aka Mata allura da ta saka ta bacci kafin Kuma dakin yayi shiru!
A takaice Zainab ta rayu cikin maraici na rashin uwa da uba, se wannan jadda wato kakar ta, da tun rasuwar mahaifiyar ta, Mr Fahad ya role ta Kan ta dawo gidan ta zauna da Zainab, shi din bashi da kowa,na shi iyayen sun Jima da rasuwa, to yanzun ma jadda kawai ta rage Mata. Kunsan mutum yayi coping da irin wannan rashin Abu ne ba Mai sauki ba.
Kafin rasuwar mahaifin ta, ta samu gurbin karatu a daya daga cikin manyan jami'oi dake kasar America, wannan rasuwar ce ta kawo tsaikon tafiyar tata, bayan wajen wata da rasuwar jadda ta lallaba ta ta wuce America.
Zuwan ta America, se taji sabuwar rayuwa, taji ta daban cikin wata duniya wadda ba irin wadda ta tashi a ciki ba, Amma yau da gobe se ta Fara coping, har ma tayi kawa da wadda suke aji daya da ita wadda baturiya ce daga kasar America, course daya suke shi ne ya kawo shakuwa a tare da su. Zainab ta kasance nutsatsiya wadda ko a tafiyar ta zaka san wannan halitta a nutse take, maganar ta, al'amuran ta da komai nata, she's too gentle and beautiful!
Shekaran farko Babu Wanda ya lura da ita, kamar yadda Bata shiga harkar kowa ban da Lily, ko da akai hutu na session se tace da jadda ba zata koma Qatar ba saboda tana tunanin yadda zata koma ba tare da taga mahaifin ta ba. Wani lokaci ta fito daga class a matukar gajiye, ga yunwa ga Kuma zafi da ake yi dukda baa Jima da dauke ruwan sama ba, Wanda ya samu ya kwanta a wasu wurare cikin makarantar, tafiya take Yi a hankali zuwa gate din makaranta Dan ta tsallaka ta Shiga taci abinci a eatery din da ta saba. Tana tafe sanye cikin bakar Abaya wadda tayi Mata kyau, ta yane Kan ta da mayafin abayar Baki, Wanda ya sake fito da asalin fatar larabawan da take da shi, tafiya take a nutse, Wanda ga masu wucewa gani suke yanga take, Amma a zahiri Haka tafiyar tata take, wani lokacin Alan tsayar da mota tare da yi Mata tayin free ride, Amma se ta girgiza Kan ta tare da godiya, ta kusa zuwa gate wata bakar sport car ta taho da mahaukacin gudu tamkar zai buge ta, har se da ta tsorata, Amma kafin ta matsa daga wajen se ji tayi ruwa tun daga Kan ta har cikin brown leather loafers din kafarta, cak ta tsaya tana kallon motar da ta wuce kamar me tukin Bai San ya watsa Mata ruwa ba, tayi shiru tana kallon jikin ta, kawai se taji hawaye ya Fara sauka saman kuncin ta, ta juyar da kanta tana kuka me ciwo, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki!
Cikin motar wani bature ne me suna Charles, a gefen shi wani bakin African ne me suna Imam, kana kallon shi kasan Dan Africa ne, idan kayi bincike da yawa zaka iya fahimtar shi din Dan Nigeria ne, idan kana neman yaran da basa Jin magana cikin entire campus dinnan to idan ka samu clique din su Imam ka gama, kowa ya San su saboda yawan su, da Kuma sun hadu ne daga various departments.
Tun da suka taho idanun shi ke Kan Zainab, tafiyar ta kawai ita ce abar da ta Fara daukar hankalin shi, na biyu Kuma shigar ta, cikin Kamala da mutunci Wanda ba kowa ke daurawa daga tarbiyar da iyayen shi Suka bashi ba, Yana wannan tunanin tare da begen ganin fuskar ta kawai se gani yayi Charles yayi Mata feshin ruwan saman da ya kwanta, wani duka ya Kai Masa unconsciously tare da fadin
" Do you want to die? Are you crazy?"
