nasa ɓangaren ma haka ya lallaɓa ya shiga bayi yayi abunda zai yi ya fito ya kwanta dan ya huta wa zaman asibitin da yayi na kwanaki.
Abba sun isa airport inda suka shige jirgi suka kama hanyahn KD
Jirginsu ya isa lafiya, suka samu dakarun sojoji da motoci suna jiran isowan su dama
Shiga Motor suka yi shi da sojojin da aka qaro masa dan staron sa(escort) suka yi gida
Tun kan Motorn nasu ya iso qofan gida aka wangale masu gate sakamakon qaran jiniyan da ya sanar da sojojin dake cikin gidan dawowan mai gidan
Umma da Little ke mata daru wai shi sai dai akaisa wajan auntyn sa Maha, tana jin qaran motocin tace "yauwa Angon gilani oya miqe ga can aboki ya dawo kaje kace masa ya kaika" ta shuwa Little yayi yai hanyan waje
Umma ganin ya fita murmushi tayi tace "kaje can ku qarata da abokin naka dan anma yarona takwara da kai dai a kama a haɗani da aikin renon ka"
miqewa tayi ta shige ɗaki dan qara gyara jikin ta kamun mijin nata ya shigo.
Gimbiya wajan Ammaan ta taje dan yanzukam jikinta Alhmdlh
abunda har yanzu bata iya yi shine dai ta taka da qafafuwanta har waje kuma abunka da ciwo in ya kwan biyu ma sai a hankali bare ciwon da ya ɗibi shekaru
suna aiki da rubutu da kuma magun gunan da Abba ke turo masu kullum
Sosai mutunci ya shiga tsakanin Mai martaba da kuma Abban 𝘼𝙈𝙅𝘼𝘿.
Hira suke da Ammaan ta amma gaba ɗaya tunaninta baya wajan Ammaan nata sosai take jin wani iri da kuma yawan kallon fuskansa a idanuwanta
Ajiyan zuciya ta sauqe, Ammaan ta dake kula da duk yanayin da take ciki murmusawa kawai tayi dan daga ganin ɗiyar tata tasan matsalar ta
Kallonta tayi tace "tashi kije ki huta ko ibnateeyh"
Tura baki tayi tace "Ammaa a'a ni ban gaji da hira dake ba kuma ni banajin bacci
To ni kuma na gaji da hiran bacci nake son yi
Qara tura baki tayi idonta ko ya kawo kwallah Ammaan ni ɗin? murmushi tayi tashi kije kiyi tunanin surkina da kyau amma adinga masa addu'a
Jin abinda mahaifiyar ta tace sai ta rufe fuskanta da hanunta ta tashi da gudu tabar ɗakin tana dariya ya akayi Ammaan ta taramfo ta
Ganin ta fita da gudu har da rufe fuska sai abun ya bawa Sarauniya Dariya
Murmusawa kawai tayi tana Allah maki albarka ibnateeyh Allah nuna mana wannan rana alfarman Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
Ko da t fita a wajan mahaifiyar ta maimakon ta wuce ɗakinta sai ta stinci kan ta da son zuwa garden tuna ranan da suka yi sallama sai ta nufi wajan kaman zata same shi zaune yana jiran ta
Kuyangunta ne da suka biyota suka yi saurin mata shumfiɗa Suna tambayanta Allah yaja kwanan Gimbiya mai za'a kawo maki ranki shidaɗe?
Fuskanta a rufe kaman ko yaushe idonta ma a lumshe bata ko mosta ba bare tace uffan
Suna ganin haka sunsan me take nufi
abunda yaban mamaki banga an shiga ciki ba a nan garden ɗin naga an taho mata da fruits ayanke kuma da alama a fridge aka cirosu, kayan itatuwan like kankana, abarba, ayaba, cucumber and apple etc.
