Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fada kamar zata ari baki, se da ta gama sannan nace " Adda, Mamaa kuyi hakuri. Bana son shi, saboda Bai dace ace tsohon saurayin Batuul ni Kuma na koma Kan shi ba." " Ke Zaki ce ga abin da ya dace, idan an barki wa zai ce Yana son ki, fuska fal kuraje da munin ki a gurin, ke ba jiki me kyau ba!!" Wani irin dagowa nayi unconsciously, na tsira Mata idanuna da Suka kada lokaci daya sukai ja, wani irin Abu nake ji cikin zuciya ta Yana taso min, a hankali naji trickle din hawaye akan kunci na, kawai se Naga ta cije bakin ta, alamar subul da baka tayi, but who even cares? Mamaa tayi shiru tare da sunkuyar da kanta, " Na tafi?" Na fada in between sobs, Kai kawai ta gyada min, na Mike na wuce daki na, na fada Kan gado, na Fara tambayar Kai na " Menene laifi na? Me yasa ake criticizing di na akan abin da bani da iko akai? Menene kyau? Menene Muni? Ko dai akwai wata alfarma da kyawawa daa Kuma farare masu kyan jiki da suke samu, yayin da muke rasawa?" Na Jima a kwance Ina tunani kafin Kuma nayi sallar ishai na koma Kan karatu. Washegari na tashi kamar mayunwa ciya, Amma saboda wani Abu da na darsawa zuciya ta cewar ni fa se nayi slimming ko da Zan dai na cin abinci ne gaba daya, ban nema abinci ba nayi wanka na shirya cikin atamfa zani da Riga, na dakko hijab na saka sannan na dauki jaka ta na fita dakin kawu! Yana zaune Yana sauraren radio freedom nayi sallama, ya amsa Yana Dan adjusting volume din radio, muka gaisa yace " Se makaranta?" Na amsa da eh, yayi min addua kamar kullum sannan na tafi wajen Adda, ta gama shirin tafiya office, tun abun jiya da ya faru bamu sake haduwa ba, dukda ba karon farko da ta Fadi hakan ba, wani lokacin you can mistaken her for ruko na takeyi! "Adda Ina kwana?" " Lafiya Lau Bintu? How was your night?" Na amsa da alhamdulillah, sannan na juya Zan fita se tace min " Jira na sauke ki a makaranta" Kamar zanyi musu se Kuma nace Mata to Amma Bari na gaida Mamaa, na wuce dakin ta tana zaune tana karatun qurani, gani na yasa ta rufe tare da min murmushi tace " Bintu an shirya?" Na zauna sannan na amsa ta, na gaishe ta ta amsa tayi min adduar kullum kafin tace " Nasan Suleiman Karya yake abin da ya fada, ki rabu da shi, kina zaune Allah zai kawo Miki naki mijin" Hakan da ta fada se ya dada min Rai na, naji sanyi cikin zuciya ta, har bansan nayi murmushi ba, daidai shigowar Adda, suka gaisa da Mamaa sannan sukai sallama na mike na bi bayanta, se da tayi warming motar sannan Muka tafi, da farko tafiyar shiru Babu wanda yake magana cikin mu, se can ta Dan rage volume din speakers din motar, " Bintu akwai abin da yake damun ki?" Na Dan kalle ta kafin na girgiza Kai na bance komai ba, " Kinsan bana son shiru ko? Idan nayi magana Nafi son ki min magana" Nayi saurin bata hakuri Dan Adda na da temper, nace " Ba komai Adda!" " Then me yasa Baki sakin jiki da kowa a gida? Kin maida kanki kamar wata bare" To me Zan ce mata? bayan su Suka maida ni hakan, su suka Fara nuna min kamar I doesn't belong