Charles ya kalle shi Baki bude da Kuma mamaki, Dan kuwa ba karon farko da suka Fara yiwa Yan Mata Haka ba. Shima yace w
" What's wrong? Is just for fun"
Ya kara dukan shi a keya Wanda ya kusa saka steerer kwacewa daga hannun shi, yayi saurin dafewa tare da gritting hankoran shi in annoyance, cikin turanci Imam yace Masa se sun koma ya Bata hakuri, wannan shi ne karon farko da suka taba yin hakan tun haduwar su, Babu yadda Charles zaiyi ya koma cikin school inda Zainab ke tsaye tana sharbar kuka, yayin da Imam ya Fara Jin wani nervousness hade da uneasiness Yana addabar shi tun kafin ma yayi idanu biyu da ita.... Tirkashi
***
Na Jima a kitchen din kafin na fito na koma daki, Babu kowa duk sun tafi parlor kallon ka'ida, na kwanta nayi shiru Ina Jin ciki na yadda yake yi min ciwo, amma saboda Hali irin nawa se na hakura har aka Kira maghrib na tashi nayi sallah, sannan Batuul ta shigo da kwanon abinci, ta aje min a gaba na, kamar mayuwaciyar zakanya da ta ga nama Haka na dumfafi abincinnan Babu sadsauci, ban ma damu da zafin dake ciki ba, buri na na jishi a Baki na ya Kuma sauka a ciki na, se da na kona makogaro na kafin na sarara ya Dan Sha iska na cigaba da ci, Ina gamawa nayi gyatsa, Haka kurum naji ya kamata nace alhamdulillah! Na furta tare da Shiga toilet na wanke hannu na, na Tara Baki na a sink na Sha ruwa, Ina fadawa gado ko minti uku banyi ba bacci ya dauke ni, bansan me ya sake faruwa ba a gidan Dan lokacin da na tashi tsakiyar dare ne, kowa yayi bacci, Nima nayi juyi na cigaba da bacci. Da safe Dana tashi nayi wanka na saka uniform, dakin Mamaa naje na gaishe ta, sannan na wuce na Adda, ta Gama shiryawa cikin fararen Kaya na nurses, ni dai babban buri na a rayuwa ta a wannan lokacin idan na girma na Zama nurse, ba karamin burge ni suke ba, ban sani ba ko Dan kasancewar Adda nurse shi yasa nake son su?
"Adda Ina kwana?"
Ta kalle ni da kyau kafin tace
" Ni wallahi mantawa nake Dake a gidannan Bintu, jiya Ina Kika je har dare ban gan ki ba?"
Kun ga fa tun laasar ta dawo Bata ganni ba Amma Bata bada cigiya ta ba, nayi murmushi nace
" Adda idan na girma Zan Zama nurse kamar ki!"
Na fada Ina murmushi, ta tabe Baki tare da fadin
" Da wani brain din? Times table ma ana yaki dake balle Nursing, ke ai sede education!"
Lokacin naji kamar an sare min gwiwa ta, I began to think meye education? Nasan dai karatu ko ilimi I dunno how to put it, Amma su marasa kokari ne kenan? Se naji wani haushi ya Kama ni, ba tare da nace komai ba na juya Dan tafiya school. Ko Dana dawo daga school nan ma dai kamar jiya ne babu abinci, yau ko biscuits din ma ban rago ba se kawai na Sha ruwa na Yi assignment di na, idanu na kadai idan ka kalla kasan yunwa nake ji, Amma babu Wanda ya maida Kan shi Kai na, karshe ma a gaba na Batuul tazo da kwanon abincin ta taci, na dinga hadiyar yawu Amma ko mhmmm bance Mata ba, Dan nasan da gayya tayi hakan, idan nace Zan ci ta Hana ni yadda zanji haushi.
Anyi sati ana haka, na Fara galabaita Dan Haka na samu Adda a daki na fada Mata abin da yake faruwa, dukda nasan ba Wai zata canja bane ba, amma dai gwadawa ce na gani me zata ce. Ile kuwa se tace Wai decision din kawu ne nayi hakuri, Ni bana Jin jiki na yayi nauyi?
