Zan Fara shawo Kan matsalar Bintu ba!"
Cikin rashin Jin dadi yaya Fadima tace
" ki nutsu tukunna, sannan ki huta, zuwa dare ko safe se muyi magana, Amma kiyi ta Mata addua"
Daga Haka sukai sallama sannan ta Shiga wankan saboda kanta Dake ciwo.
Kawu Yana kwance can cikin bedroom lokacin da Mamaa ta shig, ya juyawa kofa baya tare da yin likimo tamkar me yin bacci, Amma ba baccin yake ba ko kadan tunanin Bintu kawai yake, tausayin ta da Kuma Jin haushin Kan shi Akan halin da yarinyar take ciki, wanne irin sakaci yayi har yarinyar ta Shiga mawuyacin Hali take Kuma kokarin saukar rayuwar ta? Haka ta fito jikin ta a mugun sanyeye, se ta wuce waje na. Ina zaune akan gado da wata sabuwar Reza a hannu na Ina kallon hannu na ta wajen da na San radial artery di ta na nan!
Ta-kwalam
BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free, do contact us for payment details!
[1/3, 20:28] Maman: 020
BAYAN WATANNI UKU!
Cikin karamin apartment din su dake dad da makaranta, Wanda tun bayan shaida auren su day Kuma shagulgula da colleagues din Imam suka hada masa na taya shi murnar auren burin zuciyar shi, se Kuma yaran shi da sukai raising makudan kudi Suka Kama Masa wannan apartment din da ya zauna da zainab din shi. To fa duk wannan halin da ake ciki Imam ko da Wasa, ko da subul da baka, Bai taba fadawa wani makusancin shi a Nigeria ba, duk abin shi Yana shakkar kakan shi Wanda shi din baya Wasa, duk da tsufa da girma Amma Bai Bari wani ya taka authority din shi ba, har a wannan lokacin shi ke da ragamar komai na family business din su. Imam na daga cikin kalilan din jikokin da Alhaji Gidado ke so, tun Yana jariri yake son shi, Salma Kuma cousin din shi ce wadda iyayen su maza suke immediate. Alhaji Gidado nasan Salma kamar yadda yake son Imam, ko da zai taho nan UK karatu se da Alhaji Gidado ya tabbatar masa idan ya dawo bashi da wata matar aure da ta wuce Salma, to ya zaiyi ko dai yayi naam cikin dadin Rai ko Kuma yayi cikin bacin rai. Amma ganin zainab se da ya ruguza Masa dukkan wani lissafi da wani tsoron Alhaji Gidado da ke zuciyar shi.
Kwance zainab take akan gado, idan ka kalle t se kayi tunanin she's lifeless saboda uban aman da tayi da ya saka jikin ta saki kamar mataciyya! Ya shigo daga waje bayan ya dawo daga makaranta, da mamakin ganin Bata living room kamar yadda ta Saba idan ta riga shi dawowa, zata zauna ta jira shi har lokacin da zai dawo ta tarbe shi. Wani lokacin Kuma zata zauna gaban class din su har se ya kammalla lecture din shi kafin ya fito suyi trekking zuwa gida, soyayya iya soyayya, kauna iya kauna shi ne kawai abinda ke fitowa daga gurin su, ko minti uku kayi tare da su se ka fahimci yadda suke ji game da junan su, tun zainab tana kunyar yadda yake Mata ko a gaban mutane ne, har ta dawo Bata damuwa, itama ta Fara nuna mishi yadda take ji game da shi.
Karasawa yayi ciki, cikin sauri ganin yadda take kokarin tashi ta zauna Amma Abu yaci tura, ta Fara kokarin tashin se taga idanun ta sun rufe se ta koma jagwab Kan gado. Wannan ya tayar masa da hankali balle da ya karasa inda take kwance ya ganta kamar mataciyya se hankalin shi yayi mugun tashi, ya Fara kiran Charles akan yayi saurin kawo Masa mota, ko veil Bai yafa Mata ba Haka ya dauke ta cilak yayi waje da ita, suna zuwa asibiti aka Fara bata taimakon gaggawa, a kankanin lokaci Suka tabbatar masa ciki ne a jikin ta na kimanin wata daya, yayi murna kwarai da gaske Dan dama abin da yake ta jira kenan ya samu weapon din yakar kakan shi ya amince da zainab a matsayin matar shi, yasan auren Salma Babu makawa zai aure ta Amma fa zainab kadai zuciyr shi ke so.
