ko rinsta ido ma so take tasan wani hali yake ciki kuma yaya jikin nasa.
Abba ne yace "boɗɗi ki huta gobe Insha Allahu Monday sak mu wuce wajan Gwaggo".
Ummeyh tace "To yaya Allah ya kaimu" Ameen ya Rabbi suka amsa duka.
Tashuwa Abban yayi yace "sai da safen ku ahuta gajiya Gwaggon yara" ya faɗa ya wuce hanyan ɗakin sa.
Allah tashe mu lafiya yaya.
Umman su aje a kulamun da yayana nima ba na shige ciki na samu na huta.
Murmushi Umma tayi tom Gwaggon yara Allah ya hutacce ki gajiya sai da safe doter kema je ki kwanta.
Ummeyh haurawa sama ta yi tai ɗakin da yake nata, Mahreen ma sai da safe ta musu ta haura nasu ɗakin.
Umma kashe abubuwan wuta a palourn tayi ta wuce ɗakin mijin nata.
Mahreen bayan ta shiga ɗakin nasu kwance ta hangi Maha toilet tayi ta ɗauro alwalan kwanciya ko da ta fito banɗakin sanda tayi *shafa'i da wutiri* kamun ta haura gadon dan kwanciya.
"Ikon Allah wai dama tun shigowa na idonki biyu ko kuwa yanzu ne kika farka?" Ta faɗa ganin Maha zaune.
Addah idona biyu banyi bacci ba.
To ko ciwan kan ne? A'a fa Addah na warke.
Tom ko Man of dream ne? Ganin Maha ta girgiza kai sai ta kuma cewa. "to ko dai ya Habeeby angon Maha ne?"
Tura baki tayi idon ta ya kawo kwalla! Addah ni dai ban so kuma ba kowa ta faɗa tana juyawa ta gyara kwanciyan ta.
Shikkenan ya rage maki kwanciya tayi itama ta jawo wayan ta tana dialing layin ya Abdoul.
Maha tayi tsaki qasa-qasa ganin dare nayi kuma Mahreen taqi gama wayan bare ma tayi bacci ta samu ta fita taje ta dubo jikin nasa.
Ganin wayan Mahreen en yaqi ci yaqi cinye wa lallaɓawa tayi cikin sanɗa ta fice a ɗakin. Ko da ta fito samun palourn tayi ba kowa kuma ba haske sai deem light kawai ajiyan zuciya tayi a saɗance tayi hanyan ɗakin nasa.
Ko da ta isa bakin qofan bata buga ba bare sallama shigewa tayi ta nufi hanyan ɗaki direct.
"ke ina zaki ba sallama?" Maganan sa da taji yasa ta kusa sakin fitsari a tsaye, ta storita sosai dan bata kawo a ranta yana palourn nasa ba.
Juyawa tayi tana tura baki tai hanyan fita tana qunquni.
"Ke ina zaki kuma? Zo nan" Muryansa ya qara dakin dodon kunnenta.
Juyowa ta kuma yi a hankali kaman za tayi kuka ta dawo cikin palourn, gefe dashi ta nema ta zauna a qasa kasancewan shima a qasan yake zaune.
I"na zaki da kika shigomun ba sallama? Kuma ki kai hanyan bedroom na ko akwai bashinki akaina ne?" Ya faɗa yana kallonta.
Murguɗa baki tayi tace "dama me zan yi inba in duba ya jikin ka ba?"
Taɓe baki yayi to son asani gaida uwar miji a kasuwa.
Hararan gefen da yake tayi qasa-qasa tace "eh ɗin".
kee me kika ce? Ya faɗa cikin tsawa
A'a ni bance komi ba yaya.
Okay fine yayi kyau.
wayan sa ne ya ɗau qara, qaramin tsaki yaja ke tashi ki miqo mun waya na.
Tashuwa tayi taje tai unplugging na wayan sanda ta qarewa number mai qiran kallo kamun ta kawo masa wayan.
