samu ba kuma zuwa gobe Inshà Allah ku dai ku kula sosai kunji"
Mahreen tace "Inshà Allah Abba Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" duk aka amsa da Ameen.
Waje suka nufa duka har parking space suka raka su, Umma da Ummeyh suka shiga baya soja ya shiga mazaunin driver Abba ya zauna a kujeran gefen sa, Soja yaja motor suka fice a gidan.
Kaduna state airport suka nufa, ko da suka je Private jet da yake kusan mallakin Abba wanda wajan aiki aka miqa masa dan tafiye-tafiyen sa, shi suka shige jirgin nasu ya ɗaga sai Bauchi shi kuma Soja ya ja Motorn ya juyo gida.
Abdoul ya ɗan sha tafiya dan anguwan da ya masa kwatancen musan qarshen gari, ko da ya isa sanda ya qara qiransa ya haɗa sa da malam liman ya masa kwatancen da kansa da qyar har da tambaya kamun ya samu ya gane gidan, yana isa parking yayi a qofan gidan ya ɗau waya ya qira Amjad.
Qiran Abdoul ya shigo wayan sa ɗagawa yayi yace "ka iso ba? Dan naji qaran motor". Abdoul yace masa "eh ina qofan gida" Malam liman qira ya kwaɗawa ecleemah.
Da tazo yace "ta ɗau jakan Amjad ta kai waje" Amjad yace "Allah gafarta malam tayi hutawan ta zan ɗauka, Qanwata ki koma ciki abunki zan ɗauka".
Ecleemah bata saurare sa ba tabi umurnin mahaifin ta jakan ta ɗauka tayi hanyan waje malam liman da Amjad suka rufa mata baya.
Qofan back seat Abdoul ya buɗe mata ta saka jakan da ta ɗauko kamun ta juya idonta cike da qwalla tace "yayana Allah tsare hanya ya kaika lafiya" tana gama faɗa ta shige gida bata tsaya ko jin me Amjad zai ce ba.
Bin bayanta yayi da kallo har ta shige sau kawai yaji wani irin, maganan malam liman ne ya sanya shi Juyowa da barin kallon qofan shiga gidan. Malam liman yace "yaro kaga kalman da ake cewa baqo raɓa ko gashi a jiya zuwa yau har za muyi kewanka kaman kar ka tafi amma kuwa ba dama sai dai mu bika da addu'an Allah kaika lafiya Allah kuma yasa andace kenan" Da Ameen Amjad ya amsa sai yayi qasa da kansa kawai.
Malam liman suka gaisa da Abdoul cikin girmamawa sai yace wa Amjad "bawan Allah ka shiga ku tafi tafiyanka ba na ɓata lokaci ba" ya buɗe baki zai yi magana sai malam liman ya ɗaga hannu yace "karka damu da komi kai dai ka shiga kuje" juyawa yayi ya shiga mazaunin gefen driver Abdoul ya zagaya ya shiga mazaunin driver suka wa malam liman sallama Abdoul yaja motor, malam liman yana ɗaga masu hannu har Motorn nasu ya ɓace a layin nasu gaba ɗaya.
Juyawa malam liman yayi ya shige gida cike da kewan baqon nasa na kwana ɗaya wanda kuma yana tunanin qara haɗuwan su wataqil sai kuma a qiyama.
gaisawa Abdoul da Amjad suka yi wanda tun da Amjad ya shiga Motorn yake jin gabansa ya tsananta faɗuwa, Abdoul kallon sa yayi sai yace "bros ina muka nufa?" Amjad yace "airport zaka kaini" Abdoul ya kuma kallon da ya kalli hanya yace "haba dai airport ba zaka je gida ka gaida Amarya ba? Am Amaryan ina nufin kakata gaskiya ya kamata kaje ka gaida ta inba dai kayi booking Flight na safe ba".
Amjad yace "nop banyi booking Flight ba yanzu dai in munje zanyi sai na jira, Amarya kuma inka koma kace wani jikanta na gaida ta sai wani lokacin zanzo". Murmushi Abdoul yayi ai tunda ba kayi booking jirgi ba gaskiya daganan sai gida ba wani airport da zamu ai in bankaika gida ba yau ba mai kwata na a hannun masifaffiyar stohuwar nan, kwashe yacce suka yi da Amarya yayi ya faɗa wa Amjad yana dariya. Amjad sai da ya Murmusa jin rigiman stohuwar sai dai kuma har yanzun faɗuwan gaban sa na yawaita, da Abdoul ya dage ba yacce zai yi qarshe yarda yayi ba dan yaso ba amma bai qudiri aniyan kwana ba yana zuwa ya gaida mutanen gidan su Abdoul ɗin zai kawo sa airport ya samu ya shirya komi na tafiyan sa yau ɗin nan.
