Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sudais ya mata murmushi yace "Good girl...." ya kalli Abba yace "Allah ya bayyana iyayenta" Abba yace "Ameen My son" jin taku a bayansu Sudais ya juya, Shuraim ne ke tahowa yana tafiyar kamar bai son yi, wani kallo Abba yyi masa ya kalli Shuraim yace "Xan wuce gida ynxu, anjima ka taho can gidan ka sameni" Sudais yace "In sha Allah...." Daga haka Abba ya bar wajen xuwa gun motarsa tare da Heedayah, Sudais na kallon Shuraim da ya bi Abbansa da ido yace "Kai ma baka bada goyon bayan taimakon yarinyar da Abba ke son yi ba kenan, coz naga kallon da ya maka" Shuraim ya bude hannu yace "But.... She's blind, ta ina xa a fara kula da ita, is it even possible...." Sake baki Sudais yyi yana kallonsa a bit shock, can ya juya da sauri ya kalli parking space yaga Abba is helping her Into the car, ya kara kallon Shuraim yace "Blind? How is that?? Who told you that, ban gane ba" Shuraim ya shafa kansa yace "Yes makauniya ce..." Yana fadin haka ya juya ya koma ciki ya bar Sudais a wajen baki bude, Sudais ya kara satan kallon motar Abba har ya fita compound din.... A hankali Abba ke driving yana yi yana waigen Heedayah dake shan yoghurt da ya siya mata, muryar ta ya ji tace "Abba gida xa mu je ynxu wajen Ammina?" Ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yace "In sha Allah" wani babban eatery ya shiga yyi parking yana kallon agogon wrist dinsa da ke nuna karfe sha biyu saura, wayarsa ya dauka yyi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace "Hope you aren't going to keep me waiting Barrister" bin motar da ya shigo eatery din a dai dai lkcn yyi da kallo sannan ya katse wayar, Heedayah tace "Abba mun kai gida?" Ya shafa kanta yace "A'a, I want to see a frnd now, xa ki jirani har in dawo koh?" Ta gyada masa kai a hankali, kamo hannunta yyi yana murmushi ganin she looks sad and insecure, kamar dai tafiya xai yi ya barta din nan, mika mata wayarsa yyi yace "Ki rike min wayata har in dawo ynxu, kin ji?" Ta kara gyada masa kai, ya bude motar ya sauka sannan ya rufe ya nufi entrance din eatery din, Table din dake dauke da wata mata that is in her early fifty ya nufa, kana ganinta kaga well educated bafillatana cikin shiga ta kamala, ya ja kujera ya xauna yace "Good morning Barrister" Ta ajiye wayar hannunta da take operating tana kallonsa ta cikin siririn glass din idonta tace "Morning, ya family, ya weekend?" ya gyada kai yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Hope ba aiki xaka hadani da shi ba kace xaka yi tafiya, coz nima tafiyan xanyi gobe in sha Allah" yayi 'yar dariya yace "Not at all, how are the children?" Tace "They are all alhmdllh, ya su Rabi'ah?" yace "Lfya lau" tace "Toh Maa sha Allah" shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds ya kalleta yace "Ba aiki xan baki ba, na dai xo maki da magana mai muhimmanci ne Hajiya Rahinah..." kallonsa tayi ita ma tace "Ohk Am all ears in sha Allah barrister, Allah kuma yasa dai lafiya" yace "Sai alkhairi, Hajiya Rahinah na gayyatoki nan ne.... To ask for ur hand in marriage" Da wani irin mamaki take kallonsa wanda hakan bai bata damar iya ce masa komai ba, yyi kasa da murya yace "Yes nasan xa ki yi mamaki but ba abun mamaki bane, I want to marry you..." Ta yi wani yake tace "Haba Barrister, do you even know what u are saying, ni ynxu auren me xan kuma yi? Me nake nema a rayuwa...." Ya katse ta yace "Aure shine rufin asirinki let me tell you idan baki sani ba, idan kika yi aure kimarki da darajar ki xai fi haka a gun jama'ah, I have known you for more than 15 years now tun mijin ki na da rai...." Bude handbag dinta tayi ta ciro tissue don nan da nan har