Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaran naki ba zai wuce nan da 1 week ba in sun samu hutu gobe, daga nan su wuce Adamawa wajan Hajiya Babba ma su gaida ta. Umma tace "shikkenan Gwaggon su Allahu ya kaimu, ta amsa da Ameen. Sallama suka yi ta kashe wayan. Ta qira matan baba qarami suka gaisa da su ma, ta qira su Amarya ma suka gaisa. Ta a jiye wayan zata shiga wanka kenan sai ga qira ya shigo wayan nata dawo wa tayi taga A๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™—๐™š๐™š๐™—๐™ฎ ฦŠauka tayi, sallaman ma da shagwaษ“a aka yi! Murmushi tayi! haba de kaiko sojan Umma, Yanzu fa kai soja n bai kamata kana shagwaษ“a ba. Qara narke wa yayi kaman yana gaban Umman ta sa! Umma ni dai na gaji. Au tom shikkenan daga QATAR en ka wuce JIDDAH. In yaso sai ka dawo tare da mahreen da maha, kaga kamun nan kai ma ka huta acan ษ—in. Dan mun yi magana be jima ba da Gwaggon ku, wai za suzo mana hutu. Turo baki yayi! wato Umma baki son ma gani na yanzu? wata nawa fa ban ganki ba. Murmushi Umma tayi, ba kai kace ka gaji ba? Tura baki ya kuma yi ni umma gida zan dawo. Su zo da kansu in sun tashi zuwa kawai. Wan can fistararriyan wai me take da suna maha koh! In naje zan iya karyata ba ruwana . Iyye sannu baban ta, nace sannu babanta, Ashe Auta har ka girma, kai ma kasan an maka reni murmushi tayi shikkenan adawo lafiya. Turo baki yayi Umma nifa ba yaro ba yanzu. Kashe wayan Umma tayi tace "gwanda kai yaron nan". Aranta kuwa daษ—i take ji kaman ta ga gudan ษ—an nata a gaban ta yanzu ta haษ—iyesa dan farin ciki . ๐Ÿ„ผ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…‚๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…„๐Ÿ…ƒ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ„ฝ ๐Ÿ…€๐Ÿ…„๐Ÿ„ฑ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ„ธ๐Ÿ…‚๐Ÿ„ท ^^Yau take rana ta biyu da za'a ษ—aura daga inda aka tsaya jiya na gasan. Yauma dai kaman jiyan ne sosai filin ya cika da dan dazon taron jama'a wanda kaman sunfi na jiyan ma yawa...... ๐™”๐™– ๐™๐™–๐™—๐™—๐™ž i๐™ฃ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™ง๐™ค๐™ฆ๐™ค ๐™– ๐™œ๐™–๐™ง๐™š๐™ ๐™–, ๐™™๐™ช๐™  ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™– ๐™ ๐™–๐™จ๐™–๐™ฃ๐™˜๐™š ๐™ข๐™ช๐™ฃ ๐™›๐™–๐™™๐™– ๐™—๐™– ๐™™๐™–๐™ž ๐™™๐™–๐™ž ๐™—๐™– ๐™ฎ๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ ๐™– ๐™ข๐™–๐™ฃ๐™– ๐™–๐™›๐™ช๐™ฌ๐™– ๐™ ๐™– ๐™ฎ๐™–๐™›๐™š ๐™ข๐™–๐™ฃ๐™–. ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™ฎ๐™– ๐™ฌ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™—๐™ช ๐™™๐™– ๐™ฃ๐™–๐™ ๐™š ๐™–๐™ก๐™—๐™–๐™ง๐™ ๐™– ๐™–๐™ก๐™›๐™–๐™ง๐™ข๐™–๐™ฃ ๐˜ผ๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™—๐™ž ๐™ˆ๐™ช๐™๐™–๐™ข๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™๐™ ๐˜ผ๐™ก๐™–๐™ž๐™๐™ž ๐™’๐™–๐™จ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ข๐Ÿคฒ ๐™ˆ๐™–๐™จ๐™ค๐™ฎ๐™– ๐™จ๐™–๐™ž ๐™™๐™– ๐™ ๐™ช..... ๐˜ผ๐™™๐™™๐™ช๐™–๐™ง ๐™ ๐™ช ๐™–๐™ ๐™ค ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ช๐™จ๐™๐™š ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™จ๐™ค ๐™ฃ๐™š ๐™– ๐™œ๐™–๐™ง๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™ˆ๐™ช๐™Ÿ๐™š ๐™ฏ๐™ช๐™ฌ๐™–๐™–๐™–๐™– Ba muma yi komai ba tukun yanzu labarin ya fara. ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹ ๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:- 08146292652 ๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ. 