Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Umma ni wannan shirin baya burgeni" Mahreen tayi caraf tace "dama ta ina zai burgeki kekam kinsan me kikeyine ma" Turo baki tayi Umma kina jinta ba. Abba ne yayi magana yace "doter bamuson cin neman magana autan Ummeyhn ce ake faɗawa haka zan saɓa maku, Shiru Mahreen tayi bata ce komi ba. Can suna zaune sai soja ya fito a shirye cikin qananan kaya sunyi bala'in masa kyau, yace "bruh en uncle zo ka rakani muje yawo mu dawo yanzu ko" Little kaman mai jira dama ya tashi ajikin Abba "apoki limmi eccort unkui cai mun dawo byee" Umma tace "wannan yaro yawo kaman shanshani daga jin fita har ya miqe" Abba yayi dariya yace to Nima gwanda da yawon ta samu Kinga qafata ta huta su dawo qalau, Ɗaukan little yayi yace Umma Abba sai mun dawo Abba ne yace "captain sai ina haka irin wannan kwalliya? Idon Umma da Mahreen duka na kansa, Maha ce tun shigowansa palourn ta kauda kai tana kallonta. "Abba zamu ɗan je wani wajene zan karɓo saqo ba jimawa zamu dawo yanzun nan Insha Allah" Ya faɗa yana duba agogon dake maqale a hannunsa. "To tunda wajan bai da suna adawo lafiya Allah tsare Allah kare ya maku albarka" umma tace ita da Abba Mahar da sai yanzu ta juyo tace "my boy na akawomun tsaraba kaji zan goyaka" tom anci unkui de sayamana an kawo maci, murmushi tawa little tace byee ya ɗaga mata hanu harara soja ya aika mata dashi kan suka fice a palourn da sauri yana fita cikin compound na gidan har soja 1 daga guard ensa wanda ke tuqasa ya fito da motor daga parking lot, Shiga yayi gefen mazaunin driver ya zauna. Drivern yace sir where are we going to? "Airport" haka kawai yace masa Little dake baya, yace la unkui wajan aukan jilgi, ya fiddo wayansa yai dialing layin Ameera, Gaisawa suka yi yace sis ya mutumin Umma? " Ai kaide bruh kabari Umma saura kaɗan ta tsineman akan yayana Amjad kuma nima fa ba Umma kaɗai ba ya shiganmun rai Allah inajinsa kaman ɗan uwana saboda yanada hankali sannan yacce naga Umma ta damu dashi" Ameera ta faɗa muryanta da sautin murmushi Taɓe baki yayi ke da Umma kuka jiyo sai son kalen dangi Ni dai ya unborn little soja? dariya tayi au soja ne acikin Nide Ummeyh zan haifa ba wani soja atou, "Wlh baki isaba tun da kikawa big bro sekin mun nima ki qarisa ladanki kawai Allah sauqeki lafiya namiji zaki haifamana, Mursmushi tayi to Ameen ɗan uwa rabin jiki kai ɗaya gareni dole na in maka takwara. "Sir mun iso fa" sojan dake driving nasa ya faɗa Ok, sis mun iso inda zamu leqa bayan motorn yayi ga yaronki har yayi bcc byee take care ko Ok bruh akoma lafiya, Ameen mum little Adda Meerah, Murmushi tayi ta kashe wayan. Time ya duba saura 2 minutes jirgin nasu ya sauqa, Wayansa yakunna yana danne dannensa Qaran sanarwan sauqan jirginne ya cika airport ennn! Lumshe ido yayi ya buɗe motorn ya fita Mutanen dake jirginne ke sauqowa kowanne idonsa na kansu yana jira yaga ta inda zata bullo.... **INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN (idan masifa ta sameku ku laazinci wannan kalma) QUR'ANI Maganin kowacce irin baqin ciki, damuwa, hardama ciwo sadidan Ita qur'ani maganin kowacce cutace Kaman yacce manzon Allah SAW yace ba cutan da aka sauqeta face an sauqar da maganinta Sede banda cuta daya 1 itace stufa Tom Allah sa mugama da duniya lafiya Mu lazimci karanta qur'ani jama'a domin maganice ta ko wacce masifa harma talauciYawaita ambaton Allah Akwai ayoyi d