Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yamma. Ganin lokaci na qure wa ba lallai ya samu ba sai kawai ya karya kan dokin sa dan ya juya ya dawo gida, ganin ko yace ya kwana ko ya qara gaba wahala zai sha, sai dai in ya koma gida gobe in Allah ya yarda ya kuma tafi wata gefen in ta kama ko garin ya bari indai zai samo wannan maganin. Har ya juyo da dokin sa ya kama hanya dan ya komo gida kar dare yayi, kaman daga sama aka jefo mutumin sai kawai ganin sa yayi a gaban sa, ko kaɗan bai razana ba dan inda sabo ya saba da zuwan da wannan stoho yake masa ako da yaushe, bai storata ba sai ma hamdala da yayi dan dama ya kwaɗaitu da ya haɗu da stohon ko Allah zai sa ya taimaka masa da wani abun. Har zai sauqa a dokin nasa dan gaida stohon, wannan stohon ya dakatar dashi ta hanyar cewa "a'a yaro na ba sai ka sauqo ba" gaisar da stohon yayi. Da murmushi a fuskansa ya amsa gaisuwan, yarona nayi nisa ne shiyasa baka ganni da wuri ba amma naji zuwan ka, shidai har ransa yana mamakin abunda stohon kecewa wataran kaman ya tambaye sa amma bakin sa sai ya masa nauyi. Bude baki Amjad yayi da niyan zai faɗa wa stohon yacce ake ciki komai da komai, sai kuma stohon ya tari numfashin sa Yace "karka damu ko kaɗan yarona nasan komai yacce ake ciki, Inshà Allahu za'a yi Auren ku nan da wata huɗu sannan mahaifiyar ta zata samu sauqi sai dai akwai abinda zai faru wanda bana iya hangowa kuma bana ganewa sai dai nace maka ka dage da addu'a da kuma neman stari, Allah na tare da kai Inshà Allahu komai ya kusa zuwa qarshe, sannan ka kusa daina ganina, randa zamu yi haɗuwan qarshe a ranan zan sanar dakai haɗina da kai da komi, ina maka fatan nasara a rayuwan ka, ka riqe Umman ka da Abban ka da kyau, ko da kasamu wasu masu mastayin su nan gaba, wannan iyayen naka sune alkhaeryhn ka su suka maida ka mutum a lokacin da kake gaf da barin duniya. Sannan ganyen da kake nema da iccen suna makarin ciwon jikinta insha Allahu, Allah qara maka baiwa da basira. Amma sai dai akwai ɗan mastala ɗaya, mastalan shine ba zaka same su anan ba. Nayi qoqari tun kan kazo da maganan maganin ace na samo maka ko na aika an kawo maka, Amma bazai yuwu ba dole zaka shiga waccan qasan da nace maka NIGERIA, a garin Bauchi akwai wani jeji YANKARI a wannan jejin ne Inshà Allahu zaka samo duka maganin har kayo guzurin wasu. Jinjina kai yayi yace "Nagode sosai baba nagode Allah saka da alkhaery. In ka samu tafiya Allah stare hanya Allah kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah yasa adace, suka yi sallama ya kamo hanyan dawowa gida abun da ba tare da ya ko waiwaya ba. Shine bai isa gida ba sai bayan sallahn isha'i. Ya zuwa direct wanka ya shiga yayi, ya ɗaura alwala anan gida yayi sallolin da wanda bai yi ba. Rasa yanza zai yi ya faɗa wa Umman sa wannan magana yayi suna hira yana jinsu yayi shiru yana tunani, ya rasa ta ina zai fara yana storon kar Umman nasa ta hana sa. Abba ne ya kalle sa yace "Jarumin Umma andace kuwa? Sosa qeya yayi Tom Alhamdulillahi dai kawai Abba, Umma na kallon sa tace "akwai Magana abakin ka na sani, menene ya faru Angon Gimbiya? Ganin Umman tasa ta ramfo sa qarshe dai ba yacce ya iya haka ya faɗa masu gashi-gashi sai dai bai basu labarin wannan stohon ba kuma bai ce masu shi ya faɗa masa ba, ɓoye masu yayi yace "wani bawan Allah ne maharbi kuma shima mai bada magani ya faɗa masa hakan" ya faɗa yana kallon Abban sa