Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma gidana nake son ta xauna ba wani waje daban ba" Mami ta tabe baki sae dai bata ce komai ba, Budewar gate ya sa duk suka juya, Junaid ne ya shigo compound din hannunsa rike da Makullin mota, har ya isa inda suke ya fara gaida Abba sannan ya gaida Maminsa, Abba yace "Kana aiki ne Junaid?" Yace "Ehh ina aiki tare da Uncle dina a hospital dinsa" Abba yace "To that's good ya fi ka xauna, Allah ya taimaka" Yace "Ameen" daga haka ya wuce ciki, Abba ya kalli Mami yace "Ya kusa gama masters din nasa ne?" Mami tace "Ehh months suka rage masa idan Allah ya yrda" Abba yace "Allah ya taimaka" Junaid na shiga parlor ya ga Heedayah ce kadai parlon kwance saman kujera tana bacci, ya dauke idonsa ya wuce sama xuwa bedroom dinsa. Sae kusan la'asar Abba ya bar gidan har sannan kuma bai yi convincing Hajiya Rahinah ba dake kan bakanta na cewa bbu aure a gabanta. Yau dai har sha daya saura na dare Hajiya Maryam na xaune parlor tana jiran ganin lkcn da barrister dake compound yana ta waya xai shigo, yau kwana biyu kenan da ta lura da hakan duk da kasancewar ta mai bacci da wuri yau kam coffee me kauri ta sha tayi xamanta a parlor tana jiran ganin ikon Allah, lkci lkci take tashi ta leka waje ta dawo, lekawar da tayi na karshe ne taga ya gama wayar xai shigo ciki, da sauri ta shige kitchen ta kulle don ma kar ya san idonta biyu, sae da taji ya wuce part dinsa sannan ta fito ta dinga xaga parlor tana jiran ya kwanta sanin bashi da wuyar bacci, a haka Shuraim ya sakko downstairs ya sameta, ganinta da mamaki yace "Mum baki kwanta ba" Tace "Ehh yanxu dai xan je in kwanta na gama kallon wani film ne" Bai ce komai ba ta wuce sama shi kuma ya shiga kitchen, sae da taji Shuraim ya shiga dakinsa ta fito ta nufi part din mai gidan nata, a hankali ta bude kofar parlonsa ganin wuta a kashe ta gane ya kwanta, ta lallaba ta nufi daki tana tafiya a hankali, tana shiga duk da wutan a kashe yake tasan yyi bacci ta tafi inda tasan yana ajiye wayarsa ta dauka ta fita daga dakin, bangarenta ta koma ta bude wayar ta shiga call log dinsa, Number da aka yi saving da Great barrister taga last call dinsa, nan ta duba taga yana yawan kiran number, msg ta shiga tayi scrolling har xuwa farko, hankalin ta ya fara kwanciya ganin kawai text ne da ya shafi aiki, a hankali ta fara gwalo ido bayan tayi nisa ganin salon message din ya fara sauyawa har ta kai karshe, xufa ne ya karyo mata ta ajiye wayar ta rasa tunanin da xata yi, can ta dau wayarta ta kwashe number tas sannan tayi dialing, sae da ya kusa katsewa aka daga, daga daya bangaren Mami tayi sallama, shiru Hajiya Maryam tayi xuciyar ta na bugawa jin muryar mace, kawai ta katse ji tayi kamar ta daura hannu a ka tayi ta ihu, ta xauna gefen gado tana furta innalillahi, kallon wayarta tayi, sae kuma ta shiga call log tayi dialing wani lamba, yana fara ring aka dauka, Ta hadiye abu da kyar tace "Sadiya wllh da gaske Barrister neman aure yake, Ashe da gaske yake wllh, gashi ynxu na bincike wayarsa kaff har na samu lambar warce yake nema da aure, na shiga ukuna Sadiya, da yarinta ta ba a min kishiya ba sai yanxu a kan wata shegiyar yar tsintuwa makauniya...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "In dai Alhaji yyi auren nan ai tawa ta kare, dariya xa ayi min a gari ki bani shawara don Allah kawata, wllh dariya makiyana xa su min" Hajiya Sadiya dake saurarenta baki bude tace "Aure fa kika ce Maryam?? Ke sai ki yrda ki barsa yyi auren? Toh ynxu dai ae sai ki wanke kafarki mu tafi inda kike ikirarin bbu abinda xai kai ki" Hajiya Maryam tace "Ina???" Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace "Wa enda kike raina taimakonsu mana...." A fusace Hajiya Maryam tace "Allah shi kiyaye, tun da can da kuruciyata ban ta6a xuwa ba sai ynxu a kan yar yarinyar da na haifa?? Yar cikina? Ni nan da kike gani na ishi kowa wllh, Kuma muna nan dake auren nan baxae ta6a yiwuwa ba ni nasan me xan yi, ke dai kawai ki xo gobe don Allah, sae da safe" daga haka ta katse wayar, ta kusa awa daya xaune kafin ta iya tashi ta mayar masa da wayarsa ta dawo dakinta, daren ranan bata yi baccin kirki ba, Wai ita barrister xai ma kishiya sbda taki rike makauniya??? Tayi kwafa ta juya tana jiran dai gari ya waye. Mami na xaune tana ma Heedayah gyaran dogon gashinta dake ta kyalli, yau ma dai bata je aikin ba don har lkcn bata samu wanda xai kulan mata da Heedayah ba, Farida kuwa na boko daga safe har 6, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta kai kunne, sallama aka yi mata daga daya bangaren ta amsa, Hajiya Maryam dake xaune dakinta da Hajiya Sadiya da wata kawarsu Hajiya kyauta tace "Don Allah da barrister nake magana" Mami tace "Yes, wacece ke magana?" Hajiya Maryam ta gyara xama tace "Toh Barrister wata yar matsala ce wllh ta taso mana muna neman lawyer, shine wani abokin aikina ya bani lambar ki, yyi assuring dina you can help..." Mami tace "Allah sarki sai dai na dau hutu baxan yi aiki ba cikin satin nan gaba daya" Hajiya Maryam ta gwalo ido tace "Don Allah ki taimaka barrister, ya gaya min irin kirkin ki da taimakon ki, ke kadai xaki iya rufa mana asiri kan lamarin nan, don Allah barrister ki dubi girman Allah ki sauraremu, wllh muna cikin tashin hankali sosai" Mami tace "Kar ki damu malama xan hada ki da wani barrister, he is also good xama ki ji dadin nasa aikin fiye da nawa, I can send you his number now" da sauri Hajiya Sadiya tayi ma Hajiya Maryam alamar tace mata to ta turo... Hajiya Maryam tace "Toh ngd Barrister, Allah ya saka, ina jiran lambar" Mami tace "Kar ki damu, let me send you" daga hka ta katse wayar, cikin few seconds ta tura ma Hajiya Maryam number Barrister Ahmad, Hajiya Maryam da ta ji kmr xuciyarta ya fashe cikin tashin hankali tace "Na shiga uku, kun ga lambar mijina ta turo min dai koh???" Hajiya Sadiya tace "Toh sake kiranta" hannu na rawa ta sake kira, Hajiya Sadiya ta amshe wayar tace "Ki dubi girman Allah Barrister ki bamu lkcn ki ki saurari matsalar mu, an ce mana ke ce maganin kukan mu, wllh ko nawa kika bukata xa mu biyaki domin Allah ki taimake mu..." Da mamaki Mami tace "Wnn barristern da na tura maki numbersa ya ma fini iya aiki, xae saurare ku fiye da ynda ni xan saurare ku" da kyar da kyar suka shawo kan Mami kan ta amshi case dinsu, Mami ta girgixa kai tace "Gaskiya baxan fita gidana ba ynxu, sae dai ko ke ki xo ki sameni" Hajiya Maryam tace "Wnn ae ba matsala bane, bari in taho ynxu ma, Allah ya kara girma da daukaka Barrister, ki turo min address din plss" Mami tace "Ameen, xan tura maki ynxu" daga hka ta katse wayar, ta tura address din nata, Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta mike ta dau mayafi da Makullin mota jikinta har wani 6ari yake tace "Ku mu je" fita duk suka yi suka bar gidan a motarta. Gane gidan Hajiya Rahinah bai masu wahala ba, suka yi parking a waje bayan sun sanar ma Mai gadi Hajiya Rahinah suke nema kuma ta san da xuwansu ya bar su suka shiga cikin gidan. Har entrance din shiga gidan suka nufa suka tsaya, Hajiya Sadiya ta danna bell, Mami da ta saka Heedayah gaba tana mata tambayoyin ynda aka yi har ta fito gida.... exactly labarin da Heedayah ta bada a station ta sake ba Mami, ta kare da cewa sai taji ana tafiya da ita a bicycle kawai sai