Ganin yadda take Shan wahala se duk jikin shi yayi sanyi ya fara Jin Anya zai iya barin ta ta cigaba da Shan wannan wahalar? Haka dai ya bar ta har zuwa lokacin da ta Dan samu karfin jiki wato da daddare, ya zauna Yana yanka Mata apple da tace tana son ci, a hankali take taunawa kamar Bata so saboda bakin ta babu Dadi
" Solace!"
Ta dago ta kalle shi tana taunawa kamar Bata so, ya sake rike hannun ta yace
" Solace mun samu Baby, you're pregnant! Are you happy?"
Ta tsira Masa idanun ta masu haske da Suka Dan rine saboda wahalar da ta Sha, kamar so take ta gaskata abin da yake cewa, ita din da gaske take da ciki? Ita din ce baby yake kwance a cikin ta, Kuma Babyn ma na Imam, farin cikin rayuwar ta? Se hawaye a hankali ya Fara trickling Mata Kan kuncin ta, she was so happy, she was so elated har Bata san tana kuka ba. Amma kallon da yake Yi Mata yasa tace
"Ba wani Abu bane ba, I'm just overwhelmed ne!"
Se ya saki murmushi Yana rungume ta a jikin shi yace
" Nayi tunanin Baki son cikin ne, har na tsorata"
Ta girgiza Kai ba tare da tayi kokarin dauke hawayen ba, in fact se ma bari da tayi suka cigaba da zuba daga idanun ta, a hankali kamar whisper tace
" Chum! Ina cikin farin ciki, Wanda ba Zan iya misalta maka shi ba, I'll be able to carry the fruit of our love"
Yayi murmushi na Jin Dadi tare da shafa Kan ta. A Haka wannan masoyan Suka cigaba da rayuwa tare da rainon cikin su, sede cikin wahalar da zainab yake sosae, duk yadda take kokarin dannewa Amma hakan ya fito kowa ya ga irin wahalar da take Sha. Imam ya tada hankalin shi ganin wani lokacin se tayi kwana biyu ko ruwa ta saka a bakin ta se ya dawo, wannan dalilin yasa ya samu Murad Dake shi medical student ne, yace Masa ya kawo Masa abortion pills. Murad ya dube shi da tantamar abin da yace,
" Wa zaka bawa boss? Kada dai sister in law zaka bawa?"
Imam ya gyada Kai cikin alhini tare da fadin
"Bata da lafiya, bana son ta mutu, gwara na hakura da wannan cikin akan na Rasa solace di ta"
Murad kamar yayi dariya saboda ko da Wasa akace zaiyi wannan abun akan mace tabbas zaka Musa, shi baya ma son Abu ya dinga hada shi da Mata sosai, lallai zainab must be born with a great luck
" Boss! Kana ji, it's normal during pregnancy, duk wannan abun zasu wuce after 3 months!"
Wani mugun kallo yayi ma Murad Wanda yasa yasan shawarar shi Bata karbu ba, Kuma ba zata taba karbuwa ba. Instead se yace zai je ya kawo Masa. Only God knows how Murad ya samu pills dinnan ya kawowa Imam da ke zaune zuciyar shi kamar zata fito saboda jiran da yake yiwa Murad, ya kagu ya kawo masa maganin yaje ya saka Mata ko ta huta. Haka kuwa Murad ya kawo Masa, ko Kiran yaji directives din maganin baiyi ba ya karba ya wuce , yasan how much she likes apple drink, take yayi blending ya Kuma tace sannan ya jefa pills biyu ciki ya Bari ya narke, ya juya kafin ya wuce daki ya Kai Mata, tana kwance tayi lamo kamar wadda aka mawa duka Amma Tsabar rashin kuzari ne. Yana zuwa ta dago tana kallon shi duk ta rame kamar ba zainab din shi ba, hakan ya Kara bashi karfin gwiwar aiwatar da abin da yayi niyya. Ya dago ta jikin shi Yana mayar mata faint smile din da tayi masa, ya shafa Kan ta tare da furta
" Ya kike ji yanzun"
Ta Dan Yi murmushi tace
"Alhamdulillah! Marhaba ya Chum!"
