warke zai tafi
Ameerah ashe niba uwarki bace da baxaki faɗamun ba ko Abbanku amma de ya maki kyau daga ke har mijin naki
Umma Kashe wayanta tayi ranta a ɓace
Ameerah ce ta qirata ɗauka tayi tace "Yanzu kuma me kika qira kicemun?
Qasa tayi da murya kiyi haquri Ummata amma akwai phone number ensa a wajan Daddyn little
Shikkenan naji yanzu ina ya tafi? kwashe duk yacce suka yi da yayanta amjad en tayi ta faɗa ma Umma
Yanzu Ameerah rashin hankalinku da rashin tausayinku yakai haka dama mutum besan kowa ba tunda Allah ya haɗa ku ta sanadin hatsari ai seku temaka masa shima nan gaba sai kuga da ikon Allah ya temaka maku ko wa wani naku
Baisan kowa a Bauchi ba so kuke yaje yai ta tangariri agarin bauchi ko?
Nagode maku Ameera
Umma kiyi haquri Allah nace ya bari muzo tare yace a'a time nasa kaɗan ne
shikkenan yayi kyau Allah tsare sa ya basa sa'a
Haquri Ameera ta qara bawa Umma
Umma tace "Bakomi" sallama suka yi ta kashe wayan ta
Numbern Abba ta nemo ta qira
Ɗauka yayi "assalamualaikum hajiyata ya akayi ya gida"
Yallaɓoi kasan me yaranka suka yi
A'a sai kin faɗa maman yarana
Kwashe yacce suka yi da Ameerah tayi ta faɗa masa
Subhanallahi yanzu shi mijin nata biyewa shirmenta yayi? To shikenan Insha Allah zan qira mijin nata ya turoman numbern yaron in yaso sai na turawa Abdul ya kaisa gida ko ina fatan hakan yayi maki Hajiya ta
Allah qara girma yallaɓoi hakan yayi sosai ma, Allah shirya mana su sukuma Allah barmun kai
"Ameen hajiyata" Abba ya faɗa yana murmushi
Ɗan hiransu suka yi na masoya
Insha Allahu nima nan da kwan 2 zan dawo hajiyata dan nayi kewanki
Amma mai za'a ajiyemun haka aka damu na dawo?
"Kaima dai yallaɓoi ka sani dolema a tanadar maka abu mai daɗi koda kaman ruwan roba ne( faro)" Umma ta faɗa tana dariya
haba dai hajiyata wannan kam kice nai zamana nasha anan kawai sai dai ko acemun yar buduwar matata ta ajeman kanta
Zaka sani jin kunya yallaɓoi har da jikanne nake budurwa?
a'a nikam a wajena matata ƴar shawal-shawal take kaman ƴar 18 years
Dariya tayi yallaɓoi banda zugi fa kar kasa kai na ya fashe ba jini
Dariya suka sa duka sukai ta hiransu gwanin sha'awa har suka yi sallama.
Itama Umma hawan gadon tayi takwanta gefen Maha da ta jima da yin bacci...
washegari da sassafe ya tashi, bayan an kawo masa abun kari a gidan wannan mutumin karyawa yayi ya gode yace ze wuce
Rakasa wannan bawan Allah yayi suka yi sallama yana qara masa godiya sosai
Gaba ɗaya sai kuma ya rasa ta ina zai fara neman wannan bishiyan
Tambaya zeyi ne ko yaya? a haka dai ya samu wani bawan Allah yayi tambaya jejiin garinnan babba
kowa ce masa yake kawai ya shiga jejin dan ba nan kusa bane
Ya shiga jeji-jeji sosai sunfi a qirga dan kwanansa ɗai-ɗai har 5 amma bai samu itacen nan ba.
Mahreen gaba ɗaya ita da ya Abdoul sun zama layla da majnoon qarfi da yaji
Yayinda Maha da soja abun nasu de sai du'aee kullum kaman wuta da auduga haka suke
Yau Abba zai dawo bayan kwana biyar da aka qara masu a aikin nasu
Me aiki ta gyara gidan tsaff sa qamshi kawai ke tashi, kitchen kuma tare da su Mahreen da Maha aka yi komi
Bayan sun gama sun kammala komi kowa ya wuce dan ya shirya
Sunyi wanka duka Maha tawa little ma wanka duk sun shirya kowa yayi kyau
Umma tayi ado cikin dogon rigan swissless blue black tasha sarqanta da kunnenta na gold karkuso kuga kyawun Umma kaman wata Amarya, sai ka ranste bata haifi soja da Ameera ba
Futowa falo tayi ta zauna sai qamshi take
Maha ce ta fito ɗakinsu tana isowa palorn tace "Rassss Ummata kyau haka ai sai kisanya Abba kasa haquri ya huta"
Umma amma kinsan me saura abu 1 makeup kizo muje namiki Allah zaki ganki Amarya sak kawai
Murmusawa tayi ta mata danqwalo, Yau kuma nice abokiyar wasan taki doter?