Fav fruit nata ta ɗauka kankana yanka 1 ta kai bakinta, mai ta tuna sai ta fasa ta ɗau Apple ta tauna a hankali Lumshe ido tayi jin daɗin Apple ɗin ya ratsa mata har kai
she dont know why sosai take jin son ganin wannan kyakkyawan saurayin ko Apple ɗin ma dan ta tuna fav fruit nasa ne Shiyasa taci sai kuma taji daɗin sa daban yau....
Muje zuwaa✍️
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀
𝘿𝘼𝙂𝘼 𝙏𝘼𝙎𝙆𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙌𝘼𝙇𝘼𝙈𝙄𝙉
👇
𝙃𝘼𝙍𝙄𝙍𝘼𝙏𝙐𝙒𝘼 𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙏𝙊𝙊𝙍𝙇
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
𝗪𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗵𝗮𝗳𝗶 𝘀𝗮𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿𝘄𝗮 𝗴𝗮𝗿𝗲𝗸𝗶 𝗺𝗮𝗹𝗮𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗼𝘆𝗶𝘆𝗮 𝘁𝗮 𝗾𝗮𝘄𝗮 𝘁𝗮 𝗴𝗮𝗿𝗶 𝘕𝘈𝘕𝘈 𝘔𝘈𝘙𝘠𝘈𝘔𝘈 𝗵𝗮𝗯𝗶𝗯𝘁𝘆 𝗮𝗺
𝗞𝗶𝘆𝗶 𝘆𝗮𝗰𝗰𝗲 𝗸𝗶𝗸𝗲 𝘀𝗼 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶 𝗾𝗮𝘄𝗮𝗿 𝗮𝗺𝗮𝗻𝗮 𝗼𝗻𝗲 𝗹𝗼𝘃𝗲 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹
𝙶𝚊𝚒𝚜𝚞𝚠𝚊 𝚐𝚊𝚖𝚒 𝚍𝚊 𝚏𝚊𝚝𝚊𝚗 𝚊𝚕𝚔𝚊𝚒𝚛𝚒 𝚊 𝚐𝚊𝚛𝚎𝚔𝚞 𝚖𝚊𝚜𝚘𝚢𝚊 𝚕𝚒𝚝𝚝𝚊𝚏𝚒𝚗 𝚈𝙰𝚁 𝚂𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙲𝙴𝙴 𝚊𝚔𝚘 𝚒𝚗𝚊 𝚔𝚞𝚔𝚎 𝚊 𝚏𝚊𝚍𝚒𝚗 𝚍𝚞𝚗𝚒𝚢𝚊𝚛 𝚗𝚊𝚗 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚝𝚊𝚔𝚞 𝚊𝚔𝚘 𝚍𝚊 𝚢𝚊𝚞𝚜𝚑𝚎 𝚄𝚆𝙰𝚁 𝙱𝙰𝚃𝙾𝙾𝚁𝙻
𝙶𝚘𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚖𝚊𝚛𝚊 𝚊𝚍𝚊𝚍𝚒 𝙲𝙴𝙾 𝙻𝙰𝙵𝙰𝚉𝙸 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝚁𝚂 𝙰𝚂𝚂𝙾𝙲𝙸𝙰𝚃𝙸𝙾𝙽 (𝙰𝙱𝚄𝙱𝙰𝙺𝙰𝚁 𝚂𝙰𝙳𝙴𝙴𝚀) 𝙳𝙰 𝙳𝙰𝚄𝙺𝙰𝙲𝙸𝙽 𝚈𝙰 𝚄𝚆𝙰 𝙽𝙰 𝙼𝙴𝙼𝙱𝙾𝙱𝙸𝙽 𝚆𝙰𝙽𝙽𝙰𝙽 𝙺𝚄𝙽𝙶𝙸𝚈𝙰 𝙼𝙰𝙸 𝙰𝙻𝙱𝙰𝚁𝙺𝙰.
