Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga bayansu, sai da suka sauka Abuja Nigeria da asuba Mami ta tada Heedayah suka sauka jirgin tana rike da hannunta, sai makalewa take jikin Mami don bata son kowa ma ya ta6a ta cikin masu saukowa kallon dodo take masu, ta dinga bin ko ina da kallo bayan sun sauka jirgin tace "Mami babu Light a Nigeria din dama?" junaid ya kalleta kafin yace komai Mami tace "Noo, asuba ne har yanxu ai, anjima xaki ga haske ko ina dear" ta kalli Junaid xata yi magana sai kuma tace "Ohh not you, Yaya Sudais a nan xa mu bar jirgin mu tafi?" Junaid yace "Aa xa a daura maki a kai ne ki kai gida" Ta kalli Mami tace "Mami kin gansa ko? Nice xan iya daukan jirgin a kai na?" Mami tace "Aa sai dai shi a daura masa a nasa kan" Heedayah tace "Toh Mami ai shi ma baxai iya ba, naga kato ne ai jirgin" Sudais ne ya samar masu Taxi cab yana kallon Mami yace "Train station din xa mu wuce?" Mami tace "No this 4 am, mu tafi gidan sister na, xuwa biyar da rabi sai mu wuce station din" yace "Ohk" cikin mintuna kadan suka isa gidan Hajiya Asiya, sosai matar ita ma tayi murnar ganin anyi sa'ar aikin duk da suna chatting da Mami tun a India Mami ta sanar mata Heedayah ta warke, wanka kawai suka yi a gidan suka yi breakfast shi ma da kyar don Hajiya Asiya ta damu su yi, duk suka yi sharp sharp sbda su samu train going to Kaduna da safen, Driver din Hajiya Asiya ya kai su train station din.... Karfe tara da wani abu suka isa train station na Kaduna, duk suka sauka train din.... Mami na kallon Sudais yace "Sun taho daga gidan ne?" Sudais yace "Ehh ya turo min text ya iso" a wajen station din suka ga motar Shuraim a Parke, Bude motar yayi ya sakko Heedayah ta dinga kallonsa irin na sanka din nan har ya iso Inda suke, ya gaida Mami, Mami ta amsa, hannu ya mika ma Sudais sannan junaid da ya dinga danna waya ya ki dagowa har sai da Sudais ya d'an bugesa, sai a snn ya dago kansa ya amshi hannun Junaid, Heedayah dai sai binsu take da ido ganin abinda suke yi da hannu, ganin Shuraim xai juya ta mika nata hannun tace "Ni fa?" Very serious tayi maganan, hakan ya ba Mami dariya sosai Sudais na tayata, Shi dai Junaid murmushi kawai yyi still pressing his phone, Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya nufi motarsa, a hankali Heedayah tace "Mami me yasa ni bai min ba?" Mami tace "Maxa ne kawai suke yin haka" Tace "Mami na ta6a ganinsa ranan nan" Mami tace "That's Shuraim" Da sauri Heedayah ta kalleta tace "Shureen?" Mami tace "Yes" back seat Mami ta shiga da Heedayah dake ta kallon Shuraim, Sudais da Junaid suka gama saka kayan a mota, Junaid ya shiga back seat, Sudais ya shiga gaba, Shuraim ya tada motar suka dau hanyar gida... Bbu me magana cikin motar sai Heedayah da ta kafe idonta jikin windscreen komai ta gani sai ta tambayi Mami, Mami kuma ta bata amsa, lkci lkci Shuraim ke kallonta ta madubin gaba, hada idon da suka yi da Junaid ya sa bai sake kallon Madubin ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin suka iso, gida Mai gadi ya bude gate Shuraim ya shiga da motar, Mami ta kalli Heedayah da ta kura ma gate ido tace "We are home" Heedayah ta juyo da sauri tace "Xan ga Abba yanxu?" Mami tace "Yess of course" Bude motar Sudais yyi ya fita, Junaid ma ya fita sannan ya xaga ya bude ma Mami bangarensu, Mami tace "Sauketa" Da sauri Heedayah dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tace "No xan sauka da kai na" Tana fadin haka ta lallaba a hankali ta sauka tana kallon interlock din gidan, Mami tayi murmushi ta fito Junaid ya rufe motar, Abba ne ya fito balcony ya sakko yana kallonsu gaba daya, Mami ta xagayo da Heedayah tana murmushi