Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya mike yace "Na sallamesa" Kaka tace "Atoh, Kai baka je aikin bane yau?" Yace "Sai da yamma, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, Shureen ni dai na dawo nan gaskiya, matan Umaru kasheni suka so yi Allah bai yi ba, yau wani kwai suka ban da ya kusa kai ni lahira, shayin kuma sun cika masa kayan kamshi kamar dai buzaye... To ina dalili ga dai gidan Amadu" Shuraim dai bai ce komai ba, Kaka tace "Ka shigar min da akwatina daki dukiya ne a ciki, jama'ah Ina Deedayah, ga bredi na taho mata da shi da kwai...." Shuraim ya dau akwatin nata ya shigar da shi ciki, Mumy dai karfin hali kawai take don kiris ya rage hawaye ya xubo mata, kaka tace "Maryam tambaya nake Ina Deedayah?" Mumy ta dake tace "Wacece kuma Deedayah?" Kaka tace "Sabuwar 'yar Amadu mana...." Mumy ta wani tabe baki tace "Ayyo makauniya wai?" Kaka tace "Aa wannan kuma isgilanci kike ma ubangiji ba ruwana, ke kika halicceta da xaki kirata da makauniya, meye kuma makauniya idan ba isgilanci ba, ko ita ta xabar ma kanta makantar? Ni yanxu Ina take??" Duk wannan abun Karime na tsaye sai kallon kaka take, Mumy ta nuna mata Karime tace "Ga me kula da ita can" Kaka ta kalli Karime tace "Wacece kuma wnn sai naso take, ta kula da ita ko ta sa mata cuta, bakya wanka ne baiwar Allah?" Karime ta kasa cewa komai, Shuraim dai yyi murmushi ya nufi dakinsa, Kaka na kallon Karime tace "wa ya daukeki ki dinga kula da ita, Amadu ko wa? Tunda ita uwar rikon tata na samu labarin har ta fara fita aiki, Amadu ya fita ita ma ta fita...." Karime ta girgixa kai tace "Aa, Hajiyar ce ta daukeni..." kaka tace "Toh kuma sai kiyi ta kazanta kina naso, ba kya tashi da safe ki sa ruwa kiyi wanka ki dauko yar atamfar ki ko da kodadde ne ki saka kiyi fess da ke.. yanxu Ina yarinyar take?" Karime tace "Tana can daki kwance," Kaka tace "Wannan xama da ke ai sai cuta ya kama 'yar mutane..." Daga haka kaka ta nufi part din Mami tana cewa "Ita kuma mata daga tarewa sai fara fita aiki kamar auren banxa aka daura mata, ni ba ruwana" Zaune kaka ta ga Heedayah saman gado ta tashi tana mitsika ido, Kaka ta washe baki tace "Deedayah... Kin tashi" Heedayah ta juya da sauri tana duban Inda ta ji muryarta tace "Kaka" Kaka ta karaso tace "Ehh ni ce Deedayah, kin ga na dawo nan yanxu, kwai suka bani duk karni, kinji dalilin barin gidansu da nayi" Sakko mu je ga bredi da kwan na kawo maki kema ki ci ki ji, Heedayah ta sauka saman gadon kaka ta kama hannunta suka fita tana cewa "Ita dama ashe ba don ta kula da ke aka aurota ba, xata barma katuwar mata kazama ta sa maki wani cutan Amadu ya shiga uku...." Heedayah tace "Kaka tafiya xa ki yi da ni can gidanku?" Kaka tace "Wani gida? Ai na dawo nan sai kuma wani ikon Allah, abincin banxa fa suke bani a can gidan wllh Deedayah...." Mumy ta bi su da kallon gefen ido, Kaka ta tsaya tana rike da hannun Heedayah tace "Maryam ban fa karya ba, Kuma ni ba shayi xan sha ba gaskiya, ko me aka samu ni dai a bani in ci fisabilillahi" daga haka ta shige dakin da ta sauka tare da Heedayah, Mumy ta mike ta wuce bangarenta da sauri ta dau wayarta ta shiga Kiran Hajiya Sadiya, Hajiya Sadiya na dagawa Mumy ta sakar mata Kuka tace "Sadiya wllh shirinmu na ta rugujewa, yau dai ga wnn tsohuwa ta diro da katon akwati, ynxu haka ta dauke yarinyar ta shige da ita dakin da ta sauka, wato bbu ma ranan komawarta ne don sai kinga akwatin da ta kawo, ni dai wllh Sadiya hakurina ya fara karewa ji nake kamar in kashe