Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kaka tana washe baki mike tace "Toh" har parlonta ta kai kaka, ba a dau lkci ba aka cika gaban kaka da kayan karin kumallo, flask din ruwan Lipton me kamshi, soyayyen dankali da kwai da plantain, katon bread, sai wainar shinkafa da lafiyayyen taushe, ga farfesun kayan ciki a gefe, Kaka na kallon masu aikin dake ta jera mata abincin tace "Babu darduma in sauka kasa??" karamin carpet me laushi suka shimfida mata ta sauko kasa bayan ta cire Hijabin ta, komai sai da kaka ta diba ta ci a abincin, sai da taji tayi nak murya can kasa tace "Toh ko nan nace xan dawo da xama ai bbu me ce min komai tunda an xama daya yanxu..." Sallama aka yi kofar parlon Kaka ta amsa wani dattijjo da baxai wuce 65 ba ya shigo parlon, kasa ya xauna yace "Sannu da xuwa Baaba" Kaka na washe baki tace "Sannu, kai ne kawun Junaidun?" Yace "Ehh nine, Ina kwana" Kaka ta gyara xama tace "Lafiya lau, yau dai nace bari in xo in ganka ka gan ni, idan na biye ta uwar Junaidu baxa ayi xumuncin ba ma, kasan yaran ynxu basu san amfanin xumunci ba" Yyi dariya yace "Gaskiya ne Baaba, to ya ku ka baro mutan gidan?" Tace "Lafiya lau, ko sanin na fito ma basu yi ba, nace inyi maxa in xo kar ka fita, tunda shi Amadu na ga karfe takwas xuwa tara yake ficewa" Yace "Wannan gaskiya ne" Kaka tace "Toh bayan xumunci kuma a gaskiya har da alfarma na xo nema a gun ka" Ya xauna da kyau yace "Toh ina sauraron ki Baaba" Tace "Ba wani abu bane d'an nan, jikana Aliyu na xo nema ma auren 'yar ka, wato Farida, kaga dai Aliyu ni na haifi ubansa Amadu, tunda nake ban ta6a ganin yaro da ya tashi bashi da matsala irin Aliyu ba, bbu ruwansa da kowa, ba shi da abokin fada, kai in takaice maka shi ba me magana bane ma, to shine na ya6a da hankalin farida tunda ta xo kuma ta xauna dakina, komai ita ke min wllh, ko nayi laifi da nayi wnn tunanin bawan Allah, amma dai ya ma sunan ka tukun" Yace "Sunana Aminu" Kaka tace "Toh ai sunan babana kenan, Allah sarki, to yanxu ya kaga..." Yace "Batu ne mai kyau wannan Baaba, amma sai dai Farida ynxu karatu take wllh" Kaka tace "Oh oh Allah, karatu na hana aure ne wai dama? Ku me yasa ku ka bari boko yyi maku kaca kaca haka, Shi kansa Amadun fa haka yace min, meye a ciki idan anyi auren ta ci gaba da karatun ta, ynxu shekararta nawa ma dai tukun?" Yace "Bata cika sha shidda ba ma" Kaka tace "Shine tayi girma haka? Toh kaga kuwa ai aurar da ita shine rufin asirin mu da ku, kaga dai takanas na taso da kafafuwana na sameka a gida sbda alkhairin da nake nema da ku, a gaskiya idan kace min A'a raina xai baci Aminu, da girmana na taho wajenka.... Kuma da Rakiya ta san gidan banxa ne gidan Amadu ai baxa ta shigo ba...." Yana murmushi yace "Gaskiya ne Baaba, in sha Allahu tunda ba fin karfina alfarmar da kika xo nema yyi ba xanyi bakin kokarin ganin komai ya tafi yanda kike so, amma sai Farida ta gama secondary in sha Allah" Kaka tace "Toh tunda dai ka amsa ai shkkn, kwana nawa ne xa a ga ta gama sakandarin, shi ma massers dinsa yake yi a Zaria, kaga sai su gama lkci daya kenan, bari anjima shi xan ma kira ya mayar da ni gida sai ka gansa, yana nan ko yatsa ka sa masa a hannu baxai ciza ba, yaron kirki me girmama na gaba da shi, Kai ni ko rashin kunya na jika da kakan nan ma ni bai ta6a min ba, tamkar uwarsa haka yake min biyayya" Shi dai murmushi kawai yake yace "Toh shkkn Baaba xan fita wajen aiki sai na dawo, ai kina nan?" Tace "Aa ina nan kilan har ka dawo, yanxu