ta nuna mata Abba tace "There..." Heedayah ta kalli Mami tace "Abba?" Mami tace "Yes, go to him" tafiya ta fara ya a hankali, Abba dake murmushi ya bude mata hannunsa, hakan ya sa ta tafi da gudu, ya rungumeta tace "Abba I can see everything now, I can see you also" tana magana tana ta6a fuskarsa Abba yace "Alhmdllh daughter, now say Alhmdllh Ya Allah" Heedayah tace "Alhmdllh Ya Allah" Junaid da Sudais dai na tsaye suna kallonsu, Abba ya daga kai ya kalli Mami dake tsaye tana kallonsu ita ma, karasawa wajensu yyi yana rike da hannun Heedayah, Yyi patting shoulder dinsu yana murmushi yace "Allah yayi maku albarka my boys, I am so proud of you two..." Duk suka amsa masa da Ameen smiling back at him, Kallon Mami yyi ya nufeta, still smiling yyi mata side hug, karaf a kan idon Mumy da ta makale jikin window a parlon sama tana lekosu tun shigowar motan gidan, ji tayi ta kasa tsayuwa ga wani abu da taji ya soketa a xuciya, bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta sake labulen da sauri, Abba na kallon Mami softly yace "Welcome back Dear Rahinah, Allah yyi albarka, I will for ever be grateful to you.... Knowing you is one of the sweetest thing I can admit to in life, I am so proud of you wife" Mami dai sai murmushi take, tuni Shuraim yyi wucewarsa ciki, Abba na rike da Heedayah tare da Mami suka wuce cikin gidan, ko Abba bai fadi ba you can see how happy he is, ita kanta Heedayah lkci lkci sai ta kalli Abba ta sakar masa murmushi, sai bayan da suka shiga parlor ta dinga bin parlon da kallo kamar munafuka, Rabi'ah da Khadijah na tsaye duk suna jiran shigowar Heedayah, Abba ya nuna mata su yace "Ur sisters" a hankali tace "Hi" ganin yanda Abba ke kallonsu duk suka ce "Hello" Heedayah ta kalli Abba tace "Abba kaka fa?" Abba yace "Anjima xata dawo in sha Allah" Mami na kallon Abba tace "Let me go and freshen up barrister" yace "You need to dear, Allah ya huce gajiya, sai na shigo" Ta amsa da Ameen ta nufi part dinta, Heedayah ta kwace hannunta a na Abba tace "Mami are you leaving me" Mami ta juyo tace "No dear, stay with Abba a little" Abba yace "Mu je ki gaida Mumy" Heedayah bata ce komai ba yana rike da hannunta suka wuce bangaren Mumy. Mumy na bedroom dinta tana waya da Sadiya tana sanar mata ai sun dawo, ynda take kukan a wayan kai kace mutuwarta aka nuna mata, Sadiya tace "Toh wai ke meye na kukan, dama ba jiran dawowarsu ake ba ne, ae ke abun farin ciki ne ma a gare ki da suka dawo yanxu" Cikin kuka tace "Baxa ki gane ba Sadiya dole inyi kuka, dole inyi kuka, rungumeta fa naga Barrister yyi tana wani murmushin kissa, ko kunya bbu a gaban yaran gaba daya ya rungumeta wllh" Sadiya tace "Ita Rahinar?" Mumy tace "Wllh, runguma fa sosai, yaushe rabon ya kama hannuna ni balle ya rungume ni a kan idon wani, a fa tsakar gida ya rungumeta" Sadiya tace "Bbu komai ki kwantar da hankalin ki, da ba mu da mafita ne shine xa ki yi kuka, Amma ga mafita iri iri dai, abu tun yaushe muke baxa idon dawowarsu kuma gashi Allah ya dawo da su lfya" Jin an bude kofa Mumy tayi saurin cewa "Xan kira ki anjima, an shigo parlona" Daga haka ta katse wayar tace "Waye?" Jin shiru ta mike tana kara goge idonta sosai ta fita, Abba ne tsaye yana rike da Heedayah, Mumy ta sake fuska tace "A'a, mutan India har an iso kenan, toh kun sha kabo, Alhamdulillah, Sannun ku da dawowa" Heedayah dai sai kallonta take a tsorace jin muryarta, Abba ya sake hannunta yace "Go and greet her" a hankali Heedayah ta nufi Mumy dake kirkiran murmushin karfin hali Mumy ta jawota jikinta sosai ta rungumeta tace "Alhamdulillah ido ya bude, Alhamdulillah mun gode Allah" Murya can kasa Heedayah tace "Good morning" Mumy ta dago kanta tace "Good morning ya kike, Ina Mamin ta ki?" Heedayah ta nuna mata hanyar waje, Mumy tace "To maa sha Allah, Allah ya huce gajiya" Abba yace "Sai ki samu ki tafi kiyi ma Rahinar sannu da xuwa" Mumy tace "A'a ba abinda xai hana haka ai" Mumy ta xaunar da Heedayah kan kujera tace "Kun yi breakfast kuwa?