Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mike ta nufi kofa tace "Toh Hajiya" Mami ta xauna saman kujera don tayi deciding yau baxata fita ba xata yi monitoring yanda Karime xata kula da Heedayah. Junaid ya mike daga xaunen da yake yace "To Mami ai ni baxan san size din sweater da xan siyo mata ba, Kuma wani irin takalmi kenan?" Mami tace "To kai makaho ne? Look at her mana before going..." Ya dai yi shiru bai ce komai ba, can ya nufi kofa murya can kasa yace "Sai na dawo...." har xai fita tace "Then go with her kar kaje ka siyo wanda baxai yi mata ba har takalman ma a gwada mata, ka siyo ma Farida ma takalma biyu with a sweater" ya juyo yace "Toh" Mami ta kalli Karime dake xaune kasa tace "Ki duba daki ki dauko Hijab dinta da takalmi xa su fita, ai na nuna maki inda suke" Karime tace "Toh Hajiya" Da sauri ta shige dakin Mami, Heedayah dake xaune gefen Mami ta washe fararen hakoranta jin xa a fita da ita, Mami na lura da ita ta girgixa kai ta d'an yi murmushi, Shi kansa Junaid kallonta yake, Karime ta fito da sauri ta sa ma Heedayah hijab dinta da takalmi, Mami ta mike xata shiga daki don dauko turare ta sa mata, Karime ta dauke cup din da Heedayah ta sha cornflakes ta fita xata kai kitchen din da Mami ta nuna mata, a parlor ta tadda Mumy xaune tana kallon tv duk da gaba daya bata ma san abinda ake a tvn ba, Kwarjinin Mumy kadai ya isa a gane ita ma matar gidan ce, Karime ta d'an duka tace "Sannu da hutawa Hajiya" Mumy na kallonta a dakile tace "Yauwa.... Ke ce sabuwar mai aikin da ta xo yau?" Karime tace "Ehh ni ce" Mumy ta d'an saki fuska tace "Sannu da xuwa, daga wani garin kika xo?" Tace "Daga kano na xo Hajiya, a can mariri iyayena suke" Mumy tace "Maa sha Allah, ai ko nasan Mariri..." Karime tace "Allah sarki" Mumy tace "Toh kin ci abinci kuwa" Karime tace "Na ci wllh Hajiya" Mumy tace "Toh ki saki jikinki kin ji, ko me kike bukata ki xo ki sameni...." Karime ta kara dukawa har kasa tace "In sha Allahu Hajiya, Nagode Sosai sosai, Allah ya kara girma" Mumy na murmushi tace "Ameeen" Karime ta mike ta wuce kitchen, Mumy ta bi ta da kallo..... Ba a dau lkci ba sai ga Junaid ya fito rike da Heedayah, Junaid ya gaida Mumy, da fara'a sosai ta amsa tace "Sannu Junaid, xa ku fita ne" yace "Ehh xa mu je mu dawo" Mumy tace "Ke 'yar fara ba gaisuwa?" Heedayah dai tayi shiru, Junaid ya duka dai dai fuskarta yace "Can't you greet?" A hankali tace "ina kwana" Mumy tayi dariya tace "Ina wuni dai xa ki ce baby" Heedayah tace "Ina yini" Mumy tace "Lafiya lau, xo in gyara maki Hijabin" Junaid na rike da Heedayah ya kai ta har gaban Mumy, Mumy ta gyara mata Hijab din tana kara goge mata bakinta tace "Me kika ci haka?" A hankali Heedayah tace "Cornflakes Mami ta bani" Mumy tace "Ahh Lallai ga alama, to sai kun dawo" Junaid yace "In sha Allah" yana rike da hannun Heedayah suka nufi kofa, Mumy ta bi su da kallo har suka fita parlon sannan ta sauke ajiyar xuciya tana jijjiga kafa. Anguwa ce ta manyan mutane da suka yi fice aka kuma san da su a kasa Junaid ya shiga, a hankali yake driving, Lkci lkci yake kallon Heedayah dake gefensa xaune ta jinginar da kanta da glass din motar idonta a waje kamar dai me gani, Junaid yace "Tell me what you are seeing...." ta juyo xuwa Inda take jiyo muryarsa a hankali tace "Darkness" shiru Junaid yyi driving slowly, can ya kamo hannunta daya murya can kasa yace "What color?" Ta wara ido tace "Just dark" Bai kuma