Amsa yayi yai picking yasa wayan a handsfree,
Hello Barbie ya kake ya cikin naka?
Am fine babe, and you?
Am also fine Alhmdlh Barbie.
Aha that's gud.
Barbie yaushe zaka zo?
Ɗaga ido yayi ganin Maha na mujiyanta na kansa duka sai fasa faɗin abinda zai faɗa dama yace "babe tomorrow Sunday right?"
No barbie gobe Monday fa.
Okay na manta ne kinsan ciwon cikin sai a slow, so am all urs tomorrow Monday Insha Allah.
Wow! Really barbie?
Yes or you are doubt?
Noo barbie am just excited am really happy, I no u always stand by ur word's I can't wait to see you my captain.
So what you kept for me beb? Yana rufe baki Maha ta tashi tana turo baki zata tafi, da gefen ido yake kallonta. Murmusawa yayi ya mata alama da hanu ta dawo bai sallameta ba.
Barbie everything for you sai abun da kakeso kawai am very happy can't wait to see tomorrow barbie, spending the whole day with the love of my life awwn! Barbie I will make sure that this stomach pain heal tomorrow.
Jin abinda tace sai Maha taja staki, sanda soja ya ɗago ya kalle ta amma baice komi ba hiran su suka ci-gaba da yi tana zaune a wajan ya hanata tafiya.
Mahreen ko da ta juya tana cikin wayan sai bata ga Maha a wajen kwanciyan ta ba, mamaki ne ya kamata yaushe ta fita bata sani ba.
Har ta tashi zata fita dubo ta ganin time ya tafi sosai kar dai ba lafiya ba? Sai tace "ya Abdoul lemme check Maha in palour" You are not going to anywhere Queen, Kikasan ko wani abun take ko kuwa tana waya ne ba taso kiji ta.
Ba dan taso ba ta haqura da fita dubo Maha ɗin suka cigaba da wayan nasu amma dai hankalin ta bai konta ba sanin Maha ba waya a hanunta.
Har yanzu wayan yake da babe ɗin tashi Maha ta cika tayi fam kaman zata fashe, ba haushin ya wayan sa ko budurwan sa ba haushin ta tsayar da ita da yayi kuma tana so taje taci abu ko kaɗan ne ta samu tayi bacci.
Can sai yace "Babe let's talk tomorrow koh"
Barbie am surprise for today's call, sha i know you wataran kaman mai aljanu haka kake, ayi aiki lafiya Allah kaimu goben.
Tsaki Maha ta kuma ja a aranta cewa take "wahalalliya ai aljanun ne dashi".
Ya buɗe baki zai yi magana a ɗaya ɓangaren sai tace "wait barbie Kai da wa a midnight ɗinn nan? Naji staki"
Dafe Kai yayi yace "Sorry babe maid ce ta kawo mun coffee"
What barbie? Maid dai da uban daran nan sannan ma dawa take tsakin? Look barbie don spoil my day just tell me the truth Kai da wa?
"Kinsan dai bazan maki karya ba ko? so gudnyt." ya faɗa yana qoqarin kashe wayan
No barbie please am sorry if I provoc you am really sorry na yarda my Captain. Take good care of yourself for me barbie, very soon zan ke dafa maka coffee da hanuna na bawa barbie na a baki i will feed you with anything that you have to take, I soo much love you barbie muahhhhhhh!
tai blowing masa kiss
I do more babe and don't forget to pray Ko(addu'an bacci).
Insha Allahu Barbi mee byeee miss you ta kashe wayan kit.
Kallonta yayi up and down, hey you stupid how there you ina waya da wife to be na kina tsaki, am i your mate? Or she's ur mate? Lemme tell you one thing in kika sake irin haka i will surprise you.
Wayan ya miqa mata, go and plug it for me, hararansa tayi tukun kamun ta harari wayan ta tashi tayi hanyan tafiya.