ya wuce ya bar ta bai kai ta gun Amminta ba kuma, tana fadin haka ta fara hawaye, Mami dake ta naxarin d'an labarin ta gane daga all indication kidnapping yarinyar aka yi sai kuma Allah ya kubutar da ita, mikewa tayi jin an sake danna bell for the third time ta nufi kofa ta bude tana kallonsu Hajiya Maryam, Hajiya Maryam ta kirkiro murmushi tace "Sannu fatan ke ce barristern?" Mami tace "Oh, okay ga kujeru can bari in fito yanxu, ku jirani a can" Hajiya Maryam ta saka kai ta raba ta gefenta ta shiga ciki, tace "A'a xai fi daga cikin dai barrister, tonon asiri ai ba dadi" sauran ma duk suka shige ta gefenta, kallonsu Mami tayi da d'an mamaki, Hajiya Maryam ta isa tsakiyar parlon tana kallon Heedayah da wani expression, sauran kawayenta ma duk suka tsaya kusa da ita suna kallon Heedayar, Kasancewar Mami lawyerr yasa lkci daya ta gane abinda ya kawo matan nn gidanta ba abinda suka ce bane, Hajiya Maryam tace "Toh kinyi tsaye bakin kofa ae sai ki karaso ki ji case din mu koh barrister?" Heedayah dake xaune saman kujera da apple a hannunta ta mike da sauri don in dai ta ta6a jin murya to baya ta6a bacewa a sense of hearing dinta, ko da kuwa an dau lkci sosai sai ta gane muryar duk inda taji, Mami ta karaso parlon tace "Bana bukatar jin case din ku, domin bana hulda da Yan tasha, ku kai case din ku wani wurin, and ku fitar min a gida immediately now...." Hajiya Maryam tayi wani dariyar rainin hankali tace "Koh?? To sai ki fitar da mu ta karfi Mai gida, bari ki ji..... ba barrister ba, ko judge ce ke na xo ne in yankar maki lafiyayyen wani ki fita hanyar mijina Barrister Ahmad, shi ba gantalalle bane irin ki, kin gama xaga duniya kinyi yawon karuwancinki shine xaki wani makale masa ya aure ki sbda baki da tunani ko? To wllh kin yi kadan, mijina ba sa'an auren ki bane, Ashe ke ya kawo wa shegiyar yarinyar nan kika karba kika rike tunda dama kina sonsa da aure, to don kaza kazan ki nace baki isa ba, mijina ni kadai ne shi din, baxan hada shi da karuwa ba yar boko da ke yawon duniya don ma kiji, don haka tun wuri ki san inda dare yyi maki" Tunda ta fara Mami ke kallonta, duk da maganganun sun ma Heedayah girma ba duka xata iya ganewa ba hakan bai hanata dinga kuka ba tana kiran Mami, Mami ta nufi gun wayarta ta dauka cikin few seconds tayi dialing number Abba, yana fara ringing kuwa ya daga ta sa hands free tace "Ahmad kana ji na?" Yace "Yeah ina ji my barrister, ya gidan?" Tace "Alhmdllh, dama nace ne you can come forward with ur pride price to my elders ko gobe, na karbi tayin auren ka idan Allah ya yrda" Yace "Da gaske kike barrister, pls don't joke with me" farin ciki ne sosai tare da words dinsa, Mami tace "I'm not joking barrister, na baka go ahead, we will talk later in sha Allah" daga haka ta katse wayar, Hajiya Maryam da wani xaxxafan xufa ya keto mata ta dinga kallon Mami so speechless, Mami ta isa gabanta ta tsaya tace "xa mu shigo gidan barrister Ahmad tare da wannan yar yarinyar nan da sati daya, sai dai ciwon xuciya ya kashe ki a banxa, sannan wnn yarinyar da kike gani ita xata xamar maki nightmares dinki kafin ni.... Lastly kin ci sa'ar mijinki na da k'ima da daraja a idona sannan ga soyayyar da nake masa, wllh da yau bbu abinda xai hana ke da mahaukatan kawayen ki kwanan cell kuma in ga uban da xai bada bail dinki, amma soyayyar mijin ki baxai bar ni inyi hakan ba..." Tana fadin haka ta ja hannun Heedayah suka fita xuwa gun mai gadi tace "Salisu ka tattaro abokanan ka masu gadi ka fitar min da wasu mashaya da suka shigo min gida, and from henceforth duk wanda ya xo ka fara sanar min kafin ya shigo" da sauri ya fita yin yanda tace.