Abdoul ne jin yayi shiru yace "bros ya kayi shiru? Maganan tafiya yau fa kabar sa dan anan kam ba lallai ka samu Flight direct to Qatar ba sai dai ko in zaka hau na Abuja daga can to sai ka samu na Qatar kaga kuma duka long process ne gashi yanzu rana ya fara ka bari kawai anjuma kayi booking anan sannan mijin Ameera ya maka na Qatar ɗin in yaso d sassafe ka tafi ko in ansamu na dare sai kabi na Abuja da yamma da dare kuma ka hau na Qatar ɗin" Amjad ba yacce ya iya haka ya aminta suka nufi GRA.
Amarya sashen baba qarami ta shiga tana bambami, kai jama'a Allah raba ɗan mutum da wahala yo in ba wahala da tangaɗi ba ace wai jikanka ya mai da kai birin wasa ai wannan ba ko kaffara uwar sa ke kista masa hmm! Shi uban kuma da yake maloho tangaɗaɗɗe baya iya stawatar wa an mallakesa ni Mairo na shiga uku an raba ni da yara na. Baba qarami da ke zaune a palourn mama hafsatu yana aiki a system nasa kasancewar yau yayan sa na hanya shiyasa bai fita aiki ba, muryan mahaifiyarsu da ya jiyo ne ya sanya shi rufe system ɗin ya miqe ya nufa hanyan babban palourn da yasan bazai wuce tana can ba.
Tarar da ita yayi tsaye tana share hawayen da babu shi da gefen hijab nata, baba qarami na isowa har qasa ya durqusa yace "Gwaggo ina kwana antashi lafiya?" Wani kallo Amarya ta masa sai kuma ta fece hanci tace "yanzu ba dan ubanka mijina bane kuma ya rasu bawan na kwance cikin rahamar Ubangiji yo da sai nace dan jakar ubanka, amadu ban kwana ba kuma in mutuwa nake na rashin lafiya ba to ba ruwanka,kullum faɗi nake ka riqe azkar da salatin Annabi za ka fi qarfin duk wanni stubbace-stubbace amma dan tsabar lalacewa da tangaɗewa yaron nan ba kayi, amadu baka neman albarka" baba qarami dake stungune a qasa ba abinda yake cewa sai "Gwaggo ayi haquri a yafeni".
Mama hafsatu da ke qarasowa palourn ne tace "Alhaji ai ba haquri zaka bada ba tambayan me kayi zaka yi" Amarya kallonta tayi sai tayi qwafa za tayi magana sai baba qarami ya riga ta "ke Hafsa banson rashin hankali".
Amarya tace "a'a karka sona amadu ba laifinta bane ai komai tace kai ka nuna masu ba dai baka neman albarka ba?"
Mama saratu ta qaraso palourn itama tace "Gwaggo Barka da shigowa ki zauna mana". Kallonta itama Amarya tayi sai kawai ta sa kuka "yanzu amadu fistaran da kuke shuka mun kai da matanka har ya kai haka? Wai ni da gidan Yaro na sai ance na zauna da uban wani ya gina masa gidan to banson shishishigi shigilitu, amadu kai dai Allah staremun kai amma mata sun mallake mun kai ai daɗi na da Haruna kenan bawan Allah gashi dai mace ɗaya gare sa kaman mahaifin sa amma yafi qarfin gidan sa yanzu dan stabar ba mai ganin girmana a gidan nan ace yaranku ma kun hure masu kunne sun fistare qafafunsu sun ɗauko baqin halin ku" baba qarami jin haka to yasan tabbas wani abun Abdoul ya mata dan in hayra ce ba mai jin tsakanin su suyi faɗan su su shirya acan ba mai ji amma in ta shigo tana faɗa tom indai yara ne Abdoul ne ya mata abu ko kuma Autan ta Jamila.
Ajiyan zuciya baba qarami ya sauqe yace Gwaggo kiyi haquri Insha Allah zan ɗau mataki kiyi haquri ki zauna, Amarya kujera ta samu ta zauna har da ɗaura miqe qafa tace "tunda kana neman albarka har da haɗa ni da Allah tom na zauna Allah maka albarka amadu na Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanzu dai amadu kaji storon Allah kaji storon haɗuwa da shi wai ace ba za ka yiwa yaranka faɗa ba ka nuna masu nice uwarka nice na haifeka sai sun kyautata mun nasa maka albarka kamun suma zasu samu kasa musu albarka su gama da duniya lafiya" ayi haquri Gwaggo Insha Allahu za'a gyara.