cewa komai ba yyi parking dai dai wani gida da yake tunanin gidan da yake nema ne sbda number da ya gani daga gefen gate din gidan, dialing din number dake call logs dinsa yyi ba a dau lkci ba aka daga, yace "Gani a kofar gidan if I'm not mistaken" ajiye wayar yyi bayan an sanar masa ana xuwa, Heedayah tace "Ina muka xo?" Yace "Somewhere" tayi shiru kmr me son gane ma'anar somewhere da yace, can tace "Ohk wani waje?" Murmushi yyi yace "Yes" Bude gate da aka yi yasa ya kalli gate din ta cikin tinted glass dinsa, Mutumin jiya ne ya fito gate din, Junaid ya bude motarsa yana kallon Heedayah yace "Ki jirani in dawo yanxu" Ta 6ata fuska tace "Noo plss go with mee" yace "Yanxu xan dawo am not going anywhere" Ganin kiris ya rage ta fara kuka ya dau wayarsa yace "To rike min..." daga haka ya fita daga motar ya kulle ya nufi gun Mutumin dake tsaye, gaisawa suka yi, Mutumin yace "Fatan dai ban mu yi inconveniencing dinka ba, mu ma anyi delaying flight dinmu ne" Junaid na mika masa wayarsa yace "No, not at all..." Mutumin ya amsa yace "I am very grateful, ni Sunana Ahmad" Junaid yace "I am Junaid" Alhaji Ahmad yace "Nagode kwarai Junaid" Junaid yyi murmushi yace "Babu damuwa, ni xan koma" Alhaji Ahmad yace "Toh Allah ya kiyaye, da numberka ka kirani ai..." Junaid yace "Ehh" Alhaji Ahmad yace "To maa sha Allah I will save it" daga haka Junaid ya koma motarsa ya tada, Alhaji Ahmad dai na tsaye har yyi reverse ya wuce..... Karfe shidda saura Junaid ya koma gida tare da Heedayah bayan ya siya masu rigunan sanyi da takalma ita da Farida, Mami ta dauko eye drop da ya siyo jiya bayan ta kai kayan daki tace "Barrister yace idan ka xo sai ka gaya min yanda xa ayi da wnn" Junaid ya amshi ledan maganin ya fiddo su guda biyu yace "Wannan idan xata yi bacci da daddare xa a sa mata just two drop in each of her eye, shi kuma wnn idan ta tashi da safe, it's should be everyday ba a skipping....." Mami tace "Toh shkkn Allah ya sa a dace, su kuma maganin mene?" Yace "Toh ana sa rai with the help of this idan an xo yin operation din idon baxa a samu matsala ba idan Allah ya yrda...." Mami tace "Toh Allah ya sa" Mami tace "Babu wani wanda xata dinga sha?" Yace "A'a, sai dai in bincika" tace "Toh Shkkn...." Mikewa yyi yace "Ni xan koma Mami" tace "Baxa ka jira ka ci abinci ba?" Yace "Aa xan wuce" tace "Toh sai gobe" Khadijah ce ta shigo parlon Mami da sallama hannunta daya rike da plate me dauke da cake da aka yanka gida biyu yan madaidaita, daya hannunta kuma da wani cake din tana ci, ta karaso gun Heedayah dake xaune tace "Mumy tace ki dauki naki" Mami ta kalli Karime dake rakube waje daya tace "Ki amsa ki ajiye mata" Karime ta taso da sauri ta karba, Khadijah na kallon karime tace "Dayan aka ce ke ma ki dauka" Karime ta kalli Mami, Mami tace "Toh an gode" Khadijah tace "Cousin dinmu ne yyi birthday" Mami tace "Allah ya raya sa" Khadijah ta juya ta bi ta gefen Junaid ta fita, Mami na kallon Heedayah tace "Xa ki ci cake?" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace "Toh bata Karime ke ma ki dau naki" Karime ta mika ma Heedayah daya ita ma ta dau daya ta fara ci, Heedayah na kallon Inda take jin muryar Mami tace "Mami in tsan masa?" Mami ta kalli Junaid dake tsaye bakin kofa har sannan tayi murmushi tace "Cinye kayan ki ya wuce" Juyawa Junaid yyi ya fita dakin, Heedayah ta fara cin cake dinta, dai dai bakin kofar shigowa yau yyi karo da Salima, tana rike da gyalenta da jaka a hannu, suna hada ido ya bata hanya.... Cikin wani siririn murya tace "Noo ka wuce mana ai kai ka bude kofar...." Ya kara kallonta sannan ya bi gefenta yace "Thank you" tace "Haba thank you kuma, ai kai ka bude kofa" shi dai bai tsaya ba kuma bai ce komai ba yyi wucewarsa, ta bi sa da kallo ko kiftawa bbu... Karime ce kitchen bayan Magrib tana dafawa Heedayah Indomie, tana xuba Indomie din cikin ruwan dake tafasa kan gas aka bude kitchen din Mumy ta shigo, ganinta tace "Aiki kike yi Karime?" Karime tace "Ehh Hajiya Indomie nake dafa mata" Mumy tace "To ke kin ma ci abinci kuwa" tace "Ehh dama na rana bai kare ba...." Mumy tace "Na rana kuma, kin ga idan kin kai masu Indomien ki xo ga cous cous a kula ki diba ki ci kin ji, abincin rana ai ya huce yanxu" Karime tace "Toh Hajiya Nagode Sosai" Mumy tace "Amma fa kar ki wani ce ma uwar dakin ki nace ki xo ki amshi abinci ke dai kawai ki shigo kitchen ki diba kije can dakin ku ki ci" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" Mumy ta ajiye cup din hannunta ta fita kitchen din.....


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Washegari karfe goma saura na safe Mumy ta gama shiryawa xata fita office, Tana duban Karime a parlonta tace "Toh ni xan wuce aiki yanxu, sai ki saka ido sosai ki kula da duk abinda nace maki, karfe sha biyu na yi ki daura maku girkin abinda xa ku ci dai dai cikin ku, ita kuma Heedayah xuwa nan da sha daya abinda ki ka ga na hada mata jiya sai ki hada mata ki xuba Madara amma ban da sugar" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta dau jakarta ta nufi kofa tace "Sai na dawo" Karime tace "A dawo lafiya" Har Mami ta fita ta juyo tace "Kar ki bari ta bar parlon nan komai xakiyi kiyi mata a nan parlon, bana son ku fito" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta kulle kofarta ta wuce, A main parlor suka hadu da Mumy tana ma mai aikinta magana cikin tsawa, matar da baxata wuce Karime ba sai rawa jikinta yake tana bata hakuri, Mumy na ganin Mami ta dakata da masifar da take, idon da suka hada yasa Mami tace "Mun tashi lfya?" Mumy tayi murmushi tace "Lafiya lau wllh, ya kwanan Baby" Mami tace "Alhmdllh, ya na su Rabi'ah" Mumy tace "Lfya lau, sun ma wuce makaranta ai" Mami tace "Toh maa sha Allah, na fita..." Mumy tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Mami ta amsa da Ameen sannan ta fita parlon, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofa, ta wani ta6e baki ta kalli Sajida mai aikinta cike da masifa tace "Kin tashi a gabana ko sai na gaura maki Mari, 'yan aiki ko 'yan wahala, wllh bana son in sake tuna maki sharan dakin yarana idan ba haka ba ni ynda ake canxa sutura haka nake canxa ku don ma ki ji" Mai aikin ta mike da sauri ta tafi dakinsu Rabi'ah, Shuraim dake xaune dining ya ajiye cup din hannunsa ya mike ya dawo parlon, Mumy tace "Amma dai yau baxa ka fita aiki ba...." Yace "Sai da yamma...." Mumy tace "Na ji ma Baffan naku yyi tafiya ko?" Shuraim yace "Ehh yana Abuja" Mumy ta ta6e baki, Shuraim yyi kasa da kai yace "Mumy ki dinga hakuri da mutane don Allah, barin wa ennan bayin Allah, they don't deserve the way u are treating them, they never wished for their selves to be maid, and don't forget no condition is permanent, su Rabi'ah yara ne da baxa su iya gyara dakinsu ba idan sun tashi? Ba fa aikin da suke yi a gidan just gyaran dakin ma sai an masu?? This is...." Dakatar da shi tayi