fa na xo" yace "Toh maa sha Allah, sai anjima" tace "Allah maka albarka" ya amsa da Ameen ya fita. Yana fita wayar kaka ya fara kara ta fiddo a jaka da sauri, da yake ta san Inda ake dannawa ta danna ta kai kunne, Muryar Mami taji, kaka tace "Ke ba fa wani waje naje ba, gidan ta salla na tafi, anjima in sha Allahu xan dawo" Mami tace "Toh shkkn, amma ba sallama kaka" Kaka tace "Ehh to da yake tafiyar ta gaggawa ce, anjima dai xan dawo in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya dawo da ke lafiya" kaka tace "Ameen" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta jawo sauran farfesunta tana lasa. Har aka yi Magrib Kaka na gidan Baffansu Junaid, Matarsa kuwa Hajiya Zulaiha bata bar Kaka ita kadai ba, tare suka yini, a xamansu na yan awannin nan abinda kaka ta manta ne kawai bata gaya mata ba, tarihi iri iri, Wanda ya kamata da Wanda bai kamata ba, tun mijinta na da rai har sanda ya rasu, amma ko da wasa kaka bata gaya mata halin Mumy ba, Hajiya Zulaiha dake yanka ma kaka kankana bayan anyi sllhn Magrib tace "Na kirasa yana hanya ynxu Mama" Kaka tace "Toh kinsan shi xai mayarda ni gida kar in gigita 'ya yana suyi xaton 6ata nayi shi sa na damu" Hajiya Zulaiha tayi dariya tace "Kila yana can gun budurwar sa tun da kika ga har war haka bai shigo ba" Kaka tace "Au, yana da budurwa kenan?" Hajiya Zulaiha na dariya tace "Kwarai kuwa" Kaka tace "ikon Allah, ko da yake ga Shureen ma Ina kokarin ganin yayi aure nan da 'yan watanni balle Junaidu, da kyar idan bai girmi Shureen ba ma" Hajiya Zulaiha tace "Lallai kam" Kaka tace "Ko da yake ga Farida ma naji shekarunta ba wasu shekaru bane amma duk ta balaga, kusan sa'ar Khadijahn Amadu ce fa, Ita kuma Rabi'ah sa'ar Deedayah Ina jin, don duk kwailaye ne" Hajiya Zulaiha dai tayi dariya ta ajiye ma kaka kankanan tace "Bari in je inyi sllh Mama, amma da kawai kiyi kwanan ki a nan Mama" Kaka tace "A'a ba mutunci gare su Amadu ba sai su iya min fada ba ruwana, bari dai in tafi ba dai na ga gida ba" Hajiya Zulaiha tace "Toh shkkn Mama" daga haka ta fita parlon.... Tana fita da minti sha biyar Junaid ya shigo, kaka tace "Ashe kana da budurwa Junaidu, yanxu matar kawunka ke ce min tadi ka tafi" yace "Aa gidan abokina nake" tace "Au, to in tashi mu tafi kada su Amadu su yi ta nemana koh?" Yace "To mu je kaka, ai kin ci abinci" Kaka tace "Idan ma nace ban ci ba, ba sai Allah ya kama ni ba, Tuwo ce fa malmala uku aka saka min ga miyar kubewa duk nama da Ganda ga kifi, ga kuma lemo me sanyi... To ina xan samu haka gidan Amadu?? Gaskiya matar nan ta san mutunci, baka ga ba wllh sai ji take da ni, komai ta rarumo ta kawo min, daxu da rana har kwadon zogala ta min bayan shinkafa da miya da uban nama da ta xubo min, ni dai gaskiya an karrama ni a gidan nan, ai Rakiya sai dai ince Allah yyi mata albarka kawai, danginta sun san mutunci kam" Murmushi kawai Junaid yyi yace "Idan kin gama shiryawa Ina parlor kaka" Kaka tace "Toh, d'an Albarka" Sai bayan kusan minti ashirin kaka ta sakko da handbag dinta, tana kallon yan matan gidan guda uku dake xaune parlor tace "Toh ko Sudess ma idan ya samu daya daga cikin wa ennan bai gode ba, ynda yan mata ke wahala ynxu...." Har parlon Baffan Junaid kaka ta shiga, yace "Aa Baaba ai na xata kwana xa kiyi a nan" tace "Aa su Amadu xa su min fada" Yace "Ikon Allah, toh Junaid xai maida ki amma" tace "Eh yana jirana ma yanxu haka" mikewa yyi yace "Toh Ina xuwa Baaba" yashiga dakinsa sai gashi ya fito ya