***
🅿️ 47&48
💋💋 امى بتولة💋
Asuban farko Mahreen ta tashi ta gabatar da nafilan ta sannan ta tashi Maha
Ana qiran sallah suka bi masallaci tare da Maha, bayan sun idar da salla kowa azkar nasa yayi da lazumin safe suna shafa addu'a Mahreen ta miqe ta fice a ɗakin, Maha kuwa komawa kan gado tayi ta gyara kwanciya dan har yanzu buguwan da tayi jiya yana damun ta
Ko da Mahreen ta fita Gyaran palourn ta soma ta gyara dinning
Sanda ta tabbatar ta gyara ko ina tass ta kunna burner da ta gani
sannan ta wuce kitchen ta ɗaura ruwan abun kari
Wanke wanke ta haɗa na ƴan stiraran kwanukan da ba'a wanke su jiya ba dan ta wanke sai ga hayra ta shigo kitchen en da sallama
Amsawa Mahreen tayi suka gaisa hayra tace "sister irin wannan aiki haka da sanyin asuba gaskiya duk wanda ya aure ki ya huta na taya sa murna, ni fa duk jaraban tsohuwar nan da sanyin asuban nan ba fita zan ba atou"
Murmushi Mahreen tayi kai de sissy
Me a cikin aikin asuban yafa fi daɗi gaskiya nikam ma banjin sanyinn da kuke faɗa a nan Ji nake ma garinsu Umma yafi nan sanyi
Haka dai kika ce sister amma bauchi yafi kaduna sanyi ina ma za'a haɗa chaɓɓ
( to to kuzo ku raba mana musu yan kd da bauchi ina ne yafi sanyi)
Karɓan wanke wanken hayra tayi amma da qyar Mahreen ta bar mata sai ta koma kan girkin
A haka suka cigaba da aikinsu suna yi suna hira su bibbiyun su har suka kammala komi
Mahreen tace "tom sissy ni dai ba naje na duba wancan malalaciyar ko ta tashi ko kuma baccin ta koma, Na barki da aikin jerawa a dinning afuwan".
Caɓ sister jerawa shine aiki? Ai aikin kam ya qare dan kin riga da kin gama yau delicious naki zamu ci
Murmushi tayi ta fice a kitchen ɗin ta nufi ɗakin su
tana shiga da sallama kallon ta takai kan gado kaman yacce tayi tsammani kuwa hakan ta tarar a kwance ta samu Maha tayi ɗaɗɗaya tana sharar baccinta kaman bata yi na dare ba
Girgiza kai kawai tayi tace "dede dake ai sai yaya habeeby ɗin Allah Ubangiji yasa ya Aure ki ko zai saita mana ke"
Har zata shige bayi sai ta tuna yanxu ba safiya bane a jiddah qaramin wayanta ta jawo tayi dialing layin Ummeyn ta
Yana ringing ɗaya Ummeyh ta ɗauka tana "Assalamu'alaiki beenty"
Amsa Sallaman tayi "wa'alaikissalam Na'am Ummeyh na antashi lafiya?
Lafiya Alhmdlh ƴar Ummeyh ya ummata?
Uhmn Ummanki ki ko rigima Ummeyh daga gani ma halin tsohuwar nan Maha ta ɗauko wallahi
Eyye Ummeyh kama haɓa tayi kaman ƴar tata na gaban ta nace gidanku Mahreen dan dai kin renani ki dubi idona kice uwata rigima mun fara wasan reni ko?
Uhmn ni dai bance ba Ummeyh, ya Abeeyh?