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mumy tace "To bari a hado maki shayi" ganin haka Abba ya fita ya bar Heedayah a parlon, Mumy ta bi sa da kallon gefen ido, can ta kalli Heedayah tace "Kar fa ki fita, Ina xuwa in kawo maki shayi, xa ki ci har da bredi Koh?" Heedayah ta gyada mata kai, Mumy ta nufi kofa ta bude kafin ta fita sai da ta sake kallonta tace "Kar fa ki fita, Ina xuwa yanxun nan in kawo maki kin ji" Heedayah ta kara gyada mata kai, Mumy ta fita da sauri, Mumy na fita da few minutes aka bude kofar sai ga Shuraim ya shigo, Kallonta ya dinga yi daga Inda take xaune with surprise, can ya kalli kofar dakin Mumy ya karasa ya leka ciki bai ganta ba, dawowa yyi ya bude kofar parlon yana kallon Heedayah dake ta bin sa da kallo ya nuna mata kofar alamar ta fita, Tace "Mami tace min door ne... It's a door" ya wani daure fuska, da sauri ta dauke kanta, Ya dake yace "Xo ki fita nace...." Mikewa tayi tsaye da sauri tana kallonsa don ranan ya fara mata magana, kamar munafuka tace "Tea xa a bani da bread" Ya kara daure fuska yace "Fita na ce" da sauri ta karasa gun kofar ta bi ta gefensa ta fita tana waigosa, ganin inda xata bi ya bi bayanta da sauri, ya gwada mata hanya da finger dinsa, part din Mami da ya nuna mata ta nufa, da tayi tafiya kadan sai ta juya taga yana tsaye yana kallonta, sai da ta d'an yi nisa sannan ta juyo ta tsaya tana kallonsa ita ma, ya xare mata ido yace "Baxa ki wuce ba" 6ata fuska tayi ta juya ta nufi kofar shiga parlon Mami hawaye cike idonta tana isa kofar ta kara juyowa ta tsaya tana kallonsa, sun fi minti daya a haka yana kallonta tana kallonsa.... Daukar remote da ke kan kujera yyi, yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta durkusa a wajen, da sauri ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta bude kofarta jin muryar Heedayah tana kallonta tace "What happened?" Kamar xata yi kuka tace "Wannan da kika ce min Shureen ne, I heard his voice, xai min doka wai" Mami na bin parlon da kallo tace "Ina yake?" Heedayah tace "Ya gudu" kama hannunta Mami tayi suka shiga ciki, Mumy ta fito kitchen rike da cup din shayi da bredi da nama a plate ta wuce parlonta, turus ta tsaya ganin bbu kowa parlon, can ta nufi daki nan ma bbu kowa, ta dake tace "Heedayah?" Nan ma shiru, Ficewa tayi dakin ta wuce parlon Abba, ta samesa dakinsa, rai bace tace "Kai da ka bar yarinyar nan a parlona baka san abinda kke yi bne barrister, Wai daga in je in hado mata kayan kari shine har an shiga an dauketa..." Abba ya dakatar da ita yace "Aa, ta dai fita, wa xai shiga ya dauketa" Mumy tace "Wllh wllh shiga aka yi aka dauketa don na jadadda mata kada ta fita tace min toh, wllh dauketa aka yi" Yace "To wa xai dauketa??" Tace "Oho na sani" yace "To sae ki kai mata can parlon" tace "Baxan je ba wllh, ikon dai da ake nunawa bani da shi a kanta a ci gaba" daga hka ta fice daga dakin rai bace.... Jin shiru shiru Mami bata ga junaid da Sudais ba ya sa ta kira Junaid, nan ya sanar mata wucewa suka yi, fita tayi parlonta ta tafi dakin masu aiki ta bude tana kiran Sajida, wata mata ce ta mike tace "Aa ni ce, Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau, Ina Sajidar?" Matar tace "Ni ce sabuwar mai aikin ynxu" Mami tace "Tohhh, to Sannun ki" daga haka ta juya ta wuce xuwa kitchen ta hada ma Heedayah da ita kanta shayi.




