Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  _BINTUN BATUUL_ 001 _Ayshatuuu_ Top-notch season 3 *Somewhere around the Globe!* 1980s and there about! Tamkar me tafiya akan iska Haka ta fito daga dakin baccin nasu, kamar kiftawar idanu har ta isa wani daki dake can gefe da Wanda ta fito, tana zuwa ta murda door knob din, Wanda a take dakin ya bude, babu haske kasancewar tsakiyar dare ne, Kuma ta san da hannun ta ta kashe wutar, so hakan bai Bata mamaki ba, tana shiga ba tare da ta kunna wutar dakin ba ta karasa gaban gadon inda yaron yake kwance lullube da duvet, ta karasa har kafafun ta na hardewa gaban gadon, ko data yaye duvet din se ta samu Babu kowa a gadon illa pillows da aka jera, yayi kamar yaron ne a kwance, tayi saurin ja da baya tamkar wadda taga wani abu me tsoratar wa, sede hakan ne dai yaron baya Kan gadon da tayi coaxing din shi not long ago, tayi saurin bude wata kofar Dake dakin, tunanin ta ko toilet ya shiga, Amma wayam Babu kowa, abun ya Soma firgita ta, tunanin ta ya Fara Zama gaske, ta fito daga dakin cikin wani yanayi me firgitar wa, sede ko Ina idan ta duba Babu trace ko daya na yaron balle na uban yaro, ta tsugunna a tsakiyar parlon wani kuka Yana kubce mata, ta Fara yin shi Babu kakkautawa, tana Yi tana shesheka kamar zuciyar ta zata fito, wani irin tsoro take ji Yana shigar ta... Kada fa ace sun dauke Mata Babyn ta? Se Kuma ta tuna ai kuka ma ba maslaha bane ba, ya kamata tayi making report ASAP Dan duk inda Imam yake to tabbas baiyi nisa ba, ta Mike zuwa inda wayar gidan ta landline take, ta dialing number cops, cikin mintuna se ga shi an Fara Mata magana cikin harshen larabci, itama cikin harshen larabcin tayi filing complaint din bacewar yaron nata, Suka tambaye ta address nan ma ta fada musu, Suka tabbatar Mata zuwan su ba da jimawa ba! Ko da ta sauke wayar se ta Kuma sakin kuka, abin da Imam ya kulla kenan shiyasa yazo out of nowhere? Dama zuwa yayi ya tafi da yaron shi da ya manta shekara da shekaru? Ta Kara fashewa da kuka lokacin da ta daga idanun ta ta sauke Kan katon hoton shi Dake manne jikin bangon parlon, yaro ne kyakyawa, yayi kiba irin ta yaran da suke samun kulawa, ya daga hannun shi guda Yana sakin dariya, bakin  babu hakori ko daya amma dukda Haka idan ka kalla hoton zaka samu Kan ka da yin dariya ko Kuma murmushi! Har anan a durkushe cops suka same ta, bayan ta zauna sun Dan Yi bincike cikin gidan suka tabbatar da Babu shi fa yaron se Suka dawo Dan daukar statement din ta! Da farko dai ita din Yar Qatar ce, sunan ta Zainab, iyayen ta sun kasance musulmai Kuma larabawa kamar yadda muka San asalin Qatars! Ita din ma wanke hannu ka taba ce, kyakyawa Fara balarabiya, mahaifiyar ta ta rasu tun tana yarinya Kuma ta kasance ya daya tilo a wajen su, mahaifim ta shima ya rasu bayan ma ta Gama O level din ta. Ma'aikaci ne  a wani babban company cikin kasar, ranar da rasuwar tashi ta kasance,  Zainab ta fada Masa tana son cin abincin dare tare da shi, hakan yasa yayi ta kokarin kammalla aikin office dan cika Mata alkawari Amma aiki se ya Sha Kan shi, ya kasa fitowa sallar maghrib,  se a office