Start patronizing Heedayah lovely fans.... last free update later at night in sha Allah😍

07087865788.....



⚡ _Heedayah_⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻





Tun da Hajiya Maryam suka dawo gida da kawayenta take kuka kamar ranta xai fita, ji take kamar ta bude ido taga cewar duk mafarki take, ya xa ayi Barrister ya mata kishiya bata mutu ba?? Hajiya kyauta tace "Ke Maryam bari ki ji in gaya maki, idan xaki share hawayen ki ki san nayi ki share, don 6ata lkcn ki kawai kike, wllh wannan kukan baxai fisshe ki ba, wajen nan dai da baki son xuwa dolen ki nan xa aje da ke yau a san nayi, don wnn mata ni dai da kamar wuya mijin ki ya fasa aurenta duk haukan ki kuwa, na farko in dai kyau ne baxa ki nuna mata komai ba, ke diplomar ma da ya kika kare? Ita kuwa lawyer ce fa me xaman kanta, kinga kenan ta kure karatu, ga shi da gani dai kin san ba cikin wahala take ba tana da kudin ta, ke dake buga buga ki raruma gun miji fa?? ni wllh ba karamin kwarjini matar ta min ba ma, da ba ku fito ba dama ni wucewata xan yi kar ta sa a daure mu kamar yanda tace" Hajiya Maryam ta katse ta a fusace tace "Ni fa da ku ke gani nan babu abinda ya isa kai ni gun malami a duniyar nan, ku dai ku bar ni inyi ta kai na kawai idan baxa ku bani shawara ba, ni kadai raina na ishi kowa, wllh karuwar nan baxata shigo min gida a matsayin kishiya ba, muna nan da ku kuma xa ku ce na fada, ita kuma wnn makauniyar dama sai dai ta kara shiga duniya wani ya tsince ta a wani garin amma ba mijina ba...." Tana kai wa nan ta mike ta dau gyalenta tana share idonta, Hajiya Sadiya tayi wani dariya tana kallon kyauta tace "Bar ta, xata dawo ta same mu ne ai" Ficewa Hajiya Maryam tayi daga dakin rike da makullin motar ta..... Direct gidan Dr Umar ta nufa, yau dai ko shiga bangaren matan gidan bata yi ba ta nufi gun kaka, da sallama ta bude kofar parlon kaka dake uwar daka ta fito da sauri tana cewa "huuu Ko waye don Allah ya share kafarsa ga tsumma na ajiye bakin kofa, wllh kazamai ne matan gidan ko sharan kirki basa yi a makeken parlon nan nasu sai a tattako a xo a yasar min a nawa parlon...." Hajiya Maryam ta dinga goge kafarta a tsummar kamar an aikota, kaka tace "Aa Maryam daga ina haka da sassafe kuma" Ta karasa cikin parlon ta xauna kasa cikin sanyin murya tace "Daga gida kaka, ina kwana" Kaka ta xauna tace "Lafiya dai naga idonki a kukkumbure ko Balaraba ce ta rasu??" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ba lafiya ba wllh kaka...." Kaka tace "Ikon Allah me ke faruwa Kuma? Ni dai jiya Amadu ya shigo min da rana wai ya xo gaisheni a nan kuma yake ce min wai aure xai kara har ya samu matar yar kaduna ce, ni dai nace masa ba ruwana, ana xaune lafiya fitina ya shigo ciki, to daga haka ni bai ce min ga abinda ke faruwa a gidansa ba...." Cikin kuka sosai Mumy tace "Abinda ya kawo ni kenan ma kaka, wai aure fa xai kara...." Kaka ta saki salati tana tafe hannu tace "Ohh ni na ga abinda ya isheni ni Rahamar ubangiji, me Amadu ke nema a duniya da xai kara aure ana xaune qlau, ni dai yana gaya min ce mashi nayi ba ruwana, don bn san kan xancen ba...." Mumy ta share idonta tace "Idan ma sbda wnn baiwar Allahn ce ya kawota kawai xan riketa na amince" iyakar wnn furucin da Mumy tayi bakinta, don kuwa ta sha alwashin ko an fasa auren aka kawo mata Heedayah sai ta sake lulawa da ita wani