yarinyar nan a gaban kowa a daureni kawai in huta, wnn yarinya har in mutu xan mance da ita kuwa a rayuwata, ta janyo min dariya a duniya, Duk fa dariya ake min a boye Sadiya" Sadiya tace "Ki kasheta kuma a daure ki Maryam, me aka yi kenan? Ke ina gaya maki gaggawa na shaidan ne kin kasa fahimta ko, meye na gaggawa abinda dai ana tare...." Mumy tace "Toh ke kina ga wnn tsohuwar da ta diro mana gida ynxu baxata kawo mana wani cikas ba?" Hajiya Sadiya tace "To ke meye ruwanki da ita? Wajenta yarinyar take da xai dame ki, Kinga xa mu yi waya anjima nayi bakuwa" daga haka ta katse wayar, Mumy ta xauna gefen gado tayi tagumi hawaye na sauka idonta.... Karime da Sajida tasa suka girka ma kaka shinkafa da miya ko damuwa da ynda suka yi girkin bata yi ba... Kaka na kallon Heedayah dake kwance gefenta tace "Toh sai kuma a siya maki?" Heedayah tace "Ehh mana, har kitso Ina yi ma gashin babyn nawa...." Kaka ta rike ha6a tace "A makancen?" Heedayah tace "Na'am" kaka tace "Toh yanxu a nan wani gantalalle ne xai siya maki wani baby ana xaune kalau??" Heedayah tace "Abba mana" Kaka ta ja kunnenta tace "Ke ce gantalalliya ba d'a na ba, shi Abban ne gantalalle?" Heedayah tace "Aa ai Mami ma xata siya min" Kaka tace "Atoh sai dai ita din, Amadu ba gantalalle bne..." Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo da sallama, kaka tace "Ko kuma Shureen ya siyo maki ba?" Heedayah tace "Waye shureen?" Kaka tace "Aa nima haka naji suna ce masa amma sunansa Aliyu..." Heedayah tace "Ae ban san shi ba" Kaka tace "Toh ai sanin nasa bashi da amfani don bashi da kyakkyawan alaka da mutane, mugun hali ne da shi, kin ga ai tun daxu da na xo bai shigo gaisheni ba sai ynxu..." Heedayah tace "Shi ma a nan gidan yake?" Kaka tace "To Ina xa sa? Ai gidan Ubansa ne nan din... da dai yyi aurene sai ya bar gidan, ni da Allah xai fito masa da mata ma yyi auren kowa ya huta don wannan shiru shirun da yake yi idan xamaninmu ne cewa xa ayi aure yake so" Shuraim dake tsaye bakin kofa ya hade rai yana kallon kaka da Heedayah bai dai ce masu komai ba, Heedayah tace "To ki ce masa ya siya min babyn Kaka, babba nake so" Kaka ta kalli Shuraim tace "Kaji kai Shuraim ko ba mai tsada bane ka dubi maraicinta ka siya mata domin Allah, ya fi tayi ta xama shiruuu kamar kurma..." Yace "Toh sai ta xo ta kwata ai" Heedayah na jin muryarsa ta matsa kusa da kaka a hankali bata kuma cewa komai ba, Kaka tace "Atoh, tunda ba ajiya ta ba mutane ba ai sai ta hakura da Babyn dama" Tsaki Shuraim yyi ya juya ya fita ya rufe dakin, murya can kasa Heedayah tace "Kaka ya wuce?" Kaka tace "To me xai min dama, ya wuce" Heedayah ta turo baki tace "Ni bana son sa" Har aka yi azahar Kaka na dakinta tare da Heedayah, bbu irin labarin da bata ba Heedayah ba wanda kwakwalwarta xai dauka da wanda ma baxai dauka ba, Tun tulin shinkafa da miyan da aka kawo mata da safe ba a sake kawo mata wani abincin ba.... Karfe uku da yan mintuna Mami ta dawo gida daga office, Karime na xaune kasan carpet a main parlor tana kallo, tun kiran da Mumy tayi mata dakinta bayan sun gama yi ma Kaka girki ita da Sajida sai lkcn ta sauko kasa ganin lkcn dawowar Mami yyi, ta mike da sauri daga xaunen da take tana yi ma Mami sannu da xuwa xata amshi jakar hannunta, Mami ta ki bata jakar tace "Ina Heedayan take?" Karime tace "Ai kina fita Hajiya sai ga wata da naji suna ce ma kaka ta xo gidan, to tun safe da ta shigo ta fita da ita xuwa wancan dakin bata yadda na je gunsu ba ma, ynxu haka suna ciki" Mami