yayi, ita Kuma tun da yace ta zaba masu top restaurant, ta riga da ta isa wajen har ta bada order kafin mahaifin nata ya karaso, a banagaren shi ya kammalla komai ya Mike tare da daukar wasu takaddu Dan zuwa ya samu tilon diyar tashi, Amma yana zuwa kofar da zai bude ya fita se kawai ya yanke jikin shi ya fadi, daga wannan faduwar bai sake shurawa ba Rai yayi halin shi! Shiru shiru har karfe Tara da wani abu Zainab na jiran mahaifin ta amma bai dawo ba, a lokacin ta tabbatar Babu lafiya, Dan Haka ta Mike ta fice zuwa wani nearby phone booth, ta Kira number office din shi sede Babu Wanda ya dauka, hakan ya sake tayar mata da hankali, kawai se ta kashe wayar ta nufi office din shi a mota, tana zuwa an fito da shi daga main building din company din akan stretcher, ga ma'aikatan da Basu tafi ba dukka suna alhinin abin da ya faru da Mr. Fahad!                               *** "Bintu! Bintu!!" Na Dan mikar da hannu na tare da kwankwasa kofar bayin Wai dan na fada musu Ina toilet, Amma hakan da nayi se ji nayi " Ke Bintu wai dama tuntuni kina toilet? Kina ji Ina ta babatu akan ki, to Mamaa ke Kiran ki se ki fito" Ban ce komai ba, na cigaba da abin da nake, ni nasan ko Ina nake zaayi min uzuri tunda a toilet nake, seda na kammalla na fito na tarar dakin Babu kowa sannan na fita zuwa dakin Mamaa, tana zaune saman gado ta baza atamfofi Wanda take siyarwa, inaga tana sorting din su according to kudin su ne. Nayi sallama a hankali na shiga, ba tare da ta dago ba tace " Bintu Ina kike tuntuni nake neman ki?" Nace " Mamaa Ina toilet!" Ta dago ta kalle ni na Dan lokaci kafin tace " Suleiman na parlor, ki gyara shigar ki kije ki Kai musu ruwa!" Nayi shiru Ina kallon Mamaa, Ina Kuma son tabbatar da abin da take fada, ya zanyi Wai nayi hakan? Ya zaayi Rana tsaka ace wai na Fara soyayya da Suleiman? Ya ma zaayi Haka? " Baki ji abin da nace ba ne ba?" Ta fada muryar ta na Dan dagawa, ban ce komai ba na juya a hankali na koma dakin da na fito daga ciki! Na tsaya gaban mirror Ina kallon Kai na, wani boubou style material ne a jiki na, color din shi me duhu ne Wanda ya sake saka fata ta tayi duhu, fuska ta duk kuraje ne saman ta wanda tun da na Kai puberty nake fama dasu, ni ko kadan bani cikin sahun Mata masu kyau, shiyasa nake da low self-esteem, bana son shiga cikin mutane ko kadan, bani da confidence, a kusan komai na rayuwa ni ce karshe. Ba tare da nayi adjusting shigar tawa ba, na dakko katon hijab na kima akan boubou din, Wanda ya sake fito da kibar da nake da ita, ban ko damu ba na nufi kofa Dan fita, se mukai kicibis da Batuul Dake kokarin shigowa, nasan an turo ta taga me nake har yanzun ban fito ba, ta kalle ni tana bude Baki in exclamation " Bintu! Ba dai a Haka Zaki je wajen shi ba? Kin ganki kuwa?" Na kalle ta Ina Kara Shan kunu, Amma cikin zuciya ta da jiki na tamkar an sassare min gwiwa Haka naji, " Ki koma ki danyi touching fuskar ki, ki canja Kaya. Amma wannan ai se yaga kamar..." Kafin ta karasa na bude Baki na nace " Se yaga kamar me? Kamar giwa? Ko kamar bull?" Se tayi shiru ta kasa fadin komai, ganin har idanu na sun Fara cikowa da kwalla, na