mutum ya same ni dan wai shi jarumi ba sai dai dan ya cancanta ko in yamun, amma duk da haka ina burin auren jarumin jarumai, Allah ka tabbatar mun da alkhaeryh,amma a cikin waɗan nan bana jin akwai mijin aure na ni Ƴar Sarki Qaseem."
Haka aka shiga filin dagan domin fafata gasan, su ukun ne kaman yacce suka buqata ita kuma ita ɗaya, mai busan da ke nufi zasu iya farawa ne ya busa.
Sun fara faɗan abun gwanin burgewa ga daɗin kallo, dan kuwa faɗa suke bil haqqi, su uku sun dage ɗayan su sai yaci nasara. Ranta wasai take yin wannan faɗa ba ko alaman ta damu da kasancewan su har su uku ita ɗaya. Wani ne acikin su ukun ya nufi abun fuskan nata da biyan ya janye ganin kaman hankalinta yafi karkata kan Yarima Khaleed da yake jarumine na gaske kuma mayaqi yasan salo-salon faɗa da dama. Ai kuwa karaf ta kaiwa takobin nasa sara dan tana ankare da su dukan su ji kakeeee qasss qaqassssssssssssss har sai da takobin nasa ya ɗan lanqwashe, Jin saran da tai wa takobin nasa yayi kaman a hanunsa ta kai saran, dan sanda yaji kaman qashin hanun sa ya goce saboda qarfin saran. A haka suka ci gaba da fafata wa, ko wannen su na qoqarin samu ya kai hanun sa fuskan ta, koda da takobi ne. Yarima abdoul wanda aka kaiwa takobin sa Sara shine ta fara kaiwa qasa! Yarage Yarima Mu'azz da Yarima khaleed, ci gaba da fafatawan suka yi ba ji ba gani. A haka takuma kai yarima Mu'azz qasa! Ya rage filin su biyu Gimbiya MEHWISH da Yarima KHALEED. Fili domin su.......
🄳🄰🄹🄸
Tafiya yake akan dokin sa shi kaɗai, ba tare da jin storon girman jejin ko wani abu ba, tafiya dokin nasa ma yake a hankali, kalle-kalle yake yi, wanda da alama wani bishiyan yake nema, karatun Qur'ani yake yi qasa qasa yana tafiya akan dokin nasa, dai-dai wani babban bishiya da rasa gane na menene ya tsaya da dokin nasa, sauqa yayi ya shafa kan dokin yana masa magana "besty ka jirani ko ba na sari bishiyan nan nazo mu koma gida yau muga Umma" karkaɗa bindi dokin yayi yana miqar da kan sa, murmushi Amjad yayi yace "that's my besty dama nasan ka da jin magana, mintuna kaɗan ina dawowa." Qara sawa wajan bishiyan yayi ya sari jijiyan ya kuma sassaka bayan sannan ya ɗiba ganyen. Juyawa yayi ya koma inda yabar dokin nasa, a inda ya barsa nan ya same sa da murmushi ya shafa kansa ya haye saman sa yace "besty mu tafi ko" kaɗa bindi dokin yayi ya juya dan su koma gida. Juyawan da sukayi ido biyu yayi da......
Kan fafatawa suke tsakanin Yarima khaleed da Gimbiya Mehwish, sosai yarima Khaleed ya nuna Jarumta dan kuwa tunda aka fara gasan ba wanda ya nuna Jarumtan da ya nuna, ba tare da sun gaji ba dukansu. Ɗaga tokobin sa yayi da niyan kai mata sara kaucewan da tayi dan kare kanta, yayi amfani da daman ya kai hanunsa kan abinda tai rolling fuskan ta da niyan ya janye. Duk abinda yake Gimbiyar a ankare take, tana tare saran ta kuma yin qasa dan kaucewa hanun nasa domin hakan ne kawai kariyan da zata iya yi. Kaucewan da tayi ya sanya shi yin qasa ya faɗi domin da dukkan qarfinsa ya kai wannan harin, faɗuwan da ya janyo masa rashin nasaraa!!
haka duka ukun ta kaisu qasa. har Yarima khaleed!