dan yasan tabbas yayi qasa da kai Umma zata gane ya ɓoye wani abun ko in ya kalleta zata gane. Ba tare da Abba ya damu ba yace "Allah yasa hakan ne alkhaeri Allah sa kayi tafiyan a Sa'a Allah yasa adace" Umma ta amsa da Ameen, Sannan dan Allah inaso ka kula sosai Jarumin Umma kaga baka taɓa zuwa wannan qasan ba ka kula sosai, yanzu in ka tafi ta yaya zanke jinka? Murmushi yayi ya sauqe boyayyen ajiyan zuciya dan bai tsammani Umman tasa zata amince da wuri haka ba, ya ɗau sai sunsha wahalan bata baki da fahimtar da ita shi da Abba, cewa yayi "Umma ai bazan daɗe ba Inshà Allahu bazan wuce sati ba" Tom Allah ya yarda jarumin Umma Allah baka Sa'a. Duka suka yi Ameen Yanzu yaushe ne tafiyan naka? Inshà Allahu Umma ta gobe ko jibi dai, Tom Allah nuna mana. Ɗakin sa suka raka sa Umma tai masa addu'a da ahuta gajiya suka ja masa qofa suka yi nasu ɗakin. Umma na shiga ɗakin ta zauna bakin gado tayi tagumi, Abba da ke bayan ta Murmushi yayi dan yasan tabbas za'a yi haka, ko shi yaji mamakin amincewar ta lokaci ɗaya amma yasan hakan baya rasa nasaba da tausayin Gimbiya da take ji. Abba Zuwa yayi kusa da ita a bakin gadon ya zauna, jawo ta yayi ya haɗata da jikin sa yana bubbuga bayan ta alaman rarrashi "haba MARYAMA ta sarauniyar mata uwar Muhammadu matar Ibrahim, so kike kisa ɗan naki yayi qasa a guiwa? Kefa kikace ɗan ki jarumi ne ko kinason ki zama raunin jarumtar sa ke da kanki? Girgiza kai Umma tayi hawaye nabin idanuwan ta! Abban yaro na bazaka gane ba ko kaɗan ya nake jin wannan yaron namu a rai na, kullum addu'a ta ɗaya Allah yasa na mutu kamun ace yau ba yarona kusa dani, qaunar da nake wa yaron nan kusan kullum cikin zullumi nake inya fita zai dawo yace yasan gaskiya, kullum cikin mafarkin an rabani dashi nake, kullum cikin addu'a nake kamun wannan rana Allah ya ɗauki rai na! Kuka ta fashe dashi Abban yaro na inason yayi tafiyan nan dan tabbas inajin tausayin wannan mata da kuma yarinyar da marabin ta da Maraya mara uwa kaɗan ne. Abban yaro na kasani haka kawai zuciyata bata kwanta da tafiyar nan ba kuma inaji a jiki na kaman wani abun zai faru ko kuwa sanadin rabuwana da Amjad kenan, kuma kasan bszan iya ɗaukan haka ba daga randa akace an rabani da Amjad daga ranan nayi bankwana da farinciki har mutuwa na wataqila ma sanadin mutuwa na kenan! Ajiyan zuciya Abba ya sauqe! Tabbas acikin magana Maryam ba qarya ko ɗaya ko kowa bazaiyi shaidan son da take wa Amjad ba shi zai yi shaida tun daga randa ta ɗaga idon ta ta ɗaura akan yaron nata tabbas yasan qauna ce na ɗa da uwa Allah ya sanya tsakanin su dan Amjad ma sonda yake wa Umman sa ako ina baya ɓoyewa. Abba yace "MARYAMA ta inaso ki ɗago ki kalle ni, ɗagowa Umma tayi fuskan ta duk hawaye! Abba yace ki kalli idona Maryam, kallon Abba tayi, Abba yace mata "Maryam wa ya baki Amjad? Umma tana sheshsheqa tace "Allah" Abba ya qara cewa "wa zai ɗauki ranki ko na Amjad ya rabaku? Umma ya qara cewa "Allah". Jinjina kai Abba yayi yace Alhamdulillahi, Maryam nasan ke musulma ce kuma kin yarda da Allah sannan akwai samu akwai rashi akwai mutuwa akwai rayuwa, kuma duk kinsan mai qaddara wannan abubuwa Tom dan Allah kar maganan mu yayi nisa, kar Amjad yaji wani magana yasa kokonto a ransa ko kinason hakan ya faru? Da sauri Umma ta girgiza kai tace a'a. Tom Masha Allah inaso akoda yaushe kidinga binsa da addu'a, Allah ya ga son da kike masa kuma yaga sonda shima yake