Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu Mumy ba..... Washegarin ranan da ya kasance Saturday Mami xata koma can gidan Barrister Ahmad, shopping suka tafi tare da Heedayah, Farida da First daughter dinta Amira dake aure a Abuja, su dai sun yi farin ciki da auren mahaifiyar tasu kilan hakan ya rage mata damuwa sosai, don duk sun san barrister Ahmad, A cikin mota Amira tace "Kinga yanxu Mami sai ki bar ni mu tafi da Farida sai ta dinga xuwa maki hutu kawai ko" Mami dake ta tunanin makomar autar tata tun bayan da aka daura aure don bata ta6a jin tafiya da ita gidan barrister ba, baxai ma yiwu bane, ta kalli Amira tace "Alright dear" Amira na dariya tace "Kinga cikin ruwan sanyi kin bani ita" Babban shopping mall Mami tayi parking suka fita, Amira na rike da hannun Heedayah suka shiga ciki gaba daya, shopping sosai Mami tayi, yaranta na taya ta, Mami da ta lura Heedayah ta gaji da jan ta da ake ta yi, duk ta yi wani laushi, kana ganinta kasan ko kadan bata sa6a da wahala ba koma wani iri, Mami tayi murmushi ta samu kujera nan kusa da counter ta xaunar da ita sannan ta koma gun yaranta, a kan idon wani mutumi dake tsaye shelf din turare yana diba, ya cire glasses dinsa yana kallon Heedayah sannan ya kalli Mami da ta sha corner xuwa gun su Amira....




End of free pages


The book Heedayah is 300 via transfer

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment 07087865788

No regrets....
Patronize ur novelist lovely fans, Allah ya maku albarka ya raba ku da iyaye lafiya...💖



Mutumin ya ajiye turaren hannunsa ya isa gun Heedayah ya tsaya dab da ita yana kallonta bayan yyi make sure bbu me kallonsu yace "How are you?" Juyowa Heedayah tayi da sauri, lkci daya ta mike tana waige waige, shi dai bai sake cewa komai ba yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "ka dawo xaka kai ni gun Ammina ne?" Jin shiru, ta kai hannu to see if he is still there, komawa gefe yyi yace "Ina Ammin taki take?" Tace "A can gidan Yakumbo mana" xai yi magana ya ga Mami ta tsaya daga inda take tana kallonsu, lkci daya ya juya ya koma shelf din turaren da ya baro, Mami ta nufo Heedayah da sauri ta kamo hannunta tace "Me yake ce maki?" Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka tace "shine ya sa ni a bicycle muka tafi..." Mami ta juya wajen da taga Mutumin ya tafi taga wajen wayam, da ido duk ta bi wajen amma bata ga alamarsa ba, Heedayah da hawaye ya cika idonta tace "Baya son inje wajen Ammina" kama hannunta Mami tayi suka bar wajen har sannan tana kalle kallen mall din ko xata ga wannan mutumi, sai da suka biya abubuwan da suka siya sannan suka tafi mota, Mami na kallon Heedayah tace "But ya akayi kika san shi ne?" Tace "Na ji voice dinsa, shine...." Mami bata kuma cewa komai ba har suka bar shopping mall din. Bayan Magrib Shuraim ya iso gida, rabonsa da gidan tun jiya juma'ah da safe, dama ko wajen daurin auren Abban nasa ma bai je ba, sau daya ya kalli motar Abban nasa dake parking space ya dauke kai, ya fita motarsa ya rufe ya wuce xuwa entrance din gidan, bbu kowa parlon, ya tafi parlon Abbansa, sallama yyi still standing at the door, Abba dake rike da makullin mota alamar xai fita ne, ya amsa masa sallama sannan ya bude kofar ya shiga, Heedayah ce xaune parlon kan lallausan carpet da plate din watermelon a gabanta tana sha, kasa karasawa parlon yyi tun da ya ga Heedayah, sai da Abba ya daga kai ya kallesa sannan cike da kasaita ya karasa ciki, gaba daya bbu wani annuri a fuskarsa, can gefe ya duka yace "Ina yini Abba" Abba