gyada Kai in annoyance na bi gefen ta na wuce, wani irin radadi nake ji cikin zuciya ta, Wanda ba lallai wani ya fahimci yadda nake ji ba, ko da naje kitchen se da na danyi kuka kafin na samu zuciya ta ta huce! "Wai Kai Suleiman zaman me muke har yanzun anan?" Wannan shi ne abin da na Fara jiyowa lokacin da na nufi parlon, na ja na tsaya Ina kokarin daidai ta yanayi na kafin na shiga "Nima dai abin da na gani kenan, since ba zasu baka Batuul ba, to me kake jira" Dan kada su Fadi wani abun yasa nayi saurin summoning courage na shiga, da sallama a Baki na, dukkan su Suka dago idanu Suka zuba min Wanda yasa naji kamar na koma da baya, Amma Babu yadda zanyi na riga da na shiga. Na aje tray din hannu na sannan cikin rashin kuzari da kasa da murya na gaishe su, Suka amsa Amma ko kadan na kasa daga idanu na na kalle su, saboda gani nake dukkan su suna iya hango munin fuskata! Shiru na wajen mintina hudu kafin na Mike na dubi Suleiman a Karo na farko tun shigowa ta wajen, Sanye yake da men lace coffee da zare milk, Kan shi da hula wadda ta Kara fito da shigar ta shi, na Dan Yi ajiyar zuciya nace " Allah ya kiyaye hanya!" Ba tare da na jira sun amsa ba na Kama hanya ta Dan komawa daki, sede Ina barin wajen naji daya daga ciki yace " Sule! Wai wannan golf din zaka aura?" Yadda yake dariya, yadda dariyar take shiga kunnuwa na tana sauka a zuciya ta tare da piercing zuciyar, ba Wai nayi niyyar tsayawa bane ba, kawai dai kafafu na ne Suka tsaya Dan Kan su, "Ba kada kirki Fahad, Wai golf?!" Shima dariyar shakiyancin yake irin ta abokin shi, wannan karon se naji zuciya ta tamkar yayyaga ta ake in pieces, kafin a Kara fadin abin da zanyi shekaru Yana hunting zuciya ta, Naga gwara naja kafafu na kawai na tafi. Aikuwa Ina zuwa daki na fada gado Ina sakin kuka.... Taku har kullum Ayshatuuu Shin kina da labarin wannan karon ma tafiyar ta top-notch ce? Season 3 ake magana na shatuuu, me dambu da Kuma Aziza! Me kike jira 'yar uwa? N1300 kacal Zaki mallaki NAZNEEN, BINTUN BATUUL  da Kuma GEN. NASIR ZAKI! [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Top-notch season 3 Ayshatuuu 003 Ban Kara sanin me yake faruwa ba, ko waye a kaina ba, I loss consciousness abin da ban taba Yi ba a rayuwar, gaba daya ajin har shi Dr Akram din Suka taho Kai na, gashi Ni kadai ce mace duk ajin, tun a shekarar farkon mu wasu suka canja department, wasu aka tilasta musu, a Haka nayi surviving ni daya, dama bamu da yawa da muka fara, dukkan mu matan mu shida ne kawai. Yana karasowa inda nake kwance, Wanda suke kusa dani a zaune, already sun baibaye ni, Yana zuwa Babu hesitation kawai ya taba fuskata da hannuwa na, gumin ya daina se sanyi da jiki na yayi kamar mataciyya, flashlight din wayar shi yasa ya haska kwayar idanu na, ganin ta yi dilating, wato ta Kara budewa ya saki ajiyar zuciya, tare da kallon sauran Yan class yace " Who's the class president?" Alamin ya daga hannun shi, cikin sauri ya wulla Masa key din motar shi ya fada Masa model din ta sannan yace " Idan ka bude ta, a backseat akwai wata bakar jaka, in 30 seconds nake so ka kawo min" A guje ya fita, Ema ya bi bayan