Ba abinda kake ji yake tashi a wajan se ihun da jama'a suke yi suna qiran sunan Gimbiyar "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼" "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼" "𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼" 𝙎𝘼𝙄 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼𝘼𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃".
Iya sunanta kawai ke tashi bakin ɗauka cin jama'ar wannan wajan.
Fuskan ta ba abinda yake fidda wa sai walwalin murmushin ta!! Wanda inka tsaya kallon qwayan idanuwan ta ko ta kalle ka dasu tabbas zaka kusa sumewa! Ba tare da ta tsaya sauraron kowa ba ta wuce, dan mutumi mai magana ya tashi zai yi magana. Wucewa tayi dan nufan wajan da dokin ta yake tayi dan tafiya gida kuyangun ta suka rufa mata baya suna mata kirari! Sannan mutumin da ke riqe da Miche ma kirari yake Mata!
𝙈𝘼𝙇𝘼𝙈 𝙆𝘼𝙂𝘼 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼! 𝙆𝘼𝙇𝘼𝙉 𝙏𝘼 𝙆𝘼𝙇𝘼𝙉 𝘼𝙇𝙆𝙃𝘼𝙄𝙍𝙄! 𝙂𝘼𝘽𝘼 𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐𝙉 𝘽𝘼𝙔𝘼 𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐𝙉 𝙅𝘼𝙍𝙐𝙈𝘼𝙍 𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼! 𝙒𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃𝙄 𝙆𝙄𝙉𝙁𝙄 𝙌𝘼𝙍𝙁𝙄𝙉 𝘼𝙇𝙅𝘼𝙉𝙄 𝘽𝘼𝙍𝙀 𝙈𝙐𝙏𝙐𝙈! 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙅𝘼 𝙆𝙒𝘼𝙉𝘼 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼, 𝙏𝘼𝙆𝘼𝙒𝘼𝙍 𝙆𝙄 𝙇𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼 𝙁𝘼𝙍𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙁𝘼𝙍𝘼𝙍 𝘼𝙉𝙄𝙔𝘼.......
Kirari kuyangun nata ma ke mata! Daga qafa tayi da niyan hawa dokin nata amma sai dai me? Muryan mai martaba Sarki ne ya ziyarce ta, abinda taji ya faɗa ne yasanya ta fasa hawa dokin domin ji tayi kaman sauqan aradu a kunnuwan ta!!
Bayahn Sarki yasa an miqa masa abun magana cewa yayi. "𝙄𝙉𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙈𝙐𝙍𝙉𝘼𝙉 𝙎𝘼𝙉𝘼𝙍 𝘿𝘼 𝙆𝙊𝙒𝘼 𝘿𝘼 𝙆𝙊𝙒𝘼 𝘼𝙐𝙍𝙀𝙉 𝙂𝙄𝙈𝘽𝙄𝙔𝘼 𝙈𝙀𝙃𝙒𝙄𝙎𝙃 𝙉𝘼𝙉 𝘿𝘼 𝙒𝘼𝙏𝘼𝙉𝙉𝙄 𝘽𝙄𝙔𝘼𝙍 5 𝙈𝘼𝙎𝙐 𝙕𝙐𝙒𝘼 𝙄𝙉 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙔𝘼 𝙔𝘼𝙍𝘿𝘼". Sarki na gama magana ta ji kaman an daskarar da ita a wajan gaba ɗaya ta rasa gane mema yake faruwa, ba tare da tabi ta kan dokin da tayi niyan hawa ba ta kama hanyan komawa gida da qafa. Abun yayi mugun razanar da ita amma bata ce komi ba dan ba abinda zata iya faɗa. Ta dai wuce jikinta na rawa idonta har yanayin sa ya sauya!!
Su ma hadiman nata ba yanda suka iya da ita tunda ran uwar ɗakin nasu a ɓace yake ba mai bakin magana. Haka su ke bin ta a qafan su ma suna mata kirari. Yayin da ita kuma take ji a ranta kaman ta rufesu da duka amma bata da ko bakin magana dan abinda ke damun ta!! Haka suka miqa hanya da qafa.....
