Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

leaving too" Sudais yace "Better...." Daga haka suka fita dakin xuwa hotel din Sudais. Salima na jin alamar sun fita ta bude kofar ta leko ganin ba kowa ta fito dakin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Sudais, ita a rayuwa ma akwai wanda ta tsana kamar shi kuwa, ko gaisuwa baya hada ta da shi dama, cije yatsa tayi ta xauna gefen gado a hankali tace "Anya ma Junaid din nan na da lafiya kuwa, upon everything yesterday he isn't still moved" Da sauri ta mike ganin bbu jakar kayansa ta tafi window tana lekawa taga Inda suka nufa, tricycle taga suka shiga, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Dama Sudais ma na kasar nan ban sani ba??" Can ta gyada kai tayi wani murmushi tace "idan ka san wata baka san wata ba Junaid" Tun da Mami ta tashi yau da asuba take ta fargaba ita kadae don ranan xa a cire ma Heedayah eye pads din idonta, kuma ranan ake sa ran xata fara gani, daren ranan Mami sae da tayi sllh ta roki ubangiji yasa an dace, ya sa karshen wahalan kenan.... Karfe shidda da rabi likitocin suka fita da ita xuwa theatre, Mami dai na xaune bakin theatre din sae addu'a kawai take, ga faduwar gaban da yyi mata yawa, da taji motsi sae ta kalli kofa da sauri amma bbu wanda xata ga ya fito har karfe bakwai da rabi, kukan da ta ji Heedayah ke yi daga ciki ya fi daga mata hankali, tun daga nisa take kallonsa har ya karaso tare da wani likita baindiye walking slowly, likitan ya gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa don da shi aka yi ma Heedayah aiki 3 days back, shi ma dai yyi kasa da kai ya gaisheta, ta amsa tace "Ya hanya" Yace "Alhmdllh, ya kokari" tace "Mun gode Allah" baindiyen yayi tapping dinsa a baya da harshen turanci yace sae sun hadu anjima, daga haka ya juya ya wuce, dai dai fitowar wani likita yana kallon Mami yace "You can go in Madam, a Dr will explain everything to you inside" mikewa Mami tayi amma ta kasa tambayarsa ba ayi nasara bane aka ce ta shigo, kuma ta kasa shiga ciki, likitan yayi wucewarsa, kansa a kasa ya nufi kofar shiga theatre din walking slowly, Mami ta bi sa da kallo har ya shiga ciki, Heedayah na xaune saman gadon ta takure waje daya ta rufe fuskarta da pillon saman gadon tana kuka a hankali, likitoci biyu na tsaye suna jiran shigowar Mami, Daya daga likitan da turanci yace "Her brother?" Ya gyada masa kai sannan ya karasa gadon yana kallonta, likitan yyi murmushi yace "Yes it was successful, but it's a new world to her.... And it will take sometime before she will adapt, like... she will have problem with light, Human, infact everything, because she just left the world of darkness" Dago kanta yyi ta bude jajayen idonta a hankali tana kallonsa suka yi ido hudu, lkci daya ta fasa ihu kamar warce ta ga mugun abu, ya rungumeta, jikinta ya dinga rawa gaba daya a tsorace take, duk wnn abun Mami na tsaye bakin kofa tana kallonsu, lkci daya hawaye ya kawo idonta tana hamdala a xuciyarta ta karaso gadon da sauri tace "Heedayah" cikin rawar murya Heedayah na kara shigewa jikinsa tace "Mami tsoro nake ji, kice a rufe min idona" Likitan yace "She will adapt slowly...." wheel chair ya jawo ya ajiye don a maida ta ward dinta in ji likitan, Shuraim ya dauketa har sannan ta ki yarda ta kara bude idonta, bai daurata kan wheelchair din ba ya nufi kofar theatre din Mami ta bi bayansa, da yake abokinsa likita sai da ya fara nuna masa ward din da suke