09161720046 ๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐Ÿ˜!!! # ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ # ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š & # ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ ๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€ ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ ๐˜ฝ๐™ฎ ๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™– (๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorlโœ๐Ÿ”ฅ) ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค ๐™’๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™—๐™–๐™ง๐™ž ๐™ฆ๐™ž๐™ง๐™ฆ๐™ž๐™ง๐™–๐™ง๐™ง๐™š ๐™ฃ๐™š, ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™–๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™—๐™–๐™ฃ๐™œ๐™–๐™ง๐™š ๐™ฃ๐™–๐™จ๐™– ๐™–๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ž ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ง๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™›๐™ช๐™จ๐™ ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ž ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™ฎ๐™ž, ๐™จ๐™–๐™ž ๐™™๐™–๐™ž ๐™—๐™–๐™—๐™—๐™–๐™ฃ ๐™–๐™—๐™ช ๐™ข๐™–๐™›๐™ž ๐™ง๐™ž๐™ฃ๐™Ÿ๐™–๐™ฎ๐™š ๐™จ๐™๐™ž๐™ฃ๐™š ๐™›๐™–๐™™๐™–๐™ ๐™–๐™ง๐™ฌ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ ๐™š ๐™ฆ๐™ช๐™ฃ๐™จ๐™๐™š ๐™– ๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™ ๐™ช๐™ข๐™– ๐™™๐™–๐™ง๐™–๐™จ๐™ž ๐™ฃ๐™– ๐™ง๐™–๐™ฎ๐™ช๐™ฌ๐™–. ๐™„๐™ฃ๐™– ๐™›๐™–๐™ฉ๐™–๐™ฃ ๐™ฏ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ฆ๐™–๐™ง๐™ช ๐™™๐™– ๐™™๐™–๐™ง๐™ช๐™จ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ ๐™š ๐™ฆ๐™ช๐™ฃ๐™จ๐™๐™š ๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž๐™ฃ๐™จ๐™–. ๐™Ž๐™–nn๐™–๐™ฃ ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ฎ๐™– ๐™—๐™–๐™ข๐™ช ๐™™๐™–๐™ข๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ข๐™›๐™–๐™ฃ๐™ช๐™ฌ๐™– ๐™™๐™– ๐™ ๐™ช๐™ข๐™– ๐™–๐™ž๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฏ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ ๐™ค๐™ฎ๐™– ๐™–๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž. ๐˜ผ๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ ๐™š ๐™—๐™– ๐™™๐™–๐™ž ๐™™๐™–๐™ž ๐™—๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ฎ๐™–๐™›๐™š๐™ข๐™ช ๐™– ๐™ ๐™–๐™ฃ๐™จ๐™–. ๐™Ž๐™–๐™™๐™–๐™ช๐™ ๐™–๐™ง ๐™ฌ๐™– ๐™œ๐™–๐™ง๐™š๐™ ๐™ช ๐™ข๐™–๐™จ๐™ค๐™ฎ๐™– ๐™ฉ๐™–๐™ง๐™š ๐™™๐™– ๐™™๐™–๐™ช๐™ ๐™–๐™˜๐™ž๐™ฃ ๐™ข๐™š๐™ข๐™—๐™š๐™ง๐™จ ๐™ฃ๐™– ๐™‡๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™•๐™„ GIDAN KARAMCI. _____________________________________________________________ ๐Ÿ…ฟ๏ธ 23&24 ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹ ^^^ jama'a ne a cike filin, dan sunfi jama'ar da suka hallara a gasan da akayi jiya yawa. Kamar yacce a kabi daki-daki jiyan da ya kasance ranar farko, haka yau inma komi daki-daki aka bisa har shigowan Gimbiya wannan qayataccen fili, ita da jama'ar ta da kuma masu mata kirari......... Yariman da za'a fara da shi a yau da ya kasance rana ta biyu ne ya fito. Ga Yarima ga Gimbiya a fili!! An gwabza an gwabza a tsakanin wannan Yarima da kuma Gimbiya, gwabzawar da ta ja hankulan kusan dukkan jama'ar wajan domin kuwa wannan haษ—adden Yarima ya gwada jarumta sosai!! In daa wannan Yarima ya yi nasaran taษ“a jikin Gimbiya Mehwish da takobin sa, har ya zama jikin su ya hadu. Wanda a sakamakon wannan haษ—uwan da jikin nasu yayi, da kuma