"Karki yarda ki bari na tashi baki dawo ba" ya faɗa.
Riqe qugu tayi tace "baza'a dawon ba ita wahalalliyan wife to be ɗin taxo ta maka plugging kuma anji kunya har da cewa tayi Kana da aljanu" tana gama faɗa ta fice da gudu, direct dinning tayi dan kar ya biyo ta ɗaki.
Mahreen ce ke cewa "ya rouheei, serious bata dawo ba har yanzu Please ba na dubo ta"
"Okay Queenas your wish is my command, dubo ta tunda anfara sace mutane a gidan Abba bansani ba" bai rufe baki ba ta shagwaɓe fuska My wish is your command like how? Tun ɗazu ka hanani zuwa fa kuma ba sacewa ba dama headache na damunta so I have to check.
Tom queen am so sorry tashi kije Koh, okay ya rouheei gudnyt take care. Insha Allahu zan kula matar yayan ta, Allah maki albarka queen.
Ameen yayana mijin qanwar sa. sallama suka yi ta kashe wayan ta fice a ɗakin tayi hanyan palourn.
Dudduba saman tayi bata ganta ba. Main palourn na qasa ta dawo tana dubawa nan ma bata ganta ba, hankalin ta sosai ya tashi, har idonta ya fara tara kwalla sai taji mosti a wajan dinning.
Juyawa tayi ta nufi dinning dan ganin wa ke jin yunwa da daren nan da yake ɓurun tu. Buɗe baki tayi tace.....
Muje zuwa fan's masoya alqalamin uwar batoorl ✍️ taku me son farin cikinku ako da yaushe
Domin tallata hajarku ku tuntuɓi wannan layuka
08146292652
Chat only
09161720046
Yo can call this one
Comment
Like
Share
💦💦💦💦💦💦💦
👑𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀👑
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 67&68
💋💋 امى بتولة💋
𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!
𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.
𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢
𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋
𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750
𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄
𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎
𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏
𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.
𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......
"Maha kiji storon Allah me kike yi a dinning cikin daren nan?" Mahreen ta faɗa da mamaki.
Ga kuwa Abinda nake kin gani, abinci na gama ci yanzu zan dawo ɗakin.
Yanxu duk jimawan da kika yi abinci kike ci? Cup na ruwa ta ɗauka ta sha ta miqe tsaye, tom na gama muje mu kwanta Addah am an gama waya da ya Abdoul ɗin ne?
Gamawa tun yaushe Maha, kece ma da naga baki dawo ba na zaci ko ba lafiya ba ai.
"To Kin ganni rass nake na ma fiki lafiya" ta faɗa yayin da suke shigewa ɗakin su.
Tun da ta fita idon sa na kan qofan bai kau da ba. Me yarinyar nan ke nufi? Ina mata magana tayi banza ta wuce.
"Mtswww" tsaki yaja.
Dama ban qira ki ba ke kika kawo kanki shashasha kawai. System ɗin nasa ya buɗe yaci gaba da aikin sa in peace, amma dai qasan ran sa reaction na yarinyar na basa mamaki ko renin da ta masa har ya kai hana oho.
Suna shiga ɗakin gado suka faɗa duka ko wacce addu'an bacci tayi suka ja blanket suka lulluɓu.
Can ta leqa Mahreen gani tayi ita kam ta jima dayin bacci ma.
Qaramin tsaki ta ja tace "Ɗan renin hankali kawai wai dan an damu baka da lafiya shine har da wulaqanci wani ai mai aiki ce ta kawo masa coffee, hmnn zan rama ne ba dai ka warke ba ina dede da mutum." Juyawa tayi ta rufe idon ta dan bacci ya ɗauke ta itama.
Umma na shiga ɗakin murmushi Abban yayi mata! Ƴammata na sai yanzu aka biyo ni?
"Yallaɓoi aimun aikin gafara" ta faɗa da murmushi itama. Matata bata laifi ko tayi ma an yafe mata.