kafin ya kawo sa theater din direct ward din ya nufa, Mami dai na biye da shi, ya bude kofa ya shiga ya isa kan gadon ya kwantar da ita a hankali, har sannan taki yarda ta bude idon, har runtse idon tayi gam, ya saki curtains din ward din gaba daya, ya kuma kashe wuta haske ya ragu sosai, Mami dai na tsaye tana kallonsa, Wani likita ne ya shigo ward din ganin ynda Shuraim yyi ma dakin yace "Very good" daga haka ya juya ya fita, Mami ta xauna gefen Heedayah ta dagota tace "Daughter" a hankali tace "Mami" Mami tace "Bude idon ki" ta girgixa kai cikin rawar murya tace "Ina jin tsoro" Mami tace "Baki son ki gan ni?" Kuka ta fara yi tace "I am scared" murya can kasa Mami tace "Don't be dear, open it slowly" Shuraim dai na tsaye bakin gadon yana kallonsu, a hankali ta fara kokarin bude idon maimakon ta sauke kan Mami sai ta sauke kan Shuraim dake kallonta suka yi ido hudu, boye fuskarta tayi jikin Mami ta fashe da kuka sosai tace "Mami Noo, meye shi din? I saw something" a sanyaye Mami tace "That's Shuraim" Sake dagowa tayi da sauri ta bude idonta har lkcn kallonta yake shi ma suka kara hada ido, knowing her condition sai ya sakar mata soft sweet smile, ta fi second biyar tana kallonsa ko kiftawa bbu sai kuma ta kara boye fuskarta jikin Mami da sauri, Mami na jin yanda xuciyarta ke bugawa, duk wnn abun bata kalli Mami ba har sannan, Mami ta kwantar da ita a hankali, Heedayah ta rufe fuskarta da pillow, har bayan wani lkci bata dago ba balle ta bude ido, Mami xata dagota Shuraim na kallonta yace "Tayi bacci fa"


Idan Allah ya amince min xan yi night update later, In sha Allah.....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Kwantar da ita Mami tayi ta mike a sanyaye ta tafi kan kujera ta xauna, Shuraim dai na ta tsaye kusa da gadon idonsa kan Heedayah, Mami tace "Kayi breakfast ne?" Xai yi magana aka bude kofar ward din Sudais ya fara shigowa junaid na biye da shi rike da leda, Sudais ya d'an tsaya xae fiddo wayarsa a aljihu ya haska dakin yace "why is it dark here...." Kunna switch din Shuraim yyi ya ja blanket din saman gadon ya rufa Heedayah da shi, da mamaki Sudais ke kallonsa, ya buda ido very amazed yace "You!!!" Sau daya Junaid ya kalle Shuraim ya nufi Maminsa, ganin hka Sudais ya bi bayansa ya ajiye ledan breakfast din hannunsa saman table, nan suka gaida Mami, ta amsa tana tambayarsu night dinsu, Sudais yace "Alhmdllh, ya mai jiki?" Mami tayi murmushi sosai tace "Alhmdllh, she gained her sight, the surgery was successful Alhmdllh" Junaid ya juya da sauri yana kallon Heedayah, he couldn't help it but smile, Sudais wa wara ido yace "Alhamdulillah" a tare suka nufi gadon gun Heedayah, Mami tace "Yanxun tayi baccin, she needs much rest sbda a tsorace take..." Junaid ya kalli Mami da sauri yace "Tsoron me kuma?" Mami tace "Don't forget, she is blind all her life, every image is exactly new to her now, likitan yace sae tayi adapting a hankali" Junaid ya dinga kallon Heedayah cike da tausayinta, can ya bude blanket din a hankali yana kallon fuskarta, Sudais ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, ta gefen ido Shuraim ya dinga kallonsu su biyun, Junaid ya maida mata bargon ganin bacci take peacefully, xagayowa Shuraim yyi yana kallon Mami yace "Xan je in dawo" Mami tace "Ohk" daga haka ya nufi kofa, Sudais ya tabe baki har Shuraim ya fita ward din, Mami na kallon Junaid tace "Ba ku gaisa da shi ba Why?" Junaid yace "It's not necessary