The top-notch writers are back again, wannan karon Gen Nasir Zaki ne na Azizat Hamza, NAZNEEN na Me Dambu da Kuma BINTUN BATUUL na Shatuuu, duk Akan farashi me sauki, N1300
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL
Ayshatuuu
Top-notch season 3
010
Ban taba sanin, Kai har cikin zuciya ta da gaske na dauka Adda Bata so na, na dauka idan aka ce a cikin yaran ta waye zata iya bayarwa a bata awara ni zata bayar. Amma dai daya a rayuwa tayi min wani abu da ya nuna min cewa ita uwata ce, Kuma babu uwar da take kin Dan ta, halayen ta akai na bansan me yasa take aibata ni ba, ban sani ba ki Bata San illar da hakan yake ma zuciya ta ba! Na Kuma yadda confidence, self esteem gaba daya ana Fara gino shi daga gida, tun a lokacin yarinta, Amma ni tun a gida na rasa wannan saboda yadda aka muzanta ni, aka nuna min cewar kiba laifi ce, eh mana it's absurd Amma abin da Suka nuna min kenan, nayi laifi tunda na Zama me kiba, to Amma me yasa Adda zata biye su matsayin ta na uwa ta? Instead ace ita ke goya min baya da nuna min kiba, fari, tsayi, gajarta, Baki da dukkan wata suffa ta Dan Adam doesn't count, wannan wani hikmar Allah ce ta banbanta mu da Kuma sakawa mu gane races din mu!
Lokacin da kawu ya kawo Mata admission stuffs di na, ya Kuma dankawa Mamaa kudi me yawa Kan tayi min siyayya a Fara Shirin makaranta. Adda ta kalla makarantar wani Abu ya tsaya Mata a zuciya, ta kalla kawu da dukkan hankalain shi ke Kan business report da ake karantawa a labarai, tace
" Yallabai!"
Duk lokacin da ta Kira shi da hakan, to Mamaa zata basu guri tasan maganar su ta shafa, ya dago shima da idanun shi daga Kan TV din ya Bata dukkan hankalain shi, hakan da yayi ba se yayi magana ba, answer yake Bata Wai Ina jinki gimbiya ta!
" Yanzun yallabai duk makarantun Dake Kano da jigawa da katsina, se Niger state zaka aika Bintu! Kasan Bata son Shiga mutane fa!'
"Ita ta zaba tace boarding school Kuma kowacce ce tana so, a gaban ki na tambaye ta!"
Cikin wani irin yanayi tace
" Bintu yarinya ce yallabai, we can't let her make her own decision yet, she's slow Bata tunanin aftermath din hakan plus kasan Bata son Shiga mutane ko kadan"
Shi dai kawu ya dage lallai New horizon can zanje, ya Riga da ya Gama komai, so sede tayi hakuri. Ta damu sosae, har Kira Ni tayi wata safiya da weekend, na same ta a daki, Ina Zama tace
"Bintu Niger state Kawu zai kaiki fa!"
Na Dan Yi murmushi a hankali nace
" Na sani Adda! Ba Kya son school dinne?"
Na tambaye ta a hankali, ta girgiza tace
" Bintu yayi nisa, Wai tukunna ma menene dalilin da Kika nace se kin je boarding, Ni na son Baki son shiga mutane ko kadan! Wani Abu ake Miki da Baki so cikin gidannan?"
Cikin zuciya ta nace, to wannan amsar tambayar ai is justified, ni mecece a gidannan ban da cikin gida, waye yake kallo na a matsayin mutum a gidannan? Babu Wanda ke regarding di na, ba Wanda yake kallo na matsayin I fit in illa kallon wata alien suke min.Ā Ni da Kai na nakan Yi tunanin yadda Zan iya coping a boarding school, how can I? Bayan bana son shiga mutane saboda Ina ganin kowa kallo na yake, I don't fit in, to Amma se Naga kawai gwara na gwada Naga yadda abun zai kasance!
kwanakin da suka biyo baya har yaranta masu aure ta Kira akan su zo su roki kawu ya fasa maganar, Yaya Auwal yayi ta Mata dariya Wai dama Haka take Sona Bai sani ba, Ni kuwa se shiri na nake a hankali ni da Mamaa. Adda a karshe ta hakura ganin Babu Wanda yake Jin abin da take ki, ita dama mutum ce me so yaranta, dannewa take saboda Mamaa, Kuma yadda Mamaa ke wahala da mu ko ita Bata Yi rabin hakan ba. Kafin na tafi Adda da kanta ta kaini katsina, muka kwana nayi musu sallama, kowa na ya yimin fadan nayi karatu banda wasa ban da kuma abokan banza, daga nan se gidan su Mamaa Muka wuni sannan Muka wuce Hadejia muka kwana. Bayan mun dawo yasa Yaya Auwal ya kaini gidan Yaya Fatima da Fadima, Adawiyya da Zuhriyya.