(Mastowa nayi na ce, afuwan uwar ɗaki na! hararan da tamun ne ya storita ni har ban san sanda na ganni a 𝙉𝙄𝙂𝙀𝙍𝙄𝘼 𝘽𝘼).
🄱🄰🅄🄲🄷🄸
^^ Kakus ce ke magana "Harara wai ba zaki qira driver ya zo ya fitar masu da kayan nasu bane kam?" Hayra ce tafito kitchen tana tura baki! Tana qunquni akan sunanta da kakar tasu ke ɓatawa. Ficewa tayi tai waje, Ameera tace "Amarya ba kin gaji da mu ba dole kiyi-kiyi ki koramu ai". Salati Amaryan ta sanya yanxu dan kawai sharri da balagaggen rashin kirki da ke damunki yaushe mukayi haka dake takwara? Yanxu duk kukan da nake a zuciyata baki gani ba so kike nata birgima ko? Tom dan ubanki Haruna bazan yi ba. Wuce ma ki fice ku barmun gida dama na gaji da kallonki, dariya Ameera da mijin ta suka sanya!! Driver ya shigo ya ɗau kayan suka bi shi suka fice a part en. Mama hansatu da mama Saratu suka samu wajan da hayra, ban kwana suka masu su na Ameera ta gaida masu Umman yara. "Insha Allahu zataji mama" faɗin Ameera suna shigewa motor da Daddyn Little en. Sallama suka wa Kakus en tasu, driver ya tada motor se Amarya ta fara hawaye!! Ayya takwara ku yafe Ni in na ɓata maku har dakai Angon Amarya, Allah stare maku hanya ya kaiku lafiya Alfarman Annabi SAW, dukan su wajan amsawa sukayi da "Sallallahu Alaihi Wasallam" driver ya ja motor suka yi hanyan airport dan wuce wa KD saboda yau soja zedawo.
Haka suka rabu kakus harda sharan kwallanta tana "takwarata yar albarka yar aljannah se an kuma leqo mu ko kuma wataqilan sai na mutu a kuma zuwa. murmushi su Hayra da su mama hansatu suka yi a haba dai Amarya zasu kuma dawowa Insha Allahu. Tom Allah ya sa ta faɗa ta juya tayi hanyan sashin ta, suma sukayi nasu. Harara qawar Amarya zo ki ɗau ko man goro a ɗaki Qur'ani har na fara kewan takwara ta Allah Sarki, fece hanci tayi ta share qwalla!!
Qarfe 2 na rana ta masu a cikin kaduna garin gomna. Sun sami Umma da Abba yau kam a gida duka kasancewan yau shalelen Abba zai dawo ko aiki bai je ba. Sosai Abba Yaji daɗin ganin ɗiyar tasa da kuma mijin ta suna lafiya lau. Sannu da hanya su Abba suka masu bayan mai aiki ta kawo masu ruwa suka sha. Sallah ko wannen su ya tashi ya je yayi kamun suka dawo su ka zauna, hira suke yi kai kace Daddyn Little da Abba ba surukai ba. Shi kuwa Little yana maqale jikin kakar tasa.
Qarfe 4:00pm na rana yai masu a 𝙆𝘼𝘿𝙐𝙉𝘼 𝙎𝙏𝘼𝙏𝙀 𝘼𝙄𝙍𝙋𝙊𝙍𝙏.
dai-dai lokacin jirgin su yai landing a Nigeria cikin babban birnin Kaduna.
Sauqo wa mutane ke yi daga jirgin da yayi landing ɗin ɗaya bayan ɗaya
Leqa wa kawai Umma da Ameera keyi su ga ta inda ɗan autan nata zai fito, ita kuwa tilon qanin ta wanda bata da kaman shi a duniyar nan.
