babban palourn nasu. Waya ta ciro a jaka tai dialing number, kashewa akayi ko da qiran ya shiga. Ganin an kashe Murmusawa tayi Abeeyh rigima har gobe bazaka dinga ɗaukan qira na ba sai dai a kashe a qirani, bata gama idasa tunanin da take ba call en nasa ya shigo da murmushi ta ɗauka ta sa a kunnen ta. "Assalamualaikum wa Rahmatullahi wa Barkatuhu ranka ya daɗe ɗan fulani"ta faɗa fuskanta shumfiɗe da qayataccen murmushi mai taɓa ran duk mai kallo da saurara!! Bayan ta saurari amsar da aka bata a ɗayan ɓangaren cewa tayi "Abeeyh gani a gida kam ni ɗaya ba kai ba yara gidan har storo yake ban, saurara wa tayi tana sauraron abinda ake faɗi a ɗaya ɓangaren, sa wayan tai a handsfree ta ajiye a hanun kujeran da take zaune kai tana warware ɗan kwalin kanta. "Hajiya ta da girmanki gida ya baki storo Autan naki bai dawo bane?" Faɗin Abeeyh. Abeeyh ina Auta ya dawo da na gansa ai da sauqi, kuma ma wanne girma ne garen? Murmusawa akayi a ɗaya ɓangaren yace "Tom Hajiya ta a samu a huta ko we'll talk later". Tom ranka ya daɗe mijin Hajiya sai naji ka ko Allah taimaka ayi aiki lafiya, Abbeyh yace a ɗayan ɓangaren "au wai mijin Hajiya ko hhhh wata ta jiyoki ki kasheman kasuwa afasa aurena ni da ke ne." Byee ranka ya daɗe mijin mata huɗu, ta faɗa ta kaste wayan tana dariya! Miqewa tayi ta shige bedroom.
Bayan ta shige bedroom toilet direct ta wuce ta wasta ruwa ta fito. Zaunawa tayi bakin dressing mirrow ta janyo wayanta tayi dialing layin da akayi saving da habeebi Auta akai, sanya wayan tayi a handsfree ta ɗaura akan mirrow desk en jin layin na tafiya. "Hello Ummeyh ta" abinda aka faɗa a wayan wanda ke nuni da wanda ta qira ya ɗauka. Habeebin Ummeyhn da ya akayi? Ya kuke? Ya gida ya gajiyanka? Shagwaɓe fuska yayi kaman yana gabanta "Ummeyh ta kowa lafiya sai nine ban da laafiyah". Da yanayin damuwa tace "Habeebee me ya sameka?" Cewa yayi a ɗaya ɓangaren "Ummeyh gajiya kuma inaso na ganki" ajiyan zuciya ta sauqe! ta ɗan murmusa habeebin Ummeyh soon Ina zuwa ko tunda kaikam kaqi biyowa kawuce gida direct abun ka, yanzu ma qannen ka suna hanya duk inda suke insha Allahu nasan jirgin su ya kusa landing ka qoqarta ka ɗauko su ba dan halin su ba. Shikkenan Ummeyh ta Allah iso dasu lafiya kema yaushe zaki zo? Habeebin Ummeyh surprise zan maku amma nakusa kaji, yace "Tom Allah kaimu ya kawoki kema lafiya Ummeyh ba na tashi na shirya kamun su iso byeee Ummeyh ta" ya kashe wayan. Cigaba da shafa mai Ummeyh tayi ta tashi ta saka dogon riga dai-dai mara nauyi tabi lafiyan gado ta kwanta cike da kewan yaran nata da kuma mijin nata....