yace "Lafiya lau" mikewa yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da ido har ya fita, a compound Abba ya samesa xaune shi dai bai ce masa komai ba ya fita da motarsa da nufin maida Heedayah can gidan Mami. Washegari lahadi Abba ya tafi can gidan Mami don ranan xasu tafi gidan Baffa Mami su gaisa da kaka, Abba ne ke driving Mami na gaban motar Heedayah kuma na baya a xaune, jifa jifa suke magana da ya shafi field din aikinsu, Mami dake danna wayarta ta kalli barrister tace "Hope ba dadewa xa mu yi ba wajen mama coz xa mu yi sallama da Amira nan da sha biyu xa su wuce" Abba ya d'an yi shiru kafin yace "I mean it Rahinah... Farida baxata je Abuja ba, are you trying to show ni ban isa riketa ba" Mami tace "A'a ae hutu xata je, in sha Allah xata dawo soon..." Yace "Wani hutun?" tace "Mid term...." Yace "Am damn serious baxata xauna Abuja ba" Mami tayi murmushi tace "To shkkn" a haka suka isa gidan Baffa, bayan Abba yyi parking ya juya yana kallon Heedayah da tayi lamo jikin motar, yace "Heedayah" ta xauna da kyau da sauri tace "Abba" murmushi yyi yace "Hope
ba bacci xa ki yi ba" ta girgixa kai tace "A'a" Ya kalli Mami da ke kallonta ita ma, Mami tayi murmushi tace "Heedayah is more than lazy, tafi son tayi ta bacci" Shiru Abba yyi bayan few seconds yyi kasa da murya yace "Look Rahinah... my mother can be very weird at times kin san ynda tsoffi suke, I know she will welcome you wholeheartedly but.... Akwai halin tsufa dai, so get prepared Mamin Heedayah and Farida...." murmushi kawai tayi, ya bude motar ya fita, ita ma ta fita ta sakko da Heedayah, main parlor Mami ta xauna tana amsa gaisuwan da Yan matan gidan ke mata, Hajiya Hauwa dake kitchen ta fito don ganin su waye, ganin Abba tace "Sannu da xuwa barrister" yace "Sannu Hajiya Jiddah ya gidan" tace "Gida Alhmdllh" da fara'a tana kallon Mami tace "Sannu da xuwa Hajiya, sannun ku da xuwa" Mami na murmushi tace "Yauwa sannu, fatan mun same ku lafiya" Hajiya Hauwa tace "Alhmdllh, you are welcome to the family" murmushi Mami tayi tace "Thank you" Hajiya Hauwa ta tafi dauko ruwa, Abba ya mike ya nufi bangaren Mahaifiyarsu, Hajiya Amina ce ta sakko bayan yaranta sun tafi sun kai mata rahotu sama, tun daga step take kallon Mami har ta kusa faduwa, ta shigo parlon idonta kyar kan Mami tace "A'a Sannun da xuwa Bakuwa, lale marhaba, sannu amarya" Mami ta kalleta ta gefen ido jin salon maganan nata tace "Yauwa sannu" tana fadin haka ta mike tana kallon Hajiya Hauwa da ta ajiye mata ruwa da lemo tace "Hajiya ina ne bangaren mama?" Hajiya Hauwa tace "Mu je in raka ki" tana rike da hannun Heedayah ta bi bayan Hajiya Hauwa, Hajiya Amina ta bi ta da kallo har suka shiga parlon kaka sannan ta koma sama da sauri. Mami na shiga parlon Kaka ta xauna saman babban darduman dake shimfide tace "Sannu Mama" Kaka dake kallonta tace "Yauwa sannu 'yar nan, sannun ku da xuwa" Mami tayi kasa da kai tace "Ina kwana" Kaka tace "Lafiya qlau, kinga ynxun nan na gama karyawa, yau dai ba laifi sun ga daman kawo min karin kumallon da safe, kinsan uwa idan ba taka ba" Murmushi Mami tayi, Abba ya dauke kai daga kallon kaka da yake, Mami tace "To Allah ya rufa asiri Mama" Kaka tace "Atoh, Ameen dai, ni da so nayi ma su bar ni in dinga kayana da kaina tunda ina da karamin kitchen amma Amadu da wansa Umaru sun ki yarda, Kuma fa idan na ci abincin sae inyi ta tashin xuciya tsabar kazantar Yan gidan...." Ba dai wanda yace ma kaka komai, kaka tace "Toh ya sunan naki, kuma yaranki nawa?" Mami ta kalleta tace "Sunana