hawaye ya kawo idonta, ya girgixa kai yace "I don't mean to hurt you ko in fama maki ciwon xuciyar ki Rahinah, kar ki manta tun ba yanxu ba na sha baki shawaran kiyi aure sai ki ce min sai kinyi shawara, to yanxu na yanke shawarar auren ki for 3 reasons, which I will let you know ko ba yanxu ba" tace "I am sorry Ahmad bana tunanin xan yi aure har karshen rayuwata, rabuwan tashin hankali nayi da mijina ba wai normal rabuwa, bana da ra'ayin aure har abada" ya katse ta ya d'an buga table din gabansu yace "Stop this nonsense Rahinah..." A d'an fusace tace "In koma gida ince ma yarana xan yi aure? Me ye nake nema a duniya a yanxu? Me yarana suka rage ni da shi da xai sa inji ina sha'awar yin aure? Plss come off this barrister" Ya lumshe ido ya bude yace "Noo Rahinah, ba don kin rasa komai xaki yi aure ba sai don auren shine suturar ya mace...." Tana goge hawayen idonta tace "Idan ma sbda tafiye tafiyen da nake yi ne ko sbda Aikina ni naji xan ajiye in xauna gidana dama Junaid ya fi son haka, tun ba yau ba yake son in daina aikina coz ban rasa komai daga garesu ba, ni kuma xaman kadaici ne dama bana so" Kallonta kawai yake, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "I'm sorry I am making you cry this much, I'm sorry Rahinah" tayi murmushin karfin hali tace "It's okay...." A hankali yace "Xa mu ci gaba da magana amma ba ynxu ba, it's almost time for zuhur, but...." Jin yyi shiru ta kallesa tace "But?" Ya sakar mata murmushi yace "Ban hakura ba, anyway that aside xan baki yarinya ki tafi da ita, for now marainiya ce bata da kowa...." Da mamaki take kallonsa tace "Ban gane ba, a ina ka samo ta..." Briefly ya 6ata labarin Heedayah, wanda hakan yasa jikinta yyi sanyi tace "Allah sarki, Allah ya bayyana iyayenta, I will go with her in sha Allah" yace "Yes I know u will Rahinah, sai dai I didn't made mention of her blindness to you, she's blind" xaro ido tayi tace "Blind??" A hankali ya gyada mata kai, tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" yace "Tana mota ita kadai, mu tafi ki ganta" a tare suka fita eatery din, sai da suka kusa motarsa a hankali tace "Matar ka tace baxata riketa ba kenan?" Ya juya ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Ehh" Ta girgixa kai tace "Toh Allah ya kyauta" yace "Ameen, amma a gidana Heedayah xata xauna, she will stay with u just for few days let me settle down things" Bude mota yyi Heedayah ta juya direction din da sauri fuskarta duk hawaye tace "Abba" ya kamo hannunta yace "Kuka kike yi daughter" cikin rawar murya tace "Naga baka dawo ba" ya share mata ido yace "I'm back dear, xaki bi Maminki gida yanxu kin ji?" Tace "Abba ina xaka je?" Yace "Xan je in siyo maki sabbin kaya ko baki so" tayi shiru bata ce komai ba, Hajiya Rahinah dake ta kallon Heedayah da tausayi tace "Ba dadewa xai yi ba baby, mu je gida kafin ya kawo maki kayan" daga haka ta sauketa a motar, ya kalleta yana murmushi yace "Thanks Barrister, sai na xo anjima" ta gyada masa kai ta nufi motarta da Heedayah, sai da ya ga fitansu sannan ya ja motarsa ya bar Haraban eatery din shi ma. Hajiya Rahinah na parking a parking space ta bude motar ta fito, wata yarinya da baxata haura sha hudu ba ta iso gun motar tace "Mami sannu da dawowa" Tana mika mata handbag dinta tace "Thanks dear, har kin gama assignment din?" Tace "Ehh na gama" Mami ta xaga xuwa side din Heedayah tace "Junaid ya xo kuwa?" Yarinyar ta girgixa kai tace "A'a.." bude motar tayi ta sakko da Heedayah, xaro ido yarinyar nata tayi tace "Mami who is she?" Mami tace "Bakuwa" daga haka ta rufe motar tana rike da hannun Heedayah ta nufi entrance din shiga cikin gidan 'yar ta Farida na biye da ita a baya...