---------
A Nigeria kuwa bayan soja ya gama waya da Ummeyh har zai bi gado ya kwanta sai ya tuna ba marar kunyan bace kaɗai zatazo har da mutumiyar sa Mahreen. Dira yayi a kan gadon ya shige toilet, a gaggauce ya wasta ruwa ya fito ɗaure da towel ɗaya ɗayan kuwa yana qoge suman kan sa. Shiryawa yayi cikin qananun kaya army t-shirt da jeans, fesa turare yayi. Sanda ya qarewa kansa kallo a mirrow kamun ya fice a ɗakin ya ja qofan side nasa ya kulle kamun ya qaraso cikin main palourn nasu, bai tarar da kowa ba a palourn shiru har ya juya zai fice yaji muryan mai aikin nasu na cewa "adawo lafiya Autan Umma" amsawa yayi har zai wuce da ya tuna dai ba marar kunyan bace kaɗai kar su iso ba abun ci sai ya juya ya mata magana "yauwá mama nace ba a ɗan tanada abinci mana Umma nada baqi daga jidda, mai aikin tace "ba dai su mai sunan amarya ba?" Eh mama sune amma kar afaɗawa Umma in ta tambayi ko Kinga fitana kice mata eh naje anguwa. Shikkenan Autan Umma adawo lafiya Insha Allahu zan tanadar masu dan mai sunan Amarya mutumiya ta ce, taɓe baki yayi yace "shikkenan sai mun dawo" ya faɗa yana ficewa a palourn.
A tsakar gidan ya hangi Little na ball da wani soja, har ya juya zai yi hanyan parking lot sai yaji muryan Little en "unkui where are you going?" Big bruh anguwa zani kayi ball naka okay. Da gudu ya bar Ball en yazo ya riqe qafan sa yace "nidai a'a unkui anbika anguwa anfaca baii en". Murmushi soja yayi yace "shikkenan let's go bruh" wajan motor suka wuce suka shiga, key yawa motorn mai gadi ya walgale gate en da gudu yafice a gidan suka yi hanyan KADUNA STATE AIRPORT.
Isar su airport yayi dai-dai da lokacin da jirgin da ya taso daga jidda yayi landing, bayan wasu mintuna mutanen da ke jirgin ne suka fara futowa. Yana zaune daga cikin motorn Yana kallon mutanen dake fitowa a jirgin carabb idonsa ya sauqa a kanta tana sauqowa a jirgin, gyalen rigan jikinta iska ya ɗauke wanda hakan ya bawa gashin kanta kwantacce dogo baqi daman bayyana, siririn tsaki yaja ya fito a motorn yana faɗin "yarinya sai rawan kai". Hango mutumiyar sa da rolling tana sauqowa a nuste ya sanya shi ɗan murmusa wa! Idonsu ne ya haɗu bayan ta ɗauko gyalen nata ta qara yafawa da murmushi ta yo wajansa tana qoqarin rungumesa ya dakatar da ita "ke malama tsaya, bayan kingama tallata wa duniya cinyayyen kan naki ne kikeso kuma ki taɓani ace wai Nima banda hankali irin ke? Tom ki nistu, tunda ke ko a cikin jama'a sai kin raba halinki."
Murguɗa baki tayi ta kuma yin qwafa, da alama ranta bai yi daɗi ba! kai kuma ba'a maka gwaninta.
Wucewa tayi Inda yai parking motor ta buɗe gidan gaba ta shiga.
