Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

HEEDAYAH Complete Hausa Novel Document by HEEDAYAH


HEEDAYAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 115727



HEEDAYAH

Reading Time: 9 Hours

Added On: 27, Apr 2025

Author: Khaleesat Haidar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07087865788

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 580.96 kb

File Type: txt

Views: 169+

Download: 457+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻





All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book.... My special greetings to my lovely Mum Hajiya Hajarah, and all my small mums😍 my siblings and cousins ain't left behind too, ina son ku gaba daya.... My Isiaka Safia I greet u too, and my lovely fans that have waited so long for Khaleesat Haiydar... ina maku barka da sllh, Allah ya amshi ibadunmu baki daya, ga *Heedayah* I know u all will love it, coz I Khaleesat is already in love with it 😊
No disappoinment In sha Allah 😉



1.....

Wani d'an matsakaicin daki ne da aka xagaye da tsadaddun labulaye, dakin na dauke da katifa babba, sai kayan kallo daga gefe, sai cushion tsadadde guda daya, Dattijuwar da baxata haura hamsin da biyar ba dake xaune dakin tayi tagumi tace "Toh mu dai baxa mu gaji da addu'a ba, Allah ubangiji ya bata lafiya, watan gobe kenan dai ake sa ran komai xai yi dai dai koh?" Matashiyar matar dake gefenta ta d'an yi murmushi tace "Haka dai likitocin suka ce in sha Allah, sai dai kinsan kana naka ne Allah na nasa, amma wnn aikin shine na karshe da xa ayi mata idan Allah ya yrda, sai kuma fatan Allah ya sa a dace" Yakumbo tace "In sha Allahu xa a dace, abinda kullum gaya ma Allah muke, kaf dangi bbu mai irin laluran nan balle ace ko gado ne, sam bbu shi a danginmu gaba daya, ko ke akwai a naku??" Dariya matar tayi tace "A'a Yakumbo" Yakumbo tace "Atoh, Allah dai ya raba bawa da wahala ke ma kuma Allah ya sauke ki lafiya, Indiyan xa a kara komawa kenan ayi aikin?" Matar tace "Ameen, ehh can xa mu je" Yakumbo tace "Toh in sha Allahu karshen wahalan kenan" Matar tace "Allah ya sa" agogo Yakumbo ta kalla tace "Anya tafiyar nan taku na nan yau kuwa Amina, shiru shiru har yanxu Umar din bai xo ba" Amina ta kalli agogon ita ma tace "Kuma na kirasa daxu ban samesa ba, ina jin meeting suka shiga, kila sai gobe dama na cire rai yau" Yakumbo tace "Atoh, ku bari kawai sai gobe yamma yayi, sai kace wa inda ake kora, ga hanyar nan da ba kyau gari ya xama abinda ya xama mucuta ta ko ina...." Amina tace "Haka ne" Yakumbo tace "Naji wai matar Salihu na ta neman ki da fada ko? Kar ki kuskura ki kulata gayyar mayu ne, har ita Asama'un ma ki bar kulawa duk haushin ki suke ji suna ganin kin fi su walawa gidan miji, ba su san Allah ne ya baki ba" Amina tayi murmushi bata ce komai ba, Yakumbo ta kara da cewa "Kuma wai sai kiyi ta boye yarinya kar su gani, wai haka?" Amina ta kalleta tace "Aa ba gaskiya bane, ke kanki shaida ce Yakumbo tun tana yar yarinya ba a fiye fito da ita cikin jama'ah ba, a ko da yaushe tana daki tare da ni ko mai kula da ita, ko malamarta, har yau 'yan anguwa basu wani san kalan Heedayah ba, da kyar ki xo gidan ki ganta a parlor, to sau tari idan anyi baki har su tafi ma baxa su ganta ba shine ake ganin kamar boye ta muke kar a ganta" Yakumbo tace "Toh ai gwara haka, haka kawai baka san bakin wani ba, ayi ta sa ma yarinya baki, gaskiya kun yi dubara, ki rabu da su suce duk abinda xa su ce, lafiyan yarinya shine gaba kan komai" Amina dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Har bokon ma a gida ake mata kenan?" Amina tace "Ehh har islamiyya" Yakumbo tace "To madalla, ae gwara hakan, Ke leko yar mutane naji shirun yyi yawa, Allah ya sa dai gantalallun yaran makotan nan nawa ba shigowa suka yi suka yi waje da ita ba" Da sauri Amina ta mike tana leka tsakar gidan tace "Heedayah??" Jin shiru ta fito tsakar gidan, Katon Babyn robanta da take combing gashinta kadai ne kan tabarma da comb din sai hularta amma babu ita, Yakumbo ta mike tace "Ni da nasan sai sun shigo sun ja ta, Amma