Gidiya nake yallaɓoi baban yara.
Isowa wajan da yake tsaye yana rage kayan jikinsa tayi tana taya sa rage kayan, murmusawa yayi yace "Allah maki albarka" da Ameen ta amsa ta wuce bathroom ta wasta ruwa.
Bayan ta fito shiryawa tayi cikin dogon rigan ta na bacci, zaunawa tayi bakin gadon gefen sa kallon ta yayi yace "Hajiya ta da alama dai bakinki da magana menene ya faru?"
Yallaɓoi maganan yaron da su Ameerah suka yi jinyan sa ne, an turo mun layin nasa sai dai na qira ba'a ɗauka ba da alama ko wayan nasa baya tare da shi.
Karki damu maman yara tunda gobe Litinin zamu Bauchin inyaso sai mu tafi tare daga nan sai kiga yaron naki. Maganan da yayi na "daga nan sai kiga yaron ki" ba qaramin tsaya mata a rai yayi ba hakan ya sanya tana qara jin wani iri game da yaron, wanda bata san ko menene ba?
Cewa tayi "wai dama nufin ka yallaɓoi ku kaɗai zabkuje ni ba za'a je dani na gaida Mama ba?" A'a na isa Hajiya ta qafata qafar matata.
Murmusawa tayi, Allah kaimu goben da rai da lafiya. "Ameen ya Rabbi Hajiya ta" Abba ya amsa mata.
Bayan sun kammala abubuwan da ya kamata kwantawa suka yi sai muce safiyar alkhaery.
🅆🄰🅂🄷🄴 🄶🄰🅁🄸
Gari na gama haske Amjad ya gama kimstawa ya shirya, tuwon karin da aka kawo masa ma stakura yayi kaɗan.
Gaba ɗaya yau jin sa yake cikin farin cikin nasaran samun maganin da yayi yake, gashi kuma yau zai kama hanya wanda da yardan Allah zuwa gobe zai ga Ummansa ta gansa ya faɗa mata irin kewanta da yayi, to sai dai agefe ɗaya kuma cike yake da fargaba da kuma tunani akan faɗuwan gaban dake damun sa wanda ya tabbata akwai abinda zai faru.
Lumshe ido yayi yana faɗin "Ya Rabb ka sanya komi dake shirin faruwa dani yazo da sauqi Alfarman fiyayyen halitta SAW, tabbas stinkewan zuciya na ba alkhaeri kuma ko da akwai alkhaeryh to wani babban abu dai zai faru". Yau saura sati 1 da ƴan kai wa'adin da aka ɗibar mun su cika ya kamata ace ina gida iwar haka, Allah ka iya mun.
Liman ya iso inda yake a tsaye a qofan ɗakin baqin, sallama liman yayi shiru Amjad bai amsa ba, qara Sallaman yayi shiru kuma du.
Matsowa limamin yayi ya ɗan taɓa Amjad yace "bawan Allah mai kake tunani haka? Nayi sallama bakina uku shiru baka ko ji na ina fatan lafiya kam?".
Qasa Amjad yayi da kai yana ajiyan zuciya sai yace "lafiya lau Alhamdulillahi Allah gafarta malam"
A'a kaga yaro faɗa mun gaskiya wani abu ne ya faru kuma sai kace a'a lafiya.
Can sai ya nisa yace "Allah gafarta malam gabana ke faɗuwa sosai-sosai kuma ni tun ina yaro haka nake indai wani mummunan abu zai faru to ko nayi mafarki ko kuma na tashi da faɗuwan gaba tom ina tunanin wani abun na shirin faruwa"
Lima yace "subhanallahi! To yaro ko zaka iya haqura da tafiyan nan yau ne mu koma ciki
Qasa Amjad yayi da kai cike da ladabi yace "Allah gafarta malam amun addu'a kawai amma zan tafi yau Inshà Allah yanzu ma haka munyi magana da wanda zai zo ɗauka na ya kusa isowa".