yawa na maganin abubuwa da yawa Munemi sani sannan mu nemi masana su sanar damu Hadisi ce guda ta Rasulullahi SAW Kaicon azaba ta tabbata ga wanda bai saniba kuma bai nemi ya saniba Allah yatsaremu da wuta jama'a🤲** اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍 ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️ 💋💋 امى بتولة💋 𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!! # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣 𝘽𝙮 𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖 (𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl) اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍 _______________________________________________________________ 🅿️ 55&56 💋💋 امى بتولة💋 𝘿𝙪𝙠 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙪𝙮𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙗𝙖𝙣 𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙗𝙖 𝙎𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙞𝙙𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞 𝙮𝙖𝙘𝙞 𝙝𝙖𝙦𝙦𝙞𝙣𝙖 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙯𝙚 𝙨𝙖𝙠𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣𝙖 𝙣𝙖 𝙠𝙪𝙙𝙞 𝙣𝙚 𝙞𝙣 𝙠𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙗𝙖 𝙩𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙣 𝙗𝙞𝙮𝙖𝙗𝙖 𝙗𝙖𝙯𝙖𝙣𝙘𝙚 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙞𝙨𝙖 𝙗𝙖 𝙖𝙢𝙢𝙖 𝙞𝙣𝙗𝙖𝙙𝙖 𝙨𝙤𝙣𝙖 𝙗𝙖𝙣𝙚, A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙠𝙖𝙢𝙪𝙣 😕 Waɗanda suka jima da biyan kuɗin su ina mai qara baku haquri sannan ina godiya da uzurinku a gareni Allah bar qamna Wannan shafi sadaukarwa ne gare ki qawar kirki bestyn justice Dr Seeyerth kiji daɗin ki kiyi yacce kike so dashi. Murmushin da ya yalwata a kyakkyawan fuskansa shi ya tabbatar mun da wacce yake jiran isowanta ya hango Juyawa nai dan ganin ko wacece haka yake wa wannan murmushin, Abun da ya ban mamaki wata ƴar dattijuwa na gani wacce a shekaru za tayi sa'an Umman sa, murmushin ne itama a shinfiɗe a fuskanta wanda yawan shekaru basu ɓoye kyawunta ba. Tafiya take a hankali kana ganinta kaga babbar mace wacce kudi da hutu suka zauna mata, sanye take da dakakkiyar shadda ruwan bula ( blue) wanda akai wa ɗinkin dogon riga wuyanta sanye da sarqan gold da kunnensa da zobunansa duka ta yafa farin mayafi qafanta kuma sanye da takalmi kwantacce(flat shoe, Gucci) me ado da stone's blue. fara ce sol kyakkyawar gaske wanda in ba idonta ka gani ba ba zaka ɗauka tana da shekaru sosai ba(mace sai da gyara). Wayanta ta ciro a bag en dake hanunta (Black Gucci back) tana qoqarin qira taji anyi hugging nata, murmushin dake fuskanta ne ya qaru dan tasan bame mata haka se shi ɗin. "Habeeby karka ya damu a bainin nasi fa ace ga qatuwa ta faɗi" ta faɗa tana jan kunnen sa. Dariya yayi yace "Ummeyh bafa iya ya dake zan ba kema kin sani Hajiya Ummeyh Autan Kakus" karɓan trolly enta yayi, Joseph drivern sa yazo da sauri ya amsa yakai motor. Yace "Ummeyhna welcome to Nigeria, Ummeyh even Nigeria miss you taklless of we and ur old mother" Murmushi tayi bata ce komai ba, suna isa wajan motorn joseph ya buɗe mata back seat ta shiga tana me ambaton sunan Allah da godiya garesa. Shima Soja shigewa mazauninsa yayi Joseph bayan ya kulle masu qofa ya zagaya ya shige mazaunin driver, ya tada motor suka ɗau hanyan gida . Habeeby ina dai fatahn ba wanda yasan kazo ɗaukoni ko? Soja yace "Babu Ummeyh sai little kuma shima kinga bacci yake" Au