Mahar ce ta qaraso da murmushi! Afuwan mun sanya ya soja jiranmu, kallon ta yayi Au kema sojan zakice ko? murmusawa tayi tana kama kunne noo ya habeeby. Wajan Motorn suka nufa, Hajiya Maha na ankame a gaba haka Mahreen ta buɗe back seat ta shige shikuma ya shiga mazaunin driver yaja Motorn suka nufi hanyan gida. Mahreen da ke zaune a baya ce tace "ya habeeby ɗan wa ka samo? Kyakkyawa kaman ni haka". Dariya Maha da ke gaban Motor ta sanya, wai yanzu har zaki ce kyakkyawa kaman ke yaya Mahreen kyau ne dake? Kallon da habeeb ya aika mata dashi shi ya hanata qarisa sauran maganan ta juyar da kai tana magana qasa-qasa.. Mahreen ce tace "ya habeeby ɗan waye?" Yanzu zakiceman baki gane Little ba Reeyhn? Zaro ido Mahreen tayi tana ɗaga Little da ke shan baccin sa cikin kwanciyar hankali tace "don't tell me yaron Adda Ameera ne wannan ya habeeby?" so now anyi mumyn zamani tunda dai baki gane ɗan ki ba. "A'a fa ya habeeby kasan dai rabon mu da Nigeria tun Auren Adda Ameera bamuzo ba da ta haihu a waya kawai nake kallon sa, yanzu dai wannan kyakkyawan saurayin yaronmu ne wow ya habeeby soon zamu zama surukai" Mahreen tafaɗa tana murmushi ganin Little ya buɗe ido. Little ne yace "unkui my head" kwantar da shi Mahreen tayi a jikinta sai yaqi yasa kuka ya miqawa unkui habeeb hanu, big bruh Ina driving ne zaka zauna jikina what's wrong with you? Juyowa Maha tayi ta miqa masa hannu tana murmushi, ba ko gardama ya yarda ta ɗauke sa, lallashin sa tayi yai shiru ya qanqame ta kaman itace maman sa. Kallon su habeeb yayi yace "hali yazo ɗaya dole aso juna ai" Maha murguɗa baki tayi batace komai ba, motorn shiru ba qaran komai sai na AC dake tashi.
Suna isa gida Maha ko tsayawa a gyara parking batayi ba, little en ma ko tsayawa ɗaukan sa batayi ba da gudu tayi cikin gidan tana "ayoyo ummata ayoyo ummata ayoyoo ummata".
Kaman daga sama haka umma taji muryan Maha, aikam Mahan ce dan tana shigowa palourn jikin Umma ta faɗa. "Ikon Allah ashe kuna hanya doter, ayoyo sannun ku gajiya ko" ta faɗa tana rungume Maha. Maha tace "Umma i miss you wallahi" miss you more doter yanzu kam ba gaki ga Umman ki ba ƴar kirki. shigowan soja da Mahreen ne da Little da ke kukan Maha ta tafi ta barsa ya sa Umma ɗago kai tana washe baki tace "Lale marhabun da yaran kirki" Mahreen tazo ta rungume umman tasu itama. Maha jawo little tayi ta lallaɓa sa tayi shiru, Kallon habeeb Umma tayi "wai dama Auta kasan ƴaran nan na hanya baka faɗa mun ba Gwaggon ku ma bata sanar da ni ba, na tambayi mama wai kace mata kaje anguwa, yanzu kai zaka nemo masu abinda zasuci a take kamun adafa ko?" sosa qeya yayi Umma nima fa bansan suna hanya ba kuma ai mama ta dafa masu abinci.
Mama mai aiki ce ta shigo palourn da sallama riqe da tire a hanunta mai ɗauke da abun sha da kulolin abinci, kallon ta Umma tayi "wai mama kinsan da zuwan su ne kema tunda naga har da abinci" murmushi mama tayi tace "Hajiya ai mana afuwa ni da soja fitan sa nagani yace zaije ɗauko su shine nai sauri haɗawa ƴan ɗakina abin taɓa wa nasan tafiyan hanya akwai sa yunwa" Umma Murmusawa tayi "au wai Ni kawai kuka wa surprise shikkenan ai sannun da aiki mama, Auta sannu da gajiya, yaran Umma sannunku da zuwa sauqo kusha ruwa ko" ta faɗa tana kallon Maha da Mahreen. Sauqo wa suka yi dan shan ruwan, mama ta masu sannu da hanya, da murmushi duka suka amsa barin ma Maha dan mutumiyar mama ce sosai.