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Da yamma Mami na xaune main parlor da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, sai colleagues dinta su shidda duk sun xo yi mata sannu da xuwa da gaida Heedayah, drinks da ruwa ne da snacks iri iri a gabansu sannan ga lafiyayyen jollof da isasshen kaza sai coslow a gefe, Mumy dai na xaune parlon ita ma sai kirkiran murmushi take, lkci lkci take jefa nata hirar a hiran da suke, Heedayah na xaune kasa kusa da Mami duk tana kallonsu hannunta rike da roban Fanta, daya hannunta kuma cup cake, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da daya dayan handbag dinta da xa a iya saka karamin jariri a ciki, ta sha yafin mayafinta, ko takalmin kafarta bata cire ba ta shigo parlon, biye da ita a baya Hajiya Zuwaira ce matar Baffan Junaid da kawarta sai kanwarta Maimuna, Mami na ganin kaka tayi murmushi ta mike tace "Sannun ku da isowa kaka" A dakile kaka tace "Ehe" Heedayah sai kallon warce taji an kira da kaka take kamar idanuwanta xa su yi magana, sauran matan parlon duk suka shiga yi ma Kaka sannu da xuwa ciki har da Mumy, duk da "Ehe" kaka ta amsa su tayi wucewarta dakinta bayan ta saci kallon Heedayah da ta bi ta da kallo, Mami suka gaisa da su Hajiya Zuwaira da fara'a tana masu sannu da xuwa, kasancewar parlon is occupied tace "Bari mu je can parlon kawai" Sai da ta sanar ma bakinta gaba daya cewar tana xuwa sannan ta kai Hajiya Zuwaira da kawarta da kanwarta parlonta, mikewa Heedayah tayi da sauri ta bi bayanta, Mumy ta bi ta da wani kallo ta gefen ido, Mami ta ciro ma bak'in nata ruwa da lemo a fridge ta ajiye masu tace "Tunda ku na gida ne bari in sallami bakin parlor, abokan aikina ne da matan yayan Barrister, Ina xuwa yanxun Hajiya" Hajiya Zulaiha tace "Ba damuwa Rahinah, mu kam na gida ne" Mami ta fita Heedayah ta bi bayanta da sauri duk da kiranta da Hajiya Zuwaira ke yi, Mami ta kalleta tace "C'mon je ana kiran ki my frnd" a hankali ta juya ta koma cikin parlon ta nufi gun Hajiya Zuwaira, Mami tayi wucewarta... Mami na dawowa main parlor Hajiya Hauwa tace "Kinga ki shiga ki gaida Kaka tana iya cewa ai kin ganta kin shareta, kinsan halin abar tamu...." Dariya Mami tayi tace "Ae kuwa" Mumy tace "Ae haka ma kawai xata ce" Mami tace "Bari in je in dawo" daga haka ta nufi hanyar dakin kaka, dakin masu aiki ta fara shiga, tana kallon sabuwar mai aikin me suna Talatu tace "Don Allah ki debi abinci da su samosa da cake ki kai can parlona akwai baki guda uku" Talatu ta mike da sauri tace "Toh Hajiya" Mami ta juya ta fita ta wuce dakin kaka, kaka na share windanta da tsintsiya bayan ta cire duk labulayen dakin da ma xanin gado Mami ta shigo da sallama, Da fara'a tace "Sannu da isowa kaka, fatan mun same ku lafiya" Kaka ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Ita Deedayar bata da labarin ni na haifi Amadu da ya biya kudin gyaran idon nata ne da har yanxu bata shigo ta gaisheni ba? Kinga Amadu fa bai ta6a sanin yarinyar nan ba wllh, bbu dangin iya balle na baba, to kuma ya ina mahaifiyarsa baxata xo ta gaisheni ba sbda idonta ya budu, to ni da