Dogon numfashi malam liman yaja kamun ya jinjina kai yace "bawan Allah ba ina nufin hanaka tafiyan ka dan abinda kake tunanin faruwansa ba a'a ko ɗaya ina hanaka tafiyan ne dan samun nistuwan zuciyanka, ka riga da ka sanyawa ranka indai faɗuwan gaba ya sameka to mummunan abu ne zai faru to shiyasa nake son ka dakatar da tafiyan naka dan kasani cewa shi mumini a rayuwan sa akwai qaddara haɗe da jarabawar Ubangiji sannan duka abu biyu wanda kusan ma'anan su ɗaya ana son duk wani mumini wanda ya yarda da Allah da Manzon sa to yayi imani da su, wani lokacin alkairi zai kawo bugawan zuciyan ka wani lokacin kuma akasin alkairi sai dai duk acikin sun akwai abinda Allah ke nufi da hakan wa lau ya ɗaga matsayinka wa lau ya jarraba imaninka sannan..." sosai yai masa nasiha mai haɗe da tunatar wa.
Ajiyan zuciya Amjad ya sauqe bayan malam liman ya ida nasihan sa, Allah ya saka da alkairi Malam in Allah ya yarda zan gyara amma ina mai bada haquri da maganan tafiyana yau, tabbas nasan komai sai Allah yaso kuma sai ya qaddara amma ina mai addu'an Allah yasa tafiyana yau ɗin ya zame mun alkairi,
Bazan taɓa mance alkairinka gareni ba malam Allah ya saka da Aljanna Allah kuma ya qaddara saduwanmu.
Amarya da hayra ne zaune a dinning area suna karyawa, shiru babu mai magana (table manners).
Da sallama Abdoul ya shigo sashen kakar tasu, ganin suna dinning tsayawa yayi daga tsakiyan palourn yace "Amarya ta gud morning"
Amarya tace "ubanka ke gudu da moni, ɗan jakar uba banson ɗiban albarka da tangaɗewa da sanyi safiya ka isheni da yaren ƴan wuta, yanzu inbanda sinqin sikitin layii da tangaɗi wai ƴan adam baza suyi yaren ƴan aljanna ba sai na ƴan wuta to haram ba dani ba ni Mairo".
Tunda Abdoul yayi magana hayra ke dariya har amarya ta qare sababin ta dariya take har da kama ciki "ko shima ya Abdoul me ya kaisa oho" ta faɗa tana dariya qasa-qasa.
Amarya Juyowa kanta tayi tace "matar ubanki hansatu ce ta kaisa, ba dai matar nan ta koya maki sinqin fistara ba to zan kwashe maki ƴar buhun uba kawai".
Abdoul da ya gaji da tsayuwan jin surutun kakar tasu sai ta juya zai fice, amarya tace "yanzu Abdu renine har haka dan ni ba uwarka saratu ba ina faɗama gaskiya shine ka iza farantin goshinka a gaba zaka fice? To da mai ma ya kawo ka sashe na gulman me kazo yi? To in ban haifeka ba ai na haifi ubanka Muhammadu don haka ina zaka da sassafen nan ka faɗamun ko na kwashe maka sauran albarka".
Qaramin tsaki Abdoul yaja jin fitinan stohuwar nan, ni na kawo kaina ai dole ki isheni da surutu.
Kwantar da murya yayi yace "Amarya ta aike Umma ta sani bawan Allahn da mijin Ameera ya buge ne zanje mu haɗu dashi zai koma garinsu.
Salati Amarya tayi tace "Abdu ɗan albarka zaka aikin lada shine dan tsabar sinqin baqin hali ba za ka ce na raka ka ba, to Allah shiryeka kuma ka tabbatar ka kawomun shi na sa masa albarka, kai ina tsaya dai na ɗauko mayafi mu tafi tare tunda motar da kuɗin yarona ka saya to sai na hau" ta qarisa faɗa tana miqewa ta nufi ɗaki.