duniyar daban, duniyar ma na kauye, can xata sa aje a wurgar da ita don ma kada mistakenly wani me rufin asiri ya dauketa har ya taimaka mata, a yanxu dai duniya bbu wanda taji tana tsana kamar wnn yar yarinyar, har ta mance rabon ta xubda hawaye ta shiga tashin hankali da xai hanata bacci sai a dalilin Heedayah, Kaka tace "Aa ni ya kawo min ita ma nan kawai xan riketa, kar a ja maki kaffara kina xaman xamanki, dama bbu me min wanke wanke da shara tsigalallun yaran nan duk ba kulasu nake ba ta kaina nake" Mumy tace "Makauniya ce fa kaka" kaka tace "To makafi basa wanke wanke da shara aka ce maki Maryam, ai dai naga ba kuturwa bace, sai in kada mata kumfar in sa mata ruwan dauraya in ajiye mata kwanukan in xaunar da ita ta wanke min su tass" Mumy tace "Aa kaka wahala kawai xata baki, ni din dai xan riketa, ai d'a na kowa ne" Kaka tace "Atoh dai, ki kwantar da hankalin ki kawai, bbu wani xancen kara aure in dai da raina tunda xaki riketa, to idan ba toxarci Amadu ke son mana ba meye kuma karin aure ana xaune kalau, wannan ne kuma bai haifu ba gaskiya don baxan yrda ba" Mumy taji hankalinta ya d'an kwanta, tana share idonta tace "Toh shkkn kaka nagode" Kaka tace "Haba godiyar me kuma, ai yi ma kai ne, yanxu shawarar da xan baki a nan shine ki dau kayan ki kala daya ko biyu ki tafi gidanku, idan ba haka kika yi ba Amadu baxai dawo hankalinsa ba, ki tafi da fitsararrun 'ya yan nan naki ki bar masa gidan ba kowa sae kujerunsa da tv, nan xaki ga ya shiga taitayinsa wllh, kaddai ki gaya ma wnn dunkum din d'an naki kudurin ki don wllh hana ki xai yi ya cuce ki, ki bar masu gidan shi da ubansa kawai" Mumy da ke kallon kaka tana jinjina shawarar ta a ranta, tayi murmushi tace "Gaskiya ne kaka, hakan xan yi in sha Allahu ina komawa kuwa" Kaka tace "Atoh maxa tashi ki tafi tun yanxu ki hada hada kayan, ai mu xamaninmu haka muke yi, idan miji ya musguna maka ka hada kayanka ka bar masa gidan sa, xo ki ga yanda hankalinsa xai tashi kuwa...." Mumy ta mike tace "Toh sai anjima kaka, nagode sosai, Allah ya kara girma, sai mun yi waya" daga haka ta fita, kaka ta bi ta da kallo har ta rufe kofa sannan ta ta6e baki ta juya ta koma cikin dakinta tana cewa "To ai idan Amadu ya fasa auren nan ma ni sai naji dalili wllh, da kaina xan kai sadakin auren, huuu wai ba kunya ba tsoron Allah matar da ke bari na da yunwa me saka min nama tsoka daya ce wannan fa jama'ah, Ehh lallai duniya ya lalace....." Da yammacin ranan Abba ya tafi gidan Barrister Rahinah don sake tabbatar da abinda ta gaya masa a waya da safe, nan ta nuna masa she is serious, ko da wasa bata sanar masa cewar Hajiya Maryam ta xo gidanta ba, yana murmushi yace "Toh nagode Rahinah, in sha Allah gobe xa mu je can gun kawun ki..." Mami tace "Allah ya kai mu...." Basu wani jima ba ta koma cikin gida don tace masa girki take, shi kuma ya wuce. Mumy na komawa gida dama ta hada kayanta ynda Kaka tace mata, ta hada har da na su Khadijah da Rabi'ah ta bar gidan, makarantar su ta fara biyawa ta sanar masu inda xasu sameta idan an tashi sannan ta wuce gidan kanwar Mahaifiyarta dake nan kaduna. Mami ce xaune study area dinta tana kallon files din gabanta, gaba daya mood dinta isn't okay, ta kasa gane ko she is making the right decision marrying barrister, har xuciyarta tana son taimakon Heedayah amma ba irin taimakon da xai kai ta ga aure ba at