maki, Allah ne ya baki shi Inshà Allahu ba mai rabamu da Amjad sai mutuwa. Kici gaba da sa masa albarka kinji. Umma ta ɗaga kai, da qyar da qyar Abba ya lallashe Umma har suka yi alwala suka yi nafila, tilon ɗan nasu suka wa addu'an kariya da Sa'a sannan suka qara da godiya ga Allah da suka idar suka kwanta anan Abba yaci gaba da lallaɓa matan sa lallaɓa irin na masoyan gaske wanda soyayyan su bata stufa.... A ɓangaren Amjad kuwa shima a haka ya kusan raba dare ya juya haka da qyar dai ɓarawon bacci ya sace shi. Gimbiya bata san mai yasa ba amma har cikin ranta tana cike da kewan ganin sa yau gaba ɗaya baizo ba, kuma mai martaba yace mata zai ke zuwa. Sai dai abu ɗaya da ke kwantar mata da hankali shine ta yarda da cewan Insha Allahu zai cika alqawarin da ya ɗauka, kusan yau wuni tayi masa addu'an dacewa da Sa'an samowa mahaifiyar tata magani. Bayan ta idar da Sallahn isha'i a ɗakin mahaifiyar ta, tana kan darduma kaman ance ta juya, sai hanun Amman nata ta gani yana motsi kaman tana son ɗaga hannun. Da saurin gaske tayi wajan gadon, Bayan kusan sati gashi yau Ammaan nata halaman sauqin dai ya qara nuna wa jikin zai lafa, dan dama takan yi sati bata ko mosti, in jikin ya lafa kuma tashuwa ne da kuma cin abu bata iya wa amma zata yi magana har ta ɗan jingina da kanta, sai dai komai sai anmata duk da haka Ta sameta ta buɗe ido amma bata iya magana, sai mosta bakin ta take alaman tana son yin magana amma ta kasa, Gimbiya tace "Ammaa Sannu" gyaɗa kai kawai tayi da murmushi a fuskan ta, sai kuma ta mai da idon ta ta rufe. Ko ba komai taji daɗin farkawan mahaifiyar tata gashi har ta mata wannan murmushin nata da ke yaye mata damuwan xuciyan ta, "Allah baki lafiya mai ɗorewa Ammaah ta" shine abinda ta furta tana mai zama gefen maman nata tana ɗan daddana mata jikin ta kaman massage. Har Mai martaba ya shigo ya samesu a haka, ganin ɗiyar tasa cikin farin ciki ya sanar dashi me ke faruwa ko bai tambaya ba, tabbas shima yana jin tausayin tilon ƴar tasu dan kwata-kwata batadan daɗin uwa ba, a maimakon uwa tayi hidima da ita, ita take hidima da uwar tata tunda tayi wayo. Mai martaba yace "Ibnateey me aka bata? Tace "Papa ba komai fa. Masha Allah, Allah ya bata lafiya mai ɗorewa Alfarman Rasulullahi SAW. Da Ameen ta amsa Zama yayi a gefen gadon ita kuwa Gimbiya ta sauqa qasa, mai martaba yace mata "ya kuka yi da Muhammadun? Nan Gimbiya ta kwashe yacce suka yi duka ta faɗa masa har da alqawarin da yace ya ɗauka, kuma Papa inaji a jikina Inshà Allahu za'a dace, Allah dai ya temaka. Mai martaba yace "Ameen ya Allah, Allah ya sa a dacen. Nan ya qara da ce mata "in dai abun da ta faɗa da gasken shi take nema kan ga Auri mutum tom tabbas wannan ne mijin da take nufi akoda yaushe dan wannan ya haɗa fun yacce take so ma, Allah ya tabbatar maki da alkhaeri Ibnateeyh, da "Ameen, ta amsa tana tuno maganan su da jakadiya. Mai martaba ne ya sauqe ajiyan zuciya yace "Amma akwai abun da yake damuna". Gimbiya ta kalli Papan nata cikin damuwa tace "menene Papa? Murmusawa yayi ba komi karki damu kanki Ibnateeyh kai na ke ɗaure wa kawai, tabbas yana mun akwai mai irin fuskan sa da na sani amma abun da jimawa na kasa tunawa. Ayya Papa ai dama haka ne yawanci ance ko wanne ɗan adam da masu kama dashi guda bakwai 7 a duniya, Tom may be shiyasa kake ganin hakan. Haka dai hiran nata ita da mahaifin nata har dare yayi, ta tashi ta wa mahaifin nata sai da safe, ta wuce dan tafiya sashen ta tasamu ta kwanta. Sai dai muce safiyar alkhairi jama'a......... 