Mami...." Mami ta hade rai tace "Ban gane it's not necessary ba" ya juya yana kallonta yace "Did he even do as if he noticed us here Mami" Mami tace "But you met him here ko, Kuma kasan yau ya sauka hanya...." Sudais yyi murmushi yace "To Mami ni da nayi masa maganan kin ga ya amsa? Ko kuma ya nuna ya gane ni" Mami tace "Eh I noticed wnn halinsa ne ai koh" Disgustingly Junaid yace "Mugun hali kenan" Dariya sosai Sudais yyi, Mami ta tabe baki tace "So what's the gain da ba ku gaisa ba ynxu, kamar wasu yara?" Junaid bai kuma ce ma Mami komai ba ya ja kujera ya xauna, Sudais yace "Anyway, Junaid that's just Shuraim... haka nan yake, and am telling you ba da wata manufa yyi hakan ba wllh, he is just different, totally different, he find it hard to speak at times, but he is lovely being with...." Junaid yace "But nima ba da wata manufa nayi hakan ba, I was checking on Heedayah that's why ban ma lura da shi ba ai" Sai kusan karfe sha daya da rabi Shuraim ya dawo dakin, har lkcn Junaid da Sudais na tare da Mami suna mata hira, Kana ganin Mami kasan tana cikin farin ciki, kai kace 'yar cikinta ce Heedayah, Shuraim ya gaidata, Mami tace "But are you sure you've eaten?" Shuraim yace "Na ci" Kujera ta nuna masa ya xauna yana kallonsu Sudais yace "Sannun ku" Sudais ya rungume hannunsa daga xaunen da yake yace "Ciwo mu ka ce maka muke?" Junaid dai danna wayarsa kawai yake bai dago ba balle ya kalli Shuraim, Shuraim bai tanka Sudais ba, Mami tace "Ya ka baro mutanen gida" yace "Duk lfya lau" Mami tace "Kaka ta koma gidan ne" yace "Aa" tace "Ohk" Junaid ya mike ya maida wayarsa aljihu ya nufi kan gado ganin Heedayah na kokarin cire blanket din kan ta, dukawa yyi dai dai fuskarta yana kallonta, ta bude idonta a hankali bayan ta cire blanket din, ido hudu suka yi da Junaid, ta fasa wani ihu, Sudais ya mike da sauri yana kallonta shi ma, Junaid xai kama hannunta ta dinga komawa baya tana ihun, da ta kallesa sai ta kalli Sudais dake tsaye sai ta kara sautin ihunta, duk sai suka tsaya suna kallonta gaba daya, shi dai Shuraim na xaune yana kallonsu, Mami ta nufota tace "What happened daughter, Yaya Junaid ne, with Yaya Sudais, don't shout, they are ur brothers" Ta dinga girgixa kai tana boye fuskarta cikin rawar murya tace "I am scareddd" lkci daya ta juya masu baya gaba daya, ta bude idonta a hankali tsoro karara a fuskarta, hada ido suka yi da Shuraim da ke kallonta don ta direction dinsa ta juya, ta rufe idonta da sauri ta kara budewa, tayi hakan yyi sau uku, d'an murmushin da iyakarsa lips dinsa yyi mata, tayi masa kuri da ido without blinking, Sudais ya xagayo toward direction din Heedayah tana daura ido kansa ta fasa ihu ta boye fuskarta jikin pillow, kofa junaid ya nufa ya fita ward din, Sudais xai karasa gun gadon Mami tace "Let her Sudais" Bai ta6a ta ba kawai ya tsaya, Mami ta iso kusa da ita ta dagota a hankali tace "They are all your brothers Heedayah, Sudais and Junaid" ta fashe da kuka tace "I'm scared" Sudais ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya fita ward din shi ma. A hankali ta bude fuskarta jin karan kofa, Hada ido suka kara yi da Shuraim, ta fi second goma tana kallonsa tun daga kansa har kafansa, can ta juya suka yi ido hudu da Mami, a karo na farko kenan da ta kalli Mami, shiru tayi tana kallonta a hankali ta kai hannu fuskarta tace "Mami??" Mami ta sakar mata murmushi, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta jawota