idon sa da ya samu nasaran shiga cikin na Gimbiya, shi ya kasance nakasun sa(weakness) wanda ya temaka wajan qara kashe mai jiki!! Ba tare da wannan Yarima ya fargaba ko kuwa ankara, Gimbiya ta kaisa qasa.. Gaba ษ—aya ranta a jagule yake don kuwa yayi matuqar ษ“aci, wanda wannan ษ“acin rai har ya bayyana a qwayan idanuwan nata,wanda duk da kasancewan su blue hakan be hanasu nuna ษ“acin ran da take ciki ba, domin kuwa sun sauya daga blue zuwa dark-blue. Faษ—i take a ranta, "shi waye da har ya samu daman taษ“a jikina?". Yarima Ammar. Wanda ya kasance na biyu a jerin na yau, shine ya fito fili. Bayan ya shigo fili, sukayi-sukayi suka gwabza shi da Gimbiya kaman ba gobe. Sun tayar da qura har ya cika wajan, kasancewar shima ษ—in jarumi ne. Amma kasancewan ran Gimbiyar na ษ“ace tun haษ—uwan jikin ta da na Yarima Fu'ad, hakan yasa bai samu daman taษ“a ko jikinta ba, koda da takobin sa ne.. Har ta kusa yankan wannan ษ—an sarkin sai dai Allah ya kare kasancewan shima en ba baya ba a wajan jarumta. A haka a ranan sanda ta gwabza da yaran sarakuna biyar, a hakan dai yau ma taron nasu yawaste zuqata wasu cike da farin ciki wasu kuma saษ“anin hakan. Kowa ya koma masauqin sa bayan wastewan taro. Yayin da yaran sarakunan da suka faษ—i ko wannen su ke cike da baqin ciki. Wasun su komawa kawai suke son yi. Gashi Sarki ya basu haquri kuma an riga da an faษ—a masu sai an gama komi kowa zai koma. Sauran yaran sarakunan da basu yi ba kuwa gaba ษ—aya sun sare da irin jarumtar Gimbiyar barin da suka ga yacce tayi faษ—an yau ษ—in. Cewa suke "anya wannan macece kuwa? Qarfi haka da jarumta ace maza tara yanzu duk ta kada su." A haka suka kwana kusan dukkan su da suka rage basu gwabza gasan ba, tunani ษ—aya suke kuma da tunanin yacce zasu kaya a goben suka kwana dashi a rayukan su. ^^ Daga qarshe taya zasu yi wanin su a cikin su da suka rage yaci?^^ In da suka yanke shawaran..... ( nima dai uwar batoorl ban jiba ni daku mu haqura gobe afilin daaga muji.. ) ^^^^A ษ“angaren ita Gimbiya Mehwish. Har ta koma gida ranta a matuqar bace yake, sakamakon daman taษ“a mata jiki da Yarima Fu'ad ya samu. Ta so ace faษ—an ba na gasa bane da tabbas in bai mutu ba se ya rasa hannayen sa dan seta cire masa su. Amma duk da haka ranta wasa! "ba wanda ya isa ya haye wannan gasan da na sanya ko ba su ba na sani" faษ—in Gimbiyar. ( Ni ko uwar batoorl nace za dai ki sani amma baki sani ba kam dan nice nan oum batoolerh nasani, ni keda wuqa da nama) ^^^ Wasta ruwa ta yi. ta gabatar da sallahn ta, shiryawa tayi cikin dogon riga maroon tai rolling da milk veil har ta rufe fuskan ta kaman ko yaushe idanuwan ta ne kawai a waje, haka kawai ta ji ta sanya alkyabba. Black alkyabba ta ษ—auko a closet ษ—in ta, turawa tayi tai hanyan wajen ษ—akin nata dan zuwa sashen da mahaifiyarta take, ta dubo ta. Tana fitowa kuyangun ta suka durqusa suna mata sannu, hanu ta ษ—aga masu. Ganin tana tafiya ya sanya sauran ta shuwa suna ษ—aga mata bayan alkyabban nata! Direct hanyan sashen Sarauniya suka yi dan sun san bata wuce wajan ko kuwa garden(lambu). Suna zuwa dai dai qofan part en Sarauniya suka ja suka staya. "๐™๐™–๐™ ๐™–๐™ฌ๐™–๐™ฃ ๐™ ๐™ž ๐™ก๐™–๐™›๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™๐™ฌ๐™–๐™ง ๐™œ๐™ž๐™Ÿ๐™ž๐™ฎ๐™–๐™ง ๐™ข๐™ช, ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™ฎ๐™–, ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ ๐™–๐™ง๐™š ๐™œ๐™–๐™—๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™—๐™–๐™ฎ๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ž ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™—๐™–'๐™–๐™™๐™–๐™ก๐™ž๐™ฎ๐™–, ๐™–๐™จ๐™๐™ž๐™œ๐™– ๐™ก๐™–๐™›๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™– ๐™›๐™ž๐™ฉ๐™ค ๐™ก๐™–๐™›๐™ž๐™ฎ๐™–, ๐™ฎ๐™–๐™ง ๐™Ž๐™–๐™ง๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™Ž๐™–๐™ง๐™–๐™ช๐™ฃ๐™ž๐™ฎ๐™–,๐™œ๐™–๐™—๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™–๐™ข๐™ช๐™ฃ ๐™—๐™–๐™ฎ๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™–๐™ข๐™ช๐™ฃ ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™ฏ๐™ช๐™˜๐™ž๐™ฎ๐™–, ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™๐™–๐™ก๐™ž, ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™ฃ๐™ช๐™›๐™ž, ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™ข๐™ช'๐™–๐™ข๐™–๐™ก๐™–, ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™–๐™™๐™–๐™ก๐™˜๐™ž, ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ช๐™ฃ๐™ข๐™ฉ๐™–, ๐™ข๐™–๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™ ๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™–, ๐™›๐™–๐™ง๐™–๐™ง ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™จ๐™๐™– ๐™ ๐™–๐™ก๐™ก๐™ค," qirarin da amintattun bayin da ke gadin part en suke ma Gimbiya tun kan isowanta. ฦŠaga masu hanu tayi, shigewa tayi bayan sun buษ—e mata qaton qofan da kaman ba'a cikin gida yake ba. Tana shigewa suka rufe qofan yayin da kuyangun kuwa suka juya, dan ba'a basu daman tsayawa a qofan ba. Da sallama Gimbiya ta shiga ษ—akin da mahaifiyar nata take ciki, "Assalamu'alaikum" jin shiru ba'a amsa ba yasa yanayin ta ya sauya dan sanin da tawa Ammaahn ta ma'abociyar amsa sallama ce in dai bakin ta nada daman furta kalma. Qara sawa bakin gadon da Ammaah ษ—in ta ke kwance tayi, a yacce ta ga yanayin jikin mahaifiyar nata, shi ya qara sa mata damuwa, dan ta so bata labarin abinda ya faru tunda bata samu zuwa ba. Zauna wa tayi a gefen Ammaahn nata, tana mata addu'aoe tana tofa mata har bacci ya ษ—auke ta.. Bayan juya wan kuyangun, suna isa shashin Gimbiya ษ—ayar su ce tace laure kinga kyawun da Gimbiya tayi kuwa da ta sanya Alkyabba? Ni ko na gani hinde ai wallahi da Gimbiya ta san kyawun da Alkyabba ke mata da da dena yawo babu shi. Tabarakhalla Masha Allah, billahillzi laure in nayi aure na haihu sai na wa Gimbiya ta kwara ko zata samu ko da kaษ—an a kyawun Gimbiya ne kuma Allah yasa kan lokacin an samu wanda ya buษ—e mata fuska dan ko kallo ษ—aya na masa da ido na zan kafta hoto na ajiye a zuciyata in nayi ciki nata tariyowa ina kallo. Dariya laure ta saka amma hinde ke dai Allah yaye maki da surutu kinga ma ba na tashi nayi aiki na kan ace gulman Gimbiya muke kin san jakadiya yan zu ta shigo ta sa mana ido. Carab tana rufe baki wata kuyanga ta shigo( wacce farkon labarinmu ta bamu labarin Gimbiya a taqaice) kayan jikinta ba irin nasu bane, "laure wai kukam me yake damun ku ne? Meyasa kuka maida gustiri stome aikin yin ku ne?" faษ—in wacce ta shigon. Wacce aka qira da lauren mae zuba ษ—azun tashuwa tayi tana jakadiya a yafe mu amma dama aiki zamu tashi yi yanzun. Juya wa kuyangar da laure ta qira da jakadiya tayi ta nufi ษ—akin Gimbiya. "Hmmn hinde Wallahi wannan yarinya dan tana ganin itace jakadiya tana wa mutane abinda ranta