A fateful Monday, shi ne ranar da na bar Kano na tafi Niger, Mamaa da kawu da Batuul da sajida sukai min rakiya, ban masan ko murna nake ba ko kuma akasin hakan, na dai San kafin na dawo Yan gidan mu sun manta da ni tunda dama can ba Wai suna so na bane ba a tunani na kenan! Se da aka Gama komai na tafi hostel kafin suka tafi, tun da Muka shiga makarantar aka Fara checking Kaya na ko akwai contrabands Batuul ta Fara kuka, ai da na Fara JanĀ akwati na se ta biyo ni ta rungume ni tana kuka, Amma naji wai I made a bad decision ko daya banji ba, in fact ji nake Dan Allah su tafi su barni!
Ina shiga hostel aka raka ni daki na, aka nuna min gado na, room captain tace
" Menene sunan ki?"
Cikin turanci nace
" Fatima Bintu Ginsau! From jigawa"
Tayi min murmushi tare da sake min barka da zuwa, se naji Dadi har cikin zuciya ta, kunsan ance shimfidar fuska tafi ta tabarma. Da Kan ta ta nuna min inda Zan jera kaya na da komai, tace nayi sauri nan da 30 minutes sauran student zasu dawo daga games, itama zata wuce wajen su. Na Mata godiya ta tafi na gyara komai nayi wanka na saka sabon house wears di na sannan na zauna akan gadon da na dame da sabon bedspread,ba jimawa na Fara Jin hayaniya alamar sun dawo. Dakin mu mu biyar ne, biyu ajin mu daya, biyu SS2 suke se room captain da take SS3. Babu laifi dukkan su sunyi min magana tare da min barka da zuwa. Washegari na Fara zuwa class, Kuma a ranar na Fara period, ga bani da pad tun da shine karon farko da na Fara period din, rashin Sanin yadda zanyi yasa na tafi wajen Senior Aisha, tana zaune a class na same ta, ta dago tare da min murmushi, na mayar mata a hankali se ta tambaye ni ko akwai wani Abu? Nayi shiru kafin can na kakaro courage na fada Mata, da sauri ta Mike tace na biyo ta, mukaje clinic ta karbo min da kanta ta gwada min yadda Zan saka kafin na tafi.
Zama na a school din Bai canja min halaye na ba, I was still Bintu da kowa ya sani marar son shiga mutane da Kuma hayaniya, wadda take tsoron wanne kallo mutane suke mata, to still Haka nake. A ajin mu Babu me tsokana ta Wai ko nayi kiba ko Kuma nayi Baki, saboda na samu Wanda Suka fini kiba da tsayi, suka fi ni Muni so Babu ma Wanda yake maida hankali Kai na, hakan yayi min dadi Amma Kuma dukda Haka bana iya sakin jiki a cikin mutane. A bangaren karatu naci da nake yasa Kai na ya Fara budewa, na Fara fahimtar abin da ake yi har na Fara ganewa, idan aka zo prep bana hira karatu kawai nake, saboda Haka Yan class din mu suke cemin Bintu nerd! Amma abun da zai Baku mamaki ko a class ake tambaya wallahi ba Zan bada amsa ba, I don't want anyone to notice my existence, gani nake da zarar anyi noticing di na kowa zai Fara aibata min jiki na Yana body shaming di na. Duk ranar kuwa da aka takira se nayi magana a class to kilan se nayi kuka, I lack the confidence da zanyi magana a cikin mutane!
Wata na daya a school, visiting day tazo, dukka Yan dakin mu Bata shiri suna ta buga waya gida suna fadar abin da suke so akawo musu Amma ban dani, Ni ranar visiting din ma bayan nayi wanka se na kwanta Akan gado as though bana expecting zuwan kowa, Ina nan kwance se room captain ta saka a Kira ni, na tashi na fita, ai se na hango Batuul tsaye, mamaki ya Kama ni na ganin su, a hankali na cigaba da tafiya Ina Jin wani Dadi cikin zuciya ta marar misaltuwa ashe nayi missing din su. Tana gani na ta taho da gudu ta rungume ni, Ina murmushi na rungume ta, se na zauna kowa se tambaya ta yake ya school? Dukda ba dukkan su Suka zo ba, Adda da Mamaa da sajida se Batuul da zuhra, Suma anan suka kwana yau Suka zo. Na tambayi Kawu da sauran. Sajida tace
" Bintu kiba Kika kara, ke yanzun makaranta yafi gida kenan!"
Ban ce Mata komai ba, Amma a Rai na gani nake to ba dole nayi kiba ba hankali na a kwance Babu me takura min ko me body shaming di na! Haka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 18