Wowww!! Shi ne abun da na furta kawai, Wani kyakkyawan saurayi ne kyakkyawa ajin qarshe. Sanye yake da T-shirt na sojoji da kuma army green jeans. fari ne amman ba sosai har can ba, kyakkyawa ne na qin daɗawa jikin sa ya nuna Jarumtan sa kana ganin sa kaga Soja don a dire jikinsa yake kana ganinsa za kai tsammanin ya kai shekara 30 aduniya(abunku da girman falo)
Ai kuwa Ameera na ɗaura idon ta a kansa da gudu ta je ta rungume sa ayoyo bruh, murmushi yayi!! sisto ƴammatan Daddyn Little ayoyo too, minstinin shi ta yi kaifa ka renani matsala na da kai. Turo baki yayi ya wuce wajan umma, Wayyoo ummana!!!! Dariya dukkan su suka saka "Allah shirya ka 𝙃𝘼𝘽𝙀𝙀𝘽" faɗin Abba. Da Ameen ya amsa yana hugging Abban nasa da Daddyn Little en. Ya je ya faɗa jikin Umman sa, ta ce "ah ah tashi ni kar ka karya ni a gaban nasii" Dariya yayi Umma kina so amun dariya ko? Amsan Little yayi a hanun ta yana "Umma ta bani yaro na, my Big broh ya akayi? Washe baki Little yayi unkui fafiya. Dariya yayi suka nufi motor dukan su driver ya ja suka yi gida.
Daɗi a wajan waɗan nan iyalin ba ya misaltu wa don ganin sojan nasu.....
Kar mu shagala fan's sunan littafin namu "𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀" daga Alqalamin Uwar Batoorl 🔥
𝙈𝙚 𝙢𝙖𝙞 𝙢𝙖𝙧𝙩𝙖𝙗𝙖 𝙠𝙚 𝙣𝙪𝙛𝙞?
𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙮𝙞 𝙙𝙖 𝙂𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙈𝙚𝙝𝙬𝙞𝙨𝙝 𝙠𝙤 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝙈𝙚 𝘼𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙮𝙖𝙮𝙞 𝙞𝙙𝙤 𝙗𝙞𝙮𝙪 𝙙𝙖 𝙨𝙝𝙞 𝙟𝙪𝙮𝙖𝙬𝙖𝙣𝙨𝙖?
𝙁𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙖𝙝𝙖𝙡𝙞 𝙣𝙖 𝙜𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙨𝙤𝙟𝙖𝙣 𝙣𝙖𝙨𝙪 𝙢𝙖𝙞 ɗ𝙖𝙪𝙧𝙚 𝙬𝙖 𝙣𝙚 𝙠𝙪𝙬𝙖?
𝘼𝙪𝙧𝙚𝙣 𝙜𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖𝙣 𝙯𝙚 𝙮𝙪𝙬𝙪 𝙣𝙖𝙣 𝙙𝙖 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙗𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙠𝙪𝙬𝙖?
Muna da tambayoyi da yawa waɗan da duka amsoshi su abun samu ne in muna bibiyan wannan labari
Muje zuwa fan's
Ku nishaɗantu, ku faɗakantu, ku wa'azantu, sannan ku dara🤣 daga alqalamin uwar batoorl takuuuuuuu ako da yaushe
Fatan alheri agare ku masoya alqalamin uwar batoorl a ko ina kuke a faɗin duniyar nan....
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮𝙪𝙠𝙖:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞,
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 27&28
💋💋 امى بتولة💋
Mai martaba ne ya tashi ya fara jawabi kamar
"Da farko ina mai bawa ɗauka cin jama'a haquri da abinda ya kasance. Sannan baqin mu yaran Sarakuna na nesa da na kusa ina mai baku haquri, da abubuwan da suka faru. Nima banji daɗin yacce abubuwan suka kasance ba amma ina matuqar baku haquri da kuma maku fatan alkhaeri, Allah sanya hakan ne alkhaeri a gareku duka. Daman ita matar mutum kabarinsa, kuma kowa rabon sa yake aura. Insha Allahu zaku samu rabon ku na alkhaery wa ɗanda suka fi Mehwish!! Ina mai maku fatan komawa Masarautan ku lafiya kaman yacce kuka zo lafiya. Sannan ina mai baku haquri akan duk abinda aka muku a Masarauta ba dai-dai ba. Kuma ina mai qara gayyatan ku auren Gimbiya Mehwish wanda za'a yi nan da wata biyar 5 masu zuwa Insha Allah. In dai hakan bai zama ba dai-dai a gareku ba! Nagode sosai sosai ma'assalam".