Rahinah, yarana uku" kaka tace "To yaran me ya hanasu xuwa gaisheni bayan an riga an xama daya kuma??" Kafin Mami tace komai Abba yyi saurin cewa "Heedayah You didn't greet grandma" Mami ta daga Heedayah ta maido ta kusa da kaka tace "Greet her" a hankali Heedayah tace "Ina kwana" Kaka da ta saki baki tana kallonta tace "To wnn kuma wani irin kaya ne aka sa mata kamar 'yar anna, abu duk a d'angale jama'ah? Rahilah kike ko wa? Gaskiya kar ki sake sa mata wa Innan tsinannun kayan, da da idonta ma baxata bari a cuce ta a saka mata wannan kaya ba" Mami na murmushi tace "To in sha Allah baxa a sake ba Mama" Kaka tace "Kuma kar ki sake yi mata karin gashi ki rufa mana asiri mu ba hka muke ba" Mami tace "Ae gashinta ne mama" kaka ta cire hulan kan Heedayah tace "Auuu, to maa sha Allah, daga gani ba daga irin tsiya ta fito ba, nima dai ance ina kamarta gashina har gadon bayana wllh...." Abba ya mike yace "Baaba xa mu je, ana jirana ne" Kaka tace "Ko dai har ta tare bani da labari?" Yace "Aa tukunna" Kaka tace "To sai yaushe?" Abba xai yi magana kaka tace "A'a ni ba ruwana, ita bata da baki sae kai, ni da ita nake ba da kai ba ae koh" Mami tayi murmushi tace "Ko nan da sati kaka" Kaka tace "Toh dai kiyi ki tare kafin matar tasa ta dawo, kinsan tana d'an tabin hankali, ko da yake dai gadonsu ne, ga shi kuma ya hade da an mata kishiya, ke dai ba ruwanki da ita kiyi ta kanki ki kula da marainiya tsakanin ki da Allah, parlon ki na nan tikeke da uwar daka har da bandaki ba ruwanki da fitinanniyar, kitchen kuma ya fi parlon nan nawa da kike gani girma, komai kike son xubawa naki ki xuba duk xai cinye wllh...." Abba yace "To bari mu je Baaba" Mami dake ta murmushi kawai ta duka xata daga Heedayah, Kaka tayi saurin cewa "Kai ku ji mata ba yini ku ka kawota ta min ba dama, kinsan ynda muke da ita ne? D'a na fa ya tsinto ta tana galantoyi a titi" Mami ta mike tace "To shkkn mama, sae anjima" kaka tace "Ko anjima da daddare ba sai ki xo ki tafi da ita ba" Abba tuni ya fita, Mami tayi ma kaka sallama ita ma ta fita. Kaka na kallon Heedayah da jikinta yyi sanyi jin an tafi an barta tace "To sun baki abincin ma kuwa, don naga Amadu har wani rawa kansa yake shi a dole yyi amarya" Heedayah ta gyada mata kai kawai, kaka ta mike tace "Ni dai ba ruwana don ba barinsu Allah xai yi ba idan suka bar ki da yunwa" cup ta dauko a inda take jera su ta dawo ta bude flask ta debi ruwan xafi, shayi me kauri sosai ta hada a cup din ta bude bread ta dau slice biyu ta daura a plate ta debo dambun nama da tsoka uku na nama ta watsa kan plate din ta ajiye ma Heedayah a gabanta tace "gashi nan maxa ki cinye ki bani kwanuka na, duk cikin ki ya hade da bayanki kice min kin koshi" tana fadin haka ta mike ta koma daki tana cewa "Haka matar ta xo tsiya tsiya ba komai, kamar ta baxata kawo d'an lemonta ko ma dai turare ba tace gashi kaka" tabe baki tayi ta ci gaba da linkin da take. Heedayah dae na xaune da shayi a gabanta don ba yunwa take ji ba, ita din ba wata me cin abinci bace sosai, bude kofar parlon aka yi a hankali, Sudais ya shigo, direct inda ya hango turarensa da kaka ta dauke jiya ya nufa don dama abinda ya kawo sa kenan, ya duka xai dauka kenan ya ga Heedayah dake xaune, mikewa yyi tsaye yana kallonta sannan ya nufeta ya duka gabanta, she looks so sad, shi dai ya kasa yarda da abinda Shuraim yace masa wai fararen idon nan nata basa gani, hannu ya kai har kusa da idon ya ga bata motsa ba, ya sauke hannunsa a hankali, murya can kasa yace "How are you?" Juyawa tayi da sauri