Igiyan ajiyansa da kika ban ya tsinke ya gudu,
Ki fita idona Mahreen uwata ba sa'an wasan ku ba
Turo baki tayi Allah ya baki haquri Ummeyh
In ya bani haqurin ki qwace da kanki a wajan
Ayya dai Ummeyh na kiyi haquri Allah baki haquri
Ameen to ke kuma Allah ya maki albarka Mahreen ɗin Ummeyh da Abbeyh
Murmushi tayi tace "Ummeyh yaushe zakizo? Muna missing naki"
Very soon beenty Insha Allah
Yanzu dai ina Auta? banji mostinta ba
Gata nan kwance kaman kayan wanki Ummeyh tana bacci, Allah ba ɗiyarkin nan bata ji ko kaɗan Ummeyh ni so nake ma wataran ya soja ya taimaka ya jibge ta ko zata nistu shi kuma baya dukanta kaman me storon ya ko me ta masa sai dai surutu
Ummeyh murmushi tayi tace "duka wannan dogon bayanin akan ƴar jinjirata Autan Abbeyh tom ta Allah ba taki ba za kiji dashi ne ba mai taɓa mun jinjira bawa Auta ta waya nikam naji muryan ta
Daka mata mari a acinya Mahreen tayi "tom sarkin masu baccin safe tashi Ummeyh na magana" ta faɗa tana miqa mata wayan.
Hararan Mahreen tayi ta amshi waya sai kuma ta fashe da kuka
ni dai Ummeyh ko kizo mu koma ko na biyo ki tunda nazo ya habeebu duka na yake haka yaya Mahreen ma duk se cin zalina suke ba mai sona sai Umma da Abba da ya Abdoul da yarona
Murmushi Ummeyh tayi tom ai naga masu sonki sun fi masu dukanki yawa kiyi haquri uwata ta kaina duk wanda ya qara taɓa ki sai ki haɗa shi da Umman ki ko ki faɗawa takwaranki kinji
Insha Allah very soon nima zan zo nan da week in Allah yaso ya yarda in dai har ayyuka suka yi dama-dama kinji
Tom Ummeyh naji
Yauwá to share hawayenki Auntan Ummeyh
turo baki tayi ni dama kuka na ba hawaye
Dariya duka suka yi ita da Ummeyhn nata to Allah ya shiryaki uwata
Maza a tashi aje a gaida Ummata nasan ko gaisuwa ba kiyi ba
Uhmn kawai tace suka yi sallama ta bawa Mahreen wayarta
Sallama suka yi itama ta katse call en, ajiye wayan tayi ta shige bathroom
Maha tashi tayi ta gyara ɗakin tsaff kaman ba i taba ta kunna turaren wuta.
Mahreen ta fito wanka da mamaki taga har Maha ta gyaran ɗakin kuma tsaff har qamshi yake
Taɓe baki tayi dama haka kike kekam kaman me aljanu
Batace ma Maha uffan ba ta wuce dan ta shirya ta fita ta gaida kakus
Maha ma toilet en ta shiga sanda ta wankesa tass sannan tayi wanka itama ta fito
Kusan a tare suka gama shirya wa
Tabarakhallah Masha Allah kyau suka yi sosai kaman masu zuwa gasan kyau
Abaya suka sa ita Mahreen ta saka peach ita kuma Maha ta saka maroon gashi dukansu farare
Kar kuso kuga kyan da suka yi kyau har yana ɗiga.