07087865788



Hajiya Rahinah na xaune parlonta watching a movie, almost absentminded, lkci lkci take kallon Heedayah da ke xaune kasan lallausan carpet dake tsakar parlon, Short bread ne hannunta tana ci a hankali, irin kallon da take ma kofar kitchen sai kace tana ganin kofar ne da idanuwanta, Hajiya Rahinah ta sauke ajiyar xuciya for the countless time ta girgixa kai, ba karamin tausayin Heedayah take ba har ranta, text ne ya shigo wayarta ta dauka sanin baxai wuce Barrister ba, dai dai nan kuma aka yi knocking kofar parlon, Farida dake xaune dining tana shan cornflakes ta mike ta nufi kofar, bude kofar tayi wani matashi dake tsaye bakin kofar yana kallonta yace "Baki je islamiyya ba?" Ta langwabar da kai tace "Mami tace I should stay behind xata fita ynxu" Xai yi magana ganin Mahaifiyarsa xaune parlon ya shiga ciki da sallama, Farida ta rufe kofar ta koma dining, xaunawa yyi kujeran dake kusa da na mum din tasa yace "Ina yini Mami" tana danna wayarta tace "Lfya lau, jiya baka xo ba Why?" Ya shafa kansa a hankali yace "Mami Uncle ne ya bani aiki, amma kin manta ne nace maki baxan dawo ba" Tace "Ohk, ka kai ma Salma sakonta kuwa" yace "Eh daga can nake, har xan kawo maki Fadil wai xai biyo ni na fasa, kar ya xo yyi ta mana kuka" Tace "Gobe ma Monday akwai aiki ai" Yana kallon Farida yace "Mami wai ke kika ce kar ta tafi islamiyya?" Da sauri Junaid ya dauke kafarsa xai mike jin abu na ta6a sa, bai kai ga cewa komai ba ya ga Heedayah rakube jikin kujeran da yake xaune, Kuri tayi ma kafarsa da ido, ya mike ya dinga kallonta, Mami tayi dariya tace "Kai dai ka fiye tsoro kamar mace" Yace "Mami wacece wnn kuma?" Mami tace "Bakuwa nayi daxu" hade fuska yyi ya canxa kujera ya xauna, Mami ta mike tana kallon Farida tace "Ki dawo nan parlor ki xauna, yanxu xan fita, you make sure baki bar ta ita kadai ba, I will be back soon, kasuwa xan je" Farida ta mike ta dawo parlon, Mami ta nufi Heedayah ta duka tana kallonta ta shafa kanta tace "Kina son wani abu dear?" Gyada kai tayi tace "Xan sha ruwa" Mami tace "Farida ki kawo mata ruwa" Farida ta tafi fridge dauko ruwa, Mami ta kalli Junaid tace "Sai na dawo, I am not staying long" ya mike yace "Ni ma ai wucewa xan yi Mami" tace "Aa ka jira ni, I said I am not staying long" daga haka ta nufi kofa, da kallo ya bi ta har ta fita, sannan ya koma ya xauna yana kallon Farida yace "Who is she? I mean the girl" Farida ta bude hannu tace "Mami came back with her earlier this afternoon" Ya buda ido sosai yace "From where?" Farida tace "I don't know" girgixa kai yyi ya kara satan kallon Heedayah, direction dinsa take kallo, ya d'an hade rai calmly yace "Kin san ni ne kike kallona?" Laluben kasa ta shiga yi tana neman murfin bottle water cikin sanyin muryarta tace "Ni ba kallon ka nake ba" yace "Hoto kike daukata da idon ki idan ba kallona kike ba kenan" Ta d'an turo baki bata ce masa komai ba tana ci gaba da lalube lalubenta, Farida ta koma kusa da shi da sauri ta kai bakinta kunnensa cikin rada tace "Yaya she is blind fa!!!" irin yanda ya yo waje da ido yana kara kallon Heedayah yasa Farida tayi dariya bata shirya ba, ta dinga dariya har da kyakyatawa da saukowa saman kujera, Shi kam kallon Heedayah kawai yake da mamaki ya ma kasa cewa komai, bai ankara ba sai ganin hawaye na sauka fararen idanuwanta yyi, Bai san lkcn da ya mike ba, Farida ma ta hadiye dariyar da take tana kallonta, ya nufeta ya duka kusa da ita yace "Me yasa kike kuka??" Shessheka ta