Habeeb yace "Umma ba na shiga ciki nikam yau Little yaga mai irin halin sa yaqi ni" Umma ta kallesa zaka fara ko? Tura baki Maha tayi, hararan ta habeeb yayi ya nufa hanyan sashen sa, bin bayan sa Maha tayi da harara. Kallon su duka Umma tayi ta girgiza kai kawai cewa take a ranta "Allah shirya mun ku ya nunan randa zaku zauna lafiya".
---------
Amjad ya koma gida lafiya. Kaman koda yaushe sunci abinci tare da iyayen nasa da fara'a da dariya suna hiran su, inka gansu ba zakace iyaye da ɗan su bane.
(Ba kaman wasu iyayen namu ba a yanzu, in baka ja ɗan ka jiki ba wa zai ja maka? Mu gyara iyaye).
Umma ke stokanan sa "wato jarumin umma don anfara jin qamshin surkata shine aka kwana har biyu ajeji ba'a yi kewan Umma ba ko?" Ɓata fuska yayi yace "Allah Umma nayi kewan ki fa Kuma ni ba wacce zata sa na mance da Umma ta, Nifa Umma zakisa ma nafasa abun nan ma"( dukda aransa yarasa dalili yaji yanason yin gasan dan kansa
Amma yabar hakan wa son sauqe mata girman kan da takeji dashi na ba wanda ya isa yabuɗe mata fuska).
Umma tace "ah ah yi haquri jarumin ummansa baza'a yi haka ba ma kaji. Abba dai yana kallon su yana murmushi amma bai ce komai ba, A haka suka cigaba da hiran dukansu na dariya Amjad ya murmusa!
Dare yayi lokacin kwanciya kaman yacce suka saba kullum haka suka yi har ɗakin sa iyayen nasa suka rakasa Umma ta masa addu'a suka ka masa bargo suka yi sai da safe suka fito suka nufi nasu ɗakin. Bayan sun shiga nasu ɗakin alwala suka ɗauro suka fara nafila da niyan Allah ya bawa yaron nasu nasara in hakan alkhaeryh ne gare sa..
Amjad a ɗakin sa bayan fitan iyayen nasa juyi kawai yake yi ya kasa bacci, shi dai yasan baida damuwa da abunda zasu yi goben, amma yarasa mai yahana sa bacci, ya juya haka ya juya haka har dai ɓarawon bacci ya sace shi.
MASARAUTA
A can gidan Sarki kuwa gimbiya tayi-tayi duk iya yin ta amma ina mai martaba yaqi fahimtar ta ya dage dole aurenta nan da wata 4 huɗu, gashi gobe ne gasan da za'a kuma yi Insha Allahu. Gaba ɗaya ta rasa mai ke mata daɗi, amma duk da haka dai ta saka aranta Insha allahu basu isa suyi galaba a kanta ba
*WASHE GARI RANAR GUDANAR DA GASA**
Babban filin da ya kasance na gudanar da bukukuwan wannan masarauta, a cike yake fam da jama'a. Baqi da ƴan gari sun hallara a wannan babban fili mutane ne a cike ba masaka stinke, ganin yawansu zai sanya ka tsammanin ba kowa da ya rage a wannan Masarauta, saboda irin tarin jama'a dake wannan fili.
Manyan baqi da ya kunshi Sarakunan garuruwan da suke makwaɓtaka, manyan mutane daga qasashe daban daban sun samu daman hallattan wannan gasan kasancewar yacce Sarki ya furta na ko daga ina kake zaka iya shiga gasan sai hakan ya bawa labarin wannan gasan zagayawa har garuruwa da dama wanda ba'a tsammani ciki kuwa har da Nigeria, baqi ta ko ina anzo dan kuwa kusan zuciyoyin kowa cike yake da ɗimbin mamakin qarfi irin na wannan ƳAR SARKI...