Kamar yadda take Dan tsintar Hausa har ma da fullanci daga bakin shi, Haka shima yake tsintar larabci daga nata bakin. Ya Mika Mata tumbler hannun shi, Babu musu ta Soma Sha a hankali, a Haka ta shanye tas, a take wani bacci ya Fara kokarin daukar ta. A jikin shi tayi baccin, se da yaga tayi bacci sosae sannan ya gyara Mata kwanciya ya fita zuwa parlor.
Ta_kwalam
A Kara hakuri, jiki da Jini. Thanks for understanding
[1/3, 20:28] Maman: 019
Ban San dalilin da yasa nake Jin urge din daukar rayuwa ta ba, na San dai kawai gaba daya mind di na is blank, Babu wani Abu da nake tunani bayan wani irin kunci da nake ji cikin zuciya ta. Na lumshe idanu na bayan na fito da rezar daga cikin gidan ta, sabuwa ce dal da alama Batuul ta siyo ta ta bar ta a wajen, saboda Batuul ko kadan Bata San menene Adana Abu ba, komai darajar shi zata iya tashi ta bar shi a wajen. Ina ta kallon hannun nawa Ina tunanin na yanka ko Kuma na tsaya? Amma zuciyar da take zuga ni Akan na yanka din se ta rinjaye ni, na daura Ina Jin hawaye suna min zarya akan kumatu na, sede kafin na dadara a hannun naji Mamaa na fadin
"Bintu! Bintu!!"
Na lumshe idanu na, ba tare da na dago ba, balle na kalle ta ko kallon zai saka na fasa, instead se na Yi kamar da dai duniya bansan tana yu ba, na saita rezar a hannuna ta karaso in da nake tare da tankwabar da hannu na, duk da Haka nayi nasarar yanka hannun sede sama sama Wanda ganin jini Yana fitowa daga hannun yasa Mamaa wanka min mari, wannan Marin did awaken my soul, na dago Ina kallon ta, ta Kara kwada min mari a dayan kuncin nawa, ta Fara fadin
" Kashe Kan ki zakiyi? Ba kids hankali? Ke mahaukaciya ce Bintu? Me ya faru da ke da kike kokarin kashe Kan ki? Me ya same ki? Ina Kika bar imanin ki? So kike ki mutu kafira? Iyeee?"
Wannan ihun da take yasa Batuul shigowa da sauri da take sanye cikin jeans da customized rigar su ta graduation, idan ka kalla Batuul zaka rantse ba Yar musulmai bace ba saboda shigar da tayi, ta dame jikin ta, an Sha fixed hair da lashes, ga uban artificial nail da akai polishing din shi aka Kuma je extra miles aka jera stones akai. Wani bingilin veil ne ta yafa Wanda ko kirjin ta Bai rufe ba, Ashe fada sukai kaca kaca ita da Suleiman Akan wannan shigar da tayi, tayi fushi ta sauka daga motar ta shiga napep ya kawo ta gida, tazo dan ta kawo karar shi wajen Mamaa Kuma se me Mana aiki ta sanar Mata ai Mamaa na dakin mu shi ne ta shigo. Juyawa tayi da sauri ta Kira Adda, Kawu dake tsaye window yaga gudun da Batuul ke yi, shima Babu shiri ya zura jallabiyya ya fito, suna zuwa Suka samu Mamaa na daure min hannu na, se kuka nake yayin da ko uffan Bata Kara ce min ba. Adda tana ganin wannan abun kawai ta Fara kuka, se da ta gama daure min hannun kafin ta dubi Batuul Dake tsaye tace
" Ki zauna da ita kafin mu gama magana"
A sanyaye Batuul ta gyada kai, yayin da Mamaa tayi waje, da kawu da Adda Suka bi bayanta, se da suka zauna parlon kawu sannan Mamaa ta dube su dukkan su hanklain su a tashe yake tace
" Me yake faruwa da Bintu? Ko kunsan Reza ta dauka ta yanki kanta? Inda ban zo ba bansan wanne irin yanka zatai yiwa kanta ba"
Kawu ya dafe Kan shi Yana ambaton sunan Allah! Wannan wacce irin siririyar masifa ce ta kunno Kai gidan shi
" Ban sani ba, ban Kuma San me suka fada muku daga makarantar su Bintu ba, Amma koma menene yanzun Bintu tana bukatar a saka Mata idanu, ba a barta ita kadai ba, na fahimci kamar dukkan ku Kuna cikin damuwa, to Amma damuwa zata bayar da sahihin maslaha? Bana tunani..."