to them, dole na janye jiki na. Jin nayi shiru se Bata Kara cewa komai ba, se da ta sauke ni gaban faculty sannan ta ciro kudi cikin Jakarta ta miko min, na girgiza Kai na nace " Kawu ya bani kudi" " Na kawu daban nawa daban, karba joor!" Haka na saka hannu na karba, tayi murmushi mukai sallama, a hankali na sauka zuwa class dina mu, kamar kullum Ina cikin biyar din farko da suke zuwa da wuri. Na samu seat na zauna na dakko waya ta Ina sake duba timetable din ranar saboda semester Bata Jima da farawa ba, ban Gama haddace yadda schedules din suke ba! A hankali ya aje pen din hannun shi bayan ya duba agogon dake hannun shi, karfe takwas saura mintina goma, yasan Yana da class dole ya bar aikin dake gaban shi, wannan ne karon farko da zai Shiga ajin, hakan ya faru saboda sati biyu baya gari, ya dauka suit din Shi ya daura saman sky blue long sleeve din rigar shi, Ya dauki takardun shi sannan ya fita, mintina biyar Suka kawo shi class din mu, Yana shigowa ya tsaya Kan podium tare da gyara zaman glasses idanun shi, dukkan mu muka bada hankali Dan fahimtar abin da zai koyar. " I'm Akram Imam, I'll be guiding you on design process in Architecture!" Dukka Muka bada hankali, cikin turanci yake magana, Amma Haka kurum se nake Jim kamar a nesa nake Jin muryar ta shi, idan na dago na kalle shi se na ga Yana yin dishi dishi, na runtse idanu na Ina ayyana abin da yake faruwa da ni all of a sudden, se kawai na daina ji gaba daya, idanuna Suka Fara daukewa duk yadda nake kokarin bude su, wani irin yanayi ne me wuyar na fada muku, gumu ya jika ni sharkaf, kwace ruwa aka zuba min. Inata battling da idanu na, Naga alamar sakkowar shi Yana tahowa, na Fara kokarin composing Kai na Amma Abu yaci tura.... BINTUN BATUUL ba kyauta bane ba, na kudi. Tafiyar ba Ni kadai bace ba, tafiyar top-notch ce a Karo na uku, wannan karon Aziza tana tafe da GENERAL NASEER ZAKI, yayin da Anty Ramla ta kawo muku NAZNEEN duk akan N1500 kacal. Ki biyo mu ki Sha labari [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ 004 Ayshatuuu Top-notch season 3 Da farko dai sunana Bintu, a gidan mu na Zama tamkar wata shadow ce, wato idan nace shadow Ina nufin Inuwa, shi ne dalilin da Kai tsaye baa Kira na Bintu, sede ace BINTUN BATUUL. Da farko ban gane hakan ba se daga baya da nayi wayo na gane dalilin Kira na da hakan. Kamar yadda kuka sani, a kasar mu ta gado, wato kasar Nigeria mu nada arewaci da Kuma kudancin kasar, mu din Yan arewa ne Kuma arewar ma north west, wato arewa maso yamma. Da bana gane wannan intersection din se a hankali na Fara fahimtar yadda suke da Kuma me suke nufi. A jahar jigawa akwai wani daddaden gari me tarin tarihi, wanda ake tunanin suna daya daga cikin Hausa bakwai, wannan gari masarauta ce cikin daya daga cikin masarautu biyar da suke a garin na jigawa. Wannan garin kuwa shi ne Hadejia ginsau birnin Doki.  