Mai martaba kaman ko da yaushe yana wajan da yake tanade dan zamansa tare da fadawan sa in ana gudanar da wani shagali a garin nasa, baqi kowa na zaune inda aka tanadar dan baqi manya da sauransu. Gefe guda kuwa GIMBIYA MEHWISH ne zaune a kujeran da aka tanada domin ita, kuyangun ta ne zagaye da ita da sauran bayi maza.
Sanye take da kaya blue wanda colourn ya tafi da yanayin halittan qwayar idon ta, kayan riga da wando ne, wandon ya kasance mai ɗan faɗi wanda ba'a ganin yanayin jikinta hakama rigan bai kama ta ba sai dai ɗamaran da ta ɗaura a qugun ta wanda ya ɗan bayyanar da shape enta, ta rufe fuskan ta da baqin veil kaman koda yaushe ba abinda kake gani sai qwayan idon ta wanda yakan burge duk wani mai kallon ta. Irin shiga da haɗuwan da Gimbiya tayi da kyawun da wannan shiga ya mata, indai kana Kallonta tom kallonta kaɗai ya isa ya hanaka nasara akanta don haɗuwa kam Masha Allah!!
Gefen waɗanda za'a gwabza dasu kuwa Anwar ne a zaune tare da muqarraban sa, shiri yayi irin na masu zuwa yaqi, sosai dai shirin ya masa kyau ya amshe sa. Qaqqarfan namijine wanda kana ganin sa kaga jarumi na gaske, shi kaɗai ne zaune a gefen masu gwabzawan da dukkan alamu ɗayan bai iso ba tukunna.
Mai magana ne yake jawabi da kuma mawa manyan baqi Barka da halartar wannan taro dan wasu ba'a ma taɓa tsammanin ganin su ba. Sarkin shela na tsaka da yin magana yaji wajan yayi shiru juyawan da zai yi wani kyakkyawan mutum kuma qaqqarfa ne yake shigowa cikin taron, shigowan nasa ne ya ɗau hankalin jama'a har ya sanya kowa kusan barin zancen da yake .
Tafiya yake cikin taqama da kuma nuna stantsar Jarumta, wani bafade ne yai masa jagora har wajan zaman da yake aka tanada dan shi, zaman sa ne ya baiwa mutane daman gane cewa shine ɗayan abokin gwabzawan Gimbiya, nan take waje ya ɗau surutu qasa qasa kowa da abinda yake cewa.
Sanye take da kaya mara hayaniya zaka ranste ba dashi za'a gwabza ba, (dan ko shirin sa na zuwa jeji yafi wannan) sai dai shigen nasa yayi bala'in masa kyau Kasancewan sa fari kuma dogo sannan qaqqarfan jarumin na miji.
Siririn tsaki yaja ganin yacce duk akabi aka zuba masa na mujiyoyi(idanuwa) sosai ya tsani yawan kallo ga qananun surutun dake tashi a wajan, wanda baya da ko shakka gulman sa mutane keyi, tsakin ya kuma ja yana magana a zuciyansa "Ni wallahi Umma ba don ke ba banayin wannan wasan yaran, yanzu gashi sai qareman kallo ake ana gulma na in aka cinye maki Ni shikkenan kin huta ai" stakin ya kuma ka yana qara murtuqe fuskan sa, dan karma a raina sa gashi wai zai yi gasa da mace qanwar bayan sa kayan reni "gaskiya Ni Umma baki kyauta mun ba" ya faɗa yana tura baki kaman yana gaban Umman tasa..
Dayawan mutane a wajan kallonsu ya koma kan Amjad, sakamakon ba kowa ne ya san sa ba, ko karatu ba'a garin yayi ba in ba dai kana shiga kasuwa da Sa'a ba tom sannan ne zaka iya cewa ka taɓa ganin sa, ƴammatayen wajen duk sun masa quri da ido.