Mai shela ne ya amsa abun magana ya qara bawa yaran sarakuna haquri sannan kuma da ban gajiya, ya nawa ɗauka cin jama'ar gari ma ban gajiya, "Allah ja kwanan mai martaba zai gaya mana yacce gasan mu na gaba zai kasance" ya faɗa ya qara bawa sarki Miche ɗin.
Amsa sarki yayi yace "Ni Sarki 𝙌𝘼𝙎𝙀𝙀𝙈 na saka gasa kuma gara ɓasa ga duk wanda ya lashe gasan. Insha Allahu shi ne mijin Gimbiya nan da wata 5!! In dai zaka iya kar kayi tunanin ko kai wani abun daban ne, kawai ko ma waye zai iya shiga gasan nan ina ma kowa da kowa fatan alkhaeri.
Gasan bai sanja ba sai dai abun da ya qaru na abinda mutum zai samu in ya lashe gasan. Duk wanda yayi nasaran buɗe fuskan Gimbiya Mehwish a karo na biyu, auren su da ita nan da wata biyar kuma zan basa dukiya mai tarin yawa, Sannan zaka faɗi duk abinda kake so Masarauta kuma zata maka Insha Allahu in bai fi qarfin mu ba. Koma waye kai, a qasar nan kake, a garin nan kake, ko kuwa ba'a garin nan kake ba duka ba damuwa Masarauta na maraba da kai.
Sannan Ina son gasan ya kasance nan da wata 1 mai zuwa da yardan Allah, duk wanda zai iya qofa a buɗe yake".
Bayan Mai martaba ya gama jawabin nasa ya tashi, shi da jama'an fada suka hau dawakai Sarki da waziri da sauran jama'an fadan sarki aka nufi fada, yayin da sauran kuma manya manyan ƴan kasuwa da saura masu abun hawa suka hau kowa ya kama hanyan sa.
Nan dai taron ya watse da ihu!! ya wanci da sunan Gimbiya a bakin su suka tafi, don kuwa ta nuna Jarumta maza manya jarumai har sha biyu 12 ba wasa ba.
Yayin da a gefe ɗaya kuwa wasun su duk yawanci jikin su yayi sanyi, wanda abun da ya haddasa wannan sanyin da jikin nasu yayi ba komai bane face jin abun da mai martaba Sarki Qaseem yace na kuma yin wani gasan. gasan da sun san ba lallai bane ya faru, ko inma ya faru ba lallai wani ya cinye gasan ba. Dan suna ganin tun da waɗan nan jaruman yaran Sarakunan ba wanda yaci gasa a cikin su bare Kuma wani daban a gefe.
Gasan ne suke tunanin ba mai ci amma tabbas sun san Mai martaba Sarki-Qaseem zai bada fiye da abun da ya faɗa. domin kuwa shi ɗin adalin shugaba ne wanda babu irin shi ba iya nahiyar su ba har ma wasu nahiyoyin.
Sarki Qaseem mutum ne wanda baya ɗaukan kan sa shi Sarki ne, yace dan haka yana daban da sauran talakawan sa. Yacce yake haka yake ganin kowa ma yake, Sarki ne mai qaunar talakawan sa da kuma ɗaukacin jama'ar garin nasa, adalin shugaba wanda samun irin sa a yanzu akwai matuqar wahala, duk da kasancewan ƴa ɗaya tilo Allah ya basa amma bai zama mai fifita ta akan cewa ita ɗaya ba, shi uba na gari ne kuma shugaba na gari, shi a wajansa sarauta ta Ubangiji ne ba amfanin zaluntar wani dan mulki ma tabbata zaiyi ba..
Duk abunda ake yi daga Umman Amjad har Abbansa suna cikin masu kallo a wajan taron, sannan duk abinda akayi sun gani. Sai dai su suna ɓangaren masu yabawa bajinta irin na Gimbiya Mehwish.