Umma bafa haka nake nufi ba
Suna cikin hiransu basu ko ki dirin motorn Abba ba sai sallaman sa tare da Soja da little
Ayoyo Abbana da gudu Maha ta rungumesa
Doter an girma ba'asan an girma ba zaki karya Abban naki ai
Dariya tasa Abba inna karyaka dole a aikani aikin soja na karya soja
Shafa kanta yayi Allah maki albarka uwata.
Umma kuma zuba masu ido tayi kawai sai murmushi take
Abbane da suka haɗa ido ya kashe mata ido guda 1 kauda kai Umma tayi tana dariya qasa-qasa
Haurawa sama Abba yayi ya nufi ɗauki ganin haka sai Umma ta tashi tabi bayan sa
"Su Umma miji" inji Maha tana dariya
Buge mata baki Mahreen tayi wai ke iyayenki ma abokanan wasanki ne ba wanda kika bari
Abba na isa ɗakin yana juyawa kallon qofa sai sallaman Umma, Buɗe hanu yayi da sauri Umma ta faɗa jikinsa suka rungume juna
Hajiyata kinyi kyau na sayi wankan nan tabbas irin wannan haɗewa haka ina ma zan iya kallon kowa
Murmushi tayi shikkenan yallayboi wanka ta biya kuɗin sabulu
Umma taya Abba tayi yayi wanka
Ya shirya suka fito suka yi qasa dan yaci abinci
Abba ne yace "nifa a qasa zan zauna"
Abincin suka kawo qasan da komi duk zaama suka yi Umma tayi saving mijinta
Sunacin abinci suna fira
Kwarewa Maha tayi, da sauri kankowa ya motsa Soja ya miqa mata ruwa dan yafi kusa da kofin ruwan
Amsa tayi tasha kamun taji normal sannu kowa kece mata
Bayan sun kammala cin abincin
Abba ya kalli Soja wai son yaushe ne zaku Cairo en ne ko turkey kace?
Sosa kai yayi Abba nifa ba lalllai naje ba gaskiya
Ko meyasa son?
Abba kawai banson nisa da gida ne gaskiya
Shikenan fyne Allah temaka.
Tashuwa Abba yayi to kuyi hira lafiya ba naje na kwanta na huta gudnyt koh yaran kirki
Bayansa Umma tabi ta tayasa rage kayan jikinsa
Kwantawa Abba yayi, Umma zaunawa tayi a gefen gadon
Kallonta yayi lafiya tawan ba kwanciya zamu yi ba ko dai akwai wani abun ne?
Bakomi yallaɓoi
Uhmn yauwa nace ka amshi numbern ne?
A'a ban amsa ba kin san sai a hankali sungulloli sun man yawa
To Allah ya temaka my yallaɓoi
Yanxu ki qira mijin Ameeran ya turo bacci nakeji
Tom yallaɓoi ɗaukan wayan tayi ta fice a ɗakin duka
Qiran Daddyn little tayi suka gaisa shima ta balbalesa kamun suka shirya tace ya turo mata layin yaronta, Haquri ya bata a take ya tura mata layin.
Ganin layin ba qaramin farin ciki tayi ba shiga kan layin tayi tai...............
Muje zuwa fan's ✍️
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
𝘿𝙪𝙠 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙩𝙖/𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙪𝙮𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙗𝙖
𝘿𝙪𝙠 𝙠𝙪𝙨𝙠𝙪𝙧𝙚𝙣 𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙖𝙞 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙮𝙖𝙛𝙚𝙢𝙪 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙗𝙖𝙢𝙪 𝙞𝙠𝙤𝙣 𝙖𝙢𝙛𝙖𝙣𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞
𝙒𝙖𝙟𝙖𝙣 𝙠𝙪𝙨𝙠𝙪𝙧𝙚 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙢𝙖𝙣𝙖 𝙗𝙞𝙟𝙖𝙝𝙞 R𝙖𝙨𝙪𝙡𝙪𝙡𝙡𝙖𝙝𝙞 SAW ❤️
🅿️ 53&54
💋💋 امى بتولة💋
Abdoul ne zaune a ɗaya daga kujerun dake palourn kakar tasu, kujera me zaman mutum ɗaya 1 yana danna wayan sa. Hayrace tazo tawuce sa tana "Babban yaya sannu da zama halan yau kazo gadin kakus ne?"