Abdoul na ganin ta shige ya fice a sashen da sauri, motorn sa ya shige yai mata key da gudu ya fice a gidan sanin halin kakar tasa.
Hayra haɗa kwanuka tayi ta gyara dinning ɗin, duk abinda suke tana ganinsu dariya ne kawai take dannewa dan tasan tabbas yau akwai qaramin bori a gidan nan. Tana cikin tunanin haka Amarya ta fito a ɗaki sanye da hijab nata har da sanja kaya tayi tana faɗin "Angon kayi haquri na jima mu tafi yanzu.." bata qarisa ba ganin palour wayam ba Abdoul ba labarin sa da sauri tayi hanyan waje tana faɗin "ɗan albarka ai nace kayi haquri shine dan ka gaji da jira na sai kayi waje salon kaban wahala".
Gama duba haraban gidan tayi amma ba Abdu ba motorn Abdu, Amarya ta cika tayi fam sai ta rasa me ma za tayi ɗaya? Sashen iyayen sa ta nufa gadan gadan ko sallama ba tayi ba ta tura qofa ta shiga tana bambami..
Amjad suna staye da malam liman sai qira ya shigo wayansa, ganin layin Abdoul ne sai ya ɗauka. Magana suka yi yayi masa kwatancen gidan malam liman kaman yanda limamin ya faɗa masa, da suka gama magana sai ya kashe wayan.
Malam liman yace "yaro yanzu dai tafiyan zaka yi, to Allah ya tabbatar da alkhaeryh ya kuma kai ka gida lafiya ba na shiga gida ina fitowa kamun dai shi mai ɗaukan naka ya iso". Amjad yace "to Allah gafarta malam a fito lafiya".
Umma ce tsaye a tsakiyan palourn hannunta riqe da mayafi da kuma jakan ta waya a kare a kunnen ta tana cewa "wai kai Auta ba za ka fito bane sai mun tafi?" Daga ɗaya bangaren soja yace "Umma ina fitowa yanzu tashuwa na bacci ne shiyasa".
Umma tace "ko ma baka tashi baccin bane ka fito yanzun nan inba haka ba zan saɓa maka" kitt ta kashe wayan. Ummeyh dake sauqo wa daga step's ce ke cewa "gaskiya ana takurawa yaro na tunda ba binmu zai yi ba abarsa ta huta mana".
Umma tace "Gwaggon yara ki qyale wannan yaron naki ko kaɗan baya ji wallahi ni na rasa ma ya zan yi dashi wai dai ace yaro ka fito ka gaida iyayen ka ko ba za ka bisu ba ai ka musu addu'an a dawo lafiya amma kwata-kwata habeeb ba ya ji". Ki sa masa albarka kawai Umman yara.
Hmmn! kawai Umma tace tayi shiru.
Dai-dai Abba ma ya fito iso palourn shima Soja ya iso, kallonsa Umma tayi ta kau da kai tace "wai ina su doter ne suma ko ba za su mana a dawo lafiyan bane?" Tana gama rufe baki Maha da Mahreen suka shigo palourn su ma.
Maha ce ta fara stugunnawa ta gaida iyayen nasu kamun Mahreen ma ya gaishe su, Umma qara kallon soja tayi ganin bai gaishe su ba kuma shi ya fara zuwa palourn, qawafa tayi.
Soja gaisar da Abba da Ummeyh yayi kamun ya gaida Umma ko kallon sa ba tayi ba bare yasa ran zata amsa.
Ummeyh tace "ataimaka dan Allah da Manzon sa a amsa mana" kamun ta amsa gaisuwan sama-sama.
Maha tace "yanzu Abba tafiya za kuyi ku barmu mu kaɗai a gida?" Murmushi Abba yayi yace "doter may be yau ɗin nan zamu dawo in bai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 25