wai wannan yaron wajan uwata ce eh lallai ikon Allah haka ya girma kace Ummanku na amsan kuɗin cafane ita kaɗai shiyasa take freshh abunta. Ummeyh wani kuɗin cafane Umma ke karɓa kuɗin rigima dai, dan ma yanzu kam ya samu uwar ɗaki shugaban marassa ji irin sa. Ummeyh Murmusawa tayi dan ta fahimci wa yake nufi sai tace "koma dai me ku kuka sani kuma kunfi kusa, nidai yanzu gani kuɗin cafene har da ni, Yayana na gida Ko?" Eh Ummeyh Dukansu ma suna gida na barosu. Ajiyar zuciya Ummeyh ta sauqe tana maijin wani sanyi yau za taga ƴan uwanta bayan shekaru da dama da suka ja bata ko leqo Nigeria ba kuma dukansu sungullolinsu basu barsu sunje wajanta ba. GRA Kaduna, sun shigo anguwan nasu shiru kaman ba mutane, gaban tangamemen gate ɗin gidan general Haruna wanda tun daga waje sojoji ne ke tsaye riqe da bingida, horn Joseph yayi, a take aka buɗe gate ɗin sanin horn ɗin motorn waye, Shiga suka yi har wajan qofan shiga palourn ya tsayar da Motorn. Ummeyh ta sauqa bayan ta ɗauko little wanda ke sharan baccin sa a kafaɗanta, Soja ma sauqa yayi yace "Ummeyh na wannan lukutin yaron zai gajiyar dake kawo sa" ya faɗa yana miqa hannu ta bashi Little. Murmushi Ummeyh tayi "mijin nawa ne lukutin? tom ku ya ɗauko ai kuma lutayen ne" ta faɗa tana miqa masa Little ɗin, amsan sa yayi yasa shi a kafaɗa, kusta kai cikin palourn Ummeyh tayi bakin ta ɗauke da sallama.. Joseph yaja motorn parking lot yai parking ya fito yazo gaban soja yana sara masa yace "Sir make i help you with the boy" Soja yace "No leave am just take the luggage and come with it inside" "Okay sir" Joseph ya faɗa yana juyawa ya kwaso kayan kaman yacce ogan nasa ya umurcesa yabi bayan Soja da tuni ya kama hanyan shiga cikin gidan. "Assalamualaikum" Ummeyh tayi sallama a qofan palourn tana neman izinin shiga, Abba dake zaune a ɗaya daga royal chairs en dake palourn yana aiki a system ne ya amsa sallaman ba tare da ya ɗago ba. Umma na dinning area tana haɗowa Abba Black tea tajiyo sallaman ta amsa itama Qarasa shigowa Ummeyh tayi tana faɗin "ayoyooo yayana" sai sannan Abba ya ɗago kai dan tabbatar da muryan da kunnen sa ke jiyo masa, da mamaki ya zare glass ɗin dake maqale a idonsa yana cewa "boɗɗi ke nake gani ko kuwa waye?" Aikuwa ba tare da duba girmanta ba ganin yayanta da ɗan saurinta ta qaraso ta rungumesa yaya nice boɗɗin ka yaya nayi kewanku, Shima rungumetan yayi yana marhababukee boɗɗin yaya mutanen jiddah, Sannuki da hanya qanwata. Umma dake qarasowa palourn jin hayaniyan su ja tayi ta staya da mamaki, yallaɓoi wa nake gani dai kaman Gwaggon yara? murmushi yayi yace "itace dai aminatu" Ai da sauri ta ajiye cup en Black tea en a center table ɗin dake gaban mijin nata, rungume juna suka yi itaida Ummeyh. Umman yara ashe rai kanga rai? Ummeyhn su wannan zuwa haka ba alert ba flashing please call me yo ai ko ɗan beef ɗin nan da ake na corona kya mun nasan kina hanya, dariya duka sa suka qara rungume juna suna dariya. Amun afuwa Umman yara so nake nai maku surprise ke da yaranki da yayana shiyasa banyo maki beef ɗin ba Murmushi Umma tayi ai kuwa kinyi sai dai ni banji daɗi ba gaskiya yo ai da kin sanar dani da ko raquma ce na kadar na ferfesa maki Tom Uwar gida ran gida kuma amaryata ai mun afuwa, kuma yanzuma bai ɓaci ba Kinga dai na tayaki ko gyara kayan yaji ne, murmushi Umma tayi haka zaki ce ai, yanzu dai ga waje zauna bana kawo maki ruwa Dede soja sun shigo