Ke dai bari kawai boɗɗi Kakus hukuma ce sai da rarrashi, tace "tom nide nayi kitchen yaya kamun ta fito ta balbaleni ban gama girki ba rana tayi
Dariya yayi yace "keda kakus kam sai Allah kullum faɗa amma bata iya kwana bata ganki ba wataqil in mun aurar dake tare mijin ze aureku" Caraf sai a kunnen Amarya wacce ke fitowa yanzu daga ɗaki tace "Yo inba sinqin shishishigi shigilitu da sa ido irin naka ba ina ruwan ka tsakanina da baiwar Allah, Allah ne ya haɗa jininmu atou kuma qarshe ko mutuwa tare zai ɗauke mu bare miji da daman wannan dolen sa ne in dai ba'a tangaɗe aka haife sa ba ba mai raba mu" wucewa kitchen Hayrat tayi ba tace qala ba sanin halin kakar tata, ai kuwa dai bata stira ba dan kakus bin bayanta tayi da harara tace "kinanan a wajan kaman tangaɗaɗɗen budurwan kaza, ai da karma kije kiyi girkin yo ai ni dole ma na biki gidan miji kar kije kimana abun kunya tunda de baza kiyi abuba sai ance kiyi dan tsabar layiii" da ta gama ɓaɓatun zama tayi a kujera me ɗaukan mutum 2 tana bismillahi ni jikan mutum 4, Abdoul ne ya kalleta sannu da fitowa uwargida ta bayan ke babu wata sai dai amarya ya qarisa yana dariya
Da har ta washe baki sai kuma ta stuke bakin kallonsa tayi tace "Yau ɗan nan har yaudaran yakai haka a gabana kake faɗan sai de amarya? Tom jeka na yafe maka ka kawo badon halinka ba ɗan kwal uba"
Murmushi yayi shiyasa nake yinki amarya uwargida, gaisheta yayi ta amsa tana tambayansa ya aiki ya kishiyanta?
Murmushi yayi ai maganan kishiyan naki ma shi ya kawoni Hajiya Kakus tamu، Yauwa dai ango ai ni nafison haka kuyi aure tun da raina inga yaranku Allah raya ku ya baku zuri'a mai albarka, nifa so nake kan na mutu naga har da tattaɓa kunne na kaga ƴar albarka takwarata matar auwalu har cikin na biyu gare ta kaga da yardan Allah in ta haifi mace kan na mutu zan aurar da yarinyan, Murmushi Abdoul yayi yana jin shirmen kakan tasu bai ce komi ba shi dai .
Yauwa to wacece kishiyar tawa ma tukunna insan wacece ta shirya kishi da mairama daso, Murmushi yayi yace "wata baiwar Allah ce nutsaststiya kyakkyawa ga hankali ga ilimi ga tarbiya ga asali ga ga ga........."
Me amarya zata yi in ba dariya ba Abdu lafiyan ka ko dai duk ta tangaɗar da kai ne ta zautar mun da ango tun yanzu ta mallakemun kai, murmushi yayi haba de ai ni dake mutu ka raba, Tom irin wannan lissafowan haka ko kunya na baka ji ba yo ma ai ka rage dan ganin idona kar nayi kishi nace a'a ko, Murmushi yayi ai kema kinsan kin fita komi amarya uwargida kuma duk a wajanki ta gado su, washe baki tayi Allah maku albarka jikokina Allah sanya alkhaeri, da Ameen ya amsa yace "Kakus ba kowa bace face...