ke so". "A'a laure gyara batun ki, dan dai uwar ta bata lafiya, ta zauna a matsayin uwarta, kamun ta warke take mana rawar kai. Ai uwar tata zata warke zamu koma dai dai maga qarshen rawan kan nata" faษ—in hinde. Kema dai kya faษ—a, ace wai da ita kaษ—ai aka yarda bayan uwarta, kin ga fa har sashen Sarauniya naga ranan ta fito abinda ko masu gadin ba shiga suke ba. Hinde tace "Ke dai qyale ta maga qarshen rawan kai". Bayan wannan kuyangar ta shige ษ—akin Gimbiya gyare-gyaren ษ—akin tayi ta haษ—a kayakin da za'a wanke ta share ta goge ko ina tass-tass har bathroom nata, ta kunna buner ta kunna wa ษ—akin turaren wuta ta, ta fito da kayan wankin ta ja qofan ษ—akin ta rufe. ^^^ Sai can Sarki ya shigo ษ—akin, sallaman sa ne ya farkar da Gimbiya daga baccin da takeyi. Amsawa tayi tana "Barka da shigowa papa" amsa mata yayi yana mata sannu da gajiya. Murmusawa tayi "Papa ba wani gajiya fa". ai ษ—iyata jaruma ce nasan ba lallai ta gaji ba dama. "Ya jikin Ammaahn taki"? "Papa ga Ammaah kam sai dai muce Alhmamdulillah" ta faษ—a idon ta na kawo qwalla. Kallon ta mai martaba yayi yace "ba'a san jaruma da kuka ba Ebnateeyh, kiyiwa mahaifiyar ki addu'a shine sonki a gare ta ko bayan ranta balle da kuma ran ta, oya karki bari hawaye ya ษ“aga stadadden fuskan ษ—iyar kirkin mu ฦดar albarka, ฦดar Papa da Ammaah". Maida hawayen tayi ta murmusa kaษ—an! Insha Allahu Papa zanke mata addu'a Allah tashi kafaษ—unta ya yaye mata wannan ciwo. "Ameen ya Hayyum ya Qayyum, ko kefa ฦดar albarka" faษ—in mai martaba. Bayan ya zauna gefen matar tasa. Kallon Gimbiya yayi yace "Ebnateeyh meyasa wai kika sanya wan nan buษ—e abun fuskan naki a mazaunin zaษ“an mijinki? Sannan ba tare da shawarin mu ba. Ko dai auren ne ba kyaso? Ba kya ganin ke kaษ—ai Allah ya bamu! Kina da labarin mace bata mulki kuwa? In ba kiyi auren ba ya zakiyi da mulkin? Ko dai ki kinaso mulkin a ษ—aura wanine, bayan kinsan banda kowa nawa! Ni ni kaษ—ai haka na tsinci kai na kaman ke, ko na ce gwanda ke. Tun da ni ko mahaifiya ta baxan ce ga yacce take ba, banma san tana raye ko bata raye ba har. Ki ma kanki faษ—a Mehwish, yin auren ki shi ne farin cikin mu ni da Ammaahn ki." Kanta aqasa tana sauraron mahaifin nata, duk jikinta yayi sanyi da maganganun sa. Magana mai martaba ya qara mata "Ina jinki me yasa kika ce hakan ne a mazaunin zaษ“an mijin aure ki?" "Kayi haquri Papa" haka kawai tace kanta na a qasa har yanzu bata ษ—ago ba. Can nisa tace "Papa ban sa gasan dan wani abu ba. farin cikin ku kai da Ammaah ta shine nawa. Na sanya gasan ne kawai dan na tabbatarุŒ da jarumi zan aura, kuma tsayayye wanda ba wai nice zan tare masa komai ba, shima zai taremun a matsayin sa na wanda ke sama da ni. Wanda in ma ta kama ya mulki masarautan nan, nasan ba iya qarfin mulki ba har da cancanta na qarfin jiki da na zuciya yana dashi, wanda kuma zai yi adalci da qarfin sa ba zalunci ba, wanda zai mulki masarauta cikin amana da zaman lafiya kaman yacce Papa na yake yi. Amma in abinda nayi ya ษ“ata maka rai Allah ya huci xuciyan ka Papa, Allah baka haquri insha Allahu bazan sake wannan kuskure ba." Ajiyan zuciya mai martaba ya sauqe! "Naji dalilan ki amma duk da haka baki kyauta ba kuma bakiyi dai dai ba, sai dai ba komai Ebnateeyh Allah maki albarka ya zaษ“a maki miji nagari." Ta amsa da Ameen, cikin ranta tana hamdala, dan tasan