tace "Kaka?" Karime tace "Ehh haka naji suka kirata, kuma Sajida tace min Baabar Alhaji ce" Mami ta nufi dakin da kaka take ta yi sallama sannan ta bude ta shiga, Heedayah na xaune tana cin shinkafar da kaka ta xuba mata, ita kuma kaka na kara gyara kayan akwatinta don a birkice ta jerasu sbda sauri, Mami ta xauna nan kasa da murmushi fuskarta tace "Sannu Kaka" kaka tace "Yauwa sai yanxu kike dawowa kenan" Mami tace "Ehh yanxu na dawo" Kaka tace "Toh sannu da xuwa...." Heedayah dake washe baki jin muryar Mami tace "Mami kin siyo min Babyn" Kaka tace "Wani baby? Ki samu ma a samu lkcn kula da ke ba wani shegen baby ba, ke yanxu fisabilillahi Rakiya da kika hadata da wannan yar aiki duk wari ta kula da ita idan cuta ya kamata wa aka kai aka baro??" Mami bata ce komai ba tayi shiru tana kallonta, kaka tace "Kice min Amadu, to wllh xuwa nayi na samu mai aikin duk wari wai ita ce me kula da Deedayah, ki fa bar ganinta makauniya ki xata bata da galihu Rakiya, ke kina ganin fatan jikinta kinsan ba daga cikin wahala ta fito ba, gashi har abincin banxa na ga bata yrda ta ci sai na yan gayu, jikinta kwata kwata bai son wahala, wa ya sani ma ko daga kasar waje wani axxalumin ya sato ta ya wullota nan Nigeria da mugun abu yyi yawa?? Allah kadai yasan me yasa ya hadata da Amadu a titi, kema gashi ta albarkacin ta ya aure ki, wa yasani ko kin dade kina jin son sa a xuciyar ki sai gashi ta dalilin Deedayah ya aure ki..." Mami dai tayi murmushi tace "Ai nayi mata komai kafin in fita kaka, abincin rana kawai take bata sai abinda ba ka rasa ba, kuma baxai yiwu in dinga fita da ita aiki bane da tare xa mu dinga xuwa" Kaka tace "Toh ni dai na dawo da ita nan ba ruwana, sai in ga uban da xai dinga cutarta, mace duk wari kice ita xata kula da cin ta da shan ta, kishiyar ki kuma tun xuwana da safe har ynxu ban ga keyarta ba, duk wannan bai dameni ba tunda ke kin shigo, ynxu abinda nake so dake ga wayata ki kira min Junaidu don mun yi da shi xai xo yau kar yaje can bana nan, ba komai yasa na bar gidan ba sai kwai da suka kawo min duk karni" Mami ta amshi wayarta ta sa number Junaid sannan ta kira sa ta mika ma kaka, kaka na jin ya dauka ta washe baki tace "Junaidu... to yau dai gidan Amadu xaka taho na tattaro gaba daya na dawo nan" Junaid ya gaisheta yace "Toh shkkn kaka sai na xo" tace "Allah ya maka albarka ya kare ka sharrin makiya, ni ai ka fi min kowa" Murmushi kawai Junaid yyi ya amsa da Ameen sannan yyi mata sallama ya katse wayar, Mami na kallon Heedayah ta kama hannunta tace "Mu je ki canxa kaya" Kaka ta kalleta da sauri amma bata ce komai ba, Mami ta mike rike da Heedayah tace "Sai na shigo anjima kaka" Kaka ta bi su da kallo a hankali tace "Yauwa" Suna fita kaka ta mike ta fita ita ma ta nufi dakin Shuraim da sauri, yana fesa turare ta samesa a dakinsa da yake a gyara kamar dakin mace, ko ina fesss sai sanyin Ac, kaka ta xauna gefen gado ta fashe da kuka sosai, ya juya yana kallonta da mamaki, ganin irin kukan da take ya nufeta yace "Lafiya kaka? Me ya faru" Tana Shessheka tace "Mata ki fita tun safe ki bar yarinya Ina wahala da ita daga dawowa sai ki dauketa, Halan ita ta tsinto ma Amadu ita bani da labari ko kuma kanwar uwar yarinyar ce ita bamu sani ba, Yarinya muna xaune lafiya banda hira babu abinda muke yi tun safe ba irin labarin da bata bani ba, bbu irin labarin da ban bata ba kawai mata ta xo ta dauketa su wuce sbda bakin ciki...." Ta fashe da wani sabon kukan tana mika masa wayarta tace "Kira min Junaidu...."