mika mata dubu goma da ladabi yace "A siya goro Baaba" Kaka ta amsa ta saka a jaka tace "A'aaahh ayi haka d'an nan, ai da ka bar shi wllh, toh Allah yayi maka albarka, nagode ka ji" yace "Godiya ya tabbata ga Allah" rakata yyi har xuwa parking space tare da Hajiya Zulaiha da ta bata atamfa da turarurruka, tayi ta daga masu hannu tana washe baki har motar ya fita gidan, bayan sun hau titi tace "Gidan ma babu wahalan ganewa kaga idan xan dawo baxan sha wahala ba koh" Yace "Haka ne kaka" Tare Junaid da Kaka suka shiga parlor, Rabi'ah dake kwance parlon tana kallon Tv tace "Sannu da dawowa kaka" kaka tace "Yauwa.... Junaidu tafi ka dauko min Deedayah ga sauran nama na kulle mata a leda" yace "Toh" daga haka ya nufi part din Maminsa, Rabi'ah tace "toh mu fa?" Kaka da ta nufi dakinta tace "Uwar me na hada dake banda dai ke jikata ce, idan Maryam ce ko Amadu kya gaishesu a kwance?" Daga haka ta shige dakinta. Mami na kallon Junaid bayan ya gaisheta tace "Daga ina ku ke?" Yace "Gidan Baffanmu" Mami tace "Baffan ku? Kai da kakan?" Yyi yar dariya yace "Da sassafe ta kirani wai in xo in kaita" Mami ta dinga kallonsa da mugun mamaki tace "Sai ka kai ta?" Yace "To meye a ciki Mami?" Mami ta mike tace "Why didn't you call and ask for my opinion Junaid???" yyi kasa da kai yace "Mami naga ba wani abu bane, ai kowa ya san tsoho..." Xata yi magana aka bude kofar, shiru tayi kaka ta shigo tace "Ina Deedayan?" Mami tace "Sannu da xuwa kaka" Kaka tace "Yauwa Ina Deedayah ga nama na kullo mata" Mami tace "Suna parlon Barrister" Kaka tace "Kai Junaidu tafi ka dauko min ita, Ina iya shiga parlon yanxu Amadu ya rufeni da bala'i" Mikewa yyi ya fita parlon, Kaka tace "Wllh anguwa naje ke dai Rakiya, mutum yyi ta xaman gida kamar bashi da jama'ah" daga haka ta fita ta bi bayan Junaid da sauri, tun kan ya shiga parlon Abba ta tsayar da shi tayi kasa da murya tace "Kar ka gaya masu daga Inda muke, cewa kawai xakayi a bakin titi ka ganni ka dauko ni, har ita Rakiyan kar ka gaya mata kaji" Yana murmurshin karfin hali yace "Toh" daga haka ya shiga parlon ta koma nata dakin.... Washegari Sunday da safe Shuraim ya shiga gaida Abbansa, Abba na aiki system dinsa ya amsa yace "Anjima xaka ajiye Farida makaranta" Ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Before then, xan maka transfer ku je tare tayi shopping, da yamma sai ka ajiye ta schl din" yyi kasa da kai yace "Toh" Abba yace "That's it, Kai yaushe xaka wuce Zarian?" Yace "Gobe da safe" Abba yace "Allah ya kai mu" mikewa yyi, ya ma Abbansa sallama ya fita, direct dakin kaka ya nufa, Kaka na ta gyara kayan da ta binciko a press din dakin, Heedayah kuma na kwance saman gado tana cin naman da kaka ta kawo mata, kaka kuma na bata labarin irin abubuwan da ta ci a inda taje jiya, Heedayah tace "Toh baki gaya min sunan wajen ba...." Kaka tace "Toh wai ina ruwanki, ke dai kawai ki bari, akwai abinci a gidan" Heedayah ta tallabi chin dinta tace "Toh shine ni baki je da ni ba?" Kaka tace "Ai kinsan a boye na bar gidan shi yasa, amma ba gashi na kullo maki sauran nama ba" Shuraim ya bude kofar ya shigo dakin, kaka tayi tsit da bakinta tana ci gaba da linkin ta, Murya can kasa Heedayah tace "Kaka waye?" Kaka tace "Iska ce ta turo kofa" Heedayah ta turo baki tace "Na xata wnn Shureen din nan ne...." Kaka tace "Shureen kuma, me xai shigo ya min, baki ga tun wayewar gari bai ko shigo gaidani ba" Heedayah tace "To kaka wai me yasa yake yi ma mutane mugunta? Ni fa