da little ya ajiye sa a kan kujera yace "Ummeyh nah sannu da gajiya fa" Tray ɗin da Umma ke isowa da shi ya amsa ya qariso dashi gaban Ummeyh ya ajiye yasa mata ruwan ya miqa mata. Amsa tayi ɗan albarka habeebyn Ummeyh sannunka da ɗawainiya, Ummace tace "ai kuwa dai habeebyn Ummeyh dan shi kaɗai aka faɗawa ana zuwa da ike shi ana sonsa mukam sai akaimu bolar jiddah Ummeyh ajiye ruwan dake hannun ta tayi tana dariya, wato dai Umman yara kin ranste sai kinsa na qware, baki haqura ba ko to shikkenan aqara mun afuwa dan ko shima habeeby sanda na iso ya san da zuwa na. Abba Murmusawa yayi yana sauraran su can sai yasa baki a hiran nasu yace "boɗɗi fita harkan ta so take ta wahalar dake da surutu ko hutawa ba kiyi ba" Soja tashuwa yayi yana dariya yana jin qaunan iyayen nasa ba ruwan su in sun haɗu kaman yara qanana, hanyan da zai sadashi da ɗakin sa yayi yabar su a palourn suna hiran yaushe gamo, a ransa kuwa yana mamaki ko ina yaran suka shiga basu ji shigowan Ummeyh ba duk da uwar marassa jin. Umma tace "za kici abinci ne ko za muje ki watsa ruwa tukun Gwaggon yara? Ta faɗa tana idonta akan Ummeyh. Ah ah matar watsa ruwa dak tukunna duk da de nayi missing na girkin ki uwar gida ran gida, Umma tace "Ai inde girki nane kam zakici har sai ya gimsheki yanzu kamma nida yara na dan made kin shigo Babu flashing kin samu sunje saloon bamu san da zuwan ki ba da mun sani na tabbata ba inda za suje. Ahh no wonder shiyasa naji gidan shiru oganniyan marassa ji bata nan inji faɗin Habeeby Soja. Au kema biye masa kike ko Ummeyhn su, tom dan kuji shi ɗan naki da oganniyan marassa jin zamu haɗa sa sai suje yaga rashin jin da kyau kuma maga qarshen sharrin sa. Ummeyh dariya ta sa "in dai yarona baya so baku isa ba atou" ta faɗa tana miqewa tayi hanyan ɗakin da yake dama masauqin ta ne ko yaushe in tazo. Shiga tayi tana mai qarewa ɗakin kallo, gaskiya a duniya ba abinda zancewa yaya da matar sa sai Allah qara masu zaman lafiya ya raya zuria'a gaskiya yaya yai sa'an mata wallahi, Allah dai ya saka maku da surakunai nagari. Sosai taji daɗin ganin ɗakin da yake mallakinta a gyare staff kaman wanda suka san da zata zo, rage kayan jikinta tayi ta shige wanka. Kayayyakin ta da Joseph ya shigo dasu Umma ta jida tana kai mata ɗaki, bayan ta gama ta jawo mata qofan ɗakin ta rufe ta wuce kitchen Dan haɗa mata abinci me sauqi da kanta (me aikinsu tayi tafiya). AMISCO BEAUTY AND SALOON KD Mahreen zaune ana wanke mata kai, Mahar kuma qafa ake wanke mata Mahreen tace "Kinsan me ? Ta faɗa tana kai dubanta kan Maha". nop sai kin faɗa Wallahi haka kawai yau nake jin farinciki and I don't know why? Taɓe baki Maha tayi, yo waya sani ko ya abydoul ne kuka yi waya ko yake son maki surprise. Murmushi Mahreen tayi, ke dai ba'a yin abin arziiqi dake, waya da ya Abdoul kam ai tun kan mu fito nayi so bana tunanin dalilinshi ne, duk da dai bansan ko surprise en yake son mun ba ni kaman ma nace aiman qunshi wallahi may be ma zuwa zai yi. Kutt ai Addah kina cewa ai maki qunshi sai dai ki koma ke ɗaya nima ni ɗaya kowa ya kama hanyansa haka kawai na zauna zaman jira har ayi har ya bushe har a cire caɓ ba dai Maha ba. Hararanta Mahreen tayi tace "to inna uwasu maida wuqar nima bance zanyi ba kaman inyi nace ai" Dede lokacin aka gamawa Maha wankin qafa, ciro waya tayi a jakan Mahreen, kallonta tayi tace "back to business a ci-gaba d karatu lafiya". Murmushi tayi, Adda