Waste wa ake a wannan taron kowa da abunda yake furtawa albarkacin bakinsa. Kowa ya kama hanyan komawa gidansa.
Umma da Abba ke tafiya suna fira, Umma ce tace "Abban jarumin Umma kasan me?" A'a Maryama ta sai kin faɗa. Umma tace "wallahi wannan yarinyar MEHWISH burgeni take yi sosai sosai inason mutum haka". Murmushi Abba yayi! Yace "ai dai kam abar burgewa ce ita dan kuwa tana da qoqari sosai fa Allah dai yamata albarka ya bata miji na gari". Da Ameen Umma ta amsa. Suka ci gaba da tafiyan su suna hiran su....
^^^ Gimbiya Mehwish ko isansu fada, shigan ta gida ɗakin ta tayi direct ko takan kuyangun ta bata bi ba. Tana shiga haɗaɗɗen ɗakin nata kan faffaɗan gadon ta taiwa kanta masauqi. Rub da ciki ta kwanta. tunani take "menene ke shirin faruwa da Ni haka? kaman wanda ake xuga mai martaba akai naa mai nayi haka? Papa kyauta zai yi dani ko me?"
Lumshe ido tayi!! Tabbas wannan karon komi zai iya faruwa. Ga shi bata san wa mai martaba zai haɗata dashi ba kuma bata san mai sharaɗin nasa ba.
Amma nufinsa tasan tabbas tayi aure ne ba komai ba.
Sanda ta gama juyin ta akan gadon nata ta tashi ta shige bathroom. Wasta ruwa tayi ta futo, duk da yanayin da ake na zafi hakan bai hanata shiryawa tsaff cikin dogon riganta. ( masha allah!! hurul eyn)
Ko abakin alqalami faɗan irin kyawun da Allah yaiwa Gimbiya Mehwish ba mae yiwuwa bane. qoqartawa nike nake tara jarumta ran da muka ga fuskanta mu faɗi ko kaso 2 ne acikin 100 na kyawun wannan halittar kudai ku qirata "hurul eyn"
Wajan mahaifiyarta ta nufa bayan ta fito ɗakin nata, da kuyangun ta har ta isa qofar sashen kamun ta shiga su kuma suka juya.
Da sallama ta shiga ɗakin da Ammaahn nata take, ba'a amsa mata sallaman ba sakamakon jikin mahaifiyar tata da har yanxu sai a hankali kawai!! Kwantawa tayi gefen ta ko zata samu nistuwa dan sosai take jin wani iri a zuciyar ta ga halin da mahaifiyar ta ke ciki ga abubuwan da suka mata yawa a kai, bata da wanda zata faɗawa damuwan ta! Ko kukan ta!! Ammaaahn ta kaɗai gare ta kuma bata da ko lafiyan amsa mata sallama barai tayi lafiyan rarrashin ta!! a haka bacci yayi gaba da ita.
(Allah sarki uwa da ƴa, wani abu se soyayyyan uwa da ƴarta
Allah ka sakawa iyayenmu da aljannah
Allah kabamu yara masu albarka dason mu da tausayin mu Alfarman Annabi SAW ).
KADUNA
^^^ Tafiya suke a motorn suna hira, Ameera na zolayan Soja jefi jefi Umma da Abba na sa musu baki. Little kuwa yana maqale jikin soja tunda ya ɗauke sa yaqi yarda sauqa jikin sa. Wani wawan birki drivern nasu ya ja ji kake qiiiiiiiiiiiiiiii!!! Ameera ce ta sanya salati "innalillahi wa inna ilaihirraji'un!! Dan Allah bamu shirya mutuwa ba kabi a hankali." Soja ne yace "wai wani driver ne Abba kuka ɗauka kam? So kake ka kashemu? Can't you drive good? Mtswwwww!!" Qara qanqame sa Little yayi dan shima ya razana! Abba ne yayi gyaran murya, duk sai suka yi shiru. Ka kula da hanya ku kuma banson surutu okay. Drivern ne yace sorry sir mai mashine ɗin ne ya shigo bai duba hanun sa ba. Okay just becareful with what ur'e doing, okay Sir. Motorn sai yayi shiru har suka isa anguwan GRA horn drivern yayi, mai gadi ya buɗe suka shige. Bayan yayi parking duk suka sauqa sukayi cikin gida.