Fita suka yi a ɗakin sun samu hayra itama ta gama shirya komi har tayo wanka abunta, dukan su suka yi ɗakin Kakus dan gaishe ta
sallama suka yi ta amsa tana ɗaurin ɗankwali
juyowa tayi tana kallonsu tana murmushi Masha Allah kaga larabawan jikoki na Allah dai ya rayamun ku ya maku albarka
Gaisawa suka yi duka tana qara sa musu albarka
Hayra ce ta shigo tace "Amarya kizo mu karya"
danqwalon hayra tayi dan fatarin kakarki amma ba niba uwaki ce Amarya ba ni ba dan jakan ubanki dama tare dani kike karyawa ko neman magana
Maha da bata iya yin shiru tace "ke dai stohuwar nan ba'a maki gwaninta ko kaɗan"
Takwara ke kuma ki fita a idona kamun na taso banson aikin masu tangaɗi da sanyin safiyar nan bazaki sani sinqin surutu kaman mai layiii ba
Ita dai Mahreen murmusawa take, tashuwa suka yi suka fice duka suka bar kakus dake qoqarin fitowa itama
Bayan duk sun fito sun zauna a dinning ɗin
Maha ce ta kalli hayra tace "yanzu yaya hayra dan jaraban tsohuwan nan itama a dinning take cin abinci mutum na tafiya kaman me tete"
Dariya suka sa duka na rabaki da surutun safe na kakus Maha, kinga dai ke takwaranta ko tom wallahi ba rage maki zata yi ba jaraban masifan ta na safe yafi na ko yaushe
Maha tace "yo to ni ina ruwana tamun na mata kalass"
Kakus ne ta iso wajan tace "ke hariratu ubanki Muhammadu ne mai jaraban masifa, ke kuma mai sunan aljanu ubanki kika rena dan jakar ubanki, tangaɗaɗɗun yara kawai masu sinqin reni".
ja mata kujera hayra tayi ta zauna
Tace "to ina su sojan mijina?
Kai amma dai yaran nan baku da kirki harda ke indo da nake wa kallon mai hankali cikin carbi, yanzu dan sikitin sinqin rashin mutunci shine har za kusa abinci a gaba baku nemo ƴan uwanku ba sufa sune maza suke nemowa ku ba abinda kuka iya sai ci bari kuji tom inga ɗan kwal uban dazai ci abinci anan su soja basu zoba ingwada masa nawa tagaɗin yafi nasa"
Maha ce ke qunquni, yauwa kin fara ai kenan da wannan zagin da bansan a ina kika koyo saba
Kallonta kakus en tayi, juyar dakai tayi nide ba inda zani atou
Hayra ce ta tashi taje sashensu ta qira ya Abdoul ta kuma dawowa ta qira ya habeeby
Ta samu ya Abdoul ya gama shiryawa fitowa yayi yayo dinning ɗin, shima ya soja dinning en yayo
Zaunawa ya Abdoul yayi a setin Mahreen wacce tunda yazo wajan ta sauqe kanta qasa dan dai yanzu kuma take jin kunyan sa
Saving nasu Mahreen da kanta ta tashi tayi ta sawa kowa nasa
Da tazo kan na ya Abdoul rasa mai zata sa masa tayi shi dai ya soja yana gani sai smilling yake kawai dan burgesa suke
A haka dai tasa masa ferfesun kayan ciki da tosted-bread da soyayyen qwai a gefe da kuma ruwan zafi
Kallon gaban Abdoul kakus tayi ta kalli gabanta daga soyayyan kwai da bread se ruwan shayi
Ajiye cokalin hannun ta tayi ta saka Salati
Sai duk suka ɗago suna kallonta shi dai soja ya fahimci nufin ta tun da ya kalli kallon da take wa plate ɗin gaban ya Abdoul dan haka mai zai yi inba dariya ba harda kama ciki
Itako Maha duk da kyawun da taga ya mata yana dariya hakan bai hana ta aika masa da harara ba tace a ranta "kaga Soja mugu bai san me akayi wa salatin ba yakama dariya dan baqin hali da nema mana surutu"
Kakus ce tace "oh Ni Mairama daso yanzu ke indo dan ɗiban albarka da kuma rashin storon Allah sunan ki kaman na mayun daa Kiga abunda kika sawa abdu kiga abunda kika samun nida gidan yarana da kuɗin yarana fa aka sayi komi amma dae Allah ya kyauta don haka ban isa ba bazaki samun bushashshen biredi kaman kunnen zomo ba da wannan abu kaman wainar kashin shanu sannan ki cikawa Abdu kwano ba tun da bana uwarsa ba