shi, Basu Sha wahala ba se gashi Ema ya dawo da Jakar shi Kuma Alamin ya tsaya locking motar, wata na'ura Yar karama ya Ciro, ya zura wani strip a ciki, sannan yasa allura ya caka hannu na, a take jini ya bayyana, ya disa a strip din sannan ya jira har na'urar tayi reading, kowa se kallon shi yake in amazement, kadan ne Suka fahimci abin da yake yi, Wanda ko ni da idanu na biyu bana tunanin Zan gane me akeyi. " 1.8?!" Ya fada bayan numbers din sun watso a jikin screen din na'urar, fadar da yayi kamar me tambaya kamar me mamaki, suna tsaye ya saka min ruwa Wanda kafin 50mls su Shiga jiki na, na Fara kokarin bude idanu na, tare da kokarin tashi na zauna amma ya dakatar dani ta hanyar fadin " Be calming down! Ki Kara hutawa!" Ya fada Yana mikewa tare da komawa gaban podium, Wanda hakan ya tilasta ma sauran colleagues di na komawa wajen su. Cikin kwarewa da iya koyarwa ya cigaba da exploring din mu cikin course din, yana bayani Yana rubutawa akan farin allon Dake gaban shi, Sanin jiki na ba shi da kwarin da Zan iya rubutu se kawai na kunna recorder din waya ta dan ta nadar min bayanai. Bayan kamar awa ruwan da yake Shiga jiki na ya kare, kafin nayi Masa magana yazo ya cire min, Bai Kara minti na talatin ba ya Mana sallama ya fice! " Bintu azumi kike Yi?" Alamin ya tambaye ni, na girgiza Kai na nace " Ko daya! Abinci ne ban ci ba" Ya Bata Rai tare da tambayar " Me yasa? Me Zaki ci?" Nayi murmushi Ina gyara Zama na nace " Kawai bana Jin cin komai ne!" Yayi shiru Yana kallo na na Dan lokaci, Wanda yasa na takura nace " Alamin!" Yayi murmushi tare da mikewa ya fita, se ya zamana ni daya kawai na rage a cikin ajin. Nayi shiru deep in thought Ina ayyana dalilin halin da na Shiga dazun, ni dai a rayuwa ta ban taba Suma ba, ban taba fita a hayyaci na but what happened? Se Kuma na Zama curious akan lecturer da ya fita, waye shi? Is he a Doctor and an architect a lokaci daya? Kai hakan ba Mai yiwuwa bane ba... Shigowar Alamin tasa nayi snapping daga tunanin da nake, in da ya tashi nan ya koma ya zauna tare da aje ledar hannun shi a gaba na, " Nasan abinci ne Baki ci ba, Haka Dr Akram yace, Wai glucose din jikin ki ne yayi dropping!" Na kwalalo manyan idanu na waje nace " Likita ne? Amma me yasa yake koyar da mu?" Yayi dariya Yana bude min ledar da ya kawo, alala ce se coke me sanyi "Ko daya, kawai dai yasan abunne, PhD yake yanzun shiyasa Kika ji Dr Akram!' Na gyada Kai tare da Yi Masa godiya, ya tashi ya tafi Dan bari na naci abinci, na bude Coke din na Kai Baki na Ina ayyana to yaushe ne Zan rage kibar, gashi Ina son Fara slimming Kuma Haka kawai na Fara suma. A gajiye na fito daga faculty din mu, ni daya kamar kullum, na duba screen din wayata, biyar ta wuce sosae hakan yasa na hanzarta Fara tafiya Dan wucewa gida. Waya ta ta Fara ringing, na Dan dakata a gefen hanya, na dauka kiran " Maman Anum Ina wuni?" Daga dayan barin tace " Lafiya Lau Bintu, kin tashi a school?" Nasan wani aikin zata saka ni, nace " Eh yanzun nake fitowa!" "Yawwa, kinaji ki biya school din su Anum ki dakko su, ki wuce gida da su. Zan biyo na dauke su!" Na Kara Jin wata gajiya