jikinta ta rungume ta tace "Yess Daughter" Lamo Heedayah tayi jikinta murya can kasa tana nuna Shuraim tace "Mami what is that?" Mami tace "He is Shuraim" kara juyowa tayi ta kallesa sannan ta kalli Mami, Mami ta gyada mata kai assuring her he is the one, tace "Mami Yaya fa" Mami tace "Ya fita ynxu" Tace "Ya Sudais fa?" Mami tace "Shi ma ya fita" Kallon gadon da take xaune kai ta dinga yi tace "Mami wannan ne bed?" Mami tace "Yess" Mami ta nuna mata windown ward din tace "Wancan kuma window" Kallonsa kawai Heedayah ke yi, Mami ta nuna mata kofa tace "Door" Heedayah ta gyada mata kai a hankali tana kallon kofar, Shi dai Shuraim kallonsu kawai yake, Sakko da ita Mami tayi kasa, ta dinga kallon tiles din tana daga kafarta tace "Mami wnn ne floor?" Mami na murmushi tace "Yess daughter" Mami na lura da yanda take ta kallon jikinta tun daga kafa har hannunta sai kuma Mami ta ga tayi murmushi, Mami tace "Ki ce Alhmdllh" A hankali tace "Alhmdllh" Mami ta rungume ta tana kara hamdala a xuciyarta.... Xaunar da ita Mami tayi saman kujera tace "Let me make you tea now" Heedayah ta gyada mata kai, daga haka Mami ta tafi gun kayan shayin, Heedayah ta juya tana kallon Shuraim, d'aga kai yyi ya kalleta shi ma, tayi masa kuri ko kiftawa babu, ya dauke kansa ya ci gaba da danna wayarsa, har Mami ta kawo mata shayi kallon Shuraim Heedayah take kamar ta samu television, Mami tayi murmushi ta kamo hannunta ta sa mata shayin, Heedayah ta maido da dubanta gun Mami tace "Mami baya magana kaman ke" Mami tace "Yana yi mana, Ya Shuraim ne nace maki" Tace "Noo, I didn't hear his voice, ba shi bane" sai kuma tayi kasa da murya tace "But ya Shureen is wicked, this isn't him, wnn bai yi fada ba" Mami tayi dariya tana kallon Shuraim tace "Talk to her Shuraim" Murmushin kawai yyi shi ma bai dai ce komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, Mami ta xauna tana kallon Heedayah da sai da ta gama kare ma Cup din da shayin ciki kallo na kusan minti biyu sannan ta kai baki a hankali kamar me tsoron yin hakan, sai da ta kusa rabi ta cire cup din ta juya tana kallon Shuraim, har sai da Mami tace "Toh shanye shayin mana" sannan ta dauke kai ta ci gaba da shan shayin, tana shanyewa kuma Mami ta amshi cup din ta tafi ta wanke, Heedayah juya ta ci gaba da kallon Shuraim, ya d'an hade rai ya dago ya kalleta, wani ihu ta fasa tayi baya xata fadi ya mike da sauri ya rike kujeran, Mami ta fito da sauri tace "What happened?" Heedayah ta boye fuskarta cikin rawan murya tace "I'm scared" Mami ta dagota ta rungumeta tace "Don't be dear, no one is harming you" ta hannun Mami ta bude ido a hankali tana lekosa kuma, murmushi ya sakar mata, ta janye jikinta daga na Mami ta tsaya tana kallonsa da manyan idanuwanta da suka yi ja, sosai hakan ya ba Mami dariya, Mami tace "Take her out Shuraim kuyi strolling but don't go far..." Yana son ce ma Mami hasken waje xai mata yawa amma kuma bai son yin maganan, Mami tace "Or... we shouldn't, tunda likitocin basu bada umarnin haka ba koh" Shuraim ya gyada mata kai, ta kama hannun Heedayah ta daurata saman gado, ita fa ta samu TVn ta na farko a duniya wato shuraim da ya juya sai yaga kallonsa take keenly, Mami ma ta rasa kan wannan kallon da Heedayah ke masa, mikewa Shuraim yyi daga karshe ya nufi kofa don ya gaji da kallon, da sauri tace "Mami xai tafi" ya juya ya mata wani shegen kallo ta fasa ihu a tsorace ya bude kofa yyi wucewarsa. A waya Mami ke nuna ma