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Shuraim ya dauke kai ya juya ya koma gaban mirror ya dau makullin motarsa, Kaka ta mike tace "Baxa ka kira min shi bane Shureen?" Ba tare da ya juyo ba yace "Ehh baxa a kira ba, waye kuma wani Junaid...." A fusace Kaka tace "Aa wllh kar ka xagar min shi don in ka xagesa ni ka zaga, kar ma ka fara wllh, ance maka bai fiye min kai ba sau dubu, Ina ruwana da kai dama idan ba kaddaran na haifi uban ka ba, wllh Junaidu ya gama min komai, kana xagin sa xaka xago ma kanka fitina, don ni ka xaga...." Ta koma ta xauna ta fashe da wani sabon kukan, bude kofa Shuraim yyi ya fice daga dakin ya kulle, kaka ta tsaida kukan da take a hankali tace "Ehh lallai d'an Amadu ya ci ganye..." Mikewa tayi ta bi bayansa fa fita. Mumy ce tsaye ta wajen flowers dake bayan gida, sbda shuke shuken flowers din wajen sai ya fi kama da garden, waya ne kare kunnenta cike da damuwa tace "Wllh kuwa Baffa, ni dai nayi ta bata hakuri ina kwantar mata da hankali, to kaga bbu ddi idan ban kira ka na sanar maka ba tunda cewa tayi kai ma ba son xamanta kake a gidan ba, kuma idan anyi duniya don manzon Allah ita da gidan har abada tunda xaman dole ku ke da ita, har mayar da ita na yi niyyar yi tace ta koma a wani matsayin?? Tunda har ynxu bbu wanda ya biyo ta ko ya kirata ya bata hakuri yace ta tashi su koma, to shine nake ga gwara ka taho da kanka ka kara bata hakuri sannan ku tafi don wllh ta dau xafi sosai, ni ban ma ta6a ganin bacin ranta irin na yau ba, kuka kuwa ta sha shi har ta gode Allah, xan kira barrister in sanar masa ta hanani wai ita xaman garin ma duk ya fita a kanta, gidan nawa ma ba xama xata yi ba, wai xa a iya wayan gari a ga bbu ita ta bar garin, to shine naga gwara in kira ka..." Baffa dake ta sauraranta ya sauke ajiyar xuciya yace "Shkkn Maryam nagode, sai na shigo anjima" Mumy tace "Babu komai, amma don Allah kar kace ni na kira ka, idan ma kace mata ni na kira ka kara baci ranta xai yi tace wato ma sai da na kiraka ka xo, da ban kira ba baxa ka xo ba, kuma idan xaka xo sai ka d'an taho mata da abinda kasan ta fi so" Baffa yace "In sha Allah, sai na xo" daga haka suka yi sallama, Mumy ta katse wayar tana wani murmushi, lkci daya ta sauke ajiyar xuciya, cikin compound din ta koma dai dai shigowar Junaid, har xata hade rai ganinsa ko me ta tuna kuma sai ta sake fuska sosai, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "Sannu da xuwa junaid, kwana biyu baka shigo ba" yace "Ehh naje Zaria ne" Mumy tace "Kuna da 'yan uwa can kenan" yace "Aa, naje wani uxuri ne a can" tace "Ayyo... To sannu da xuwa" yyi mata godiya sannan ya nufi entrance din shiga gidan, ta bi sa da wani kallo har ya shiga parlor... Sajida ce ke ta share share a parlor, ta mike tana gaishesa ya amsa yace "Wani dakin Kaka take?" Sajida ta nuna masa hanyar dakin, can ya nufa, yyi sallama bakin kofar, Kaka ta amsa da karfin ta, ya bude kofar ya shiga, kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya, Khadijah na jera mata tarkacenta na tsofaffi a gaban madubi, kofar bathroom a bude Karime na ciki tana ta faman wankewa, Junaid ya xauna nan kasan carpet yace "Sannu kaka, Ina