ta sakko min Amma Babu yadda Zan Yi nace " To!" Ban jira abin da zata ce min ba kawai na kashe wayar, Babu yadda zanyi Haka na tari me napep ya Kai ni school din yaran, kusan su kadai suka rage baa dauke su ba, suna gani na Ahlam yace " Ina Mama? Me yasa Kika zo?' Ko kula shi banyi ba, nayi signing sannan na dube su nace " Baku iya gaisuwa ba ko?" Anum ta gaishe ni Amma Ahlam se Bata fuska yake, na tafi da su gida, Muna Shiga suka wuce wajen Mamaa ni Kuma na wuce daki na. Ban Kara saka su a idanu na na se da naji muryar Maman su a parlor, na fito Ina sanye da hijab, tana zaune da su Mamaa har da Adda ma, yaran duk sun baibaye ta, daga shigar Dake jikin ta ya tabbatar min biki taje, na zauna na gaishe ta Amma maimakon ta amsa se ta Fara fadin " Dan Allah Bintu yaran nan kiga ko Kaya baa canja musu ba, haba Bintu ke kuwa!" Na kallo yaran sannan na kalle ta Amma bance uffan ba, maimakon tayi min godiya Akan wahalar dakko su day nayi, shi ne tazo take korafi, to Haka kusan dukka Yan gidan mu suke, in dai aikin wahala ne to Ni zasu saka, Amma babu godiya da Kuma zarar an Dan kuskure shikenan se korafi. Adda da se lokacin tayi magana tace " Suleiman zai zo anjima ki shirya!' Na kalle ta Ina marairaice fuska nace " Ayya Adda wallahi na gaji, banyi karatu ba yau dukka, Kuma na karba order shawarma. Beside Ni gaskiya bana son shi" Maman Anum ta dube ni tace " Ban gane Baki son shi ba, ke har option ne dake dama?" Se na kalle ta da rashin fahimtar abin da take fada, nace " Kowa ai Yana da option din ya kawo Wanda yake so, ni me yasa ake denying min wannan right din?" "Tun da kike waye ya taba zuwa gidannan da sunan Yana son ki?..." Kafin ta karasa kawai se na Mike Dan komawa daki, bansan meye amfanin Adda ba Dake wajen, na rasa gane dalilin da yasa iyayen mu ke kasa depending din mu irin wannan. Ko Dana koma daki se naji na Kara tsanar Kai na da rayuwa ta, na duba mudubi Wanda a kullum nakan kalli Kai na kamar sau goma Naga ta inda Zan Fara rage wannan fat din Dake jiki na, kilan shi ne dalilin da yasa kowa baya so na, shi yasa kowa yake kallo na kamar wata kasakantaciyya. Har karfe biyu na dare idanu na Basu runtsa ba, Ina zaune saman gado na wayata a hannu na Ina duba online methods na rage kiba,  da farko Naga akwai dieting, akwai pills akwai Kuma tea, na kudiri aniyar da gaske wannan karon ko zam mutu se na rame, no matter what! Na zata abun me sauki ne, na zata idan na rame na Zama Yar caras Zan tsira daga bakin mutane, Ashe ko Mai kayi ba zaka taba tsira daga bakin mutane ba, ba zaka taba burge su ba Kuma ba zasu fasa magana ba! To be continued... Top-notch season 3! Kun Yi subscribing kuwa? Ko har yanzun? To ku tuntube mu ta wannan number 09063467258 [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Top-notch season 3 Ayshatuuu 002 Na Jima akan gadon Ina Jin amsa kuwwar Kira na da golf da abokin shi yayi, me yasa mutane suke min haka? Why am I being criticized akan abin da bani da power Akan shi? Shigowar Batuul yasa na dawo daga tunanin da nake, ta zauna gefe na tana bi na da kallo, Batuul kyakyawa ce, kamar ta daya da Adda akasin ni da