Kamar yadda kowanne gari zaka ga Allah ya hallitta musu irin mutane, yaren su da Kuma abincin su, ways of living, norms din su day values din su, to Suma a Hadejia suna da wannan! Na farko dai idan ka fiye Baki a jigawa we consider you Bahadeje (No offense, this is the reality) Yan garin bakake ne, saboda suna da asali da barebari, Amma Kuma akwai farare tunda ana samun auratayya tana hada su day wasu! Akwai Kuma miyar kuka, ban sani ba ko sune founders din miyar kuka, Amma mu a jigawa kirarin da ake ma kuka is always "Bahadejiya kin fi giya tsiya" Wai kuka fa ake cewa Haka, gaskiya justice for miyar kuka....lol Suna da ruwa,  shiyasa suke da kifi, garin Hadejia akwai kifi akwai Kuma ruwa, I remembered duk shekara Kawu zai ce ya tafi Yi musu jaje, either flooding ko Kuma garin is about to flood. Haka dai maganar take. Mahaifi na Dan asalin Hadejia na, tun daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, tun mahaifi na Yana karami Allah yayi Masa son fararen mata, hajja tana yawan fada Mana ko bakuwa akai in dai Fara ce, to ko an aike shi sai saa zai je, da ya Fara girma kuwa kusan duk wadda ya gani Fara se yasan yadda yayi yayi Mata magana, se Kuma yasan yadda yayi ta kula shi ya Fara zuwa gidan su. Wannan shi ne mahaifi na!! Bansan me yasa maimakon Baba ko Kuma Abba ko ka Daddy, da ywanacin ake Kiran iyaye mu a gidan mu Kawu muke cewa, Haka muka tashi muka hi sauran yayin mu na Kiran shi muma Kuma muka dauka. Asalin sunan mahaifi na Hamisu, mutum ne dogo da Kuma jiki, irin mutanen nan da ake Kira da giant, Kuma Baki ne sosae, Dan kuwa Bai bar gida ba. Labarin da na Baku na rashin son bakaken Mata yasa yake da nacin nema, tun da mahaifiyar shi tace Masa ai fararen Mata masu kyau tsada ne da su, shikenan ta birkita wannan bawan Allah, karatu yayi na primary anan cikin Hadejia, kafin da ya Gama ya taho minjibir yayi makarantar maza ta karamar secondary! Da ya kammalla se ya dawo nan tsohuwar makaranta me cike da tarihi wato Rumfa college da ke cikin birnin na Kano. Anan Yana zaune gidan wani kanin mahaifin shi Kawu Sabaru, daga can yake Hawa Keke yaje makaranta, idan aka tashi ya cire uniform ya kulle a Leda ya tafi kasuwa inda nan ne yake yaron shago cikin kasuwar kwari, idan yamma tayi Kuma ya tuko Keke ya dawo gida. Yana ta fama har Allah ya nufe shi da kammalla secondary School, kamar ba zai cigaba ba Amma uban shagon ya nuna masa muhimmanci da yake gani a tattare da karatun Boko, cikin saa da kullum yake fada, Yana Kuma alfahari da shi din me sa'a ne a rayuwar shi. Ya samu gurbin karatu nan cikin bayero University, dukda Haka Yana kasuwancin shi, Yana Kuma yin taro yadda Baku tunani, a kwana a tashi , karatun shi yayi nisa haka ma kasuwan cin shi, mahaifin shi ya aike Masa da sakon komawa gida Dan an zaba Masa Mata. Kunsan dai ya Riga da yayi alkawarin mace in dai baka ce to Bata da gurbi a cikin gidan shi, Bai Yi musu ba ya tafi Hadejia Dan ganin Mata, Yana zuwa ya tarar da Yar kanin baban shi ce Salamatu, shi yarinyar saboda bakin ta ko magana ba yayi Mata, kuji fa gwano baijin warin jikin shi, shi ma da bakin ne. Ya nunawa mahaifin shi rashin son auren Amma mahaifin shi yace Babu fashi, shikuwa ya