jin murya kusa da ita, Amma kuma tayi shiru tayi tana kallonsa directly in the eye, yace "How are you?" a hankali tace "Fine" yace "To ki sha shayin ki...." Tace "Na koshi" hannu ya sa aljihunsa ya fiddo chocolate biyu ya kamo hannunta yace "Toh ga chocolate ki sha, ko in bude maki?" Ta gyada masa kai, ya bude guda daya ya saka mata a hannunta, xai yi magana sae ga kaka ta fito, tana ganinsa tace "Ni dai wllh ba ruwana idan baki na ya bi ka Aliyu, nace kar ka sake xuwa min nan xan ja Allah ya isa, Kuma wllh na ja a raina tun ranan" Yace "Tunda ke ba Baffa bace kuma ba Umma bace me xai dameni, Allah ya isan ki iyakarsa lebenki" ko kadan bata ma san me yake cewa ba, don bude baki tayi kawai tana kallon shayin gaban Heedayah, can tace "Naga ikon Allah, Ke baki sha shayin bne har ynxu kika bar shi a walakance?" Heedayah ta marairaice tace "Na koshi" kaka tace "Amma ke dai muguwa ce, kina kallo ina hada shayi duk na yi barna da madarata da banvita kiyi shiru ki kyaleni sbda mugunta??" Sudais yace "To da idon ki taga kina hada shayin ta maki shiru kaka" Kaka tace "Ba ruwana da wnn, ance maka haka Allah ya bar su, duk suna sane da komai ke faruwa a inda suke, kawai tayi niyyar walakanta ni ne, amma tana sane lkcn da nake kada shayin" Sudais ya dau cup din shayin yace "Toh bari in Shan....." Kaka tace "Haram.... Ban baka ba har xuciyata, Amadu ne ya siyo min kayan shayin ba Umaru ba" dariya yyi yace "Toh shi din ba Abbana bne, Kuma ae dama abincin Haram dadi ne da shi" kaka ta fashe da kuka ta nemi kujera ta xauna, sai da ya shanye shayin ya ajiye mata cup yyi ficewarsa..... Hajiya Hauwa ce ta kawo abincin rana bayan azahar, Heedayah na xaune kan darduman da Kaka ta shimfida mata wai tayi sllh, Hajiya Hauwa da suke ce ma Aunty a gidan, ta gaida kaka tace "Ga abinci kaka" kaka tace "Toh yau dai kun bar yunwar ta gigitani gaskiya, Amma bbu komai Allah yyi albarka, amma fa ni dai nasa yar nan tayi sllh bn san ko ba musulma bace" dariya sosai Aunty tayi tace "Musulma ce mana kaka" kaka tace "Atohh naga dae ta iya alwalar..." Aunty tayi murmushi tana kallon Heedayah ta isa kusa da ita ta kai hannu kanta tace "Bari in kawo maki naki abincin kin ji daughter?" Heedayah ta gyada mata kai kawai, Aunty ta juya ta fita, sae ga ta ta dawo da plate din shinkafa da miya da salad a gefe sae neman kaza ta ajiye gaban Heedayah tace "Ki jira ya huce sae ki ci, kaka xata baki ruwa idan kika ci" daga haka ta fita, kaka na kallon Heedayah tace "To me kika yi ma iyayen naki suka sallama ma duniya ke d'a na ya kwaso ki?" Heedayah dai bata ce komai ba don Hausan ya mata girma, kaka ta tabe baki tace "Toh, Allah shi yasan dai dai, mu dai gashi mun kwaso ki bbu dangin iya balle na Baaba, muna neman lada wajen Allah" Bayan la'asar Kaka ta kwashe Yan wanke wankenta ta bude wani kofa da xae fitar da ita bayan gidan, inda aka yi mata pamponta ta kada kumfa ta ajiye ruwan dauraya ta dawo ta daga Heedayah dake bacci tace "Taso ke ma a dinga cin amfanin ki ba wai ki ci ki sha kiyi kashi kiyi ta bacci ba, tun xuwan ki kike bacci" a haka ta kai ta bakin tap ta xaunar da ita kan kujeran tsugunno dake wajen tace "Maxa kiyi ta lalubawa kina daukan kwanukan kina wankewa ga ruwa a gefen ki, mace kike gidan wani kuma xa ki" daga haka kaka ta wuce ciki ta bar ta, tunda Heedayah take bata ta6a wanke wanke ba, bata ma san meye shi ba, hka ta dinga daukan kwanukan tana tsoma su cikin ruwa tana fitarwa, har taji bbu wani nan kuwa duk suna gefe daya a ajiye, mikewa tayi pink wandon jikinta da