fara yi tace "Xan tafi gun Abba" Farida ta dawo kusa da ita da sauri tace "Yanxu fa Mami xata dawo" Junaid ya kai mata rankwashi a kai yace "She thought u are laughing at her... What's making u laugh that loud at the first place" Farida tace "Kiyi hakuri, ba dake nayi dariya ba wllh" Ita dai Heedayah sai juya biscuit din hannunta take hawaye na xuba idonta, Junaid yace "Kin ji ta baki hakuri, kiyi hakuri kin ji" Shiru tayi masu, ya dafa goshinta yana goge mata hawayen da hannunsa yace "Kin hakura?" gyada masa kai kawai tayi, nan kuma ta daina hawayen, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna so relieved ganin ta daina kukan, shi dai fa har sannan ya kasa yrda bata gani don gashi sai kallonsu take tana kifta fararen idanuwan, Farida ta rufe bottle water din ta mike ta koma kan kujera ita ma, Junaid ya dau wayarsa ya shiga gun msg yyi typing kamar haka, "Da gaske bata gani? Don't joke with me" mika ma Farida wayar yyi, Farida na karantawa ta kallesa tayi masa alamar rantsuwa cewar Heedayah bata gani, kara kallon Heedayah yyi da shock, can ya mike ya wuce sama yana kara waigo ta. Farida ta canxa tasha ta maida hankalinta kan movie din da ake yi, bayan kusan awa daya taji muryar Junaid ya sakko kasa yace "Why don't you tell her to lie down Farida?" Farida ta juya da sauri tana kallon Heedayah da ta kwantar da kanta saman kujera tana bacci daga xaunen da take, Farida ta mike tace "Ban sani ba" nufenta tayi ta ta6a ta tace "Ki tashi in raka ki daki" Heedayah ta bude ido da sauri tace "Aa" Farida tace "To hau kan kujera" mikewa tayi ta fara laluben kujeran, shi dai Junaid kallonta kawai yake, Farida ta sa ta kwanta kan kujeran sannan ta koma ta xauna. Shidda da yan Mintuna Mami ta shigo gidan da ledoji manya manya, Farida dake parlon har sannan ta mike tana mata sannu da xuwa ta amshi ledojin, Mami da hankalin ta na kan Heedayah tace "Me yasa kika bari tayi bacci ta yamman nan?" Farida tace "Ina son in tasheta daxu yaya yace in bar ta" Mami tace "Ina yayan?" Kafin Farida tace komai sai gashi nan sakkowa, Mami ta nufi Heedayah ta dafa kanta tace "Dear" bude ido tayi da sauri, Mami tace "Yamma yayi tashi kar ki yi sake bacci" Heedayah tace "Abbana fa?" Mami tace "Ga kaya nan Abban ki yace a kawo maki..." Heedayah ta katse ta tace "A'a ina son in je wajensa" Mami tayi murmushi tace "To yana jiran ki a waje" kallon Junaid Mami tayi tace "Take her outside, xaka ga mota a waje, ka kai ta motar" shiru yyi yana kallon mum din tasa, ganin ko kallonsa bata yi ba sai bude ledojin da Farida ta ajiye take, ya karaso cikin parlon yace "But Mami I thought she's blind how will I take her outside" Mami ta hade rai tace "Kama hannunta xaka yi ku tafi, ko in kai ta da kai na?" Ya girgixa kai yace "Aa" ya nufi gun Heedayah, Farida sai dariya take kasa kasa, ya kamo hannun ta jin haka ta sakko daga saman kujeran, kamar me counting steps dinsa ya nufi kofar fita yana rike da hannunta, Farida ta bi su da kallo tana danne dariyar ta, sai da suka fita parlon, Heedayah dake ta bin sa tace "Ha'an da sauri kake tafiya xan je in fadi" kallonta yyi sannan yace "To ba sai ki fadi ba" Bata ce masa komai ba har suka fita gate, ya nufi motar da ya gani a bakin gate din, Bude motar aka yi barrister ya fito, ganinsa Junaid ya yi kasa da kai ya gaishesa da ladabi, Abba ya amsa da fara'a yace "How are you doing Junaid?" Yace "I'm fine sir" Abba yace "Ashe ka dawo, kuna hutu ne?" Junaid yace "Ehh Abba mun yi