cikin tsawa tace "Rufe min baki malam, ni xaka taso kayi ma fada?" Yace "Ni ba fada na maki ba, I am telling you what I think is right" Ta kuma yi masa wani tsawan tace "Baka isa ka gaya min what to do and what not to do ba, out of my sight now.... Duk walakanci da cin fuskan da ubanka ke min a gidan nan ka ta6a tunkararsa ka gaya masa what is right? Sai ni marainiyar wayon ka, to baka isa ba ne...." Shuraim ya shafa kansa bai dai ce komai ba yyi wucewarsa dakinsa, ta bi sa da wani irin harara tace "Wawa kawai...." Karfe sha daya da rabi Karime ta fito hada ma Heedayah cornflakes, Mumy ce xaune parlor da Hajiya Sadiya, Karime ta duka har kasa ta gaisheta, da fara'a Mumy tace "Lafiya lau Karima, ya aiki" Karime tace "Mun gode Allah" Mumy tace "Toh madalla" Karime ta gaida Hajiya Sadiya ita ma ta amsa sannan ta mike ta wuce kitchen, Hajiya Sadiya na kallon Mumy murya can kasa tace "Ita ce mai aikin" Mumy ta gyada mata kai, Hajiya Sadiya ta jinjina kai alamar gamsuwa, can sai ga Karime ta fito rike da cornflakes da ta hada, Mumy tace "Ga kwai can da na soya a kitchen ki dauka, na ci ya isheni gashi ba almajirai a nan" Karime tace "Toh Hajiya Nagode" xata koma kitchen din Mumy tace "Toh ajiye kofin cornflakes din kar ya xube, ta ajiye ta wuce kitchen din da sauri da sauri, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya dake mata magana cikin rada, Mumy ta gyada mata kai kawai, Karime ta fito dauke da tulin kwai a plate, Mumy tace "Ki fito da ita mana ta sha cornflakes din a nan, gashi nn ma duk ya jike...." Karime ta d'an fara kame kame, tace "Hajiya dama Madam tace kar take fitowa ne, komai xa mu yi muyi a can ciki" Mumy dake saurarenta sosai tace "Ayyo, toh tunda ita ta kawo ki ba ni ba shkkn kai mata ciki, dama so nayi in d'an sa ki gyaran bangarena ne, shi sa nace ki fito da ita nan sbda a sa mata ido, amma dauka ki wuce xan yi da kai na, na aiki tawa mai aikin kasuwa ne dama shi yasa" Karime ta d'an risina tace "A'a ba haka bane Hajiya kiyi hakuri, d'an dai gyaran bangaren ki ai xan maki, bari in kawo ta nan din" Mumy tace "Aa kar uwar dakin ki ta ga kin karya mata doka kiyi laifi...." Karime tace "A'a da wuri ae xan yi in gama" daga hka ta wuce ciki, sai ga ta ta fito da Heedayah dake sanye da wando iya gwiwa da karamin riga an daure mata kalabanta waje daya, she look more of a half cast sbda irin haskenta, dai dai fitowar Shuraim waya kare kunnensa da ganinsa kasan fita xai yi, Karime ta ajiye ta nan gefen Mumy ta dauko cornflakes din ta sa mata a hannu tace "Toh gashi ki sha masaran naki 'yar kyakkyawa" Shuraim dai sai kallonsu yake walking slowly, Heedayah ta laluba cokalin ta deba content din cup din ta kai baki, girgixa kai tayi ta fito da na bakinta saman tafin hannunta da sauri tana yamutsa karamin bakinta tace "Yyi soakkk....." Mumy ta saci kallon Hajiya Sadiya ta dalilin hakan kuma ta hango Shuraim da ya tsaya don bata san ya fito ba duk da kamshin turaren sa da ya gauraye parlon, Karime na kallon Heedayah tace "Kika ce?" Heedayah na kara tofar da sauran na bakinta tace "Xai sa in yi amai, it's soft" Mumy tayi murmushi tace "Kai yaro ma dai, wai tana nufin ya jike, ki hado mata wani kawai" Karime tace "Au... toh..." Sannan ta dau cup din ta wuce kitchen da sauri, ba a wani dau lkci ba ta dawo da wani Cornflakes din a cup ta mika ma Heedayah, sannan ta kama hannunta ta juye na bakin ta da ke kai kan nata hannun, Heedayah