𝘾𝙝𝙖𝙠𝙬𝙖𝙠𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙪𝙣𝙖𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙁𝙞𝙡𝙢.. 𝙆𝙪𝙣𝙖 𝙜𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙩𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞𝙣 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙙𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙩𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙘𝙚 𝙠𝙤 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙖𝙗𝙪 𝙙𝙖𝙗𝙖𝙣? 𝙏𝙖𝙪𝙨𝙖𝙮𝙞𝙣 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖𝙖 𝙙𝙖 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙮𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙟𝙞 𝙯𝙖𝙞 𝙞𝙮𝙖 𝙟𝙪𝙮𝙚𝙬𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖 𝙠𝙪𝙬𝙖? 𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙯𝙖'𝙖 𝙮𝙞 𝙨𝙝𝙞 𝙠𝙪𝙬𝙖? 𝙒𝙖𝙣𝙚𝙣𝙚 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙨𝙩𝙤𝙝𝙤𝙣? 𝙉𝙖𝙨𝙖𝙣 𝙩𝙖𝙢𝙗𝙖𝙮𝙤𝙮𝙞𝙣 𝙢𝙪 𝙙𝙖 𝙖𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙪𝙘𝙞𝙮𝙖𝙧𝙢𝙪 𝙯𝙖𝙩𝙖 𝙠𝙚 𝙨𝙖𝙦𝙖 𝙢𝙖𝙣𝙖 𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙬𝙖.... ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️ Nace ba jama'a muje zuwa, labari fa yanzu aka fara ✍️ 💋💋 امى بتولة💋 𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa suka sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi!!! # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦💦 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣 𝘽𝙮 𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖 (𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl) اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍 _______________________________________________________________ 🅿️ 35&36 💋💋 امى بتولة💋 WASHE GARI.. Qiran farko na asuba, Umma ta farka a ɗan razane har jikin ta na sassafo da zufa, salati tayi tana dafe qirji! Wannan salatin da tayin shi yayi nasaran tada Abba a bacci. Miqewa Abba yayi ya laluɓi hasken ɗakin ya kunna, kallon ta yayi yace "Lafiya kuwa maryama? Ko dai kinyi mugun mafarki ne? Umma ta kasa cewa qala sai kawai jingina da tayi da kan gadon ta rufe ido tana mai da numfashi! Miqewa Abba yayi ya fice yaje dan ya tashi Amjad amma ya samu har ya tashi, magana Abba ya masa "kayi alwala mu tafi masallaci ko" amjad dake miqa a kan madedecin gadon sa yace "Tom Abba na, yau fa ina Umma ta Bata zo tashi na ba" ya faɗa yana miqewa. Umman ka na can tana fama da rigima ta kusa yin jika bata san ta girma ba har yanzu. Dariya Amjad ya sanya! Yanzu dai Abba wannan abu da kake faɗa cin fuska ne, uwattawa ce ke rigima? Ɓata fuska Amjad yayi! Daga kafaɗa Abba yayi ya fice a ɗakin yana "da kai da Umman taka duk Allah ya taroku" ɗakin su ya wuce. Cikin lallami Abba ya fara magana "Mero ta kina son saka ɗan naki cikin damuwa ko? Kinga ganin ni naje tashin sa ba ke ba har yana tambayan ko baki da lafiya ne, in dai bakyason zuwan ɗan naki can qasar shikkenan ki faɗa masa nasan shi kuma in dai bakyso bazai je ba. Amma inason ki sani Alqawari ya ɗauka masu sannan kuma kece kika fara yarje masa maganan wannan gasa dan girman Allah da Manzon sa Maryam ki lallashi zuciyanki" ganin da alama har ran Abba ya fara ɓaci sai Umma ta sauqo a gadon faɗawa jikin Abba tayi, Abban jarumin Umma kayafeni amma kayi haquri wallahi Nima banson saka damuwa a rai na abunne ya