Maganan hayra ne ya tsaida shi tace "ya Abdoul yi sauri ka faɗa na matsu naji wacece akewa yabo ba kunyan kakus Allah yasa dai wacce nake tsammani ne"
Danqwalan ta kakus tayi to ƴar kwal uba haɗasu kasa rabasu bazaki shiga tsakanin mu ba kuma baza'a faɗa ba tafi ki bamu waje gulmammiya kawai, taɓe baki hayra tayi tace "in tayi tsami za muji" ta wuce abinta
Yace yauwa kakus AISHA ce fa MAHREEN
Guɗa Kakus tayi tare da kabbara tace "ALHAMDULILLAHI Allah nagode maka ni mairo, amma naji daɗin wannan batu Allah maku albarka Abdu, a Yauwa kaga ina ma wayana ne laluɓosa tayi ta miqa wa Abdoul tace "gashi dannamin layin ita uwar tasu tunda ta balaga ta balage garin su ba abinda ake koya masu sai tangaɗi bata neman albarkan uwarta to ni uwarta zan nemi albarkanta ƴar jakar uba kawai"
Qiramun ita in bazata zo ba ni zan iya zuwa har qasan masu layiin inba ma tsabar tangaɗe wa ba asawa gari sunan mutum wai fa sunan uwata sunan garin nasu tom dai bazai hanani qira ba, qasan kulu masu tangaɗaɗɗiyar hali suna koyawa yaran mutane fitsara da rena iyayensu wannan baqin halin har ina ni Mairo ɗan nan qiramun ita da wuri
Karɓa yayi haba kakus surka tace fa kibar zaginta nikam
Au ashe surkar ka ce? tom ban sani ba hanani faɗan abunda nayi niyan faɗa dan kwal ubanka jai'ri kawai ina ruwanka ni da ɗiyata inma me nace wani ya haifarman ita ba dai nice na haifi abata, shekara nawa ban sata ido ba ba dole abun ya dameni ba tunda zuciyata ni ba irin na ƴan kasar su bane, ita fa kaɗai gareni ɗiya mace, tom don haka karka shiga tsakanina da ƴata yar albarka
Murmushi yayi dama abunda ya sashi saka baki kenan ta dena mita gashi hartasawa ummeyhn tasu albarka
Numbern Ummeyh ya dubo ya qira, yana shiga aka kashe aka qira.
Miqawa kakus wayan yayi Kinga ma ta kashe ta qiraki gashi kuyi magana to
Yanzu dan tsabar ka renani baka ganin girma na ni uwar ubanka shine bazaka ɗaukan mun qiran ba na ɗauka da kaina dan jakar uwaka bazan ɗauka ba to
Ɗauka yayi da sauri gudun kar qiran ya yanke "Assalamu Alaiki gwaggo"
Amsawa tayi ah ah yaron gwaggo sai yau ake jinku kenan nasan yau ma albarkacin uwata aka qiran ko?
Sunkuyar da kai yayi yana sosa qeya ayi haquri Ummeyh abubuwan ne sai a hankali, Ummeyh taace "Bakomi yaron Gwaggo" gaisawa suka yi yace mata "ga kakus" ya miqawa amarya wayan
Amsa wayan Amarya tayi bayan ta karkata ɗaurin kwalinta
Sallama Ummeyh tayi kakus tace "bazan amsaba dan gidanku wato de Jamila kin girmi neman albarkan uwaki sede ni na nemoki bazaki iya zuwa ki ganni ba bare gaisuwa kema kinbisu kun taru kun tangaɗe kunzama tangaɗaɗɗu masu layi to yayi kyau ni Mairo bazan maki baki b Allah shiryaki y maki albarka, amma nasan wannan balaraben mijin naki baze hanaki zuwa ba dan hankali garesa ga sanin girman iyaye tunda dai yaron nan habu har yamun takwara, Ammade Allah ya shirya mun ku wallahi.
Ummeyh najin ta bata ce komi ba har ta gama magana sanin halin mahaifiyar tata "Kiyi haquri Gwaggo Insha Allahu bazan wuce kwana 2 ba zaki ganni" Ummeyh ta faɗa cikin ladabi
Yauwa dai yar albarka ko kefa ni shiyasa nake sa maki albarka kullum ko baki nema ba dan kinfi sauran jin maganata Allah de ya maki albarka ya rabaki da tangaɗewa har abada
Ta amsa da Ameen suka yi dan hira sama-sama can suka yi sallama kashe wayan tayi ta aje, qwalawa hayra qira tayi "Harirtu qawar kakus kawo man ruwa nasha ƴar albarka bakina sai zikiri yake duk sun bi sun sani surutu kaman kanari"
Hayran ta shigo da sallama ta miqo mata ruwan ta karɓa tasha, Abdoul ne ya murmusa yace "yanzufa kika koreta gashi da kanki kin qirata" hararan sa kawai Amarya tayi bata ce masa komi ba. Abinci hayra ta shirya masu suka wuce dinnig kowa ta zuba masa, cin abincin suke bame cewa komi
Sede kakus da bakinta baya shiru kana ganin bakin kasan akwai abunda yake son cewa..