yini" tana washe baki tace "Lfya lau Junaidu, sai ynxu??" Yace "Ehh kaka, ashe kin dawo nan..." Ta gyara xama tayi narai narai da ido tace "Baxan dawo ba Junaidu, kwai suka soya min duk karni gashi fari fatt sai uban albasa to hakan ba alamar an gaji da kai bne, to shine naga tun kafin sun barbadamin shinkafar bera gwara in gudu, ynxu hka ba wanda ya san ina nan, kilan suna can hankali tashe sun kai rahotu gidan 'yan sanda" Junaid da kansa ke kasa yana murmushi yace "Da dai kinyi hakuri Kaka...." Shiru tayi tana kallonsa can tace "Aa kar ka xama gantalalle kai ma mana, ae in kowa ya gaya min wnn mugun magana kai bai kamata ka gayan ba, inyi hakuri su cuceni su kasheni a banxa, sae kace Umaru kadai na haifa, ga dai Amadu, Aa ba ruwana, ni duk wanda yace in koma can gidan ma haushi na kawai yake ji ya tsaneni" Junaid ya ajiye ledan hannunsa yace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Kaka tace "Toh ka ga ynxu kayi magana, Kuma in sha Allahu alkhairin ne dama" murmushi kawai yake yi, kaka tayi kasa da murya tace "kana ji Junaidu, dama uwarka haka take ban sani ba?" Junaid ya daga kai yana kallonta, kaf ta kwashe labarin abinda Mami tayi mata ta sanar masa tana matsar kwalla, tace "A gantale fa ta barta gun mai aiki dake naso uwa an tuttula mata jarkan man gyada, ynxu hka fa ga Mai aikin can na sa ta wanke bandaki na, kuma ban amince ta shiga bandaki na ba sai da tayi wanka wllh, to mata daga dawowa kuma sai ki dauke min yarinya haka kawai, yini fa muka yi tare da yarinyar bbu wanda ya ji kanmu, muna ta hira fa in gaya maka" Junaid yace "Gaskiya bai kamata....." Kaka tace "Allah ya maka albarka, daga shigowa gida sai ta fara fito da mugun halinta da wuri wuri hka tun ba aje ko ina ba, ni sai nayi tunanin ma ko tasan uwar yarinyar ne wnn isa haka da ta nuna min...." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Xan je in dauko maki ita ynxu kaka" kaka tace "Amma fa kar kace nace maka komai, ba ruwana kar ta kullaceni, kawai dai kayi mata nasiha ta canxa halinta, wannan ba halin xaman gidan miji bane..." Ya mike still smiling yace "In sha Allah kaka, bari in je in dawo" Kaka tace "Allah maka albarka, ni dai gwara min kai a kan kowa ma a gidan nan" Kaka ta kalli Khadijah da sauri tace "Ke 'yar banxa kin gaishe sa ma kuwa da ya shigo? Ku dai 'ya yan Amadu baku da hali tirrr" turo baki Khadijah tayi tana ci gaba da abinda take, shi dai Junaid tuni ya fita ya rufe mata kofa, part din Mami ya nufa ya sameta xaune parlor ta daura kan Heedayah a cinyarta tana mata gyaran gashi, Heedayah ta mike xaune da sauri jin muryarsa, ya xauna saman kujera ya gaida Mami, Mami ta amsa tace "Na xata da Farida xa ku xo" yana kallon Heedayah yace "Aa, Uncle said she should stay" Mami tace "Okay, how are you" yace "Alhmdllh, ya aiki" tace "Mun gode Allah" Ya mike ya koma kujeran da suke ya xauna gefen Heedayah yana kallonta yace "How are you Heedayah" Ta wara ido tace "Fine, me yasa baka xo ba jiya har da shekaranjiya" Yace "Ae gani na xo yanxu" Ta laluba fuskarsa tace "To ka dinga xuwa kullum ka ji?" Mami dai ta tabe baki tana harhada kayan gyaran gashinta, Junaid na murmushi yace "Mami kaka