Heedayah da ta makale jikinta hoton Abba, Farida, da Junaid.... Da Mami ta tafi sai Heedayah ta sa hannu ta dawo da hoton, sai ta kalla yyi na kusan minti biyu sannan Mami ta wuce, ana haka aka bude kofar, Heedayah ta daga kai da sauri, Sudais ne ya shigo, Mami na nuna mata shi tace "Yaya Sudais, that's him...." Heedayah ta dinga kallonsa har ya karaso yana mata murmushi yace "Hi...." A hankali tace "Hello" yace "You get my voice??" ta gyada masa kai tace "Ya Sudais" Ya wara ido yace "Yess, how are you?" Tace "I'm fine" ta kalli Mami tace "Mami Yaya fa?" Mami ta kalli Sudais tace "Ina Junaid?" Sudais yace "He told me he will be coming back later, ya fita" Mami tace "Ina yace maka xai je?" Sudais yace "I have no idea" Heedayah dai sai kallon Sudais take, ya sakar mata murmushi, ta xaro ido tace "Mami" Mami ta kalli Sudais sannan ta kalleta tace "He smiled at you, smile back" murmushin ita ma tayi kokarin yi masa. Har yamma Junaid bai shigo ward din ba, Mami da Sudais ne kadai dakin, Heedayah ta tambayesa ya fi a kirga, daga karshe Mami ta kirasa, yana dagawa tace "Where are you?" yace "Hotel" Tace "To ka taho yanxu" daga haka ta katse wayarta, ba a dau lkci ba Junaid ya shigo ward din, tun da ya shigo Heedayah ke kallonsa, ya karaso cikin dakin suka gaisa da Sudais ya gaida Mami sannan ya kalli Heedayah, a hankali tace "Yaya" yace "Ba shi bane" Tace "Toh ai muryarsa ne na ji" Ya d'an saci kallon Mami ganin kallonsu take yace "Kin san muryarsa ne kike ihu daxu?" Shiru tayi tana kallonsa, ya karasa kusa da ita ya sakar mata lallausan murmushi ya xauna gefenta yace "How are you?" Ta kai hannu hancinsa a hankali tace "I am fine, is that ur nose" Ya wara idanuwansa yace "Noo it's urs" ta kai hannunta nata tana ta6awa, ya ja mata hancin nata yana murmushi ta mayar masa da murmushin.... Throughout ranan komai Heedayah ta tambaya Mami bata gajiya da bata amsa don she's just so curious, she wants to know everything, idan Mami bata gaya mata ba Sudais xai gaya mata har Magrib, Junaid ne ya kawo masu abinci, wajen karfe takwas xa su wuce hotel dinsu Mami tace "Wai Shuraim fa" Junaid ya nufi kofa, Sudais yace "I don't know, ba mamaki ya koma Nigeria ma" Da mamaki Mami ke kallonsa ya fita yana dariya... Har washegari Mami bata ga Shuraim ba, ta kira Junaid da sassafe tace ya ba Sudais waya, bayan sun gaisa tace "Ka turo min lambar Shuraim" Sudais ya amsa mata da toh, cikin few seconds kuma ya tura mata, dialing number tayi, yana fara ringing aka daga, tace "Where are you..." Yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, kana Ina ne?" Yace "Ina Abuja" Tace "Abuja?" Yace "Ehh, tafiyar ya xo min a gaggawa ne" tace "Toh yayi kyau" daga haka ta katse wayarta. Dariya Sudais ya dinga yi da Mami ta gaya masa Shuraim na Abuja, yace "I told you, ni nasan ba karamin aikinsa bane, kadan daga abinda xai aikata kenan" Junaid yace "That's foolishness" Mami dai bata ce komai ba... Haka suka ci gaba da kula da Heedayah da ta fara sabawa da abubuwa da dama yanxu, likitocin har suka bada izinin a dinga fita da ita ana xaga clinic din, xuwa ynxu ta daina tsoron jama'ah sai dai fa idan taga cinkoson jama'ah jikinta ya dingi rawa kenan, bata son crowd, a haka likitocin suka sanar ma Mami xa su sallamesu nan da kwana uku. A bangaren Salima kuwa, hotel hotel ta dinga bi tana kwana har ta samu ta harhada kudin komawa Nigeria, sai da a ranta ta dau kudurin bata kyale Junaid ba....