Bayan ya turo mata layin ɗauka tayi ta qira amma sede be shiga ba ta gwada yakai sau uku 3 amma baya shiga akashe take ji, hankalinta ne ya tashi sosai dan haka kawai take jin kaman ba lafiya ba, dafe kai tayi tana ambaton sunan Allah "Ubangiji yasa ba wani abun ta sameka ba yarona" sai kuma tunanin ɗan ta yafaɗo mata rai nan take hawaye ya cika idonta jin kaman mostin mutum ya sanya ta saurin sharewa ta seta kanta, Mahreen ce ta shigo palourn zuwa wajanta tayi da sauri tana cewa "Ummanmu lafiya? Mai ya faru?"
Murmushi tayi bayan ta ɗago kai tace "lafiya lau doter kawai na qira wani layine auntynku Ameera suka turomun sai de bai shiga ba" Mahreen tace "to amma Umma tagumi ba kyau ki dena kinji Insha Allah lafiya lau layin kuma zai shifa kibari anjuma ko gobe ki gwada inyaso in bai shigaba sai ki qirasu ki faɗa masu ko zasu qira maki layin ko Umma"
Shikkenan doter ina Auntan Ummeyh fa? Tana can ɗaki da waya banmasan me take ba, Umma tace "to je ki qiramun ita" tashuwa Mahreen tayi tana to Ummanmu
Wucewa Mahreen tayi ɗaki dan qiran Maha, Umma Qiran aminiyar ta ne ya shigo wayanta ta ɗauka suna gaisawa da alama magana me muhimmanci suke yi.
Mahreen bayan ta shiga ɗakin ta samu Maha akwance tana danna waya, fisge wayan tayi tace "wai me kikeyi ne awaya kam maha?" Turo baki Maha tayi tace "ni don Allah ki bani kar ki batar dani inda nake abu ya ɗauko daɗi" Kallon fuskan wayan tayi ta kalli Maha mene wannan kuma? littafi ne? Maha tace "eh novel ne wallahi Adda kuma me shegen daɗi"
Kallonta tayi tace "ooh kekam da novel bansan waya koya maki karantawan ba ma ni Indo"
Allah kema Adda Mahreen in kin fara karanta littafinnan ba zakiso ki tsayaba ga abun tausayi ga darasi aciki ga daɗi kuma ayya barin ma maisunana ta cikin ɗayan littafin abun tausayi bakiga Yacce mamanta take treating nata ba, Kallon Maha tayi tace "to yanzu dai faɗamun sunan littafin dai ko"
Guda biyu 2 ne aka turomun masu shegen daɗi kekam ma ba'a gama labarin ba tukun ɗayan dai sunansa JAHILCI KO AL'ADA ɗayan kuma something maita ne ko me na mance amma Adda kinji daɗin littafin nan kuwa wallahi ya burgeni, murmushi Mahreen tayi ai kuwa zan karanta nima ba na samu zama
( KUMA FAN'S KARKU SAKE A BAKU LABARI DOMIN KUWA DA ƊUMIN SA YAZO
JAHILCI KO AL'ADA?
VERY SOON ZA'A SAKE MAKU SHI
𝙊𝙪𝙧𝙢𝙢𝙖𝙝𝙣 𝙗𝙖𝙩𝙤𝙤𝙡𝙚𝙧𝙝🔥 𝙛𝙤𝙧 𝙡𝙞𝙛𝙚 )
Tom yanzu tashi muje Umma ce tace na qiraki, tare suka fice a ɗakin sukai palourn wajan Umma..