tace a maido mata da Heedayah" Mami na kallonsa kafin tace komai ya kara da cewa "She wants her to be staying with her, bata ji dadin xuwa da kika yi kika dauketa ba daxu" Mami ta rike ha6a tace "Tohhh, ikon Allah" Junaid yace "Yess allow her ta koma wajen ta Mami, since ita ta bukata" Mami tace "Toh ai naga kamar wani nauyin Heedayah xata xame mata, baxata iya da tsirfan Heedayah ba" Junaid tace "Tunda ita ke son hakan ki bar mata kawai Mami" Mami tace "kai yaushe ta gaya maka haka?" Yace "Yanxu, har da kukan ta" Mami ta bude ido tace "Ahh to dauketa ka kai mata ita" Heedayah dake jin su tace "Mami wajen kaka xai kai ni?" Mami tace "Ehh" Heedayah tace "Amma xan dawo koh?" Mami tace "Ehh xa ki dawo" Junaid ya mike ya kama hannunta suka fita parlon, Mami ta bi su da kallo.... Mumy dake xaune parlor kamar dai ko da yaushe ta bi su da kallon gefen ido har suka wuce dakin kaka, Kaka na ganin Heedayah ta washe baki tace "Deedayah, ga kaza Junaidu ya kawo min, ai kin iya cin kai da kafar kaza koh?" Heedayah tace "A'a ni lap na iya ci" Kaka ta kalli Junaid tace "Meye lam kuma?" Yyi yar dariya yace "Cinya" Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "To sai ki kwata ai, ka ji min dai" Ya xaunar da ita gefen kaka yace "Kaka xan je Masallaci in dawo" Kaka tace "Toh yi maxa gashi can an fara kira" a hankali Heedayah tace "Are you coming back?" Ya juya yana kallonta yace "Yess" Yana fadin haka ya juya ya fita, Kaka tace "Toh ko wnn lafiyayyen turancin da kike ai ya ci kowa ma ya san ba daga gidan gantalallu kika fito ba, da kyar idan baki fi Shureen iya turancin ba don ni tunda nake ban ta6a jin ma yyi turancin ba, ga dai makaranta me tsada uban ya sa shi yana karami amma bai jin turanci, ko wnn kwam din da kowa ya sani baya ji" Heedayah ta kyalkyale da dariya tace "Kaka to sai in dinga koya masa mana" Kaka tace "Atoh, bari dai Allah ya shigo da shi mu ga ko xai yadda" Heedayah tace "Kaman ni yake?" Kaka tace "Ka ji ki wannan a haihuwar kaji ai yyi jika da ke, Shureen fa nace maki" Heedayah tace "Ni ban san shi ba" Kaka tace "Idan ya shigo xan Kai ki ki tattabasa ki ji" Heedayah tace "Toh" Tare Junaid ya shigo cikin gidan da Baffa, Baffa ya xauna parlor shi kuma ya shiga wajen kaka yace "Kaka Baffa ya xo" Kaka tace "Waye kuma Baffa, uban wa yace masa Ina nan, Kai ni dai gaskiya ana shiga hakkina, to me ya xo min kuma kamar dai wata yar karamar yarinya" Junaid na murmushi yace "Ya xo ne ya tabbatar nan din kika xo" Kaka ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana wllh" Bude kofar dakin aka yi sai ga Hajiya Amina da Hajiya Hauwa sun shigo da sallama, Kaka tace "Su waye wannan kuma" Hajiya Hauwa tace "Sannu kaka" Kaka tace "Yauwa, daga ina haka kamar an koro ku, ko daga anguwa ku ke?" Hajiya Amina tace "Daga gida muke kaka, mun xo biko...." Kaka tace "Yaji Maryam din ta kara yi ina gidan bani da labari??" Hajiya Hauwa tayi dariya tace "A'a kaka, kawai sai mu ka ga ba ki a gida" dai dai nan Mumy ta shigo dakin, kaka tace "Wllh na so shiga in maku sallama amma sai nayi tunanin bacci ku ke don na San ku da baccin safe, tashi nayi

Please Login or Register in order to submit comment