"Ina ga Zan aika ta wajen Fadima a sokoto!"
Adda ta fada tana Jin wani irin rashin Dadi cikin zuciyar ta. Kawu ya girgiza Kai yace
" A'a Asiya, gwara ta zauna anan akan mu tura ta wani gurin taje ta zame musu burden.."
"Gwara ta zauna nan, Ni Zan kula da ita, Zan Yi magana da ita, idan tana bukatar likita se muje"
Adda ta dinga Yi Mata godiya kafin Mamaa ta Mike Dan komawa daki ta ganni, Ina zaune na kurawa pillow na idanu, Amma a zahiri ban masan a wacce duniyar nake ba, Batuul tayi jugum se kallo na take, ta Kuma rasa abin da zata ce min, Wanda hakan yayi min dadi Dan bana son hayaniya ko kadan. Haka ta shigo ta same mu, muryar Batuul da ke amsa maganar Mamaa yasa na dawo hayyaci na, na Dan kalle ta, itama sashen nawa take kallo, idanuna da fuskata sun rame kana kallo na kasan akwai abin da yake damu na, ko dai rashin lafiya ko wani abun.
" Tashi muje Bintu!"
Babu musu na mike a sanyaye na bi bayanta, har cikin bedroom Muka je, ta nuna min gefen gadon ta akan na zauna Babu musu na zauna, ta fita se can ta dawo da abinci ta aje min tare da kura min idanu da ya saka ni Babu yadda Zan yi na dauki spoon na Kai Baki na, wani irin daci naji rice din tana Yi, Amma kallon da take min yasa na cigaba da taunawa Ina Jin rashin Dadi a Baki na, se da naci da Dan yawa har naji Dadi a ciki na kafin na Sha ruwa Mamaa ta Fara yimin magana cikin tausashen murya.
"Bintu kinsan hukuncin Wanda ya kashe Kan shi kuwa?"
Ta fada tana ruko hannaye na cikin nata, ganin ba zanyi magana ba tace
" Idan Kika mutu a Haka to kin mutu kafira, duk sallar da kikai, duk azumin da kikai, duk dokar Allah da Kika bi ta tashi a banza. Yaushe Bintu? Yaushe zakiyi wannan danyen hukuncin. Duk abin da rayuwa ta yi ai karki manta Allah Yana tare dake"
Har lokacin ban ce komai ba, tasan maganar ta Bata shige ni ba, hakan yasa ta kyale ni. Wajen yamma ta shirya tace Nima na shirya mu fita, se lokacin nace
" Ina son Zama a gida"
Tace
" Eh ba jimawa zamuyi ba!"
Haka na shirya muka fita, Babu inda Muka je se zagaya unguwa, a hankali naji abin da yake cikin zuciya ta Yana Dan raguwa musamman da Banga wani yayi min wani irin kallon kalla wannan katuwar! Muna Shiga gida ana Kiran maghrib, tare mukai sallah tace na daga hannu na roki Allah gafara Dan tana da tabbacin Allah fushi yake Dani, wannan abin da ta fada se kawai na Fara kuka Jin wannan abun, dama abin da take so kawai taga nayi kenan. Kilan idan nayi kuka akwai tendency nayi magana, magana ta kuwa zai rage min radadi cikin zuciya ta!
A kalla se da Muka dauki sati tare da Mamaa, kullum tana Kan yimin nasiha da nuna min babban laifi na aikata, Adda kullum se ta shigo ta ganni, Haka kawu ma, wannan dan abin da nayi se yasa na samu attention daga gurin iyaye na, na manta da jin wani yace min wai nayi kiba ko wani abu. Hankali na se ya Fara kwamciya har zuciya ta sanyaya na Fara Jin loved and belong!
Sai da akai sati sannan da safe bayan mun kammalla breakfast ta Fara tambaya ta
" Bintu bani labari, fada min me yasa Kika Sha Dettol a school?"
Nayi shiru Ina kokarin battling da zuciya ta Akan na fada ko kada na fada a karshe na bude Baki na, na Fara fada mata
"Mamaa bakwa so na, Babu Wanda yake so na a cikin gidannan, kowa blaming di na yake saboda Ina da kiba Mamaa, Amma Kun manta ai ba laifi na bane ba, Nima da an bani zabi bazan Zama me kiba ba...."