nasan haka ne xai faru da nace ma Amadu ba da yawuna ba idan aka gyara mata idon, ace tun dawowar ku ba ki xaunar da ita kin sanar mata wacece ni da abinda ya kamata tayi idan ta gan ni ba, kin ga rashin gaskiyar jama'ah ko? To ni dai ba ruwana, ai ba wani ya haifar min Amadun ba, kwanana uku ina nakudar sa wllh" Mami da ke ta kallon kaka tace "Toh kiyi hakuri, kuma Heedayah har yanxu ba wai ta gama sakin jikinta da mutane bane, Kar ki manta kaka tun da aka haifeta makauniya ce ita, Kinga da girmanta ta fara ganin duk wani halitta, to banda ynxu da ta fara sakewa ai da ko mutum ta gani ta dingi ihu kenan tana tsoro" Kaka ta daga hannu tace "Toh ni ina ruwana, ni dai ba ni ce na haifi wanda ya tsintota yyi silar gyaran idonta ba, Taimakonta Allah Taimakonta Amadu a duniyar nan, don haka ai ban cancanci raini wajenta ba, baki ga kallon rainin hankalin da naga tana min ba, ni a gaskiya da na sani da an barta a makancen ma kawai tayi ta ma mutane ladabi a hakan" Mami bata kuma ce mata komai ba ta juya ta fita don ranta ya gama baci, Sai bayan da ta fita kaka tace "Wa ya sani ma ko 'yar ta ce ta makala ma Amadu don kawai ya aureta, mutane dai bbu gaskiya" Mami na fitowa ta wuce parlonta, Tayi ma su Hajiya Zuwaira sannu sannan tace "Heedayah taso mu je" Mikewa Heedayah tayi ta bi bayanta suka fita, Mami ta wuce da ita dakin kaka suna isa kofar ta juyo tana kallonta tace "Idan mun shiga ki xauna a kasa ki gaisheta, ita ce kaka" Heedayah ta gyada mata kai sannan Mami ta bude kofar suka shiga dakin, a bakin kofa Heedayah ta xauna tace "Ina wuni" Kaka dake share bangon dakinta ta juyo ta kalleta ta ajiye tsintsiyar tace "Toh ki gode ma Allah ki gode ma d'a na Amadu, kuma ni nan nice kaka ni na haifi Amadun da yyi silar gyaran idonki, ko iyayenki na da rai yau basu da iko a kanki kamar yanda Amadu ke da iko a kanki amma ya xa ayi in shigo kina xaune rike da goran panta da kenk ki kasa ce min komai kin ji kowa na min sannu da xuwa kaka" Heedayah dai sai kallon kaka take, duk Inda ta bi da hannu sai ta kalla kai kace TV ta samu, Kaka ta kalli Mami dake jira ta fitar da Heedayah daga dakin tace "Kin gani ko Rakiya, hararata fa take" Mami tace "Wani harara kuma kaka, ance maki yarinyar har yanxu bata gama sabawa da komai ba, yaushe ma ta fara ganin ki idan ba yanxu ba, sai fa a hankali xata saki jiki da kowa ta dawo kamar ko wani mutum, ynxu haka da xa ki kawo mata mage ko tsuntsu bata san su ba bata ta6a ganinsu ba, sae dai sunansa, to kinga kuwa dole ayi ma mutum uxuri, ranan da idonta ya bude tsoron kowa ta dinga yi, kuna hada ido xata fasa ihu, sbda duk rayuwarta a duhu yake banda ynxu da Allah ya yaye mata" Kaka tace "Haka abun yake?" Mami ta daga Heedayah dake ta xaune tana kallon kaka tace "Sai hakuri kaka, ni xan tafi in ji da mutane" Daga haka ta fita da Heedayah dake waigo kaka... Fitowa kaka tayi tana kallon mutan parlon ganin Mumy tace "Xo Maryam" Mumy ta mike ganin kaka ta nufi nata bangaren ta bi bayanta har suka shige parlon Mumy, Kaka ta xauna saman kujera ta fashe da kuka tace "Rakiya ce ta shigo ta min wankin babban