Suna shiga side nasa yayi da already yake a gyare, har yanzu Little na maqale da shi. Ajiye sa yayi a kan kujeran da ke cikin ɗakin yace "my boy let me take shower an coming" ok unkui.
Shiga yayi ya wasta ruwa ya fito ya shirya ya ɗau yaron nasa sukayi palourn. Ya same su duka suna jiran sa cin abinci, da murmushi ya qarisa wajan!! "Umma ni fa abaki zaki bani dan nayi missing en feeding na da kike yi" ya faɗa yana zauna wa gefen Umman tasa. Unkui in granny ta baka food a mouth nima you wiy gim me a baci (you will give me a baki). Duka wajan dariya suka sa da turancin nasa da ko nuna maganan bai yi ba bare turancin, har Abba sanda ya murmusa!!! Abincin suka soma ci wajan yayi shiru baka jin qaran komi sai na spoon's da kuma taunan abinci, soja na ci yana bawa yaron nasa a baki..
After kaman 1 hour na dawo palourn
Zaune suke sun gama cin abincin hira suke cikin nishaɗi da farin ciki!! Ameera ce tace "habeebyn Ummeyh wai yaushe zaka Bauchi ne? Kakus fa tana neman ka" caɓ gashi Ni kuwa ban shirya zuwa Bauchi ba. Umma ce tace "Aikuwa sai kaje dan nice nan zan kora ka" tura baki yayi Umma bakison ganina ko? Carab Ameera ta amsa "ai kuwa Umma ke son ganinka kai dai asirin ka a rufe ka kama hanyan Bauchi state gobe. Harara ya doka wa Ameera ko ba gobe ba kam sai ta ganni. "Haba bros angon Kakus so kake Amarya ta buga mu a court in bata ganka ba" Daddyn Little ya faɗa yana dariya. Tura baki soja yayi ya kalli Umma!! Murmusawa tayi tace "ku fita idon Auta na ko na saɓa maku son kai da Ameeran, sunkuyar da kai Daddyn Little yayi yana "Allah huci zuciyan Umman mu mun daina.
Dariya Soja ya saka!!! Yace "sistor kinsan mai na tuna kuwa?" Girgiza kai Ameera tayi a'a ban sani ba sai ka faɗa. Dariyan ya kuma sanya wa amma dai gaskiya storon ki yayi yawa sistor wai ɗaxu kin ganki kuwa, Kinga azara'ilu kawai abinki. Harara ta masa ta haɗa fuska!! Daddyn Little ne yace "karfa kaga kai soja kasan dai mun girme ka kuma zamu iya maka bulala kabar taɓa Adda Babba. Umma ce ta murmusa in ga mai taɓa mun Auta inaji dai ba sharri ya mata ba. Haka suka ci gaba da hiransu tsakanin su suna darawa!! Kowa farin cikin ganin soja ne tattare da shi.
Abba kuwa kaman yafi kowa jin daɗin ganin ɗan nasa barin ma da ya gajesa a dai-dai lokacin da yake kusa da yin retire a aikin nasa. kasancewan shekaru sun ja kuma gashi babba sosai a cikin sojojin. Farin ciki yake sosai na ganin iyalan nasa kuma cikin farin ciki, yana kuma gode wa Allah da addu'an wanzuwar farinciki na har abada a gare su. Sai dai gefe guda na zuciyar sa, yaron sa yake tunani yana jin inama ace dashi duka a zaune anan wata qila da shima har da iyalan sa.
Umma ke stokanan Autan nata. "Wai yaushe zaka je ɗauko mun yarana en tunda ka dawo gida" ɓata fuska yayi! Umma nifa in yarinyar nan Maha tazo gidan nan Tom barinsa zanyi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 25