Ai nasan zaka gyara amadu wai ni zancewa Abdu ya jira ni na ɗauko lufaya muje aikin ladan tare amma wannan yaro da farantin goshinsa kaman na uwar sa tunda shina dai kaman hariran matar ubansu tana hure masu kunne tunda ita bata haifa ba ita ta mallake ku duka da kai da uwarsu da su ɗin dan kar kuyi albarka, yaron nan ya ja akwalan motar sa ya tafi ya barni tsaye riqe da lufaya kaman mata mai takaba yo Allah na tuba tun ba'a auri uwarsa ba na gama takaba na ja'irin yaro zai dawo ya same ni, du Allah miqo mun ruwa na jiqa maqoshi na duk yaro ya sani surutu maqoshi na kaman zai tsage bani ruwa na yayyafa masa".
Mama hafsatu da ke kusa da fridge miqewa tayi ai Amarya da sauri tace "haramun ni Mairo ban aike ki ɗibamun ruwa ba Saratu ƴar albarka tashi kiban"
Mama Saratu tashuwa tayi ta ɗauko ruwan ta bawa baba qarami yasa a cup ya miqawa Amarya ita kuma ta amsa ta kai baki da mugun sauri ta tufar da ruwa ta ɗaura hannu a kai tace "amma dai Saratu Allah shiryaki shi kawai zance maki kashe ni za kiyi wannan sanyin ruwan ai kurɓa ɗaya sai lahira, kinga Hansatu ɗiyata ƴar albarka bani ruwa nasha" mama Hafsatu ta miqo mata ta amsa tasha tayi hamdala.
Kallon baba qarami tayi tace "Amadu kai da matanka ni Mairo ba abinda zance muku sai Allah ya maku albarka Allah yasa kuma yaranku su kula da ku su muku biyayya Allah sa ku gama da duniya lafiya, amma ke Hansatu ki dena mun fistara in ba haka ba kwashe maki albarka zan yi ba naje na jira ja'irin yaron naku da kuka hure wa kunne yau sai ya faɗa mun sadakin uwar sa tunda ni zai ɗauka birin wasan sa ya tafi ya barni kaman stinkakken silifas" qarisa maganan tayi tana miqewa, baba qarami haquri ya qara bata Mama Hafsatu da Mama Saratu duka suma haqurin suka bata, tayi gaba suka bi bayanta suka nufi hanyan waje dukansu.
Amjad bayan zuciyansa dake stinke wa yanzu kuma da yaga sun shiga anguwan sai yana jin wani irin zafin wuta na bugun sa kaman yana tunkaran wajan da aka hura gunguman wuta haka yake ji, ga faɗuwan gaba ga kuma wannan zafin da yake ji yana tunkara.
Abdoul ne ya juya ganin yanayin sa sai yace "brother lafiya kuwa?" Lafiya lau amma Please in bamu kusa iso gidan ba mu juya.
Kallonsa Abdoul ya kuma yi mu juya kuma? Ga gidan nan fa banda waɗan can gate ɗin da kake gani wancan na gaban shine gidan. Amjad suna qara tunkaran gidan tururin wutan da yake ji na qara daɗuwa suna iso qofan gidan kuma kaman an kama masa maqoshi sannan ji yake kaman tsakaninshi da wutan da zafin sa ke damun sa bai wuce taku ɗaya ba.
Qofan fitan baba qarami ya buɗe ma Amarya ta fito shima ya fito mama Saratu ne ta fito itama Mama Hafsatu kuwa da ke staye a bakin qofan haka kawai sai taki kaman ana juya mata gidan jiri lokaci ɗaya ya kamata ha wani kukan jarirai da take ji ya cika mata kunne, dafa qofan sashen nasu tayi ta jefo qafan ta waje. Amarya da ke zuba surutu har yanzu kaman zata ari baki sun iso tsakiyan haraban gidan kenan mai gadi ya wangale gate sakamakon horn na motorn Abdoul da yaji.
Suna shiga cikin gidan tun bai qarisa parking ba Amjad da ya sanya hannunsa a wuyan sa sanadin jin shaqan da aka masa yayi yawa kuma kaman an jefa sa acikin wutan wani wawan qara ya saka wanda ya kusa da Abdoul sakin staring motorn, yana sakin qaran hannun sa a wuyan sa sai ya faɗo jikin Abdoul a matacce ba numfashi Ba shiri Abdoul yayi parking.