Nima samun ferfesun atou
Mai zasu yi a wajan in ba dariya ba dukan su kowa ta basa dariya dan duk sun ɗauka wani abun ne ya faru ganin irin salatin da ta rafka
Ya abdoul ne yace "haba amaryata kishi kike dani tom juyo muci tare"
Ɗan qwal uba banson yaudara kayi kaɗan nayi kishi da kai Ni dai tunda ba uwarka ce ta saya ba yaronane ɗan albarka ya sayo to maza azubamun banson tangaɗanci
Hayra ce dan ta kashe surutun ta tashi ta sawa kakus kaman na abdoul en har da chip's da suke ci suma
Ai kuwa tana loma ɗaya da ferfesun ta kurma ihu ta tufar
Yanzu dai ke ja'irar ƴar nan kasheni zaki yi wato ki huta wannan barkonon kike aikaman nasa a ƴan hanji na da nake maleji dasu to ta Allah ba taki ba
Ai nasan wannan yar albarkan sona take shiyasa bata saka mun ba
Maha ce ta turo baki ke dai takwara kin cika surutu abincin ma bazaki barmu muci a nuste ba dan Allah
Bafa kyau surutu anacin abinci so kike muci tare da sheɗan halan
Subhanallahi cubulle bakinki ya sari ɗanyen kashi Allah tsaremu haɗa hanya da sheɗan
A'uzubillah bismillahi
Yo kunga na koresa ai ba naci abinci na nayi shiru Allah zubo maki albarka cubulle.
Shi dai ya Abdoul duk abun da ake bayama jin su gaba ɗaya idonsa na kan Mahreen
Ita kuwa sai sunne kai take
Kakus ce tace "jarababben kallo dai ba kyau sai ya sanya mutum tangaɗi gwanda a nistu aci abinci yafi lada ko ƴar mutane ta sarara" ta faɗa tana hararan ya Abdoul
Murmushi yayi bai ce komi ba sanin sarai dashi take
Wayan Mahreen ne yayi qara alaman saqo ya shigo taga ya habeeby ta gani ya turo mata text
*qanwata ki barmun yaya haka ya karya mana karki zautasa da yawa kinji stohuwa ta fara banbami kar takai mana mazga*
Ɗagowa tayi suka haɗa ido da ya soja en dariya ya mata sai ta harare sa a wasa ta tura baki ta kau da kai da kallon kowa tana karyawanta ita ma
Sannan ya Abdoul ya ɗan nistu yana cin abinda ta zuba masa cikin nistuwa
Bayahn sun kammala kowa yayi hamdala
Main palourn suka koma dukan su
Hayra ce da Mahreen suka tattare wajan, bayan sun kai kitchen suka haɗa wanke wanken suna yi
Mahreen ta fita tabar hayra a kitchen ɗin zata ɗaura sanwa.
Gimbiya Mehwish itace bata koma cikin gidan ba sai yamma liss
Direct ɗakinta ta wuce tana shiga tai jefi da abun fuskan ta takwanta a gadonta tana faɗin "washhh Ammaa ta na gaji da tunanin ba nayi bacci yanzu kam before magrib....
𝘽𝘼𝙔𝘼𝙉 𝙎𝘼𝙏𝙄 𝙂𝙐𝘿𝘼 1
Rayuwa nata tafiya yayin da bawan Allahn da Daddyn Little ya buge satin sa ɗaya 1 ciff da sallama yau da ya kama Lahadi qafa kuma Alhmdlh sai dai ɗan abunda baza'a rasa ba
Ameerah da Daddyn Little sun gwada tambayan sa da mamakinsu kuma ya amsa masu tambayan
"Yace masu shi bauchi yake son zuwa" sai dai apart from haka bai faɗa musu komi ba dangane dashj sun haqura tun da ya yarda zai zauna har satin ya cika
A ɗan satin da yayi a gidan sosai suka shaqu da Ameerah in da take ta roqonsa karya tafi ya zauna dasu inyayi sai suje Bauchin tare suma akwai family house nasu a can
In ta faɗi haka baya cewa komi sai dai yayi murmushi kawai
Shi dai shirinsa yake zai tafi dan a lissafin sa bai wuce wata 2 bane yanzu ya ragemasa
Gashi be isaba bare yace ya samo abun da yazo nema.