halin mahaifin nata sarai...... ฦณAR SARKI CE Daga alqalaminโœ๏ธ ๐™๐™ฌ๐™–๐™ง ๐˜ฝ๐™–๐™ฉ๐™ค๐™ค๐™ง๐™ก ๐Ÿ”ฅ ******* * kai daga fara chan charas chas chas sai kace hasti duka matan dake wajan sun taso abun su chasssss.......... Muje zuwa my people Ku nishaษ—antu, ku faษ—akantu, ku wa'azantu, sannan ku dara. daga alqalamin uwar batoorl takuuuuuuu ako da yaushe Fatan alheri agare ku masoya alqalamin uwar batoorl a ko ina kuke a faษ—in duniyar nan.... ๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎ๐™ช๐™ ๐™–:- 08146292652 ๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ. 09161720046 ๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, # ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ # ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š & # ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š ๐™๐™ฌ๐™–๐™ง ๐™—๐™–๐™ฉ๐™ค๐™ค๐™ง๐™ก ๐Ÿ”ฅ ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ ๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€ ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ ๐˜ฝ๐™ฎ ๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™– (๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorlโœ๐Ÿ”ฅ) ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค ๐™’๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™—๐™–๐™ง๐™ž ๐™ฆ๐™ž๐™ง๐™ฆ๐™ž๐™ง๐™–๐™ง๐™ง๐™š ๐™ฃ๐™š, ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™–๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™—๐™–๐™ฃ๐™œ๐™–๐™ง๐™š ๐™ฃ๐™–๐™จ๐™– ๐™–๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ž ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ง๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™›๐™ช๐™จ๐™ ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ ๐™ฌ๐™–๐™ž ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™ฎ๐™ž, ๐™จ๐™–๐™ž ๐™™๐™–๐™ž ๐™—๐™–๐™—๐™—๐™–๐™ฃ ๐™–๐™—๐™ช ๐™ข๐™–๐™›๐™ž ๐™ง๐™ž๐™ฃ๐™Ÿ๐™–๐™ฎ๐™š ๐™จ๐™๐™ž๐™ฃ๐™š ๐™›๐™–๐™™๐™–๐™ ๐™–๐™ง๐™ฌ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ ๐™š ๐™ฆ๐™ช๐™ฃ๐™จ๐™๐™š ๐™– ๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™ ๐™ช๐™ข๐™– ๐™™๐™–๐™ง๐™–๐™จ๐™ž ๐™ฃ๐™– ๐™ง๐™–๐™ฎ๐™ช๐™ฌ๐™–. ๐™„๐™ฃ๐™– ๐™›๐™–๐™ฉ๐™–๐™ฃ ๐™ฏ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ฆ๐™–๐™ง๐™ช ๐™™๐™– ๐™™๐™–๐™ง๐™ช๐™จ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™–๐™ ๐™š ๐™ฆ๐™ช๐™ฃ๐™จ๐™๐™š ๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž๐™ฃ๐™จ๐™–. ๐™Ž๐™–nn๐™–๐™ฃ ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ฎ๐™– ๐™—๐™–๐™ข๐™ช ๐™™๐™–๐™ข๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ข๐™›๐™–๐™ฃ๐™ช๐™ฌ๐™– ๐™™๐™– ๐™ ๐™ช๐™ข๐™– ๐™–๐™ž๐™ ๐™ž ๐™™๐™– ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฏ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ ๐™ค๐™ฎ๐™– ๐™–๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž. ๐˜ผ๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ ๐™š ๐™—๐™– ๐™™๐™–๐™ž ๐™™๐™–๐™ž ๐™—๐™– ๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ฎ๐™–๐™›๐™š๐™ข๐™ช ๐™– ๐™ ๐™–๐™ฃ๐™จ๐™–. ๐™Ž๐™–๐™™๐™–๐™ช๐™ ๐™–๐™ง ๐™ฌ๐™– ๐™œ๐™–๐™ง๐™š๐™ ๐™ช ๐™ข๐™–๐™จ๐™ค๐™ฎ๐™– ๐™ฉ๐™–๐™ง๐™š ๐™™๐™– ๐™™๐™–๐™ช๐™ ๐™–๐™˜๐™ž๐™ฃ ๐™ข๐™š๐™ข๐™—๐™š๐™ง๐™จ ๐™ฃ๐™– ๐™‡๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™•๐™„ ๐™œ๐™ž๐™™๐™–๐™ฃ ๐™ ๐™–๐™ง๐™–๐™ข๐™˜๐™ž. *** yau take rana ta qarshe ga masu gasa a masarauta! Yau take sojan umma zai dawo! Yau take Ameera uwar little zata taho Kaduna garin gwamna itama