bana son sa" Kaka tace "Haka nan Allah ya halicce sa, Kuma ya xa ayi ki so sa, ke da baki hada komai da shi ba...." Heedayah dai tayi shiru sbda kamshin turare da ta fara ji, kaka tace "Tun yana karami duk da baya magana haka yake narkan 'ya yan mutane, yyi ta cin xali, uwarsa kuma tayi ta goyon bayansa" Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ya kika yi shiru kuma" Heedayah ta turo baki a hankali tace "Bayan yana dakin xaki ce min baya nan" Kaka ta kyalkyale da dariya, Shuraim da ya wani hade rai yana kallon Heedayah yayi kwafa ya juya ya fice, Heedayah dai bata ce komai ba ta wani cinno baki, kaka tace "Atoh, yarinya sai fitsara da gulma wai don ma bbu ido..." Da rana Farida ba don ranta ya so ba ta shirya xa su je shopping kamar yanda ita ma Abba ya gaya mata, Heedayah ma ta sa Hijab dinta don tare Mami tace su je, can kofar gida yyi parking don ma kar Mumy tayi noticing xa su fita, Farida Ta bude ma Heedayah back seat tana rike da hannunta ta shiga, ita kuma ta shiga gaba, ko kallonsu bai yi ba ya tada motar suka bar layin. Wani shopping mall xai shiga Farida tace "A na gaban nake yi shopping, nan ba dukka abinda nake so suke da shi ba" Ya wani daure fuska bai dai ce komai ba ya shiga yyi parking ya kashe motar, Farida ta dauke kai ta ta6e baki ta bude motar ta sauka, ta bude side din Heedayah ta kama hannunta ta sauka, ta gefen ido yake kallon Heedayah da Hijab dinta ya wuce gwiwa da kadan, sae pink wandon dake jikinta amma bai kai ankle dinta ba, Farida xata rike hannunta su wuce ciki ya fixge hannun yace "Wa xata bi a hakan???" Farida ta kalli Heedayah daga sama har kasa, ya bude bayan motar yace "Maida ta ciki" Farida tace "But there is nothing wrong with her dressing, I dressed same also" Da kansa ya mayar da Heedayah da ta fashe da kuka cikin motar ya rufe, Farida ta rungume hannunta ta hade rai ta jingina da motar tace "Ni na ma fasa shopping din" Wani kallo yyi mata yace "Gaura maki Mari xan yi idan baki shiga mun wuce ba" Ta fashe da kuka tace "Toh why will u lock her all alone cikin motar, don't you know there is heat, ni baxan bar ta ita kadai ba" Atm card dinsa ya ciro ya mika mata still frowning his face yace "Double five, double zero.... Tafi kiyi shopping dinki ke kadai" Ta leka motar tace "Toh xaka tsaya da ita ne" Kin bata amsa yyi, ta amshi ATM card din ya bude maxaunin driver ya shiga ya xauna, A hankali Farida ta nufi cikin mart din. Heedayah dai ta daina kukan da take sai share idonta take, ta gaban madubin motar yake kallonta, bayan kusan minti goma jin shirun yyi yawa ta matsa a hankali kusa da driver seat ta sa hannu xata lalabu ko akwai mutum a nan, Kirjinsa ta ta6a ta janye hannunta da sauri ta koma ta xauna tana turo baki... Bayan wani 15 mins din sai ga Farida ta fito da labourer dake dauke da ledojin kayanta, Bude booth yyi kafin su karaso, mutum ya saka kayan gaba daya a ciki ta bude jakarta ta ciro kudi ta basa sannan ta bude back seat ta shiga ta rufe tana kallon Heedayah tace "Didi na siyo maki chocolates and Biscuits har da teddy..." Heedayah ta wara ido ta kamo hannunta tace "Thanks Farida" Ya d'an ta6e baki ya tada motar yayi reverse ya bar shopping mall din. Karfe biyar saura Farida ta gama shirin komawa makaranta, Heedayah har da hawayenta daga Inda ta xauna ta takure kanta, Mami da ta ji tausayinta sosai tace "Ku tafi tare Farida, sai ya dawo da ita" Farida da duk jikinta yyi sanyi ta kama hannun Heedayah suka fita parlon