bargo bbu abinda ta mance bata gaya min ba, a takaice dai a baibai kirana tayi da fitinanniya, ni dai ina tsaye bance mata uffan ba ta ja hannun makauniyar da Amadu ya kashe kudi ya warkar suka fita" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Mumy tace "Ikon Allah, to ke me kika yi xata maki haka daga dawowarki" kaka tace "Wllh Maryam daga nace mata Deedayah lafiya bata shigo ta gaisheni ba naga kamar ma hararata take da na shigo ko bata gane ni bane ta min irin wnn kallon, Kar ki d'a d'a kar ki raga, Rakiya ta hau ni da bala'i wai ni bana yi ma mutane uxuri, ai Deedayah a duhu take ynxu Allah ya fito da ita Amadu ya fito da ita haske, Kuma ai dole ta ji tsorona tunda ita ma ta ji tsoronta da suke asibiti, to idan Rakiya na da hankali da tunani sai ta hada kanta da ni? Ni fa na haifi Wanda yayi silar warkewar Deedayan" Mumy ta hade rai tace "Gaskiya wnn raini ta maki, bata kyauta ba, gani take ta fi kowa Iko da yarinyar a gidan nan daxu fa daga Barrister ya kawota parlona na fita kitchen hada mata shayi matar nan ta shigo ta dauke ta" kaka tace "To kuwa ta ci kanta, Kuma sai na sa an karbe Deedayan hannunta in ga ta tsiya, idan ma Amadu baxai bani ita ba ke ya baki ki rike, abinda ma xai faru kenan wllh wllh, a ina take da iko da yarinya bayan ita ma makalewa tayi aka aurota dalilin yarinyar, da ba don yarinyar ba mu muka san wata Rakiya" Mumy tace "Ae shine, ni wllh a bani ita dama lkcn can shaidan ne ya shiga xuciyata ya hanani amsar ta amma wllh tllh ynxu xuciyata daya xan amsheta in riketa kmr yanda xan rike d'an cikina, abinda yarinyar har ta fara sabawa da ni da suka dawo har ta kusa awa biyu a parlona" Kaka tace "Toh kin ga dai, bari Amadun ya dawo shi ma gantalalle, xan ji ko maganan Rakiya xai dauka ko tawa" Mumy tace "Atoh dai" mikewa kaka tayi ta fita parlon, Mumy tayi wani murmushi ta xauna tana kara naxarin maganganun Kaka. Kafin Magrib duk bakin gidan suka watse har ma da makota da suka shigo duk da basu wani san Mami ba sai Mumy, suka yi mata sannu da xuwa suna ma Heedayah barka suka fita, Mami da kanta ta taimaka ma Talatu gyaran gidan don kai kace wani karamin walima aka yi a gidan, Mumy kuwa ta shige bangarenta da yaranta ta kulle kofa don ma kar su dauke ko da cup, Duk inda Mami tayi Heedayah na makale da ita, Mami har ta gaji da ce mata taje ta xauna ta kyaleta, Mami na kitchen suna gyaran kitchen din aka yi Magrib, sai da Mami ta tabbatar ko ina ya dawo fess ta fito parlor tare da Heedayah ta bar talatu ta karasa wanke wanken, Kaka ce ta fito dakinta, Mami tace "Sannu kaka, abincin ya ishe ku ai koh?" Can ciki kaka ta amsa tace "Ya Isa..." Daga haka ta nufi bangaren Mumy tana rike da wayarta tana cewa "Ina Maryam ta kira min Junaidu shiru ni ban gansa ba, ko a indiyar suka baro sa" Mami dai bata ce mata komai ba har ta shiga bangaren Mumy, Mami ta wuce nata bangaren da Heedayah. Bayan isha Abba na parlonsa tare da Shuraim sai su Rabi'ah da Khadijah, Mami ta shigo ciki da sallama holding Heedayah's hand, Gun Abba Heedayah ta nufa ta xauna tace

Please Login or Register in order to submit comment