tattara na shi ya nashi ya dawo Kano ya cigaba da sabgar shi, aka daura aure kamar yadda aka saka rana, Amma ango har amarya tayi wata guda Babu shi Babu dalilin shi, Haka mahaifin shi ya dakko Salamatu ya taho da ita Kano, ya aje Masa ita dakin shi na zaure Dake gidan Kawu Sabaru. Se dare ya dawo kamar kullum, da bredi na kullum da yake tahowa da shi da Kuma alawa saboda Yara. Yana zuwa ya shiga dakin shi Kamar yadda ya saba, ya cire Kaya ya fito zuwa wani shago Dake makwabtan su yayi wanka sannan ya dawo, se da ya saka Kaya sannan ya lura da dankwali an kulle Kaya da shi, ya saka kafa ya shura dankwalin se Kuma ya dauki biredi da sauran kayan shi yayi cikin gida, Jin sallamar shi yaran Suka taho da gudu, dukda ba kula su yake can sosae ba, Amma dai Yana Basu alawa, shi Kuma alkhairi Yana saka mutum ya Shiga ran Wanda yake bawa, shiyasa kayi kokarin ganin ka kyautatawa mutane. Ya Mika musu ledar alawar su, sannan ya bawa babbar biredi Dan ta kaiwa mahaifiyar su, anan zaune yayi Ido hudu da Salamatu,  da taimakon aci balbal din Dake gaban ta wadda aka kunna Dan ta haska gidan, ya Bata fuska Yana ayyana wannan mayyar har nan ta biyo shi ko ko me? Suna gaisawa da Inna talatu matar Kawu Sabaru, se ga Kawu Sabarun ya shigo, Suka gaisa da Kawu Dake kokarin juyawa Amma Kawu Sabaru ya dakatar da shi, tabarma Salamatu ta shimfida musu Suka wanke hannu Suka ci tuwo tare, wannan cin tuwon tare implies alot, ya tabbatar akwai gagarumar magana a kasa Yana Kuma fata Bata danganci auren Salamatu ba, Dan kuwa ba zai aure ta ba, ba zai zauna da bakar mace marar wayewa irin ta ba. Idan Kuma suka matsa to gaskiya ba zai jure ba, zai bijire duk abin da zai faru ya faru, wannan shi ne  tunanin da yake yawo a cikin kwakwalwar Kawu. Bayan sun Gama cin tuwo an wanke hannu, Bayan Gama sude sude saboda Inna talatu ba dai girki ba, matar nan da ace a wannan zamanin take, to tabbas zata buge food content Creators da yawa! Cikin lallami, da Kuma tsara kalamai Kawu Sabaru yayi wa Kawu bayanin halin da ake ciki, na an Riga da fa an daura Masa aure da Salamatu, shi ne dalilin dawowar ta nan, ya kada Baki da fadin Kuma Yana son yayi hakuri ya zauna da matar shi lafiya su samu zuri'a dayyiba. Kawu da yake ta auna kalaman cikin Kan shi, like for real shi akaiwa auren Dole? Ko Kuma bashi Hamisun ba? To su wanne digimi ne ya kaisu entrusting Yar su gare shi, bayan he clearly said it, baya so, baya son ta ba Kuma zai aure ta ba. To fa cikin Abu biyu Dole zaayi daya, ko dai ayi Abu cikin lumana ko Kuma hatsaniya ta biyo baya domin shi dai Bata da space cikin rayuwar shi! " Kawu Sabaru, gaskiya maganar Allah bana son yarinyar can, bana kaunar ta ba Kuma Zan zauna da ita ba!" Kawu yayi saroro Yana kallon shi da mamaki a fuskar shi yace " To Hamisu waye yayi auren soyayya? Ai dukka Hadi akai Mana Kuma gashi mun manta cewa ba soyayya mukai ba! Ka da kake neman albarka..." "Wannan fa ya wuce Kawu! Ni na fadawa malam (mahaifin shi) ni ba Zan aure ta ba, saboda ni matar da Zan aura ba irin wannan