hutu" Abba yace "To maa Sha Allah, Allah ya taimaka son" Junaid yace "Ameen nagode" Heedayah sai murmushi take jin muryar Abba, ta fara lalube lalube xata ta6a sa, Murmushi yyi ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace "How are you my dear?" Ta fada jikinsa a hankai tace "I am fine Abba, are you taking me with you now??" ta gefen ido Junaid ya dinga kallonta, nan kuwa he is trying to vividly recall weda he said anything bad daxu da turanci da yyi magana da Farida.... Abba yace "No, xaki tsaya tare da Mami kinga ni xan tafi aiki ne" tayi shiru bata ce komai ba, amma gaba daya mood dinta har ya canxa, yace "Ga kaya Mami ta siya maki da yawa sai ki ce mata thank you idan kun koma ciki" a hankali tace "Ohk" yayi patting kanta yace "Good girl" cikin sanyin murya tace "Abba yaushe xan koma gun Ammina da Abbuna?" Tana magana har hawaye ya kawo idonta, Shiru yyi yana kallonta, can yace "Soon daughter, in sha Allah soon xa ki koma wajensu" mikewa yyi yana kallon Junaid yace "Ku koma ciki Junaid" Junaid ya kama hannunta yace "Toh Abba Allah ya kiyaye hanya" Abba yace "Ameen" Sai da suka shiga gate sannan Junaid ya kalleta yace "Ina Ammin taki da Abban ki???" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Baki ji na ne?" A takaice tace masa "Ehh" tsayawa yyi da mamaki yana kallonta, can ya saketa ya koma gefe ya tsaya yace "To ai sai ki kai kanki ciki"


⚡ _Heedayah_ ⚡





_By Khaleesat Haiydar_✍🏻




Da asuba bayan an idar da sllh a masallaci da kusan minti sha biyar Shuraim ya mike ganin Abbansa xai fita masallacin don dama shi yake jira, sai da suka fita masallacin ya isa gun Abban nasa, ya d'an risina yace "Barka da asuba Abba" Abba ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Yauwa...." Shuraim na biye da shi yace "Abba dama ina son baka hakuri ne kan abubuwan dake faruwa...." Abba ya katse sa yace "A'a kaje dai ka ba babarka hakuri, ita ta fi daukan abun da xafi, sannan kuma dama a bayanta kake as always" Ya girgixa kai yace "A'a Abba, ba wai ina bayanta bane, just that muna tsoron abinda xai je ya dawo ne a kan lamarin...." Abba yyi murmushi yace "Ehh gaskiya ne Ali, barin ma da ya kasance cewar duk abinda yaro ya hango ba lallai babba ya hango ba" Shuraim yace "A'a ba haka bne" Abba yace "No haka ne" Shiru Shuraim yyi yana dai biye da Abban nasa, can yace "Toh Abba tana ina yarinyar ynxu?" Abba ya tsaya ya juya yana kallonsa yace "Do you have any problem with that?" Bai iya yace komai ba, Abba ya watsa masa wani kallo ya ci gaba da tafiyarsa, Har suka shiga gida babu abinda Shuraim ya sake ce masa. Reaction din Abban nasa bai hanasa bin sa har cikin parlonsa ba, Abba ya xauna saman kujera ya dau remote xai powering TV, Shuraim ya xauna kasa daga gefensa, a hankali yace "Kayi hakuri Abba, ni ban ga aibun abinda kayi ba haka ma ban ga aibun abinda Mumy tayi ba, she's right in many ways" kallonsa kawai Mahaifin nasa yake, can ya girgixa kai yace "Baxa ka ta6a yin alkibla ba dama, look... Ur mother like it or not dole gidan nan Heedayah xata xauna har sai naga she's back to her parent, idan ku ka ga Heedayah bata dawo gidan nan ba to iyayenta ne Allah ya bayyanar, amma I mean it, bbu abinda xae hana hakan, kuma tare xata dawo gidan nan da matar da xan aura ta kula da ita, ur mother can do whatever she want bbu wanda ya isa canxa ra'ayina" Shuraim dake kallonsa da wani expression yace "Abba aure?? I'm sorry to say... you want to spoil ur home because of a mere