wa ennan yara iyayensu sun haifi jaraba kawai, yara kauyawa bbu kamun kai kawai malam..." Dawowa Amina tayi dakin ta dau Hijab dinta sannan ta fita waje, Yakumbo na biye da ita tana cewa "Ni dai Allah ka rufa min asiri ba rafi suka ja ta suka kai ta ba in shiga uku, yarinya dai ba ido ba, daga kawo min ziyara shaidan ya fake ta nan yayi abinda ya ga dama tawa ta sameni ina xaman xamana...." Tun Mahaifiyar Heedayah na daurewa ana shiga bukkokin makota duba Heedayah a kauyen har taji hankalinta ya fara tashi sosai ganin babu alamar yar tata.... Yakumbo dai sai salati take xabgawa a rikice tana yafa gyalen da ya ki xama tana cewa "Toh me xance ma kanina Umaru jama'ah?? Ina xan ce yar sa ta shiga?" Wata mata ce tace "Daxu fa naga sun yi hanyar kasuwa da su Hinde da Bibalo, har da fatu, kusan dai su shidda suna rike da hannun ita yarinyar" Yakumbo ta saki salati tace "Toh kuwa wllh Ubanta a Habuja yake kuma duk iyayensu xae sa a daure idan abu ya samu yar sa, ita fa kadai garesa sae ynxu da uwar ke da sabon ciki, shekararta goma sha biyu, kuma ba idanuwa gareta ba, to a kan me gantalallun yara xasu ja ta su tafi da ita kasuwa, uwayensu xa su siya mata a kasuwar? Tun shekaranjiya da suka xo kauyen nn nake ja ma ja'iran yaran nan kunne ganin ynda suke makale mata har da masu wasa da gashin kanta nake ce masu su fita harkarta, ita dai ba fuskarsu take gani ba balle ace, to wannan wani irin bala'i ne, hanyar kasuwan nan da babu kyau sace sace yyi yawa, haba jama'ah??" Tuni duk aka watse aka dau hanyar kasuwa aka bar Yakumbo tsaye ita kadai tana kumfar baki, can dai ta bi su da sauri ganin sun yi nisa. Yara ne duk mata kusan su biyar karkashin bishiyar mangwaro sai mata biyu dake saman bishiyar suna tsinkar nunannun mango suna jefowa kasa matan dake kasa suna kwasa suna xubawa a karamin buhu, wata yarinya ce warce duk baxata wuce sa'aninsu ba tana durkushe hannunta rike da mango tana sha, daya hannunta kuma na rike da rigar fatuu don ita ke mata jagora, fara ce sosai, kana ganinta kasan jinin Fulani ce don gashinta dake bude ko hula babu ma ya shaida haka, idanuwanta farare ne kal kamar Madara tana kifta su a hankali kai kace ras take ganin kowa a wajen, sai dai babu abinda take gani banda duhu, wajen duk ya kauraye da surutun yaran dake tsinkar mangwaro xa su kai kasuwa su siyar, wata bakar mota ce ta ja tayi parking a wajen, duk suka juya yaran, lkci daya kattin maxaje biyu suka fito motar da sauri, gudu yaran suka yi har da Fatuu da ta warce rigarta daga hannun Heedayah, na saman bishiyar ma duk suka diro suka ruga aguje, Heedayah ta saki mango din hannunta ta dinga waige waige a tsorace, maxan suka bi bayan yaran suka samu kamo uku daga cikinsu, Heedayah ta mike ita ma suka daga ta suka saka cikin motar, kan kace me driver ya ja motar da gudu suka bar wajen. Gaba daya ihu yaran ke yi cikin motar har da Heedayah dake ta kwala ma Mahaifiyarta kira tana cewa "Ammina...." Wanda ke xaune a baya ya ciro bindiga yana nuna masu da jajayen idonsa fuskarsa a murtuke ya daura hannu a lebbansa alamar su yi shiru, lkci daya su ladi duk suka yi shiru sai rawa jikinsu yake, Zulai har da sakin fitsari a gun, Heedayah ce kadai bata fasa ihun da take ba, Mutumin ya shake wuyarta yana nuna mata bindigar yace "Ohh ke baxa ki rufe mana baki ba koh?" Jikin Ladi na 6ari tace "Bata gani" Mutumin ya shiga kare mata kallo sannan ya gyada kai yace "Kuma duk yanxu xaku daina gani" yana fadin haka duk ya rufe ma sauran ido da kyalle, Heedayah da ta ki yin shiru kuma ya dinga buge mata baki yana marinta, hakan kuma bai hanata ci gaba da ihu ba tana lalube laluben inda xata fita, daga karshe jin taki shiru wanda ke xaune gaba ya miko masa wani leda yace "Bada mata a fuska" hakan kuwa aka yi, nan da nan kuwa ko ina yyi tsit a motar, a hankali Heedayah ta fada jikinsu Ladi. A hanya mutan kauyen suka hadu da su Hinde da sauran matan da suka samu guduwa, Nan su
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download HEEDAYAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album