suffar nake so ba" Mamaki ya Kara kama Kawu Sabaru, ai se ya Fara fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Amma wannan fadan Bai saka ya janye kalaman shi ba, Haka suka rabu baran baran, ya koma daki Yana ta pacing cikin tsukakkaen dakin Yana Kuma nemawa Kan shi mafita, a karshe se ji yayi an turo kofar an shigo, ya dago idanun shi Yana tunanin wanne isashen ne? Se gata a tsaye ta Sha lullubi Wanda ya Bata Masa Rai, maimakon Barin ta ta shigo se ya maida kofar ya barta a nan tsaye. A takaice kowa baccin bacin Rai yayi, kowa jira yake safiya tayi ya dauki mataki. Asuba nayi ya hade kayan shi tas saboda yasan idan ya aiwatar da abin da yayi niyya to tabbas zaman shi gidan Kawu Sabaru yazo karshe,shi Kuma saboda gurin Zama ba zai cuci rayuwar shi ba. Ana idar da sallah yayiwa Tasha tsinke ya hau mota se Hadejia, shima Kawu Sabaru Yana idar da sallah wanka ya dawo yayi a gida sannan ya dauki hanya se Hadejia! Ko da yaje gidan su ya wuce, ya samu mahaifin shi ya dawo daga su, wato kamun kifi saboda sanaar shi kenan, Bayan sun gaisa aka kawo Masa tuwon buski da miyar kuka, ya zauna yaci yayi hani'an kafin mahaifiyar shi ta Fara tambayar shi wajen su Inna talatu da Kuma amaryar ta shi? Lafiya kawai yace Mata sannan ya fice zuwa wajen baban shi, ya samu har Kawu Sabaru ya iso Kuma an Kira Kawu Mamman wato mahaifin Salamatu, dukka suna zaune suna sauraron abin da Kawu Sabaru yake fada musu. Ko dar baiji ba yaje ya zauna, malam ya Fara fada se Kawu Mamman ya dakatar da shi yace " Hamisu baka son Salamatu ko?" Ya gyada Kan shi, ba tare da yaji ounce of rashin dacewar abin da yayi ba "Bana son ta Baba, ban shirya aure ba. Ku gafarce ni, bana son zumunci ya lalace, ba Kuma nasan Bata muku, ko Kuma na zalunce ta shiyasa nazo nace muku ni na sawwake Mata igiyar aure na daya dake kanta idan ta samu miji tayi aure" Kun Yi subscribing top-notch season 3? To kada ku Bari NAZNEEN, BINTUN BATUUL da Kuma GEN NASIR ZAKI ya wuce ku. Wannan tafiyar daban take, labaran daban suke. N1300 for 3, N1000 for 2 and N500 for 1. [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Ayshatuuu Top-notch season 3 006 Ni fa ban yadda ace Wai wannan matar ba tada kishi ba, kowacce mace tana da kishi, Kuma tana da nata salon yadda take bayyana shi. Dan namiji yace zaiyi aure ba Wai Yana nufin ya gaji da ke ba, ko ya tsane ki ko Kuma irin kin kasa ta wani bangaren, it's a call they answer, raayi ne Haka Kuma yiwa mace kishiya a nawa ganin ba laifi bane ba, Amma dai a dinga kokarin yin adalci da Kuma gane concept din polygamy! A gani na laifi da akw shi ne path din da ake bi wajen auren da Kuma bayan auren, yadda wasu mazan ke muzgunawa matan gidan ko su wofantar da su, wannan shi ne laifi, Kuma Ina ganin abin da yawancin mu Mata muke tsoro kenan, kishiya Adda ta Kan ce tayi Dana sani tada hankali da dukkan abubuwan da tayi, idan da har tasan Mamaa ce kishiyar. Ni fa a gidan mu nake kasa banbance iyayen mu, su Adda suna da wani exceptional relationship tsakanin ta da Mamaa, shiyasa