ta fara shan cornflakes din, Karime ta tafi kitchen ta xubar da na hannunta ta dawo tana kallon Mumy da ladabi tace "Ina xa a gyara maki?" Mumy tace "Ki tafi sama xaki ga kofofi duk ki shiga ko wanne ki share ki goge" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" daga haka ta wuce sama, Shuraim ya karasa dinning ya xauna, Mumy ta d'an kalli Inda yake, sai kuma ta juya tana kallonsa da kyau tace "Ba fita xaka yi ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ehh ina jiran Umar ne..." Mumy tace "Toh ba sai kaje can gidan nasu ka samesa ba" Shuraim yace "Yace in jirasa a nan...." Mumy tace "Toh ma yaushe ku ka fara fita da Umar?" Shi dai Shuraim bai ce komai ba, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace "Ni da ka d'an taimaka Shuraim ka amso min MTN nan waje naga da wani me kiosk a layin..." Ya kalleta sannan yace "Toh bari in maki transfer kawai...." Hajiya Sadiya tace "Aa kar ka wani ba kanka wahala, ga kudin ka amso min" Yace "Gashi ina yi, na ma yi ynxu" Hajiya Sadiya bata sake ce masa komai ba, Mumy dai ya girgixa kafa take, Tasss Heedayah ta shanye cornflakes din cup din tace "I want to take water" Mumy ta d'an kalleta tace "Sai jira ta xo ta baki ai" Shuraim dai yana ta danna wayarsa, har Karime ta fito bayan kusan minti talatin, tace "Hajiya duk na gyara na goge" Ba tare da Mumy ta kalleta ba tace "Sannu" Karime ta daga Heedayah tace "Mu je ki kwanta lkcn baccin ki yyi" Heedayah tace "Xan sha ruwa" Karime ta ja ta har xuwa gun da fridge din dinning area yake, Heedayah ta taji ta taka abu me tudu, tsayawa tayi ta kara kai kafarta kan abun, Shuraim ya dauke idonsa daga kan screen din wayarsa yana kallonta, ta kara takasa, ta kuma takasa just wanting to know what she's matching, ta kara cire kafarta ta kara mayarwa, Karime dai na kokarin dauko mata ruwa a fridge bata ma san me ake ba, Heedayah ta duka ta sa hannu tana lalubawa ta ji me take takawa, dagota yyi ya rike duk hannunta biyu ya bugesu da karfi, sannan ya ja kunnenta daya fuska daure yace "Dutse aka ce maki kike takawa??" Kara buge hannunta yyi ya ja kunnenta ta fashe da kuka sosai, Karime dai ta ja gefe bata ce komai ba, cikin kuka Heedayah tace "Sai na gaya ka da Mami, ni ba Ina ce baby na taka ba" Ya buge bakinta ya tura ta can kusa da Karime, duk wnn abun Mumy na kallonsu amma bata ce komai ba, Karime ta kama hannun Heedayah bayan ta dau ruwan tace "Kayi hakuri Yallabai, bata sani bane" Ya hade rai yace "Ku fita gabana ke da ita" Karime ta bar wajen da sauri tana rike da hannun Heedayah dake rusa kuka, Sai da ta xo wuce Inda Mumy take, Mumy tace "Sai hakuri, ita tsiwa shi kuma saurin hannu, haka nan dai" Karime ta wuce part din Mami rike da Heedayah dake Shessheka, Sai da suka shiga ciki Mumy tace "Ai kaga irinta, ba dai ana ganin ni bala'e'iya bace, to gashi tun ba a je ko ina ba bakin yarinya ya fara budewa tana ma mutane fitsara, ai kadan kayi mata na so ka yi mugun xaneta ne, rashin idon ya ci uwarsa, wllh idan yarinyar nan ta samu waje duk taka ku xata yi a gidan nan, kuma ubanku baxai ce komai ba tunda idonsa ya rufe.... Kai kuma ka xo ka xauna ma mutane a parlor ka hanasu sakata da can kana xaman parlon nan ne ko neman magana???" Shi dai bai ce mata komai ba, can ya mike ya nufi kofa yace "Sai an dawo" daga haka ya fita parlon, Hajiya Sadiya tace "Ai kuma ya lalata mana shirin yau sai mu tari gaba...." Mumy da ranta ya kara baci tace "Ni fa da ba don idon da kika dinga min ba gabansa ma xan iya duk abinda xan yi, to tsoronsa nake ji ko ubansa xai min?? Wllh ke ce kika hanani" Sadiya tace "A'a ke dai, ai komai yana son sirri a rayuwa, ni sai naga kamar da wata manufa ya xauna parlon har ya ki fita siyo min kati, ni kinga ko godiyar katin ban masa ba ma, ke dai kawai ki sa ma ranki salama ba dai duk ana tare a gidan ba, kuma da alaman jawo hankalin yar kauyen nan ba abu bne me wuya, da ganinta xata so abun duniya ne sosaiiii, bbu abun hanxari a wannan lamarin mu bi komai a sannu...." Mumy tace "To ko da wata manufan ya xauna akwai yanda xai yi da ni ne balle ma bbu wata manufa kawai coincidence ne, ke baki ga irin jibgar da yyi mata ba ynxu bbu ko shakka bbu, da kyar idan hannuwanta basu tashi ba, ai ko kadan bai bada goyon bayan kawota da ubansa yyi ba, kawai dai kin san sa da xurfin ciki ne, Amma har ynxu ina lura ba wani shiri suke yi da uban ba duk kan wnn case din...." Hajiya Sadiya tace "To ke dai kiyi ga kyautata ma wnn yar kauyen, step by step xa mu yi ta abun mu bbu wanda xai xarge mu ko da kuwa alkali ne shi ba lauya ba, lkci daya farat din da kika so ayi da farko shi xai ja a xarge mu, amma kinga wnn bbu wanda xai kawo mu a rai" Mumy tace "Haka ne kam" Hajiya Sadiya ta mike tace "Yanxu dai xan wuce, gobe in sha Allahu xan xo da karfe sha daya" Mumy tace "Toh Allah ya kai mu din, ina nan ina jiran ki" Har bakin gate Mumy ta rakata sannan ta dawo tana jin ranta fari fat.... Karfe uku da 'yan mintuna Mami ta dawo gidan, Bbu kowa parlor ta shiga part dinta, Karime na xaune saman kujera tana ta kallon tashar Hausa ga dambun nama cikin leda a hannunta tana ci cike da jin ddi, Heedayah kuma na rakube kasa a xaune ta kwantar da kanta saman kujera, Karime ta mike da sauri ganin Mami tana mata sannu da xuwa ta amshi ledan hannunta da handbag dinta, duk idon Mami na kan Heedayah da ta mike da sauri jin shigowar Mami, Mami tace "Karime ya xa ki bar ta ita kadai xaune a kasa??" Cikin rawar Karime tace "Aa, sauka tayi Hajiya ai tare muke, naga kamar ta fi son kasan ne" Mami tace "Meye wnn a hannunki??" Karime ta hadiye abu da kyar tana kara tuna warning din Mumy tace "Aa ba wani abu bane, dama naje wanke filet ne sai na hadu da Sajida Hajiyar da take ma aiki ta bata dambun nama shine ta debar min a leda, har nace ta bari amma ta tilasta ni na amsa, shine na shigo na tsam ma Hinda sai na ke cin sauran yanxu" Mami tace "Bbu wani alaka tsakanin ki da kowa na gidan nan banda gaisuwa, kin ji me nace?" Karime tace "In sha Allahu Hajiya, dama ni ba ruwana da kowa tun safe muke nan xaune, to naje wanke wanke shine...." Mami bata tsaya kara saurarenta ba ta kama hannun Heedayah suka wuce ciki, Karime gabanta sai faduwa yake, ta isa a hankali jikin kofar dakin ta makale don jin me Mami xata ce mata..... Har dai ta gama labenta bata ji komai ba, ta koma ta xauna, nan ko tsoro ne ya kara shiganta da ta tuna Mami fa na iya Kiran Sajida kila ta tambayeta, nan ko ko maganan kirki bai hada su da Sajida ba tun jiya da ta xo, Mami ta gama sauya kayanta ta xauna gefen gado tana kallon Heedayah da tayi shiru tace "Me ya same ki daughter?" A hankali Heedayah tace "Mami wnn Mutumin ya dokeni a hannuna kuma ya ja min kunne...." Hawaye ta fara tana Shessheka, Da mamaki Mami tace "A ina ya gan ki?" Cikin kuka sosai tace "Xan sha ruwa, shine ya ja

Please Login or Register in order to submit comment