Wannan qaran ya razana duk wani halitta dake cikin gidan, Amarya da Mama Saratu san da suka kusa sakin fistari a staye duk suka rikice, baba qarami nufan Motorn yayi sai kuma suka kuma jin wani qaran a bayan su da kuma sautin faɗuwan mutun, waye za kuma su gani? Mama Hafsatu ce yashe a qasa. Amarya zama tayi dirsham a qasa gaba ɗaya ta rikice Mama Saratu kuwa ba'a magana, baba qarami qara juyawa yayi sai ya kuma jin....
Jirgin su Abba yayi landing a tafawa ɓalewa airport dake garin Bauchi, Abba waya ya ɗaga yayi qira shiru ba'a ɗauka ba, ganin haka sai ya tare taxi ya juya dan mawa su Ummey magana suzo su shiga sai kawai yaga Umma ta yanke jiki ta faɗi.....
TIRQASHI TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASA RANA KENAN!
CAKWAKIYA, SARQAQIYA GAMI DA ƊAUREWAR KAI.
WAI ME KUKE TUNANI?
ME KE FARUWA?
DUK ME YA JAWO WANNAN TASHIN HANKALIN?
ME YAKE FARUWA DA AMJAD?
MENENE YA SAMU MAMA HAFSATU LOKACI ƊAYA?
ME KUMA KE FARUWA DA UMMA?
DUK MENENE HAƊIN WANNAN TASHIN HANKALI DA YA SAME SU LOKACI ƊAYA?
INA LABARIN UMMAN AMJAD?
INA LABARIN GIMBIYA DA MAGANAN AUREN SU DA AMJAD?
ANYA WANNAN NE DALILIN FAƊUWAN GABAN DA KE DAMUN AMJAD?
IN BA WANNAN BA ME ZAI FARU GABA KENAN DALILIN FAƊUWAN GABAN SA?
ANYA MA KUWA AMJAD NA DA RAI?
TAMBAYOYI BARKATAI DAI
SANNAN ANAN NA KAWO QARSHEN FREE PAGE'S DOMIN SAMUN AMSOSHIN WANNAN TAMBAYOYI DA SUKE RANMU DA KUMA KUNCEWAR WAƊANNAN RIKITATTUN AL'AMARIN KUYI HANZARI KU BIYA NAIRA ₦300 KACAL DAN ACI GABA DA LABARI DA KU.
NORMAL PAYMENT GA WAƊANDA KE GROUP ALREADY ₦300
GA WAƊANDA BASA GROUP ₦400
GA MASU BUQATAN COMPLETE PAGE'S ₦500
V.I.P COMPLETE DOCUMENT ₦500 ONLY
TA WANNAN ACCOUNT
👇
2220553988
HARIRA SALIHU ISAH
UBA BANK 🏦
KO KATIN WAYA TA WANNAN LAYIN
09161720046 MTN
07015870735 AIRTEL
SANNAN ZAKU TURO SHEDAR BIYA TA WANNAN LAYI A WHATSAPP 09161720046
Ina mai qara baku haquri waɗanda tun farkon littafi suka biya sannan ina da babban garaɓasa gareku a next book namu da kuma baku zaɓi akan labarin da kuke so mu fara.
Ƴan uwa abokan arziqi masu daraja gaisuwa gare ku Ako da yaushe kuma ako ina kuke a faɗin duniyan nan daga taku har kullum mai nishaɗantar daku HARIRA SALIHU ISAH (UWAR BATOORL)
MARUBUCIYAR 🥀 𝐌𝐀𝐅𝐀𝐑𝐊𝐈 𝐍𝐀𝐇 🥀
YANZU KUMA 👑 𝐘𝐀𝐑 𝐒𝐀𝐑𝐊𝐈 𝐂𝐄 👑
Sannan da labarai daɗaɗa da na tanadar domin ku da nishaɗin ku.
Kar ku manta sunan labarin da muke ciki 👑ƳAR SARKI CE 👑 DAGA DAUSAYIN ALQALAMIN UWAR BATOORL 🔥
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
09161720046
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
07015870735
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 domin yanzu baya aiki both whatsapp and call.
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN
Anan na kawo qarshen BOOK 1 Wand yake a FREE BOOK
Masu buqatan ci-gaba BOOK 2 👑'YAR SARKI CE👑
Sai subi process da nayi magana ko su mun magana via WhatsApp number na
09161720046
Masu comments wasu bana samun yin reply afuwan abubuwan sai a hankali
Fatan alkairi a gare ku daga uwar batoorl taku
Sai mun haɗu da ku a book 2 fan's
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 25