Umma ce zaune a palour tare da Abba da angonta Little tana masa karatu Abba kuma na karanta jarida
Wayanta dake gefen Abba ya ɗau qara Umma tace "yallaɓoi a taimaka a miqamun"
Murmushi Abba yayi bai ce komi ba yasa hannu ya ɗauka ya miqa mata karɓa tayi ta amsa qiran
Tana sallama tace "Mijin mata huɗu 4" Ummeyh tasa dariya kaji wani batu yanzu in ba wan da ya sani ba ai sai ya ɗauka haka ne alhalin zance ne bayan kinbi kin mallake ni gaki ke kaɗai a wannan qaton gida kin hanani qara amre
Murmushi Umma tayi jin abinda Ummeyh tace
Haba Gwaggo yara dan dai baku samu bane nasan da kun jima da yin huɗun
hiran su suka cigaba dayi cikin barkwanci da raha
Ummeyh ce tace "Umman yara guess what?
Umma tace Gwaggon su amun da yaren da zan fi ganewa
Tom albishir tace "goro fari tass, ina jinki ya akayi"
Insha Allah jibi iwar haka ina Nigeria muna tare
dan Allah da gaske kice Gwaggon su? Sosaima da gaske in Allah ya yarda
Da farin ciki Umma tace shikkenan bauchi yayi qira dama nayi kewan Amarya ko naje na ganta nima
Kede bari kawai Umman yara Insha Allah sena zo zamu je
Allah kawoki lafiya mijin mata huɗu 4
Sallama suka yi tace a gaida mun yaya na
Insha Allah yayanki zai ji gaisuwa
Kaste qiran Ummeyh tayi.
Umma ta kalli Little to nan da kwana huɗu 4 zan kai ka wajan auntyn ka Maha sai kabar damu na ko angon gilani
Tura baki yayi nifa gilani ai anci ba'a cona an faca binta apoki na anbi muje mu ciga jilgi
Jan kunnensa tayi duk girman rashin jinka zaka fama sai munje sai dae ko ka zauna kai ɗaya a gidan dan har da abokin zamu tafi
Kukan sakalci ya saka
Abba dake sauraran su yana murmushi
Miqowa Little hannu yayi oya come on abokee bar grannynka ba zata shiga jirginmu ba kuma ita za'a bari a gida
Tashuwa yayi ya fasa karatun ya tafi wajan kakan nasa ya zauna yanawa Umma gwalo wai bazata hau jirginsu ba ita zata zauna a gida
Umma ta murmusa tace "ranka ya daɗe boɗɗinka na gaidaka wai insha Allahu nan da kwana biyu tana hanya"
Abba yace "Allah kaimu Allah ya kawo ta lafiya
Da Ameen Umma ta amsa
Ta tashi ta haura sama ta barsu a palourn.
Ɗaukan wayansa yayi dan ya duba wani number, bayan ya duba kaman wanda akace masa ya shiga gelleryn sa me zai gani Maha ta goge masa photos na wayan sa duka
Kaɗan ya rage yayi kuka dan har da sani contract da aka basu na aikin da za'a tura su turkey ta gogen photos ɗin ransa yayi mugun ɓaci ya rasa mai zai ma yarinyar nan ya huce
Har jikinsa na rawa yama rasa mene zeyi yayi maganin yarinyr nan
Qara kallon wayan yayi, tsaki yaja ya jefa wayan kan sofan dake ɗakin yana huci
"Tabbas sai na zane ki yau Maha ba tausayinki Indae kince ke rashin ji ke ɗawainiya dake ba mu zuba" yana gama faɗan haka tashuwa yayi ya fice a ɗakin.
Yana fitowa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 25