xuwa dakin Kaka su yi mata sallama, Shuraim na xaune main parlor da makullin motarsa cox Mumy bata gidan, Ya bi su da kallo yace "If she is not changing that clothe she shouldn't bother entering my car..." Farida ta juya tana kallonsa don tun da take bata ta6a jin yyi magana me tsayi hka ba, ta dauke kai ta ta6e baki, Heedayah ta rike hannun Farida sosai kamar xata yi kuka tace "Pls kice Mami ta bani dogon Hijab in sa" Farida ta d'an ja tsaki suka koma bangaren Mami, Mami na kallon Heedayah daga sama har kasa tace "Does he have any business with her dressing, ko ya siya mata Hijabs ne? Or is he stupid??" Farida dai bata ce komai ba ta dauko ma Heedayah wani Hijab din har kasa ta saka sannan tayi ma Mami sallama suka fita, Kaka har da kwallarta, ta daure ma Farida cin cin da bai fi kwaya shidda ba a leda ta mika mata tana cewa "Ashe baki nan xa a kai Deedayah India" Farida tace "Kilan muna jarabawa lkcn" Kaka tace "Toh ai shkkn, Amadu yace min nan da sati uku ne, ga kayana har na hada" Farida tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka ta dauko maltina daya ta kara mata, ta rakasu har bakin motar Shuraim, tana kallon Shuraim tace "Toh ko in dauko gyale mu tafi tare Shureen?" Ya gyara xama yace "Ehh" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya tada motarsa ya fice daga gidan, Heedayah ta rufe fuskarta a Hijab tana dariya a hankali, Farida kuwa sai hararansa take.... Suna Isa makarantar Shuraim yyi parking, tsadaddun motoci ne iri iri an kawo students, Farida ta kamo hannun Heedayah tace "Till I come back Didi..." hawaye ya kawo fararen idanuwan Heedayah, ta madubi Shuraim ke kallonsa, Jikin Farida yyi sanyi tace "Baxan dade ba xa mu yi hutu...." Heedayah ta fashe da kuka sosai ta daura kanta saman jikin Farida, Shuraim ya hade rai yace "Malama sauka ki bude booth ki sauke kayan ki" Ta galla masa wani harara tana share idonta ta sauka motar, sauka yyi shi ma don sauke mata kayan don ya san sun mata nauyi, Heedayah na jin haka ita ma ta bude motar ta sauka, Tsaye yake jikin black ride dinsa ya rungume hannu idonsa sanye da bakin space, he looks so gentle and calm, dai dai saukowar Heedayah, a hankali ya cire Glasses din idonsa yana kallonta, Shuraim kawai gani yyi ta ci karo da daya daga jakan Farida da ya sauke kasa Farida kuma tana gun booth tana fiddo kananun ledojin, kafin ya karasa ya riketa tuni ta fadi kasa, shi kansa Mutumin har ya taho da sauri kafin ta kai kasa ganin Shuraim sai kuma ya tsaya cak, Shuraim ya dagota yace "Wa yace ki sakko?" Ta fashe da kuka tana yarfe hannunta tace "Wayyo na buge kafana, and there is sand in my eyes" Tuni Farida ta durkusa kusa da su tana ma Heedayah sannu, da ma sauran mutanen wajen, Bude idon Shuraim yyi, yyi blowing mata iska gently, ganin yanda ake kallonsa kawai ya dagata ya bude back seat ya sa ta ciki, ya karasa sauke ma Farida kaya yace "That's all" daga haka ya bude back seat din ya shiga yana kallon Heedayah dake ta murxa idonta matsawa yyi kusa da ita ya dafa forehead dinta yana kallon cikin idon, ta kauda kanta kamar xata yi kuka tace "Ya daina" Saketa yyi still looking at her eyes.... Tuni Mutumin ya shiga mota ya mance abinda ya kawosa bakin makarantar ya tada motarsa yana kallon motar Shuraim ta madubi, Shuraim ya daga hijab dinta ya kalli kafarta ya ga just little bruises ne a farin kneel dinta, Bude motar yayi ya sauka ya koma driver seat, ya tada motar yana fara tafiya Mutumin ya bi bayansa......