kasa bari na, Mafarki nayi fa akan yaro na. Umma ta buɗe baki da niyan labarta wa Abba mafarkin sai Abba ya ɗaura yastan sa akan bakin ta yace "shiiiii, ya isa ba sai kin faɗa mun ba yanzu sallah zaki yi, ki sanar da Ubangijinki sannan kiyi wa ɗan ki addu'an nasara da ta kariya, kuma kada ki manta wani lokacin akwai sharrin shaiɗan, da yawa mafarki kan zama gaskiya amma wani mafarkin sharrin shaiɗan ne. Wani lokacin mukan kwanta a tunanin abu a ranmu Tom ba shakka wannan abun ya damemu har a mafarkin mu ya zo mana. Akwai kissar wani bawan Allah da yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass(RA) yace masa "ance in kana yawai ta salatin Manzon Allah SAW Tom tabbas zaka gansa, me yasa kullum ina yi amma ban taɓa kallon sa ba? Sai Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Annabi kake so ka kalla? Wannan bawan Allah yace "eh" Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Tom yau in zaka kwanta inaso kaci abinci kawai kar kasha ruwa, ka kwanta haka ko mai ka gani a mafarkin ka kazo kaban labari. Wannan bawan Allah ya tashi ya tafi da yaje gidan sa dare yayi ya ci tuwo bai sha ruwa ba ya kwanta, washe gari asuban fari yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass (RA). Sheikh Ibrahim inyass ya ce masa "bawan Allah labarta mun abun da ka gani a mafarkin naka. Bawan Allah yace "malam nayi yacce kace amma da na kwanta mai makon naga Annabi sai kuma nayi mafarkin inata shan ruwa kawai har dai na farka, murmusawa Sheikh Ibrahim inyass yayi yace masa "Tom in zaka kwanta da qauna da kuma begen son ganin Annabi SAW kaman yacce kaman ka kwanta da qishin ruwan nan Tom tabbas in kana qishin ganin Annabi wataran Manzon Allah SAW zai baka ruwan kashe qishin qaunan ganinsa". Tom inaso ki sani tabbas akwai mafarkin da suke gaskiya kaman labarin dake cikin (MAFARKI NAH littafin Uwar Batoorl) da kuma ( A MAFARKI NA littafin A'isha Mika'il) akwai kuma waɗan da suke ba gaskiya ba. Dogon ajiyan zuciya Umma ta sauqe tana mai jin nistuwa ya shige ta sosai, hamdala tayi ga Allah sannan ta ce "kar Jarumin Umma ya jira ka sosai Abban sa a samu a tafi masallaci" kallon ta Abba yayi yana murmushi yayi hanyan fita a ɗakin yana cewa "inma ya gaji jira ya zai yi ba uwar sa ce ke mun rigima ba ta tsayar dani, mutum har ya kusa yin jika ya girmi yin rigima amma yaqi dai nawa, dole ma na hana Amjad maki takwara dan rigiman masu suna Maryam in ya haɗamun ku har biyu zaku qarisa ni, ya qarasa faɗa ya bar ɗakin dan yin alwala ganin an kusa shiga salla. Murmushi kawai Umma tayi, tabi bayan mijin nata dan ita ma tayi alwalan ta samu jam'i. Fitowan Umma Abba kaɗai ta gani ya fara alwala, wucewa ɗakin Amjad tayi dan tasan halin sa sarai zai iya komawa ya kwanta. Tana shiga ɗakin nasa ta hango sa kan sallaya yana addu'a, tsayawa tayi har ya shafa kamun tace "kar dai jarumin nan yace mum har yayi Sallah? Tashuwa yayi yana murmusawa a'a fa Umma ta nafila nayi kamun Abba ya fito mu wuce. Umma ta buɗe baki zata yi magana Abba da ke tsakiyan gida yace "jarumin Umma ka fito mu tafi kar mu rasa jam'i. Bayan fitan su alwala Umma tayi dai-dai ana shiga sallah a masallaci, jam'i ta tasamu ta bi da aka idar lazumin ta tayi da addu'oeen ta kamun ta shafa, tashuwa tayi ta shiga aikin gida dan tasan in ɗan nata ya dawo ya samu tana yi zai ce zai taya ta. Umma tayi sharan ta da wanke-wanke san da ta ɗaura abincin karyawa