I'm not feeling well today, ayi manage da wnn plss....


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Mami na xaune office din likita a ranan da aka sallamesu asibiti yana bata conditions na kula da idanuwan Heedayah idan sun koma gida, do's and don't kawai yake xayyane mata, sosai Mami ke sauraronsa don ko kadan bata son a samu wani matsalan, da turanci take tambayarsa ko har kwana Heedayah xata dinga yi da Glasses din nata da aka bata, ya amsa mata da A'a, amma.... throughout the day the glasses should be on her eyes ko bandaki xata shiga, nan ya kara sanar ma Mami after wata shidda xa su dawo for check up yana nan rubuce takardan da aka bata, godiya Mami tayi masa sosai sannan ta fita office din, dole hotel xa su koma don sai dare jirgin Nigeria xai tashi, A cikin Tricycle din da xai kai su hotel din Heedayah ta rufe idonta jikin Mami don duk Inda ta kalla mutane ne in group kuma hakan na rikitar da ita ba kadan ba ga kuma Haske da yyi mata yawa sosai wanda tun asibiti hakan ke sa mata ciwon kai, Bayan sun shiga dakin hotel din Heedayah na kallon Sudais tace "Ya Sudais why are some people black and others White in color??" Mami dai tayi dariya bata ce komai ba, Sudais ya dawo kusa da ita ya duka yace "The black are the Africans, and the white may be indians or Americans...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta kalli Mami tace "Is Mami an Indian also?" Junaid dake tsaye jikin window yana danna waya bai ko kallesu ba, ya d'an yi murmushi amma bai dago ba still, Mami tayi dariya tana jiran jin me Sudais xai ce mata, Heedayah ta kalli hannunta tace "And I am also white, does this mean I am an indian?" Sudais ya d'an juya manyan idonsa yace "Noo Neither Mami nor you are Indians...." With confusion Heedayah tace "But how, we are white also" Sudais yace "Ohk let me explain to you better, but ur brain is small to understand my explanation..." Heedayah ta xaro ido tace "Ohk wait... is yours big?" Dariya Sudais yyi yana kallonta yace "Yess" tace "shi sa kanka kato ne, nawa karami?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "To idan nawa ya kai kmr naka sae ka min explanation din?" Sudais yace "Yess dear" Kofa Junaid ya nufa, Mami ta bi da sa kallo tace "Where to?" Yace "I will be back soon Mami, I want to get something" Heedayah tace "Yaya should I accompany you?" Juyawa yyi yana kallonta bluntly yace "Noo" Ta wani tabe baki ta juya masa idanuwanta tace "Just pulling ur legs, I am going no where" Bude kofar yyi ya fita, Sudais dai yyi murmushi kawai, Mami ta kamo hannunta tace "Heedayah yayanki ne fa kike masa rashin kunya" Heedayah tace "Mami shi ma fa ya min rashin kunyan, daxu da safe he even pinched me, Sudais yace "Idan kina yi masa haka zae xaneki ne one day, and bbu ruwana" Heedayah tayi shiru sai kuma tace "Shi ma Mami xata zanesa ae" karfe bakwai da few minutes jirginsu ya tashi daga india xuwa Nigeria... Ganin ynda Heedayah ke bin kowa na cikin jirgin da kallo Mami ta jawota jikinta tace "Kiyi baccin ki" tace "Mami su ma duk gidanmu xa su je wajen Abba?" Mami bata san lkcn da tayi dariya ba tace "Nooo dear, but we are all going to Nigeria that's our country" Heedayah tace "Toh Ina xa su je su" Mami tace "Nigeria is a very large County with 36 states ba kin sani ba??" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace "Toh everyone u are seeing inside this plane is going to various state, some Kaduna, other kano, and so on" Heedayah tace "Jirgin ne xai kai mu gida wajen Abba?" Mami tace "Noo mota xa a kawo airport sai mu shiga a kai mu gida" A Hankali Heedayah tace "Ohk" daga haka tayi lamo jikin Mami nan da nan bacci ya dauketa, Sudais da Junaid na xaune

Please Login or Register in order to submit comment