Tayi shiru Allah kadai yasan yadda zuciyar ta take wani irin tafasa, tamkar zata fito Haka take ji, ko itama ta tuna watarana da na taba tambayar ta me yasa basa so na, Amma amsar da ta bani ba me Dadi bace ba
" Laifi na ne Mamaa? Shiyasa Naga rayuwa ta Bata da amfani naga gwara na kashe Kai na kowa ya huta, kunga Kuma ba zaku damu da ganin mummuna a gidan ku ba!"
Wannan karon rungume ni tayi, hakan yasa na Fara kuka ita Kuma tayi shiru Amma dai Bata ce komai ba. A washegari da Kuma nasihun da take Yi min yasa na Fara neman gafarar ubangiji, Ni kaina se naji kunyar Kai na nake, balle Allah, na tabbatar Allah yayi fushi Dani . Na dage Babu dare Babu Rana na dukufa neman gafarar shi, yadda nake rokon Allah se zuciya ta ke washewa, nake Jin kamar ni din wata sabuwar halitta ce. Na Fara mantawa da wani BashPrince00 da Samiha, dukda wani lokacin se naji I'm crazily missing him, Amma idan na tuna abinda sukai min se naji babu wani Abu da ya rage da Zan zauna Ina neman shi. Cikin iyayen nawa su uku kowa kokarin kyautata min yake. Wasu lokutan har Adda idan zata je office se ta tafi Dani dukda ba son hakan nake Yi ba Dan kunsan bana son shiga cikin mutane. Shikuma kawu se ya sake biya min naje na sake advance cake training, to wannan yafi komai yimin Dadi. I got to understand how much flour means to me, I find solace duk lokacin da na Fara kwabi. Cikin hukuncin Allah na Fara karbuwa hadi da naci da nake. Ina yin cake na sako su meat pie da wasu cikin assorted snacks!
Ta_kwalam ce
BINTUN BATUUL, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI is not free!
[1/3, 20:28] Maman: 021
Peacefully zainab tayi bacci har wajen tsakiyar dare se wajen uku na daren sannan ta Fara Jin kamar ana mintsinin ta cikin marar ta, cikin rashin Jin dadi ta Yi juyi tare da Kara stretching kafarta, Amma a hankali se ciwon ya tashi daga mintsini ya koma ciwo sosae, Wanda Babu shiri zainab ta bude idanun ta tangararau, anan ta tabbatar da cewar ciwon da gaske ne. Ta tashi ta zauna a daddafe, taree da kallon gefen ta inda Imam ke baccin shi hankalin shi a kwance, Dan kada motsin ta ya tashe shi se ta Mike zuwa can living room ta Fara safa da marwa, wani lokacin ta durkushe a wajen ta saki siririyar Kara, ciwo yayi ta gaba, har tazo ta kasa ko da daga kafafun ta, gaba dayan su are numb. A hankali taji kamar Abu Yana sauka daga jiikin ta, tana Kai hannun ta Kan wandon sleeping wear din Dake jikin ta se taji danshi, ta saka hannun ta ta shafo kasan a take taji ruwa, ai kawai ta saki wata Kara Dan.tasan definitely jini ne. A gigice Imam ya hantsilo daga gadon, har Yana a dungure ya kunna fitilar bedroom din, sede Babu kowa hakan ya tabbatar Masa tana linving room, cikin hanzari ya nufo in da take durkushe tana kuka Kuma ta damke marar ta. Yayi saurin karasawaya tsugunna gaban ta Yana fadin
" Solace! Me ya faru?"
Ta Fara kuka a hankali tana fadin
"Chum Mara ta, I'm bleeding, I'm losing my baby!"
Ya rungume ta sosae cikin jikin shi wani irin guilt Yana addabar zuciyar shi, dama Haka ake barin? Shi yayi tunanin silently cikin zai fita Babu wani ciwo, Amma me yasa zainab din shi ke wannan irin ciwon hakan? Tsoron kada fa ta mutu yasa ya koma daki ya canja kaya, itama ya samo Mata wasu kayan sannan suka tafi asibiti, cikin gaggawa aka karbe ta a gynae, bayan hoto da akai Mata aka tabbatar da cewar ciki ya lalace, Dan da yawa ma ya fita, suka fito bayan sun daura Mata ruwa hade da Mata allura wadda zata easing Mata pains din da take ji. Imam na zaune a waiting area kamar yadda aka umarce shi da ya zauna ya jira, Yana ganin fitowar mutumin ya Mike tare da nufar shi Yana tambayar yadda jikin ta yake yanzun, se ya tabbatar Masa Babu yadda zasuyi su saving cikin sedd ya saka hannu idan ya yadda ayi Mata wankin mahaifa. Cikin sauri yace
" Will she be ok? Kana ganin Babu complications da zai biyo baya?"