Kakus ce a hakimce a kujera baba qarami na zaune a qasa, gaisheta yayi ta amsa fuska a sake "Allah maku albarka yaran nan kuma Allah sa yaran ku su maku biyayya su kula daku fin yacce kuke mun nide aihuwa tamun rana Alhmdlh sai kuma ta ja gefen ɗan kwalinta tana fece hanci ga hawaye "Allah sarki malam ina kake dai kaga yacce yaranmu suka zama da jikoki, qara fece hanci tayi Allah maka rahama Allah sa ka huta". Da Ameen baba qarami ya amsa
Share hawayen tayi tace "Yauwa dama akwai maganan da nake so muyi dakai amma ya kamata sai yayanku ya shigo In da son samune da qanwarku amma tunda nasan halinta itakam ta fistare qafanta tangaɗaɗɗiyar garinsu sun koya masu rashin neman albarkan iyaye to taje can ta qarata ku kuma tunda kuna storon ta tafi qarfinku to sai kuci gaba dayi karku daina manyan wofi, nasan ba lallai mu ganta ba dan haka dakai da Harunan zamu yi maganan in yayi sai ka qirasa yazo shima ɗayan tangaɗaɗɗe mata ta mallake sa sai yanda tayi dashi wai shi soja ko zuwa gaida uwar sa baya yi sai aturo wannan a turo wannan sai kace nace masa kuɗin sa nake kwaɗayi in bai sani ba tun kan na auri ubansa komi inada"
Baba qarami dai kansa na qasa ba abinda yake sai aikin bawa Amarya haquri dukda dai yasan ba laifin da suka mata har qanwar tasu ma aure ne ba laifinta ba
Amarya ci-gaba tayi da surutun ta "ita Jamila In yaso in tayo wa kanta tazo in kuma neman albarkan uwata ya isheta sai tayi zamanta can taita ganin larabawa, shi kuma Haruna zai zo ya sameni dani yake in yayi wasa sai ya qara Aure kuma budurwa inga ta stiyan matan tasa, Murmusawa baba qarami yayi yace "Allah huci zuciyanki gwaggo a qara haquri damu"
Hararansa tayi tace "Ni karka sa mala'iku su amsa su rubutawa ɗiyata zunubi ni bana fushi da diyata haka ma yarona Haruna ɗan albarka, kana wani Allah bani haquri ya huci xuciyata ni banson haɗa uwa da ɗanta na hane ka da halin nan, kaga Haruna ai ba abinda zance wa wannan yaro sai Allah sanya mun shi a Aljanna ai matar sa Aminatu har aljannah Insha Allahu ita ce uwar gida dan dai ance akwai kyawawan ƴammataye acan (hurul eyn) da zance ko a aljanna bata da kishiya dan tafi hafsatu da saratu hali mai kyau Waɗan nan matan naka masu sinqin rashin mutunci ai dai amadu kullum da tausayinka arai nake kwana nake tashi" sai kuma ta fece hanci, amadu dole na dai na nemo maka mata ko nan qauyen su mijin Jamila ne ka gansu kyawawa ƴan Adamawan nan, oh ni Mairo baki na dawo kar yaran nan su jiyo ni su nemi kasamun halinsu. Baba qarami yace "gwaggo aimana afuwa baza'a kuma ba in Allah ya yarda kuma Yacce kike so haka za'ayi"
To Yauwa ɗan albarka Allah dai ya maka albarka amadu na Allah shiryamun ku duka ya qara maku albarka.
Dama na qiraka ne maganan Ango na Abdu da ƴar wajan qanwar taku menene ma sunanta ni bana riqewa sunje sunsa masu suna kaman na ifiritan aljanu kai dai babban A'isha takwarata maman habu, baba qarami yace "eh Gwaggo na gane ta menene ya faru?" Nan Amarya ta kwashe komi ta faɗa masa yayi murna sosai a haka suka cigaba da hiran nasu..
Yau take Laraba wanda yayi dai-dai da auren Gimbiya saura sati 3 da kwana 2 shiri bana wasaba akeyi kota ina shiri ake a masarautan sai qawata masauran ake duk da yake dama a qawace yake ko ina ka leqa kasan bikin namasu garin ne, Dukda kasancewar sarauniya ba lafiya hakan bai hana ta sanya jakadiya kuma amintacciyar baiwanta nemo me gyaran jiki ba dan agyara mata ɗiyar tata gyara na manyan mata gyara na kece reni
(Koba makeup ai mune kyau in aka qara da gyara kuma akwai babban tashin sense Gimbiya mehwish🤣).
Abba, umma, Maha, Mahreen da little dukansu zaune suke a babban palourn gidan suna kallon arewa 24 ana maimaicin shirin gidan badamasi, Maha tace "wallahi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 25