Duk abun da ake ciki Gimbiya bata da labari kuma bata sani ba dalilin ta faɗa tunanin yacce zata damu ta kada su a agasan nan ko Papan ta zai bar batun auren ta yanzu, taɓatan da jakadiya tayi shi ya dawo da ita daga tunanin da ta faɗa, tana ɗaga ido Carab sai a kan fuskan Amjad, qare masa kallo tayi kamun ta taɓe baki "wannan mutum har mutum amma sakali sakalci da girman sa harda tura baki kaman mace a haka ya shiga gasan Gashi dai da zubin jarumai" bayan ta gama zancen ta a ranta taɓe baki ta kuma yi.
Jakadiya dake gefen ta ne ta murmusa tace "Allah ja kwanan Gimbiyar mu ƳAR SARKI KUMA JIKAN SARKI SANNAN DAI MATAN SARKI, wannan yarima namu na gobe yayi qoqari tunda har idon Gimbiyar mu ya sauqa a kansa." Girgiza kai Gimbiya tayi wanda hakan ya bawa jakadiya daman fahimtar Yaren uwargijiyan nata abinda take nufi.
Wasu ƴammataye can gefe ke surutu "ke fa mastala na dake rahama rashin hankali wallahi, bar batun hassada da kike wa Gimbiya yanxu ace kece a matakin datake ga wannan kyakkyawan halittar na tabbata bazakice haka ba, nifa wallahi da ace nice wallahil Azeem da kaina zan buɗe masa fuskan nawa, ai dai duk kyawun ta ba lallai ta kamosa ba" wacce aka qira da rahama ne tayi shewa hehehe! Lallai ma ita fa ƳAR SARKI CE ina zaki haɗa kyawun ta da namiji kede faɗi gskyh yamaki shiyasa kikace haka, murmushi tayi "rahama kenan, Allah dai ya bawa mai rabo Sa'a namu kallo ne amma duk da haka nide inaso yayi nasara" da Ameen sauran qawayen nata suka amsa....
Sarkin shela ne ya buqaci ganin Gimbiya da kuma ɗaya daga cikin masu gwabzawa da ita, Sarkin shela bai gama rufe bakinsa ba, anwar ya miqe ya fito don baiso Amjad ya fara ballema yaci dan tun da ya ɗaqa ido ya gansa yaji kishi ya rufe sa.
Bayan ya shiga Filin ya tsaya, Gimbiya ce ta shigo filin itama cikin takun ta mai ɗaukan hankali, tun da ta tashi har ta shiga idon Amjad da Anwar na kanta haka ma ɗokacin jama'an wannan fili duk kowa kallonta yake, Amjad ne ya kauda kai "yanxu in ba Umma ba wannan qaramar yarinya zan aura" stakin ya kuma ja ya kauda kai.
Anwar da Gimbiya Mehwish sun fara fafatawa, Faɗa Anwar keyi da gaske cikin qwarewa da kuma burgewa, abunda ya sanya har Gimbiya ta murmusa ganin Anwar faɗa yake bilhaqqi da gaske kaman ba wanda zai janye abun fuskan ta ba, duk ta inda ya juya in ya kawo sara tarewa take, ko halaman kai masa sara ba tayi ba kawai kare nasa harin take ba ta mai da martani ba. Tana yi tana kallon idon sa duk wani mostin sa da yanayin kai saran sa ta haddace,
Wasan da suke ya stuma jama'an wannan fili dan ba abinda kakeji sai ihu ana kiran sunan "GIMBIYA" da kuma "ANWAR" kaman ance ya kalli idon Gimbiyar karaf yasa idonsa cikin nata wanda hakan ya basu daman kallon juna sosai kallon da ya janyo wa Anwar shagala da kusan mancewa a filin gasa yake, Murmushin gefen baki Gimbiya tayi wanda rashin ganin fuskanta baze hanaka gane hakan ba ganin kwayar idonta kaɗai ya isa sanya mutum hasaso irin kyawun da murmushin ya mata!! lumshe ido tayi ta kuma buɗewa kaman mai jin bacci g kuma wannan haɗaɗɗen murmushi akan fuskan nata abun da bai wuce seconds ba ya gigita Anwar, yana ganin abun da tai da ido ya susuce be ankare ba ya jishi aqasa.(subhanallahi sannu!!)
𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 " 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖"𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 ba abun da kakeji yake tashi a wajan dai sunan GIMBIYA mutane na ihu suna qira.
Amjad dake zaune taɓe baki yayi ya kau da kai. Runste ido Anwar yayi, yana jin kaman ya buɗe qasa ya shiga dan kunyan da yaji ys lulluɓe sa!
Amjad kau da kai yayi kaman bai san mai ake awajan ba, zaka ranste besan mai ke faruwa ba. Amma yafi kowa sanin mai yafaru yana kallon duk yacce tayi wa anwar har ta faɗar da shi, qaramin tsaki yaja "kai ka jawa kanka bansan mai ka tsaya kallo ba a wajan wannan qaramar yarinya."
Bayan Anwar ya fice a filin da kan sa aqasa bai ko tsaya ba yabar tsakiyar taron muqarraban sa suka bi bayansa.
Sarkin shela ne ya qira sunan Amjad dan ya shiga fili, Gimbiya kuwa tana tsaye a filin tana jiran shigowan sa. Amjad yaji anqira sa amma bai ko mosta ba, daga inda Umma ke zaune tare da Abba ta zubawa ɗan nata ido, yana ɗago kai idon su ya haɗe da na Umman tasa ba shiri ya miqe ya nufi cikin filin.
Tafiyarsa ma kaɗai abun kallo ne da burgewa gaba ɗaya anzuba mashi ido kuma abinda ya stana kenan kallo!! Umma daga inda take zaune ta murmusa ganin yacce ɗan nata ya haɗa fuska kuma tasan idon da yaji yamasa yawa ajiki ne shiyasa cewa tayi "Allah ka shiryamun yaron nan" da Ameen Abba ya amsa, wannan yaron naki ai ko mace albarka yanzu fa kallon ne ya damesa haka muke fama kullum a kasuwa su kuma ƴammatayen kaman me kallo kam, umma tace "Tom sunga ɗan kyakkyawan saurayi ba dole ba, Allah dai ya basa Sa'a" da murmushi Abba yace Ameen.
Cikin tsakiyan filin ya tsaya fuskan nan a haɗe kaman anmasa albishiri da mutuwa, ko alaman murmushi babu a fuskan sa wanda hakan bai ɓoye kyau en sa ba.
Wallahi rahama wannan bawan Allah duniya ne dubi fa ya haɗa rai ma kyau ya qara wayyo garin daɗi na nesa inji hausawa inama nice Gimbiya, "Allah taroki bintalo" faɗin rahama
Yana tsaye tana staye ko kallon inda take bai yi ba, fuskan sa a haɗe (wai kace dan ma ƳAR SARKI CE).
Suna staye shiru dukan su biyun ba wanda ya mosta kowa na kallon ikon Allah, a haka za'a yi gasan? Mai shela ne yayi magana "Allah ja kwanan GIMBIYA za'a iya fara wasa" Amjad yana jin abinda Sarkin shela ya faɗa amma hakan bai sanya shi motsawa ba staye yake yana kallon duk wani mostin ta.
Ganin yayi shiru kaman mai tunani hakan ya bawa Gimbiya daman ɗaga takobin ta dan kawo masa saran lokacin ɗaya ta kadar dashi, sai dai kashhh tana kawowa........
*manxon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yace duk wanda ze kwanta bayan adduan baccinsa ya liximci
"Hasbiyallahu la ilah ha illah huwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul arshil azeem"
Qafa bakwai, Allah zai karesa daga dukkan wani sharri acikin wannan daren, Na mutum ko aljan,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 25