ya wuce gwiwarta a jike jagab, kofa taji an bude a tunaninta kaka ce tace "Na gama" duk a tsorace take hannunta rike da plate biyu da cup daya, Shuraim ne tsaye bakin kofar alamar shigowansa kenan gidan a tunaninsa kaka ce backyard din, hannu Heedayah ta sa tana laluba wajen xata wuce ta ci tuntube da kujeran da ta tashi daga kai, cikin few seconds komai ya faru, duk da effort din Shuraim kuma jikinsa ta fada hakan bai hanata buge kneels dinta a kasa ba, shirun da Shuraim ya ji tayi ya sa yyi saurin daga kanta yana kallon fuskarta, sae a sannan ta wara ido ta fasa wani ihu da ya raxana shi, lkci daya ta kankamesa tana cewa wayyo kafanaa, kaka ta saki flask din ruwan xafin hannunta ta taho a guje tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, yar mutane ta mutu a gidana, na shiga uku na banu, me xance ma Amadu" Shuraim ya kalli kafan nata yana kokarin dagata ta rirrikesa cikin kuka tana cewa "Wayyo a kai ni wajen Abba, wayyo Abba ya xo...." kin fitowa kaka tayi ta dinga lekowa jikinta na rawa, Shuraim ya hade rai, ganin Heedayah ta ki tsayawa yace "Baxa ki tsaya ba sae na mare ki?" Kuka sosai take yi tace "Baxan iya ba kafan yana min ciwo..." Daukarta yyi ya shiga parlon kaka da ita ya kwantar da ita saman kujera yana kallon kafar, cikin rawar murya Kaka tace "Kaddai karyewa kafar yyi Ali?" Ta gefen ido Shuraim ya kalleta kafin ya mike yace "Ni na sani..." Kofa ya nufa zai fita ta cafkosa ta fashe da kuka tace "Don Allah ka rufa min asiri ka duba mata kafar tun da kai ma likita ne, Kar Amadu ya kullaceni, wllh sai in iya tattara kayana in gudu ba ruwana da bacin ran Amadu, ya takarkare ya tsinto yarinya kuma ace a gidana ta karye...." Heedayah dai sai kuka take tana kiran Abba, kaka ta xauna kasa ta saki matsanancin kuka tace "Ka ji algungumar wai Abba ko??" Shuraim ya hade rai yace "To ina xuwa in dauko abu a mota" daga haka yyi ficewarsa, dawowar da bai sake yi ba kenan.
Abba ne tsaye kan Heedayah dake bacci saman gadon kaka, Mami kuma na xaune gefenta tana rike da hannunta, Aunty da Baffa da Umma ma duk suna dakin, kowa yyi jigum, can na hango kaka rakube jikin kofar bandakinta ko ganinta bata son a dinga yi sosai, Baffa yace "Toh wai ma ina aka ta6a sa mara ido aiki fisabilillahi??" Kaka tace "A'a ni dai kar a min sharri ita tace xata yi, tana ganin na hada kayan wanke wanken tace Kaka kawo in taimaka maki, to sai in hanata sbda mugun hali ko me? Kuma da kke wnn maganar so kke Allah ya tambayemu tarbiyar da muka mata? Don tana makauniya shkkn sae a fake da haka a ki bari ta ta6uka komai??" Baffa yace "Ta ina makaho xai iya wanke wanke kaka???" Kaka tace "Ni dai kar a min rashin kunya ba ruwana, Kuma flask din ruwan xafi na da ya gamu da ajalinsa daxu da plet dina da suka fashe guda biyu duk a biyani kayana, hatta kujerar tsungunnon ma yyi targade ba ita kadai ba, targade mana tunda kafa daya ya karye, Kai kuma Amadu wllh jidali ka haifar ma kanka kana tunanin d'a ne, sam xuciyar wnn yaro naka shuree yake ko wa, bashi da kyau, xuciyarsa bakikirin yake, ni Yaron ma idan ba tsoro yake bani ba shegiya nake, mugu ne axxalumi na bugawa a jarida, wllh yarinyar nan na tsala ihun axaba gwanin ban tausayi ya tsallake da shegen idanuwansa kamar naka yyi wucewarsa ko ta mutu ko tayi rai oho, tsaf xai iya kashe mutum har ya kai sa makwancinsa, ni abun hannunsa ma na daina ci daga yau, inda Sudess ya fi sa kenan, shi dai bar shi da cin Haram amma xuciyarsa fari ne fatt wllh" Abba dai bai ce komai ba kuma bai kalli mahaifiyar tasa ba....