kamun ta shiga ta gyara wa ɗan nata ɗaki ta sanya masa turaren wuta mai daɗin gaske. Cikin qanqani lokaci gidan gaba ɗaya yayi staff baka jin komai dai qamshin turaren wutan da tasa a ɗakin ta da kuma ɗakin yaron nata, sai kuma qamshin ruwan shayin da take dafawa. San da gari yayi haske tarr kamun Abba da Amjad suka dawo gida, sun shigo gidan lokacin Umma na banɗaki tana wanka. Abba ɗaki yayi, shima Amjad ɗakin sa ya wuce direct ya kwanta dan mai da baccin da bai yi ishashshe jiya ba. yana kwanciya ya rufe idon sa da zummar yin bacci, kyakkyawar fuskan Gimbiya da wannan murmushin ta mai mantar dashi ko sunan sa ke masa gizo, buɗe ido yayi ya kuma kullewa ita ɗin yake qara gani, laɓɓan ta da yafi ɗaukan hankalinsa da kuma kalan qwayan idon ta su suka hana sa sukuni, duk ya juya haka ya juya haka amma yana rufe ido ita ɗin yake gani tana masa gizo. Tashuwa yayi ya zauna a stakiyan gadon nass magana yake shi ɗaya "wannan kwailar yarinyan mai take nufi dani ne? Guntun tsaki ya ja! Fasa baccin yayi ya tashi ya fita a ɗakin. Umma da ke qoqarin shigowa ɗakin nasa da qiran sa ya karya tukun yayi bacci, ya kusa yin karo da ita, ja baya Umma tayi tana kallon sa tace "lafiya kake surutu kai kaɗai har ka kusa ya da ni? ina son nazo na ganki ne Umma ta. kallon sa Umma tayi da murmushi tace "kadai faɗa gaskiya ko Gimbiyar zuciyar taka kake tunani? Ɗago kan sa yayi da zumman kallon Umman tasa da mamakin ya aka yi ta gane abun da yake tunani, ganin yan da idon Ummansa ya kumbura sannan yayi ja kaman mai ciwon ido san da yaji gaban sa ya faɗi! Umma ganin ɗan nata ya zuba mata ido, nan take ta tuno da yacce idon ta ya kumbura tai saurin juyawa dan kar ya fahimci wani abu ya sawa kansa damuwa, sanin halin ɗan nata. Jarumin Umma biyo ni ka karya sai ka koma baccin ko kaje wajan Gimbiyar taka in kuma yau zaka tafi tom. Bin bayan Umman tasa yayi yana qara nazarin yacce ya kalli idon Ummansa mai ya same ta? Mai ya hana ta zuwa tada shi da asuba kaman ko yaushe? Zama yayi a gefen Abban sa a kan tabarman ta yacce zai ke kallon Umman tasa da kyau. Kunun tsamiyan da ya gani a kofi ya ɗeba ya fara sha, kallon sa Abba yayi yace "yau kuma kunu za'a sha kenan rogimammen Umman sa" Umma ta murmusa ta ce "a qyale mun yaro komai ma yake so in dai akwai tom yasha, Jarumin Umman sa sha abunka dama wa kai nai wa kunun. "Ummata tafiyan nawa ne har ya sanya idonki kumbura da ja haka? tambayan da Amjad ya jefowa Umman sa wanda bata yi tsammanin ji ba, Abba da ke shan ruwa zafi ajiye kofin yayi a take ya kalli Umma ya kalli Amjad, kamun Umma tayi magana Abba yayi saurin cewa "jarumin Ummansa idon Ummanka ke ciwo". "Abba ciwon ido dai? tun yaushe haka? Abba ka kalli idon Ummata fa yacce ya kumbura yayi ja kaman wanda yayi kuka, Abba akwai dai abun da Ummata ke ɓoyemun ko kuke ɓoyemun duka, ko dai Umma bata son tafiyan ne na haqura? Ya faɗa fuskan sa na nuna da gasken yake zai haqura. Umma tace "jarumin Umma idona kawai ke ciwo, ka karya ma kasamu kaje ka gano surkar ta in ya so sai kayi shirin tafiya. Shiru Amjad yayi bai ce komi ba, ba don ya yarda idon Umman tasa ke ciwo ba kawai yasan dai wani abu ne suka ɓoye masa, ya san Umman sa duk in yace zai yi tafiya na kwana biyu in dai ba jeji ba Tom hankalinta baya kwanciya har sai ya dawo, ya rasa mai yasa haka? Kuma bare wannan karon da zai je qasa ne wanda bai sani ba bai taɓa

Chapter 12 of 25