tabar kakus da sinkin sikitin tijaranta! Muje zuwa cikin littafin namu mesuna ๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€ Dan jin ya abubuwan zasu kasance, wa zai lashe gasa? Waye soja? Sannan Ameera na komawa? Muje labari kai tsaye masu karatu!! *** _____________________________________________________________ ๐Ÿ…ฟ๏ธ 25&26 ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹ ^^Zaune suke suna karyawa. Ummace tace "Abban jarumin Umma wai yau ba zuwa kasuwa ne kam?" Wanne zuwa kasuwa kuma Maryama ai sai an qarqare wannan gasa a ido na Insha Allahu. Murmusawa Umma tayi! Tace "Ni ko naji haushi da Jarumin Umma bayanan, dan naso ayi gasan nan a idon sa". Ai ko bayanan dole ma na basa labari Maryama, dan nasan ษ—an ki ko yana nan ba lallai ya yarda yaje wajan taron can ba, mutum sai kace ษ—an aljanu bakason shiga jama'a bakason magana da mutane. Umma ce ta haษ—a fuska tace "nifa Abban jarumin Umma ba nason cin fuska ษ—an nawa ne ษ—an aljanu? Tom ashe ni da kai aljanu ne. Dariya Abba yasa! Allah baki haquri Sarauniya Maryama ta Abban jarumi daga ke ba qari! ฦŠan ki ษ—an mutane ne ba aljanu ba kyakkyawan yaro mai kama da Umman sa. Ba shiri Umma ta murmusa!! "Yauwa ko kai fa mijin Maryama daso". Yanzu dai tunda ษ—an ki baya nan tashi na tayaki ayyuka mu samu muje wajan taron nan da wuri dan so nake in ga qaqa zata kaya, ya zasu qare. Umma ce ta miqe tana cewa "Tom Abban ษ—ana, Nima dai inaso naga mace mai kamar mazan nan ya zata qare gasan, dan da ace yarinyar nan namiji ne ba mace ba, wannan Masarauta ba zata kuka ba dan anyi rashin mai martaba sarki. Amma ita ษ—in ma muna mata addu'an samun miji na gari alfarman Annabi SAW!! ๐Ÿ„ผ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…‚๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…๐Ÿ„ฐ๐Ÿ…„๐Ÿ…ƒ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ„ฝ ๐Ÿ…€๐Ÿ…„๐Ÿ„ฑ๐Ÿ„ฐ๐Ÿ„ธ๐Ÿ…‚๐Ÿ„ท ** inji malam ba haushe yace "๐™™๐™ช๐™  ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™–๐™ ๐™– ๐™จ๐™–๐™ฌ๐™– ๐™ง๐™–๐™ฃ๐™– ๐™ฉ๐™ค ๐™ฉ๐™–๐™—๐™—๐™–๐™จ ๐™ฏ๐™–๐™ž๐™ฏ๐™ค, ๐™จ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™ช๐™  ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ฎ๐™ž ๐™›๐™–๐™ง๐™ ๐™ค ๐™ฉ๐™–๐™—๐™—๐™–๐™จ ๐™ฏ๐™–๐™ž ๐™ฎ๐™ž ๐™ฆ๐™–๐™ง๐™จ๐™๐™š". Kuma ๐™Œ๐™–๐™ง๐™จ๐™๐™š๐™ฃ ๐˜ผ๐™ก๐™š๐™ฌ๐™– ๐™Œ๐™–๐™จ๐™–!! Yau take Ranan fafatawan nasu na qarshe a gasan. Ranar da tayi dai-dai da ranar Asabar(Saturday), Rana ta uku kuma ranar qarshe a gasan. As usual(kaman ko wacce rana) wajan da yake ake yin gasan, ya cika sosai-sosai fun tunani! Kasancewan yau ne rana ta qarshe kowa nason ganin ya abun zai qare, wa zai yi nasara? Za'a samu mai faษ—ar da Gimbiyar kuwa? Daga waษ—an da aka fara dasu har waษ—an da ba suga farkon ba yau sun hallara taro yayi taro jama'a ba masa stinke, kaman ba kowa a cikin Masarautan bayan jama'ar wannan fili dan cikan wajan.