ba zaki fahimci daɗin littafin nan ba se kin fara karantawa wallahi dan ya haɗu. Karatunta taci gaba dayi, har aka gamawa Mahreen gyaran kai. Mai wanke kanne ta kalli Maha tace "Hajiya kizo a wanke maki naki kema mun gama na sisternki" shiru bata jita ba. Mahreen tace sister ina zataji ki hankalinta na kan novel, Mahreen ta minstineta du Allah je ki a wanke maki kai mu samu muyi gida yunwa nake ji, turo baki Maha tayi Allah zai saka mun banmaki komi ba. Zaunawa tayi me wanke kan tana dariya qasa-qasa sister plss kamun ku tafi kituramun novel ɗin dan nasan zeyi daɗi yacce hankalinki duka yake kansa ɗinnan, murmushi Maha tayi to zan tura maki. Amma na littafin wacce marubuciya ce plss? Maha tace "Kinsan uwar batoorlerh? No ban gane ta ba gaskiya, amma kaman naji labarin wani book nata MAFARKI NAH ko? Yauwa dai kekam ashe kin gane ta ita dai sunan littafin nata na yanzu JAHILCI KO AL'ADA? Mai wanke kan tace "Wowww daga ji littafin zai haɗu plss zan baki WhatsApp number na in yayi ki bada a sani a group nata dan a wani group na novels naji ana labarin haɗuwan littafin nata na MAFARKI NAH" Shikkenan karki damu sai mun gama sai ki bani ke kuma ki turamun MAFARKI NAH ɗin dan Allah ban qarisa ba. A haka suna hira tana wanke mata qafan har suka gama, me wanke kan nata yabon gashinta gaskiya sister kuna da kyau ke da sistern ki gashinku yamun kyau kaman larabawa. Murmushi Maha tayi bata ce komai ba, dan ita aduniya tana son taji ana yabonta ( abunda ke saurin haɗata da Soja cewa da yake bata da ko kyau) Tura mata book en tayi kaman yacce ta buqata suka yi exchanging number, Suka yi mata sallama bayan sun mata transfern kuɗinta,kasancewan sanja kuɗin da akayi ba a cika samun cash ba, fita suka yi suka shige motor driver ya jasu. Maha ce tace "driver ka kaimu Rufaidah plaza" Ok ma'am Rufaidah plaza ya kaisu, suka shiga suka jido rufaidah ice-cream, rufaidah-bread, rufaidah-chocolate, rufaidah-yoghurt etc. Bayan Maha ta gama jidan abunda suke buqata ta juya kenan wani bawan Allah ya buge ta, saura kaydan abubuwan hanunta su faɗi. Salati tayi, na shigesu da wani makahon na haɗu ni Maha kai jama'a gaskiyan takwaran mutane suna tafiya dai suna layi, qan-qance ido tayi zata yi tijara, sanin halinta Mahreen dake kallon duk abinda ya faru tana qumshe dariyan ta tayi saurin cewa "bawan Allah kayi haquri bata gani bane" ta faɗa tana qara riqe dariyan ta. Murmushi yayi be ce komai ba idonsa na kan Maha dake aika masa da harara tayi qwafa ta juya kan Mahreen tace "Yanzu sabida Allah da Manzon sa Adda ya kama ya bankaɗe ni kaman makaho ne shi yayi abu kuma ki basa haquri gaskiya ni ki dinga tafiyar ki daban nayi tawa daban haka kurum" ta faɗa tana qara haɗe fuska ganin irin kallon da yake mata ji take kaman ta shaqesa. Wucewa tayi qarshe Mahreen ce ta kai kayan wajan accounter(payment table) suka tsaya aka lissafa komi Mahreen tayi masu transfern kuɗin, kasancewan Abba already yasa masu enough kuɗi a account nata. Sa musu akayi a ledan dake ɗauke da tambarin plazan, ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ɗauka yace "madam's we can go". Murmushi Maha tayi, wato dai su anan in ka saya abunsu har motor ake kai maka, abun ya matuqar birgeta ( ita dai har ranta taso girma) Duk abun nan dake faruwa wannan matashin na kallo ba abinda yake yi sai murmushi dan stiwan yarinyar ya mugun burgesa. Bayan sun fice an sa masu ledodin