little girl da baka san ma me ya rabata da iyayenta ba, baka san daga inda ta fito ba, think about it plss Abba, this is wrong" Abba yyi wani murmushi yace "It's my home not urs, ko da wasa ai baxa ka gaya ma uwarka irin wannan maganar da kake gaya min ba yanxu, ni kuma ga abokin rainin ka, check out pls my frnd" Mikewa Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Kayi hakuri" daga haka ya fice daga parlon, lkci daya ya hade rai bayan ya fita ya nufi dakinsa, who the hell is this forsaken girl that's trying to cause confusion in their home.... Muryar Mumy yaji tace "Ya aka yi Shuraim? What's wrong?" Tsayawa yyi ya juyo bbu walwala yace "Ina kwana Mumy" tace "Lafiya lau, ya naga ranka a bace haka?" Yyi kasa da kai yace "Nothing mum, xan shirya ne yanxu" daga haka ya juya ya shige dakinsa, sarai tasan daga parlon Abbansa ya fito, ta d'an yi jim kamar me naxari sannan tayi murmushi ta juya ta nufi dakinta a ranta tace Idan barrister ya san wata bai san wata ba ai.... Karfe sha biyu saura na safiyar ranan barrister ya isa gidan Yayansa Dr Umar, yana shiga main parlor bangaren Mahaifiyarsu ya nufa, ya bude kofar parlon tare da sallama, a guje kaka ke kokarin boye bowl din gabanta tana cewa "Naga fitina waye kuma wannan" d'an murmushi yyi ya karasa cikin parlon, tace "Au ashe Amadu ne, wllh na xata yaran nan ne masu halayyar bera, to idan na ajiye d'an nama na da cin cin sai su bi dare su yashe...." Abba yace "Ina yini Baaba?" Kaka tace "Lfya lau Amadu, ya aikin" yace "Alhmdllh, ke daya ce gidan kenan" Da sauri tace "To da fa?? Ai Kullum a haka suke bari na, kar fa kayi xaton basu gidan, duk suna nan wllh, dama wannan yaro Aliyu ne me shigo min, shi ma kuma na koresa gaskiya, don raini ya shiga tsakanin mu" Abba yace "Daga gun aiki nake nace bari in xo mu gaisa" Kaka tace "To ae ka kyauta, Allah yyi maka albarka, Wai ya maganar da kayi ranan na cewa xaka kara aure ne naji shiru" yace "Ehh dama xan gaya maki maganan na nan in sha Allah..." Kaka na washe baki tace "Toh Alhmdllh, yar ina ce?" Yace "Nan kaduna" kaka tace "Abu me sauki, to ni dai Allah ya sa ta kirki ce, don Maryam ta gasa mana Aya a hannu gaskiya, to ta amince xata rike yar makauniyar??" Abba yace "Ehh ba matsala" kaka tace "Atoh ita da ke tsoron Allah kenan, Maryam ae shaidaniya ce sanye da kaya irin na mutane" Abba ya mike yace "Bari in je kaka sai na shigo ko gobe" Kaka tace "Toh, ni dai haka nn nake sae bin yara nake ina rokon hamsin, dari, suna xagina suna ba ni" Abba ya juya yana kallonta da sauri, ta tsuke fuska tace "A'a kai ba ubana bne da xaka min kallon tuhuma Amadu, idan gantalalliyar dubu ashirin din ka ce ta shekaranjiya to ta kare tun jiya wllh" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya bude yace "Sae anjima" Daga haka ya fita. Hajiya Rahinah ce xaune tare da Barrister kan kujerun dake karkashin inuwar bishiyar tsakar gidanta, barrister ya ajiye wayar hannunsa yace "Sae kuma kika yi shiru" Sae a sannan ta kallesa tace "Ehh shirun naga xai fi, barrister in dae har sbda wannan yarinyar kke son aurena, ina nufin indan sbda in riketa ne to kar ka damu ni me iya rike little girl din ne har bayyanar iyayenta idan Allah ya yrda, ina hada ka da Allah ka rabani da xancen auren ka, bbu aure a tsarin rayuwata ynxu...." Shiru yyi yana kallonta, sannan ya d'an yi murmushi yace "Sae dai fa kiyi hakuri Rahinah, you can't stop me from marrying you, Heedayah

Please Login or Register in order to submit comment