(mai karatu kawai ka kwatanta hakan iya ganinka dan taro yayi taro).. Umma da Abba ma har sun hallara suna maqale a wajan( shi kuwa gogannaku baima san mai ke tafiya a garin ba dan tsabar miskilancinsa da rashin shiga hayaniya ko jama'a gashi kuma yana daji). Sarki na munbari wajan zaman sa da fadawan sa kaman koda yaushe. ฦดaฦดan Sarakuna dukkan su kowa na wajan da yake na zaman sa shi da muqarraban sa, da waษ—anda sukayi da waษ—anda ba suyi ba, dukansu sha biyu 12 Yarima Ahmad Yarima Abham Yarima Khalil Yarima Suhail Yarima Fu'ad Yarima Ammar Yarima Jawad Yarima Waheed Yarima Jaay(jabir) Yarima Khaleed Yarima Mu'azz Yarima Abdoul. Duk ko wannen su na mazaunin sa. Gefe guda kuwa wanda yake an qawata shi da ado gwanin burgewa da sha'awa! Gimbiya ce a zaune a wani haษ—aษ—ษ—en kujera da yaci ado, ado irin na sarauta, sanye take da kaya irin na mayaqa da ษ—amaran ta hallau da rolling nata da ya rufe mata fuska, kayan nata daga sama har qasa Black ne,wanda ya amshi fatar ta kasancewar ta fara. Jakadiya na gefen ta a durqushe da kuma sauran kuyangu wanษ—anda daga cikin su na hango, Laure da Hinde, sannan dogarai da suke staye gefe suna mata kirari....... Mutumin da ke riqe da Miche(abun magana) ne ya tashi yai magana, kaman ko da yaushe, sannan ya gaida manyan-manyan baqi da kuma sauran jama'a. Magana yaci gaba da yi kamar haka:- "Kaman yacce muka sani duka, yau shine rana ta qarshe a wannan gasa namu wanda aka ษ—auki stawon kwanaki uku anayi, kuma duk wanda ya cinye bi ma'ana ya samu nasarar buษ—e fuskan Gimbiya tom shine ya lashe gasa. Sannan insha Allahu shine mijin Gimbiyar mu kuma Sarkin mu na gobe, kaman yacce kuma muka sani duka ฦดaฦดan Sarakuna sha biyu 12 ne suke gasan, sannan a yanzu uku ne kawai suka rage waษ—anda ba'a fafata da su ba, a yanzu kuma za'a soma gudanar da gasan wanda muke sa ran yau za'a gama da yardan Allah, ga wanda ke da abun cewa tom fili domin sa, in Kuma babu tom zamu iya cewa, Allah bawa mai rabo Sa'a. Bissalam". Wasiqa aka miqawa wanda ke magana da Miche ษ—in, kawar da Miche en yayi a bakin sa yace "wasiqan Menene?" Dogarin da ya kawo yace "saqo ne daga sauran yaran sarakunan da suka rage" to shikkenan ba mu isar da saqon wasiqan nasu. Buษ—ewa yayi ya karanta, sai da wasiqan ya isa wajan mai martaba yace ba komi sannan aka dawowa da mutumin wasiqan. Magana ya fara yi kamar haka:- Assalamualaiki ya ke Gimbiyar wannan Masarauta tamu mai albarka, ฦดaฦดan Sarakunan da suka rage suna neman wata alfarma, acewan su tunda gasan da mutum ษ—aษ—ษ—aya akeyi, tom alfarman da suke nema shine a yanzu su ukun da suka rage, Yarima KhaleedุŒ Yarima Mu'azz, da Yarima abdoul. Suna son su gudanar da gasan lokaci ษ—aya ma'ana su ukun duka za'a fafata dasu a take, sannan suna fatan mai martaba Sarki da kuma Gimbiya zasuyi na'am da wannan alfarman da suke nema. Jama'a ne suka fara surutu ko ta ina suna cece kuce kowa da abinda yake faษ—a, "wasu na faษ—in hakan baiyi ba, wasu na faษ—in hakan ba dai-dai ba, wasu na faษ—in haka ne ya kamata," kowa dai da abinda yake faษ—a a nasa ra'ayin. Magana mai shelan yayi(wanda yake magana dama) "kowa yayi shiru jama'a, mai martaba Sarki ya amince da wannan buqata naku Yarima Mu'azz, Yarima abdoul, Yarima khaleed. Haka zalika a ษ“angaren Gimbiya tayi na'am da buqatan ku, fatan nasara" ya faษ—a yana neman waje ya zauna. Sarki da yaji abunda mai shelan yace, lumshe ido kawai yayi! yana addu'an Allah ya sa wani a cikinsu su ukun yayi nasara, shiyasa ma yayi na'am da wannan buqatan nasu. Ita kuwa uwar gayyar, ko a jikinta sai ma daษ—i da taji komi zai qare yau Insha Allahu, dan tafisu jin daษ—in amincewan Sarki kuma tafisu jin daษ—in shawaran da suka yake, ko ba komai itama zata huta da shirmen nan. Idanuwan ta ta lumshe faษ—i take a ranta "Ni MEHWISH ba dai

Chapter 5 of 25