zakuyi mistaken dina for Yar riko. "Bintu ya kikai da Suleiman?" Ta tambaya tana bani dukkan attention din ta, na kalle ta da kyau amma bance Mata komai ba, " Matsala ta Dake kenan, Ina Miki magana kiyi min banza!" "Ki Kira shi ki tambaye shi Mana!" Na fada Ina kokarin janyo handouts dita ta intro to landscape design, tana ganin Haka tayi saurin dauke shi saboda tafi kusa da bedside table din akai na, haushi ya Kama ni Akan Wanda already nake ji " Ai nasan da shi nake tambayar ki, Kinga Bintu kowa na kokari akan ki, duk abin da ake yi Dan ke akeyi..." Na daga Mata hannu Ina fadin " Batuul Dan Allah ki tafi, ki rabu da ni, ki kyale ni" Ina fadin Haka na warci handout din da ke hannun ta na bude na Fara karantawa, wani Abu Dani inada determination, idan na dage akan Abu mussamman karatu, to zaku ga nasara ta same ni cikin hukuncin Allah! Asali bani da kokari ko kadan, I'm always last a ajin mu, saboda yadda suke min akan rashin kokarin hakan yasa na dage na Kuma daura damara, se gashi nayi succeeding, dukda hakan Bai saka anyi acknowledging di na da kyau ba. Ba Wanda ya sake bi ta Kai na, se bayan maghrib, na idar da sallah na wuce kitchen Dan zuba abinci, rabo na da na ci tun breakfast din safe, anan mukai kicibis da Adda, ban masan ta dawo ba. Na gaishe ta Ina fadin " Adda sannu da zuwa!" "Yawwa Bintu, tun dazun kina Ina?" Na gyara tsayuwa ta Ina karbar yoghurt din hannun ta nace " Ina daki!" Aikuwa se ta Fara sababi " Ke kam kullum kina daki? Baki da gurin Zama se daki? Wai ke wacce irin yarinya ce?" Nayi shiru Ina tunanin to menene laifi na anan? Yawo ake so na tafi ko mene? " Karatu nake Adda! Kiyi hakuri" Na fada Ina Ciro Mata tumbler daga inda ake adana su, ta amsa ba tace min komai ba tayi ficewar ta. Ban koma ta kanta ba na zuba abinci dai dai yadda zai ishe ni cikin plate, Amma kafin na dakko spoon town crier gidan, wato Batula Fatima Hamisu Ginsau ta Fara kwala min Kira "Bintu Fatima Hamisu Ginsau!" Na aje plate din hannu na Ina kokarin fitowa, Alawiyya me Mana aiki ta shigo tana fadin "Wani yazo karbar cake a waje uwar daki na!" Tana daya daga cikin Wanda ban hada komai da su na jini ba, Amma suna mutunta ni. " Wayyo na manta, Kuma tun dazun ya Kira ni! Bari na Baki Dan Allah ki Mika Masa!" Ta amsa ni da to, ni Kuma na wuce nayi packaging eight inches fondant cake, se da ta fita kafin na tafi Kiran da ake yimin. A parlon Adda na same su dukka, na gaishe su sannan na zauna bayan Mamaa tace min na zauna " Ya kukai da Suleiman?" Kuma Kan ku nasan Kun gaji da karanta sunan Suleiman dinnan, balle ni Kuma da ake tambaya, for God sake magana Bata karewa a gidan nan ko menene? " Wanne tambaya kike Mata haka Mamaa? Bayan shi Suleiman ya riga da ya fada Mana abin da tayi Masa!" Adda ta fada kamar zata Kai min duka, na sunkuyar da Kai na, Ina ayyana ko wanne irin sharri yayi min a wajen su? Allah masani " Duk abin da ake yi ba Dan ke akeyi ba, ba kokari ake aga yadda kuka tashi tare da Batuul ba tayi aure ta barki ba, shi ne Zaki musu rashin arzikin naki ko?" Nanma bance uffan ba, hakan ya Kara hasala ta, ta cigaba da yimin

Chapter 1 of 18