har zuciya ta bana ganin polygamy as a problem, rather wadan da suke cikin polygamy dinne masu matsala! Bari na fada muku Adda tayi balai, ta tada hankalin ta yadda Baku tunani, a ganinta wannan shi ne karshe, ta Yaya ma zaace Bata shekara biyar ba ayi Mata kishiya, akwai Rights din Kawu da ta daina saukewa, Wai ita tana fushi. A irin wannan lokacin, it's a crucial moment saboda aure zai iya mutuwa, idan namiji baiyi da gaske ba se kaga aure ya mutu. Lokacin da zaa yiwa Adda Sajida kishiya, akwai wani Abu da ta yiwa mijin ta Wanda se da ta dawo gida tayi zaman wata data, daga yace zaiyi aure Adda aka Fara throwing tantrums, zagi ta uwa ta uba, kishi dai na hauka, mutuminnan ya dauke idanun shi, lokacin harvest yayi ya kawo amfanin gona gida, mutuniyar ku tace to ita fa anan zatai ramuwa, ta dauki dawa ta hada da alkama, ridi da shinkafa, Kai Adda Sajida Bata da kirki, Dole se da ta dawo gida Amma Kuma mijin Bai sake ta ba, cewa yayi ta fitar Masa a gida ya daina ganin ta har se ya huce, to se da akai biki da sati uku amaryar har ta Zama Yar gari kafin uwargida Adda Sajida ta koma. To kunga hakan Bai Hana shi auren ba, se ma darajar ta da ya rage, Saboda maza basa uzuri akan kishi ko kada. Abin da ya karya lagon Adda shi ne zuwan Alhajin KT da Kuma Iya wato mahaifiyar ta, kunsan yadda iyayen da suke, mutane ne masu Kara da Kuma dattako, dukda a yanzun Ina ganin abin odd na goyawa mijin yata baya bayan nasan shi ne bashi da gaskiya, gaskiya bazan iya ba, dukda ance Wai hakan shi ne siya ma Dan naka daraja a gidan aure, this is all by the way! Alhajin KT da Iya sun Yi kokari matuka wajen tausar Adda, har ta samu ta Dan dangana Amma cikin zuciyar ta Bata tunanin rift din da aka samu tsakanin ta da Kawu Abu ne da zai cike, dadin dadawar bacin ran ta se Alhajin KT yayi uwa ya Kuma Yi makarbiya wajen ganin aurennan ya tafi, a karshe ma dai Wai shi ne walliyin Mamaa, ciwo goma da ashirin kenan! Aka kawo amarya dakin ta, kowa tausar Adda yake, tare da nuna Mata yadda zatai ta kwaci Kan ta, Amma da se idan ta rike wannan girman nata, idan ta Bari kuwa to zata kwace ita Kuma ta Zama Yar kallo, wasu Suka ce Mata duk namiji se yayi daukin amarya, se yayi rawar Kai se Kuma yayi falli, Amma idan uwargida tayi hakuri da zarar gishiri ya ishi Kan kaza to fa ungulu zata koma gidan ta na tsamiya, ai dama ance tsohuwar Zuma ita ke magani. (A soothing message to uwargidas' I'm rooting for you!) Dama bacci Kam dai rabi da rabi akai, kusan kwana tayi tana karatu Dan ya debe Mata kewa, Amma dukda haka amidst karatun zata kwanta tayi kuka ta godewa Allah, a Haka safiya tayi ta Mike jiki a sanyaye tayi wanka tayi sallah sannan kuma ta wuce kitchen ta daura sassaukan abinci kamar yadda Iya ta Nanata mata, tace Mata lallai lallai ta daure tayi girki ta Bata, shi ne girman, tana kammallawa ta koma daki ta zura fararen uniform din ta da suka Sha guga suka daukar idanu, a karshen hannun akwai lanyard na nuna ita din student ce, ta daura katon hijab akai da ya rufe Mata uniform din