this stage, ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin ta ina xata fara sanar ma yaranta wannan xance me girma, amma kuma ai idan bata Aure Barrister ba ta 6ar matarsa ta ci bulus kenan, ta shigo har gida ta yi mata cin mutunci sannan ta bar ta haka nan, muryar junaid taji yace "Mami aiki kike?" Ta daga kai da sauri ta kallesa don bata ji shigowansa ba ma, ta mayar da glass din da ta sakko idonta tace "Sure, ka shigo kenan" yace "Nayi sallama naji shiru" ya ja kujera ya xauna yace "Mami this two days naga kamar kina da damuwa, meye matsalar ki gaya min" shiru tayi kuma bata daga kai ta kallesa ba, yace "Talk to me Mami" ta sauke ajiyar xuciya tace "Junaid barrister ne ya xo min da xancen da ya saka ni cikin damuwa kwarai, I don't know I am really confuse junaid...." Yana kallonta sosai yace "Me ya faru Mami?" Ta kuma yin shiru, bayan few seconds taga bbu wani amfanin boye boye kuma, nan ta sanar ma d'an nata intention din Barrister Ahmad a kanta, junaid bai iya ya ce komai ba na kusan second talatin, can dai yyi gathering courage ba tare da ya kalleta ba yace "Toh, idan hankalin ki ya kwanta da hakan Mami, Allah ya sa shine mafi alkhairi a gare mu baki daya" kallonsa kawai take bata ce komai ba, ya mike yace "Na xo daukan system dina ne" daga haka ya wuce sama ta bi sa da ido, dakin Farida ya bude, ya ga Heedayah kwance edge din gadon tana bacci, riga ne da wando jikinta kamar dai 'yar turawa, he wondered if she is neva tired of sleeping, karasawa cikin dakin yyi walking slowly ya isa kusa da gadon yana kallonta, a hankali ya mayar da ita tsakiyar gadon ya gyara mata dogon gashinta dake rufe idonta, jin an bude kofar dakin ya mike tsaye da sauri, kafin Mami tace komai yace "A gefen gadon na sameta...." Mami ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita dakin.... Da daddare Barrister ya tafi gidan Yayansa, bayan sun gaisa da kaka yace "Na je can gida na tarar Maryam ta kwashe yara sun bar gidan Baaba" Kaka tace "Kila ganin gida taje...." Shiru yyi yana kallon mahaifiyar tasa, kaka tace "Toh ina dama xata je idan ba ganin gida ba, ai ta kwan biyu bata je ba, kaga kai kuma kafin ta dawo sai amaryarka tayi kokari ta tare xuwa nan da ranan juma'ah tunda yau talata, wannan makeken bangaren da nake sauka sai ka sa a gyara ma amaryar ayi fenti da komai da komai kawai, ita kuma Maryam ban ce ka kirata ba balle kace xaka mata fada, uwarta taje gani...." shigowar Baffa ya sa Kaka tayi gum, ta sauya xancenta. Ranan juma'ah aka daura auren Barrister Ahmad da Barrister Rahinah, though they did it in a confidential way, bbu wani gayya, duk abubuwan nan dake faruwa Hajiya Maryam na can ta lula xuwa gidan wata childhood frnd dinta a Zaria tare da su Rabi'ah wai kar barrister ya biyota gidan kanwar mamarta, ita a dole sai ta basa wahala, Shuraim kadai take kira don samun update, sai dai me? Shi ma bai san da auren ba sai a ranan juma'ar, shi ma kuma da asuba Abban nasa ya sanar masa a masallaci da suka hadu, he was so shock ya ma kasa cewa Abban nasa komai, haka nan Abba ya wuce ya bar sa wajen a tsaye, ita kanta Hajiya Amina mum din su Sudais ranan ta ji xancen daurin auren daga bakin Baffa da safe, nan tayi ta kiran Hajiya Maryam amma wayarta a kashe, bata fasa kira ba har sai da aka daura wnn aure amma bata

Please Login or Register in order to submit comment