su a motor ma'aikacin ya juya ya koma ciki abinsa. Mahreen har ta shige motor, Maha ta ybude motor zata shige kenan taga wannan saurayin a staye a bayan ta, haɗe fuska tayi a ranta tace "wannan mara ganin kuma uban ne yake nema dani ne" Yawaltaccen Murmushi ne a kwance a kyakkyawan fuskansa, sallama yayi mata yace "Ƴammata in ba laifi ki taimakamun da numbern" Shigewa Motorn tayi bata ko kallesa ba ta banko murfin tana jan staki. Mahreen ta sauqe glass en gefen ta tace masa "brother ga numbern nata zan baka" da murmushi ya za gaya site nata basa numbern tayi yace "thank you sister nagode Allah tsare hanya agaida gida" "Ameen" tace Maha da haushi ya cika ta kaman ta fashe tace "hey you wa kake da suna will you drive the car or i should come and drive us?" Da sauri drivern yace sorry ma'am yaja sukai hanyan gida Mahreen ce ta kalleta tace Allah ya shiryeki Maha wato dai wulaqanci kika sawa kanki ke ba ƴar kowa ba in baki kula samari ba zama za Kiyi ba Aure? Dubi fa yacce bawan Allahn nan ya haɗu ga kuɗi ga kyau. Maha ta tura baki tana hararan gefe "Oho ina ruwanki kuma a kunnen ya Abdoul kin bawa wani gardi layin ki. " hmmn" Mahreen tace kawai bata qara cewa komai ba har suka isa gida yamma liss. Suna sauqa a motor soja na fitowa daga cikin gida, Kallonsu yayi bai ce komai ba ya kau da kai, Maha ta taɓe baki tace a ranta "kai ka jiyo me baqin hali kawai ko ance ma dole in zamu fita sai mun faɗa maka tunda gaka ubanmu oho dai". Mahreen ce tayi qarfin halin cewa "ya habeeby sorry mun je wanke kai ne fa bayan fitan ka kuma Abba ya sani" Bai ce komai ba ya wuce yayi waje, su kuma cikin gidan suka shige da sallama dukan su. Maha na wayyo! Ummata ina kike na gaji washh! Saurin haɗiye sauran maganan dake bakin ta tayi tana zaro ido itama Mahreen zaro idon tayi tana kwalla qara ta mirza ido Wayyooooo!!!!... Wannan kenan ✍️ Muhadu a next page fan's 𝙁𝙖𝙘𝙚𝙗𝙤𝙤𝙠 @ justice Hayratou saleehou eyserh 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥@ 08146292652 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙩𝙥𝙖𝙙𝙙 @ourmmahnbatoolerh 𝙏𝙚𝙡𝙚𝙜𝙧𝙖𝙢@ 08146292652 𝙆𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙨𝙝𝙖𝙛𝙪𝙠𝙖, 𝙙𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙩𝙖𝙛𝙖𝙞𝙣𝙖 𝙎𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙙𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙤𝙟𝙞𝙣𝙠𝙪 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙨𝙝𝙖𝙛𝙪𝙠𝙖 Akan 𝙍𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙚 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞 👌 💦💦💦💦💦💦💦 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣 𝘽𝙮 𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖 (𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl) اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍 _______________________________________________________________ 🅿️ 57&58 💋💋 امى بتولة💋 Dukansu yada ledodin hanunsu suka yi da ihu suna ayoyoooo Ummeyhn mu, da gudu suka je suka faɗa jikinta dukansu. "Wayyoo! Ummeyh na nayi kewan ki" Maha ta faɗa idonta na kawo kwallah Ummeyh ce ta haɗe fuska kinga Umman yara kice su tashi mun a jiki bansan su ba kar su karyawa mijina Ni. Qara qanqameta Maha tayi, Ummeyh Allah ba inda zanje muce munyi kewanki kice mu sake ki, sai ga hawaye sharr-sharrr a idon ta Ummeyh ba kiso kallon mu bama wato, Itama Mahreen idonta ne ya kawo kwalla. Umman yara kina kallonsu ko

Chapter 20 of 25