sannan ta dauki jakar ta Dan ficewa, sede tana kokarin kulle kofar parlon ta se ga Kawu ya nufo ta, da ta kalle shi se taga kamar Yana murmushi, kamar wani annuri ne ke exuding daga fuskar ta shi, taji kamar ta shake wuyan shi kowa ya huta, Amma se ta Fara Nanata auziyya Dan korar shaidan, ya karaso tare da karbar makullin da kulle Mata saboda battling da take tayi da shi ta kasa kullewa, saboda hankalin ta da Kuma tunanin ta dukka baya gurin, bayan ya rufe dakin ya Mika Mata makullin tare da amsa gaisuwar da ta Masa ciki ciki. Duk yadda Taki se da ya Kai ta har makaranta kamar yadda ya saba, sannan da ta tashi yaje ya dakko ta, lokacin da ta dawo Mamaa ta kammalla abinci, ta gyare gidan tsaf, tana daki tana sake sake. Se dare suka hadu yayi musu nasiha sosae tare da Yi musu alkawarin adalci. Da farko Adda Bata Shiga harkar Mamaa, ko abinci tayi se taki ci, Amma hakan Bai Hana Mamaa cigaba da kyautata Mata ba, a Haka har Adda bayan wajen watanni hudu ta fahimci sincerity din ta Kuma ga laulayi da ta Fara me ban wahala, Haka Adda ta yada makaman ta ta rungume ta, shikenan zaman lafiya se ya wanzu a gidan. Bayan watanni Adda ta Gama makaranta ta Kuma samu aiki cikin asibitin murtala Muhammad dake cikin kano, Fara zuwan ta Babu jimawa itama se ga ciki ya bayyana a jikin ta, lokacin na Mamaa wata wajen takwas. Kawu yayi murna kamar zai zauce, Mamaa ta Haifa mace aka saka Mata suna Fatima ana Kiran ta Haka, Bayan watanni Adda ma ta haihu aka saka Mata Fadima. Kunsan yadda Kawu ya dinga saka Mana suna Fatima se Dana Fara tunanin Anya kuwa bamu Hadi da shi'a? Yo Ina dalili mu kusan takwas suna daya, Fatima, Fadima, Sajida, Adawiyya, Zuhriyya, Zuhra, Zahra, Batuul da Kuma ni Bintu! Mu Tara kenan fa! To Haka sunan mu suke se maza guda uku Wanda yasa Auwal, Sani da Kuma Salis. Gidan mu kamar su kusan daya, farare Kuma kyawawa, sirara, dogaye. Yadda iyayen su Mata suke Haka Suma suke, kunsan it can't be a coincidence Dan akwai gidan da zakaje kaga kowa ya nada kyau, to gidan mu kenan, har alfahari suke da wannan kyan nasu! Bayan set din su Fatima da Fadima, se Kuma Mamaa ta Haifa Adda Sajida ita Kuma Adda ta haifa Yaya wato Auwal, tana aikin ta yayinda Mamaa ita ke zaune a gida, tamkar ministan cikin gida, komai indai na cikin gida ne to kada ma kaje wajen Adda kawai Mamaa ce komai. Mamaa ta sake haifan Yaya Adawiyya, ta sake haifan Yaya Zuhriyya se lokacin ita Kuma Adda ta haifa Yaya Sani, Mamaa ta haifi Zuhra, se Kuma sukai goyon Yaya Salis Wanda shi ne namiji kadai wajen Mamaa, Adda Kuma ta Haifa Zahra. Shikenan se haihuwan ya tsaya kamar daukewar ruwa, har su Yaya Zahra sukai shekara biyar abin da baa taba Yi ba a gidan, a yi shekara biyar Babu sabon jariri gidan. Lokacin Adda ta Gama BNSc din ta tana kokarin Fara masters se kawai ciki ya bullo a jikin ta, ta kance wannan cikin ba karamin katsalandan yayi Mata ba, saboda tana kokarin pursuing dream din ta se ga ciki ya fito, to ya zatayi? Haka ta hakura ta jira zuwa lokacin da zata haife abin da

Chapter 2 of 18