I appreciate ur patronage and patient fans, Allah ya kawo budi me yawa ya bar mu tare.... Su kuma masu jiran Heedayah su karanta a bati, here is it... But don't forget it's not free, it's nothing don ka fidda dari uku kayi subscription to read what gives you so much joy, bbu abinda hakan xai raga ka da shi, and it's a way of showing u appreciate ur novelist and her handwork, don't forget writing isn't easy even if it's a hobby..... I Khaleesat Haiydar write just once a year and I make sure na sa farin ciki a xukatan mutane da dama, toh me yasa nima baxa a min haka ba, patronize so I will be happy too.... kyautatawa ma yana cikin so ai... 😇
All the same ina ma kowa fatan alkhairi, anywhere, anytime.💖


Heedayah is 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then u show ur evidence my WhatsApp digit 07087865788 sai in sa ka group.


Parking Junaid yyi kofar gidan Baffa ya kashe motar sa ya bude ya sauka, sanye yake da kananun kaya, walking calmly ya isa gate suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga gidan, baya bukatar tambayar entrance don tuni ya hango, yana isa bakin kofar yayi knocking, bbu bata lkci aka bude kofar, kanwar Sudais ce ta bude kofar, yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Good evening" tana kallonsa irin kallon rashin sanin tace "Welcome..." Muryar Abba suka ji yace "Is that Junaid" Junaid yayi kasa da kai yace "Ina yini Abba" Abba yace "Lfya lau, Zainab ki kai sa bangaren Kaka" Zainab na kallon Junaid tace "Toh" bin bayanta yyi suka nufi parlon kaka, Abba kuma ya fita rike da makullin motarsa, da sallama Junaid ya shiga parlon kaka, Mami dake tsaye rike da jakarta alamar xata wuce ta juya tana kallonsa, Kaka ta kalli Junaid sannan ta kalli Mami tace "wannan ne d'an naki?" Mami tayi murmushi tace "Eh Mama" kaka tace "Ahh ba shakka... Kyakkyawan bafillatani da shi wllh, ya ma fi ki kyau ai, da ganin ubansa ya yo...." Mami dai na murmushi tace "To sai na shigo da daddare kaka, bari in je" kaka tace "A'a ki yi xaman ki kar ki wani wahal da kanki ba gashi ina kula da ita ba tsakanina da Allah...." Mami tace "Toh shkkn mama" Daga haka ta fita parlon, Kaka na kallon Junaid dake tsaye har sannan tace "To kai ko ka xauna mana d'an nan" ya xauna smiling broadly, with respect yace "Ina yini" Kaka na washe baki tace "Lafiya lau, ya sunan naka?" Yace "Junaid Muhd..." Tace "Junaidu sai kaji kuma wai yarinya ta gurde koh? To ni kai na ban san yanda akayi wnn bala'i ya faru ba, amma dai na gode Allah tunda ba karyewa tayi ba...." Junaid yace "Allah ya kara kiyaye gaba" Kaka tace "Ameen kai dai.... Don ma uwarka na da fahimta na lura ita ta lallaba Amadu bai dau abun da xafi ba, kasan sa da xuciya, Kuma kasan shi ya tsinto makauniyar a titin kano tana galantoyi...." Junaid dai bai ce komai ba, kaka tace "To ka leka ta tana bacci can uwar daka ka duba ta, amma ta fiye son jiki yarinyar, d'an bugewa fa kafar yyi amma duk makota bbu wanda bai shigo gidan nan ba, ke Zainab kai sa ya ganta, kuma bance ki tsaya kusa da kumbo na ba, kinfi kowa min sace sace a gidan nan" kasa motsi Zainab tayi, shi dai junaid kansa na kasa, kaka ta ja tsaki ta mike tace "Haka nan suke min ban isa in sa su aiki ba, ae dai kaga taki kai ka, to ba ruwana ba biyesu nake ba, tunda 'ya yana

Please Login or Register in order to submit comment