Gaba daya Yana cikin tarin da na sani da guilt, da yaji shawarar Murad ya batta tun da ya tabbatar Masa duk inda ta Kai wata uku zata daina at most ta Kai wata biyar. Me yasa tausayin ta ta rinjaye shi har ya kara saka ta cikin pains haka?
" Complications din kadan ne wani lokacin ma babu gaba daya, just sign the consent form, muyi mu Gama"
Haka kuwan yayi seda yayi signing sannan ya shiga inda har lokacin zainab bata daina murkususu ba, yaje ya zauna ya ruko hannun ta, idanun shi sun kada sunyi jawur saboda tsananin tashin hankali da kaduwar da yake ciki.
" I'm sorry solace! I've caused you a lot of pains!"
Ta cije bakin ta cikin azabar ciwo, da azabar ciwon zuciya na fitar yaron da ta kwallafawa Rai akai, tace
" Chum I'm sorry, I failed to protect our child!"
Duk mazantaka irin ta Imam se gani yayi hawaye kawai suna sauka Masa daga kuncin shi, me yasa yayi Haka? Me yasa ya raba ta da abin da kullum yasan se tayi zancen shi, se yake Jin kunyar hada idanun shi da nata.
A ranar akai komai, Wanda Bayan an Gama Mata wankin marar baccin da Bata samu tayi ba ya dauke ta ba tare da ta shirya ba. Shima se lokacin ya samu ya runtsa, a hankali ta Fara dawowa daidai duk da kullum se tayi kuka tare da bashi hakurin bata kula Masa da yaron sa ba, duk lokacin da tayi hakan se yaji Babu dadi cikin zuciyar shi, se yaji kamar bai cika masoyin ta na gaske ba, a Haka yayi deciding fada Mata gaskiya, aikuwa tayi ta kuka, tayi fushi da shi Wanda ya zamana shi ne na farko a zaman su, dukka sun wahala kafin ban Baki da Kuma shishigi da yake Mata yasa ta hakura!
***
Fast forward, na cigaba da rayuwa ta, yadda na dukufa da istigfar da Kuma yin abubuwan da zasu saka na dauna yawan tunani yasa na daina kawo suicidal thoughts cikin zuciya ta, duk lokacin da na tuna ma ai na taba attempting kashe Kai na se na ji kunyar Allah nake ji, gani nake na kasance butulu akan tarin ni'imomin da yayi min.
A gidan mu duka sun shiga hankalin su, tun daga kan iyayena har siblings di na ma. Mamaa wuta ta bude musu sosae, akwai ranar da bana mantawa na karba order mocktail na wasu masu bridal shower, Wanda Suka turo zai karba musu ko kadan bana Jin shi, Dan Haka na fito da 500 di ta Dan a siyo min airtime na Kira shi tunda lokacin event din ya kusa, ban samu ko matazu me Mana wanki ba, kawai se na wuce dakin Mamaa na samu sani a zaune Yana kallo, Ina Shiga ana Gama haska series din, na dube shi na marairaice fuska nace
" Dan Allah Yaya airtime zaka karbo min Dan Allah, kaga maghrib yayi bazan iya fita ba!"
Yayi kamar bai jini ba, na sake narke murya nace
" Kaji Yaya"
Yayi tsaki Yana karbar kudin yace
" Uban me zakiyi da Kati da Daren nan? Kede nasan ba saurayi gare ki ba, yau yadda kike dinnan kamar wata giwa ai sede sugar daddy!"
Wannan abun kawai Mamaa taji, aikuwa ta rufe shi da fada kamar zata Kai Masa hannu,
" Baka da hankali zaka fada Mata Haka, idan sugar daddy ne ma Ina ruwan ka, Kai kayi kanka da zaka tanka halittar wani? Wawa kawai!"
Se Kuma ta dawo Kai na tana tambayar me ya hada ni da shi in the first place, nace
" Kawai tsokana ce Mamaa, ba se kinyi fada ba. Yaya Dan Allah siyo min Mana suna jira na"
Ya wullo min dari
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 18