*pls fans masu son min magana su dinga typing instead of voice note, cox listening to voice note is stressful wllh, idan typing ne cikin few seconds mutum xai karanta yyi replying nn take, but voice note yana cin time when they are other messages to reply to, thanks for understanding*


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


Shuraim bai yi wani nisa ba ya kula da motar bayansa dake bin sa, slowly ya dinga tafiya to see idan motar xai yi overtaking dinsa ya wuce, but sai ya ga motar ya ki yin hakan sae ma rage nasa tafiyar da yyi shi ma, Shuraim ya samu waje yyi parking har sannan yana kallon motar ta madubi, Mutumin dake cikin motar dake ta lura da Shuraim shi ma kuma ya san Shuraim ya gano yana bin sa ne kawai yyi wucewarsa bai tsaya ba, Shuraim ya bi motar da kallo har da plate number din motar, juyawa yyi ya kalli Heedayah dake xaune bayan motar, she looks so sad kiris ya rage ta fashe da kuka daga ynda tayi da fuskarta, dauke kansa yyi ga mamakinsa har sannan motar bai bace masa ba, sbda a hankali me motar ke tafiya kan less busy road din, Shuraim ya kalli layin dake gefensa kawai ya karya kan motar ya shiga layin.... Sai kusan Magrib Shuraim ya isa gida, a hankali yake tafiya ganin motar Mumy dake tsaye bakin gate tana jiran me gadi ya bude gate din, sae da ta shiga snn yyi parking gefen flowers dake gaban gate din ya kashe motarsa, Mai gadi na ganin baxai shiga gidan da motarsa ba ya kulle gate din, Shuraim ya juya yana kallon Heedayah dake bacci bayan motar, sauka yyi motar ya kulle ya nufi cikin gidan, tsaye ya ga Mumy alamar shigowarsa take jira, ya karasa Inda take ya gaisheta tace "Daga ina kke da magariban nan" Yace "Asibiti" tace "Ohk, goben xaka tafi Zarian?" Yace "In sha Allah" tace "Toh nima xan je Zarian gobe, amma bance ka gaya ma kowa ba, karfe nawa xaka fita?" Yace "Takwas..." Tace "Toh kayi hakuri ka bari karfe tara, kafin nan Abbanku ya fita" Shi dai kallonta kawai yake don ya san basu da 'yan uwa a Zaria, can yace "Me xaki je ki yi a Zaria Mumy?" Mumy tace "Yar Hajiya Sadiya ba can take aure ba, to ta haihu gobe suna, ko barka ban je ba, kuma idan na gaya ma Barrister ba lallai ya yrda ba, ni ko Sadiya ai ta wuce haka a wajena" Shuraim yace "Aa da dai ki fara sanar ma Abba Mumy" Mumy ta daure fuska tace "Toh ban yi niyya ba" Bai kuma cewa komai ba ta juya ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo har ta shiga parlon snn ya juya ya koma waje, Bude back seat yyi Heedayah ta bude ido da sauri, hannunta ya kama ya saukar da ita daga cikin motar ya kulle motarsa, har da xai mika ma Mai gadi hannunta ya kai ta ciki sai kuma kalli cikin compound din ya shiga yana rike da hannunta, yana isa balcony ya bude kofar parlon yana kallon ciki, bbu kowa hakan yasa ya shiga parlon da ita ya kai ta har kofar dakin kaka sannan ya juya ya fita xuwa masallaci, Kaka da ta fito daga bandaki tayi alwala tace "Waye wnn?" Heedayah tace "Ni ce" Kaka tace "Toh ai na ganki, sai yanxu ku ka dawo kai faridan makaranta?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "To ina Shureen din?" Heedayah tace "Nima ban sani ba, ya wuce" Kaka ta ta6e baki tace "Toh me yasa kika yo min nan, Rakiyar bata nan ne" Heedayah ta turo baki tace "Toh ai shine ya kawo ni" Kaka tace "Toh ni dai na gyara dakina na share, na sa turaren wuta, gadon ma yau ko hawa ban yi ba tun da garin Allah ya waye" Heedayah ta turo baki ta juya tana laluba hanya

Please Login or Register in order to submit comment